Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yarima
hulkas ya dubi basmar yace kai kuwa yaya akayi ka gane haka
basmar yayi murmushi yace ai na lura ne da duk irin yanayinka
kuma da irin tsananin farin cikin da kake ciki a yau wanda ke nuni da cewar baka taba samun sakewa ba irin na yau
sa adda hulkas yaji haka sai yayi ajiyar zuciya cikin alamun takaici yace ai ni nan da kake ganina
in ba don albarkacin wannan
tafiya da mukayi zuwa wannan gari naku ban taba ma fita
daga cikin gidan sarautarmu ba saboda mahaifina baya
son naje ko ina dare da rana muna tare babu abinda yake rabamu saboda tsananin shakuwar
da ke tsakaninmu.
Koda jin wannan batu sai yarima basmar ya cika
da tsananin mamaki yace
ai kuwa rayuwarka da tawa tazo kusan iri daya domin
nima haka mahaifina ya kafa min takunkumin fita baya barina naje ko ina amma sai dana shammaceshi ya zamana cewa ina shiga har cikin gari ba tare da kowa ya sani ba a yanzu hakama akwai wata jarumar yarinya da na
hadu da ita wacce tayi matukar burgeni kuma ta bani tsoro domin ban taba ganin karamar yarinya mai jarumtaka kamarta ba don a gabana tayi gumurzu da karti
goma duk ta bazar dasu a kasa da karfin damtsenta ba makami
ina mai tabbatar maka da cewa shekarunta ba zasu fi namu ba wato ina nufin sa'armu ce
koda yarima basmar yazo nan a zancensa sai hulkas ya bushe
da dariya yace haba yakai abokina wannan kuma wace irin
tatsuniya ce haka kazo min da ita ai wannan kawai almara ce kazo mini da ita sai dai idan harkar tsafi ce amma ba zahiri ba
koda jin haka sai yarima basmar ya kama yin
rantse rantse yana cewa lallai al amarin wannan yarinya ba tsafi bane
yarima hulkas yace idan har kana son na yadda da wannan labari daka bani sai dai ka kaini naga yarin yar a zahiri da
Idanuna yanzu ta yaya kake ganin zamu iya fita
daga cikin wannan gidan sarauta taku harmu shiga
cikin gari muje ka kaini inda wannan yarinya take?
Sa adda yarima basmar yaji wannan tambaya sai yayi murmushi yace ai wannan mai sauki ne kamar cire silin gashi daga cikin tandun mai muddin zaka iya
yin duk abinda zanyi
hulkas yace ai yanzu tuni zuciyata ta kwadaitu
da son ganin wannan yarinya da ka bani labari kuma raina ya kagu damu tafi can
inda take saboda a rayuwata babu abinda nake so sama da jarumtaka da iya yaki
gashi kuma ko sau daya ban taba jarraba yin suba kai in dai wannan labari daka bani
gaskiya ne zan iya biyan wannan yarinya dinare dubu domin ta koya mini yaki
da jarumtaka ina mai rokonka daka tashi mu
hanzarta shiga cikin wannan gari naku koda jin haka sai yarima basmar ya
kama hannun yarima hulkas suka duro kasa tare daga kan lilon suka ruga izuwa wani bangare
daban dake gidan
saida sukayi gudu na tsawon yan dakiku masu yawa
sannan suka iso karshen gidan sarautar suka shiga cikin wani kwararo wanda ya kaisu inda matattakalar shaddar gidan sarautar take gaba daya
da zuwa suka iske wadansu wulakantattun bayi suna ta debo kashi suna lodashi a cikin wani amalanke
koda bayin sukaga shigowar yarima basmar tare da hulkas sai bayin suka zube kasa gaba dayansu suka gaida basmar
a lokacin da doyin kashin ya ishi hulkas ya kama kau da kai yana toshe hancinsa shi kuwa basmar ko kadan bai damu ba
ga dukkan alamu ma ya saba da zuwa wajan
basmar ya dubi shugaban bayin yace yau mu biyu ne
nida abokina
ina son ku fitar damu zuwa cikin gari kamar yadda kuka saba a sirrance
koda jin haka sai shugaban yayi dariya yace an gama ya shugabana bamu ladan aikinmu kamar yadda ka saba
cikin alamun damuwa yarima basmar ya ce yau na sha afa ban taho da shiri ba ama ai kasan ba zanyi muku wasa ba
gobe zan baku ladanku
gama fadin hakan keda wuya sai suka jiyo takun sawun dakarun dake kulle dasu cikin hanzari bayin suka boye su yarima hulkas
a karkashin amalanken da suke loda kashin
faruwar hakan keda wuya sai ga wadansu dakaru biyu
sun shigo wajan rike da bulalai da shigowarsu sai suka
tsaya a gaban amalanken dai dai inda su yarima basmar suke har daya daga cikinsu ya take danyatsan hulkas guda da katon
takalminsa har hulkas zaiyi ihu sai yarima basmar yayi sauri ya toshe masa baki da tafin
hannunsa
daya daga cikin dakarun ya dubi shugaban bayin ya daka masa tsawa yace a cikinku waye mai murya irin ta yara
tabbas daga can nesa na jiyo muryar yaro a nan
har shugaban bayi ya budi baki zaice wani abu sai wani daga cikin yaransa ya tari numfashinsa yayi magana
da karamar murya iri daya sak da ta yarima basmar al amarin da yayi matukar baiwa kowa mamaki kenan
koda jin hakan sai dakarun suka kyalkyale da dariya wanda yayi magana da farko ya
dubi bawan da yayi muryar yarima basmar yace tabbas kana da hikima watarana zan gabatar
dakai gaban sarki domin ka debe mana kewa
koda gama fadin hakan sai dakaru biyu suka juya suka fice daga cikin wannan kwararo
da ake aikin kashi
fitarsu keda wuya sai bayin suka sauko buhuhuna da suka dura kashi a ciki suka zura yarima basmar da hulkas
a kansu suka kulle bakin buhuhunan amma sai suka yi dabaara suka farka buhun a dai dai kan fuskokinsu
yadda zasu iya shakar numfashi duk da haka sai da yarima hulkas ya kama kakarin amai
saboda doyin kashi gashi an labta wadansu buhuhunan a samansu nauyi ya damesu
nan take yarima hulkas yaji kwalla ta cika masa idanu yace oh duniya juyi
juyi kwado ya fada ruwan zafi wai yau ni yarima hulkas
nine a cikin buhun kashi saboda kawai ina son shiga cikin gari naga abin al ajabi
tabbas neman duniya ba wasa bane kuma ba a samunta cikin sauki sai ansha wuya yarima hulkas na cikin yin wannan tunani ne yaji an ja amalamken da suke kai anyi gaba dasu
nan fa akayi ta tafiya dasu ana wucewa ta cikin
sako sako da lungu lungu na gidan sarautar har sai
da aka wuce dasu ta cikin kofofi shida
duk kofar da aka zo sai sun tsaya an caje buhuhunan kashin
wani lokacin ma sai dakaru sun caccaka tsinin
takobi a cikin buhuhhunan saboda zargin ko an
sato wani abu a ciki
in ba don Allah ya kiyaye ba saura kiris takobin wani
badakare ta tsire ido guda na yarima Hulkas
shikuwa yarima barmas ma sai da aka dan sokeshi a kafada
jini yayi tsartuwa yaji kamar ya kurma ihu amma sai ya
daure
a
haka dai aka samu aka fice dasu ba tare da asirinsu
ya tonu ba
kafin a isa bakin kogin garinne yarima hulkas yaji nadama
ta zo masa bisa wannan ganganci da sukayi na sai
da ransu don kawai suna son su shiga cikin gari
Ana isowa bakin kogin ne aka sauke buhunhunan dasu
yarima hulkas ke ciki ko da aka fito dasu aka ga yarima barmas ya sami rauni
a kafadarsa sai hankalin bayin ya dugunzuma
ainun suka firgice
shi kuwa yarima Hulkas yana ganin
rauni a kafadar barmas bai san sa adda ya kama rigarsa
ya yagata ya daurewa barmas raunin don tsaida jiniba
cikin rudewa hulkas ya dubi barmas ya ce yakai
abokina tunda dai ka sami wannan rauni zaifi
kyau
Mu hakura mu koma cikin gidan sarauta mubar batun
ganin wannan jarumar yarinya domin muje ayi maka magani
da sauri
koda jin wannan batu sai yarima barmas yayi murmushi
yace aini idan nayi gaba bana komawa baya kuma
idan har muka koma gida bamuga wannan yarinyar
ba ai mun sha wahalar banza kenan mun sayar da rayuwarmu a wofi, tunda dai ka tsayar da jinin dake zuba a jikina
babu komai zan iya gabatar da abinda muka fito yi
lafiya har mu kammala, yanzu sai mu shiga cikin kogin
nan mu wanke kashin dake jikinmu don kada muje
wajan ta muna wari
nan take yarima basmar ya sallami bayin akan cewa
idan sun kawo sawun karshe na kashin suyi
tafiyar kada suyi shakkar komai
don haka suka saba yi shi dasu domin shine ya san
dabarar da yake yi yake komawa cikin gidan sarautar
ba tare da an ganshi ba
ba tare da bata lokaci ba yarima barmas da yarima hulkas suka ruga zuwa cikin
kogin suka kwabe kayan jikinsu sukayi tumbur sai da suka
wanke kayan nasu tas sannan suka fito
suka shanyasu akan wata bishiya suka sake komawa cikin gefen kogin suka kama wanka
a wannan lokaci ne yarima hulkas ya tsinci kansa a cikin wani iein nishadi wanda bai taba jinsa ba na
farinciki
walwala da annashawa abin da yafi burgeshi shine
ganin yadda yau ya sami yancin kansa har yake yiwa
kansa wanka da wanki alhalin bai taba yiwa kansa
wata hidima ba sai dai ayi masa komai
sai da kayan da suka shanya suka bushe sannan suka fito daga
cikin kogin suka je suka sanya kayan nasu sannan yarima basmar ya wuce gaba
hulkas na biye dashi suka nufi wata siririyar hanya wacce zata kaisu cikin gari a wannan lokaci yammaci ne mai
dauke da yanayi mai kyau da dadi domin wata irin iska ce mai sanyi ke kadawa
kafin su iso cikin garin sai yarima basmar da yarima
hulkas suka rude fuskokinsu da rawaninsu ya zamana cewa idanunsu kadai ake
gani don kada a shaidasu
haka dai suka ci gaba da tafiya suna ratsawa ta cikin
unguwanni har suka iso wata unguwa dake can karshen
gari kuma suka tunkari gida na karshe a unguwar wanda
shi ne mafi muni
da kaskanci
Da ganin gidan kasan cewa na talakawa ne fitik
marasa gata ko kuma bako wanda bai kasance dan gari
ba
saboda an gina gidanne da katako ko kyakkyawan tsari
baiyi ba
tun daga nesa su yarima hulkas suka hango wani
mutum mai kwarjini zaune a kofar gidan fuskarsa
cike da kasumba amma kuma hannunsa guda na hagu a yanke yake sannan kafarsa
guda a lankwashe take sai da sanda yake dogarawa
mutumin na tsaye a can gefe daya yana kallon wadansu
tsuntsaye dake ta wasa akan wata bishiya saiga
matarsa wata yar kyakkyawar mace yar kimanin shekaru
talatin da doriya wacce ba zatafi sa ar gimbiya shadila ba
ta fito daga cikin gidan dauke da kofin shayi ta nufi mijin nata
A dai dai wannan lokaci ne mijin matar ya hango su
yarima hulkas sun durfafoshi shi da matar tasa sai suka kurawa su yarima hulkas
idanu kawai cikin sanyin jiki da mamaki
Dama A wannan lokaci su yarima basmar sun cire rawanin
da ya rufe fuskokinsu kyawunsu da kwarjininsu irin na yayan sarakai ya baiyana
a fili kururu
bisa mamaki sai yarima hulkas yaga mijin matar ya kura musu
idanu ko giftawar ba yayi
koda suka iso daf dasu sai yarima basmar ya risina a cikin
biyayya ya gaishe da mutumin da matarsa sannan
ya gabatar da kansa yace nine yarima basmar dan sarkin garin nan wanda kuma
abokina ne sunansa hulkas munzone wajan yarka
siyama domin muga baiwar da take da ita ta jarumtaka
da iya yaki saboda abokina bai amince da tana da
wannan baiwar ba a sa adda na bashi labarinta..
TSATSUBA
Littafi Na Uku (3)
Part.E
Koda yarima basmar yazo nan a zancensa sai
mutumin da matarsa suka dubi junansu sukayi murmushi
sannan mutumin ya dubi basmar yace hakika wannan abokin
naka zaisha mamaki kuwa domin a yanzu hakama tuni
siyama ta shiga gasar jarumtakar da za ayi a fadar mahaifinka
wacce za a fara gabatar da ita gobe kuma ina sa ran cewa itace zata karbi kambun
wannan gasa
koda jin wannan batu sai yarima hulkas ya kyalkyale da
dariya yace haba ai wannan ma almara ce ya za ayi karamar
yarinya wacce aka ce batafi sa a taba zata shiga wannan
gasa wacce manyan mutane zasuyi kuma jarumai na daga sassa daban daban na
duniya har ace talashe gasar
koda jin wannan batu sai ran mahaifin siyama ya
baci
ya murtuke fuskarsa nan take cikin fushi ya kwalawa siyama kira
itakuwa
sai gata ta fito daga cikin gidan a cikin shigar yaki
siyama ta kasance kyakkyawar yarinya ta gaban kwatance duk da cewar yarinya ce yar
shekara shida sai mutum yayi zaton takai shekaru goma sha saboda ta kasance
doguwar gaske sai mutum ya dubi fuskarta sannan zai gane cewa yarinyace tana da cikakkiyar sura da zati irin na
cikakkun mata ababan kwatance
koda yarima hulkas yayi arba da siyama sai yaji nan take ya kamu da tsananin kaunarta
amma da yaga ta kalleshi tana mai gabza masa harara
sai zuciyarsa ta buga da karfi tsoro ya bai bayeshi yaji kamar ya ruga da gudu saboda kwarjininta
siyama ta karaso gaban iyayanta
ta risina a garesu tana mai amsa kira kawai sai mahaifin
nata ya daga sandar dake hannunsa da hannun nasa lafiyayyan yayi nuni a gareta ko da ganin haka sai siyama
ta zare takobinta ta kwala ihu sannan ta daka tsalle sama tamkar daga cikin baka aka harbota ta fada kansa
suka ruguntsume da azababben yaki mai tsananin ban tsoro ga dukkan mai kallo
nan fa duk su biyun suka wanzu suna masu kaiwa junansu mugayan hare hare
cikin bakin zafin nama duk sa adda takobin siyama ta hadu da sandar mahaifinta sai dai kaji kal
sautin haduwar karafa gami
da tartsatsin wuta na tashi
tunda yarima basmar da hulkas suke ganin gumurzun mazaje masu tsananin zafin nama da jarumtaka ba kamar siyama da mahaifinta
siffanta jarumtakar tasu da kwatantata ba zai yiwu ba
sai dai abinda idanu suka gani
babu wani jarumi daya fadowa yarima hulkas
a rai dayaga jarumtakar siyama da mahaifinta sai mahaifinsa sarki shardas
hulkas ya numfasa sannan yace a cikin zuciyarsa babu
wani jarumi da zai iya fafatawa da wadannan mutumin ko yarsa siyama ya samu galaba a kansu face mahaifinsa sarki shardas
kash ina ma tare da sarki mukayi wannan tafiya da yaga wadannan jarumai masu ban al ajabi
da idanunsa yanzu dama she a wannan duniya akwai irin
wadannan jarumai
sai da siyama da mahaifinta suka shafe sa a daya da rabi
suna fafatawa amma dayansu bai sami nasarar koda kwarzanar jikin
dayan ba
duk da cewar suna yakinne a fusace da
dukkan karfinsu da iyakar kwarewarsu tamkar abokan gaba masu neman hallaka juna
koda sukaga sun kasa cutar da junansu da makami sai sukaja da baya sukayi
cirko cirko suna haki da kallon junansu tamkar zakaru kuma suna murmushi
shidai mahaifin siyama murmushin da yake yi bana komai bane face na farin
ciki
bisa ganin abinda ya koyawa yasa ta kware a a kansa
ainun harma ta fishi kwarewar a matsayinta na ya mace
ai dama ance kyan da ya gaji ubansa kuma barewa batayin gudu ba danta yayi rarrafe
babban abinda ya daurewa su yarima hulkas kai shine
ganin yadda mahaifin siyama ya iya yin wannan bkin gumurzu alhalin ya kasance mai hannu daya
kuma gurgun da yake dogara sanda
kwatsam sai siyama da mahaifinta suka ajiye makamansu
a kasa gefe daya wato shi ya ajiye sandar karfen dake
hannunsa
itakuma ta ajiye takobinta faruwar hakan keda wuya sai sukayi alkafira
a kasa suka afkawa juna suka ci gaba da kaiwa juna naushi da bugu
hannu da kafa sai gashi siyama tana shanye naushi da bugu kai kace wata katumar namiji
ce ba mace ba
kuma yarinya karama yar shekara bakwai tabbas horon da siyama ta samu zata iya gumurzu a tsakiyar
miliyoyin dakarun yaki
ma kuma ta dade tana fafatawa tana mai taka rawar gani
a wannan fadan hannu ma sai da siyama da mahaifinta suka shafe kusan sa a biyu
gashi dai sun hadawa junansu jini da majina
kuma sun gaji likis amma saboda tsananin juriya naci da
dakakkiyar zuciya sunki su daina fadan, Koda
matar mahaifin siyama taga abin ya wuce gona da iri ta
ruga ta shiga tsakiyansu ta tsaida fadan,
a sannan ne siyama da mahaifin suka zube kasa suna haki da dariya daga can mahaifin siyama ya dago kai
ya dubi yarima hulkas yace shin yanzu ka gamsu kuma ka yarda
cewar yata zata iya shiga wannan gasar jarumtaka da za ayi a fadar birnin nan?
Koda jin wannan tambaya sai yarima hulkas yayi murmushi yace tabbas na gamsu kuma na yarda dari bisa sari Al amin , zata iya ya kai abul siyama idan ba zaka damu ba ina son na nemi wata alfarma guda a wajanka
cikin mamaki mahaifin
Siyama yace yaro ina sauraronka fadi tambayarka naji
in dai na sani zan baka amsarta, hulkas yayi gyaran murya yace ina son ka bani
takaitaccen tarihin rayuwarka sannan ina son na sani shin
wannan lalura da na ganka da ita ta rashin hannu da kafa daya ta
sameka ne da girmanka ko kuwa a haka aka haifeka
kai mutumin wace kasa ne kuma ya akayi kazo nan
birnin domin ga dukkaln alamu kai bakone a garin nan
bisa lura da yanayin gidanka da na gani wanda ya banbanta da dukkan gidajen birnin nan
lokacin da yarima hulkas yazo nan a zancensa sai jikin mahaifin siyama yayi sanyi yayi sauri ya sunkui da kansa kas don
hawaye ne ya subuto masa
kawai saiyayi shiru baice komai ba, caraf sai matarsa wato
ummul siyama ta dubi yarima hulkas tace ka tambayi mijina tambayoyinda idan ya tuno da amsarsu yake shiga
cikin tsananin bakin ciki mara misaltuwa
lallai a yanzu ba zaka sami amsar wadannan tambayoyi
ba sai dai wani karon
koda jin haka sai yarima hulkas da barmas sukaji sun kamu da tausayin mahaifin siyama
nan take hulkas ya tako kafafunsa yazo har gaban mahaifin siyama ya dafa kafadarsa ta dama da tafin hannunsa yace ka gafarceni yakai abul siyama
inda na san cewa tambayoyina a gareka
zasu sosa maka zuciya su tuno maka da wani abin
damuwa da ba zan gabatar dasu ba a gareka mun barku lafiya sai gobe a filin fada zamu hadu idan kunzo filin gasar jarumtaka
Koda gama fadin haka sai su hulkas suka juya
da nufin ya kama hannun barmas su tafi amma sai yaji abul siyama ya dafa
kafadarsa cikin mamaki hulkas ya juyo suka fuskanci juna yaga abul siyama yana
yi masa wani irin kallo mai nuna alamar kamar ya sanshi kuma akwai alamun dumbin magana a zuciyarsa wacce ya kasa amayar da ita daga bakinsa
har abul siyama ya budi baki zaice dashi wani abu sai kuma
ya kasa yace yaro mun gode bisa ziyarar da kuka kawo mana amma nima ina rokon
alfarma guda daya a wajanku amma bata komai bace face ina son kada ku sake xuwa nan wajanmu domin a duk sa adda na kalli fuskarka ina fama wani mugun rauni dake cikin kahon zuciyata
abu na biyu kuma ina rokonku da kada ku bayar da labarina ko na yata ga waninku saboda wani
babban sirri na rayuwarmu har sai bayan an kammala gasar jarumtakar da akeyi a garin nan
koda gama fadin hakan sai abul siyama ya dafa kafar matarsa da hannunsa lafiyayyan
ita kuma siyama sai ta tallafa kugunsa suka taimaka masa
suka juya suka nufi cikin wannan gida nasu na katako
koda suka isa daf da bakin kofar gida zasu shiga sai ab
siyama ya juyo ya yiwa hulkas wani irin kallo idanunsa
cike da kwalla take hulkas yaji tsigar jikinsa gaba daya ta tashi kuma kaunar abul siyama ta kara shigarsa
tamkar dama can sun kasance yan uwan juna
nan fa yarima hulkas ya kasa motsawa daga inda yake kuma yaji kamar yace da yarima
basmar ya barshi ya kwana a nan gidansu
siyama domin ji yayi babu abinda yake so sama da kasancewa
tare dasu
kawai sai hulkas ya bisu da kallo har suka kule a cikin gidan
koda ganin haka sai yarima basmar ya rugo ya kama hannun yarima hulkas ya jashi da gudu suka bi hanyar
da zata mayar dasu can gidan sarautar
maimakon su wuce kai tsaye izuwa gidan sarautar
sai yarima basmar ya kaisu
gidan wani dan kasuwa mai suna abul yamzin wanda kullum sai ya kaiwa sarki hulkasu tulunan ruwan giyar da
yake sha gami da ruwan inibi
sarki hulbasu ya aminta dari da attajirin
abul yamzin don haka ko caje tulunan
giyar sa da na inibi ba ayi a duk sa adda ya shige dasu cikin
gidan sarautar
Tsakanin yarima basmar da attajirin abul yamzin akwai
kyakkyawar alaka da fahimtar juna don haka sun san sirrin
junansu sosai
da zuwan yarima basmar da hulkas gidan attajiri
sai aka sanyasu a cikin manyan tuluna guda biyu
wadanda babu komai a cikinsu aka hada da wadanda ke dauke da ruwan giya guda goma dana ruwan inibi goma aka
zuba su a cikin dana ruwan inibi
aka zuba su a cikin wannan amalanke aka tura aka tafi dasu gidan sarki
a can gidan sarki kuwa hankalin gimbiya shadila dana luzuraina ya tashi ainun
domin ganin cewa tunda su yarima suka fita basu dawo ba har bayan tsawon sa a uku
nan da nan aka baza dakaru zuwa kowani sako na gidan ana nemansu koda aka duba ko ina ba a gansu ba sai hankalin
su shadila ya sake tashi
suna shirin su tura aje a sanar da sarki hulbasu kenan saiga yarima hulkas da basmar sun shigo cikin
turakar
koda ganinsu sai shadila ta ruga izuwa yarima hulkas cikin
matukar farin ciki ta rungumeshi daga nan
ta jashi zuwa cikin dakin barcinta da aka bata ta kulle kofa
ta dubeshi cikin fishi
da matukar damuw atace ina kukaje kuka buya
haka har kukayi matukar tayar mana da hankali
koda jin wannan tambaya sai yarima hulkas ya sunki
da kansa kas ya tuna cewa shifa
a rayuwarsa bai taba yin karya ba
dan haka take ya yanke hukuncin ya sanar da ita gaskiyar duk abinda ya faru tun daga
lokacin da sukaje bangaren da ake aikin kashin gidan
kawo sa adda aka kaisu bakin kogi sukayi wanka
sannan suka wuce gidansu siyama
hatta kamannin siyama dana mahaifinta dana babarta sai da ya zaiyana mata har dama irin tsananin jarumtakar baban
Siyama a matsayinsa na musaki mai
hannu daya da kafa daya sai da ya shaida mata
koda shadila taji siffifin baban siyama da yadda yake yakinsa sai nan take zuciyarta ta
kama bugawa da karfi, ba komaine ya haddasa hakan ba face tunowa da tsohon
masoyinta hailur wato mahaifin hulkas na gaskiya domin
shine kadai yake da siffa da sura irin wacce hulkas ya shaida mata yanzu kuma shine
kadai mutumin da ta san cewa yana irin salon
yakin da aka fada
cikin firgici da razana shadila ta mike tsaye zumbur
ta kama kafadun hulkas ta girgiza dakarfi tace a ina kaga
wannan jarumi mahaifin siyama
ya za ayi ka kaini inda yake
na ganshi
cikin alamun matukar mamaki yarima hulkas ya dubi
shadila yace yake ummina shin kinsan wannan
mtum ne ko kuwa kun taba jin labarinsa ne a jana wani baniba?
Koda jin haka sai shadila ta tuno da gargadin da shardas yayi mata akan cewar
idan ta kuskura ta shaidawa hulkas cewar bashi
bane mahaifin sa na gaskiya sai ya kasheta ya lalata dukkan rayuwarta nan take shadila ta wayance ta
bagazar da maganar ta nunawa hulkas cewar kawai
jarumtakar baban siyama ce ta burgeta
nan dai ta lallaba hulkas yaje ya kwanta saboda ya
mance da komai ita kuma saita juya masa baya a lokacin
da hawaye ya zubo mata tace a ranta
duk yadda za ayi sai nayi naje na ga mahaifin siyama
domin na gani da idanuna ko tsohon mijina ne
ya zama nakasashshe
kai ba zata yiwu bama ya za ayi ace hailur yana na a raye
a duniyar nan amma har ya
manta dani yayi wani auren harma ya haifi ya
alhalin yana tsananin kaunata fiye da komai a rayuwarsa......
.
SHIN SU SARAUNIYA LARBISA ZASU SAMI NASARAR SAMO
SAURAN ABOKAN TAFIYARSU..??
.
SHIN SHADILA ZATA SAMI DAMAR ZUWA INDA MAHAIFIN SIYAMA YAKE??
.
SHIN ZARGIN DA TAKEYI CEWAR TSOHON MIJINTA NE MAHAIFIN SIYAMA GASKIYA NE???
.
TSAKANIN SARKI SHARDAS DA YARIMA HULKAS WAYE ZAI FARA MALLAKAR HULAR LAMSARA
.
Mu hadu A Littafin Tsatsuba Na hudu (4) Don jin Cigaban
wannan labari
Amma kafin nan
Nida na jagoranci rubuta muku shi ba dare ba rana
ba ruwa ba iska, komai rintsi da tsanani typing nake
ba tsayawa
Wato
TSATSUBA
Abdulaziz s madakin gini
Hausaebooks
Made:- by shuraih Usman
Domin samun wasu kayatattun littatafan hausa amatsayin hausa ebooks sai ku ziyarci shafinmu na yanar gizo gizo akan wannan adireshin http://shuraih.waphall.com


SATSUBA
Littafi Na Hudu (4)
Part A.
.
Marubucin Littafin
Abdul azis Sani M/Gini
Typing by..
Al amin Ahmed Misau.
Inkiya..
Shagala Ko Guyson
whtsap No. 08064594218
Doka Banyarda ayi edit na post dinaba ba tare da izinina ba
.
Labari ya Zowa Shagala Cewar:.....
LOKACIN DA SHADILA TA tambayi kanta a cikin zuciyarta cewar
'Anya kuwa Hailur yana raye a duniya amma bai nemeta ba?
Kuma ta kasa baiwa kanta amsa sai idanunta suka kekashe ga barin barci ta kasa koda risinawa a wannan dare
haka dai taci gaba da mutsu mutsu akan gadonta
taci gaba da tunanin jarumi hailur
A wannan rana dai
shadila kwata kwata bata rintsa ba har sai da alfijir ya keto
a sannan ne barcin ya saceta ba tare da ta sani ba
Al'amarin su yarima hulkas kuwa lokacin da gari ya waye
ya farka yaga mahaifiyarsa na ta barci bata ma da niyyar
farkawa sai ya ki tashinta cikin doki da zumudi
hulkas yaje yayi wanka ya kimtsa
gama hakan ke da wuya
sai ga yarima barmas ya shigo cikin dakin shima ya caba ado fuskarsa cike da annuri
ko da yaga hulkas ma ya gama shiri tsaf sai yayi murmushi yace hakika naga alamar cewa ka fini
dokin son zuwa kallon wannan gasar jarumtakar da
za ayi Yau.
Hulkas ya maida masa da martanin murmushin yace Ai ji nake ina ma kamar na zama tsuntsu na ganni a can
ba don komai ba sai don ma kawai na sake ganin kyakkyawar fuskar nan ta jaruma siyama
kuma naga yadda zata fafata yaki da manyan mazaje
barmas ya kyalkyale da dariya yace Ai dama nasan cewa
tatsuniyar Gizo Bata wuce ta Koki, to ai saikayi sauri kazo muje
muyi buda baki a can turakar mahaifiyata
amma me ya faru naga har yanzu mahaifiyarka tana yin
barci bata farka ba?
Koda jin wannan tambaya sai yarima Hulkas yayi ajiyar
zuciya yace ina kyautata zaton cewa jiya

Please Login or Register in order to submit comment