Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

mai zare takobina
na dubi sarki nace yakai abbana kayi sani cewa idan muka bi
wannan sharadi na sarki tamkar mun zamo bayin sane
domin zamu rike masa saniyar tatsa ne ya rinka tatsar
nononta
AA Misau Sunana zamu zamo bamu da wani sirri na
kanmu a cikin kasarmu kuma tattalin arzikin mu zai raunana mutanenmu zasu iya fuskantar fatara
da talauci
kafin na gama rufe bakina tuni sarki ya daka min tsawa
yana mai tarar numfashina ya ce, idan muka ki bin umarnin sarki shardas sai ya kashe
kowa a kasar nan ya mallake komai namu idan mukace
zamu yakeshi komai yawan nan namu sai ya karar damu
saboda yana kan sharafinsa abin da boka zamaranu ya
gaya mini kenan
A matsayinka na dana kuma yarima mai jiran gado ya kamata ka zamo mai kishin
kasarka da jama arka, abinda sarki shardas ke bukata kawai
shine na kaskanta kaina a gareshi kuma mu bashi dukiya
kada ka dubi matsayina da kimata a wannan nahiya, zan iya

sallama rayuwata ma gaba daya don kare jama ata da
kasata dukiya kuwa shirme ce idan ka rasata zaka iya samun wata, ina mai dada ja
maka kunne babu batun yaki tsakaninmu da sarki shardas kuma kada ka kuskura
ka yi wani abu wanda zai jefa kasarmu ko jama armu cikin hadari
ina mai umartarka da ma za kaje kasa a shirya mana tafiya
gobe gobe zamu durfafi birnin sarki shardas don amsa kiransa, kuma dakarun da zasu yi mana
rakiya kada su wuce su
dari biyu don samun kariyar hanya daga sharrin
yan fashi da dabbobin daji, koda gama fadin hakan sai sarki
ya mike tsaye daga kan karagar mulkinsa ya shige cikin
gidan sarautarsa, ni kuwa sai bakin ciki ya lullube ni
na sunkui da kaina kasa a lokacin da idanuna suka ciko da kwallar takaici
a wannan lokaci ne fadar ta watse kowa ya kama gabansa
aka barni ni kadai a zaune babban abin da ya kona zuciyata shine idan na tuna cewa
mahaifina zaije gaban sarki shardas ya durkusa masa alhali a nahiyar mu gaba daya
babu wata masarauta mai tsohon tarihi da daukaka sama
da tamu
AA Misau Ke Magana, idan har sarki ya durkusawa sarki shardas shikenan darajarsa da kwarjininsa
a idanun
jama a sun zube har abada kuma ba za su kara dawowa ba
ina zaune cikin wannan halina bakin ciki dana yarima
huzein ya zo gareni ya dafa kafadata koda na dago kai nayi arba dashi sai naga
shima yana zubar da hawaye, cikin sanyin murya huzein ya dubeni yace yakai abbana
ka zamo mai hakuri da juriya bisa wannan kaddara data same mu
ina so ka sani cewa komai nisan jifa kasa zai fado
don haka komai dadewa akwai ranar da sarki shardas zai fadi
duk wulakancin da zamu fuskanta daga gareshi yanzu
yana da iyaka wataran sai labari, ina mai tabbatar maka da cewa
idan sarki shardas ya kuntata mana a yanzu da zamaninka to nan gaba namu zamanin
sai komai ya sauya
sa adda huzein yazo nan a zancensa sai na cika da mamaki bisa dalilin yin
wannan jawabi tamkar wanda ya jiyo wani abu daga
wajen bokaye
nan take na rungume huzein iana kuka nace yakai dana
zan kasance mai fatan ganin ranar da sarki shardas zai fadi
kafin mutuwata
koda jin wannan batu sai huzein ya janye jikinsa daga cikin
nawa ya dubeni cikin murna da murmushi yace yakai abbana ina neman alfarma guda daya a
wajenka
cikin mamaki na dubeshi nace yakai dana kai kuwa wacce
irin alfarma kake nema a wajena ? Huzein yace ina son kuyi
wannan tafiya tare dani gobe zuwa birnin sarki shardas
koda jin haka sai idanuna suka zazzaro na dubeshi cikin alamun damuwa nace
haba yakai dana ka tuna cewa idan sarki baya nan
nima bana nan kuma babu kai babu wanda zai gajemu kenan
koda tsautsayi yasa mun hallaka
wannan tafiya da zamuyi mai hadari ce komai zai iya faruwa
a garemu ko akan hanya
ko kuma a can birnin sarki shardas, bugu da kari a halin yanzu mahaifiyarka na dauke da tsohon
juna biyu haihuwarta yau ko gobe idan babu ni
babu kai a kusa da ita wa zata kalla taji dadi?
AA Misau Ke Magana sa adda yarima huzin yaji wannan batu nawa sai jikinsa yayi sanyi

amma duk da haka sai yaci gaba da rokona akan na
Rarrashi sarki ya amince ayi wannan tafiya tare dashi, muna cikin wannan hali ne muka ji takun
sawu a bayanmu
cikin sauri muka waiga mukayi arba dashi, ba wani bane
face mahaifina fuskarsa cike da annuri kawai sai ya karaso
garemu ya zauna a tsakiyarmu sarki ya dubeni sannan ya
dubi yarima huzein yayi murmushi yace naji duk abinda kuka tattauna, kuma na amince zamu tafi
tare dakai
gobe
koda jin wannan batu sai farin ciki ya lullube yarima huzein ya
rungume sarki yana mai sumbatar goshinsa kawai sai sarki ya janye jikinsa daga cikin
na huzein ya dubeshi cikin alamun tsananin damuwa kamar
zaiyi kuka yace yakai jikana kayi sani cewa na amince muyi
wannan tafiya tare dakai ne saboda dalili daya rak
dalilin kuwa shine nima sa adda na taso a wannan gidan
sarauta daga san da aka haifeni zuwa lokacin dana kai
shekarunka wato shekaru bakwai a duniya sau daya rak aka
taba barina na fita wajen birnin na, bai kamata ace yarima guda wanda zai mulki al umma da yawa
ba ya kasance
kifin rijiya
yana da kyau ka shiga duniya kaga yadda talakawa
ke rayuwa kuma kayi gwagwarmaya kasha wahala sosai domin ka san menene rayuwa amma ka
sani cewa akwai sharadi guda uku a
kanka daga ranar da muka fita daga cikin garin nan,
sharadina farko shine ba ka da ikon zuwa ko ina walau
a cikin daji ko a cikin gari face da izinina ko na mahaifina sharadi na biyu shine duk abinda zakayi
saika shawarcemu sharadi na
uku kuwa shine ba zaka ci ko ka sha wani abu ba
face wanda muka baka da hannunmu,
shin ka amince da wannan sharadai guda uku
dajin wannan tambaya sai yarima huzein yayi murmushi kuma
ya zube kasa a gaban sarki ya kama godiya cikin farin ciki tare da tabbatar da amincewarsa
ga wadannan sharudda
Kashe gari kuwa da sassafe aka yi shirin tafiya dakaru dari
biyu ne suka yi mana rakiya dauke da isashshen guzuri sai kuma
kuyangi goma wadanda za su rinka yi mana hidima
tsakanin yan fashi da mugayen dabbobin daji sai da
mukayi karo da rukuni rukuni har guda bakwai kafin mu
isa birnin sarki shardas amma sai da muka tarwatsa su muka kashe na kashewa masu gudu
suka tsere dakaru guda arba in kacal muka rasa a cikin
wannan gumurzu AA Misau Ke Magana, da la asar sakaliya muka iso birnin sarki shardas
koda muka tsaya a bakin kofar gidan sarautar akaje akayi
mana iso sai sarki shardas yaki fitowa saboda jin izzarsa da takamarsa kawai sai ya turo wani
hadiminsa aka kaimu
masauki
bayan mun zauna munci abinci muna hutawa sai tunanin
gida ya fado min inda na tuno lokacin da muke yin bankwana
da matata luzuraina wacce ke dauke da tsohon juna biyu hm Kunya AA Misau, sa dda ta rungumeni
mu biyu ni da yarima huzein ta fashe da kuka
tana mai cewa
yakai mijina kayi sani cewa bana son wannan tafiya da zakuyi
domin ina bukatarku a kusa dani a yanzu fiye da ko

yaushe ba don komai ba sai don saboda ita haihuwa bata da
tabbas
zan iya rasa rayuwata a wannan tafarki ko kuma na rasa abinda na
ke dauke dashi
haka zan iya rasaku tunda kuma tafiya zakuyi mai hadari
tun a jiya da sarki ya shirya wannan tafiya sai naji zuciyata ta kama bugawa
yadda naga rana haka naga dare ina mai tabbatar muku da cewa ba zan taba samun sukuni da
kwanciyar
hankali ba face naga dawowarku lafiya, koda luzuraina ta zo
nan a zancenta sai ni da huzein muka kamu da tsananin tausayinta muka kara kankameta a jikinmu
mukaci gaba da
kuka kamar ba zamu daina ba, daga can sai na janye jikina daga cikin nasu na dubi luzuraina cikin
nutsuwa da murmushin
karfin hali nace yake matata kiyi sani cewa bana son nayi
wannan tafiya saboda rashin sanin halin da zaki iya shiga amma kuma idan har na bar sarki yayi
wannan tafiya shi
kadai zan shiga cikin tashin hankali da wasi wasi akan halin da shima zai iya shiga don
haka dole ne na bishi ko don na bashi kariya
ina son ki kwantar da hankalinki ki sani cewa nayi miki
alkawari duk wuya duk tsananin sai na dawo gareki a raye
kuma na dawo miki da yarima huzein cikin koshin lafiya
gama fadin hakan keda wuya sai ga babban hadimina ya shigo cikin falon nawa ya risina
gareni yace
ya shugabana sarki ya fto ku kadai ake jira
koda jin haka sai ni da yarima huzein muka mike tsaye da
sauri muka nufi kofar fita, a guje luzuraina ta sha gabanmu
tana kuka ta sake rungumemu sannan ta janye
jikinta ta dubeni tace idan na haihu baka nan wanne suna za a sakawa abinda
na haifa
ka sani cewa yarima huzein zai samu kani koda jin wannan batu sai mamaki ya kamani na dubeta
nace yaya aka yi kika san cewa da namiji zaki haifa
luzuraina ta ce sau uku ina yin mafarkin na haifi da
namiji don haka ina ji a jikina cewar lallai da namiji zan haifa
sa adda naji wannan batu sai nayi murmushi sannan na dubi
yarima huzein na ce na baka dama ka zabi sunan da za a sawa kaninka yayin da yazo duniya
cikin murna yarima huzein ya daga kansa sama yayi dan tunani sannan ya dubi mahaifiyata
yace
ki sawa kanina suna YARIMA BASMAR, kuma kiyi masa bushara da cewa ya jira yayansa yazo
suyi was
Lallai nine zan koya masa yadda ake sarrafa doki da takobi
koda jin wannan batu sai hawaye ya zubowa luzuraina ta
sake rungume yarima huzein tana mai sake fashewa da
wani sabon kukan
A dai dai wannan lokaci ne muka jiyo muryar sarki yana mai
kwala mana kira cikin hanzari na fisge yarima huzein daga
cikin luzuraina na ja shi da gudu muka fice daga cikin falon
huzein na waigen mahaifiyasa yana hawaye itama tana
kuka
lokacin da na zo dai dai nan a tunanina sai yarima huzein ya dafa kafadata na
dawo cikin hayyacina
yarima huzein ya dubeni cikin alamun damuwa yace yakai abbana anya kuwa babu
wani mugun nufi a zuciyar sarki shardas a kanmu ? Yakamata ace ya fito ya tarbemu a bisa irin

matsayin mahaifinka da daukakarsa a wannan nahiya amma kuma sai kawai ya aiko da hadimi aka
taho damu nan
masauki
sa adda naji wannan batu sai nayi murmushi nace kada ka damu ya kai dana
duk wannan ba komai bane, babu wani mugun abu da sarki
shardas zai yi mana, kawai dai wulakanci ne irin nasa
da son nuna isa, A A Misau Ke Magana, koma menene ai da zarar mun isa gabansa za a yita
ta kare yaz sallame mu mu koma izuwa kasarmu
burina kawai shine mu koma gida mu iske mahaifiyarka
ta haihu lafiya
kafin na rufe bakina saiga sarki ya shigo cikin dakin namu
kuyanginsa guda hudu na biye dashi dauke da abinci
cikin hanzari muka zube kasa muka kwashi gaisuwa
su kuwa wadannan kuyangi sai suka ajiye wannan abincin
da abinshan a gabanmu suka juya da baya suka fice
sarki ya zauna a gabanmu ya dubemu cikin annashuwa yace na kasa cin abincina
shi yasa na yanke shawarar na zo har nan dominku muci tare
koda jin wannan batu sai mamaki ya kamamu
na dubi sarki nace yakai abbana kai kuwa menene dalilin
daya hanaka cin abinci ? Sarki ya yi ajiyar zuciya yana mai sunkui da kansa kasa sannan yace
tun da muka shigo cikin garin na naji zuciyata tana bugawa
abu ne mawuyaci mu bar garin nan lafiya cikin farin ciki
musamman idan muka yi duba da irin karbar da sarki
shardas mana ta wulakanci da rashin nuna muhimmancina a gareshi
ya yinda sarki yazo nan a zancensa sai nayi dariya nace haba yakai abbana
akan wane dalili zakayi irin wannan tunanin alhali mun kasance masu biyayya ga sarki shardas
gami da bin
umarninsa, ni na san cewa babu wani tsautsayi da zai same
mu lafiya kalau zamu koma gida
kawai mu jira muga yadda
zata kasance tsakaninmu da sarki shardas
koda jin wannan batu sai sarki ya saki ransa hankalinsa ya
kwanta nan take muka kama cin abinci cikin raha da nishadi
muna ta hira da ban dariya har sai da muka koshi......
Wow littafi fa yanzu ya fara tafiya domin yanzu ne zaku san
an fara karanta TSATSUBA zakuji yadda zata kaya tsakaninsu
da yadda Ake tsantsan yaudara da cin amana gami da rashin
imani
Kafinnan dai Nidinne
Al amin Ahmed Misau
AA Misau Ke Magana
Admin Na Zauran Labarai
Page.
Ke cewa Ku huta Lafiya...SATSUBA
Littafi Na Shida (6)
Part C.
.
Marubucin Littafin
Abdul azis Sani M/Gini
Typing by..
Al amin Ahmed Misau.
Inkiya..

Shagala Ko Guyson
whtsap No. 08064594218
Doka Banyarda ayi edit na post dinaba ba tare da izinina ba
.
Labari ya Zowa Shagala Cewar:.....
.
NAN TAKE MUKA KAMA CIN ABINCI CIKIN RAHA DA NISHADI
MUNA TA HIRA DA BAN DARIYA HAR SAI DA MUKA KOSHI,
A wannan rana sarki bai koma dakinsa ba anan dakinmu
ya kwana saboda ko kadan baya son nisanta damu
sai da muka kwana uku a cikin gidan sarautar sarki shardas
amma wai har tsawon
wadannan kwanaki sarki shardas bai kirawo mu ba duk da
cewa kullum yana zama a fada, duk sa adda ya bukaci
ya gana da shi sai yace a gaya masa cewa ya kara sauraro
KAJI MANYA MASU JI DA KAI SARKI SHARDAS KENAN HM
a ranar kwana na ukun ne da safe bayan mun gama kalaci sai
ga hadimin sarki shardas yazo mana take hadimin ya shaidawa mahaifina cewar sarki yace muje mu
riskeshi a fada
cikin farinciki muka mike tsaye muka yi shiri sarki ya
taramu gaba dayanmu dakarunsa da kuyanginsa sannan aka
debo wadannan bayi guda dubu ashirin gami da akwatunan
dukiya guda dubu muka wuce izuwa fadar sarki shardas
fadar ta cika makil ta batse da mutane ko ina ka duba saikaga fadawa dakaru
da manyan attajirai da sauran masu fada aji a kasar
A gefe daya kuma mutanen gari ne maza da mata a durkushe
a kas babu wani mutum guda daya a tsaye ko akan kujera face sarki shardas wanda ke kan
karagarsa ta mulki, koda muka shigo cikin fadar mahaifina na kan gaba muna biye dashi
gaba dayanmu sai naga an zubawa mahaifina idanu kawai mutane so suke su gani shin zai iya
durkusawa a gaban sarki
shardas ya kaskantar da kansa? Babu abin takaici sama da
ganin yadda mahaifina yayi gagarumar shiga ta alfarma mai tsananin tsada wacce ta
ninka ta jikin sarki shardas sau uku amma kuma gashi
zai kaskanta a gaban dubunnan talakawa
a wannan lokaci ina rike da hannun yarima huzein muma munci ado na kwatance
domin ko a cikin fadawan sarki shardas da duk jama arsa babu wanda ya sa suturar data kai tamu
daraja
ni da huzein ke bin bayan sarki sai kuma kuyangi da sauran
dakarun da muka taho dasu daga birninmu don yi mana rakiya lokacin da ya rage
saura baifi taku goma ba tsakanin mahaifina da karagar mulkin
da sarki shardas ke zaune a kai sai yaja da baya cak
muma da muke bayansa sai dukkanmu muka ja muka tsaya cak a bayansa
nan take mahaifina da sarki shardas suka fara kallon kallo fuskar sarki shardas
a murtuke take ko kadan babu annuri kuma jikinsa ya kama tsuma har fuskar tasa na yin gatsine
saboda fishi bisa tunanin cewa ko mahaifina
ba zai durkusa masa ba kawai sai akaga mahaifina ya durkushe
kasa bisa guiwarsa guda ya risina yana mai dukar da kansa
ga sarki shardas cikin murya mai dauke da ladabi yace
gaisuwa gareka ya shubana a madadina da al umar kasata nazo domin mu jaddaja mubaya armu a
gareka ya sarkin duniya
kuma na amsa kiranka, gani nazo da duk abinda ka bukata
koda mahaifina yazo nan a zancensa sai fuskar sarki shardas ta fadada da murmushi

ya mike tsaye daga kan karagarsa ta mulki cikin matukar murna sannan ya tako yazo har inda
mahaifina ke durkushe
ya kama kafaduna ya tashe shi tsaye suka fuskanci
juna yace lale marhaban da sarki mai birnin Askandariyya
lallai ka tsira daga dukkan fishinmu kuma daga yau ka zama amintaccenmu
nan take fadar ta rude da shewa aka kama yiwa sarki
shardas jinjina da kirari bisa ganin yadda sarki mai daraja da cikakken iko kamar mahaifina
ya mika wuya a gareshi
a wannan lokaci takaicida bakinciki suka lullubeni har idanuna suka ciko da kwallah
ban sani ba
A A Misau Sunana , sarki shardas ya daga hannu sama sai
fadar tayi tsit kamar mutuwa ta gifta , A sannan ne sarki shardas ya bushe da dariyar
farinciki ya kirawo wani hadimi nasa mai dauke da tambulan na ruwan giya gami da
kofi guda biyu
da zuwan hadimin sai sarki shardas ya dauki kofi guda hadimin ya tsiyaya masa ruwan giyar sannan
ya dubi
mahaifina yayi masa tayi, batare da fargabar komai ba
mahaifina ya dauki daya kofin shima aka tsiyaya masa ruwan
giyar amma sai yaki yasha
koda ganin haka sai sarki shardas ya bushe da dariya
sannan ya kurbi ruwan giyar har sau biyu ya dubi mahaifina yace kwantar da hankalinka
abokina ai ba zan shayar dakai guba ba, saboda me kake tsoron shan wannan giya mai
albarka wacce nasa aka yi ta musamma don tarbarka?
Koda jin wannan batu sai mahaifina yayi murmushi yace ai ba komai bane yasa naki sha ba
sai don yin ladabi a gareka
kada na rigaka dandana dadinta
dajin haka sai sarki shardas
ya sake bushewa da dariya a karo na biyu sannan ya kamo
kafadar mahaifina ya juyo dashi suka fuskancemu
sarki shardas ya dubeni sannan ya dubi yarima huzein yace wannan danka ne yarima hulbasu mai
jiran gado tare da dansa yarima huzein ko ?
Mahaifina ya gyada kai yace kwarai kuwa sune sannan ya dubemu yace kuyi gaisuwa ga
sarkin duniya
AA Misau Sunana, da farko sai na dan noke a lokacin da
huzein tuni ya duka kasa ai kuwa sai nan da nan
fuskar sarki shardas ta juye izuwa fishi har sai da nima na durkusa na gaisheshi sannan
yayi murmushi yazo ya dafani ta yadda har muna iya jin
numfashin juna ya budi baki cikin karamar murya yadda babu
mai iya jinmu ba sannan yace,
Samari nasan abinda kake ji a ranka bisa kaskantar da
kan da mahaifinka yayi a gareni domin jaddada min mubaya arsa amma ina mai
shawartarka da ka zamo mai biyayya idan har baka
son daular birnin Askandariyya ta fadi, yana gama fadin
hakan sai ya wuce gabana ya shiga duba bayin da aka kawo masa guda dubu
ashirin har sai da ya tabbatar da cewa gaba dayansu lafiyayyune
sannan yaje kan akwatunan dukiya guda dubu
sai da aka bude gaba dayan akwatunan yaga dukiyar dake cikinta
nan take sarki shardas ya sake bushewa da dariyar farin ciki sannan ya dawo
wajen mahaifina ya kama hannunsa ya jashi har
zuwa kan karagar mulkinsa suka zauna tare
a wannan lokaci fadar tayi tsit ko tsinke ne ya fadi kasa
sai an ji kararsa

sarki shardas ya dubi mahaifina cikin nutsuwa ya ce ya
batun sharadin da muka gindaya maka a cikin wasikarmu?
Shin ka amince zaka yi abinda muke so ko kuwa ba zaka bi ba ? Sa adda mahaifina
yaji wannan tambaya sai ya risina cikin biyayya yace
ya sarkin duniya na amince da duk bukatarka amma
ina neman wata alfarma guda daya, alfarmar kuwa
itace ina son ka rage yawan bayin da zan rinka kawo
maka duk shekara da kuma yawan akwatunan dukiya su koma rabin wadanda na kawo maka yanzu
ba don komai ba sai saboda hakan zai iya kawo karyewar tattalin arzikin kasata
domin a halin yanzu bayi sunyi karanci a kasata
kuma bayin nan sune suke yi mana aikin noma a gonakinmu
noman kuma shine yake kawo mana dukiyar da zamu tara mu kawo maka
koda jin wannan batu sai sarki shardas ya fusata ya dakawa
mahaifina tsawa yace babu ruwanmu da wannan matsala domin kai ta shafa bamu
ba
don haka sai ka san hanyar da zaka bi ka nemi bayi koda
kuwa sai kayi farautarsu ne a sauran kasashen da ke kusa daku
ka sani cewa gobe goben nan zan hadaka da wakilina
mutum uku wadanda zaka tafi dasu izuwa fadarka a dinga
gabatar da harkokin mulki tare da su domin su rinka kawo mini
rahoton duk abubuwan dake gudana, a karshe ina mai gargadinka da cewa digon jini daya na
wadannan
wakilai nawa dai dai yake da digon jinin saba in na jama arka don haka a kula da su da kyau kuma a
basu
duk abinda suke bukata
sa adda sarki shardas yazo nan a zancensa sai nayi wuf
na matso gaba kusa da karagar mulkin sa na dubeshi nace yakai wannan sarki
ka yi sani cewa idan ka hadamu da wadannan wakilai naka
tamkar ka rushe karfin mulkin mahaifina ne gaba daya
tunda ba shi da ikon yin wani sirri a cikin harkokinsa na mulki kuma ba shi da ikon zartar da komai
sai da saninka da amincewarka
ni ina ganin A A Misau Ke magana, wannan ba adalci bane
zalunci ne da kaskantarwa....... Kafin na gama wannan jawabi tuni jikin sarki shardas
ya kama tsuma saboda fishi har gumi ya fara tsatstsafowa daga fuskarsa
shi kuwa mahaifina a wannan lokaci ya firhita ainun
so yake ya hanani ci gaba da magana amma ya kasa, kawai sai sarki shardas ya mike tsaye
zumbur
daga kan karagarsa ya zo daf dani ya zare takobinsa ya dora kaifinta akan wuyana
yana mai ci gaba da tsuma ni kuwa ko gezau ban yi ba
A lokacin gaba dayan mutanen dake fadar sun firgita ainun
kowa ka kalla sai kaga jikinsa na bari don gudun kada
laifin wani ya shafeshi, sarki shardas ya daka min tsawa ya ce kai dan samari kaine
mahaluki na farko wanda ya taba shigowa har cikin fadata
yayi mini bakar, don haka yanzu zan kasheka domin na gusar da kishirwar
karya wannan lago nawa da kayi, koda gama fadin hakan sai
sarki shardas ya daga takobinsa sama da nufin ya
sareni amma sai mahaifina yayi wuf ya janyeni daga gabansa sannan yayi sujjada a
gareshi ya dago kai yace ya sarkin duniya ina nemawa dana
afuwa
ka san cewa har yanzu akwai kuriciya a tare da shi
koda jin wannan batu sai sarki shardas ya sake
bushewa da dariyar mugunta sannan ya mayar da takobinsa cikin kufe ya dafa

kafadata yace samari ka tsira daga kaifin takobina yau, amma ka
sani cewa idan ka sake aikata kuskure irin wannan ba zaka taba tsira ba
yana gama fadin hakan sai ya juya ya fuskanci fadawansa ya kirawo wadansu mutane uku
daga cikin dan uwansa wanda ake kira MUHAIRU wanda ya
kasance dan yayarsa
sarki shardas ya dubi muhairu ya ce yakai dan uwana
daga yau na cireka daga matsayin gwamnan birnin DAILUFA
a yanzu kaine shugaban wakilaina na birnin Askandariyya saboda haka kaje ka fara shirin binsu
gobe
amma kafin goben ina so ka zauna da yarima hulbasu
ya sanar dakai iya adadin biranensu da kauyukansu da kuma duk harajin da suke
tarawa a kowacce shekara ka rubuta komai ka kawo min
muhairu ya risina yace an gama ya shugabana
kawai sai sarki shardas ya juya ya fice daga fadar ya wuce
izuwa cikin gidan sarautarsa, shi kuwa muhairu sai ya zo
gabana ya tsaya yana mana wani irin murmushi na mugunta
da raini ya dubeni yace ka saurari zuwana nan da lokaci
kankani
yana gama fadin hakan sai ya kyalkyale da dariyar mugunta ya wuce abunsa
sauran wakilai guda biyu na take masa baya suma suna
kyalkyala mana dariya
Nan take dakarun sarki shardas suka ingiza keyar bayin da
muka kawo guda dubu ashirin aka wuce dasu izuwa can wani
bangare na gidan sarautar sarki shardas, kuma aka kwashe
Wadannan akwatunan dukiyar da muka kawo , A sannan ne fadar
ta watse ya zamana cewa daga mu sai jama armu kacal a tsaye cikin tsananin bakin ciki
da takaici
A dai dai wannan lokaci ne zuciyata ta kama tafarfasa
kamar zata kone ban san sa adda na kurma uban ihu ba
mai tsananin firgitarwa na durkushe kasa ina mai fashewa da matsanancin kukan bakin
ciki
Al amarin daya janyo hankalin dakarun sarki shardas kenan
suka zare takubba suka rugo izuwa kanmu, koda suka ganni durkushe a kasa ina
kuka sai suka kama dariya suka tafi suka barni
a wannan lokaci ne mahaifina da yarima huzein suka durkusa a gabana sa adda
suma suka fara zubar da hawayen bakinciki
kawai sai sarki ya rungumeni tare da fashewa da kuka sosai
mu duka sai muka kama kukan, sai da muka dan jima zaune a cikin fadar muna kuka sannan muka
mike tsaye muka tafi izuwa masaukinmu.......
.
Wow Zan dakata A wannan guri saikuma Allah ya kaimu Gobe
zan cigaba daga nan
Amma kafinnan Nidinne Dai
Al amin Ahmed Misau
AA Misau Ke Magana
Admin Na zauran labarai
page.
April 1SATSUBA
Littafi Na Shida (6)
Part D.
.
Marubucin Littafin

Abdul azis Sani M/Gini
Typing by..
Al amin Ahmed Misau.
Inkiya..
Shagala Ko Guyson
whtsap No. 08064594218
Doka Banyarda ayi edit na post dinaba ba tare da izinina ba
.
Labari ya Zowa Shagala Cewar:.....
.
SAI DA MUKA DAN JIMA ZAUNE A CIKIN FADAR MUNA KUKA SANNAN MUKA MIKE
TSAYE MUKA TAFI IZUWA MASAUKINMU....
Bayan mun isa masaukinmu mun zauna cikin bakinciki
muna tunanin wannan hali da muka tsinci kanmu a ciki
na takaici da wulakanci, sai sarki ya dubeni a lokacin da
hawaye ya zubo masa yace yakai dana ka yi sani cewa
wadannan sharadai da sarki ya gindaya mana sai sun janyo
fari da talauci a kasarmu kuma wannan shine lokacin da
na dade ina tsoron gani a rayuwata
fadin hakan keda wuya sai sarki ya fara wani irin tari mai
karfi kafin a jima kuwa sai ya kama aman jini
cikin rudewa na kwallah ihu ina mai kiran likitan sarkiwanda
muka taho tare
dashi tun daga birninmu domin duba lafiyarmu, nan
da nan wata kuyanga ta ruga taje ta kirawo likitan yazo ya shiga duba mahaifina
dan ceto rayuwarsa
da kyar likitan ya samu ya shawo kan cutar sarki ya
tsayar da jinin dake zuba a bakinsa sannan kuma ya bashi magani ya sha
faruwar hakan keda wuya cikin dakika kadan nannauyan
barci mai karfi

Please Login or Register in order to submit comment