Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

nima nayi amfani
da maganar manya da suke cewa idan babba ya rike
girmansa dole ne karami yayi masa biyayya. Lokacin da kika shigo cikin wannan daji namu ke da jama arki baki
hanasu kokarin yi mana sata ba
dalilin
da ya sa na ki karbar bakuncinki kenan tun da farko
amma yanzu dana gane cewar wata kila kina da
mahimmanci ga rayuwata shi yasa nake yi miki
ladabi da biyayya
larbisa ta bushe da dariya sannan tace ai kowane mutum
yana da rana komai kaskancinsa shin zaki iya
gaya mini babban burinku na duniya keda mahaifinki
wanda har kuke tunanin zan iya taimaka muku a kansa?
Sa adda shumaira taji wannan tambaya sai tayi murmushi tace me kikeci
na baka na zuba ehm wato ( what are you eating na baka is falling down )
zakiji amsar wannan tambaya taki idan mukayi
zama na musamman mu dake kuma a sannan ne
muma zamuji taku bukatar a wajanmu, kodajin
wannan batu sai sarauniya larbisa tayi murmushi tace
tabbas zancenki dutse ne, haka dai shumaira da larbisa suka ci gaba da hira har
suka gama cin abincin kuma dare ya raba sannan
suka kwanta sukayi barci, kamar yadda aka karrama
sarauniya larbisa hakama aka karrama sadauki
humaisu da dukkan dakarunsa suka ci suka sha sukayi
hani'an kuma suka kwanta a masauki mai kyau
Al amarin da yayi matukar daure musu kai kenan
suka cika da tsananin mamakin yadda wadannan
mafarauta suka tara arziki mai yawa haka
++
Kashe gari da safe bayan sarauniya larbisa ta yi
wanka ta kimtsa sai ta ga shumaira bata kawo musu abincin
kalaci ba
kawai ta zauna tana jiranta ta gama kimtsawa tana gama
kimtsawa kuwa sai shumaira ta mike tsaye ta dubeta
tace iyayena suna jiranmu acan turakarsu domin
muyi mude baki tare dasu kuma mu sami damar
tattaunawa akan abubuwan da muka sa a gaba
koda jin haka sai sarauniya larbisa ta mike da sauri
cikin murna ta bi shumaira a baya suka fice daga cikin
dakin suka nufi hanyar da zata kaisu bangaren da
iyayen shumaira suke, sai da sukayi yar tafiya mai
dan tsawo kadan sannan suka iso wani babban falo mai
dauke da
Wani faffadan tebu A karkashin teburin kujerune guda
biyar
tsoho Imshal tare da matarsa larisa na zaune
akan kujeru biyu ga abinci nan wajen kala uku
akan teburin dake gabansu, da isowar shumaira da
larbisa sai tsoho imshal da larisa suka mike tsaye suna
musu girmama
sarauniya larbisa gami dayi mata barka da isowa
nan take larbisa da shumaira suka janyo kujeru daga cikin
karkashin teburin suka zauna aka fara cin abincin
Tsawon yan dakiku da fara cin abincin dayansu baice
uffan ba daga can sai tsoho Imshal yayi gyaran murya
yace
yake wannan sarauniya mai daraja yanzu saiki gaya
mana abin da ya kawoki garemu kafin muma mu
gaya miki bukatar da muke da ita a wajanki
Koda jin wannan batu sai sarauniya larbisa tayi murmushi sannan tayi
gyaran murya tace ba wani abu bane ya sa na baro
kasata ba
mulkina da jama ata face don na riski kogon
Kitabul sihir inda littafin TSATSUBA yake, littafin da shine kadai zai cika mini babban
burina na duniya na samun damar yin aure gami
da samun magaji kuma na mallaki komai da kowa dake
cikin wannan duniya ba zan iya isa inda kogin
yake ba face na ratsa ta cikin dazuzzuka guda uku
Daji na farko shine ake kira da Shajarul Shaljuma
wanda ke dauke da mugayen dabbobi da mugayen
tsuntsaye. Bokaye sun tabbatar mini da cewa babu
wani mahaluki wanda zai iya wucewa dani ta
cikin wannan daji a raye face wannan ya taku shumaira
daga nan ne zamu wuce izuwa dajin Ujurul Majnun bisa
jagorancin Jaruma Larifat, daji na uku kuwa wanda ake kira
darul maut zamu shigeshine bisa jagorancin jaruma Lubaina
muna wuce wadannan dazuzzuka sai kuma mu tunkari
dajin da kogon Kitabil sihir yake
shi kuwa kogon
babu mai iya yi mana jagora izuwa cikinsa face
jarumi Ruhaisu dan sarki Zaiyanu na birnin kufa
A cikin kogon kitabul sihir ne zan iya dauko littafin
TSATSUBA domin na lalata duk sihirin tsafin dake
cikinsa don na sami damar yin aure na sami da ko
yar da zata gajeni idan ban lalata sihirin dake cikin
wannan littafi ba na tsatsuba har abada burina ba zai
cikaba
Koda sarauniya larbisa tazo nan a zancenta sai tsoho
Imshal ya tuntsire da dariya Al amarin da ya baiwa
larbisa dasu shumaira mamaki kenan daga can
kuma sai Tsoho Imshal ya murtuke fuska tamkar an
aiko masa da sakon mutuwa a lokacin da idanunsa
suka ciko da kwalla har hawaye ya zubo masa..
Nan fa sarauniya Larbisa ta kara cika da tsananin mamaki
ta dubi tsoho Imshal tace yakai Abul Shumaira ina
dalilin yin dariyarka gami da zubar hawayenka a bisa
abinda kaji na fada??..TSATSUBA
Littafi Na Biyu (2)
Part B.
.
Yayinda tsoho Imshal yaji wannan tambaya sai yayi
Ajiyar numfashi ya dubi sarauniya larbisa cikin
nutsuwa yace yake wannan sarauniya mai daraja
kiyi sani cewa ba wani abu bane ya sakikaga na bushe
da dariya ba sai saboda nasan cewa kin daukowa
kanki gagarumin aikin da sai kinyi nadamar yinsa
domin aikine wanda babu tabbacin samun nasara
a kansa, sannan kuma zaki iya shan bakar wahala
da bata da misali kuma dake da duk abikan
tafiyar taku zaku iya rasa rayuwarku ko lafiyarku.
Ke a takaice dai fiye da shekaru dari baya ba a
taba samun mahalukin da ya ratsa ta cikin wadannan
dazuzzuka guda uku har ya isa kogin sihir a raye
ba
don haka ni yanzu ina kallonki ne a matsayin wacce
ta gaji da rayuwar duniya take neman mutuwa ruwa
a jallo! Ko kuma ince wacce ta sami tabin hankali !!
Dalilin da yasa kikaga ina zubar da hawaye kuwa shine
biwa wannan TAFARKI da kike son bine na rasa
iyayena da kakannina domin suma sun bar gida
sun tafi izuwa kogon kitabul sihir domin magance wata matsala data addabi gaba
daya zuri armu tsawon shekaru masu yawa
amma dayansu bai dawo a raye ba, wannan matsala
kuwa ba komai bace face wani sihiri wanda wani abokin gabarmu ya yiwa kakanninmu, shi dai wannan abokin
gaba namu mafarauci ne kuma takadarin boka ne
tunda akayi GASAR FARAUTA a birninmu kakanmu ya lashe gasar sai wannan
boka yayi masa sihiri ya kasa ci gaba da zama a cikin
gari shi da iyalinsa yaji kamar ana konashi da wuta
Matansa da 'ya'yansa da jikokinsa ma haka suka rinkaji
ya zamana cewa ba shiri suka hada nasu 'i' nasu suka koma cikin daji da zama
bisa dole kakan namu ya hakura da sarautar sarkin
daji da aka bashi ya daina zuwa fada gaba dayan
zuri armu sai suka tsani cikin gari daga wannan rana kawo
iyanzu babu sauran mutum daya daga cikin zuri armu
wanda ke rayuwa a cikin daji duk mun watsu a cikin
dazuzzuka har yau har gobe ni din nan da matata da
yata shumaira da kike ganinmu bamu taba shiga cikin gari ba mu tsaya
tsawon rabin sa a sai dai muyi siyayya a kasuwa mu
fito babu irin kokarin da bamu yi ba wajan neman
yadda zamu karya wannan sihiri amma abu ya gagara
kafin mahaifina ya rasu ya shaida mini cewa ba
zamu taba iya samun nasarar karya wannan sihiri
ba face mun bude littafin TSATSUBA mun karanta wata kalmar tsafi guda
daya wadda ke shafin tsakiya , yake wannan sarauniya mai daraja kiyi sani
cewa bukatarki kusan iri daya ce da tamu amma ni ba zan
iya barin yata shumaira tayi wannan tafiya ba
tunda ita kadai gareni a wannan duniya kinga nidai tsufa ya riskeni mahaifiyar tama gata nan ta fara manyanta , yau idan babu ita shikenan zuri armu gaba daya ta shude kenan tunda
mu ne kadai mukayi saura
kafin tsoho Imshal ya gama rufe bakinsa sai jaruma shumaira ta mike zumbur ta durkusa bisa guiwoyinta a gabansa ta rike hannayansa biyu
a lokacin da hawaye ya zumo mata tace ya kai abbana kayi
sani cewa ko ka barni ko ka hanani yin wannan tafiya watarana sai mutuwa
ta daukeni
shin ka manta cewar ka gaya mini cewa dukkan mai nema
yana tare da samu lallai ina son na karya wannan asiri wanda ya gagari
iyayenmu da kakanninmu domin na barwa birninmu
abin tarihin da baza a taba mancewa dashi ba ka tuna cewa har yanzu sarautar
sarkin daji tana hannun zuri ar babban makiyinmu boka zarratu tunda mu mun kasa
zama a cikin gari
lallai ta kowanne hali saina kwato mana yancinmu na dawo mana
da sarautarmu mun koma mun zauna a cikin
wannan gidan sarauta namu na sarkin daji wanda
kai kanka rabonka da shi tun kana jariri ina mai rokonka daka bani wannan dama ayi
wannan tafiya dani
da izinin iyayenka dake kwance cikin kabari saina sami nasara
na kwato mana
yancinmu.
koda jaruma shumaira tazo nan a zancenta sai tsoho Imshal
da matarsa larisa suka kamu da tsananin tausayinta suka
rungumeta sunamasu fashewa da kuka itama
saita tayasu kukan
Al amarin da ya karya zuciyar sarauniya larbisa
kenan a karon farko a rayuwarta taji tausayin wani
ya kamata har itama idanunta suka ciko da kwalla kuma ba komai bane
ya janyo hakan ba face ganin matsalar ta tazo
iri daya da tasu
Saida tsoho Imshal da larisa suka dan jima a kankame
da shumaira sannan imshan ya janye jikinsa
daga cikin na shumaira ya
dubeta cikin Alamun tsananin damuwa yace yake
yata hakika kinzo mini da babban Al amari wanda ya dugunzuma hankalina kuma wanda a halin yanzu ba zan iya yanke
hukunci ba a kansa lallai ina bukatar ki bani lokaci daga nan zuwa gobe muyi
tunani da nazari akan al amarin nida mahaifiyarki
koda jin wannan batu sai hankalin sarauniya larbisa ya dugunzuma
ainun fiye da ko yaushe domin ta fara tunanin
cewa tsoho Imshal ba zai yarda da wannan tafiya
ba don haka duk shirinta ya rushe,
Nan dai shumaira ta mike tsaye ta kama hannun
sarauniya larbisa ta jata suka fice daga cikin falon
duk su biyun jikinsu a sanyaye, lokacin da dare ya sakeyi
sai shumaira da sarauniya larbisa suka kasa barci saboda
zulumi da fargabar sakamakon shawarar da iyayen
shumaira zasu yanke akan wannan tafiya suna cikin wannan hali ne shumaira ta mike
zaune daga kan gadonta ta dubi larbisa tace
ranki ya dade ni fa tunda ina cikin zulumin abinda
zai biyo baya ba zan iya barci ba, ina mai tabbatar miki
da cewar rayuwata gaba daya yanzu babu wani
abu da ya shiga raina sama
da yin wannan tafiya koda kuwa ina da yakinin zan
mutu
nafi son na mutu jaruma akan na mutu raguwa a
cikin rashin yanke wannan bakin ciki na zuri armu
saboda haka yanzu zanje na gana da mahaifina domin naji
hukuncin da ya yanke
koda gama fadin hakan sai shumaira ta mike tsaye ta fice daga cikin dakin
ita kuwa sarauniya larbisa saita bita da kallo kawai
cikin alamun tsananin damuwa, jikinta na tsuma
zuciyarta na dukan uku uku tana fargabar abinda zaije
ya dawo
lokacin da shumaira ta isa falon mahaifinta saita iske
mahaifiyarta zaune akan kujera tayi tagumi kanta a sunkuye tana zubar da hawaye
shi kuwa tsoho Imshal yana tsaye yana kai kawo duk
su biyun fuskokinsu na nuna alamun tsananin damuwa da fargaba
koda shumaira taga iyayenta a cikin wannan hali sai
hankalinta ya dugunzuma ainun taji kamar ba zata iya tunkararsu da maganar ba
tunda su ma suna cikin irin halin da take ciki
kawai sai shumaira ta juya da nufin ta koma izuwa dakinta
take tsoho Imshal ya kira sunanta shumaira , kada ki koma kizo mu tattauna wata muhimmiyar
magana
koda shumaira ta juyo tana mai amsa kiransa
saita ga fuskar tsoho Imshal ta juye izuwa murmushi
da annuri
cikin mamaki shumaira ta tunkari mahaifin nata
ta iso daf dashi yadda har suna iya jin numfashin juna
tsoho Imshal ya dafa kafadar shumaira yace, yake
yata ki kwantar da hankalinki kiyi sani cewa ba zan iya hanaki
yin wannan tafiya ba saboda ganin muhimmancinta
Amma akwai sharadi guda daya da zamuyi dake
wannan sharadi kuwa shine ba zamu yarda kiyi
wannan tafiya ke kadai ba sai tare damu
koda jin wannan sharadi sai idanun shumaira suka
zazzaro hankalinta ya dugunzuma ainun ta dubeshi
tace haba yakai Abbana tayaya zanyi wannan tafiya tare daku alhalin girma ya
kamaku baku da karfin jiki gami da jarumtaka irin tawa
koda jin wannan batu sai tsoho Imshal ya sake yin
murmushi a karo na biyu yace Ashe kin manta da cewar
nine na koya miki yadda ake farauta a cikin daji
da yadda ake yin yaki a cikin dandazon mayaka??
To kiyi sani cewa ko giwa ta fadi tafi gaban a dasa mata
wawa malami har abada malami ne akan dalibansa
ina mai tabbatar miki da cewa ni da mahaifiyarki
zamu baku gagarumar gudumawa a cikin
wannan tafiya yadda zaku sha dumbin mamaki saboda
haka ki koma dakinki ki gayawa sarauniya larbisa cewar
ku fara shirin
wannan tafiya tun a daren yau amma ina son ta turo
mini babban abokin tafiyarta tsoho Huzallatul marwas
yanzu take kuma ta gaya masa cewa ya taho tare da jakar
sihirinsa shumaira ta juyo jikinta a sanyaye ta koma izuwa can
turakarta zuciyarta cike da zulumi. Fargaba da tsananin damuwa
lokacin da shumaira ta isar da wannan sakon mahaifinta
izuwa ga sarauniya larbisa ta firgita kuma ta kamu da tsananin mamakin yadda
akayi tsoho Imshal ya san da batun jakarsa ta sihiri
alhalin bata gabatar dashi ba a wajansam nan take larbisa ta gano cewar lallai
shi ma tsoho Imshal ya cika boka masanin abinda ke boye
ba tare da boye komai ba sarauniya ta tashi ta tafi izuwa masaukinsu tsoho
huzallatul marwas ta jashi izuwa gefe daya ta sanar
dashi sakon tsoho Imshan, koda jin hakan sai huzallatul
marwas ya bushe da dariya Al amarin da ya baiwa
larbisa mamaki kenan kuma ranta ya baci ta dubeshi
a fusace tace menene kuma abin dariya a cikin wannan Al amari??
Huzallatul marwas ya numfasa yace
hakika mahaifim shumaira ya cika hatsabibin boka domin ban taba zaton zai gano
da batuna ba a cikin wannan tawaga taki bare ma har ya san da batun jakar sihirinsa
babu komai ki kwantar da hankalinki yanzu jamuje na riskeshi domin
naji dalilin da yasa ya bukaci ganina,
koda gama fadin hakan sai tsoho huzallatul marwas
ya yunkura da nufin ya juya ya nufi hanyar da zata kaishi inda turakar tsoho Imshal yake
Tsulum sai suka ga aljani subauratu ya baiyana a sama daf da fuskarsa yana mai
kyalkyala dariya lokaci guda kuma sai ya hade fuskarsa
ya risina ga huzallatul marwas yace ya shugabana
kayi sani cewa zuwanka kai kadai izuwa ga tsoho Imshal yana da hadari don haka duk yadda za ayi ka tafi tare da sarauniyarka
komai rintsi da tsanani kada ka yadda kayi wata magana dashi sai sarauniya na kusa tana sauraronka, kafin tsoho Huzallatul marwas ya budi baki ya tambayi subauratu dalilin
da yasa ya bashi wannan shawara tuni subauratu ya bace bat,
sai jin motsinsa yayi a cikin jakarsa ta sihiri
Huzallatul marwas ya dubi larbisa yace ranki ya dade menene
abinyi? Larbisa tayi murmushi tace yadda
Aljani subauratu ya fada haka za ayi, nan take suka
dunguma su biyun suka koma can turakar tsoho Imshal inda suka
iskeshi tare da yarsa shumaira da matarsa larisa a zaune
koda Isham yaga larbisa ta biyo tsoho huzallatul
marwas sun dawo tare sai ya murtuke fuskarsa tamkar an aiko masa da sakon
mutuwa ya dubi larbisa yace ai sai ku bamu wuri
don ina son na gana da huzallatul marwasu
koda jin haka sai huzallatul marwas ya matso gaban Isham ya mika masa hannu
suka gaisa sannan yace yana daga cikin sharaddan tafiyarmu
nida sarauniya cewar komai tare da ita zanyi, ba zan boye mata komai ba
koda jin wannan batu sai jikin tsoho Isham yayi sanyi kawai
sai ya kyalkyale da dariya ya rungume huzallatul marwas yana mai cewa lale marhaban
da babban aboki ma abocin hikima da hangen nesa shi kenan kuje ku
kwanta domin ku dan rintsa kafin gari ya waye mu kama hanya
dajin haka sai larbisa da tsoho Huzallatul marwas marwas suka dubi junansu suka yi murmushi nan take suka yiwa su tsoho isham sallama suka
juya suka fice daga cikin falon,
fitarsu keda wuya sai jaruma shumaira ta dubi isham fuskarta cike da alamun tsananin
damuwa tace ya kai abbana yanzu ta yaya kenan zamu san shafin da ya kamata mu karanta
a cikin littafin tsatsuba domin kawai da wannan
matsala tamu tunda gashi sarauniya larbisa taki yarda ta barka ka kebe da tsoho huzallatul marwas bare
har kuyi wannan yarjejeniya damu ka tsara?
Koda jin wannan batu sai tsoho isham ya bushe da dariya yace ai maso abinka
ya fika dabara kuma masu iya magana sunce samu yafi iyawam idan har muka
mallaki littafin tsatsuba a hannunmu munyi
mai wuyar da sannu zamu gano duk wani
sirri dake cikinsa
da jin wannan batu sai hankalin jaruma shumaira ya kwanta
zuciyarta ta cika makil da farin ciki amma da ta tuno irin
mugun hadarin dake cikin tafiyar da zasuyi kuma gashi tare da iyayen nata za ayi
wannan tafiya sai hankalinta ya
dugunzuma ainun ta rasa abinda yake yi mata dadi
haka dai ta yiwa iyayen nata sallama cikin sanyin jiki
ta tafi izuwa turakarta
kashegari kuwa tun kafin Alfijir ya keto kowa ya gama shirin
tafiya nan take aka hau dawakai aka kama hanya aka nausa cikin daji tsoho huzallatul marwas, sarauniya larbisa da sadauki humaisu ne akan gaba
jaruma shumaira da iyayenta kuwa sune a karshe domin
dakarun larbisa ma suna gabanta
bayan an shafe sa a guda ana tafiya sai tsoho
huzallatul marwas ya dubi sarauniya larbisa a
lokacin da suke tafiya kafada da kafada bisa dawakansu
yace ya shugabata kiyi
sani cewa ruwa baya tsami banza lallai akwai wata hujja mai karfi
wacce tasa iyayen shumaira suka siyar da rayuwarsu wajen
biyomu a cikin wannan tafiya mai hadarin gaske.
Yayinda sarauniya larbisa taji wannan batu sai tayi murmushi tace koma menene
a ransu ai zamu gani tunda dai sannu sannu bata
hana zuwa sai dai a dade ba a jeba
.
Kamar yadda sannu sannu ba zata hana
ci gaba da rubuta muku wannan littafi ba saidai
a jima ba ajeba..
A nan nake cewa sai Allah ya kaimu Gobe domin
jin Yadda zata kaya a cikin wannan Littafi Na tsatsuba
TSATSUBA
Littafi Na Biyu (2)
Part C.
.
YAYINDA SARAUNIYA larbisa taji wannan batu
sai tayi murmushi tace koma menene a ransu ai
zamu gani tunda dai sannu sannu bata hana
zuwa
sai dai a dade ba aje ba, Tsoho Huzallatul
marwas ya
gyada kai yace tabbas zancenki Dutse ne
Larbisa tace wai shin yanzu ina Muka dosa ne?
Huzallatul marwas yayi murmushi yace in banda
abinki
ya zaki tambayi kaza hanyar rafi, ni kaina ina bin
jagorancin jaka ne, duk inda naga ta nuna nan
nake
bi damu
Amma ai idan baki manta ba zamuje neman
jaruma
larifat ne wacce zata yi mana jagora a cikin
daji na biyu wanda shine dajin Ujurul majnun
ki kwantar da hankalinki don nasan cewar ba
zamu dauki wani dogon lokaci ba muna tafiyar
zamu riske ta
bisa taimakon wannan jakar sihiri nawa.
Koda jin haka sai Larbisa tayi shiru bata kara
cewa
komai ba
haka dai aka ci gaba da wannan tafiya ba dare ba
rana
babu abinda yake sawa a tsaya ko a yada zango
face
gajiya ko yunwa da kishirwa, har tsawon kwana
uku
sannan suka iso wani babban birni mai kyau
gaske wanda aka kawatashi da gine gine masu
kyau da kawa
ita kanta sarauniya larbisa sai da wannan birni
ya birgeta ta raina kyawun nata birnin harma
tana
cewa a cikin ranta lallai duniya da fadi hakama
abin cikinta a iya tunanin sarauniya larbisa ba za
a taba samun birnin da
yafi nata girma da kawatuwa ba a duniya da yafi
nata
girma da kawatuwa ba a duniya amma sai gashi
tun
kafin ma tafiya tayi nisa ta fara ganin cewar ba
haka
bane
Tun daga nesa da masu gadin kofar birnin suka
hango
tawagar sarauniya larbisa sukaga alamar cewar
manyan mutane ne masu daraja sai suka bude
musu kofada sauri har daya daga
cikinsu yayi musu jagora izuwa fadar birnin
tun akan hanya kafin a isa fadar sai jaruma
shumaira
ta matso kusa da larbisa ta dubeta tace to wai
shin mu
yanzu menene yashigo damu cikin wannan
gari alhalin mun zo ne neman jaruma larift kuma
ga
yadda aka bayar da labarinta ba zata yi rayuwa
ba
a cikin gari sai dai a daji?
Koda jin wannan batu sai sarauniya larbisa tayi
murmushi tace ai da dan gari
akanci gari, yanzu idan muka ce zamu tafi
neman jaruma larifat
bamu san a cikin dajin da take ba amma da zarar
mun shiga cikin birnin zamu sami labarin inda
take
wata kilama mu sami karin haske akan yadda
zamu tunkareta ba tare da mun fuskanci
wata matsala ba
koda shumaira taji wannan batu sai tayi ajiyar
zuciya tayi shiru bata kara cewa komai ba...
Fadace kasaitacciya abar kwatance domin
lokacin
da aka shigo dasu sarauniya Larbisa cikin fadar
sai gaba
dayansu suka kama kalle kalle suka zama kamar
yan kauye
saboda ganin irin kyan fadar da kawatuwarta
A wannan lokaci ne larbisa ta dada tabbatar
da cewar gaba da gabanta Aljani ya taka wuta
Ita dai a iya saninta a can nahiyoyin dake
bangarenta
babu wata kasa mai
girma da karfin Arziki kamar kasarta don haka sai
ta
fara tunanin cewa a duniyar ma gaba daya ba a
taba samun kamarta ba amma a yanzu
da ta tsinci kanta a cikin wannan birni da
wannan
bakuwar fada sai ta karyata kanta, wani
kyakkyawan
saurayi ne na kwatance bisa karagar mulkin
wannan fada ya yi babbar shiga ta
alfarma irin wacce attajiran sarakai da suka
gawurta
ne kadai ke iya yinta
domin tufafin dake jikinsa darajarsu takai jarin
wani mashahurin attajirin, hatta takalminsa da
kwagirin dake
hannunsa na lu'u lu'u ne a yatsun hannayensa na
hagu da dama akwai zobuna guda shida kuma
duk na
zinare ne masu tsadar gaske, shi kansa rawanin
dake
kansa da falmaran din dake jikinsa da zaren
zinare
a aka dinkasu
koda jaruma shumaira da sarauniya larbisa
sukayi Arba da wannan sarki sai kyawunsa da
kwarjininsa
ya dimautasu sukaji nan take sun kamu da
tsananin sonsa
Hakika babu wata 'ya mace da zata ga wannan
sarki
bataji ta kamu da tsananin sonsa ba, saboda
baiwar
da allah yayi masa ta kyau da arziki, gashi idan
yayi ado sai kaga tamkar dawisu ne
koda shigowar su sarauniya larbisa cikin fadar
sai sarkin ya dubesu sau daya ya kau da fuska
kuma
babu annuri akan fuskar tasa, Al amarin da ya
dugunzuma
hankalinsu kenan domin a tunaninsu kyawunsu
kadai zai iya sawa sarkin yayi marhaban dasu
bare
kuma ga matsayi na sarautar larbisa, cikin sanyin
jiki suka karasa kusa da karagar mulkin sukayi
cirki
cirko
caraf sai tsoho isham ya zube kasa gaban sarki
ya
kwashi gaisuwa sannan ya gabatar da sarauniya
larbisa da jaruma shumaira ya kara da cewa
yakai wannan sarki mai daraja kayi sani cewa ba
wani abu bane ya kawomu birninka ba face
neman
jaruma Larifat ma abociyar basira da hangen
nesa
saboda muna son tayi mana rakiya izuwa dajin
ujurul majnun domin biyan
wata muhimmiyar bukata ta sarauniya Larbisa.
Koda jin wannan batu sai sarkin ya mike tsaye
zumbur
daga kan karagarsa ta mulki. Fuskarsa cike da
annuri
ya kama kafadun tsoho Isham ya tashe shi tsaye
ya jashi har kan karagarsa suka Zauna tare, su
sarauniya larbisa ma sai yasa aka
basu kujeru na alfarma suka zauna sannan aka
kawo
musu abinci da abin sha na alfarma suka kama
kimtsa
cikinsu suna masu murna da mamakin yadda
akayi
nan da nan ra'ayin sarkin ya sauya bisa jin
abindake
tafe dasu
sai da kowa ya gama kimtsawa ya sami natsuwa
sosai
sannan kyakkyawan sarkin ya dubi tsoho isham
yace yakai wannan dattijo kayi sani cewa yau
shekara
bakwai kenan ina fama da tsananin so da begen
wannan jaruma larifat amma ko sau daya bata
taba
kallona ba tayi mini murmushi bare ta karbi tayin
soyayyata sai dana kwanta rashin lafiya sau
bakwai
sakamakon ciwon sonta da ya kayar dani amma
bata
taba zuwa ta dubani ba ni da ita bata taba yi
mini magana
ba kuma bata taba amsa gaiyatata ba izuwa
wannan gidan sarauta
Lokacin da na dameta da aika manzanni da
kyaututtuka
iri iri na duniya sai ta tattaro duk abinda nake
bata na tsawon shekaru bakwan ta dawo mini
dasu
gami da wasika
A cikin wasikar ne ta shaida mini cewa na daina
bata lokaci
na da tunanina a kanta
domin ta daukarwa kanta alkawari cewar ba zata
taba yin aure ba ko soyayya
har sai tayi gagarumin abin gwanintar da wani
bai taba yi ba a duniya
lokacin da naji wannan batu sai na kamu da
tsananin
bakin ciki kuma na fashe da kuka na takaici
domin banga ranar da larifat zata cika wannan
buri
ba
daga wannan rana ne nima na yi alkawarin na
daina cin abinci mai dadi na daina kwanciya a
wuri
mai kyau kuma na daina murmushi da sukuni
har izuwa karshen rayuwata face a ranar da naji
cewar ta sami damar da zata cika burinta
A tsawon shekaru bakwai da suka gabata
wannan dama bata
samu ba sai yanzu naji kunzo mini da wannan
batun
na zuwa kogon Kitabul sihir inda littafin tsatsuba
yake sai naji
a jikina cewar lokacin samun yardar larifat yayi a
gareni
domin a yanzu ne zata iya yin jarumtakar da har
abada
ba za a mance da ita ba a duniya, ko shakka
babu na san cewa
larifat zata karbi wannan
tayi naku domin bata tsoro ko shakkar wani abu
mai rai akan biyan bukatarta, babu wani abu
wanda
zaku iya biyanta da shi domin ta wuce daku ta
cikin
dajin ujurul majnun face kwadayin cika na ta
burin
ba wani abu da yake burge jaruma larifat a cikin
wannan duniya, saboda ta rasa iyayanta yan
uwanta da dukkan danginta
bisa wannan daliline ta kebe kanta daga cikin
mutane
ta koma cikin daji da zama inda ta zabi ta karasa
sauran
rayuwarta gaba daya
yanzu dai a gajiye kuke, don haka zan sa a kaiku
masauki ku huta washe gari da safe ni da kaina
zanyi muku jagora izuwa dajin Da jaruma larifat
take domin ku gana da ita, ku sanar da ita
bukatar dakuka zo da ita a gareta.
Amma ina neman wata alfarma guda daya a
wajanku?
Alfarmar kuwa itace ina son nima nayi muku
rakiya a cikin wannan tafiya domin idan kuka tafi
kuka barni fargaba tunani da begen halin da
larifatke ciki zai iya jefani cikin wani mugun hali
koda sarki AYUBUL HASNU yazo nan a zancensa
sai kowa
ya cika da mamaki musamman sarauniya larbisa
da shumaira
Kai ni kAina saida na cika da mamakin
wannan sarki
sarauniya larbisa ta dubi sarki Ayubul hasnu cikin
mamaki tace yakai wannan sarki mai daraja kayi
duba izuwa wannan daula da kake ciki ka dubi
girman kasarka da tarin arzikin dake cikinta ka
sani cewa
akwai mata da yawa masu kyau a sassan duniya
wadanda zaka iya mallakarsu da karfin dukiyarka
da mulkinka saboda me yanzu zaka siyar da
rayuwarka don baiwarka?
Lokacin da sarki ayubul hasnu yaji wannan
tambaya daga
bakin sarauniya larbisa sai ya bushe da dariya
kamar ba zai daina ba

Please Login or Register in order to submit comment