Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kallonta yama kara gaba yaki yarda su jera tare
yaci gaba da sha aninsa kawai
HAKAN NE YASA ITAMA jikinta yayi sanyi kuma taji a
zuciyarta cewar abinda ta yiwa tsohon bata kyauta ba don
ya fadi gaskiyaamma saboda girman kai irin na
masu sarauta sai ta basar taki yarda tayi masa magana har suka shafe yini na biyu aka
yada zango na biyu
A cikin wani daji mai yawan bishiyoyi da duhuwoyi
tabbas wannan daji yana da kwarjini gami da ban tsoro
domin komai jarumtakar mutum idan ya tsinci kansa
a cikinsa dole ne ya san cewa ya shigo wuri ma hadari
sunana kenan daga zauran labarai
bayan an kafa tantuna
sai sarauniya larbisa ta tara gabadayan
dakarunta ta shaida musu dacewa kada dayansu ya kuskura
yayi barci domin akwai alamun mugayen abubuwa
a cikin wannan daji saboda haka wani abun zai iya
kawo harin sumame a yayin da dare yayi
koda jin wannan batu sai shugaban dakarun nata wanda ake kira da
sadauki muhairu ya risina ya ce
ya shugabata kiyi mini izini mu kewaye sansaninmu
da dogayen manyan itatuwa domin samar da cikakken tsaro kinga indai wani abune
mai rai zai kawo mana harin ba zai samu damar afko
mana ba kai tsaye
koda jin wannan batu sai sarauniya larbisa tayi
murmushi tace hakika kazo da shawara mai kyau amma
idan ta nine ban damu da sai an kewaye sansanin ba
sai dai saboda ku da kuyangina koda gama fadin haka
sai sarauniya larbisa ta juya ta tafi izuwa cikin tantina
nan take sadauki muhairu ya umarci wadansu daga
cikin dakarunsa dasu je su saro manyan bishiyoyin da za a kewaye su
haka ramukan da za a sanya itatuwan
Nan take kuwa dakaru suka kama aiki ba lalaci a lokacin
dasu kuma kuyangi suka kama aikin dafa abinci
ai kuwa kafin magariba tayi an kammala dukkan aikin
ya zamana cewa an kewaye gaba dayan sansanin da manyan
bishiyoyi yadda koda giwaye ne suka zo sai sun sha wahalar gaske kafin su
sami damar ture bishiyoyin da aka kewaye sansanin
bayan anci abinci sai dakaru suka ki su kwanta sukayi
lambo suna masu dana kwari da bakansu masu
takubba ma suka zauna a cikin shiri kuma aka
kashe dukkanin fitilun iccen dake ci a sansanin ko ina yayi
duhu dundum
sarauniya larbisa kuwa kayan yakinta ta sanya ta zare takubba guda biyu
tayi lambo a gaban dakarun nata saboda ita a jikinta
ta san cewa lallai ba za a rasa wani mugun abu ba
a cikin wannan daji kuma lallai abin zai iya kawo
hari a koda yaushe
har dare ya raba ba a ji wani bakon motsi ba
a cikin dajin
Al amarin da ya karya zuciyar dakarun sarauniya
larbisa kenan suka fara tunanin cewar babu wani
mugun abu da zai kawo hari dama a wannan lokaci da
yawa daga cikinsu sun fara hamma saboda jin barci
koda sarauniya larbisa ta lura da halin da dakarunta
ke ciki sai ta dubi sadauki muhairu wanda yayi kwanciyar
lambo kusa da ita tace maza ka gayawa sauran yaranka
cewar duk wanda ya kuskura yayi gyangyadi na dakika daya ni zan sareshi da hannuna
Nan take muhairu ya radawa daya daga cikin wannan batu
shima sai ya radawa na kusa dashi a haka sauran gaba dayan
dakarun suka sami wannan sako bayan faruwar
hakan da kamar nisan dakika dari uku sai kawai
kawai su sarauniya larbisa suka fara jiyo wani irin
gurnani mai yawan gaske daga can nesa gurnani ne na wadansu irin halittu masu yawan
gaske kamar na dodanni ko manyan birirrika
inka dauke sarauniya larbisa da sadauki muhairu babu
wanda hantar cikinsa bata kada ba a sansanin
shikuwa tsoho huzallatul marwas kuwa fitowa yayi daga
cikin tantinsa ya tsaya a tsaye yana mai rike kugunsa yana
kallon can bakin kofar sansanin don yaga abinda zai faru
alhalin kowa ya sami wuri ya buya a wannan lokaci
kwatsam sai yaji jakarsa ta sihiri ta bude aljani subauratu ya baiyana a sama
dai dai fuskarsa yana mai kare hancinsa da hannu sakamakon
iska mai kare hancinsa da hannu sakamakon iska mai karfi dake
kadawa yace yakai mai gidana me kake takama dashi har
da zaka fito ka tsaya a cikin wannan sansani alhalin kana gani cewar
jaruman ma da suka yarda da kansu kwanciya sukayi
a kasa sukayi
lambo ko kuwa kunnenka baya jiyo sautin gurnani halittun dake shirin kawo farmaki
izuwa wannan sansanin?
Lokacin da tsoho huzallatul marwas ya ji wannan
tambaya sai ya bushe da dariya sannan yace haba yakai subauratu in banda
abinka akan wane dalili tsoho zaiji
tsoron mutuwa
musamman ma kamata wanda bashi da kowa kuma bashi
da komai
ka tuna fa cewa ni yanzu na rasa babban masoyina
wato mahaifina kuma na rasa uwata tun ma ina jariri
na rabu da yan uwana na jini wadanda a halin yanzu
ma bani da tabbacin suna raye ko sun mutu
idan ma suna raye basu da wani amfani a gareni tunda sun kasance manyan
makiyana a doron kasa
lokacin da tsoho huzallatul marwas yazo nan
a zancensa sai Aljani subauratu ya dubeshi yayi murmushi yace
ai yan uwanka suna nan a raye duk su hudun
amma a halin yanzu duk duniyar nan babu matsafan da
suka fisu
karfin sihirin tsafi amma hadin kansu ya watse sun zama abokan gabar juna
ba don komai ba sai saboda kowannansu yana
son ya mallaki littafin tsatsuba shi kadai saboda ya mulki
komai da kowa na cikin wannan duniya
koda jin wannan batu sai mamaki ya kama huzallatul
marwas kuma hankalinsa ya tashi ya dubi Aljani
subauratu cikin alamun tsananin damuwa yace kai kuwa
menene dalilin da yasa tuntuni baka labarta mini
wannan labari ba tun ina da sauran kuruciyata da
karfin jikina ba yanzu ba da shekaruna suka haura hamsin?
Koda jin wannan tambaya sai
Aljani subauratu ya kyalkyale da dariya sannan yace ai
gaya makan bashine wani amfani tunda ba zaka iya
yin komai ba akan lamarin dolene ka jira har zuwa lokacin
da zaka sami daukakar da tafi tasu
kafin huzallatul marwas ya budi
baki ya kara cewa wani abu
sai kawai sukaji kasa ta kama
girgiza tamkar zata tsatstsage su rufta cikinta
kuma sai gurnanin da suke jiyowa a can nesa ya kara
kusantosu sosai
bayan kamar dakika hamsin sai sukaji gurnanin
ya cigaba da wanzuwa a lokacin da yake kara kusantosu
suna nan a tsaye sai kawai suka ga dandazon cincirindon tarin
birirrika sun durfafo inda suke
kai tsaye
yayinda huzallatul marwas yaga haka sai yayi maza ya
mayar da Aljani Subauratu cikin jakar sa
a lokacin da sarauniya larbisa ta fito daga cikin tantinta
suma sauran dakaru haka
suna fitowa ne sukayi Arba da tahowar wadannan
birirrika nanfa hantar cikin kowa ta kada Amma banda na sarauniya larbisa saboda ita tasan cewa Jarumar gaske ce
amma kuma matsalar itace basu da zafin nama da jarumtakar
da zasu iya yakar wadannan birirrika
nan take sarauniya larbisa taji nadama tazo mata bisa bitowar da tayi neman
wannan littafi na tsatsuba tunda gashi tun ma tafiyar
batayi nisa ba zata rasa rayuwarta....
Wow
nima A nan zan dakata sbd ganin wadannan
birirrikan
kuma nake cewa sai Allah ya kaimu gobe zan ci gaba
TSATSUBA
Littafi Na Daya (1)
Part D.
.
Nan take sarauniya larbisa taji nadama tazo mata
bisa fitowar da tayi neman wannan littafi na tsatsuba tunda gashi tun ma tafiyar
batayi nisa ba zata rasa rayuwarta, gama aiyana hakan keda wuya sai wani
daga cikin birirrikan ya shammaceta ya gabza mata
naushi a haba saboda karfin
dukan sai da tayi sama tamkar an janyeta da majajjawa
koda shugaban dakarun nata sadauki Humairu ya hango
shugabarsu a can sama
kuma ya tabbatar da cewa idan ta fado kasa cikin wadannan
birirrika ta zama gawa sai ya
falfala da gudu
izuwa kan birirrikan yana mai kwalla ihu
Ai kuwa sai birirrikan suka raba hankulansu biyu
ya zamana cewa wasunsu sun daga kawunansu
sama suna jiran sarauniya larbisa ta fado cikinsu su dasa
mata wawa
wasunsu kuma sai suka ruga izuwa kan sadauki Humaisu
yayinda ya rage saura yan dakiku kadan larbisa ta fado
kan birirrikan shi kuma humaisu yayi karo dasu sai kawai humaisu
da larbisa sukaji an suresu
anyi sama dasu cikin tsananin gudu na ban al ajabi tamkar
za a taba hadari dasu
kawai sai gani sukayi an diresu a tsakiyar sansaninsu
nan take Aljani subauratu ya baiyana tsulum a gabansu yana mai kyalkyala dariya
ya risina ga tsoho huzallatul marwas yace
yanzu na cecesu ya shugabana amma kayi sani cewa
anan ne kawai zan iya taimakonku amma da zararr mun kara gaba sai dai ku
ceci kanku
kafin larbisa ko tsoho huzallatul marwas dayansu yace wani
abu tuni Aljani subauratu ya rikide ya zama guguwa guguwar ta tafi da tsananin gudu
irin na tauraruwa mai wutsiya ta fada cikin dandazon birirrikan
kawai sai gani akayi kawunan birirrikan suna guntulewa suna faduwa kasa
gangar jiki na bingirewa sai dai kaga jini na tsiri da feshi
daga cikin wuyansu
koda birirrikan suka ga suna ta mutuwa kuma sun rasa
wanda yake yi musu wannan barna sai suka haukace suka rinka ruri da kururuwa
suna kaiwa iska duka amma duk a banza domin dada
ragargazarsu ake yi suna zama gawa tabbas wuya ba dadi kuma idan kaji
ana cewa ga ki gudu to tabbas sa gudu ne baizo ba
lokacin da wadannan birirrika sukaga sun kasa kare kansu
daga sharrin guguwar da ta addabesu sai suka
fara juyawa da baya a guje suna kokarin komawa
inda suka fito amma sai guguwar ta rinka kure musu
gudu tana ci gaba da cire musu kawuna har saida ya zamana cewa babu sauran daya daga cikinsu wanda ya
tsira da rayuwarsa
A wannan lokacine dakarun sarauniya larbisa suka fara firfitowa daga cikin
wuraren da suka buya cikin alamun kunya
suna masu sunkui da kai kas
cikin fushi sadauki Humaisu ya rufesu da fada yana
kokarin hukuntasu kawai
sai sarauniya ta tari numfashinsa tana mai
kallonsa cikin murmushi tace kada ka hukunta su domin
banga laifinsu ba bisa guduwar da sukayi suka buya
kai kanka ai kasa tarar birirrikan kayi sai da kaga zan hallaka sannan kayi kundunbala
ka rugo domin ka kawo mini dauki hakika kayi gagarumar gwaninta wacce
ta burgeni don haka idan mun koma gida zan yi maka wata gagarumar kyauta wacce
ban taba yiwa wani mahaluki ba
koda jin wannan batu sai farin ciki ya lullube sadauki
Humaisu ya zube kasa bisa
guowoyinsa a gaban larbisa yana godiya nan dai larbisa ta bayar da umarnin aje
a kwanta
ba tare da wani bata lokaci ba kuwa kowa yaje ya kwanta cikin kwanciyar hankali ba tare da fargabar komai ba.
Kashe gari kuwa da sassafe aka kimtsa bayan an yi kalaci
sai sarauniya larbisa tsoho huzallatul marwas tace Ljaninka ya gaya mana cewar tafiyar yini biyu da rabi zamuyi mu
riski dajin da jaruma shumaira take tabbas yanzu mun shafe tafiyar yini daya kunga kenan saura ta yini daya jal a gabanmu shin akwai sauran
wani mugun abune da zamu hadu dashi kafin mu isa
dajin da jaruma shumaira take?
Koda jin wannan tambaya sai tsoho huzallatul marwas
da sadauki Humaisu suka dubi juna sukayi
shiru
larbisa ta dubi huzallatul marwas cikin fishi tace ai kai ne
ya kamata ka bani amsar wannan tambaya
huzallatul marwas yayi ajiyar numfashi sannan yace ya shugabana aini a ganina
yanzu bai kamata kiyi
shakkar wani abu ba tunda dai gashi mun ga bayan
wadannan mugayen birrirrika saboda nasan cewa abu ne mawuyaci mu sake haduwa da wani mugun abu
wanda ya fisu hadari
koda jin wannan batu sai sarauniya larbisa ta yi murmushi tace tabbas
kazo da magana mai ma ana yanzu kawai saimuci
gaba da tafiya
ba tare da bata wani lokaci ba kuwa aka hau kan
dawakai bayan an debe komai aka ci gaba da tafiya ba sassauci
tsoho huzallatul marwas ne akan gaba yana jagorantar
rundunar, sarauniya larbisa, da sadauki Humaisu na biye
da shi sannan sauran dakarun, Kamar yadda Aljani
subauratu ya fada haka Al amarin ya kasance wato sai da
suka shafe tafiyar rabin yini guda sannan suka iso
wani katon daji mai yalwar
Bishiyoyi, koramai da fadamomi, kai da ganin wannan
daji kasan cewar dajine mai ni'ima irin wanda mafarauta ke
so domin dole ne a samu dabobin daji da tsuntsaye
masu yawa a cikinsa
da shigarsu sai suka hango wani katon garke na
ragon dawa cike da raguna da tinkiyoyi abin
mamaki shine an kewaye garken ne da siraran itatuwan bishiya marasa kwari
wadanda dabbobin zasu iya kakkaryasu su watsu amma kuma dabbobin basu ture
itatuwan ba sun gudu
koda dakarun sarauniya larbisa suka hango garken wannan dabbobi sai suka cika da farin ciki suka
ruga izuwa cikin garken suka dasawa dabbobin wawa
da nufin kowa ya kama iya rabonsa
kwatsam ba zato ba tsammani sai sukaji ana naushinsu
ta sama suna zubewa kasa
duk wanda akayi wa naushi daya sai dai kaga yayi
sama ya fado kasa a matukar galabaice wanda ke naushin nasu kuwa a samansu
yake shawagi kamar tsuntsu har sai da ya gama bazar
dasu kasa sannan ya duro kasa bisa kafafunsa aka
fara kallon kallo tsakaninsa da sarauniya larbisa
ba wani bane yayi wannan gagarumar jarumtakar
ba face jaruma shumaira kai da ganin irin kallon da
sarauniya larbisa ke yiwa jaruma shumaira kai kasan cewa
tana cikin tsananin mamaki
ba wani abu bane yasata wannan mamaki ba face a rayuwarta bata taba zaton cewa zata ga
wata ya mace ba mai kyau kamarta ba amma a yanzu da tayi arba da
shumaira saita raina kanta kuma ta tabbatar da cewar babu abinda
zata fi shumaira dashi face mulki da dukiya
cikin tsananin fishi shumaira ta dubi su larbisa tace
dame kukazo wannan daji shin yan fashine ku ko kuwa
matafiyane wadanda basu san ya kamata ba duk mai
hankali idan ya dubi wadancan dabbobi ya lura da yadda aka
kebancesu yasan akwai mai su duk da cewa kuwa a cikin daji suke kuyi sani cewa wannan daji nawa ne
don haka komai na cikinsa mallakina ne babu wanda
yake da ikon yin farauta a cikinsa face ni
A cikin wannan daji kakana na bakwai yayi rayuwarsa
kuma tun daga zamaninsa kawo i yanzu babu wanda
ya isa ya taba komai a nan sai da izininmu da yardarmu
ku gaya mini abinda ya shigo daku cikin dajin nan
in ba haka ba kuwa sai dai na yakeku koda
jaruma shumaira tazo nan a zancenta sai larbisa ta matso
gaba kusa da ita ta sauko daga kan dokinta ta dubi
shumaira cikin murmushi tace yake shumaira yaga mafarauci Imshal ki yi sani
cewa nice Sarauniya Larbisa mai mulkin birnin
darul kaizul kuma musamman nazo wannan daji naki
domin na gana dake bisa wata muhimmiyar bukata tawa
koda jin wannan batu sai jaruma shumaira ta gyada kai
cikin alamun fishi da rashin yadda tace mu bama mu amala da masu mulki kuma baki
da wani abu wanda zaki iya biyana dashi na taimakeki
saboda haka ina mai
shawartarku daku gaggauta fita daga cikin wannan daji
nawa idan ba so kuke muyi yaki ba koda gama fadin hakan
sai jaruma shumaira ta juya da baya ta nufi wannan
garke na dabbobin ta ta shiga gyara turakan dake
ciki tana daure dabbobin
koda ganin haka sai sarauniya larbisa ta dubi gaba
dayan dakarunta tace duk abinda zai faru tsakanina da jaruma
shumaira kada ku saka baki ko hannu nan take larbisa tabi
shumaira izuwa cikin wannan garken dabbobi ta kama tayata aikin daure dabbobin
Al amarin da ya fusata jaruma shumaira kenan ta kaiwa
larbisa wawan duka da kafa a wuya, cikin bakin zafin
nama larbisa ta kaucewa dukan nan fa suka kaceme da azababben fada suka
wanzu suna masu kaiwa junansu sara da suka cikin
tsananin zafin nama juriya da bajinta
tun da su jarumi Humaisu suke ganin gumurzu na fadan
hannu tsakanin jarumai basu taba ganin fada mai tsananin ban tsoro ba kamar wannan domin gwanintar ta hadu da gwaninta kuma sadaukantaka
tayi kada da kishiyarta
Sai da wadannan jarumai biyu suka shafe rabin sa a suna naushi da bugun juna hannu
da kafa ya zamana cewa sun hadawa junansu jini da majina kuma sun fara galabaita
amma saboda bakar zuciya sunki su daina fadan
amma kuma jaruma shumaira tafi sarauniya larbisa
jure duka domin ita tana iya shanye duka
uku na larbisa amma data naushi larbisa sau daya sai
kaga ta fadi kasa sai dai tayi hanzari ta mike taci
gaba da fadan
Al amarin da ya dugunzuma hankalin su sadauki
Humaisu kenan domin sun tabbatar da cewa idan aka ci
gaba da wannan fada a haka har zuwa wani dan
dogon lokaci shumaira zata iya sumar da larbisa ko
kuma tayi mata wawan rauni Gashi kuma larbisa ta
gargadesu akan kada su
kuskura su shiga cikin wannan fadan
Ana cikin wannan bakin gumurzune shumaira ta shammaci larbisa
ta daka tsalle sama ta doki fuskarta sau uku da kafa take larbisa ta dimauce
kuma ta gigice ko da taji zafin dukan saita zare
takobinta ta kaiwa shumaira sara cikin sa a kuwa ta yanki
shumaira a damtsen hannunta na hagu har wajan ya dan dare kadan jini ya fito
shumaira tayi tsalle gefe daya tana mai yin yar kara
bisa jin zafi da zugin da taji koda ta dubi hannun nata
taga raunin da larbisa tayi mata sai ta fusata ainun itama
ta zaare rantsatstsiyar takobinta ta ruga izuwa kan larbisa
itama larbisa saita rugo izuwa kanta
koda ya rage saura baifi taku uku su hadu ba sai kowacce
ta daka tsalle sama suna masu kai mugun sara
Takubbansu na haduwa saita larbisa ta rabe gida
biyu, A saman shumaira ta doki kirjin larbisa ta fado
kasa a dimauce kafin larbisa ta mike tsaye shumaira ta
duro kanta da nufin ta soka mata takobinta a gefen jikinta......
.
Wow lallai Yakamata nima nakaiwa Larbisa Dauki
Amma bari naje na
dauko Rantsatstsiyar takobina sannan na dawo
.
Anan ne kuma littafin Tsatsuba Na daya yazo Karshe
marubucin yace...
SHIN SHUMAIRA ZATA SAMU DAMAR SOKAWA SARAUNIYA LARBISA TAKOBINTA KUWA?
.
SHINSU SARAUNIYA LARBISA ZASU SAMI NASARAR SAMUN ABOKAN TAFIYARSU?
.
WANE IRIN MASIFU DA TASHIN HANKALI ZASU FUSKANTA KAFIN SU ISA KOGON KITABUL SIHIR?
.
SHIN SARAUNIYA LARBISA ZATA CIKA BURINTA NA MALLAKAR LITTAFIN TSATSUBA?
.
Mu Hadu A Tsatsuba Littafi Na Biyu Domin Jin Ci Gaban Wannan Labari
Daga Mai debe muku kewa a Kullum kuma a ko Yaushe
TSATSUBA
Littafi na biyu 2
Na Abdulaziz sani m gini
Ebook creator::- Shuraih 99%
You can download more hausa novels ebooks At http://shuraih.waphall.com
Zaku iya downloading na wasu littatafan mu amatsayin ebook ta hanyar latsa wannan blue din rubutun www.shuraih.waphall.com

SATSUBA
Littafi Na Biyu (2)
Part A.
LOKACIN DA TAKOBIN SHUMAIRA TA ISA kirjin sarauniya
larbisa sai ta dan soketa a kirji, tana kokarin danna takobin a cikin kirjin nata
kafin larbisa tayi kara sai shumaira taji an daka mata tsawa
daga baya
bisa dole ta fasa dannan takobin izuwa cikin kirjin larbisa,
ta mike tsaye daga kanta ta waigo tayi arba da wanda yayi
mata tsawar, ba wani bane face mahaifinta mafarauci
imshal.
Mafarauci Imshal ya kasance dogon mutum mai kirar sadaukai sai dai girma ya
kamashi sosai domin shekarunsa zasu kai kusan arba in
gaba daya gashin kansa sajensa da gemunsa duk farin
gashine, yana rike da wata doguwar sanda a hannunsa ya rataya kwari da baka
a bayansa
rigarsa, wandonsa da takalminsa dake kafarsa duk anyi
sune da fatar damisa
Koda jaruma shumaira ta hango mahaifinta Imshal sai
ta rugo izuwa gareshi ta dukar daki tana mai nuna
girmamawa a gareshi, A wannan lokaci ne sarauniya
larbisa ta mike tsaye tana mai dafe gefen kirjinta inda
shumaira ta soka mata takobi don har dan jini ya fito
kawai sai sarauniya larbisa ta sunkuya cikin biyayya
ta gaisheda tsoho Imshal. Imshal ya karbi gaisuwar
yana mai kare mata kallo sama da kasa sannan ya karewa
dakarunta kallo ya dubi shumaira yace akan wani dalili kike yaki da wannan mace mai
daraja? Shin bakya ganin alamar cewa mai mulki ce
koda jin wannan tambaya sai shumaira ta dago kai ta
dubi imshal ta ce yakai abbana kayi sani cewa haka kawai
wannan sarauniya tare da dakarunta suka shigo cikin dajin nan suka dasawa
dabbobinmu wawa, bisa wannan daliline na tarwatsa dakarun nata kuma na
umarcesu da su fice daga cikin dajin nan tun kafin fishinmu ya tabbata a kansu
amma saboda naci sai wannan sarauniya ta biyoni
har cikin
garken dabbobi, ni ina ganin cewa kawai ka kyaleni na
gama da ita yanzu domin da ita da yaran nata su gane
cewa ruwa ba sa an kwando bane kuma bakin rijiya ba wajan wasan yaro bane
koda jin wannan batu sai tsoho imshal ya bushe da
dariya sannan ya hade fuska ya dubi shumaira yace
ai ruwa baya tsami banza, shin a farkon bayaninta gareki
bata gaya miki cewar tana da wata bukata ba a wajanki?
Cikin alamun sanyin jiki shumaira tace ta gaya mini cewar
tana da wata bukata a wajena amma saina gaya mata
cewar bata da abinda zata iya biyana da shi don haka babu abinda zan iya yi mata
koda jin wannan batu sai imshal ya gyada kai yace
yarinya kinyi hanzarin yanke hukunci shin bakya
tunanin cewa bukatar da tazo mana da ita wata kila
a sanadinta ne muma zamu fita bakin cikin da ya addabemu
tsawon shekaru bakwai.. Shin kin manta ne
cewar na gaya miki zamu iya nasarar samun abinda
muke nema a cikin wannan shekara idan kin hadu da wadansu bakin
jarumai guda uku?
Koda jin wannan batu sai jikin shumaira yayi sanyi ta
sunkui da kanta kas ta kasa cewa komai daga can kuma sai
ta dago kai da sauri ta dubi tsoho imshal tace amma ai wannan
sarauniya ba ta da kama ko siffa irin ta mutane ukun dakayi
mini bayani
imshal yace hakane amma dai ki tsaya muji abinda ya
kawota wajanmu babu mamaki a sanadin hakan a samu dacewa
cikin nutsuwa
tsoho Imshal ya dubi sarauniya Larbisa yace yake wannan
sarauniya ma abociya kyawu da karjini
wace bukata ce dake tasa har kikayi tattaki kikazo
har wannan daji namu?
Kafin larbisa ta budi baki tace wani abu sai tsoho Imshal ya kara tarar numfashinta
yace
amma kafin kice komai ya kamata ku fara yiwa raunikan
jikinku magani yana gama fadin hakan sai ya bude
wata jaka dake rataye a bayansa ya dauko wani farin
magani me maiko da kauri kamar daskararren nonon shanu
ya mikawa yarsa shumaira yace ungo ki shafa a rauninki
kuma ki shafawa bakuwar tamu
cikin alamun damuwa shumaira ta karbi maganin ta fara shafawa kanta sannan
taje ta zauna a gaban larbisa ta kama shafa mata
fuskarta a daure babu annuri, su kuwa su sadauki Humaisu
sai hankalinsu ya kwanta sukayi murna da ganin yadda
tsoho Imshal ya karbesu hannu biyu, bayan shumaira ta gama sawa larbisa magani
a rauninta sai tsoho Imshal ya dubi larbisa yace yake
wannan sarauniya kiyi sani cewa ni yanzu na karbeku
keda jama arki a matsayin bakina saboda haka yanzu zan
kaiku zuwa gidana domin ku huta in yaso bayan kun nutsu
saimu zauna mu tattauna mu dake idan har zamu iya
taimakon juna zamu iya yarda da buqatarki, idan kuma ke
kadaice zaki amfana damu to sai dai muyi miki fatan
samun nasara ki kara gaba, koda jin wannan batu sai
farin ciki ya lullube sarauniya larbisa , Tare dani mai Rubutu,
ta dubi Tsoho Imshal cikin murmushi tace nayi farin ciki da wannan tayi da
ka bani ya kai Abul Shumaira kuma zuciyata ta
bani cewa nima zan iya baku taimako bisa taku bukatar
Tsoho Imshal yayi
murmushi yace sai an gwada Sannan ake sanin na kwarai
yana gama fadin hakan sai ya kama hannun shumaira suka nufi bayan wani katon
dutse yana mai yafito su larbisaa
Da hannu cikin hanzari larbisa taje ta kama dokinta ta hau
tabi su.
Tsoho Huzallatul marwas ne ya fara bin bayanta sannan
sadauki Humaisu da sauran Dakaru.
Ana zagayawa bayan wannan katon dutse sai kowa
ya cika da mamaki bisa ganin wani dankareren gida
wanda aka ginashi da duwatsun wuta
Gidan katone kuma anyi masa fasali na gidan sarauta
dauke da bangare bangare, banbancinsu da gidan sarauta kawai shine
babu bayi, dakaru da kuyangi mutum daya kacal suka gani a cikin wannan gida
kuma ba wani bane face larisa mahaifiyar Jaruma shumaira
lokacin da larisa ta hango mijinta imshal da yarta
shumaira tare da bakin mutane sai tsoro ya baibayeta
domin wannan shine karon farko a iya zamansu a cikin
wannan daji da ta ga sun zo mata da mutane har
gida don haka bata yarda ta bude kofar gidan ba sun shigo
har sai da suka matso kusa taga cewar babu wata alamar
damuwa akan fuskar mijinta da 'yarta
Ita kanta larisa shekarunta sun kai hamsin da biyu koda
uku amma saboda tsananin kyawun jikin da Allah ya bata mutum ba zai taba zaton
ta kai hakan ba
Da isowarsu tsoho Imshal ga larisa sai ya gabatar da sarauniya
Larbisa a gareta sannan ya gaya mata cewa ita da jama arta bakine masu mahimmanci
cikin farin ciki larisa ta karbi sarauniya larbisa
tana maiyi mata barka da zuwa, nan take aka kaisu
sadauki Humaisu izuwa wani bangare daban na gidan ita kuma larbisa sai tabi jaruma
shumaira izuwa dakinta
Cikin hanzari shumaira ta dafa ruwan dumi ta kaiwa larbisa kewaye ta shiga wanka
kafin larbisa ta fito daga wankan tuni shumaira ta shirya
musu abinci. Larbisa na fitowa daga wankan sai itama
shumaira ta shiga wankan sai da ta fito daga wankan sannan
suka zauna tare bisa wasu kujeru dake karkashin wani
tebur suka fara cin abincin, tsawon yan dakiku da fara cin abincin dayansu baice
uffab ba
Abinda ya daurewa shumaira kai shine ganin yadda larbisa
ta saki jiki take ta cin abincin Alhalin ba abinci ne mai
dadi ba irin nasu na sarakai Abincine irin wanda kowane talaka zai iya ci
musamman mazauna daji
cikin matukar mamaki shumaira ta dubi sarauniya larbisa
tace yake wannan sarauniya menene dalilin da yasa kika saki jiki kike ta cin irin wannan
abinci namu na talakawa alhalin nasan a guzurinki akwai
irin naki abincin da kika taho dashi?
Koda jin wannan tambaya sai sarauniya tayi murmushi tace ai dokar bakunta
itace yin koyi da irin mutanen da ka riska, ni kaina nayi mamakin yadda akayi naji ina
matukar jin dadin wannan abinci naku amma fa babu abinda
ya bani mamaki a yanzu sama dake
koda jin haka sai shumaira ta dago kai da sauri ta dubi larbisa cikin mamaki tace
ke kuma me nayi wanda ya baki mamaki? Larbisa ta ajiye cokalin da take cin abinci
gami da yin ajiyar numfashi sannan tace gani nayi da
farko baki karbeni da wata daraja ba har ma yakata kikayi
kikauda batun matsayina na sarauta yanzu kuma sai
gashi kina yin biyayya da hidima a gareni
Yayin da shumaira taji wannan batu sai tayi murmushi tace ai

Please Login or Register in order to submit comment