Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

daga bisani kuma sai ya
hade fuska tamkar an aiko masa da sakon
mutuwa
nan fa fadar tayi tsit kamar babu mai rai a
cikinta
kawai sai aka ga idanun sarki ayubul hasnu sun
ciko
da kwallah har hawaye ya zubo masa, sarki
ayubul hasnu
ya dubi sarauniya larbisa cikin nutsuwa yace
yake sarauniya larbisa kiyi sani cewa a duniya
babu
wani abu wanda yafi soyayya karfi da hadari
masoya da yawa sun rasa rayuwarsu akan
tafarkin mallakar masoyansu
ba komai ne ya janyo hakan ba face duk rayuwar
da babu masoyi dai dai take da zama a cikin
kurkukun
daurin rai da rai kisan sani cewa ke da jaruma
shumaira duk kun kasance kyawawan matan da
babu kamarsu a duk cikin fadin kasata da
nahiyarmu amma kuma baku kama farcen kafar
jaruma larifat ba a fagen kyau kunga kenan
a yanzu babu wata ya mace da zata iya maye
gurbin
larifat a wajena banda fagen kyau a bangaren
jarumta
kuwa ina mai tabbatar muku da cewa in daku
biyun
nan zaku hada karfinku ku yaketa ba zaku taba
samun galaba a kanta ba
koda jin wannan batu sai sarauniya larbisa da
jaruma shumaira suka bushe da dariya domin su
a
ganinsu ma tatsuniya ce abinda sarki Ayubul
hasnu yake fadi
shumaira ta dubeshi tace aiko yarima RUHAISU
dan sarki ZAIYANU na birnin kufa wanda masana
da masu
bincike suka tabbatar da cewar babu mai karfin
damtsensa da sa arsa idan muka hada karfi nida
larbisa sai mun gama dashi bare wata jaruma
larifat wacce ta
kasance 'ya mace kamarmu
yayinda sarki Ayubul hasnu yaji wannan batu sai
yayi murmushi yace ai
shi kenan inda babu kasa nan ake gardama
Kokowa, ni dai shawarata guda daya ce a gareku
duk abinda zakuyi kyi shi da cikakkiyar hujja
domin banson ku yi irin kuskuren da SADAUKI
HULKAS MAI HULAR LAMSARA YAYI.
Koda jin wannan batu sai sarauniya larbisa da
jaruma shumaira suka
dubi junansu cikin mamaki larbisa ta juyo ta dubi
sarki
Ayubul hasnu tace wanene kuma sadauki Hulkas
mai hular lamsara?
Koda jin wannan tambaya sai sarki Ayubu
hasnu yayi ajiyar zuciya gami da sauke dogon
numfashi sannan yace labari ne mai tsawon
gaske sai dai nayi
iya kokarina na gani ko zan iya gajarce muku
shi...
SADAUKI HULKAS YANA DAGA CIKIN MANYAN
JARUMAN DUNIYA GUDA UKU
wadanda akayi musu lakabi da MAZAN JIYA
jarumai ne wadanda ba a taba yin kamarsu ba
kuma ba za ayi ba
a yanzu da nan gaba domin sun bar abin tarihin
da ba za a taba mancewa dasu ba
sai dai kash
duk su ukun rayuwarsu ta salwanta ne a
tafarkin soyayya
Yanzu dai saiku saurara da kyau kuji wannan
labari domin
akwai dumbin darasi a cikinsa, nan take sarki
AYUBUL HASNU ya shiga basu labari kamar
haka......
.
Hm yanzu ne zamu shiga cikin labarin gadan
gadan
a yayinda zakuji Labarin sadaukin sadaukai
Hulkas mai hular
lamsara
kuma daya daga cikin jaruman duniya Mazan jiya
saboda haka
sai ku gyara zamanku zuwa anjima zanci gaba
da suburbudomuku lbr
February 4 at 11:35 AM
TSATSUBA
Littafi Na Biyu (2)
Part D.
.
NAN TAKE SARKI AYUBUL HASNU YA SHIGA
BASU LABARI KAMAR HAKA.
kimanin shekaru Ashirin da hudu da suka shude a
birnin Romaniya
anyi wani azzalumin sarki mai suna SHARDAS
IBN KAUMIL
sarki shardas ya kasance gawurtaccen jarumin
sadauki mai tarwatsa maza
a filin daga yana da tsananin karfin damtse na
Allah ya isa
don ance ko giwa ya yiwa naushi daya saita fadi
kasa
kisan kai kwace da cin zali kuwa bai maidasu
komai ba
A cikin wata daya yakan shirya dakarun sumame
su kai mamayar bazato izuwa ga ayarin fatake
ko
izuwa ga manyan garuruwan da suke da karfin
arziki
cikin bad da kama su kwato bayi da dukiya da
mata ba
tare da an shaida ko su waye ba, a bisa wannan
halaiya ne ya
addabi gaba dayan kasashen
dake nahiyar gaba daya kuma gashi an kasa
gano
mutanen dake yin wannan barna, babu irin
matakin da sarakuna
basu dauka ba kuma babu irin binciken da bokaye
basuyi ba don gano rundunar
dakarun dake wannan mummunar barna amma
abu ya gagara
babban abin bakin cikin ma shine sarki shardas
ya
tara dukiya mai tsananin yawan da jikokinsa ma
da
tattabakunnansa ma ba zasu iya cinyeta ba
amma duk da haka
bai daina yin wannan fashi
da kwace ba
Masana da masu bincike na wannan zamani sun
tabbatar da cewar duk duniya babu wani sarki da
ya kai
sarki shardas tarin dukiya kuma babu wani gidan
sarautar da yakai nashi girma da kawatuwa,duk
bayin da ya kamo da mata ana boye sune a
gidajen gonarsa
da wani bangaren daban na gidan sarautar inda
har
abada ba za a sake ganinsu ba bare ma wani ya
shaida dayansu asirinsa ya tonu a gane cewa
shine
dan fashin da ya addabi Mutane a nahiyar
Tunda yake kamo Bayi da mata ba ataba samun
wanda ya
taba guduwa ba daga cikinsu ya tsira da
rayuwarsa
face sarki shardas yasa anbi bayansa an
kasheshi
saboda tsananin tsoron da ake yiwa dakarun
sarki shardas ne
yasa aka musu lakabi da suna DAKARUN AJALI
wata rana sarki shardas tare dakarunsa kimanin
mutum dubu uku sun fito mamayar bazato izuwa
wani babban kauye da ke gefen wata makociyar
kasa da ake
kira salmas sai suka kai
hari izuwa ga ayarin wadansu matafiya masu
yawan gaske wadanda suka yada zango a gefen
kauyen
wanda ake kira Malgur.
Su dai wadannan matafiya suna da tarin shanu
tumaki da raguna masu yawan gaske kuma Allah
ya albarkacesu da kyawawan mata ababan
kwatance
ga kuma tarin zuri'a
Al amarin ya faru ne da yammaci sakaliya daf da
faduwar rana shugaban wannan ayari saurayi ne
ma aboci kyau kwarjini da jarumtaka ana kiransa
da suna Hailur, a wannan rana ne hailur yayi
aurensa na farko a duniya kuma matar da ya
aura
budurwace yar shekara goma sha takwas a
duniya wacce
babu mai kyawunta a duk cikin zuri ar ayarin
gaba
daya
A wannan lokaci wannan ayari sun shagala a
cikin
bikin auren hailu ana ta kade kade da raye raye
saboda murna
kowa da kowa ya zage yana ta rawa
maza da mata yara da manya gaba daya dakarun
ayarin dake tabbatar da tsaro sun ajiye
makamansu
sun shiga cikin taron 'yan rawa suna cashewa
kwatsam ba zato ba tsammani sai gani akayi
dakarun Ajali sun bullo daga kowace
kusurwa gabas da yamma kudu da arewa bisa
dawakai aguje kuma sun zare makamai suna ihu
da
kururuwa nan fa taron biki ya watse mata, yara
da tsofaffi suka kama ihu da guje
guje suna neman maboya, a dai dai wannan
lokaci
ango Hailur na tare da amaryarsa shadila a cikin
tantinsa
suna more amarcinsu kwatsam sai suka jiyo
iface iface
da guje gujen jama arsu
a rude ango Hailur da amarya shadila suka mike
tsaye zumbur daga kan shimfidarsu suka suri
suturarsu suka sanya
hailur yayi waje ya dauko takobinsa da
garkuwarsa ya
dubi shadila yace komai
wuya komai rintsi kada ki fito daga cikin wannan
tanti
indai kika kiyaye wannan umarni nawa ni dake
duk zamu
tsira daga sharrin wadannan yan harin bazati
kada ki kuskura kiyi ihu ko maganar da wani zai
jiyoki
shadila ta kada kai cikin alamun tsananin
damuwa
tace lallai zan kiyaye wannan umarni naka
nan take hailur ya sumbaci goshin shadila
sannan ya
juya zai fice daga cikin tantin sai tayi wuf ta
ruko hannunsa ta rungume shi tana mai fashewa
da kuka
ba komai ne ya sa tayi hakan ba face taji a
jikinta
cewar abune mawuyaci su sake ganin juna,
ba komai ne ya tabbatar mata da hakan ba face
ta
dan leka wajan tantin daga tsananin yawan
dakarun
sumamen da suka kawo musu hari tasan cewa
tabbas an shammaci nasu dakarun ba zasu iya
kare kansu ba
Cikin hanzari hailur ya janye jikinsa daga cikin
nata ya
sake dubanta cikin yanayi mai nuna yarda dakai
yace ki barni kamar yadda kika saba
ni nasan dabarar da zanyi na kubutar da
rayuwarki da tawa, shin kin
manta ne da cewar irin wannan ta taba faruwa
shekaru
uku baya sa adda wata rundunar yan fashi suka
ritsamu a daji mu biyu rak nidake muna kiwo?
Ko dajin wannan batu sai
Shadila ta gyada kai cikin murmushin karfin
hali tace haba ya masoyina ai ba zan taba
mancewa da
wannan gagarumar jarumtaka da kayi ba, koda
jin haka sai fuskar hailur ta fadada da murmushi
yace
to wannan karon ma abinda zai faru kenan baya
ga
wannan ina mai yi miki wani babban albishir
cikin matukar mamaki da zakuwa shadila ta zaro
idanu tace wane irin albishir kuma zakayi mini
yanzu?
Hailur yace boka zaifur ya gaya mini cewa a
ranar
farko dana sadu dake juna biyu zai shiga don
haka
yanzu ina mai tabbatar miki da cewa kina dauke
da
cikin dana
kona mutu a wannan yaki bani da nadama ko
takaici
na san cewa na bar wanda zai kula dake
Yayinda shadila taji wannan batu sai hawaye ya
zubo mata tace lallai ina son ta kowanne hali
ka rayu a wannan yaki kuma mu tsira tare domin
babu abinda
na tsana a wannan duniya sama da dana ya
taso maraya
hailur yayi murmushi yace nayi miki alkawari
cewar
danki ba zai taso a maraicin rashin uba ba
yana gama fadin hakan sai ya juya da sauri ya
fice da gudu
daga cikin tantin
Ai kuwa yana fitowa yaga yadda ake ragargazar
jama arsu ana saransu
da sukarsu suna ihu jini na tsartuwa
fallatsi da malala suna zama gawa sai ya fusata
ainun ya kwarara uban ihu ya zare takobinsa
daga
cikin kufenta ya afkawa dakarun sumamen ya
hausu
da sara da suka ya zame musu guguwar annoba
a wannan lokaci hankalin sarki shardas yana kan
bayi mata
da ake ta kamawa da kuma dukiyar da ake diba
amma ko da yaji ihun dakarunsa ya yawaita a
wani
bangare daban sai ya juyo da sauri izuwa wajan
take ya hango jarumi Hailur yanata ragargazar
dakarunsa
duk inda hailur yasa gabansa sai dai kaga maza
na.
Zubewa kasa tamkar ana sassabe a gona Al
amarin
da yayi matukar baiwa sarki shardas mamaki
kenan
dimin tunda yake fita sumame da yaki bai taba
ganin jarumi
mai irin
zafin naman hailur ba gami da tsagwaron
jarumtakarsa
duk da cewar a wannan lokaci dakarun sarki
shardas sun kashe kaso takwas daga cikin kaso
goma na
jama ar jarumi hailur sai da ran sarki shardas ya
baci
ainun
zuciyarsa ta kama tafarfasa kamar zata kone
cikin tsananin fishi sarki shardas ya takarkare ya
kwarara wani uban ihu wanda ya firgita komai da
kowa
dake cikin dajin aka
daina yakin aka tsaya cak tamkar babu abu mai
rai
a wajen
a lokacin da amon ihun sarki shardas ke tayin
amsa
kuwa a dajin gaba daya
shi kansa jarumi hilairu sai da ya firgita bisa jin
wannan kururuwa
ya kura idanu izuwa sashin da
kuwar ta fito
da yake a sannan ne kurar yakin take lafawa sai
da yan dakiku
suka shude sannan ya hango sarki shardas ya
tunkaroshi daga
can nesa kadan take zuciyar jarumi hailur ta
buga da karfi ya ji tsoro ya
darsu a cikin ransa a karon farko a duk
gwagwarmayar
da yakeyi da mazaje a rayuwarsa bakomai ne ya
haddasa
hakan ba face a iya rayuwar jarumi hailur bai
taba
ganin mutum mai kirar sadaukai da kwarjininsa
ba kamar sarki Shardas duk da cewar fuskar sarki
shardas a rufe take cikin rawani sai da jarumi
hailur ya gane cewa lallai wannan sadaukiba
saurayi
bane shekarunsa sun kai arba in da 'ya'ya kuma
idanunsa
ya kalla kawai ya gane hakan,
abinka da jarumi mai dakakkiyar zuciya kuma
wanda baya fidda rai ga samun sa a da rabo sai
hailur ya gyara tsayuwarsa ya rike takobinsa da
garkuwarsa da kyau
koda ganin haka sai sarki shardas yayi
murmushin
mugunta kawai sai shima ya zare takobinsa daga
cikin
kufenta wata irin takobi ce mai tsawo da kaifi
kuma
anyita ne da wani irin karfe na musamman
wanda sai kwararren makeri ne zai
iya gano hakan take sarki shardas ya falfalo
da gudun tsiya izuwa kan jarumi hailu
duk sa adda sawun kafafun sa suka taba kasa
sai
kaji kamar takun giwa ne saboda nauyinsu
Koda jarumi Hailur ya hango sarki shardas ya
rugo
izuwa kansa cikin mugun nufi haka sai shima ya
ruga izuwa
gareshi duk su biyun suna ihu
da karaji
yayin da ya rage saura baifi taku biyar ba su
hadu
sai kowannansu ya daka tsalle sama yakai
wawan
hari
sarki shardas ya kaiwa hailur sara a wuya da
nufin ya cire masa kai hailur ya kare saran da
garkuwarsa take garkuwar ta rabe gida biyu
tamkar
an yanka tsakiyar tufa da wuka cikin zafin nama
hailur
ya kaiwa shardas suka da takobinsa a ciki
shardas yasa garkuwarsa don tare sukan amma
duk da haka sai da takobin ta huda rigarsa
ta tsargeta in ba
don ma ya kare harin ba cikin zafin nama dasai
takobin ta huda cikinsa
koda suka duro kasa sai kowannansu ya cika da
mamaki shi dai sarki shardas bai taba karo da
jarumin
da ya taba samun nasarar ko da lakutar rigar
jikinsa ba
amma yau gashi ya hadu da wanda ma ya
tsargeta
da takobi shi kuwa jarumi hailur firgita yayi ainun
bisa ganin yadda takobin sarki shardas ta tsarge
garkuwarsa gida biyu
don haka ya tabbatar da cewar duk sa adda
takobin
shardas ta sami jikinsa ba karamar illa zata yi
masa ba
nan fa Hailur ya fara tunanin hanyar da zaibi ya
iya
kare kansa koda ya dubi garkuwar dake hannun
sarki
shardas
sai yaga anyi tane da irin karfen da akayi
Takobin, cikin sauri hailur ya dubi kaifin
takobinsa
sai yaga she har ta dan dakushe a wajen tsininta
sakamakon haduwa da tayi da garkuwar sarki
Shardas
Al amarin da ya kara dugunzuma hankalin
hailur kenan ya
tabbatar da cewar babu wata hanya da zai iya
kare
kansa a wajen sarki shardas face ya kwaci
garkuwar
dake hannunsa yin hakan kuwa yasan cewa ba
karamar sa a bace da nasara
A wannan lokaci gaba dayan dakarun sarki
shardas
da tsirarun dakarun su hailur da sukayi saura a
wajan
sun zuba idanunsu a kansu kawai kowa so yake
yaga yadda karshen wannan gumurzu zai
kasance
tamkar dacan ba yaki ake ba a wajan su kuwa
matan da aka kama amatsayin bayi aka
daddauresu
tuni sun fara kuka tare da ya yansu kananan
yara wadanda kusan su duka
an kashe iyayansu maza an mai dasu marayu
sai da kimanin dakiku dari da arba in suka shede
ana
kallon kallo tsakanin sarki shardas da jarumi
hailur kowannansu tunanin dabarar da zaiyi
ya cutar da abokin gwaminsa yake sannan suka
sake
rugawa izuwa kan juna a karo na biyu
suna haduwa asama sai sarki shardas ya
kawowa
hailur sara a cinya shi kuma yakai masa sara a
ka kowannansu
yayi iya kokarinsa
wajan kaucewa harin
cikin zafin nama amma sai da takobin sarki
shardas
ta yanki hailu ta dara naman cinyar jini yayi
tsartuwa hailur ya kwala uban ihu sakamakon
tsananin
zafi da zogin da yaji
shi kuwa sarki shardas bai ankara ba sai gani
yayi
hailur ya tuje rawanin dake kansa ya fado kasa
sai ga fuskarsa ta baiyana a fili karara kafin su
duro kasa
gaba daya tuni hailur ya doki hannun sarki
shardas mai dauke da garkuwa garkuwar ta
subuto
kasa cikin bakin zafin nama hailur ya fada kan
garkuwar
ya sureta kuma yayi 'yardungure sau uku
izuwa can gaba
yana mikewa tsaye yayi sauri ya yagi rigar jikinsa
ya daure raunin cinyar tasa don tsaida jini
shi kuwa sarki shardas ko da yaga tsirarun
dakarun
su hailur sunyi arba da fuskarshi kuma sun
shaida
ko shi wanene sai ya dakawa dakarunsa tsawa
yace
su karasasu gaba daya
take dakarun suka hau tsirarun dakarun da sara
da suka
suka karkashesu a cikin 'yan dakiku kadan
koda ganin abinda ya faru sai jarumi hailur ya
kurma
uban ihu ya ruga izuwa kan sarki shardas
har dakaru sun yunkura zasu tareshi sai sarki
shardas ya tsaidasu yace ai wannan nawa ne
ba naku ba kuma abin kunya ne a ce nidaku
munyi masa rubdugu
ku zuba ido kamar yadda
kukayi da farko kuga yadda
zamuyi dashi
koda gama fadin hakan sai sarki shardas ya tari
jarumi
hailur suka ci gaba da kaiwa juna mugayen hare
hare
wannan karon dai sarki shardas yana kaiwa
hailur sara da suka ne da dukkan karfinsa cikin
azababben zafin nama na gaban kwatance
Kaico mai karfi sai Allah ya isa kuma na gaba
yayi gaba
na baya sai labari
duk da irin tsananin juriya da jarumtaka irin ta
hailur
wannan karon sai da ya raina kansa domin
bambancin a baiyane yake kuma sarki shardas
ya shammaceshi wajan sauya salon fadan, a
lokaci
guda ya hada da kai masa naushi da bugu da
hannu da kafa sai gashi nan da nan ya hadawa
hailur jini da majina yana bal dashi kamar
tamola...
.
Tab ganin wannan yanayi da hailur yashiga
ya sa ni na tsaya a nanSATSUBA
Littafi Na Biyu (2)
Part E.
.
SAI GASHI NAN DA NAN YA HADA MISHI JINI DA MAJINA
YANA BAL DASHI KAMAR TAMOLA, ashe duk wannan abu
dake faruwa shadila ta leko ta cikin tantin da take
tana ganin abin dake faruwa cikin tsananin fargaba da tashin
hankali kwatsam
sai sarki shardas ya sami nasarar saran kafadar hailur ta
hagu hailur ya kurma
ihu a lokacin da jini yayi tsartuwa a kafadar tasa amma sai yayi sauri ya rike
takobin ta
sarki shardas a lokacin da shi sarki shardas ke son ya danna
takobin ta nutse a cikin kafadar
koda shadila ta hango abinda ya faru ga mijinta saita
kurma ihu bata san sa adda ta fito da gudu daga cikin
tantin da take boye ta rugo izuwa inda suke
jiyo ihunta da gudun tane yasa sarki shardas ya waigo
yayi arba da ita koda yaga irin tsananin kyawunta sai ya dimauce ya juya
da sauri ya doke kirjin hailur da karfin gaske saboda
karfin dukan saida hailur yayi tsalle sama da baya
kamar an janyeshi da majajjawa ashe bayan nasa
wani rami ne mai tsananin zurfin tsiya wanda karshensa
kwazazzabo ne da magudanar ruwan wata korama
koda hailur yaji ya fada cikin wannan rami sai ya
kwarara uban ihu irin na wanda ya saddakar mutuwa zaiyi
ita kuwa shadila tana ganin abinda ya faru ga mijinta sai ta sulale kasa sumammiya
sarki shardas ya bushe da dariyar farin ciki ya
ruga da baya izuwa inda shadila ke kwance ya dauketa ya azata
akan dokinsa
nan take
dakarunsa suka kwashe gaba dayan dukiyar wannan ayari nasu hailur suka ingiza keyar bayin da suka kama akayi gaba
ana tunkarar birnin Romaniya
Ana fara tafiya sai sarki shardas ya sake rufe fuskarsa da
bakin rawani kuma ya shakawa shadila banju barcinta ya sake nauyi
don haka bata farka ba har aka isa birnin romaniya
da tsakiyar dare
lokacin da shadila ta farka daga barci sai ta tsinci
kan wani luntsumemen gado na alfarma a cikin
wani kasaitaccen daki na sarauta cikin razana ta mike tsaye da sauri ta sauko daga
kan gadon, ta kama
kallon kowacce kusurwa
koda tagama ganin kayan kawar dake cikin dakin sai
tunanin mijinta da sauran jama arsu ya fado mata
ta tuno da duk abinda ya faru a sansaninsu sa adda
aka kawo musu sumame na mamayar bazato
nan take shadila ta dafe kunnuwanta da hannayanta biyu ta kurma uban
ihu tana mai fashewa da matsanancin kuka
faruwar hakan keda wuya sai taji an bude kofar
turakar
ba wani bane ya shigo cikin turakar face sarki shardas a cikin wata irin
kyakkyawar shiga ta sarakai fuskarsa cike da annnuri
ya durfafeta
koda tayi arba dashi sai ta razana ainun taja
da baya tana mai nunashi da yatsa a lokacin
da hawaye ya zubo mata tace ka cuceni ka kashe
mini miji
kuma ka kashe dukkan mazajen ayarinmu ina sauran
yan uwana mata?
Me kake nufi dani ka kawoni nan ni kadai
kawai ka kasheni na huta da kunci da bakincikin
rayuwa tunda ka rabani da masoyina da dukkan
zuri ata
koda jin wannan batu sai sarki shardas ya bushe
da dariya lokaci guda kuma ya turbune fuska ya dubeta yace
yake wannan ma abociyar kyawu da cikar zati
kiyi sani cewa kece mafi sa a bisa dacewa da zama
matar sarkin birnin Romaniya a yanzu
duk wata rayuwa da kikayi a baya ki manta da ita
ki manta da komai da kowa ki fuskanci
sabuwar rayuwar da tazo miki wacce zaki tsinci
kanki a cikin daular da baki taba ji da gani ba
koda jin wannan batu sai zuciyar shadila ta kama tafarfasa kamar zata kone
saboda tsananin fishi taji ta tsani sarki shardas
fiye da komai a doron kasa koda idanunta suka kai
kan wata wukar dake kan wani faranti babba mai
dauke da tuffa masu yawa sai tayi zumbur ta suri wukar
ta ritsa sarki shardas da ita tace kada ka kusanceni
idan ka matso kusa dani zan kasheka. Sarki shardas ya bushe da mahaukaciyar
dariya ya durfafeta kai tsaye
ai kuwa yana kusantarta sai ta caka maza wukar a kirji take wukar ta balle gida biyu taji kamar akan
dutse ta bugata
kawai sai sarki shardas ya hankadata ta fada kan gadon dake bayanta sannan ya bita izuwa kan
gadon bai rabu da ita ba har sai da bukatarsa ta biya
tana ta faman rusa ihu da kukan bakin ciki
daga wannan rana shadila ta zama matar sarki
shardas da karfin tsiya ya zamana cewa kullum a cikin daula take
babu abinda takeyi da hannunta sai dai kuyangi da barori
suyi mata duk da cewar ta tsinci kanta a cikin daula irin
wacce bata taba ji da gani ba sai ya zamana cewa
kullum a cikin kuka da bakinciki take musamman
idan ta tuno da tsohon masoyinta kuma sabon
angonta hailur da kuma sauran danginta da zuri arta
lokacin da shadila ta matsawa sarki shardas
akan sai taga inda aka kai sauran +yan uwanta mata wadanda
aka kama a matsayin bayi sai yayi mata jagora
izuwa wani bangare daban na gidan sarautar wannan ranace
ta farko wacce shadila
ta sami damar fita daga bangaren da turakarta take
koda taga yadda girman gidan sarautar yake da yawan dakarun dake tsaro a ko ina sai hankalinta ya dugunzuma ainun domin take
burinta na son guduwa ya yanke, haka dai sarki
shardas yaci gaba da yiwa shadila jagora suna ta
ratsawa ta cikin lunguna da sakuna har sai da
sukayi tafiya mai nisa
duk inda suka ratsa sai dai kaga bayi barorim hadimai da dakaru suna risinawa suna
gaishesu har suka iso wani katon gida wanda ke cike da bayi mata
koda shadila tayi arba da yan uwanta mata
yan zuri arsu suna ta yin ayyuka na bauta iri iri sai ta ruga garesu tana mai
kiran sunayansu daya bayan daya tana zubar da hawaye
take suma bayin suka rugo gareta suka rungumeta suna kuka
bayan ta dan jima a kankame dasu sai ta janye jikinta daga cikin nasu ta juyo ta dubi sarki
shardas tace ina neman alfarmar ka yanta wadannan yan uwa
nawa daga matsayin bayi masu aikin bauta zuwa ga kuyangina.
Koda jin wannan batu sai sarki shardas yayi
shiru yana mai sunkui da kai ya dubi shadila
cikin murmushi yace yake matata kiyi sani
cewa babu wani abu da zaki nema a wajena ki rasa
saboda tsananin irin son da nake yi miki don haka
zanyi miki wannan alfarma bisa sharadi guda
shardin kuwa shine wadannan bayi idan suka koma can wajanki ba zasu
taba fita ba daga cikin harabar gidanki
duk wacce aka kama da laifin hakan hukuncin
kisane a kanta
koda jin haka sai farinciki ya lullube bayin suka fara
rungume shadila sunayi mata godiya ita kuwa shadila sai ta dubi
sarki shardas
tace na amince da wannan sharadi naka
nan take sarki shardas ya sa dakarun dake kula da
wadannan bayi suka kwankwance musu
sarkokin dake wuyansu da hannayensu sannan aka
tafi dasu izuwa can bangaren gidan shadila a nan ne aka basu suturu masu
kyau sukaje sukayi wanka suka sanya suturu
tunda aka kawo shadila wannan gidan sarauta na birnin
romaniya bata taba yin farin ciki ba sai a wannan rana
da aka 'yanta wadannan bayi kuma bata taba yiwa
sarki Shardas murmushi ba sai a yau din nan
Hakika shadila ta tsani sarki shardas fiye da
komai a duniya kuma inda tana da ikon kasheshi
ko guduwa daga gidan sarautar da tuni ta aikata
haka dai dai da rana daya shadila bata taba
mancewa da mijinta ba Hailur kusan kullum sai
tayi mafarkinshi
sau tari a mafarkin nata ana nuna mata cewar hailur
yana nan a raye bai mutu ba amma idan ta tuno
da tsananin zurfin ramin da ya fada sai taga cewar
mafarkin nata ba zai taba zama gaskiya ba
babban abinda take yin nadamar aikatashi shine karya sharadin
da tayi a lokacin da hailur ya gaya mata cewa
komai tsanani kada ta kuskura ta fito daga cikin
wannan tanti da take amma sai ta mance da sharadin
ta fito da gudu bisa dimaucewar da tayi a lokacin
da taga sarki shardas ya sareshi da takobi a kafada
ta kwalla ihu ta fito da gudu ta baiyana kanta
Tabbas inda bata fito ba da sai hailur ya kubuta
daga sharrinsa kuma da sai sun gudu tare
lokacin da shadila ta sami wata uku a cikin gidan sarautar
sarki shardas sai alamun juna biyu suka baiyana
a gareta
ya zamana cewa tana fama da tashin zuciya, kumallo
da zazzafi da ciwon kai
ko da sarki shardas yaga shadila bata da lafiya
sai hankalinsa ya dugunzuma nan take ya tura aka
kirawo wata likita tazo ta dubata cikin murmushi
likitar
ta dubi sarki shardas tayi masa bushara cewar matarsa
ta sami juna biyu
Koda jin haka sai sarki shardas ya kamu da tsananin farin
ciki amma da ya tuno da wani al amari sai hankalinsa
ya dugunzuma ainun kuma ransa ya baci take zuciyarsa
ta kama tafarfasa kamar zata kone jikinsa ya kama kyarma bai san sa adda yasa
hannu ya zabgawa shadila mari ba, saboda karfin
marin saida ta fadi kasa bakinta ya fashe jini yazubo
sarki shardas ya sunkuya ya kamo kafadunta yana mai
daka mata tsawa yace wanene yayi miki ciki ban sani ba
a cikin gidan sarautata kiyi sani cewa yau shekara
ashirin kenan ina neman haihuwa ban samu ba kuma matana
na aure guda goma sha shida ne a cikin gidannan
bokana ya tabbatar mini da cewar ba zan taba haihuwa
ba har sai na mallaki wata hular sihiri wacce ake kira
LAMSARA.
Lallai wannan ciki da kike dauke dashi ba nawa bane
maza ki hanzarta sanar dani maishi kona shakeki ki
mutu yanzu
Koda sarki shardas yazo nan a zancensa sai shadila ta
bushe da dariya al amarin da yayi matukar baiwa sarki
shardas mamaki kenan kuma jikinsa yayi sanyi ya
mike tsaye yana mai kura mata idanu, shadila ta yunkura
ta mike tsaye ta dubi sarki shardas a fusace tace shin kana
tunanin ina tsoron mutuwa ne? To ka sani cewa duk wannan
daula da nake ciki a wannan gidan sarauta daidai
yake da kurkuku a wajena, gaba daya rayuwar duniya
ta fita daga raina tun daga ranar da ka wargaza
rayuwata ka rabani da babban masoyina hailur
kuma ka tarwatsa ayarinmu, ka sani cewa wannan hari
da kuka
kai mana an kashe uwata da ubana da dukkan dangina
a yanzu bani da sauran masoyi a doron kasa face masoyina
hailur wanda har yanzu xuciyata ke wasu wasin
cewar yana nan a raye bai mutu ba idan har yana raye ina tabbatar maka da
cewa sai yazo har nan gidan sarautar ya daukeni
mun tafi domin wannan juna biyu da nake dauke dashi nasa
Ne bana wani ba, kafin shadila ta gama rufe bakinta ya
sake zabga mata mari ta baje a kasa sumammiya nan take
kuyangi suka rugo izuwa kanta suka shiga ceto rayuwarta
koda ganin haka sai sarki shardas ya rude yayi nadamar
abinda ya aikata saboda tsananin son da yake yiwa
shadila don haka bai san sa adda ya kwarara uban ihu ba har kwallar takaici ta zo masa
A fusace ya

Please Login or Register in order to submit comment