Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yanzu sanar dani alfarmar da kake so nayi maka
Hulkas yayi ajiyar zuciya yana mai sunkui da kansa kas
cikin alamun kunya da damuwa kamar ba zai iya magana ba sannan yace yakai abbana ka sani cewa tun da
aka haifeni a birnin nan ban taba zuwa ko da wani
garin ba daga cikin sauran manyan biranen dake kasar tamu ba, labari ya zo mini cewar hakimin birnin Istanbul ya shirya gagarumar gasa ta jarumtaka
kuma an gaiyato manyan jarumai daga bangarori
da yawa na duniya lallai ina son na halacci wannan
gasa domin a rayuwata babu abinda nake so sama da ganin
mutum mai jarumtaka da iya yaki na dade
ina rokonka akan ka koya mini yaki a matsayina na
jarumin da zai shahara a wannan nahiya tamu
amma kaki
kuma baka taba gaya mun dalili ba tunda baka son
ka sanar dani dalilin nima bana bukatar na sani
ni dai yanzu ka amince mini nayi wannan tafiya
zuwa birnin istanbul
koda yarima hulkas yzo nan a zancensa sai
sarki shardas yaji hankalinsa ya dugunzuma ainun
don haka sai ya yunkura da nufin ya juya ya dubi
boka barwas domin ya nemi shawararsa amma sai
yarima hulkas ya kama hannayansa yace yakai abbana kayi sani cewa
bai kamata a sami shamaki ba a tsakanin da da mahaifi
muddin wannan da ya kasance jinin mahaifinsa,
babu bukatar kayi shawara da wani akan alfarmar
da zan nema a wajanka tunda dai nafi karfinta
a wajanka
koda jin wannan batu sai jikin sarki ya yi sanyi
kafin ya bude baki yace wani abu sai boka barwas
ya tari numfashinsa ya dubi hulkas yace haba
ya kai yarima ai bai kamata kace zaka fita daga
cikin birnin nan ba kaje wani wuri ba tunda kasan
cewa bincike ya nuna cewa duk ranar da kayi
dogon zango kasar nan zata shiga cikin fari da annobar
talauci
kafin boka barwas ya gama rufe bakinsa tuni
shima hulkas ya tari numfashinsa yana mai cewa
amma ai cewa kayi sai idan na fita daga cikin yankin kasar
nan gaba daya sannan hakan zata faru
ya kai barwas kayi sani cewa kana da iyaka a tsakanin
da da mahaifi don haka bai kamata ka wuce gona da iri ba yarima hulkas yayi
wannan furuci ne fuskarsa a murtuke yana mai
hararar boka barwas amma da ya dubi sarki shardas
sai fuskarsa ta juye zuwa annuri
kawai sai sarki shardas ya maida masa da martanin
murmushin yace jeka abinka yakai dana lallai nayi
maka izinin ka tafi zuwa birnin istanbul domin
idanunka su more da kallon abinda zuciyarka ke so
koda jin wannan batu sai farinciki ya lullube
yarima hulkas ya rungume sarki shardas yana mai yi
masa godiya
nan take yarima hulkas ya janye jikinsa daga cikin
na sarki shardas ya koma wajen mahaifiyarsa
shadila
yana riskarta ya rungumeta yana mai yi mata bushatar
cewar sarki ya amince masa yayi wannan tafia
nan take itama shadila ta cika da farin ciki
amma koda ta dago kai tayi arba da fuskokin
sarki dana boka barwas tagansu
a murtuke babu
annuri sai hankalinta ya tashi nan da nan cikin sauri
ta kama hannun yarima hulkas taja shi suka juya da baya
suka koma cikin gidan sarautar
cikin alamun tsananin fishi boka barwas ya dubi
sarki shardas yace wannan shine kuskure na uku
wanda na gaya maka cewar kada ka aikatashi amma
gashi idanunka sun rufe saboda soyayyarsa ka
aikatashi
ko dajin wannan batu sai sarki shardas ya juyo
da sauri ya fuskanci boka barwas cikin tashin
hankali yace ban gane abinda kake nufi ba yanzu saboda kawai na bar yarima
hulkas yaje yayi kallon gasar jarumtaka a birnin
istanbul shine na aikata babban kuskure? Barwas yace
kwarai kuwa rashin aiki da shawarata yasa ka
aikata babban kuskure na uku wanda nake ta kokarin hanaka
ai tunda dai ka fahimci cewar ban son ka bar yaron nan yayi wannan tafiya
bai kamata ka barshi yayi ba bincike ya nuna mini
cewar yarima hulkas zai sami wata babbar dama ta
yakarmu a cikin wannan tafiya da zaiyi
amma kuma a dalilin tafiyar ne shima zai sadu da abinda zai zamo sanadin ajalinsa anan gaba
Lokacin da sarki shardas yaji wannan batu sai hankalinsa
ya dugunzuma ainun fiye da ko yaushe yaji kamar
ya kirawo yarima hulkas yace dashi ya janye
izinin da ya bashi nayi wannan tafiya amma kuma
sai yaji ba zai iya ba.
Kafin ya budi baki yace wani abu sai kawai yaga boka barwas ya bace bat
tamkar bai taba wanzuwa ba a wajan, cikin alamun
tsananin damuwa sarki shardas ya juya ya sauka daga
kan matattakalar barandar ya nufi cikin gidan sarautar zuciyarsa cike da sake sake da tunani
abinda ya fara fado masa a rai shine wai shin
yaya akayi nema har ya bari son yarima ya shiga zuciyarsa alhalin ya san
cewa ba jininsa bane
asalima ba shi da wani makiyi wanda ya fishi a doron kasa tunda komai dare dadewa
sai ya nemi daukar fansar ran mahaifinsa hailur a kansa
wata zuciyar kuma sai tace dashi hakika babu
abinda yafi soyayya hadari a wannan duniya domin inda tun farko
bai kamu da son shadila ba da tun sa adda ya kashe mijinta
itama zai kasheta dashi kenan ya huta da fargabar
komai don da yanzun bata haife masa alakakai
ba kuma kadangaren bakin tulu wato yarima Hulkas
maimakon sarki shardas ya wuce zuwa turakarsa
sai ya wuce zuwa turakar shadila kai tsaye
duk inda ya ratsa sai dai kaga hadimai suna zubewa
kasa suna kwasar gaisuwa da isarsa dakin sai ya iske shadila
tare da hulkas a zaune
cikin nishadi da farin ciki suna cin tuffa
a karon farko sai hulkas yaga babu cikakken annuri
a fuskar sarki shardas kafin hulkas yace wani abu sai
shardas ya dubeshi yace yakai dana ina son ka bamu dan
lokaci zan tattauna da mahaifiyarka
koda jin haka sai hulkas ya mike tsaye yana mai yin
murmushi ya nufi kofar fita daga cikin dakin yace
babu matsala
fitarsa keda wuya sai sarki ya tura kofar ya rufe ta
sannan yazo daf da shadila ya zauna ya sumbaci wuyanta
suka rungume juna suna soyayya
hm Kunya nakeji Ni uhm
daga can sai yayi wuf ya janye jikinsa daga cikin
nata ya hankadata ta fado kasa daga kan kujerar da take
zaune ya cafi makoshinta ya shaketa
Nan take idanunta suka zazzaro suka kada sukayi
jawur ta fara kakarin mutuwa a sannan ne ya saketa ta zube kasa tana numfarfashi kamar ranta zai fita tana mai kurawa
shardas idanu
A fusace shardas ya dubeta yace wannan jan kunne ne
nayimiki gami da tuni bisa alkawarin dake tsakaninmu
akan wannan yaro
zakuyi tafiya tare kedashi zuwa birnin istanbul
domin halattar taron gasar jarumtaka na duniya
da aka sabayi idan kikayi amfani da wannan dama kika gayawa
danki sirrin dake tsakani na dashi a bakacin
ranki
ki sani cewa duk abinda zai faru tsakaninki dashi boka
barwas zai gani a cikin madubin tsafinsa yanzu zan fita na barki kada ki kuskura
ki bari danki ya gane cewar nayi miki wani abu yanzu
koda gama fadin haka sai sarki ya juya ya fice daga
cikin turakar yana fita sai shadila ta mike zumbur a lokacin da hawayen bakin ciki
da takaici ya zumo mata kawai sai tayi sauri ta dauko wani farin kwalli ta sanya
a cikin idanunta nan take idanun nata suka washe sukayi
fari kal tamkar bata taba yin kuka ba
tana ajiye kwallin saiga yarima ya shigo idanunsa
sun ga sa adda ta ajiye kwallin don haka sai ya zargi
cewar akwai wani abu da ya faru tsakaninta da sarki
shardas
doomin baiga dalilin da zaisa tayi amfani da kwalli ba alhalin
dama can ta gama yin kwalliya
cikin alamun zargi hulkas ya dubi shadila yace
yake ummina menene ya faru tsakaninki da
abbana??
Shin ya gaya miki wata magana ne wacce ta
sosa miki rai?
Koda jin wannan tambayoyi guda biyu sai shadila tayi
murmushi tace
babu wata magana wacce ta sosa mini zuciya farinciki ne
kawai yasa kaga alamun sauyin yanayi akan fuskata
domin ya shaida mini cewar zamuyi tafiya nida kai zuwa birnin istanbul
koda jin haka sai murna ta kama yarima
ya rungumeta yana mai cewa burina ya cika yake
ummina lallai idanuna zasu ga abinda suka dade suna mafarkin gani
A wannan rana gaba daya yarima hulkas bai
sami damar hutawa ba ko tsayuwa a waje
daya
saboda murna sai kai kawo yake yana ta shirye
shiryen tafiyar da zasuyi gobe
lokacin da dare yayi sai bacci ya kauracewa hulkas da yake akan gado daya suke kwance tare da sarki shardas sai yarima
hulkas ya cika da matukar mamaki bisa ganin yadda shima sarki shardas din ya
kasa yin barci sai juye juye yake yi kawai akan gado
Yarima Hulkas ya dubi sarki
cikin alamun mamaki yace yakai abbana wai shin
menene ya hanaka barci ne a yau?
Koda jin wannan tambaya sai sarki shardas
yayi murmushi yace yakai dana kai yarone
don haka baka son dacin rabuwa da masoyi ba tunda
aka haifeka a cikin wannan gidan sarauta ban taba rabuwa dakai
ba tsawon sa a daya jal kullum muna tare dare da rana hatta kwanciyar barci bata rabamu
yau gashi an wayi gari zakayi tafiya zamuyi rabuwa ta a kalla tsawon sati
biyu
a cikin wace irin damuwa da kadaici kake tunanin zan kasance?
Koda sarki shardas yazo nan a zancensa sai Jikin yarima Hulkas yayi sanyi nan take idanunsa
suka ciko da kwalla har hawaye ya zubo masa bai san sa adda ya rungume
sarki ba yana mai cewa.......
.
A nan zan dakataTSATSUBA
Littafi Na Uku (3)
Part C.
.
Lokacin da Hulkas yazo nan a zancensa sai shima sarki
shardas jikinsa yayi sanyi ruwan hawaye ya subuto daga cikin idanunsa
ya janye jikinsa daga jikin na hulkas suka fuskanci
juna yana mai rike kafadunsa yace yakai dana
kayi sani cewa ko kadan nima bana son abinda zai
sosa maka zuciya kuma babu abin da nake so sama da ganin
farin cikinka amma in ba don haka ba da tsawon sa a daya
zan kasance a cikin zumudi da dokin dawowarku lafiya kaida mahaifiyarka
domin kune ginshikin rayuwata, haka dai sarki shardas da yarima hulkas sukayi ta hira ta bankwana har asubahi ta
riskesu basu sani ba a sannan ne hulkas ya fara gyangyadi kafin
a jima barci ya daukeshi
faruwar hakan keda wuya saiga shadila ta shigo sanye
da rigar barci wacce ke baiyana kyakkyawar surar
jikinta
babban abinda ya daurewa sarki shardas kai shine
bai taba ganin murmushin shadila ba a duk sa adda
zata shigo turakarsa da daddare sai yau tun a farkon
ranar da ya satota daga sansaninsu ya kawota wannan gidan sarauta saboda ya
tabbatar da cewar ta tsaneshi kamar yadda ta tsani mutuwarta
kai tsaye shadila ta fado kan sarki shardas ta fara jan hankalinsa domin ya kwadaitu da ita
maimakon ya karbeta hannu biyu sai kawai taga ya
bangajeta ta fadi can gefe daya
akan gadon ya dubeta a fusace yace menene
dalilin da yasa yau kika shigo cikin turakata kina mai
murmushi alhalin baki taba yi mun murmushi ba a
dukkan dararen da suka shude na barcinmu??
Koda jin wannan tambaya sai shadila ta bushe damahaukaciyar
dariya kamar ba
zata daina ba karfin dariyar nata baisa yarima hulkas
ya faka daga barcin da yake yi ba mai nauyi
saboda kasancewar barcin mai nauyi ne
daga can sai shadila ta tsuke bakinta ta daina yin
dariyar tana mai murtke fuska ta dubeshi tace
yakai mijina na dole ka sani cewa ban taba jin
kaunarka ba a cikin zuciyata dai dai da darajar kwayar zarra
kaine ka rabani da farin cikina kuma kaine ka
shayar dani gubar bakin cikin da har abada ba zan iya
amayar da ita ba sai dai ajalina ya zame mini
saukin ciwon data sa mini Abinda yasa kaga na shigo
cikin turakarka ina murmushi a yau ba komai bane
face farin ciki bisa sanin cewa gobe zan rabu da ganin wannan fuska taka
kuma ba zan sake ganinta ba har sai bayan a kalla sati byu
ka sani cewa duk sa adda na kalli fuskarka sai naji kamar
bakin kumurci nake kallo haka kuma duk sa adda
ka kwanta dani nakanji mugun bakin ciki
tamkar na kashe kaina
saboda ba masoyina hailu bane yake amfani da wannan
kyakkyawan jiki nawa, yanzu na kawo maka
kaina ne gareka domin ka more iya son ranka
saboda kwanaki goma sha hudu masu zuwa a mafarki
jikin nawa zai zama na masoyina wanda ka datse
rayuwarsa ka mayar da dansa maraya
koda shadila tazo nan a zancenta sai zuciyar sarki
shardas ta kama tafarfasa kamar zata kone
jikinsa ya kama tsuma ya daga hannu da nufin
shararawa shadila mari amma sai ya kasa saboda tsoron
kada ya maretan hulkas ya farka daga barci ya gane
abinda ya faru tsakaninsu
koda shadila taga sarki shardas ya kasa marinta saita sake
bushewa da dariya a karo na biyu ba tare da tace dashi
uffan ba sai tasa hannayanta biyu ta dauki danta hulkas ta
rungumeshi a kirjinta ta juya ta fice daga cikin turakar
shi kuwa sarki shardas sai ya bita da kallo kawai cikin
tsananin takaici da bakin ciki fuskarsa nayin
gatsine yana jin kamar ya zare takobi yaje ya sareta
gari na wayewa sosai sai sarki Shardas ya kirawo mataimakin sarkin yakin kasar wanda ake kira sadauki marzanu ya dubeshi yace ina son ka
zabo zakwakuran dakaru mutum dubu biyu daga cikin
manyan dakarunmu kayi musu jagora a cikin rakiyar
matata da dana yarima hulkas izuwa birnin
ishtanbul kayi sani cewa zan baku guzuri ishashshe
kuma zan baku kudade masu yawan gaske
domin ku kawai da dukkan bukatunku amma ku sani cewa idan kuka dawo
daga birnin istanbul naga kwarzane guda daya a jikin matata ko dana ko kuma kuka dawo mini dasu babu lafiya ko babu rai
a bakacin rayukan iyalanku daku kanku
koda jin wannan batu sai sadauki marzanu yarisina yace
an gama ya shugaban nan take marzanu ya juya da sauri ya nufi wani bangare daban na gidan sarautar domin
ya hado kan dakarun daya dace suyi masa rakiya a cikin wannan gagarumar lafiyamai hadari
kafin rana ta take tuni kowa ya gama kimtsawa daga cikin jama ar da zasu yi wannan
tafiya shadila da yarima hulkas kuwa sai suka caba
ado mai daukar hankali suka shiga cikin keken dokin sarauta
sadauki marzanu da sauran dakaru kuwa suka hau dawakai cikin gagarumar
shigar yaki suka sa keken dokin a tsakiya sai
kuma kuyangi guda uku kacal da aka tanada domin
su yiwa shadila da hulkas hidima a cikin wannan tafiya
ba tare da bata lokaci ba wannan zuga ta kama hanyar
fita daga cikin gidan sarautar, abinda ya daurewa yarima Hulkas kai shine
rashin ganin sarki shardas a wannan safiya bare
suyi sallama har ya budi baki zai tambayi shadila
dalilin da yasa sarki baizo sunyi bankwana ba sai
kawai ya hango sarki shardas a can saman bene yana dago
masa hannu kuma idanunsa sun ciko da kwalla
nan take zuciyar yarima hulkas ta karaya shima ya
ji hawaye ya zubo masa take yaji kamar ya fasa yin
wannan tafiya kawai sai hulkas ya daka tsalle ya duro kasa
daga kan keken dokin ya ruga da baya izuwa
inda sarki yake can saman bene, babu shiri mai jan keken
dokin yaja linzami ya tsaidashi itama shadila sai ta duro daga cikin keken dokin
a dimauce don a zatonta wani mugun abune ya faru
amma sai taga ashe yarima ne ya ruga izuwa inda
sarki yake
lokacin da sarki shardas yaga yarima hulkas
ya rugo izuwa gareshi sai shima ya gangaro da gudu
daga saman benen da yake tsaye ya tari yarima
a tsakiyar filin gidan sarautar suka rungume juna kuma suka
kama kuka a lokaci guda saboda bakin cikin rabuwa
yarima hulkas ya dada kankame sarki, yace yakai abbana.menene dalilin da yasa kaki
zuwa muyi bankwana tun dazu alhalin kasan cewa ina
ciikin kewarka da tunanin rashinka a kusa dani
Sa'adda sarki shardas yaji wannan batu sai ya janye
jikinsa daga cikin nasa suka fuskanci juna a lokacin da kowannansu ke zubar da hawaye
sarki shardas ya numfasa yace yakai dana kayi sani cewa ni jarumi ne kuma gwarzon
mayaki wanda bai taba zubar da hawaye ba komai
wuya da azaba kuma komai farin ciki da bakin ciki
tun daga kuruciyata kawo izuwa girmana amma yau
gashi kai ka sani na zubar da hawaye ina mai tabbatar
maka da cewa in banda mahaifiyarka
babu wani mutum wanda na taba jin ina sonsa dari bisa dari
a cikin zuciyata sai kai kuma a halin yanzu soyayyata a gareka ta linka
dari bisa dari fiye da komai kuma kai kadai ne mutumin
da nake jin cewar ba zan iya cutar da shi ba bisa
duk irin laifin da zakayi mini koda kuwa bakin cikin
abin dakayi min zai zamo sanadin ajalina
koda jin wannan batu sai yarima hulkas ya sake rungume
sarki ya fashe da matsanancin kuka yace
yakai abbana tabbas nasan kana kaunata fiye da kima
amma ni ina jin kusancinka a raina fiye da kusancin jini
da hanta
inaji a raina cewar idan babu kai a wannan duniyar
ba zan rayu ba kuma ina jin cewar rashinka a kusa dani
dai dai yake da jefani cikin kurkukun da babu ci ba sha kuma babu hasken
da mutum zai iya ganin ko da tafin hannunsa face matsanancin duhun daba zai misaltu ba
koda jin haka sai sarki shardas ya janye jikinsa daga cikin
na yarima hulkas kansa na sunkuye yana zubar da hawaye kawai sai ya daga hannu
ya yiwa sarkin yaki marzanu inkiya nan take marzanu
ya rugo ya dauke yarima hulkas ya ruga da shi izuwa bakin keken dokin ya sashi a ciki
itama shadila sai ta koma cikin keken dokin ta zauna
nan take aka sakarwa dawakan linzami keken
dokin yayi gaba su sadauki marzanu sukabi
keken dokin a baya suna maiyi masa kawanya
gaba daya
gefe da gefe don tabbatar da tsaro
nan dai sarki shardas ya bisu da kallo har sai da suka
kule ya daina ganinsu sannan ya juya ya koma cikin gidan sarautar
cikin tsananin bakin cikin
rabuwa da yarima hulkasa
bai ankara ba saiji yayi hawaye ya kara zubo masa
a wannan lokaci kuma inda yake wucewa akwai dakaru
a tsaitsaye kuma ga bayi
barori da kuyangi suna ta kai kawo da hidimomi
duk wanda yaga hawaye a idanun sarki sai kaga ya firgice
domin kowa ya san cewa a tarihin rayuwar sarki
shardas babu wanda ya taba ganin hawayansa sai yau
da yake an san irin shakuwar dake tsakanin sarki shardas
da
dan sa yarima hulkas kuma an san cewa yau sun rabu
sai kowa ya gane dalilin zubar da hawayan nasa
abin da mutane basu sani ba shine wannan hawaye bana
soyayyar hulkas bane ba kadai har da takaicin
tunanin ainihin alakarsa da hulkas gami da sanin
cewa hulkas ba jininsa bane da kuma bakin cikin rashin
samun soyayyar shadila a gareshi ta gaskiya
kai tsaye su sadauki marzanu suka durfafi cikin
daji suka sukayi ta tafiya babu sassauci babu
tsoro ko shakkar wani abu saboda sun yarda da kansu
tabbas masu iya magana sunyi gaskiya da sukace
dole a ce da mijin iya baba hakika komai
yawan yan fashi da shirinsu idan suka hango wannan
runduna ta su sadauki marzanu saikaga sun fasa
taresu sun bace daga kan hanyarsu, ba komai bane ya haddasa hakan ba face kwarjininsu kuma ido ba mudu bane ammma yasan kima
ma ana kai da ganin dakarun marzanu kasan
sun cika zaratan jarumai masu tarwatsa maza domin dukkansu sun kasance manya manya
masu kirar mutanen farko, gashi jikinsu a murde
yake kuma sun tara kwanji da jijiyoyi kai kace da dutse aka yi gabobin jikin nasu
irin shigar yakin da sukayi kuwa mai ban tsoro ce domin kowannansu yana daukeda miyagun makami yaki irin wanda idanu basu
saba gani ba kai ba wai yan fashi ba hatta mugayan
dabbobin daji da bakaken aljanu wadanda suka kasance
azzalumai suna ganin wannan runduna sai kaga sun bace
daga wajan saboda boka barwas ya shirya wadannan dakaru
tuntuni da karfin sihirin tsafi mai tunkararsu sai cikakken shiryayye abin kwatance a duniya
kwana uku kacal wadannan dakaru suka shafe suna
tafiya suka iso birnin askandariya suna shigowa
suka iske birnin a cike makil da jama a duk inda mutum
ya duba babu abinda zai gani face kawunan jama a
fiye da rabin jama ar da suke gani baki ne wadanda sukazo
halattar gasar jarumtaka mafi akasarin bakin kuwa sarakai ne da attajirai da
yayansu da kuma fatake da shahararrun bokaye
tabbas gaba da gabanta aljani ya taka wut
lokacin da keken dokin gimbiya shadila ya kunna kai
cikin birnin sadauki marzanu da dakarunsa na biye dashi
sai gaba dayan jama ar dake wajan suka dare suka basu hanya kuma kowa ya
zuba ido ana kallonsu aka zama kauyawa
ba komaine ya haddasa hakan ba face ganin irin dukiyar
da aka kashe wajan kera keken dokin da gimbia shadila ke ciki da kuma kayan yakin
da dakarunta ke sanye da su domin an sanya jarin wani sarkin ne gaba daya
nan fa sarakuna masu ji da kansu ma suka ringa raina kansu
basu san sa dda suka rinka leken cikin keken dokin ba domin suga
wanda yake ciki amma da yake an saki labulan
keken dokin damar hakan bata samu ba a gunsu
nan fa aka bi keken dokin a baya duuu har izuwa kofar
gidan sarautar birnin ana isa sai akayi cirko cirko
kawai sai sadauki marzanu ya zaro wata wasi ka ya baiwa masu gadin gidan
sarautar yace su kaiwa sarkinsu, wasikar na isaga
sarki hulbasu yana budeta yayi arba da hatimin sarki
shardas cikin zumudi ya mike tsaye zumbur ya taho da
sauri izuwa kofar gidan sarautar yazo gaban keken
dokin yana mai cewa lale marhaban da gimbiya shadila matar sarki shardas na Birnin Romaniya
Koda jin wannan batu sai jama a suka zuba idanu domin
suga gimbiya shadila saboda labarinta ya gama bazuwa a nahiyar gaba daya ana ta surutun tsananin kyawunta
santaleliyar kafarta ta fara zurowa kasa daga cikin
keken dokin tun kafin ma jama a suga ragowar jikin
nata suka fara gigita da dimauta ai kuwa tana fitowa gaba dayanta aka
yi arba da kyakkyawan surar da Allah yayi mata sai mutane suka kama sambatu wasu
kuwa basu san sa adda suka kama dalalar da yawu ba
tamkar masu hauka sabon shiga
a wannan lokaci shadila na sanye da wata shudiyar doguwar riga damammiya wacce ta baiyana dukkan siffofin jikinta a fili
wohoho kyawu kyauta ce daga Allah. Mutum ba zai iya baiwa kansa ba, kai ko namijin da bai cika namiji ba idan yayi arba da wannan gimbiya
a wannan lokaci sai ya zama namiji domin
mace ce doguwa wacce bata kasance siririya ba kuma ba kakkaura ba tana da dara daran idanuwa masu dan karen haske da
fari
hancinta dogone siriri tamkar fikakken alkalami a kasansa an dasa mata
dan kankanin baki kamar yankan wuka cikinta a
shamule yake tamkar bata taba cin komai ba
kugunta mai fadi ne sosai ga mazaune masu tudu
kirjinta a cike yake fal kamar bata taba shayarwa ba gashin ta baki ne sidik kuma dogo
ya zuba har kasan marar ta sai haske da kyalli yake
kamar madubi
TSATSUBA
Littafi Na Uku (3)
Part.D
.
Tana gama fitowa daga cikin keken dokin saiga danta yarima hulkas shima ya fito
sanye da koren tufafi na alfarma irin nasu na sarakai
shima take tsananin kyawunsa ya tafi da hankalin kowa dake
wajan domin albasa tayi halin ruwa
cikin farin ciki da girmamawa shadila ta risina ta gaida sarki hulbasu har ta budi baki zatace wani abu
sai sarki Hulbasu ya tari numfashinta yace yake tauraruwar sarki shardas
ai nan ba muhallin yin magana bane
kece bakuwa mafi daraja daga cikin dukkan bakin da
suka shigo wannan birni nawa
ina tsoron dukkan abinda zai bata miki rai koya
taba lafiyarki
don haka dolene na riritaki tamkar rai guda daya
zaifi kyau mu karasa ku sami hutu da nutsuwa keda
danki yarima hulkas
Koda gama fadin hakan sai sarki Hulbasu ya kira sarkin
Yakinsa ya hadashi da sadauki marzanu yace yaje a basu nasu masaukin shi kuwa sarki hulbasu sai ya juya Ya nufi cikin
gidan sarautar Gimbiya shadila da kuyanginta su uku tare da yarima hulkas suka bi bayansu
basu yi wata doguwar tafiya ba suka iso turakar
gimbiya LUZURAINA matar sarki hulbasu inda suka isketa
tare da danta yarima Basmar wanda shima yarone dan kimanin shekara tara wato ya girmi yarima hulkas tazarar shekara uku
koda yarima hulkas da basmar sukayi arba da juna
sai nan take sukaji jininsu ya hadu kafin ma luzuraina ta taso ta taryi gimbiya
shadila tuni basmar ya taso da sauri ya tari hulkas yana mai mika masa hannu domin su
gaisa
ba tare da shakkar komai ba kuwa hulkas ya baiwa basmar hannu suka gaisa basmar ya gabatar da kansa a gareshi
a sannan ne sarki hulbasu ya gabatar da gimbiya
shadila a wajan matarsa suka rungume juna
cikin farin ciki
nan take sarki hulbasu ya juya ya fito daga cikin
turakar ita kuwa luzuraina ta karbi shadila hannu biyu cikin matukar farin ciki
kamar taga yar uwarta ta jini wadda suka dade basu
hadu ba nan da nan tasa aka kawo musu abinci da abin sha na alfarma
suka ci tare sama wadannan kuyangi guda uku na gimbiya
shadila sai yan uwansu kuyangi suka janyesu suka fice dasu suka taf dasu izuwa nasu bangaren
koda aka fara cin abincin sai yarima basmar ya kama hannun yarima hulkas ya jashi suka fice daga cikin turakar luzuraina
yana mai cewa da umman tasa zamuyi dan tattaki domin na nuna masa gidan nan
cikin daga murya luzuraina tace da basmar lallai kada ka fice daga cikin harabata domin sarki ya gargadeni
akan na kula da abokinka sosai
ko sauraronta basmar baiyi ya yaci gaba da jan
hulkas da gudu suka nausa cikin harabar gidan basu
tsaya a ko ina ba sai da sukaje
wani babban fili wanda aka kawatashi da suke shuke
furanni kala kala kuma aka shirya kayan hutu dana wasa a wajan kamar su
lilo dawakan katako da wadansu irin gadaje na wasan yara
da zuwansu wannan wuri wanda aka kirkireshi
musamman saboda yarima basmar sai wajan ya burge yarima hulkas suka hau lilo suna shela kansu suna ta kyalkyala dariyar farinciki
daga can sai yarima basmar ya dubi hulkas a lokacin
da ya tsaida lilonsa cak yace yakai hulkas kayi sani cewa kaine abokina na farko
a duniya kuma na lura cewa kaima nine abokinka na farko
koda jin wannan batu sai mamaki ya turnuke

Please Login or Register in order to submit comment