Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya sace sarki
a wannan lokaci ne ni da huzein muka dawo cikin hayyacinmu
na dubi likitan sarki cikin alamun mamaki nace
yakai likita wannan wane irin ciwo ne ya sami mahaifina alhalin ina tare dashi
tsawon shekaru amma ban taba ganinsa a cikin irin wannan
hali ba sai yau
koda jin wannan batu sai likitan ya sunkui da kansa kasa
yayi shiru kamar ba zaice komai ba har sai da na daka masa
tsawa sannan ya dago kai ya dubeni a tsorace bakinsa na rawa yace ka gafarceni ya
shugabana ka sani cewa sarki ya haneni da na sanar da kai komai dangane da
rashin lafiyarsa, sa add anaji wannan batu sai na sake fusata na zare takobina na
dora kaifinta akan wuyan likitan nace na rantse da
darajar sarki idan baka sanar dani wannan al amari ba yanzun zan kashe ka
koda jin haka sai jikin likitan ya kama tsuma ya budi b baki
cikin in ina ya ce tun ranar da wasikar sarki shardas
ta iso birninmu na askandariyya fadar mahaifinka yaji sakon
da ta kunsa a lokacin ya kamu da ciwon zuciya ina mai sanar dakai cewa
wannan ciwo yana da tsananin hadari domin zai iya zama
sanadin ajalinsa a ko yaushe cikin kankanin lokaci muddin zai rinka fuskantar abinda zai bata masa
rai koda likita
yazo nan a zancensa sai na durkusa kasa na fashe
da matsanancin kuka
al amarin da ya karya zuciyar yarima huzein kenan, shima

ya fashe da kuka AA Misau Ke Magana
nan take naji na tsani sarki shardas fiye da komai
a duniya kuma na kudurce a raina cewar in dai wannan ciwo
ya zamo sanadin ajalin mahaifina sai na yaki sarki shardas gaba
da gaba duk da na san cewa hallaka zanyi
muna cikin wannan haline muka ji an kwankwasa mana kofa
sai ga wakilin sarki shardas kuma dan uwansa mubairu
ya shigo cikin dakin da muke, koda ya ganmu muna kuka kuma
ya ga sarki a kwance a gefe daya yana barci
ga likita zaune a kusa dashi sai yayi dan guntun murmushi
sannan ya dubeni yace yakai yarima hulbasu ka sani cewa nazo ne gareka domin ka sanar
dani abubuwan da sarkina ya umarceka daka sanar dani
domin na rubutasu nakai masa, koda jin haka sai na dago kai na dubeshi
cikin tsananin fishi nace ashe baka da hankali da nutsuwa?
Kana ganin halin da mahaifina yake ciki ne zaka zo min
da wannan maganar banzar ? Ta yaya kake tsammanin zan iya maka bayani a yanzu bayan
ina cikin tashin hankali da damuwa, koda jin haka sai ran mubairu ya baci
ya daka min tsawa mai karfi tare da nunani da dan yatsa
yace
babu ruwana da batun halin da mahaifinka yake ciki domin kuwa umarnin sarkina na gaba dashi
maza ka sanar dani abinda nazo sani kafin fishin sarki ya
tabbata a kanka
yana gama fadin hakan sai ya zauna a kusa da ni ya fiddo littafi, tawada da alkalami domin yin
rubutu
ni kuwa sai na tattare hannun rigata kamar zan zauna a
gabansa amma sai na shammaceshi na gabza masa wawan naushi a
fuska
sabo da karfin naushin sai da ya wuntsila da baya sau uku a lokacin da jini
yai feshi daga cikin bakinsa, ai kuwa sai ya taso da alkafira yai tsalle ya doki
tawa fuskar da kafarsa, nima na gwaru da bango na fasa baki
kafin na mike tsaye ya danneni kuma ya zaro wata wuka zai caka min a kirjina
sainayi wuf na rike hannunsa, a sannan ne likita da sauran
hadimanmu suka kurma uban ihu suka ruga waje da gudu
suna kiran dakaru domin su kawo dauki, yarima huzein
ne kadai tsaye a gabana yana kallon abinda ke faruwa
jikinsa na karkarwa sabo da tsananin razana
mubairu yaci gaba da kokarin dannan wukarsa a cikin kirjina, ni kuma naci gaba da kokarin
hanashi samun nasara, amma sai karfinsa ya rinjayi nawa
har wukar tasa ta dan sokeni na kwalla ihu sakamakon
tsananin zafi da zogin da naji, a lokacin da jini ya fara bulbulowa daga cikin kirjina
duk wannan abu dake faruwa sarki na kwance a gefe daya
yana shara barci bai sani ba
Koda yarima huzein yaga saura kiris mubairu ya sami nasarar hallakani sai yai
wuf ya zare wuka a jikinsa ya dako tsalle sama ya sokawa mubairu a wuya
take wukar ta lume ta faso makogwaronsa ya sulale
kasa matacce
huzein ya sunkuya a rikice ya kama
Wukar tasa domin ya zareta daga cikin wuyan mubairu
A dai dai wannan lokaci ne dakaru
sarki shardas suka rugo
izuwa cikin dakin su da yawa rike da makamai, koda suka
ga yarima huzein yana zare wuka a cikin wuyan muhairu

kuma gashi ya zama gawa sai suka yi caraf suka daureshi
ni kuwa sai na taso da sauri izuwa kansu na hausu da sara
da suka domin na kwaci dana a hannunsu
duk da cewa suna da yawa amma sai da na tarwatsa su na kashe sama da mutum arba in
Al Amin Ahmed Misau Ke Typing,
ina cikin tsakiyar yin
yaki dasu ne naji anyi min wani wawan duka a kirji
saboda karfin dukan sai da nayi sama na gwaru a jikin
katangar dakin na fado kasa a galabaice
lokacin dana farfado sai na tsinci kaina a tsakiyar fadar
sarki shardas kwance a kasa
A gefen damata yarima huzein ne a daure cikin sarka
a haguna kuma mahaifina ne tare da dukkan dakarunmu da
kuyanginmu suma duk a daure cikin sarka zaune akan karagar mulki sarki shardas ne
rungume da gawar dan uwansa muhairu yana ta
faman rusa kuka, nan take zuciyata ta buga da karfin gaske na kamu da tsananin tsoro irin wanda
ban taba jinsa ba a rayuwata
ba komai ne ya sa ni jin wannan tsoro ba face tunanin cewa
sarki zai kashe mune gaba dayanmu, idan ya kashemu
kuma matata luzuraina ta mutu a wajen haihuwa shike nan fa duk
burinmu ya tarwatse kuma lokacin faduwar kasarmu yazo
a dai dai wannan lokaci ne yarima huzein ya dubeni a lokacin da
hawaye ya zubo masa yace yakai abba na ka gafarceni
domin na janyo mana abinda zai kawo karshen mu gaba daya
AA Misau Sunana
sa adda naji wannan batu sai hawayen takaici ya zubo min na
dubeshi nace
yakai dana baka bukatar rokona gafara domin baka aikata
laifin komai ba
tabbas ka kashe muhairu ne domin ka ceci rayuwata
babu wani da da zai bari a kashe mahaifinsa a gaban idanunsa
muddin zai iya hanawa
koda jin wannan batu sai mahaifina ya dubi yarima huzein cikin alamun tsananin
tausayi a lokacin da shima hawaye ya zubo masa yace yakai jikana huzein hakika
kayi babban kuskure daka ceci rayuwar mahaifinka a
hannun muhairu domin hakan zai janyo asarar da babu abin
da zai biyata
gama fadin hakan ke da wuya sai sarki shardas ya mike
tsaye daga kan karagar mulkinsa ya ajiye gawar muhairu akan karagar sannan
ya share hawayansa ya dubi mahaifina fuskarsa a murtuke sannan ya dubeni
kuma ya dubi huzein yace yaro ka kashe mini dan uwa
wanda shi kadai ne ya rage mini a duniya inda zan kashe gaba dayan mutanen kasarku mazanku da
matanku
jininku ba zai goge bakincikin abinda na rasa ba
zan dasawa mahaifinka bakin cikin da har ya mutu ba zai manta da ni ba domin hakan ne kadai zai
sa zuciyata ta lafa daga
ruruwar wutar bakinciki
koda gama fadin haka sai sarki shardas ya sa aka kwanceni daga cikin sarkoki
sannan ya zare wata sharbebiyar wuka ya cillo mini ita na
cafe kuma ya zare takobinsa yace nine na doki kirjinka dazu ka suma sa adda kake kashe dakaruna
koda ka manta cewa na gaya maka cewa digon jinin
daya na wakilaina da zan tura birninku dai dai yake da digon jinin mutanenku saba in

to ku sani cewa a yanzu jinin mutum saba in ba zai zamo fansar dan uwana ba
abinda nake bukata shine ina son uba ya yanka dansa
da hannunsa yanzu a gabana ko kuma na kashe ka da dukkanin jama arsa gaba daya
koda jin wannan batu sai mahaifina ya fashe
da kuka ya risina ga sarki shardas kuma ya zube kasa gaba daya ya yi masa sujjada
sannan ya dago kai ya dubeshi a lokacin da hawaye ke
shatata bisa kumatunsa ya kuma dubi gaba dayan fadawan
sarki shardas da mutanan gari yace yakai sarkin duniya ka dubi yadda na kaskanta kuma na
wulakanta haka a gaban
talakawanka a matsayina na sarkin da ya gawurta a wannan nahiya tamu ka dubi darajarr sarauta ka
canja wannan nufi naka
koda jin haka sai sarki shardas ya girgiza kai yace
ai bana yin magana biyu na gama yanke hukunci
ko danka ya yanka nasa dan yanzu take ko kuma na kasheka a gaban idansa kuma na kashe gaba
dayan dakarunka
da kuyanginka da duk hadimanka, mahaifina ya fashe da kuka yace yanzu
jinina ni kadai ba zai fanshi jinin dan uwanka ba ? Sarki shardas ya dubi katon badakarensa mai rike
da wata katuwar gudumar danko yace dashi
yakai KALBAN ka buga gangarka sau goma idan yarima
hulbasu bai yanka dansa ba kafin bugu na goma zan kashe mahaifinsa da duk jama arsa
koda jin wannan umarni sai kalban ya daga gudumarsa ya
doki wata katuwar ganga dake rataye a jikin wani
dogon karfe
take sautin gangar ya cika birnin gaba daya
a dai dai wannan lokaci ne huzein ya kama jan guiwarsa
kasancewar a daure yake cikin sarka ya iso gabana ya kwanta kasa ya dubeni yana mai murmushi
gami da zubar da hawaye yace yakai abbana ma za ka yankani domin ka kubutar da mahaifinka da
jama armu
ka sani cewa zan mutu a cikin farin ciki tunda da jinina ya zama fansa ga rayuka masu yawa
a wannan lokaci kalban yaci gaba da buga gangarsa
har yayi bugu na biyar
sa adda naji wannan batu na dana huzein sai hawaye ya zubo mini na
dubeshi nace ka gafarceni yakai dana kayi sani cewa
zan yanka ka ne ba don na ceci rayuwata ba ko ta ubana ba sai don Rayuwar jama armu ga su can
wadanda suka sallama
rayuwarsu don biyayya a garemu lallai ina son su koma
gida a raye domin su rungumi iyalinsu.........
BABBAR MAGANA KENAN
SHIN HULBASU ZAI YARDA YA YANKA DANSA YARIMA HUZEIN ?
.
IDAN YA KASHE SHI IDAN YA KOMA BIRNIN ASKANDARIYYA MAI ZAICE DA
MAHAIFIYARSA ?
.
SHIM MAHAIFIYAR YARIMA HUZEIN TANA HAIHUWA LAFIYA?
.
INA LABARIN JARUMA SIYAMA DASU YARIMA HULKAS ?
.
Marubucin Littafin Yace Mu Hadu A Littafin Tsatsuba Na gaba Don Jin Ci Gaban Wannan
Kasaitaccen Labari.
Marubucin Littafin Wato
The King Of Adventure Story
Malam Abdul aziz Sani M/Gini

Saikuma Ni Al Amin Ahmed Misau wanda nake jagorancin typing din wannan littafi
nake cewa Mu zama lafiya saimun hadu a littafi na bakwai....
Dont Forget My Name
AA Misau

TSATSUBA 7
Littafi na bakwai 7
Hausaebooks
Abdulaziz sani M gini
Made by:- Shuraih Usman

Domin samun wasu littatafanmu sai ku shiga nan kuyi like http://fb.com/hausaebooks

SATSUBA
Littafi Na Bakwai (7)
Part A.
.
Marubucin Littafin
Abdul azis Sani M/Gini
Typing by..
Al amin Ahmed Misau.
Inkiya..
Shagala Ko Guyson
whtsap No. 08064594218
Doka Banyarda ayi edit na post dinaba ba tare da izinina ba
.
Labari ya Zowa Shagala Cewar:.....
.
Lokacin da Sarki Hulbasu ya gama fadawa dansa
yarima Huzein wannan bayani sai ya rufe idanunsa
a lokacin da hawaye ya zubo masa cikin tsananin
bakin ciki mara misaltuwa ya yanga Yarima Huzein
tare jini yai tsartuwa daga cikin wuyan huzein a
lokacin da Hulbasu ya kurma uban ihu na takaici da
bakin cikin ganin cewa ya yanka dansa da hannunsa
shi kuwa mahaifin Sarki hulbasu wato Sarki yana
ganin sa adda Hulbasu ya yanka yarima huzein da
hannunsa sai nan take ya hadiyi zuciya ya sulale ya
baje a kasa matacce
koda sarki hulbasu yaga mahaifinsa ma ya
mutu kuma ga gawar dansa yarima huzein a gabansa
sai ya kama sambatu yana kai kawo a tsakanin
gawarwakin biyu tamkar mahaukaci sabon shiga

shi kuwa sarki Shardas sai ya bude da dariyar farin ciki
yayi ta kyalkyala dariyar tamkar ba zai taba dainawa
ba
lokacin da sarki hulbasu yazo dai dai nan a labarin
da yake baiwa hailur sai yayi shiru sa adda hawaye
ya zubo masa
yana hada idanu da hailur sai yaga shima hawaye ke
sartu akan kumatunsa yana mai kurawa hulbasu idanu
cikin tsananin tausayawa
hailur yaja dogon numfashi yace tabbas cin zarafin da
sarki shardas yayi maka ya ninka nawa saboda kai
ya tilastaka ka yanka danka da hannunka kuma
ya zamo sanadin mutuwar mahaifinka kuma
yanzu gashi ya mai daku bayinsa tunda duk arzikin
kasarku wajansa yake komawa, hakika damu daku
yanzu bamu da wani makiyi a doron kasa wanda
yafi sarki shardas, kuma a halin yanzu yafi karfinmu
babu abinda zamu iya yi masa kuma muna cikin
mugun hadari na masifarsa domin da zarar ya
fahimci cewa ina raye kuma ina tare dakai mu duka
har iyalanmu tamu ta kare, koda hulbasu yaji wannan
batu sai yai ajiyar zuciya cikin alamun tsananin
fargaba da takaici sannan sai jikinsa ya kama tsuma
zuciyarsa ta kama tafarfasa kamar zata kone, yace
to yanzu shike nan haka zamu cigaba da zaman jiran
ranar da sarki shardas zai gano sirrinmu sannan yazo
ya gama damu
hailur ya girgiza kai yace babu wani abu wanda ba zai
yiyu ba a cikin wannan duniya face ba a jarraba
shiba komai nisan jifa kasa zai fado kuma komai karfin
mutun da isar mulkinsa akwai ranar da zai fadi
babu wata cuta wacce bata da magani kamar yadda boka
zamaranu ya shaida maka cewa zaka iya hallaka sarki
shardas amma sai an mallaki hular lamsara to me zai
hana mu tafi neman wannan hula tunda ance mai nema yana
tare da samu
gwara mu rasa rayukanmu a kokarin neman
wannan hula da dai mu zauna har makiyinmu yazo ya samu
nasarar hallaka mu muna ji muna gani ka sani cewa
ba karamin aiki bane a gabanmu idan har muna son
mu ga bayan wannan babban makiyi namu
dolene sai mutum ya sadaukar da wani abu idan
yana son ya sami wani
da farko dai dolene ka ajiye sarautarka kuma ka
cire dukkan tsoro daga cikin zuciyarka dolene mu kawai da gaba dayan
dakarun sarki shardas da hadiman da suka rako
matata domin mu aiwatar da abinda ke gabanmu
ka ayyana a ranka cewa zamu fita neman hular lamsara ne ba don komai ba sai domin
mu dauki fansa akan sarki shardas
shin yanzu zaka iya
hakura da karagarka ta mulki da kuma kasarka da
jama arka domin cika wannan buri naka

koda jin wannan batu sai hawayan takaici ya
zubowa sarki hulbasu yace ai bani da wani zabi wanda
yafi na hakura da komai din nayi wannan gagarumar
tafiya in ba haka ba kuwa zan rasa komai da kowa nawa
yanzu akwai abu daya nake tunanin yadda zamu
sami nasarar yinsa a cikin nasara wato yadda zamu iya
kawai da dakarun da suka rako shadila, koda jin
wannan batu sai hailur yayi murmushin yake yace
haba ya shugabana a cikin kasarka fa suke wadannan
dakaru ai kowa a gida sarkine, ni ina da shawara bisa
yadda zamu kawai da su cikin kankanin lokaci a
saukake
ba tare da mun fuskanci wata matsala ba
shawarar kuwa guda biyu ce da farko zamu iya amfani
da sanya musu guba a cikin abincinsu duk suci su mutu
idan kuma wannan hikima bata yi aiki ba sai mu ritsasu
a cikin masaukinsu mu da dakarun masu yawan da ya
ninka nasu sau uku mu yakesu, ni ka bar mini jagorancin
dakarun da za suyi wannan aiki
iana mai tabbatar maka da cewa zan yi iya
kokarina na tabbatar da cewar dayansu bai tsira
da rayuwarsa ba don kada yaje ya kai wa sarki
shardas labarin abinda muka aikata, lokacin da
sarki hulbasu yaji wannan shawara guda biyu na
hailur sai yaja dogon numfashi gami da ajiyar zuciya kuma ya dubeshi cikin
alamun damuwa da fargaba sannan yace
da farko dai idan muka yi yunkurin kashesu
da guba ba lallai bane ya kasance cewa dukkaninsu zasu
ci abincin kaga kenan akwai yiyuwar wani daga
cikinsu ya tsira da rayuwarsa kuma ya sulale daga cikin birnin ya gudu bamu sani ba
idan kuwa hakan ta faru asirinmu ya gama tonuwa haka kuma
muka ce zamu yakesu anan cikin birnina a
masaukinsu jama a zasu jiyo kururuwar yakin koda
kuwa cikin dare ne sannan kuma ka san cewa suma fa
zakwakuran mayaka ne wadanda suka san TUGGUN YAKI
za a iya samun wani daga cikinsu ya sami damar sulalewa
ya gudu
idan ma hakan bata faru ba babu mamaki a cikin
jama ar gari akwai dan leken asirin sarki shardas mai sa ido
akan wadannan dakaru
Nasa da suka rako gimbiya shadila izuwa kasata don
haka ko wani dan motsi ya gani wanda bai yarda dashi ba
yana iya garzayawa yakai labari, lallai akwai mummunan
hadari a cikin duk wadannan batu sai ya numfasa yace ya kai
abokina yakamata ka sani cewa matsoraci bashi zama
gwani ko waye don haka dolene mutum ya siyar
da ransa wajan neman sa a bisa bukatar dake
gabansa
ko ka so ko kaki ko ka gudu ko ka tsaya watarana sai sarki
shardas yazo ya cika da yaki har gida tinda shi makiyi
har abada a cikin kokarin ganin bayan makiyinsa yake
lokacin da hailur yazo nan a zancensa sai jikin

sarki hulbasu yayi sanyi ya gamsu a ransa cewar bashi
da wani zabi wanda yafi ya yi amfani da wannan shawara
ta hailur don haka sai yayi shiru yana tunani har izuwa tsawon
yan dakiku daga can kuma sai ya dago kai ya dubeshi
yace
na amince da duk shawarar da ka bani a daren yau zan
hadaka da amintaccen sarkin yakina domin
ku shirya duk abinda kuke ganin ya dace akan
wannan makiyi namu nidai kawai na baku wuka da nama
amma ina son ku gaggauta shirya yin wannan gagarumar
tafiya tamu ta neman hular lamsara Al amin Ahmed Misau
nake magana
koda jin wannan batu sai farin ciki ya lullube hailur yayi
godiya sannan ya mike tsaye da nufin ya fice daga
cikin dakin sai sarki hulbasu ya ruko hannunsa yace
ya zaka tafi baka tsaya kagana da tsohuwar matarka ba
babu wanda ya isa ya raba Hanta da jini
soyayyarka da matarka shadila tafi gaban wani dan
adam ya rubuta saboda tsoron sarki shardas ba zan hanaka
ka gana da ita ba tuni na shirya wannan ganawa naku
koda gama fadin hakan sai sarki hulbasu ya tafi zuwa bakin
kofar wannan daki da suke zaune ya kira sunan wani hadimi
nasa yace dashi ya ruga izuwa can cikin gidan sarautar bangaren matarsa ya taho
da shadila cikin hanzari hadimin yace an gama ya shugabana
nan take ya ruga da gudu izuwa cikin gidan sarautar shi
kuwa sarki hulbasu sai ya yiwa Hailur sallama ya tafi
tafiyarsa keda wuya sai farin ciki mai dumbin yawa ya turnuke hailur yaji
kamar duniyar nan gaba daya aka bashi don haka sai ya
mike tsaye ya kama kai kawo fuskarsa cike da annuri
gami da farin ciki wanda ba zai misaltu ba
yana cikin wannan haline yaji an turo kofar dakin
an shigo cikin sauri ya waigo kawai sai yayi arba
da shadila a tsaye ta kura masa idanu tana zubar da hawaye
daki daki nan take shima idanunsa suka ciko da kwallar
ya fara zubar da hawaye tsawon yan dakiku sun kurawa
junansu idanu suna ta zubar da hawaye kamar ba zasu
daina ba
daga can kuma sai suka yi murmushi a tare suka ruga suka rungume
junansu kuma suka fashe da kukan farin ciki na
sake saduwa suna masu kankame juna sosai
ba tare da son saki juna ba sai shadila ta ce yakai
mijina yanzu ashe kana nan raye a cikin wannan duniya
amma ban sani ba
koda jin wannan tambaya sai hilairu ya janye jikinsa
daga cikin nata suka fuskanci juna yace yake abar begena
dare da rana
Al amin Ahmed Misau kiyi sani cewa ban taba mancewa
dake ba tsawon dakika daya daga
sa adda muka rabu
kawo i yanzu ban taba zaton cewa zamu sake
saduwa ba a cikin wannan duniya tunda ke kanki kin
sa a ranki cewa na mutu na sani cewa sarki shardas

ya aureki bisa dole to amma abu daya nake so na gani
shin kin haife cikin dana dana barshi a tare dake
ko kuwa sarki shardas ya kasheshi, koda jin wannan
tambaya sai shadila tayi shiru ta kasa bashi amsa
cikin hanzari hailur ya janye jikinsa daga cikin na shadila ya girgiza
kafadunta ya ce cikin daga murya ki gaya mini
gaskiyar ala amari kada ki boye mini komai shin
dana yana raye ko ya mutu koda jin haka sai shadila
ta fashe da kuka ta kasa bayani saboda tsoron abinda
zai biyo baya
kwatsam sai sukaji an turo kofar dakin an shigo duk su biyun
suka waiga bayansu a firgice da sauri don ganin ko wane ne ya shigo ba wani bane
face yarima Hulkas tsaye idanunsa suna zubar da hawaye
kuma ya kurawa hailur idanu koda shadila taga hulkas
tsaye a gaban hailur kuma taga irin kallon da yake yi
masa har yana zubar da hawaye sai ta kamu da
tsananin tsoro jikinta ya kama tsuma saboda ta
fahimci cewar abinda take tsoron kada ya faru ya gama
faruwa
cikin sanyin jiki da alamun tsananin takaici
hulkas ya nufi inda shadila ke tsaye a lokacin da hailur
yabi hulkas da kallo ko kiftawa baya yi domin ya gane
cewa lallai wannan yaro hulkas dansa ne domin hatta irin gabobin jikinsa iri daye ne
nan take shima hailur yaji idanunsa sun ciko
da kwallah
lokacin da hulkas ya iso daf da shadila sai ya kama
hannayanta ya ruke yace yake ummina menene
dalilin da yasa tuntuni baki shaida mini cewa sarki shardas
ba shine mahaifina ba, kinsan irin tsananin son da nake
yiwa sarki shardas, kuma kinsan yadda na shaku da shi ainun
tun ina kankani kawo i yanzu, yanzu da wanne ido
zan fuskanceshi
Al amin Ahmed Misau Nake magana A matsayin babban makiyina Alhalin
shine ya rene ni ya inganta rayuwata
ki sani cewa sarki hulbasu ya bani labarinki kaf
da asalinki da yadda sarki shardas ya murkushe
jama arku kuma ya jefe mahaifina karkashin wannan
tsauni mai mugun zurfi sannan ya kamaki da karfin
tsiya ya
Maisheki matarsa har da dub irin barazanar da yake
yi miki akan kada ki sanar dani komai sannan ya sanar
dani yadda sarki shardas ya tilastashi ya yanka
dansa na cikinsa sanadin da ya zamo mutuwar mahaifinsa
ya kunsa masa bakin cikin da har abada ba zai gushe ba a doron kasa
tabbar sarki shardas ya cika babban azzalumi da babu
kamarsa a doron kasa kuma dolene na
kasheshi da hannuna, koda yarima Hulkas yazo nan a zancensa sai
ya kurma uban ihu kuma ya durkushe kasa bisa
guiwoyinsa biyu ya fashe dda matsanancin kuka
koda ganin haka sai itama shadila ta fashe da kuka ta kasa rarrashinsa
cikin sanyin jiki hailur ya dingisa ya isa gaban hulkas
ya sunkuya ya dafa kafadar hulkas, koda hulkas yaji

hannun hailur ya tabashi sai yai shiru tamkar daukewar
ruwan sama sannan ya dago kai suka kurawa
junansu idanu a lokacin da kowannansu ke zubar
da hawaye har izuwa tsawon yan dakiku daga can kuma
sai hulkas ya mike tsaye zumbur ya rungume hailur
suka fashe da kuka a tare
komai rashin tausayin mutum idan yaga lokacin
da wannan da da mahaifinsa suka rungume junansu
alhalin basu taba ganin juna ba basu san juna ba
sai yau
dolene zuciyarsa ta karaya ya tausaya musu
Al amin Ahmed Misau Sunana, Koda ganin abinda ya
faru sai farin ciki ya lullube shadila
sai da hailur da
hulkas suka dan jima a kankame da juna sannan hailur
ya janye
jikinsa daga cikin na hulkas ya dubeshi a cikin
nutsuwa yace yakai dana ina son ka yayyafawa zuciyarka
ruwan sanyi ka sani cewa komai yana da lokacinsa
ina mai tabbatar maka da cewa a halin yanzu in da
duniyar nan gaba daya zata taru kaf ba zata iya
kawar da sarki shardas ba saboda yana kan sharafinsa
babu mai iya ganin bayansa a yanzu face jarumin
da ya mallaki HULAR LAMSARA; Kai ni Al amin naji
sai wani Zancen Hular Lamsara suke da wahalar Samunta
Naga dai Nima jarumine fa Saboda haka nima bari
na dauki Takobina Na je neman wannan Hula domin na
kawar da Sarki shardas Hahahaha
zan iya Kuwa Freinds ?
Bisa wannan dalili ne ni da sarki Hulbasu muka yanke shawarar
mu rokeku kuma mu
kawar da dukkanin dakarun da suka rakoku sannan
mu bazama duniya neman Hular lamsara saboda kai
kanka yanzu rayuwarka na cikin mugun hadari idan har shardas ya gano ka san cewa shine ya
tarwatsa rayuwar
mahaifinka na asali ba zai barka da raiba to amma
akwai wata matsala guda daya, koda jin wannan batu sai
hulkas ya dubi hailur cikin alamun matukar mamaki yace yakai
abbana me cece matsara kuma
Hailur yace sarki shardas ma ba zai iya hallaka ka ba
face ya samo wannan hula ta Lamsara kuma a halin
yanzu tuni shida bokansa sun fita farautar wannan hula
sun bar garinku a cikin mugun hali domin yanzu haka ana fama
da fatara yunwa da fari a kasar tun daga ranar da kuka
baro birnin kai da mahaifiyarka
ya zamana wajibi
mu gaggauta tafiya neman hular lamsara tun
gabanin makiyinmu sarki shardas ya rigamu samu
Koda jin wannan batu sai
hankalin yarima Hulkas ya dugunzuma ainun ya rasa abinda ke masa dadi
a duniya
musamman da yaji cewar mutanan kasarsu na can cikin

mugun hali na fatara
da yunwa kuma ga batun gagarumar tafiyar dake gabansa ta neman hular
lamsara
hular da babu wanda ya san inda take....
Kai bari dai na dakata A nan domin nima naje nayi
shirin tafiya neman wannan hUla saboda naga Alamar
sun tsorata suna tsoron fita nemanta
amma akwai wanda zai iya rakani kuwa hahahaha
Kafin nan Nine
Al amin Ahmed Misau
Guyson Ko A square
nake cewa sai gObenkuSATSUBA
Littafi Na Bakwai (7)
Part B.
.
Marubucin Littafin
Abdul azis Sani M/Gini
Typing by..
Al amin Ahmed Misau.
Inkiya..
Shagala Ko Guyson
whtsap No. 08064594218
Doka Banyarda ayi edit na post dinaba ba tare da izinina ba
.
Labari ya Zowa Shagala Cewar:.....
.
Hular da babu wanda ya san ina take
Shikuwa yarima barmas tunda suka shigo cikin wannan
daki tare da yarima hulkas ya zauna a gefe daya yana
ta sauraran bayanin da Hailur ke yiwa hulkas sai takaici
da tausayi suka sashi ya kama zubar da hawaye
dama da dadewa mahaifin sarki hulbas ya bashi tarihin
yadda sarki shardas ya tilastashi ya yanka dan uwansa
yarima Huzein wato yaya ga yarima barmas
sanadin da ya zamo na mutuwar kakansa kenan
nan take zuciyar yarima barmas ta kama tafarfasa
kamar zata kone babu abinda ya tsana a duniya
sama da sarki shardas A cikin wannan haline
aka ga

Please Login or Register in order to submit comment