Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

zaton zai
Samu ba, A tunanin sarki shardas zai yi amfani da
wannan gasa ne ya talauta gaba dayan sarakunan
nahiyar da attajirai domin ya kasance duk karfin
arzikinsu ya dawo hannunsa, shi kuwa wannan gida da aka gina
akan tsakiyar kogi sai da aka shafe shekaru goma sha shida
ana gininsa
ba wai mutane ba hatta aljanu tsegumin gidan suke
suna ta yadashi a duniya, lokacin da aikin ginin
yayi nisa sai da sarki shardas ya sare, domin gani yayi
tattalin arzikinsa na neman karyea, bisa dole ya kara ninka harajin da mutane ke
biya a kasarsa kuma ya tsananta farautar bayi da kai
harin sumame ana kwace dukiyoyin jama a wata nahiyar ana maishe su bayi
A haka dai aka samu aka kammala wannan kasaitaccen gida
na gaban kwatance, bayan an kammala ginin gidan ne
sarki shardas yasa rana ta wannan gasa wacce a ranar za 'a
bude wannan
gida
wohoho tun kafin ranar tayi da tsawon sati hudu
birnin nasa ya cika ya tumbatsa da baki daga ko'ina
na duniya, yazamana cewa ko ruwan sha mutum ke
siyarwa a garin yana samun kudade masu yawa a
wannan lokaci kudin shiga birnin ma da aka samu ba'a
taba samun kamarsu ba
Al amarin mahaifina kuwa wato Attajiri Amsar............

Wow Domin jin yadda zata kasance mu hadu a part na gaba
amma kafinnan
nidinne dai
Al amin Ahmed Misau
Guyson ko A square
nake cewa mu zama lafiyaTSATSUBA
Littafi Na Takwas (8)
Part C.
.
Marubucin Littafin
Abdul azis Sani M/Gini
AA Misau Ke Magana
.
Labari ya Zowa Shagala Cewar:.....
.
AL'AMARIN MAHAIFINA KUWA WATO ATTAJIRI AMSAR, a
cikin daji ya yada sansani da tazarar kwana uku
a sannan ne ya debi dakaru dari biyu kacal ya bar
ragowar dari takwas domin suyi gadin mahaifiyata
koda yazo zai yi sallama da mahaifiyata sai ta
fashe da kuka tace yakai mijina ban taba rabuwa dakai ba
tsawon yini guda amma yanzu gashi zaka tafi halartar
wannan gasa har tsawon kwanaki bakwai lallai zan
kasance a cikin kewarka da begenka,
ka sani cewa na sami labari cewa wannan gida da sarki
shardas ya gina a duk fadin duniya a yanzu babu
kamarsa a kyau da kawatuwa lallai ina yi maka
fata da addu ar ka mallakeshi, kuma lallai ina son
naga wannan gida da idanuna koda kuwa ba zan
sami damar shiga cikin sa ba
sa adda mahaifyata tazo nan a jawabinta sai nan take
idanun mahaifina suka ciko da kwallah ya dubeta cikin alamun
tsananin takaici
yace ki gafarceni ya masoyiyata kiyi sani cewa wannan
ne karo na farko da kika tambayeni abinda ba zan iya
baki shiba a cikin wannan
duniya
ki sani cewa idan na kuskura na shigar da ke cikin
wannan birnin karshen zamana dake yazo bare ma
har na kaiki kiga wannan kasaitaccen gida wanda za ayi gasa a kansa, wannan
shine kashedin da bokayena suke yi mini idan kuma
kina son mu rabu ne to shikenan sai na kaiki kiga
wannan gida
koda jin wannan batu sai mahaifiyata ta rungume attajiri amsar ta
fashe da matsanancin kuka tana mai kankameshi a
kirjinta tace ai ko duniyar nan kaf za a bani in dai za a
rabani dakai bana bukatarta, koda jin haka sai farin ciki ya
lullube mahaifina
Al amin Ahmed Misau, sai da sukadan jima a kankame
da juna sannan ya janye jikinsa daga cikin nata sukayi
sallama ya hau kan dokinsa, kafin ya tafi sai da ya dada
jan kunnen dakarun nasa su dari takwasa da zasu yi gadinta

da kuma kuyangi uku da zasu yi mata hidima yace
lallai su tabbatar da cewar wani abu bai kusanceta
ba bare ya cutar da ita
nan dai mahaifina attajiri amsar tare da dakaru dari
biyu suka nufi cikin birnin sarki shardas , mahaifiyata
da sauran jama arsa suka bisu da kallo har sai da
suka ga sun kule
'' '' ''
BIRNIN ya ciki ya tumbatsa da al uma duk inda ka duba
babu abinda zaka gani face kawunan bil adama
rututu babu masakar tsinke, sai da ta kai cewa an rasa
gidaje na haya inda ake saukar baki, dole jama a
suka rinka kwana a kasuwa wasu ma a gefen gari suka
rinka kafa tantuna sai dai siye da siyarwa ya shigo dasu
cikin birnin
gidan sarautar sarki shardas kuwa ya cika da manyan
sarakuna manyan attajirai manyan bokaye da
manyan yarumai kuma kowannansu an bashi masauki mai daraja kuma
an girmamashi
A rayuwar sarki shardas yana son zama tare da wadannan
mutane guda hudu wato sarakai, attajirai bokaye da
jarumai
wato Mu ke nan ehm Al amin nake, har izuwa
safiyar ranar da za ayi wannan gasa hankalin sarki shardas bai
gama kwanciya ba duk da cewa shi ya tara
dukkanin sarakunan nahiyar da kuma amsu gayyata
Al amarin daya sa wazirin sarki shardas ya fahimci
cewar sarkin nasu yana cikin wata damuwa don, haka sai
ya dubeshi cikin girmamawa yace wai shin menene yake
damunka ?
Naga sai kallon kofar fada kake yi shin akwai wanda kake
son ganin zuwansa ne, sarki shardas yayi ajiyar
zuciya sannan yace ai banga sarkin attajiran ba attajiri
Amsar ibn Warhas,
anya kuwa zai amsa wannan gayyata tawa, koda jin
wannan batu sai waziri ya dafe kirjinsa kuma ya
zazzaro idanu yace, haba ya sarkin sarakuna , kaine fa zaki
uban dawa kuma kaine dodon maza sa gudu maganin
ki gudu
yanzu kai a tunaninka akwai wani daya isa a wannan
duniya
da zai ki amsa gayyatarka, kome mutm yake takama
dashi kafishi, kuma duk wanda yaja dakai sai yakai
kasa
sarakuna nawa ne suka mutu a dalilin bakincikin da ka
kunsa musu
bokaye nawa ne suka jarraba karfin tsafinsu akanka
suka mutu
Attajirai masu tarin dukiya nawa ne ka talautar dasu
ai ina tabbatar maka da cewar ajali ne kadai zai
hana attajiri amsar halartar wannan gayyata taka
kuma ko don ma ya nuna matsayinsa akan sauran attajirai dolene ya amsa gayyatar ka

amma abin tambayar shine wai shin menene dalilin da yasa
ka damu da zuwan attajiri Amsar ibini warhas ?
Koda jin wannan tambaya sai sarki shardas yayi dan
guntun murmushi sannan yace lallai ina son attajiri
amsar yazo wannan gasa saboda sai yafi kowa siyan
wannan gida nawa da daraja, to amma fa ina tsoron
abu guda daya
shin baka ganin cewa yana da kudin da zai iya siyen
wannan gida nawa har ni kuma ya hanani mallakarsa ?
Waziri ya gyada kai yace haba ya shugabana yanzu ashe
akwai attajirin da zai fika kudi a wannan nahiya tamu
ai a ganina ko nawa attajiri amsar ya siyi wannan gida kai
kuma sai ka kara kudinka ko ka ninka akan nasa
sau talatin tunka ka san cewa babu asara a cikin aikata
hakan ka tuna fa cewa daga cikin dokar wannan gasa shine
duk kudin da mutum ya taya wannan gidan ba za a dawo
masa dasu ba
Al amin Ahmed Misau, kaga kenan komai yawan kudaden
da aka tara naka ne kai kadai, koda jin
wannan batu sai farin ciki ya lullube sarki shardas ya
kama yin murmushin murna yana mai cigaba da kallon
bakin kofar fada sannan ya dubi wazirinsa yace gaba
dayan manyan sarakuna da attajiran da na gayyata
sun iso tare da iyalansu tun tsawon yan kwanaki
kafin zuwan wannan rana ta yau me ya sa shi attajiri
amsar baizo da wuri ba bare da iyalansa alhalin na
dade ina son naga matarsa saboda naji ance agaba
dayan birnin hindu babu mai kyanta, abinda yake bani
mamaki shine duk karfin shirin nan nawa na tsafi na
kasa ganin hoton siffar matar tasa a cikin madubin
tsafina kuma a iya bincikena nakasa ganin ranar da zan
ganta
bisa wannan daliline yasa na ke dan shakkar al amarin
attajiri amsar ibn warhas, domin lokacin dana fara zurfafa
a cikin binciken sirrinsa sai na gano cewa yana samun
kariya ne daga wani takadarin aljani wanda ni
kaina ban sanshi ba kuma na kasa gano ko waye shi
hatta bokana abin dogarona ya kasa gano min aljanin
da yake baiwa attajiri amsar kariya, sarki shardas na zuwa dai dai nan
a jawabinsa
kwatsam sai ga attajiri amsar ibn warhas ya shigo cikin
fadar dakaru dari biyu kacal nakewaye dashi
Da shigowar attajiri amsar cikin fadar sai gaba dayam
jama ar dake wajan suka mimmike tsaye suka rinka dukawa suna gaishe da
attajiri amsar saboda kwarjininsa tamkar ya kasance
wani babban sarki, tufafin dake jikinsa ma babu wani
basarake a wajan daya sanya mai kyansa da tsadarsu
saini Al amin Ahmed Misau hatta shi kansa sarki
shardas din kuwa
kai ko mutum bai san attajiri amsar ibn warhas ba yana ganinsa dole ne ya girmama
shi saboda tsabar kamalarsa da kwarjininsa
ko shi kansa sarki shardas wanda kowa ke tsoronsa da

yi masa biyayyar dole ba shi da irin wannan kwarjini
da kamala na attajiri amsar don hatta manyan fadawan
sarki shardas basu san sa adda suka rinka rugawa izuwa
ga attajiri amsar suna kama hannunsa suna sumbata ba
haka ma sauran sarakunan da ke cikin fadar domin kowa
gani yake kamar idan har ya sami nasarar sumbatar hannun
attajiri amsar ya sami tabarrakin da shima zai zamo gagarumin
attajiri kamar attajiri amsar din, koda sarki shardas
yaga yadda ake girmama attajiri amsar sai ya kamu da
tsananin kishi gami da matukar baki ciki ya fara
tunanin cewa babu abinda yafi attajiri amsar dashi face
jarumtaka, tunda yana da mace mai kyan da bashi da
kamarta kuma yana da dukiyar da wata kila tafi tasa yawa
bayan attajiri amsar ya gama gaisawa da manyan
mutane wadanda suka yi ta shan gabansa suna
hanashi zuwa wajan sarki shardas sai ya kukuta da kyar
ya isa inda sarki shardas ke zaune bisa karagar mulki
yana zuwa daf dashi sai ya zube kasa wanwar ya kwashi
gaisuwa tamkar zaiyi masa sujjada don girmamawa
al amarin da yai matukar baiwa kowa mamaki kenan
shi kuwa sarki shardas sai farin ciki ya lullubeshi yaji
kansa yayi nauyi don haka sai ya mike tsaye daga kan
karagar sa ya taka matattakalar ya sauko har kasa har
gaban attajiri amsar ya kama kafadun sa ya tasheshi
tsaye ya rungumeshi cikin tsananin farin ciki tamkar wanda yaga dan uwansa na jini
sannan kuma sai ya kama hannun sa ya jashi zuwa kan karagar
mulki suka zauna tare akan karagar, Al amarin da yai
matukar baiwa kowa mamaki kenan domin ba a taba ganin sarki shardas ya girmama
wani mutum ba kamar haka yadda ya yiwa attajiri amsar
nan take sarki shardas ya bada umarni kuyangi suka shigo cikin fadar dauke da
abinci da abin sha irir iri na musamman irin wanda ba a taba kawowa ba tun daga
ranar da aka fara saukar baki, sai da aka gama ciye ciye da shaye
shaye
ya zamana cewa kowa ya sami nustuwa sannan sarki shardas ya mike tsaye a lokacin
da fadar tayi tsir tamkar mutuwa ta gifta yayi gyaran murya
yace
yaku manyan baki kuyi sani cewa yanzu taro ya cika
tunda sarkin Attajirai amsar ibn warhas ya iso
saboda haka yanzu ba tare da bata lokaci ba zamu
dunguma gaba daya mu tafi izuwa inda wannan gida
yake wanda nayiwa lakabi da suna
DARUL DAULAT !
Duk wanda ya san zai shiga wannan gasa to ya
tafi da dukkan shirinsa amma yanzu za a fadi dokoki
uku na shiga wannan gasa, doka ta farko itace dole ne kowanne
sarko ko kowanne attajiri
ko boka ko jarumin da ya amsa gayyata ya shiga wannan gasa
kuma duk kudin da
ya zuba a gasar ba za a dawo masa dasu ba walau yayi
nasara ko bai yi ba
doka ta biyu itace idan aka shiga cikin wannan gidan gasa
babu wanda zai fito har sai an kammala kuma kowa ya

kwantar da hankalinsa domin an tanaji masauki da isashshen
abincin da kowa zaici har a kammala
Al amin Ahmed Misau, doka ta uku wacce itace ta karshe
itace duk wanda ya lashe wannan gasa dole ne ya baro
kasarsa ya dawo wannan gida da zama tare da iyalansa
har izuwa karshen rayuwarsa, koda sarki shardas
yazo nan a zancensa sai hankalin gaba dayan masu
gasar ya dugunzuma ainun musamman attajiri
Amsar
domin wannan doka ta karshe ba karamar tayar masa
da hankali tayi ba
Nan take ba tare da bata lokaci ba aka fito daga cikin
fada aka debo jakunkunan dinare aka loada akan dawakai
da rakuma da alfadarai sarki shardas ne da kansa ya
jagoranci gaba dayan yan gasar kowa dakarunsa
Na bashi tsaro da kariya aka nufi bakin kogi inda gidan
Darul Daulat yake
sauran jama ar gari kuwa sai da wannan zuga tayi gaba
da tsawon rabin sa'a sannan aka sa dakaru suka yi
musu rakiya
tafiyar kusan rabin sa a akayi aka iso bakin katon
kogin dake bayan gari tun daga nesa hasken gidan
darul daulat ya fara dallare idanun mutane kuma
tsananin girman gidan da kyawunsa ya dimauta kowa hatta su attajiri amsar
kuwa duk da cewa gidan a can nesa yake a tsakiyar
kogi amma kowa ya firgita da ganin irin gini da
akayi masa
a bakin tekun an ajiye manyan jiragen ruwa sama da
guda dari wadanda za a shiga a ketare kogin a isa gidan
na sarakai , attajirai da wadanda suka isa sannan kuma akwai
kwale kwale kimanin guda
dubu na talakawa
da zuwan su sarki shardas bakin tekun sai kowa ya sauka
daga kan dokinsa suka rinka shiga cikin jirgin ruwan
jirgin sarakai daban haka mana na attajirai da sauran
bokaye da jarumai
ko kyakkyawan motsi sarki shardas baya barin
attajiri amsar yayi ma ana baya yarda yayi nesa dashi
don gudun kada wani tsautsayi ya rabasu lokacin da
jiragen ruwan suka yi nisa a cikin kogin suka kusanci
tsibirin da aka gina gidan darul daulat sai kowa ya sake
cika da tsakanin mamaki ba komai ba sai domin ganin tsananin
girman nasa ya kai rabin birnin gaba daya na
sarki shardas
abin da yafi daurewa mutane kai shine' wai shin ta yaya
aka iya gina wannan gagarumin gida ? Tabbas aikin
ginin wannan gida yafi karfin ace mutane ne sukayi
shi dai sai aljanu aljanun ma sai dai idan wadanda suka
gina birnin farisa ne suka yi ginin wannan gida
nan fa kowa ya zama cikakken dan kauye aka rinka
wangame baki ana kallo wasu ma basu san sa adda suka fara
dalalar da yawu ba

sai da gaba dayan jiragen suka iso bakin gabar kogin
daf da kofar gidan sannan kowa ya fito daga cikin jirgin
aka bi sarki shardas a baya, ita kanta kofar wannan
gida inda za a cireta a baiwa mutum ta isheshi
gudanar da sauran rayuwarsa ta duniya kai Madaki Al amin Ahmed Misau Sunana
domin jarine babba saboda anyi tane da zallan dutsen
lu u lu u mai tsawo da kaurin gaske gami da fadi
inda karti dubu zasu taru ba zasu iya daga kofar sama ba
saboda nauyinta su kansu aljanun da suka kerata sai da
aka zabo majiya karfi arba in sannan suka iya
dagata sama suka kafata a jikin ginin, nan take
sarki shardas ya zaro wata kuba ta zinare ya mitsitsiya kuma
siririya ya zurata a cikin kofar mukulli, shigar kubar
keda wuya sai aka ji sakata na zare kansu, wani
zagayayyen mukulli mai kauri da tudu ya rinka zagaya kansa
a tsakiyar kofar har sai da ya kewaya sau goma sha
biyu sannan sakatun suka gama zarewa duka, take
kofar ta bude wanwar da kanta, a dai dai wannan lokaci
ne sarki shardas ya waigo cikin murmushi ya dubi gaba dayan yan gasar yace
duk wanda ya lashe wannan gasa shizan damkawa
kubar wannan gida, yana gama fadin haka sai ya zura
hannunsa cikin kofar mukullin ya zare kubar ya zurata
a cikin Aljihun wandonsa sannan ya kama hannun
attajiri Amsar ibn warhas yaja shi suka kunna kai izuwa
cikin wannan gida na darul daulat, take suma sauran, sarakai
Attajirai da jaruman gasar suka rufa musu baya
Wohoho !! An dade ana bautawa kasa anyi mata ado da
dukiya !
Duk wanda ya sanya kafarsa ya taka lu'u lu'un da aka
shinfida a kasan gidan ya ga yadda ko ina ya kasance
fes fes ! Babu ko kura ko guda daya bare yanah, sai
ya cika da al'ajabi kai kace kullum akwai hadimai sama da
miliyan goma masu share ko ina da gogewa alhalin
babu wata halitta guda daya mai rai a ciki
ba tare da wani bata lokaci ba sarki shardas ya wuce
kai tsaye izuwa cikin wani babban falo na gidan wanda ya
ninka fadarsa sau goma a girma da kawatuwa...
Nima kuma sai nabishi a bayaaaa.
Al amin Ahmed Misau
zan dakata Anan
saikuma Allah ya kaimu
Gobe zamu cigaba
Nidinne dai
Al amin Ahmed Misau
Inkiya
Guyson Ko A square
Dan garin KadunaTSATSUBA
Littafi Na Takwas (8)
Part D.
.
Marubucin Littafin
Abdul azis Sani M/Gini

AA Misau Ke Magana
.
Labari ya Zowa Shagala Cewar:.....
.
BA TARE DA WANI BATA LOKACI BA SARKI SHARDAS YA WUCE
KAI TSAYE IZUWA CIKIN WANI BABBAN FALO NA GIDAN
WANDA YA NINKA FADARSA SAU GOMA A GIRMA DA KAWATUWA
hatta kujerun da shimfidar dake cikinsa babu wanda ya
taba ganin makamantansu, duk yawan jama ar da suka
halarci wannan gasa suna shiga cikin wannan falo sai
suka zama yan kadan tamkar an sanya kwayar gero
guda daya jal akan faranti, har izuwa wannan lokaci
sarki shardas na rike da hannun attajiri amsar ibn warhas,
shi kuma attajiri Amsar yana dogara wani dan karamin
kwagiri na zinare dake hannunsa, kwagiri ne na zinare
wanda aka kawatashi da adon sarauta, irin sane
kwagirin da manyan sarakai ke dogarawa yayin da suke
tafiya don kawata kwalliyarsu, kai tsaye sarki shardas
yaja attajiri amsar suka je suka zauna akan wata
luntsumemiyar doguwar kujera mai daraja, shi kuwa
wazirin sarki shardas tare da sauran fadawansa
sai suka rinka kai sauran manyan baki izuwa mazaunin
da ya dace dasu
Kafin kowa ya zauna sauran talakawa sun iso a cikin
kwale kwale dakaru na shigowa dasu suma ana zaunar
dasu a inda ya dace duk a cikin wannan babban falo
sai da kowa ya gama zama sannan sarki shardas
ya mike tsaye yayi jawabin farinciki na ganin wannan
rana gami da godiya ga dukkanin manyan baki da suka
amsa gayyata sannan yace yaku jama ata ina mai sanar
daku cewa inda zan jagoranceku mu zagaya cikin wannan
gida domin muga ko ina da ina kuma muga duk irin
daular da aka shirya a cikinsa da sai mun shafe a kalla
tsawon kwaanaki bakwai bamu gama shiga kowanne
daki da kowacce fada ba
A cikin wannan gida na darul daulat akawai dakuna
guda casa'in da tara
sannan akwai fadoji guda arba in kowacce fada guda ta
ninka fadata sau talatin a girma, akwai kasuwa da asibiti
a cikin wannan gida kuma akwai gidajen gona guda arba in
da bakwai
Sannan lambu na shakatawa kala tamanin da bakwai
Al amin Ahmed Misau , duk wanda ya lashe wannan gasa
ya mallaki wannan gida to a ranar da ya tare a cikinsa
ne hadiman Aljanu dubu dari tara da casa in da tara
zasu fara kular masa da gidan, sauran hadimai na aljanu kuwa ya nemo iya adadin
da yake bukata
Yanzu take ba tare da bata wani lokaci ba zamu fara
wannan gasa kuma ta kaina za a fara don haka ni na
bude wannan ciniki da dinare miliyan uku
ga kudina lakadan yanzu zan dankasu a hannun
alkalan Kasa !!?

Sarki shardas na gama fadin hakan sai ya tafa hannunsa
nan take hadimai sukaje can wajen kofar gidan
suka fara dauko buhunhunan dinare daga kan dawakai
da rakuma na sarki shardas suna shigowa dasu suna zubesu
a tsakiyar wannan babban falo har sai da suka ajiye jaka
talatin wato kowacce jaka na daure da dinare dubu
dari
koda ganin wannan al amari sai sarakai da attajirai
suka kama yin murmushi saboda sun raina kudin da sarki
shardas ya fara bude wannan gasa dasu duk kuwa da cewa
kudade ne masu yawan gaske sun ishi talaka iya rayuwarsa
koda sarki shardas yaga yadda sarakai da attajirai keyin
murmushin murna
don ganin suna da ninkin kudin da aka fara gasar dasu sau da yawa sai yayi
dariyar mugunta a cikin ransa yace a zuciyarsa
Uhm ! Ai sai miya ta kare sannan ake sanin maci tuwo
muje zuwa wai mahaukaci yahau kura, tsawon yan dakiku
sai falon yayi tsit ba a sami wanda ya sake taya gidan
ba har sai da sarki shardas ya sake budar baki yace, wai shin
babu yan kasuwa ne a wannan waje ? Koda jin wannan tambaya sai sarkin birnin
misra yace ya ninka wannan kudin da sarki shardas ya siyi gidan sun koma dinare
miliyn dubu shida
take aka kawo kudin aka zube a gaban jama a
daga nan ne fa kowa ya sami bakin magana sai da
sarakai da attajirai dari uku suka ninka kudin kuma aka
kawo kudaden aka zube a tsakiyar fadar ya zamana cewa
yan gasar mutum dubu uku da doriya gaba dayansu
kowa ya zuba kudinsa saura mutum daya ne jal bai sa
ba
ba wani bane fwannan mutum guda da ya rage ba
face ATTAJIRI AMSAR IBN WARHAS wanda har izuwa
wannan lokaci ba a daina kawo rakuma da dawakan
dake dauke da dukiyarsa izuwa bakin kofar wannan gida
na darul daulat ba
Kaji Manya Hm dama ance ta safe ta yara ce Ai Al amin
amma kowa an gama kawo tasa dukiyar sai ta sarki
shardas take ta bayan tasa, kafin a gama shigo da dukiyar
wacce ta ninka duk ta sauran attajiran gasar dare ya
raba
a sannan ne fa gaba dayan sarakunan da attajiran
suka tsorata ainun da al amarin Attajiri amsar
suka fara tunanin cewa Aljanu ne ke sato dukiya daga
bangarorin duniya suna kawo masa, haka kuma a sannan ne
suka tsinke da al amarin sarki shardas ma domin har a
sannan shima ba a gama shigowa da dukiyar daya tana da ba don wannan gasa
koda sarki shardas ya fahimci cewa dare ya raba kuma
kowa ya gaji ana jin yunwa da barci sai ya mike
tsaye yace to a halin yanzu dai babu wanda yafi attajiri
amsar farashi na wannan gasa, kuma tunda jama asun gaji
kuma gashi dare ya raba to za a tsayar da wannan gasa domin akai kowa masaukinsa
yaci abinci ya kwanta yayi barci sai gobe da safe
a cigaba da wannan gasa

A zagaye na biyu
Koda gama fadin hakan sai fadawan sarki shardas
suka yiwa manyan baki jagora aka kai kowa masaukinsa duk
wanda ya shiga falonsa sai dai ya iske abinci da abin sha
a shirye yana jiransa na kasaita kuma kala kala
wani kalar abincin ma mutum bai taba ganin irinsa ba
da idanunsa
Al amarin daya bai wa kowa mamaki kenan kuma ko ya
kwayar abinci daya ta dira a kasa sai dai aga ta bace bat
Don kada a sawa wajen datti kai da gani ka san cewa
wannan aiki ne na mutanen boye, bayan sarakuna da
attajirai sun ci sun sha sai kowa ya zauna tare da jama arsa
aka shiga tsegumi ana tattaunawa akan gasar inda kowacce
jama a ke baiwa shugabanta shawara akan cewa kada
ya kara zuba kudinsa a cikin wannan kasa tunda Al amarin ya shallake tunanin
mutum
Duk sarkin da ya ce zai fara zuba kudi ko attajiri
to lallai
karayar arzikinsa tazo, nan take kowanne sarki ya gama
yanke hukunci a ransa cewa sai dai ya zama dan kallo
a wannan gasa yabar wa manyan giwaye biyu dama kuma kudin
da ya zuba a yanzu ya bar su a matsayin asara da
kaddara
Al amin Ahmed Misau, Kashi gari kuwa da sassafe aka
sake haduwa a wannan babban falo na cikin wannan
gidan darul daulat
sauran jama ar gari ma yan kallo duk a wajen kofar gidan suka
kafa tantuna suka kwana don kada wannan gagarumar gasa ta wuce su
bayan dakin gasar ya gama cika ga tarin jakunkunan
dinare jibge a tsakiya sai gaba dayan sarakunan da
attajiran gasar suka sanar da alkalan gasar cewa su sun janye sun barwa sarki
shardas da attajiri amsar sun sallama cewar ba zasu iya ba
koda jin wannan batu sai sarki shardas ya bushe
da dariyar mugunta gami da farinciki saboda ganin
cewa gaba dayan wadannan makudan kudaden
da yan gasar suka zuba sun yi asararsu kuma shine
zai mallake su
a banza.
Sannan kuma har a can karkashin zuciyarsa yana ganin
cewa lallai shine zai lashe wannan gasa saboda ya yarda
da dukkan shirin da yai akan gasar da kuma tanadin da
yayi na tsawon shekaru goma sha, ba tare da wata
fargaba ba sai sarki shardas ya dubi Alkalan gasar cikin takama
da jin izza yace
na linka kudin da attajiri amsar ya siyi wannan gida
a yau
koda jin wannan batu sai falon ya rude da shewar jama a
aka shiga yiwa sarki shardas kirari ana kodashi, saboda
ana ganin cewa ya gama lashe wannan gasa domin attajiri
Amsar ba zai iya linka wannan kudin ba
nan take aka fara shigo da kudin da sarki shardas ya siyi wannan
gida adadin ninkin wadanda ke zube a wajen saboda yawan wadannan kudade sai da

aka yini ana shigo dasu sannan aka kammala
duk yawan dabbobin da suka dauko kudaden na sarki
shardas sai da kaso daya da rabin dukiyar cikin uku
ya kare
Shi kansa attajiri amsar yayi mamakin yadda akayi
sarki shardas yayi wannan kundunbala
shi kuwa sarki shardas sai ya kamu da tsananin farinciki
ya rinka washe baki saboda gani yake kamar attajiri
amsar ba zai iya sake ninka wadannan kudade ba sai
dai ya hakura da gasar
tsawon dakiku alkalan gasa suna tambayar attajiri amsar
shin zai iya ninka wadannan kudade ko kuwa ya sallama
amma sai yai shiru ya kasa cewa komai saboda jinjina
wautar sarki shardas yake yi a cikin ransa
har alkalan gasar sun mike tsaye zasu fadi jawabin cewa
gida ya zama na sarki shardas sai attajiri amsar ya tari
numfashinsu yace na sake ninka wannan kudi wanda sarki
shardas ya siyi wannan gida
Koda jin haka sai gaba dayan jama ar da ke wajan suka kame
kAm ! Inji Gwanja Haha Al amin Ahmed Misau Nake
Kamar Gumaka kowa ya wangame baki tamkar
matattun kadoji
a wajen saboda tsananin mamakin kasassabar da attajiri amsar yayi, nan take
kuwa aka fara shigowa da jakunkunan kudin har sai da aka gaji , lissafi ya kwace
musu a lokacin da zakara ya fara carah sakamakon wanzuwar
asubahi
Duk da haka a kofar wannan gida na darul daulat dawakai
da rakuman dake dauke da jakunkunan dukiyar
Attajiri Amsar sai ketaro kogin ake yi dasu
bisa dole alkalan gasar suka dakatar da gasar domin
kowa yaje ya kwanta yayi barci
nan fa jama a suka watse kowa ya tafi
yana fadin albarkacin bakinsa
wasu suka rinka cewa
' duk yadda akayi wannan dukiya ta attajiri amsar dukiya ce
ta iska kawai wato aljanu ne ke kawo kudin
Wasu kuma suka rinka cewa
' to ai shima sarki shardas din ai tasa dukiyar ta iska ce
tunda ba a gama kureshi ba
nan fa jama a suka yi ta dokin ganin

Please Login or Register in order to submit comment