Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ne wato kai bama ka damu da
lafiyarka ba kawai so kake na kaika kaje kayi kallon
gumurzun wasa
to ka sani cewa kai rago ne ba jarumi ba kuma baka iya
komai ba a yaki
Ba zaka iya tsinana abin arziki ba a cikin gagarumar
tafiyar dake gabanmu dole sai na baka horo mazaka
dauko dan jagoranmu ka rikeshi a hannunka yanzu nan
zamu tafi birnin sarki hulbasu kafin a fara wannan gasa
ga jagoran namu can a bayanka, koda gama fadin haka sai
rulaiya ta bude wata akwatu dake kusa da ita ta
debo kayan yaki ta shiga yin damara, shi kuwa yarima
hulkas sai ya waiga bayansa da sauri nan take yayi arba da
Wannan tsuntsun sihiri wanda aljani Arwasul masdul
ya bashi
kawai sai ya bude tafin hannunsa shi kuwa tsuntsun sai ya taso
a sama yana mai kada fuka fukansa ya dira akan hannunsa yana
mai kura masa idanu cikin murna, cikin kankanin lokaci rulaiya ta gama yin gagarumin
shigar yaki ta rataya tagwayen masu a gadon bayanta
bayan ta sanya wani bakin sulke da bakaken takalmi dogaye iya
kwaurinta sannan ta lullube
kanta da fuskarta da bakin mayafi ya zamana cewa
idanunta kadai ake gani a fili, koda gama wannan
kimtsawa sai ta suri yarima hulkas daga kan gadon da yake
kwance tamkar ta dauki buhun auduga ta goyashi a
bayanta suka fice daga cikin gidan gaba daya, shi kuwa
yarima hulkas sai ya damke tsuntsun sihirin a cikin
tafin hannunsa guda yana mai matukar farin ciki
bisa ganin cewa zasu tafi izuwa birnin sarki hulbasu
wajan iyayensa da yar uwarsa, da fitowarsu kofar gidan
sai yarima hulkas ya ga wani farin ingarman doki a tsaye
shi kadai yana harbin iska tamkar aikoshi akayi garesu
ba tare da jiran komai ba kuma ba tare da rulaiya ta dorawa
dokin sirdi ba sai ta kama dokin ta haye bayansa tana
goye da yarima hulkas din sannan tace dashi maza ka saki
wannan tsuntsu dake hannunka shine zai nuna mana hanyar
da zamu isa can inda kake so muje, koda jin haka
sai yarima hulkas yai sauri ya bude tafin hannunsa
nan take wannan farin tsuntsu ya tashi sama ya bi gabas
ai kuwa sai rulaiya ta zaburi dokin da gudu suka bi inda
tsuntsun ya nufa
nan fa yarima yaga dokin nasu yana yin wani irin
matsanancin gudu na ban al ajabi tamkar tashi sama
yayi domin karfin gudunsa yafi gaban kwatance
Al amin Ahmed Misau, abin da yarima hulkas ya

ayyana a ransa kawai shine wannan ba doki ba ne irin sauran dawakai kuma
tabbas yayi imani shi wannan sihirtaccen dokine
domin gani yake kamar dokin zai iya zagaye duniya
gaba dayanta a cikin rabin sa a
wannan shine abinda ya faru ga yarima hulkas bayan barci ya daukeshi a turakar
yarima barmas kuma ya farka ya tsinci kansa a wani wuri
daban mai ban Al'ajabi..
'' '' ''
AL AMARIN sarki shardas da bokansa labarusa kuwa
sai da suka kara shafe kwanaki tara cif a cikin daji suna
farautar Aljani Arwasul masadul amma duk tsawon wadannan
kwanaki basu sake haduwa da shi ba kuma ko duriyarsa basu
gani ba
Al amarin da yai matukar fusata sarki shardas kenan
ainun
bai san sa adda ya cakumi kwalar boka labarusa ba ya daka masa tsawa yace
kai labarusa ! Nifa na gaji da wannan farauta ta jaki
mai kaho ya zama dole a gareka ka gaggauta yin
bincike a cikin hallarar tsafinka ka gano mana wata
hanyar daban da zamu bi mu iya zuwa inda hular lamsara
take cikin gaggawa
Koda jin wannan batu sai boka labarusa ya fisge kwalar
rigarsa daga hannun sarki shardas ya dubeshi yace ka kwantar da hankalinka ya
shugabana idan ba don ance tsafi kogi bane da sai ince
dakai bamu da wata mafita ko hanya da za a samu wadda
zata kaimu ga mallakar hular lamsara cikin sauki da gaggawa
to amma ba a koda yaushe
kuma a kowanne irin yanayi a ko'ina komai na iya
sauyawa lokacin da ba a zata ba, ba zan ki ta taka ba
bari na duba mana na gani ko akwai wata mafitar
bayan wannan
gama fadin hakan keda wuya sai boka labarusa ya zauna a
kas dirshan cikin rairayi
sannan ya fiddo madubinsa na tsafi ya shiga karanta
wadansu dalasimai na tsafi irin wadanda sarki
shardas bai ma taba jin su ba, sai da boka labarusa ya dauki
lokaci mai tsawo yana shafa madubin tsafin nasa
idanunsa a rufe sannan ya tsaya cak, boka
labarusa yace ya dodon sarakai ka yi sani cewa a cikin
binciken nawa na gano mana wata hanya mafi sauki
wacce zata kaimu ga isa kogon da aka ajiye hular lamsara cikin
sauki da gaggawa
amma sai dai akwai wata matsala babba data bullo a cikin
wannan lamari
ka sani cewa yanzu a halin da ake ciki Aljanin da muke
farauta ruwa a jallo aljani Arwasul masadul sun hadu da
yarima hulkas harma ya bashi tsuntsun tsafi wanda zaiyi
masa jagora izuwa inda hular lamsara take
sannan kuma sai abu na biyu yarima hulkas ya hadu
da wata babbar sabuwar abokiyar gabar taka mai suna
Rulaiya
wadda take da burin daukar fansa akanka kuma a yanzu

haka ta goya yarima hulkas akan wani dokin sihirin
tsafi da Aljani arwasul masadul ya hadasu dashi
sun tafi izuwa birnin sarki hulbasu inda matarka shadila take
bisa jagorancin wannan tsuntsun sihiri da Arwasul masadul
ya bashi
Al amin Ahmed Misau, na gano cewa akwai wani
mugun shiri da ake yi maka a can birnin sarki hulbasu
don haka lallai ina tabbatar maka da cewa sarki hulbasu
yaci amanarka kuma yana son ya rabaka da matarka
shadila
a yaune za ayi gasar karshe ta jarumtaka a birnin nasa
kuma a yau dinne ya shirya kashe gaba dayan dakarunka
dake tsaron lafiyar gimbiya shadila, idan bamu je birnin ba akan lokaci zamu iske tuni
ya gama dasu
kuma yabi su yarima hulkas izuwa dauko hular lamsara
koda boka labarusa yazo dai dai nan a jawabinsa sai kan
sarki shardas ya daure ya cika da tsananin mamaki
da fargaba da kuma takaici, ya dubi boka labarusa
cikin damuwa yace akan wanne dalili sarki hulbasu
zaici amanata
alhalin yana tsananin sona?
Shin wacece wannan sabuwar abokiyar gaba tawa wacce
naji ka ambashi sunanta rulaiya wacce suke tare
da yarima hulkas? Koda jin wadannan tambayoyi
sai boka labarusa yace wannan sabuwar abokiyar gaba
taka ba wata bace face Yar attajiri Amsar wanda ka kashe shi
a cikin gidan darul daulat
bayan yaci gasar da kukai ta siyen gida a karshe ka gaje
dukiyarsa
babban burin wannan yarinya rulaiya a duniya shine
ta dauki fansar ran mahaifinta akanka kuma ta mallaki gidan darul daulat tunda
mallakin mahaifinta ne Attajiri Amsar, haka shima a yanzu
yarima hulkas bashi da wani buri wanda ya wuce ya hallaka ka
don daukar fansar abinda ka yiwa ubansa hailur da dukkan zuriarsu
ina mai sanar dakai cewa a halin yanzu tuni
hailur da matarka gimbiya shadila sun mayar da
auransu a cikin birnin sarki hulbasu Al amin Ahmed Misau
har sun tare a cikin wani kasaitaccen gida da
sarki hulbasu ya basu
koda boka labarusa yazo dai dai nan a zancensa sai
sarki shardas ya takarkare ya kwarara uban ihu
irin wanda ke tarwatsa mazaje a filin fama komai jarumtakarsu
da rashin tsoronsu
Kai inda ace akwai mace mai ciki a wajen da tuni ta
kama nakudar dole saboda firgita da za tayi na jin wannan
ihu na sarki shardas
kananun jarumai da dakarun yaki kuwa firgicewa
zasuyi su dimauta su kama sakin fitsari a wando
hehe Al amin Ahmed Misau, shi kansa boka labarusa
wannan ihu na sarki shardas ya razanashi yasa
zuciyarsa ta buga
tsuntsaye da dabbobin dake cikin dajin kuwa gaba dayansu

sai da suka kama guje guje da iface iface
suna sauya sheka da shigewa cikin ramuka
cikin matsanancin fishi sarki shardas ya dubi boka
labarusa yace maza ka hanzarta kaini birnin sarki hulbasu
kafin su yarima hulkas su isa can, cikin rawar jiki
boka labarusa yayi tsafi wani katon Aljani ya bayyana tsulum
a gabansa suka haye bayansa ya tashi dasu sama ya
luluka izuwa cikin gajimare yana mai tsala azababben gudu
tamkar tauraruwa mai wutsiya, Abinda sarki shardas bai sani ba shine shi
kansa boka labarusan bashi da tabbacin zasu iya isa
can birnin Na sarki hulbasu akan lokaci kafin komai ya gudana
+i ++ ++
ACAN birnin sarki hulbasu kuwa gari na wayewa aka tashi
da tsananin tashin hankali a gidan sarautar saboda an nemi yarima
hulkas sama da kasa an rasa
babu inda ba a duba ba acikin birnin ba har da cikin
dazuzzuka amma kamar maye yaci shirwa ga shi kuma
a can filin gasa jama a sun taru makil ana ta shewa
da ihu ana jiran isowar sarki hulbasu da su jaruma siyama
babu wanda yafi kowa tashin hankali sama da shadila
domin tunda akace yarima hulkas ya bata take ta faman
rusa kuka saboda gani take kamar ya fada hannun
sarki shardas ne
Da kyar hailu ya shawo kanta ya rarrasheta don kada ta
tarwatsa musu dukkan shirinsu na ranar inda ya tabbatar
mata da cewa yayi bincike a hallarar tsafinsa ya gano
cewa yarima hulkas na nan a raye kuma zai dawo kafin a gama
wannan gasa
nan dai ya lallabata suka shiga cikin ayarin sarki hulbasu
aka tafi filin gasa
koda jama a suka jiyo bushin Algaita da bugun
tambura alamar cewa sarki ya iso filin gasar sai filin
ya sake rudewa da shewa gami da tafi
nan fa aka bude kofar filin gasar sarki da mukarrabansa
suka shigo bisa
dawakai dakaru na take musu baya, amma abin da ya daurewa
kowa kai shine sarki hulbasu yayi gagarumar shigar yaki
tamkar yana cikin jaruman gasar
haka ma dakarunsa na musamman masu tsaron lafiyarsa
kuma a cikinsu
har da wadansu bakin dakaru wadanda suka rufe fuskokinsu
ba wasu bane wadannan
bakin dakarun da ke bayan sarki hulbasu ba face su jarumi hailur
Lokacin da dakarun sarki shardas masu tsaron lafiyar
gimbiya shadila sukaga sarki hulbasu ya fito da
wannan shiri sai suka sha jinin jikinsu suka fara
zargin cewa lallai akwai wani abu dake shirin yi musu
don haka sai suka fara yin kus kus a tsakaninsu
Al amin Ahmed Misau, Abinda basu sani ba shine
wanda duk ya rigaka kwana dole ne ya rigaka tashi
kuma maso abinka yafika dabara, jaruma siyama na daga cikin
tsakiyar dakarun sarki tayi gagarumar shigar yaki tare da

mahaifiyarta bisa doki guda,
koda yan kallo suka ga siyama sai suka rude da ihu aka
kama yi mata jinjina, ita dai kawai jaruma siyama tana
yin murmushin karfin haline amma hankalinta a wannan
rana a tashe yake saboda rashin ganin dan uwanta
yarima hulkas
Bayan sarki hulbasu da tawagarsa sun gama shigowa
filin gasar kuma sun zauna a inda aka tanadar musu sai
mai gabatarwa ya fara da kirawo sunan sadauki darkus
nan fa magoya bayan darkus suka rude da shewa gami
da tafi suka shiga yi masa kirari gami da jinjina
koda aka bude wata kofa sadauki darkus ya fito yana
tafiya kamar wani toron giwa a cikin gagarumar shigar
yaki sai filin gasar ya yi tsit tamkar mutuwa ta gifta
saboda kwarjininsu da karar sautin takun sawayensa
har sai da sadauki darkus ya iso tsakiyar filin gasar
ya tsaya mai gabatarwa ya kirawo sunan jaruma siyama sannan filin gasar ya sake
kaurewa da shewa gami da yafi, cikin nutsuwa jaruma
siyama ta fito daga cikin tawagar sarki hulbasu ta shiga
filin gasar, har sai da ta isa
Daf da sadauki darkus sannan ta ja ta tsaya a lokacin da
tazarar dake tsakaninta da sadauki darkus bata wuce taku uku ba, ba tare da bata
wani lokaci ba alkalan gasar suka bada umarnin a fara
gasa nan take, aka buga tambarin fara gumurzu
kamar hadin baki sai duk su biyun a lokaci guda
kowannansu ya juya da baya
yayi taku bakwai sannan suka tsaya suka juyo suna
masu zare takubbansu, kawai sai suka ruga da masifaffen
gudun tsiya tamkar zasu tashi sama suna masu
kwallah ihu mai firgitarwa suna jijjiga makamansu a
sararin samaniya
kafin su hadu sai kowannansu ya daka tsalle sama yakaiwa
dan uwansa mummunan sara..
Kai nima Al amin Ahmed Misau
ganin wannan saran ne yasa na tsaya a nan
nake cewa sai Allah ya kaimu gobe kafinnan
nidinne dai Al amin Ahmed Misau
inkiya Guyson Ko A square
daga Kaduna State.
TSATSUBA
Littafi Na Tara (9)
Part C.
.
Marubucin Littafin
Abdul azis Sani M/Gini
AA Misau Ke Magana
.
Labari ya Zowa Shagala Cewar:.....
.
Kafin su hadu sai kowannan su ya daka tsalle sama ya kaiwa
dan uwansa mummunan sara , duka su biyun a tare suka duro kasa lokacin suna
masu juyawa junansu baya, bisa mamaki sai aka ga

kowannansu ya tsaya cak a inda yake ba tare da
ya juyo ya cigaba da yaki ba, Al amarin da ya baiwa
kowa mamaki kenan A filin Gasar harni kaina Al amin da nake
typing aka sake yin tsit a karo na biyu
daga can kuma sai aka ga jaruma siyama da sadauki
darkus sun waigo sun fuskanci juna shi yana mai dafe saman
kirjinsa jini na zuba ita kuma tana mai dafa hakarkarinta
Na hagu jini na zuba
A sannan ne yan kallo suka gane cewa ashe kowannansu
ya samu nasarar yiwa dan uwansa mugun rauni
Cikin matukar juriya da jarumtaka sadauki darkus ya yagi
rigarsa ya daure kirjin nasa tamau don tsaida jini
itama jaruma siyama sai tayi sauri ta cire mayafin dake
zagaye a wuyanta ta daure hakarkarin nata
ba tare da jiran komai ba sai suka rugo izuwa kan juna suka
kacame da masifaffen yaki mai matukar ban tsoro da ban
al ajabi
a wannan lokaci mahaifiyar siyama na zaune daf
da hailur kuma tuni ta fara kuka bisa ganin yadda aka
yiwa yarta rauni tun a farkon fara wannan gasa
shikuwa hailur sai ya dubeta yace kwantar da hankalinki
yake matata ni na san ko wacece yata ina mai tabbatar miki
da cewa ba zata mutu ba kuma ita ce zata lashe
wannan gasa
sai da aka shafe sa auku cur ana wannan mummunan
BAKIN ARTABU tsakanin sadauki darkus da jaruma
siyama ya zamana cewa sun galabaitar da juna domin kowannan ya sami rauni kimanin guda biyu a
jikinsa jiri ne ke
dibarsu tamkar zasu sake yin RAGAS saboda karfi
yazo daya
ana cikin haka ne sadauki darkus ya shammaci jaruma
siyama
ya dankara mata wani karkarfan naushi a ciki saboda karfin
naushin sai da jaruma siyama tayi sama da baya bayanta
yaje ya gwaru da katangar filin gasar ta fado kasa da rub
da ciki a matukar galabaice tana aman jini
koda sadauki darkus yaga ya sami wannan nasara sai ya
bushe da dariyar mugunta ya
daga takobinsa sama ya ruga izuwa inda
take ya daka tsalle sama da nufin ya duro kanta ya soke gadon
bayanta
tuni a wannan lokaci kowa ya gama sallamawa cewa
jaruma siyama ta mutu
ba zato ba tsammani sai aka ga jaruma siyama ta mirgina
can gefe guda takobin sadauki darkus ta lume a cikin
kasa
kafin sadauki darkus ya zaro takobin tuni siyama ta doki
kasa da tafin hannayanta biyu kawai sai gani
akayi tayi sama kuma tayi katantanwa sannan ta doki kirjin sadauki
darkus da kafafunta biyu, saboda karfin dukan sai da
shima sadauki darkus yayi sama yaje ya gwara bayansa
a jikin katangar filin gasar ya fado kasa a kan fuskarsa

fuskar tasa ta dauje jini ya rufe masa idanu
kafin a goge jinin dake kan idanun nasa tuni siyama ta daka
sufa a sama izuwa inda takobinsa take ta zarota daga cikin
kasa ta luma masa ita a ciki
take takobin ta faso gadon bayansa sadauki darkus yayi
mutuwar tsaye ya sandare
kawai sai jaruma siyama tasa kafarta ta sake dukan kirjinsa
sannan gawar tasa ta fadi kasa
rikica kamar giwa ta fadi
nan fa filin gasar ya rude da shewa gami da tafi ana yiwa jaruma siyama
kirari bisa wannan gasa bayan ta kashe sadauki
darkus
a wannan lokaci ne kuma kwatsam sai aka ga jaruma siyama ta yanke jiki
ta fadi kasa sumammiya
A guje likitan sarki hulbasu da masu taimaka masa
suka ruga zuwa filin gasar kan jaruma siyama don bata
taimakon gaggawa
a dai dai wannan lokaci ne hailur yazo daf da kunnen
sarki hulbasu yayi masa rada yace ya shugabana gada
daya fa dakarun sarki shardas da suka rako shadila duk sun
sulale sun gudu ga dukkan alamu sun
gano shirinmu da jin wannan batu sai sarki hulbasu yayi
murmushi yace ai nima tun dazu na lura da hakan amma ko kadan ban damu ba saboda
na san cewa duk shirin da zasu yi a yanzu ba zai kai namu ba
maza kaje ka karasa shirin komai ni da dakaru zamu fara yin gaba saika taho
da sauran iyalansu
gama fadin hakan keda wuya sai aka ga wani karamin tsuntsu ya shigo filin gasar
a sama
bai dira a ko ina ba sai akan jaruma siyama wacce ke
kwance magashiyan likita na yi mata magani
tsuntsun na dira akanta sai aka ga ta bude idanunta ta
rmike tsaye zumbur tamkar babu abinda ya sameta ta kurawa bakin kofar fita
daga filin gasar idanu
A dai dai wannan lokaci ne aka jiyo sukuwar doki ya nufo
cikin filin gasar
tashin kurane ya hana ganin dokin amma kurar na lafawa
sai aka ga ashe wani farin ingarman doki ne dauke da mutum biyu
na gaban dokin yarima hulkas ne na bayansa kuwa
wani jarumi ne a cikin shigar bakake tufafi
goye da tagwayen masu
koda jaruma siyama ta hango dan uwanta yarima hulkas
bisa doki ya tunkarota sai fuskarta ta fadada da murmushi
ta ruga gareshi da gudu
Nan take shima yarima hulkas ya duro daga kan dokin ya
karasa gareta a guje suka rungume juna cikin
tsananin farin ciki yana ma tayata murnar lashe wannan gasa
a dai dai wannan lokaci ne yarima hulkas yaji an dafa
kafadarsa ta baya
yana waigawa yaga ashe sarki hulbasu ne shima ya rungumeshi cikin farin ciki
sarki hulbasu yayi masa rada a kunne yace bamu
da isashshen lokacin
Lokacin yin wani bayani ga juna yanzu domin yin

hakan zai sa mu bata lokaci yanzu mun gama shirin komai
dama kai kadai muke jira
maza ka dauko yar uwarka akan wannan doki naku duk da
cewa ku uku ne ku sameni a bayan gari mahaifinka ma zai riskemu a can
nan take aka kawowa sarki hulbasu dokinsa ya hau
dakarunsa suka take masa baya a lokacin da ya
zaburi dokin nasa da gudu ya fice daga filin gasar
Al amarin da ya daurewa yan kallo kai ke nan suka cika
da tsananin mamakin dalilin da ya hana a tsaya a bayar
da kyauta ga jarumar da ta lashe wannan jarumtakar da
akayi wato jaruma siyama
nan dai filin gasar ya waste mutane suka tafi suna
hasashe da zargin cewa lallai babu lafiya yau
Al amin Ahmed Misau,
Al amarin dakarun sarki shardas kuwa ashe gaba dayan
suka sulale daga cikin filin gasar suka ruga izuwa cikin daji
inda suka sake haduwa suka tattauna akan yadda za su sace gimbiya shadila cikin ruwan
sanyi
domin su mayar da ita gida kada fishin sarki shardas
ya hau kansu
nan take shugabansu sadauki Murzanu ya dubesu yace
na yarda da jarumtakarku da nacinku gami da iya
yakinku
saboda haka yanzu zamu koma izuwa cikin wannan birni
na askandariyya daya bayan
daya kamar yadda muka hadu a nan yanzu
kuma sai dare ya raba sannan zamu shiga har cikin gidan
sarautar sarki hulbasu mu aiwatar da nufinmu
A halin yanzu sarki hulbasu ya gaya mini cewa yanzu
zai mana rakiya tare da gimbiya shadila da dakarunsa domin mu isa gida lafiya
na nuna masa cewa na amince da hakan amma na san karya
yake yi so yake ya shirya mana wani tuggun ya cutar damu
shi yasa nace mu rarrabu mu buya a cikin birnin nasa ba
tare da ya sani ba
tuni na aika da dakarun yan leken asiri domin su kai labarin abinda
yake faruwa ga can birninmu
saboda a sanar da sarki halin da muke ciki ta hanyar
karfin sihiri a duk inda yake
koda sadauki murzanu yazo nan a zancensa sai ya sallami
gaba dayan dakarun nasa suka rarrabu a cikin
shiga ta bad da kama suka bi hanyoyi daban daban
shi dai sadauki marzanu tare da wadansu dakarun
nasa mutum dari biyu sai suka bi wata barauniyar
hanya ta bayan wani katon tsauni sai da suka yi yar doguwar
tafiya ta kusan tsawon dakika dari bakwai da arba in sai suka
yi kicibis da sadauki Ruhaisu babban yaron hailur shima dakarunsa mutum
dari biyu da goma na take masa baya, cikin tsananin kaduwa
da mamaki sai sadauki marzanu suka tsaya cak suka
dora hannayansu akan kufen takubbansu domin basu
taba zaton cewa za a tarfasu ba haka, suma su sadauki
ruhaisu sai suka dora hannayansu akan kufen takubban
aka fara kallan - kallo

Al amin Ahmed Misau, Take sadauki marzanu ya
tuno da sadauki ruhaisu sa adda suka fafata kazamin yaki
a can shekarun baya sa adda sarki shardas ya kaiwa
kabilar su hailur hari suka karkashe su har sarki shardas yaje fa hailur kasan
wannan tsauni mai tsawon gaske kuma ya dauke
matarsa shadila ya tafi da ita
koda shima ruhaisu ya gene sadauki marzanu sai zuciyarsa ta kama tafarfasa
kamar zata kone saboda tsananin kiyayyar dake taso masa
cikin tsananin fishi ya dubi sadauki marzanu yace
yakai tsohon abokin gaba kayi sani cewa jama arku da sarkinku sun dasa
mana bakin cikin da har abada ba zamu taba mantawa
dashi ba
amma na dade ina jiran wannan rana da takobina zata dau fansar
jinin kabilata akanku
na rantse da darajar shugaba hailur tsakaninmu daku dole ne wasu su zama
gawa anan kafin
mu rabu
koda jin wannan batu sai sadauki marzanu ya bushe da dariyar mugunta yace
kai samari hakika tsautsayi ne ya sa kuka yi wannan
babban ganganci na tunanin taremu da yaki
da kuma kokarin kwacewa sarki matarsa, ina mai tabbatar
maka da cewa a wannan karon sai mun karar da ku gaba dayanku
ta yadda har abada ba za a kara ganin irin
zuri arku ba a doron kasa, koda sadauki marzanu
yazo nan a zancensa sai sadauki ruhaisu ya tari
numfashinsa yana mai daka masa tsawa yace kai
wawa mara hankali da tunani shin ka manta ne cewa sarkin
naku ne ya fara kwatar matar mu ?? Yanzu ne zamu dawo
da abarmu garemu kuma mu dauki fansar jinin yan uwanmu da kuka salwantar ka
sani cewa ku azzalumai ne masu cin zarafin talakawa
sata kwace da danne hakki tsawon shekaru
to ku sani cewa shi ramin karya kurarre ne kuma gaskiya
dokin karfe ce wanda baya taba mutuwa
koda gama fadin hakan sai sadauki ruhaisu ya zare takobinsa ya yiwa
dakarunsa nuni da a afkawa abokan gaba, ai kuwa ba su tsawa jiran komai ba sai
suka zare takubbansu cikin hanzari suma su sadauki marzanu suka zare nasu
takubban aka ruguntsume da azababben yaki
nan fa wuri ya hargitse kura ta tashi karar karafa da
kururuwar mazaje ta fara cika kunnuwa
-- -- -RAGOWAR dakarun murzanu kuwa su dubu daya da dari
takwas sun sake rarrabuwa izuwa mutum dari hurhudu
wannan shine babban kuskuren da suka tafka domin
inda a cure suke gaba daya sai an kai ruwa rana kuma an kai
gwauro an kai mari kafin a ci galaba a kansu
++ ++ ++
MUTUM dari hudu da suka nufi gabashin birnin askandariyya
sai suka yi kicibis da tawagar sarki hulbasu
nan ma sai aka kacame da
Yaki amma da yake su sarki hulbasu sun ninkasu sau
goma a yawa nan suka karkashesu a cikin kankanin lokaci basu bar daya ya tsira
da rayuwarsa ba

++ ++ ++
DAKARUN da suka nufi yammacin birnin kuwa sai sukayi
kicibis da yarima hulkas jaruma siyama da jaruma rulaiya
bisa doki guda su uku, koda ganinsu sai yarima hulkas
da siyama suka zare takubbansu da nufin su afka musu amma
sai jaruma rulaiya ta dakatar dasu tana mai daga musu hannu
har izuwa wannan lokaci
rulaiya bata yarda koda jaruma siyama taga fuskarta ba
domin a rufe take cikin bakin kyalle, take jaruma
rulaiya ta duro kasa daga kan dokinta ta dubi
dakarun nasu sadauki murzanu taga basu fi su dari
hudu ba
kawai sai tayi tsaki sannan ta juya ta dubi yarima hulkas
tace ai abin kunya ne ace mu ukun nan ne zamu yaki wadannan
kananan kwari kawai ku barni dasu rabin sa'a tayi
min yawa na gama dasu
koda gama jin wannan batu sai dakarun sadauki marzanu suka
fusata ainun suka zare takubbansu suka afkawa jaruma rulaiya gaba dayansu
Wohoho Hakika mai karfi sai Allah ya isa kuma duk wanda
ya iya ya huta
ana fara wannan yaki sai jaruma siyama ta cika da tsananin mamaki bisa ganin irin
jarumtakar jaruma rulaiya da kuma tsananin zafin namanta, domin duk yawan dakarun su
dari hudu sai ya zama na
banza
saboda duk inda ta kutsa a cikinsu sai dai kaga maza na zubewa kasa
domin gididdibasu ta rinka yi sassan jikinsu
ya rinka zubewa yana faduwa kasa suna ihu kuma jini
na feshi da fantsama
Al amin Ahmed Misau
Nan fa aka rasa mutum daya daga cikin dakarun wanda
ya sami nasarar koda lakutar jikin jaruma rulaiya nan take
jaruma siyama ta raina dukkan jarumtakarta ta fara
tunanin cewa duk yadda akayi wannan hatsabibiyar bakuwar jaruma wacce yarima hulkas yazo da
ita ba
mutum bace Aljana ce
Koda gama ayyana hakan a cikin zuciyarta sai ta kasa
hakuri ta dubi yarima hulkas tace yakai dan uwana wai shin
wacece wannan bakuwar jarumar da ka zo da ita
kuma a ina ka sameta har yanzu ta fa ka bani labarin
inda ka tafi ba muka nemeka muka rasa
koda jin wannan tambaya sai jarimi hulkas yayi murmushi yace me yasa baki da hakuri
ne yake yar uwata yanzu ina nake da lokacin baki
labari a cikin wannan yanayi da muke ciki ki bari sai mun
gama da wadannan abokan gaba namu tukunna
mun isa can inda hular lamsara take in yaso bayan mun
daukota mun kashe sarki shardas sai mu zauna na
baku labari keda iyayenmu a cikin nutsuwa da kwanciyar
hankali
koda jin haka sai jaruma siyama ta bata rai tace yama za ayi
nayi ta hakurin jin wannan labari har sai mun kai ga
wannan lokaci
me ye tabbacinka ma cewa zamu tsira da rayukanmu

har mu sami nasarar dauko hular lamsara
har yarima hulkas yabudi baki zai ce da ita wani abu
sai ya ga jaruma rulaiya ta daka tsalle sama ta kama yin
wata irin katantanwa a sama
tana fille kawunan dakarun
sarki shardas
nan da nan ta karar da sauransu gaba daya
ya zamana cewa babu dayansu da ya rage a raye
saboda tsananin mamakin wannan gagarumar jarumtaka
da jaruma rulaiya tayi
yarima hulkas da siyama basu sansa adda suka wangame
bakunansu ba suna kallonta
koda jaruma rulaiya ta dago kanta ta dubesu sa adda take goge
jinin takobinta a jikin gawar abokan gabar

Please Login or Register in order to submit comment