Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yi tunanin sauyikan da ta gani a tare da shi kafin ya tafi, sai ta samu kanta cikin rudu a kan al’amuran Dr. Sulaiman, ta kasa tantance cewa yanzun yana son ta ko ba ya son ta?
“You are darling! Duk wanda ya zauna da ke na lokaci kankani, zai so ci gaba da zama da ke muddin rayuwar shi”.

Ta tuno kalaman shi ana i gobe zai tafi. Gaba daya maganganun da suka yi a ranar take tunawa filla-filla, wadanda in aka auna su a ma’auni na hankali da tunani suna nufin Dr. Sulaiman ya sauya muguwar fahimta da akidar shi a kanta.
To amma why yake kin neman ta a waya ko common gaisuwa ce su yi? Me hakan ke nufi? Babu wanda zai amsa mata tambayoyin ta sai shi. To ina za ta gan shi? Ta MAIRON HURE da ta ce,

“He is far away.....’ (Ya yi nisa).
****
















Da la’asar sakaliya suka yi shiri suka nufi Bakori dukkannin su, za su yiwa Inna week end (hutun karshen sati).
Direba Malam Habu ne ke jan su, zuwa karfe shida na yamma suna cikin garin Bakori. An yi sa’a Saude, Ruma da Anti Ramatu kannen Sulaiman duk suna gidan sun je biki sun dawo suka zarto wajen Inna.
Don haka falon Inna yau ya yi albarka, ya kauraye da hira. Ita dai Fati ba ta magana illa in anyi abin dariya ta yi murmushi, suna son yarinyar sosai saboda sanyin ranta.
Anti Ramatu da yake sarkin barkwanci ce, ta ce, “Fati sai yaushe za mu zo suna ne? Mun kosa fa Nana ta samu kani ko kanwa”.
Kunya ta kama ta, musamman da yake Inna tana wurin. Ta rufe fuska da mayafinta, haka suka yi ta tsokanar ta su lallai suna jiran baby da Yayansu ya dawo.
Wayar Inna ta yi kidi tana neman agaji, Inna ta amsa cikin nutsuwa don ta gane lambar ta Sulaiman ce.
Bayan sun gaisa ya ce, “Hirarrakin me nake ta ji haka?”
Ta ce, “Su Ruma mana, sun sanya Fati gaba duk sun hanata sukuni, gasu nan sun zo dukkannin su baka ga yadda Nana ta yi wayo ba”.
Ya lumshe ido yana sauraron Inna, amma bai ce ta ba shi Fati ba sai ‘ya’yansa. Sun dade suna ta shirmen su kamar ba kudi suke narkarwa ba, har gwalantun Nana an sanya mishi ya ji, sannan suka shiga gaisawa da kannen shi.
Ya ce, “Ina Khalid?”
Inna ta ce ya je Malumfashi ta aike shi wajen Inna Atika kanwar ta.
Cike da kewa ya yi sallama da su, ya koma ya kwanta ya ta da kai da hannayen shi a rest chair irin kujerar nan da turawa ke sakawa da zaren roba da katako.
Ya mika hannu ga zungureriyar robar coca-cola ya daga, ya tashi zaune yana daddaka. Sanyin lemon da karfin ‘gass’ din shi na soya mishi makoshi, amma bai kula ba.

Ga wanda duk ya san Dr. Sulaiman-Sulaiman a da, lokacin Hadiza, ya kuma gan shi a yanzu, to ba zai gane shi ba.
Gaba daya ya rame, ya kara yin duhu, sai dai hakan bai boye zahirin kyawun halittar sa ba. Ba abin da ya sa gaba sai abin da ya kawo shi, sai dai hakan bai sa tunanin yarinyar ya barshi ya huta ko na second daya ba, kamar yadda ya yi tsammanin nisa da ita shi ne hanya mafi sauki da zai yaki kutsowar soyayyarta.
Ashe hakan tamkar zubawa wuta fetur ne? Tunanin sa na cewa yin nisa da Fati shi ne babban makamin yaki da farmakin data kawowa rayuwarsa ashe ba shi ne maslaha ba.
Abinda bai sani ba sai bayan tahowarsa Fati ta riga ta yiwa zuciyar shi kamun kazar kuku, ta yadda dai-dai da rana daya tun tahowar sa zuciyar sa ba ta taba hutawa ko na dakika da tunanin ta ba.

Dr. Smith ya iske shi a hakan, ya dade yana magana bai san yana yi ba. Kafin dan lokaci ciwon ciki ya turnike shi, ya kama cikin ya soma juyi, sai ya fado bisa kilishin dake shimfide a farfajiyar wajen.
Da sauri Dr. Smith baturen Chicago ne na asali, ya kama shi ya soma binciken abin da ke damun shi, tare da ba shi taimakon gaggawar duk da ya dace.
Bai samu kansa ba sai bayan awanni biyu, lokacin ciwon cikin ya lafa. Ya sa ido yana kallon Dr. Smith wanda ke shan lemo a gefen shi, shi ma kallon shi yake amma bai fasa shan lemon sa ba. Ya mike zaune a hankali suna kallon-kallo.
Dr. Smith ya dauke kansa ya ce,
“A lokuta da dama bakar fata ku kan birge ni wajen rike amanar matan ku, mazanku da matan ku, da wuya daya ya ci amanar daya a cikin aure. Wannan dabi’a ce mai kyau, in ka san ba za ka iya zina ba, me ya hanaka tahowa da matar auren ka? Sai ka zauna kana tara abu har sai ya kashe ka a banza?”
Ya aje tambulan din hannunsa ya dubi Dr. Sulaiman sosai, ya ce,
“Don me baka taho da matarka ba, alhalin gidan da aka baka yalwatacce ne? Sannan dai-dai gwargwado ba za ka kasa rike ta a nan ba.
Tun wancan karon na gaya maka abinnan yana barazanar kwantar da kai, wanda in ka ci gaba da tara shi zuwa wani lokaci sai anyi maka aiki. Duk me ya yi zafi? Ka aika matar ka ta zo, mene ne wahala a ciki?”
A sanyaye ya ce da shi,
“Hadizah ta rasu!”
Dr. Smith ya ce, “Oh dear! Tun yaushe ne?”
Ya rausayar da kai ya ce, “For almost a year and a half kenan”.
Smith ya ce, “Why not ka kara yin wani auren Dr. Sulaiman?”
Ya yi shiru kamar ba zai yi magana ba, har Smith ya kara maimaitawa. Ya dago idanun shi da suka shagide ya dube shi.
“Ina da wata matar Smith”.
“To me ya sa baka taho da ita ba?”
Ya yi murmushi ya ce, “Ba zan iya bane, saboda kanwar mata ta ce, auren hadin iyaye aka yi mana”.
“Which means….. baka son ta….?”
“Ko ina son ta ba zan iya hada jiki da ita ba! Idan na yi hakan GIRMA NA ZAI FADI A IDANUN TA. Ka gane, ina tattalin mutunci na ne, duk da Hadiza da kanta hakan take so kamin ta rasu, wato ‘yar uwarta ta maye gurbin ta, amma ni ba zan iya ba!”
Smith ya ce, “Wannan shirme ne, baka da hujja kwakkwara. Idan har kana son matarka ka aje girman kan nan ka daidaita da ita, domin kana zalintar ta. Kana zalintar kanka.
Dubi yadda kake suffering (wahala) baka tunanin ita ma haka take, sai dai ta nuna kawaici? In kuma baka son ta ne ka sahile mata ka ba wa iyayen ku hakuri, ba za ta rasa mai son ta ba, kai ma ba za ka rasa samun wadda za ka so ba.......”
Ya yi saurin katse shi da cewa, “Babu saki tsakani na da Fati, har abada, babu. Ko bana son ta balle halayen ta da nagartar ta sun sayo mata soyayya mai yawa a gare ni.
Hujjar nan dai da na gaya maka ita ce, wato tana ganin girmana bana so ta raina ni, bana so GIRMA NA YA FADI a idanun ta”.
Abin ma sai ya baiwa Smith dariya, ya murmusa ya ce, “Babu zancen raini a harkar aure, ka yarda dani Dr. Sulaiman, ka daidaita da matarka don samun lafiyar ka da nutsuwar dukkanin ku, sannan da albarkatun da ke cikin aure.
Poor Fati! Na tausaya mata, aure kusan shekara biyu ba ta san albarkar da ke cikin shi ba. Wallahi ka yi a hankali, tun hakki bai kama ka ba”.

Da maganganun Dr. Smith ya kwana, yana cizawa yana busawa. Ta yaya zai doshi Fati da bukatar aure? Gaskiyar Hadiza ne he is not taking things easy (ba ya daukar abubuwa da sauki). Fati yarinya ce mai hankali da zuzzurfan sani a addini, mawuyaci ne ta raina shi don ya gyara rayuwar auren su.
Ya juya a hankali ya rungume filo, ya samu kanshi da flashing no Fati, cikin shekara daya da rabi da ya yi bai taba kiran ta ba, don ko abin ya ciyo shi ya dauko wayar zai neme ta fasawa yake yi.
Yau dai ya tabbatarwa kanshi Fati ta ci kwallon, ta yi winning a kansa, ta kayar dashi warwas, duk da tana kidahumar ta. Kenan a so mutum, soyayya ta gaskiya ba ya nufin a nuna tsiraici, ko abubuwa na jan hankali. Halin mutum shi ne jarinsa, ‘yammata sai ayi hattara!

****
T
ana kwance a gadon bonon Inna, lokacin da wasu lambobi rankacau suka shigo cikin wayar ta. Ba a jima ba sako ya shigo.

“Ni na san ni mai laifi ne, amm ina neman afuwar ki kamar kullum. Fati, zan samu?”

Ta maimaita sakon ya fi sau hamsin, babu wanda ta sani a kasar waje sai mijinta Dr. Sulaiman. Ta mike ta yi sujjada ga Allah da ya karkato mata da zuciyar abin sonta, cikin addu’o’in da take kwana da yini tana yi.
Amma ba ta ba shi amsa ba, don ta dade da sanin shi hawainiya ne canza kala yake yi. Tana tsoron kar ta kara sakin jiki da shi ya zo ya sake guje mata kamar baya, bayan ta sakankance da shi ta amshi ban hakurin sa da soyayyar sa.
Tun yana sauraron amsa har ya koma ya jingina da balcony na harabar flat din shi. Ya kira wayar har ta gaji ta tsinke ba ta daga ba.

Ya san Fati ta yi fushi! Haba!! Ai ko shi ne, shekara guda da rabi ba kwana guda da rabi ba. Sai dai ya san sanyin halinta, da wuya su yi arba ya ba ta hakuri ba ta hakura ba.
Hankalin sa ya tashi sosai,
“Wallahi ka yi a hankali tun hakki bai kama ka ba”.
Ya tuno kalaman Smith, kirista ma kenan, balle shi da yake a cikin musuluncin sa.

Inna na tuyar masa, Fati na wankin kayan Nana a jikin famfo, sanye take da riga da zani na atamfa (super) ruwan ganye. Ta makala dan karamin hijabi iya kafadun ta. Babu wani make up a fuskarta, sai tsabar kyawun halittar tsurar sa.
Nana na gefe ta yi fes cikin fararen suwaita da (mini skirt) kanta ya sha ribbons da rufaffen takalmi da socks a kafarta, tana ta wasa da Saddika ‘yar Anti Ramatu.
Khalid ya soma shigowa da wasu firda-firdan jakunkuna, can kuma sai wani kamshi da ta dade da sani na turaren ‘Chris Adams’ ya bakunci hancinta, kamin ta gama tantance abin da ke faruwa ta jiyo ‘husky’ muryar Dr. na Hadiza suna gaisawa da Malam a soro.

Ranta ya yi fari, duk wani kunci da ke cikin zuciyar ta sai ya yaye, ta tabbata ya kasa hakuri ne da yin biris din da ta yi da shi, shi ne ya taho, ba zato ba tsammani.
Ba ta fasa aikinta ba amma kar ki so ki tona zuciyar ta, da soyayya ta yiwa illa mai yawa. Ji ta yi kamar an dauke numfashinta, tana shirin faduwa a gindin famfon, ta yi sauri ta kama kan famfon, harshen ta na addu’ar neman nutsuwa daga rabbil izzati.
Karasowa ya yi gindin famfon ya yi tsuguno a gaban ta, ya leka fuskar ta yana murmushi. Ta gan shi ya yi kyau, amma ya rame, fatar shi ta kara taushin gani a ido, ya zama cool kamar ba shi ba.
Ta yiwa Allah tazbihin kasancewar ta matar Dr. Sulaiman-Sulaiman Bakori, domin ba ba kowadanne maza ne irin Sulaiman ba, ko da ba ya son ta ai ya damu da ita, tunda fushin ta ya tunkudo shi har inda take.
Ya mika hannu ya dauki Nana yana sumbatar ta, fuskarta babu fara’a ta ce mashi,
“Sannu da zuwa”.
Hararar ta ya yi,
“Bana son sannun ki, rike abin ki”.
Inna ta fito daga cikin kitchen bakinta ya kasa rufo, suka wuce dakin ta yana dauke da Nana wadda ke ta kukan ya sauke ta don ba ta san shi baMunib da Muniba suka shigo, sai suka tsaya saroro suna kallon sa, sannan suka tafi da gudu suka rungume shi suka soma zubo masa hira.
Inna ta kawo mishi waina da taushe ta ji tantakwashi da lemukan zobo da na Aya da ta ke siyarwa cikin firjin da ya saya mata.
Fati ba ta shigo ba, tana gama wankinta ta shanya ta dau mayafinta jikin igiya ta gudu makota gidan wata makociyar Inna Goggo mai gyada. Ba ta shigo gidan ba sai bayan azahar, lokacin shi da Malam suna kofar gida suna sallah da mutane. Ta zaga ta bayan su ta shiga gidan ta shige uwar dakin Inna.
Ya dawo dakin Inna suna hira, shiru-shiru bai ga Fati ba. Ya ce,
“Wai yarinyar nan Inna gudu na take yi?’
Ta ce, “Ni ina na sanar muku, ai kun fi kusa”.
Ya ce, “Tana ina ne?”
Ta nuna mishi uwar dakin ta da dan alinta, ita kuma ta fita don ta dora sanwar dare.
Tana jin shi zai shigo ta yi linkim a gadon Inna, ita a dole barci take. Ya karaso ya zauna a saitin kanta yana kallon kyakkyawar fuskarta ta dan hasken tagar Inna da ya ratso, babu wadatar haske a dakin don haka ya fiddo wayar shi yana haskata sosai.
Ta soma rikide mashi tana komawa Hadiza! Kanshi ya dinga zagayawa jiri ya soma diban shi, a lokacin da ya soma romancing din ta da fuskar Hadizahh……...
Ta yi wani irin juyi ita a dole barci take, kamin wani dan lokaci al’amura suka rikice musu, tun tana pretending har al’amarin yafi karfin kawaicinta da juriyar ta. Jin maganar Inna a falo ya sa ta daddage ta kwaci kanta, jikinta babu inda ba ya rawa saboda firgici da sabon al’amarin da ba ta taba tsintar kanta a ciki ba.
Idanun shi a galabaice ya ce, “Haba Hadizah! Don Allah Hadizahh.....!!”

Wani haushi ya kama Fati, karona farko a rayuwarta da kishin Hadiza ya darsu a ranta, wato ma da sunan Hadiza yake alakanta ta, sannan ne zai iya auratayya da ita?
Za ta fita ya cafke hannun ta, ta wani irin juyo tana hararar sa. Wai an ce aikin banza, harara a duhu. Don kuwa bai gani ba.
Shi ma ya juyo kukan Nana da maganar Inna, don haka ya yi saurin sakin hannun ta, ta fita amma shi bai fito a lokacin ba, sai da ya daidaita kansa tukunna. Sai dai fa shaddar Ghanilla baka wul duk ta yamutse.
Yana tsaye a falon Alti ta shigo suka gaisa, ya ce,
“Goggo Alti sai ku shirya tafiya zamu yi”.
Ta ce, “To ranka ya dade”.
Fati ta kwakkwabe fuska ta ce,
“Nifa Inna sai gobe zan tafi”.
Inna ta ce, “A’a, ga mijin ki ya zo tun daga wata uwa duniya ai wurin ki ya zo, yana bukatar kulawar ki, tashi ku tafi idan ya koma sai ku dawo, mu kullum muna maraba daku”.
Ba da son ranta ba ta tattara kayan su suka tafi. Wannan karon ma a baya ta zauna ita da Alti, duk yaran har Nana suna gaba.
A ranshi ya ce,
“Tunda na rasa Hadiza ai ba abin da ba zan gani ba, ga shi na zama direban Fati ina ji ina gani…..”.

Har suka isa gida babu wanda ya ce da dan uwansa uffan, don babu fuska a wurin Fati, fushi take sosai kan biris din da ya yi da ita tsayin shekara guda da doriya.
Sai shi da Munib suke ta hirar su, Alti na mamakin wadannan ma’aurata da ba ta san yaushe za su saduda su san Annabi ya faku ba. Ba ta san kuma laifin na wane ne a tsakanin su ba.
Suna zuwa gida ta dauko makullin dakin sa ta shiga ta soma gyara, duk da dama a gyare yake, domin duk bayan sati biyu take shiga ta share ta gyara ta wanke toilet.
Shi kuma da ya ajiye su fita ya yi, bai dawo ba sai karfe goma na dare. Ya yi wanka ya yi excercise ya zuba pajamas da turaren shi na kullum, amma a yau sai ya samu kansa da karawa da ‘Boss-Intense’, ya cakuda da ‘far away’. Sannan ya kara da ‘Gio-Gio Armani….’ Ango sosai. Mai ji da koshin lafiya da kuruciya, wanda Allah yayiwa duk wata ni’ima ta rayuwa.
Ya tadda Fati a dakinta, ita ma lokacin ta yi wanka tana busar da gashin ta da hand dryer, cikin wasu tausasan nighties, masu shara-shara, ya kashe dirayar ya ajiye a gefe, cikin kunnuwan ta yake rada mata.
“…..Ki yi hakuri mana Fati…..don Allah ba don ni ba”.
Ta ce, “Da aka yi me fa?”
Ya ce, “Rashin kiran ki a waya, ba haka kawai bane ina da hujjoji na”.
Cikin raunin murya ta ce,
“Kana da hujja sosai, hujjar baka damu dani ba, kana kiran kowa ban da ni, ba sai ka yi haka zan san cewa baka so na ba, lika maka ni aka yi. Tuni na kwana da sanin wannan......” Hawaye suka balle mata.
Ya juyo ta da sauri suka fuskanci juna, sanyin numfashin su na dukan fuskar kowannen su. Ya ce,
“Ni na ce da ke bana son ki?”
“Baka fada ba amma ka nuna mini, ka nunawa zuciyata. Tunda har ka iya ka yi shekara baka nemi jin lafiya ta ba, saboda ni kadai ka tsana a duniya, a kan laifin da ban sani ba”.
Ya yi murmushi sosai ya ce, “Dole sai ta bakin ki zan ji lafiyar ki? Ina ji a bakunan da ba za su yi min karya ba.
Maganar lika min ke aka yi, sai in ce MADALLAH da wadanda suka lika min ke, yaa ke ma’abociyar YAKANAH!.
Domin na hadu da alhairori da yawa a tare da auren ki. Ki yi min afuwa Fatima kamar kullum, ban san ki da kullaci ba, saboda ke na jingine komi dake gabana na zo, kada ki sagar min da gwiwa, saboda in gyara zaman mu, in gyara kurakurai na.
Na tabbata Hadiza ta tafi;

She is my past…... and you are my present.....!!!”

Haka ya ci gaba da kalallame ta da kalami masu dadi, har ya samu ya karbi abin nan mai matukar daraja daga gare ta. Ya rungume ta tsantsan yana fadi a ranshi,

“Yaya, (Sa’adatu) ta haifi ‘ya’yan baiwa”.

Albarka da addu’a, hadi da godiya mara iyaka Fati ta samu daga Dr. Saiman har ta gode Allah. A bisa yanayin daya risketa. Idan aka ce mata wani abu mai kama da MAFARKI to wannan ranar ce. Ranar da bata taba mafarkin gani cikin mafarkanta ba. It’s a dream that comes true. Bata jin akwai wani sauran buri da ya rage mata a rayuwa bayan na cikawa da imani da dorewar wannan ‘indescribable moment’ har karshen rayuwarta.
****







Kwanaki biyar din nan da yayi bai zuwa ko’ina sai barzar amarci, har Fati ta saba, duk da tana matukar cin kwakwa, tana galabaita matuka da wannan sabuwar rayuwa data samu kanta. To abin ne an tara shi fal, tsawon shekaru biyu ba kadan.

Albarka kam tana shan ta, ya soma tunanin yadda zai iya komawa ya bar Fati, saboda yadda ta zamo wani bangare na gangar jikinsa, zuciyar sa da ruhin sa gabadaya, ga shi suna tsaka da karatu balle ya yi mata visa in ya so yaran a kai su wajen Yaya.

A gobe ne zai tashi zuwa Lagos, daga nan ya bi jirgi mai zuwa Chicago. Fati tana hada mishi kaya, duk jikinta ya yi sanyi saboda mugun sabon da suka yi cikin kwanaki shidda kacal, sannan ga wata iri kewa na cin zuciyarta mai wuyar bayyanawa.

Ya fito daga wanka yana tsane kanshi da karamin tawul, jin kansa yake wani sabo, fresh, kamar yanzu aka bare shi a leda. Tunda ya samu ya sauke al’amuran da suka takurawa zuciyar shi da lafiyar shi. Inda zai iya maida Fati ciki, da watakila ya yi hakan ya sanya ta cikin ya gudu da ita.

Abin alfahari ce ga duk namijin da Allah ya baiwa, ya gode Allah da bai bi son zuciyar shi ya bijirewa iyayen shi ba. Ya tabbata da tuni yazo yana nadama. Nadama mara amfani kuwa.
Ta mika mishi wasu kayan barci ‘yan Indonesia marassa nauyi, ta ci gaba da hada sauran. Ashe hawaye take zubarwa shi bai sani ba, ya sanya kayan barcin, ya zauna a gabanta ya janye jakar kayan da ta ke hadawa, ya kamo dukkan hannuwanta biyu ya rike cikin nashi.

“Haba Fati! Ai sai ki karya min gwiwa, ku yi shiri ke da Nana ku raka ni har Lagos, sai in sanyo ku a jirgi ku dawo. In kin yi kuka ke da kike da ababen debe kewa (‘ya’ya) ni kuma in yi ya ya?
Kamar yau ne za ki ga na je na dawo, mai da hawayen nan maza-maza bana son ganin su”.
Ta ja shessheka tana kokarin mai da hawayen, daga nan kuma aka koma aikin lada, mai gigitarwa.

Karo na farko da Fati ta taka matattakalar jirgi a rayuwarta. A Lagos sun jima suna tsimayen lokacin tashin jirgi me zuwa Chicago, yana ta tausar ta da kalami masu dadi kamar ba Dr. Sulaiman ba, da cewa; ta kula da kanta, karatunta, da ‘ya’yanta. Suna daga mishi hannu ita da Nana ya bi matattakalar jirgin da sauri, ba tareda waiwaye ba, ya tabbata zai yi kewar su.

Karfe biyu na rana nasu jirgin (Bell-View) ya dawo dasu gida (Kano). Malam Habu ya debe su a Airport.

Tun tana damuwa da rashin Sulaiman har ta saba, ta sanyawa ranta salama, musamman kuma da yake duk dare suna tare a waya, ta maida hankali kan karatun ta da rainon ‘ya’yan ta.


Shekara kwana ga mai yawan rai, Dr. Sulaiman-Sulaiman Bakori, ya gama course din shi cikin nasara da shi da sauran likitoci ‘yan uwansa. Aka yi mishi sauyin aiki da karin girma zuwa babban asibitin koyarwa na Abuja, a lokacin Fati na mataki na uku a jami’a, dauke da tsohon ciki na haihuwa yau ko gobe.

Zuwa wannan lokacin Fati ta gama mallake komi na Sulaiman, da da’arta, halayen ta da addinin ta. Ita ce matar shi mafi kusanci da shi, sannan kawar shi abokiyar shawarar shi. A gefe abin so da kaunar shi.
Iyayen na matukar alfahari da wannan aure da suka hada a bayan ran marigayiya Hadiza, wadda har gobe, jibi, har gata basu daina yi mata addu’a ba. Kuma tunaninta bai taba gushewa daga zuciyar kowannensu ba.

Dr. Sulaiman yana Abuja, sai week end yake zuwa musu, sai ko in duk sun samu hutu suma su ke bin shi Abujan.

Ranar wata litinin kwana daya da tafiyar Sulaiman nakuda ta kama Fati, suka nufi asibiti ita da Alti, yaran duk suna Karkasara.
Kafin magariba ta haifi sankacecen danta mai kama da Baban shi har farcen kafa. Sai waya Dr. Surayyah ta yi mishi cewa baby ya iso. Sai ga shi a washegari kamar an jefo shi, ya tadda Fati da baby a ‘aminity’, sai dai dakin cike yake da ‘yan uwanta. Sai daga nesa yake jifanta da murmushin
‘bani da abin da zan gode miki’.
Ita ma murmushin take masa da su kadai suka san ma’anar abin su.
Ba da son ranshi ba Yaya ta wuce da ita gida inda za ta yi wanka, don Alti an aiko mata rasuwar danta a kauyen su Kukawa, don haka za ta tafi a washegari.

Dakin ta na da Yaya ta gyara mata suke wankan, Munib dan kankanba ya kasa sukuni saboda ya yi kani namiji dan uwan sa. Bini-bini zai ce a ba shi ya dauke shi, ita kuma Fati ba ta gajiya da mika mishi shi.
Kawarta Fa’iza ta zo mata barka wadda ita ma an yi auren ta tuni, suka wuni sur suna hirar bayan rabo, don Fati ta zamewa Fa’iza abin sha’awa ganin yadda ta yi kyau ta kara girma, yanda duk wanda ya dube ta duba daya zai tabbatar tana da kwanciyar hankali a gidanta.
Sabanin ita da kishiya ta sa ta gaba, ta hana ta zaman lafiya. Fati na tausar ta tare da ba ta shawarwari na gari.

Ranar suna yaro ya ci sunan Malam, wato Ja’afar. Malam ya roke su kar su boye mashi suna su kira shi da Jafarun shi.

Juma’a yamma lis, Dr. Sulaiman ya iso Kano daga Abuja, kai tsaye gidan surukan sa ya fara dosa. Bayan motar shi dankare da himilin tsaraba, Yaya ta yi mishi shimfida da sabuwar tabarma, ta sunto baby da ke bayan ta ta mika mishi.
A lokacin Fati

2 Comments On YAKANAH
avatar
rabiatu-2

1 year ago

Reply

Thanks

avatar
fatima-2-7-5

1 year ago

Reply

very nice book

Please Login or Register in order to submit comment