Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta mai jan su a jiki tare da nuna musu kauna. Yana tambayar ta ina Munib?

Daga can dakinta na 'yammatanci, wanda a yanzu ya zan mallakin Fati, sautin Abdurrahaman Sudais ke tashi a hankali cikin suratul Al-Imran, wannan ya tabbatar mata Hafiza FATIMA JA’AFAR na gida.
Ta samu gefen Yaya ta zauna, Yaya ta mike daga kwanciyar da ta yi bisa tabarma. Kai da ganin kyakkyawar fuskarta ka san ta ji dadin ganin diyar tata, ta ce,
"Da daddaren nan Hadiza? Shin ba Sulaiman ya hanaki tukin dare ba?”
Ta ce, "Wallahi Yaya, Dr. ne ya tare ni da magana, tun dazu na tashi, aikin kwana zaiyi shiyasa bamu zo tare ba, na kawo ma Fati kudin ne".
Ta ce, "Amma kin kyauta, don da ta yi ma Yayan ku maganar ta waya ya ce ba zai samu zuwa Kano wannan satin ba, ga shi baban ku kwanan nan kasuwar ta ja baya, kuma ta ce daga wannan satin za a rufe".
Ta ce, "Baba bai dawo bane?"
Yaya ta ce, "Ya dawo tun yamma, ya tafi dubiyar dan gidan Malam Abdu ne babur ya buge shi dazu".
Ta ce, "Allah ya sauwake, Fati na ciki ko".
Yaya ta ce, "Yanzu ta gama cin abinci ta shige ciki tana rehearsal, jibi za su yi musabakar jiha kuma ita za ta wakilci jihar Kano, kin san Fati ba daga nan ba".
Cikin alfahari da kanwar tata a zuciyarta, Hadiza ta tura kofar dakin cikin sallama ta danna kai, Fati ta diro daga gado ta rungume 'yar uwarta tana yi mata oyoyo.
Hadiza ta dubi Fati sama da kasa, yau sai ta ga ta zame mata cikakkiyar budurwa sosai. Ta kama baki.
"Fati girma haka?"
Fati ta yi murmushi, kumatunta duka suka lotsa gwanin sha'awa, wushiryarta ta fito siririya da ita.
Hadiza ta ce, "Wane course aka samu?"
Ta ce, "Course din da na nema ne (B.A Islamic Studies)".
Ta ce, "Masha Allah, da an je kuma sai a samo saurayi, irin wannan girma haka Fati?"
Ta ji kunya, ta boye fuskarta cikin tafukanta, ta ce,
"Ai hijabi zan ke zumbulawa irin mai hannun nan, kada a ce ana so na".
Hadiza ta ce me za ta yi ba dariya ba, duk girman Fati baka raba ta da wauta.
Ta kirgo kudi a jakarta naira dubu ishirin ta ba ta, Fati ta yi godiya ta ce,
"Allah Yaya Hadiza kwana biyu ba’a kawo su Munib ba".
Ta ce, "Makaranta ta boye su, amma da anyi hutu suna nan tafe insha-Allah". Sai sannan ne ta ga hakoran Fati. Ita shaida ce kan cewa ba abinda Fati ke so a duniya irin ‘ya’yanta Munib da Muniba.
Ta ce, "Ashe kuma musabaka za a yi Fati ba labari? To Allah Ya ba da sa'a".
Ta yi murmushi ta ce,
"Ameen".
Tana shirin fita Baban su na shigowa, ya ce,
"A'ah, manyan likitoci ne yau a gidan namu? Ina matas da abokin?"
Ta yi murmushi ta tsuguna har kasa ta gaida tsohon ta, ta ce, "Suna nan lafiya basu samu hutu bane, da sun samu za su zo".
Ya ce, "Kinga kafar nan tawa kwanan nan bana jin dadin ta, har na gaji da hadiyar magani".
Ta ce, "Wane magani ne Baba? Likita ne ya rubuta?"
Ya ce, "A'a, maganin ciwon kashi ne kawai nake saya a wajen masu talla".
Ta kama baki cikin gigicewa,

"Baba irin wadannan magungunan ba masu kyau bane, yawanci ma sun yi expiry don Allah ka daina sha. Baba meye amfanin mu nida Sulayman? Da har zaka sayawa kanka magani? Yanzu bari in rubuta maganin in bawa Fati ko Hamza su je su siyo".
Ya ce, "To na gode".

Ta baro Karkasara karfe goma dai-dai na dare, dauke da tazbihi a bakinta domin ba abu ne da ta ke so ko ta saba ba, abu ne da mijinta ke matukar ki, wato (night driving) tukin dare.
Ta biyo ta titin Court Road ta hawo titin Gandu, ta yi kwana ta hau titin B.U.K Road. Ta iso Kabuga ta dau titin sabuwar jami'ar Bayero, wanda zai sadata da Janbulo. Babu wadatar motoci a titin.
Daga gefen ta wayarta ta yi kara, sunan Sweetypie ya soma yawo a screen din. Ta yi murmushi ta mika hannun damanta ta dauka, ta rike sitiyari da hannun hagu cikin sanyin sauti ya ce,

"Yaya dai D.Z? Hope for now kina gida???"
Ta yi ajiyar zuciya cikin karyayyar murya ta ce,
"Na kusa dai, ina kan hanya.........".

Iya abin da ya ji ke nan sai wata irin kara da ta fi kama da fashewar taya, ya yi kira "Hello!.....Hello....Hadddizah!" Amma ba amsa.
Motar ta hantsila ta shige karkashin wata trailer da ke cike da buhunhunan abinci, duk da kokarin da direban ya yi wajen kauce mata hakan bai samu ba, motocin da ke gabansu da bayan su duk suka yi birki cikin salati, tsirarun mutanen da ke gefen titi suka runtumo don kawo agaji.

*******
10/15/21, 11:47 AM - Buhainat: An bawa Malam Ja'afar da Sulaiman gawar Hadiza cikin mota ambulance, zuwa nan unguwar Karkasara. Inda daruruwar jama'a suka yi jana'izar ta. Mijinta da Mahaifinta suka sanya ta a kabarin ta, suna masu yi mata addu'ar fatan alheri, yafiya, afuwa da addu'ar Allah ya yi mata masauki da aljanna, Annabi ya san da zuwan ta. Su kuma ya basu imanin jurewa.

Sulaiman ya baiwa kowa mamaki, saboda yadda ya tsaya a kan jana'izar Hadizah, babu ko digon hawaye a idanunsa. Ba su san shi kansa kukan na zuwa ne idan an san abin da ake yi ba. To bai san me yake yi ba, bai san halin da kwakwalwarshi ke ciki ba.
Ya san dai kawai Hadizar sa ta rasu, sun kaita makwancin ta na gaskiya, bayan wannan bai san komi ba, bai san kansa ba, bai san a ina yake ba.
Ya dai bude ido ya gan shi a gidan su Hadizah, dakin Mukhtar, ba ya rintsawa, yadda ya ga rana haka yake ganin dare, ya wuni yana karbar ta'aziyyar 'yan uwa da abokan arziki. Tun a ranar Inna Halima, Malam Sulaiman da sauran kannen shi suka zo Kano, da su ake karbar gaisuwa har zuwa kwana uku.
Ranar lahadi suka juya Bakori cike da juyayin halin da Sulaiman ke ciki. Malam ya ce zai dinga aiko mishi da rubutu tsayin kwana bakwai. Ya ce, "To". Wadda ta zama kalma mafi saukin fada a bakinsa, sai kuma bin kowa da ido, amma abinci da ruwa wannan kwanan shi uku bai dandana su ba.
Alti ma tana gidan ita da yara wadanda suka damu kowa da tambayar ina Momin su? Alhamis aka yi sadakar uku, Alti ta koma kauyen su tana kuka da hawayen ta, ta ce sai ranar sadakar arba'in za ta dawo.

Tambaye ni ina baiwar Allah Fatima Ja'afar Mai-Yadi?

Tana can dakinta tana kuka, inna ce kuka ina nufin kuka, mai futa daga karkashin zuciya da ruhi, tana kuma fama da jaririya, bini-bini ta hada madarar (SMA) ta dura mata, ta ba ta ruwan zam-zam. Ba ta barin ta tayi kuka, idan ta bata madarar da ruwan sai ta sa ta a baya ta goye, ta zauna ta yi ta jijjiga ta, har sai ta samu barci, ta sakko ta ta sanya ta a gadon ta, ta zauna a gabanta ta yi ta girka kuka. Idan kukan ya ishe ta sai ta bude littattafan addu'o'in ta, ta yi ta karantawa tana rokon Allah ya kai ladan makwancin rabin jikin ta Dr. Hadiza Ja'afar Mai-Yadi.

Mutuwar Hadiza ta girgiza kowa a gidan nan, haka duk wanda ya santa ya koka ya gode Allah. Kada Dr. Surayyah ta ji labari, to ina ga wanda farin cikin rayuwar sa ya ta'allaka ne kacokam a wuyan ta? Ya ke kwana da ita yake tashi da ita, yake yi mata son da ko iyayen ta sai dai su ce su suka haife ta?
Don haka Doctor Sulaiman-Sulaiman Bakori, yana cikin wani irin hali da duk masoyinsa dole ya koka masa, in har yana da imani, ya bishi da addu'ar Allah ya ba shi dangana da YAKANAH!

Tuni Mukhtar ya koma Kaduna, ranar da aka yi bakwai shi ma Malam Ja'afar ya ce ya koma bakin aikin sa. Ya bishi da "To". Kamar yadda yake bin kowa da ita.
Ya tattara ya koma gidansa, shi kadai kwal kamar maye. Sai da ya gwammace da bai dawo ba, a lokacin da ya ci karo da wheel chair din Hadiza da kayan ta dake watse a dakin barcin su, a nan ne komi ya dawo masa danye, karo na uku da ya soma kukan da ya tabbatar har abada ba zai daina ba.
Haka ya kulle kansa, ba shi da abinci sai ruwan lipton wanda yake dafawa a kettle ya dura a flask ya wuni yana sha, babu ko tunanin sa sukari.
Cikin kwanaki ashirin da mutuwar Hadiza ya zama babu kyawun gani, kasumba ta cika fuskar sa. Duk wannan gayun ya daina shi, wanka ma ba kullum yake yi ba sai ya ji alamar jikin shi na dan wari-wari, ya kashe wayoyinsa gaba daya, ya yi sallama da aikin sa, amma bai fasa kwana yana yiwa Hadiza addu'a ba.

Uwa, mahaifiya, duk ta rasa sukuni, tana can Bakori, hankalinta na Kano, ta san cikin kowanne hali Sulaiman yake yana cikin halin da yake neman matallafi. Kuma cikin halin da yake bukatar mai tausar sa, da nuna masa kauna da kulawa.
Don haka yau ta tambayi Malam Sulaiman cewa za ta taho Kano wajen Sulaiman. Ya ce hakan ya yi.
Yana zaune a falo, daga shi sai wata dukunkunanniyar jallabiya ruwan makuba, da kofin ‘tea’ a hannun shi da ‘remote’ yana kallon tashar Saudiyyah, inda suke gabatar da sallar magariba. Aka danna kararrawa wajen sau biyar kamin ya yunkura ya aje kofin a kan side table ya bude kofar.
Inna Halima ce tsaye cikin atamfa holland ta sha lullubi da koren mayafi kalar atamfar ta, har ranshi ya ji dadin ganin ta, ya ba ta hanya ta wuce cikin falon, ya tsuguna ya gaishe ta.
Ba ta amsa ba sai kallon shi take cikin al'ajabi, "Haka ka lalata kanka Sulaimanu saboda Allah? To wannan rashin tawakkalin da kake shi zai dawo da Hadiza duniya ko me?
Ka sani Hadiza ta riga ta koma ga mahaliccin ta, ba za ta taba dawowa ba, ka fuskanci rayuwar da take jiran ka a gaba, ka zamo mai YAKANAH cikin duk halin da ka tsinci kanka.
Tsakanin ka da Hadiza yanzu addu'a ce, ba wannan lalata rayuwar ba. Idan Hadiza tana raye, ba za ta so ganin ka haka ba, ka yi hakuri mai sunan Malam. Shin yaushe rabon ka da cin abinci?'
Ya sunkuyar da kai bai yi magana ba. Ta jawo ledar da ta shigo da ita ta fiddo ma'adanan abinci guda biyu, ta bude ta tura masa, tuwon shinkafa ne lafiyayye da miyar taushe ta ji nama zuku-zuku, ta ce,
"Cinye maza ka bani kwanon".
Ba musu ya dauka ya soma ci kamar Allah ya aiko shi.
Inna ta mike ta soma tattare bolar falon, ta share shi tsaf, ta shiga dakunan ta gyare ko ina, ta wanke masa toilet. Sanda ta gama ya dade da yin barci a carpet, ta zauna a gefen kansa tana tofa masa addu'a.
Yana tashi ta ba shi rubutun da ta zo da shi cikin jarka ya sha, ya mai da kai kan tuntun ya koma barci. Bai tashi ba sai la'asar, ta je bandaki ta hada mishi ruwan wanka cikin kwami, ta dawo falon ta same shi ya idar da sallar la'asar, ya mike kafa yana kallon ceiling, ta tsuguna a gabansa ta ce,
"Tashi ka je ka yi wanka, ka shirya muje mu ga mai sunan Hadiza".
Wannan karon ma bai yi musu ba, ya mike ya je ya yi wankan, ya zubo farar shadda dinkin Mohammed, ya dora hula fara sol amma bai fesa turare ba, ya fito ya tadda Inna ta idar da sallah tana lazimi. Ta yi addu'a ta shafa, ta mike suka fito harabar adana motoci, duk motocin sun yi kura futuk! Alamar an dade ba a taba su ba.
Ya sa key ya fiddo motar dai-dai inda Inna take, Malam Ilu ya karaso da sauri ya gaida Inna, ya sa ‘duster’ ya karkade motar cike da jin dadin ganin yau Ubangidansa ya fito, wanda yake kwana cikin wannan gida shi kadai ransa, sai dai yana tausaya masa, don ya san rashin matar kwarai kamar Dr. Hadiza ba karamin abu bane.
Inna na baya shi kuma yana tukin suka nufi unguwar Karkasara. A dai-dai titin asibitin AKTH kamar an ce da Inna ta juya, ta hango Fati rike da hannun Munib da Muniba cikin kayan makaranta tana tare tasi, da alama ta dauko su ne daga makaranta.
Da sauri Inna ta ce,
"Ka ga Fati can tana tare mota, yi kwana mu dauke su". Ya yi kamar bai ji ba, ya karawa motar shi gudu. Inna ta yi salati ta ce, "Baka ji ni bane? 'Ya'yan ka fa ta dauko daga makaranta!".
Sai a sannan ya juya, tuni ta tare tasi suna kokarin shiga. Ya ce, "Ai sun shiga mota ma hadu a can". Inna ta yi shiru tana mamaki, har suka iso gidan su Fati ba su shigo ba, don ba za ka hada motar gida da ta haya da ke yin tsaye-tsaye ba.
Tun daga soron gidan yake jiyo kukan Baby Nana Khadijah. Ya rintse ido tsigar jikinshi na tashi. Inna ce ta yi sallama ya biyo bayan ta. Yaya suka tarar tana ta fama da Baby Nana, wadda ke ta tsandara kuka kamar ta tsaga gidan ta ki karbar madarar da take bata.
Ta amsa musu sallama cikin sakin fuska da walwala, ta shimfida musu sabuwar tabarma, sannan ta mikawa Inna Baby Nana. Yaya ta dubi Sulaiman ganin yadda ya rame ya yi kasumba, sai ta ji hawaye sun ciko idon ta.
Ta ce,
"Me nake gani haka ni Sa'adatu? Sulaiman me ya yi zafi? Hadiza ba ta yi gaggawa ba, muma jiran namu wa'adin muke. Karbi 'yarka tunda ta zo duniya baka taba daukar ta ba, ita kuma laifin me ta yi? Ka zamo mai YAKANAH, wannan ba shi ne karshen rayuwar ka ba!!".

Inna ta mika mishi yarinyar, ya fi karafin mintuna uku kamin ya karbe ta, ya kura mata ido yana mamakin kamannin shi da ita har sun fi nashi da Munib.
Dai-dai sanda Fati da yaran suka shigo cikin sallama, tana sanye da katon hijabin ta har kasa mai hannaye, rike da lunch box din yara da jakunkunan su.
Cikin nutsuwa ta tsuguna har kasa ta gaida Inna, ba tare da ta kalli Sulaiman ba ta ce, "Ina wuni?' Bai amsa ba, ita ma ba ta tsaya sauraron ya amsa ba ta wuce ciki.
Ai Munib da Muniba suna ganin Baban su suka fada mishi suna ta tsallen murna, ya mikawa Inna Baby ya zaunar dasu duka a cinyoyin sa, suka soma ba shi labari iri-iri, duka rabi ‘AUNTY FATI’ ta yi mana kaza, ta yi mana kaza. Yana jinsu bai ce komi ba.
Malam Ja'afar ya shigo hannayen shi rike da manyan ledoji yayo cefane ciki har da madarar SMA da Nana ke sha, ya kwalawa Fati kira ta fito ya bata.
Sai a sannan ya lura da bakin takalma har da na namiji a kofar dakin Yaya, ya ce da Fati, "Waccan madarar ta kare ne?" Ta ce, "Eh, saura kadan". Ya ce, "To ki dinga gaya min kafin ta kare ba sai ta kare kaf a barta tana kuka ba".
Ta ce,
"Ai masassara take shi ne take kuka, amma dama gobe zan kaita asibiti". Ya ce, "To Allah ya sauwake, ke kuma Allah ya ba ki ladan hidimar da kike yi da 'ya'yan ki, ya sa suji kan ki kamar yadda kika ji kan su, ya kai rahama kabarin mahaifiyar su".
Ta ce,
"Amin Baba".
Shi ma Sulaiman da ke can daki yana jin su ya ce "Amin". A zuciyar shi.
Malam ya daga labulen ya ce, "A'a! Ashe Inna ce, barka da zuwa kin sha hanya, ya ya aka baro Malam?"
Ta amsa, suka ci gaba da gaisawa suna hirar 'yan jikokin su, tare da kara yiwa juna ta'aziyya. Malam Ja'afar ya dubi Sulaiman sosai ya ce,
"Ina maganar aiki ta kwana?"
Ya yi shiru kanshi a sunkuye, can kuma ya ce,
"Zan koma gobe insha Allahu".
Malam ya ji dadi, ya kara mishi da nasiha mai sanyaya zuciya.

Ba su baro gidan ba sai karfe biyar na yamma, bayan Inna da Yaya sun yanke shawarar yaran za su ci gaba da zama a nan saboda ya fi kusa da makarantar su.
Har za su tafi ya dubi Yaya fuska ba walwala ya ce,
"Duk abin da ake bukata Yaya, don Allah a gaya min".
Yaya ta yi murmushi ta ce, "Me ake bukata ban da madara? Bayan ita babu abin da zai gagara da izinin Allah".
Ya ce,
"Duk da haka ina son sanin sauran abubuwan da ake bukata, ai ragi-ragi ne".
Ta ce,
"To ka tambayi Fati".
Ba don ranshi ya so ba ya nufi kofar dakin nata. Ta goya Nanah tana jijjiga ta, wannan karon babu hijabin a jikinta, kwayar idanun su ta hadu, ya yi saurin dauke kansa don gani ya yi kamar Hadiza, hatta digon tauwadar Allah da ke kan tsinin hancin Hadiza akwai shi a tsinin hancin Fati.
Zuciyar shi ta yi wani irin mummunan bugu, don gani ya yi tana rikide mishi Hadiza sak, kasancewar bai taba ganin ta babu hijabi ba. Ya tsaya daga bakin kofar hannun shi duka biyu zube cikin aljihu. Da kyar yake magana kamar an tilasta mishi, ba tare da ya kara kallon ta ba.
"Na tambayi Yaya abubuwan da yara suke bukata, ta ce in tambaye ki?"
Kanta a kasa ta ce,
"Sai ko pampers da madara".
Ya ce,
"Bayan su ba wani abu?"
Ta ce, "Eh, amma malamar su ta ce akwai prize giving day ranar asabar kuma ana son iyayen yara su je".
Sannan ta dauko report card na yaran na wannan zangon ta mika masa.
Garin karba hannayen su suka gogi juna, sannan suka kara hada ido a lokaci daya babu wanda bai ji a jikin sa ba. Ita tsoro ta ji, shi kuma ji ya yi kamar hannun Hadiza.
Bai ce komi ba ya karba ya sanya a aljihun shi ba tare da ya duba ba, bai kuma ba ta amsar zai je ko ba zai je ba ya fita. Ya tadda Inna har ta fito suka tafi, ya bar Fati cikin tunani.

Ta zauna a gefen gadon ta, ta sauko Nanah wadda ta samu barci ta rungume cikin hannayen ta, tana tunanin me Hadiza ke nufi da ta ce ta kula da Baban Munib???

"…..Munib kulawar Uwa yake nema, Sulaiman kulawar MATA yake nema….".
Ta tuno kalaman Hadiza.
To ai ita ba matar shi ba ce, ba gidansu daya ba, ta ina za ta kula da shin kada rashin Hadiza ya tagayyara shi?
Wannan baudadden mijin nata dake yi mata kiyayya maras dalili? In har Hadiza na nufin ta auri mijinta ne wanda ba ta fito baro-baro ta fada ba, sai hannunka mai sanda da ta yi mata, ta hada ta da wani al'amari da ba zai taba yiwuwa ba.
Ba ta fata, kuma kada Allah ya tabbatar ta yi tarayya da Hadiza a kan abin da take so, ta tafi ta bari ba don ba ta so ba, sai don hukuncin Allah wanda ya fi karfin dan adam ya yi jayayya da shi. Hakika ta dauki alkawarin da ba ta san yadda za ta yi ta sauke shi ba.
****
10/15/21, 11:47 AM - Buhainat: ****
Inna ba ta koma Bakori ba sai bayan watanni biyu, lokacin laulayin Hadiza ya ragu, tana yi mata dabaru irin na manya har ta samu sauki.
A lokacin cikin ya shiga wata hudu, sannan ne laulayin ya tsaya. Sannan ciwon kanta ya jima bai tashi ba, saboda Dr. Bunza ya sauya mata magani, Fati ce ke zuwa ta karbo ba tare da sanin Sulaiman ba.
Ganin ciwon ya dade bai tashi ba sai Hadiza ta watsar da shawarar Fati ba ta gayawa Yaya ba, shi dama Sulaiman tuni ta binne shi ya kuma yarda cewa migraine take.
Cikin Hadiza wata bakwai, ya fito ya yi tororo kamar watanni tara. Haka za ka ganta fus! A cikin wheel chair tasa cikin a gaba tana kallo tana mamakin sarautar Allah, wanda ya ga damar ta haihu a cikin halin da take ciki. So da kulawa wurin Sulaiman kamar ya yi mata nakuda.
Watan Aprilu ya kama, wanda ya yi dai-dai da EDD din ta, cikin dare wani azababben ciwon kai ya tashe ta, ta soma bubbuga kanta a jikin gado, kafin a yi haka ta yi dogo suma jini ya kece kamar da bakin kwarya.
Duk wani kokari da zai iya shi ne kiran Dr. Abdullahi ko Dr. Surayyah a waya, amma hannun shi ya kasa kama wayar saboda dimaucewa. Sannan shi ya manta kansa balle ya yi tunanin wane irin taimako zai iya ba ta komai kankantarsa, a matsayin shi na cardiologist wanda kuma ke da general knowledge a kan komai.
Sai ya sunkuto ta ya nufo harabar gidan, ya shimfidar a bayan mota. Malam Ilu ya wangale mishi ‘gate’ ya fita, cikin ranshi yana cewa kai wannan yarinya kina cikin jarrabawa kala-kala, Allah ya baki lafiya.
Da taimakon innalillahi........ da yake ta ambato ya samu nutsuwar da har ya iso AKTH, aka karbe ta a bangaren ta wato dakin haihuwa, su Dr. Surayyah, Dr. Abdullahi suka rufu a kanta, ba ta san inda kanta yake ba. Suka soma ba ta duk wani taimako da ya dace don ta haihu da kanta kamin su yi bincike a kan wata matsala daban da suka hango wadda da alama dadaddiya ce.
Amma duk iya kokarin su sun tabbatar da ba za ta iya haihuwa da kanta ba, don haka suka miko mishi takardu don ya sanya hannu a shiga da ita tiyata. Da kyar yake iya sarrafa 'yan yatsun shi a lokacin da yake rattaba hannun, zuciyar shi ta riga ta bushe da tashin hankali.
Yana tsaye aka turo ta a kan gadon daukar marassa lafiya zuwa dakin tiyata, bai yi tunanin gayawa kowa ba sai da safe, kasancewar ba shi da nutsuwar yin hakan.
Da ya ga wannan ba za ta yi mishi ba, sai ya nufi ofishinsa ya murda kofar ya shiga, ya jingina da kofar ya soma tunanin wasu al'amura da ya lura Hadiza na boye mishi, da yawan waya da take yi da Dr. Bunza na mene ne? Sannan da kwayoyin maganin da ya gani a leda babu suna babu takardar su a karkashin gadon su.
Ya yi wani irin huci mai zafi,
"Akwai wata matsala wadda da alama dadaddiya ce".
Ya tuno furucin Dr. Abdullahi.
A sukwane ya bude kofar ya fita ya nufi ofishin Dr. Bunza a Neurolgy.
Dr. Bunza na rubuce-rdubuce a file suna hira da Dr. Karaye, Dr. Sulaiman ya bankada kofar ofishin ba tare da ya yi sallama ko neman izinin shigowa ba, ya kai wa Dr. Bunza shaka ya ce,

"Gara in kashe ka, kafin ka kashe ni….".
Dr. Karaye ya soma kokarin kwatar Dr. Bunza wanda ya sha shaka matuka, duk idanun sun yo waje. Ya ce,
"Ba zan cika shi ba, sai ya gaya min abin da ke damun matata, da magungunan mene ne yake dirka mata?"

Dr. Bunza ya ce,
"Ka yi hakuri Dr. Sulaiman mu yi maganar cikin nutsuwa".
Ya samu ya sake shi da kyar ya koma kujerar sa yana gyara wuyan rigarshi, yayin da Sulaiman ya yi mishi kerere a kai, idanun shi a jujjuye, shi dai kawai so yake ya ji mene ne matsalar Hadiza?
Dr. Karaye ya ce,
"Ka yi hakuri ka zauna Dr. Bakori, Dr. Bashir ba zai cuce ka ba……".
Ya juyar da juyayyun idanunsa a kan Karaye,
"Akwai wata cuta wadda ta wuce wadda ya yi min? Matata na dauke da cuta shekara guda amma bai taba gaya min ba? Ya biye mata suke yi min rainin hankali, na yi kama da wanda bai je makaranta bane Dr. Karaye?"
Dr. Bunza ya ce,
"Ba haka bane Dr. Bakori, ina bisa aikina ne, akwai sirri tsakanin likita da petient din sa, wannan shi ne hujja ta. Sannan Dr. Hadiza na da tata hujjar, ta boye maka cewa tana da (brain cancer) don samar maka da kwanciyar hankali, ta ce idan ka ji babu kai babu sauran kwanciyar hankali, kuma nima na yarda you are not taking things easy (ba ka daukan abubuwa da sauki). Ka bini a hankali in maka bayani".

Ya kunna computer inda (record) din Hadiza yake

2 Comments On YAKANAH
avatar
rabiatu-2

1 year ago

Reply

Thanks

avatar
fatima-2-7-5

1 year ago

Reply

very nice book

Please Login or Register in order to submit comment