Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yaran bayan sati daya za a kawo su.
Ruma ta ce,
"Yaya baki yiwa Fati nasiha ba".
Ta yi murmushi ta ce,
"Duk nasihar da zan yi mata na yi mata jiya, Allah ya sa ta je a sa'a".

A dakin Malam Ja'afar kowa ya fita ya bar su, ganin irin kukan da Fati ke yi kamar ana zare mata rai sai zuciyar shi ta motsa. Ya ce,.

"Fadimatul-Zahra'u, ki daina kuka, ban aurar da ke ba sai a hannu na gari, hannun dana san cewa ba zan taba yin dana sani ba".

Har aka iso gidan, wanda ba bakonta ba ne tana tauna maganar Babanta, me ya sa Yaya da Baba suke son Dr. Sulaiman har haka? Me ya sa kowa ya budi baki kyakkyawan kalami yake yi a kanshi? Me ya sa ita ba ta ganin kirkin nashi da nagartar tashi? Kenan ita kadai yake yiwa rashin kirki, to laifin me ta yi masa?
Babu wanda zai ba ta amsar sai Sulaiman din kansa, wanda ta tabbatar har abada ba za ta ji amsar ba in har sai shi din ne zai amsa mata.

Inna ta tarbe su ta rungume ta, ta kama hannun ta har dakin da a yanzu ya zan mallakin ta, ta aje ta a bakin katifa. Fa'iza da Karima kawayenta na gefen ta, wannan ya shigo wannan ya fita, amma ita tunanin ta ya tafi ga Baby Nanah wadda ta baro a wajen Yaya, ta shaku da yarinyar sosai ta yadda har take mantawa cewa ba ita ta haife ta ba, ta alkawartawa ranta za ta roki Inna ta karbo mata ita gobe ba za ta iya yin kwanaki bakwai ba tare da ita ba.
Zuwa karfe goma na dare gidan ya yi shiru, masu tafiya sun tafi, masu gajiya sun kwanta barci. Su Fa'izah duk sun tafi, Inna ta shigo dakin rike da kulolin abinci guda biyu, ta ce,
"Kin yi barci ne Fati?'
Ta mike zaune rike da carbi a hannun ta, ta ce, "A'ah".
"To tashi ga abinci ki ci, tun dazu na so in kawo miki na san ba za ki iya ci cikin mutane ba".
Ta mike zaune ta karba, jellop din cous-cous ne wanda ya ji kayan lambu a filas din farko, sai farfesun kayan ciki da ya ji kayan kamshin gargajiya a daya filas din. Inna da kanta ta zuba mata ta soma ci.
Inna na kallon ta cikin tausayi, ganin yadda take cin abincin hannu baka hannu kwarya. Allah kadai ya san tun yaushe rabon ta da abinci, mai yiwuwa tunda aka yi mata zancen aure da mijin Yayarta.
Ta gama ci ta kora da gwangwanin fanta, ta koma ta kishingida Inna ta yi mata sai da safe ta kwashe kulolin da plate din da gwangwanin fantar ta fita.

Karfe daya na dare Dr. Sulaiman ya shigo gidan, ya tabbatar zuwa yanzu dai kowa ya kwanta balle a dame shi. Yana shiga dakinsa ya danno kofa ya murza key, hoton Hadiza cikin dan kankanin ‘frame’ da ke kan ‘side drower’ na gefen gadon shi ya yi mishi sallama, tana murmushin ta ni'imtacce cikin farar shirt din calvin-klien wato C.K.
Ya zare falmaran din suit din shi ya zare tie ya fada a kan gadon, ba tareda ya cire takalmi da safar kafarshi ba, ya fizgo hoton ya rungume a kirjin shi, ya yi magana cikin muryar kuka,
"Why do you leave me Hadizahh….???
Mai ya sa kika boye min cewa kina da brain cancer? Likitancin ki bai gaya miki cewa babu ciwon da ba shi da magani ba? Hatta kanjamau ana nan ana kokarin nemo maganin ta. Mai ya sa baki jira ni mun tafi tare ba? You left me incomplete, shattered….!"
Ya mirgina ya kara rungume hoton ya feso wani irin huci mai zafi.
“Da gaske Allah ba ya barin wani don wani, na tabbata da ba zai dauke ki ya barni ba. Ya za ai a ce na zama mijin kanwar ki? Wannan cin fuska da cin amanar soyayya har ina? Ba za a yi ta dani ba! I am for Hadizah only….!! Zan jira wa'adina Hadiza in iske ki acan mu ci gaba da rayuwar mu a inda babu mutuwa…. balle ta sake raba mu……".


Ya lumshe ido, hawaye suka mirgino, ya budesu a hankali ya kai ‘frame’ din ga siraran lebban sa, ya yi masa sumba mai tsayi da zurfi, kafin ya yi masa murmushi ya ce,

"I love you HADIZAH….Cikin kowanne hali INA SONKI HADDIZAHH!!!"
****

Masoyan Hadizar na da yawa, domin ita ma a can, Fadima, a dai-dai wannan lokacin, goshinta na gaban mahalicci, cewa take.
"Ya Allah! Ka yi rahma ga baiwar ka Hadiza, ka yalwata kabarinta da haske da kamshi, ka yaye mata duhun kabari, ka shayar da ita ruwan Alkhausara, ka bani juriyar cika alkawarin ta duk da na san ba abu ne mai sauki ba……….".

Kafin gari ya yi haske tuni Dr. Sulaiman ya fice, sai karar motar shi Inna da ke lazimi ta jiyo. Ranta ya baci sosai, ta dauki waya ta yi kiran sa, anyi sa'a wayar na bude ba shi kuma da hujjar kin amsa kiran Inna.
Yana amsawa ta ce,
"Dabbobin da ke cikin gidanka za su koma makyankyasar su, sai in ce Allah ya hada mu da alheri".
Kafin ya yi magana ta kashe. Ya juya wayar a hannun sa, "Dabbobi? Dabbobi? Su waye dabbobin? Eh, dole ta kira kanta dabba a gidansa, tunda har za ka iya fita tana cikin gidan ba ka gaishe ta ba".
Jikinsa ya yi sanyi, a hankali ya yi round ya juyo. Lokacin da ya iso gidan har sun faka kayan su suna sawa a motar Jibril mijin Ruma, tana kokarin fitowa yana kokarin shigowa suka yi karo, karaf, ya yi saurin ja da baya.
Ya ce, "Inna ki yi hakuri in je in yi signing yanzu sai in dawo in kai ku".
Ta harare shi ta ce,
"Ai ba kai kadai ke da mota ba, tunda ka iya ka kwana cikin gidan ka wayi gari ka fice ba tare da ka binciki halin da muke ciki ba ai dabbobi ka dauke mu. Ni matsa ka bani hanya bana son motar taka".
Ya soma magiya,
"Ki yi hakuri Inna, mu koma ciki mu yi magana, wallahi dama ban yi niyyar dadewa ba zan je ne in dawo kuma ban san yau za ku koma ba".
Ta balla masa harara sai kuma ya ba ta tausayi. Wanda ya san Dr. Sulaiman a baya, ya kuma ganshi a yanzu, zai yi wuya ya shaida shi in ba ya yi masa farin sani ba. Duk da ya aske kasumbar da ta cika mishi fuska, hakan bai voye muguwar ramar da ya yi ba.
Ita kanta muryar shi ta canza ta zama mara amo, kamar ta mai fama da mura. Dara-daran idanunsa sun zurma ciki. Kallo daya za ka yi mishi ka tabbatar da cewa har yanzu mutuwar matar shi ba ta gama dukan shi ba.
Ta juya suka koma ciki, suka zauna a falo. Ta ce, "Ka kara YAKANAH Sulaiman, a kan wadda kake da ita. Ka rike Fatima da amana, domin amanar ce a hannun ka. Jiya baka je ka ga ya take ba, ya ta zo, meye matsalar ta balle lafiyar ta. Sannan yanzu ma ka fita ba tare da ka neme ta ba”.
Ya yi shiru kansa a kasa, a gaskiya! An takura rayuwar sa, an kakaba masa abin da bai san ya zai yi da shi ba. Ba ya jin ko sautin shi zai iya bai ma Fati. Amma Inna gaskiya ta fadi, dole ya dinga bincikar lafiyar ta.
A sanyaye ya ce, "Ki yi hakuri Inna, insha Allah, zan kula".
Ta ce,
"To Allah ya yi maka albarka".
Ya ji dadi har kokon ransa, ya ce,
"Za ku jiranin in je in dawo in kai ku?"
Ta ce, "A'a, ka maida hankali kan aikin ka. Ga Jibril zai kai mu, sai mun yi waya, Allah ya hada mu da alheri".
Ya zaro kudi cikin aljihun sa ba tare da ya kirga ba ya mika mata, "Sai a ba Jibril ya sha mai". Ya sake zaro wasu, "Wannan kuma sai a rabawa su Ruma, karshen watan nan zan zo insha Allah in abin da nake jira ya fito".
Ta ce, "Meye abin da kake jira?"

Ya yi murmushi kadan,
"Sai na zo din dai Inna".

Bayan fitar sa ta shiga dakin Fati, ta tarar da ita ta yi wanka ta sauya kaya, cikin doguwar riga kirar Omman ruwan makuba, ta makala dan kankanin hijabi fari iya wuyanta, fuskarta sumul babu ko tabon pimples ko daya, sannan babu wani make-up amma ta yi kyau sosai.
Akwai wata boyayyar kauna da Inna Halima ke yiwa Fati, wadda ta dasu a ranta tun daga lokacin da ta fara zama da ita daki daya, ta fahimce ta, ta fahimci akidar ta.
A wancan lokacin ta ce a ranta, ina ma ina da wani babban da in aura mishi Fati ko ya samu tabarrakin da ke tattare da ita, Khalid bai isa aure ba. To ashe dukkan su rabon Sulaiman ne, haka Allah ya tsara.
Ta zamo daga gadon ta russuna tana gai da Inna, ta kama hannun ta suka zauna a gefen gadon tare, ta ce,
"Mun kwana lafiya Fatima?" Ta ce, "Lafiya kalau Inna, ya ya gajiyar ku?" Ta ce, "Gajiya ta bi lafiya Fatima, mu za mu wuce Bakori, sai kuma Allah ya hada mu cikin alherin sa".
Idanun ta suka yi rau-rau kamar za ta yi kuka, Inna ta ce, "A'a, kada mu yi haka da ke, mun yi waya da Alti tana nan dawowa karshen wannan satin, ba za ki zauna cikin kadaici ba. Sannan ungo wannan".
10/15/21, 11:47 AM - Buhainat: Ta mika mata kwalin karamar waya kirar Nokia, ta ce "A hade take da caji da komai har layi an sanya, jiya na aika Jibril mijin Ruma ya siyo, duk wata matsalar ki kada ki nemi kowa ki neme ni. Sannan kada ki ji shayin gaya min komai wai don ina uwar Sulaiman, dukkanin ku 'ya’yana ne, baki da wata damuwa?"
Cikin nishin kukan da ke son ya balle ta ce,
"Dama........dama ina so a karbo min Nana ne".
Inna ta yi shiru kamar tana tunanin wani abu, can kuma ta ce, "Ki dai yi hakuri zuwa rana ‘i ta yau din, ko kin manta ke AMARYA ce?
Ki huta kwana bakwai, ki kula da mijin ki. Rana ita yau za a kawo miki 'ya'yan ki dukkan su. Allah ya yi muku albarka kan biyayyar da ku kai mana, kuma ya sa 'ya'yan ku su yi muku fiye da ita.
Kada ki yi wasa da GIRKI Fati, domin shi ne mafi saukin hanyar isa ga zuciyar miji. Na barku lafiya".

"AMARYA! AMARYA!!"
Fati ta maimaita kalmar Inna. Bayan fitar Innar. Sannan ta koma ta kwanta rub da ciki a kan katifar ta “I'm not a bride Inna (ni ba amarya ba ce Inna).
Ita amarya cikin farin ciki take, cikin sa take kwana, cikin sa take wayar gari, cike da soyayyar mijinta. Amma ni yaya na kwana?

Kwana na yi cikin suyar zuciya da tunanin 'yar uwata abar sona, wadda take min soyayyar da babu mai yi min ita a duniya, in ka cire iyayena.
Bana kin sa shi yake kina, a kan laifin da ban sani ba. Ban san so ba balle in ce bana son sa. Amma ni meye laifina a kan auren da nima ba so nake ba?

"Kulawar MATA yake nema…..".

Ta tuno furucin karshe na Hadizah. To ga ni na zama matar tasa Yaya Hadiza, wace irin kulawa kike nufi in ba shi? He is old enough ya kula da kansa, wanka zan mishi ko pampers zan cire masa? Goyon shi zan yi ko feader zan ba shi? Ban san wacce irin kulawa kike nufi ba.
Ta kai bayan hannu ta shafe hawayen ta, banda GIRKI kamar yadda Inna ta ce, in za a kashe ta ba ta san wata extra kulawa ta daban da mace ke yiwa miji ba. Sannan ba ta iya shisshigi da cusa kai a inda ba za ta yi kwarjini ba.
Bayan tafiyar su Inna gidan sai ya yi shiru, babu sauran wani mahaluki in ka dauke Malam Ilu dake can bakin ‘gate’ yana gadi, an bar ta daga ita sai halinta. Ji ta yi kamar an kawo ta kabarin ta, ta yi kuka ta yi kuka har ta gode Allah. A karshe ta tattara komi ta mikawa Allah, ta jawo kular da Inna ta ajiye mata ta debi abinci tana ci.
Ai ba ta tashi jin tsoro ba, sai da karfe tara na dare ya yi, Fati ba ta taba kwana a gidan da babu mutane ba, ta tabbatar ita kadai za ta kwana a wannan katon gida, don tuni ta san Dr. Sulaiman ya saba aikin kwana.
Jikinta ya soma mazari kamar ana kada mata gangi, ta daddage ta takure a can karshen katifa ta kudundune cikin bargo tana dakacen ina ma ita ce ta tafi, Hadiza ta zauna, ko babu komai Hadiza ta fita bukatar rayuwar.
Na farko tana aikin lada, ta hanyar ceton rayuwar mata ‘yan uwanta. Na biyu tana da 'ya'ya tana kula da tarbiyyar su da rayuwar su, na uku tana da mijin da ke son ta suke rayuwa cikin so da kaunar juna.
To amma ita fa? Babu sidi babu sadada. Ba ta kai karshen tunanin ta ba ta ji karar fashewar tangaran a kitchen, wannan ya tabbatar mata ba ita kadai ce a gidan ba, to wane ne? Ta san dai ba maigidan bane, don shi in ya dawo karfe shida ba ya kara fita sai takwas, ba kuma zai dawo ba sai past ten sai dai in yana da aikin kwana.
Ta ji dan tsoron ya ragu, ko ba komi tana da confidence na cewa akwai mutum cikin gidan ba ita kadai ba ce. Ta mike ta fito ta nufi kitchen, wanda ba ta zata ba shi din ta gani, ya tara hannu cikin famfon sink yana wanke jinin da ke bulbula daga hannun sa, ga kuma kwai yana ta kauri a kan cooker.
Ta karasa da sauri ta sauke, ta kashe gass din. Ta dauki tsintsiyar laushi ta soma tattare fasashshen tangaran din, kafin ta farga ya fice a kitchen din yana ta disar da jini a kan tiles.
A take ta hada wani kwan ta soya masa, ta juye a farantin tangaran ta debi ‘cake’ samosa da spring roll cikin firji ta dumama a microwave , ta tafasa ruwa nan da nan ta juye a karamin tea flask ta kwasa ta yo falo don ta bashi.
Ya tada kai da karamin filo yana kwance a tsakiyar kilishi, sanye da fararen riga da wando na barci marasa nauyi, har yanzu dan yatsansa bulbular da jinni yake, amma bai damu ba, kamar ba jikinsa ba, ta zo gaban shi ta russuna ta aje mishi, sannan ta sanyaya murya ta ce,
"I'm sorry!".
Bai kalle ta ba, haka bai amsa ba kamar bai san Allah ya yi ruwan tsirar ta a gun ba. Kai bangaren data ke ma bai kalla ba. Ta mike za ta koma daki cike da tunanin hannun shi da ke ta kwararar da jini, amma matsayin shi na likita bai yi wani kokari ba ko yaya ne don dakatar da gudun jinin ba.
Ta san da Hadiza tana nan Allah kadai ya san irin gigicewar da za ta yi, sannan za ta sa mishi magani ne ta daure, sannan ta yi ta jinyar ciwon har sai ya warke.
Hakan ya taba faruwa da ya sharce babban dan yatsan sa garin ferar tuffaha, irin wannan kulawar kenan Hadiza ke nufi ta yiwa mijinta? Da kamar wuya wai gurguwa da auren nesa.
Aka ce wargi ma wuri shika samu; ko fuska babu, ba ta son tuno yadda ya yi da fuska kaman an aiko mishi da manzon mutuwa lokacin da ta shiga kitchen din.
Ba ta kai ga shiga daki ba ya yi mata wata irin tsawa wadda ta gigita ta, ya ce,
"Ke!"
Ta juyo da sauri. Ya ce,
"Zo ki batar min da wannan shirgin naki a nan, na ce da ke ina bukatar taimako ne?"
Jiki na rawa ta dawo ta russuna za ta dauke, ya kama fatar kunnuwan ta da riko mai karfi, ta sa kuka don azaba. Ya ce,
"Daga yau sai yau kada ki kara shiga shirgina, ko me za ki ji na yi kada ki zo inda nake, tunda ban neme ki ba. Na yi kama da saurayin ki ne? Be careful ni Yayanki ne, mijin Yayarki, Hadiza. Idan kin manta in tuna miki. Tun da kin yarda a kawo ki ki yi zaman 'ya'ya ki lalata kuruciyar ki a banza, to ki yi ta yi. Ranar da kika gaji, ki gaya min in maida ke gida, kina ji na?'
Cikin kuka ta daga mishi kai, ya saki kunnen ta ya ce, "To kwashe su a nan tun ban yi ball dasu ba, kema in babballaki". (Yana nuna wa da hannayen shi irin yadda zai babballa ta din).
Jikinta na kyarma ta kwashe ta yi kitchen dasu, ya ja tsaki "Tsuu…." A ranshi ya ce,
"Kai! Inna da Malam sun takaice ni wallahi, me zan diba a jikin wannan fingi-fingin?" Ya yi ball da filon da yake kwance ya mike ya nufi (exercise area) din sa.

Fati bata daddara ba, washegari tunda ta tashi da asuba ba ta koma ba, kitchen ta shiga ta shirya kalacin funkason alkama da miyar agushi. Wanda ta kwaba tun daren jiya. Ta kara da Quaker oat da plantain soyayya ta aza a ‘master dining’ din shi kamar yadda ta ga Hadiza na yi.
Da gudu ta koma daki ta kulle, yana fitowa zai fita rike da ‘brief case’ ya yi tozali da sabbin warmers, sai kamshi ke tashi bisa dining din shi. Da gaske yunwa ta gallabe shi, hanjin cikinsa har rawa yake. Sai dai yana ganin idan ya ci ya zama sakarai tunda ga abin da ya ce da ita jiya, kuma raini zai gitta.
Don haka ya hadiye azababbiyar yunwar shi ya fice. yana shiga AKTH ya nufi gun cin abincin manyan likitoci na asibitin, can ya yi kalacin sa. Sai dai a bakinsa babu dandano, don Hadiza ta riga ta sangarta shi da cimar Fati mai dadin da ba ya misaltuwa, ya kuma fi na Goggo Alti wadda a da yake ganin babu wadda ta kaita iya sarrafa abinci, musamman na Hausawa wanda ya fi kama mishi ciki kasancewar shi ma'abocin tara yunwa kafin ya yi quenching din ta.

Da ta tabbatar ya fita, ta fito ta bude ma’adanan abincin, babu abin da aka taba. Bata ji haushi ba, ta tattara ta mikawa Malam Ilu bayan ta dibi iya wanda take ganin za ta iya ci, ta koma daki ta yi wanka sannan ta zauna cin abinci.
Tana kammalawa wayarta da ta sa a caji ta yi kara, ta amsa cikin kamilalliyar muryar ta, Inna ce. Suka gaisa, sannan ta mikawa Malam Sulaiman shima suka gaisa.
Ya yi mata addu’a sosai, ya kara da cewa, ta jure duk wani rashin jin dadi da za ta fuskanta daga mai sunan shi, nature (halittar shi) kenan, fara nuna kiyayya ga abu kamin ya so shi. Da yardar Allah watarana za ta tashi da riba.
Ranta ya yi fari, zuciyarta ta yi haske, a kalla ta san ta samu surukai na gari da ke son ta. Ta kara jin karfin gwiwar son ci gaba da kyautatawa Sulaiman, ba don ya yabe ta ko ya so ta ba. Ita ma ba son na shi take yi ba, sai dai ba za ta iya yin watsi da al’amarin shi kamar yadda ya bukata ba, saboda alkawarin da ta daukar wa Hadiza, ta tabbata sakayyar ta na wurin Allah.
Don haka ta mike ta nufi dakin shi don ganin ko akwai gyararrakin da za ta iya, cikin sa’a rufe kofar kawai ya yi amma bai sa key ba.
Ta murda ta shiga cikin sallama duk da babu kowa, wannan tarbiyya ce mai kyau sabida mala’ikun rahma. Dakin babu kintsi, ko ina takardu baja-baja, gado a yamutse, kayan wanki a toilet fal cikin kwando.
A jikin bed side ta yi tozali da ‘yar uwarta tana murmushi. Ta karasa ta dauki ‘frame’ din hoton tana shafawa a hankali tana murmushi itama, hawaye fal idanun ta.
Ta maida shi mazaunin shi ta nade hannun riga ta soma gyara komai neatly, ta cire bed sheet ta canza wani. Ta kunna A.C don dakin ya yi sanyi.
Ta koma toilet ta hau wankin da ya dauke ta har zuwa azahar, ta fito da kayan inda suke shanya ta shanya, ta wanke bandakin sosai da parazone, sai daukar ido yake, ta jawo kofofin ta fito ta soma aikin falo wanda babu datti sosai don su Inna sun tsaftace ko ina kamin su tafi.
Zuwa la’asar kayan sun bushe, sai tashin kamshin Dr. Sulaiman suke kamar yanzu aka fesa turaren gidan (Chris Adams) ba’a sanya su a omo ba.
Ta yi shimfida a falo ta soma goge su da dutsen guga, ta kammala cikin dan lokaci, ta je ta jera mishi a wardrove ta kunna burner ta turare dakin da bandakin da touch me, sannan ta fita ta koma dakinta ta yi wanka ta kwanta tana hutawa.
Bai dawo gidan ba sai goma na dare, nan ya soma shakar daddadan kamshin amarcin da gidan ke yi, ya kara cin karo da sakon Fati a kan dining cikin wasu flasks din asu zabar kyau ba na dazu ba.
“Wato yarinyar nan ba ta jin magana”.
Ya fadi a zuci.
Ya danna kai dakin shi, kamar ya sume don daddadan kamshin da dakin ke yi, da wata ni’ima ta musamman dake fita, wanda ya gauraye da rabar split mai sanyaya zuciya da kasalantar da gangar jiki.
Ya bude wardrove don ya sauya kaya, nan ma ya cimma sakon Fatima Ja’afar Mai-Yadi. Ya girgiza kai ya ce,
“Na san maganin ki tunda baki da zuciya”.
Washegari ma Fati ta kara yin kalacin kunun tsamiya dan leda, da poncake ta aza dining. Yau ma da ya gani wucewa yayi yana girgiza kai, cikin ransa yake fadin.
“Lafiya ce ta yi miki yawa kike losing energy din ki a banza!”.
‘Surely’ yana bukatar abincin, amma girman sa da yake tattali a idanun ta ya hana shi. In ya ci girkin ta ashe tana da amfani cikin gidan kenan, shi kuma so yake ya nuna mata da ita da babu duk daya. Babu wani amfani da mace za ta yi masa tunda ya rasa wadda yake so, ya jure rashin Hadiza ma balle rashin cin abincin da yake so?
Haka suke ta gangarawa har tsayin sati guda. Ranar lahadi yana gida, Mukhtar ya yi sallama ta hanyar danna kararrawa.
Ya tashi daga kan computer ya je ya bude, Mukhtar Ja’afar ne rungume da Baby Nanah, Munib da Muniba na biye da shi, suka rangada da gudu suka rungume mahaifin su.
Shi ma ya rungume su yana bin kowannen su da sumba, idon shi a lumshe. Suka karasa cikin falon shi da Mukhtar, Mukhtar ya mika mishi Nana, ya karbe ta ya rungume yana sunsunar ta. Sannan ya tsaya yana kallon ta, kamannin shi da ita har sun yi yawa.
Suka yi musabiha da Mukhtar, yake gaya mishi Inna ce ta yi waya ta ce a kawo su wajen babar su. “Ina Fatin ne? Ko barci take?”
Cikin dauriya ya ce, “Bari in duba”.
Ta fito daga wanka ke nan tana rufe kofar bandaki, karamin towell ne ta daura daga kirji zuwa cinyoyin ta, kanta cikin hular wanka, tana jona hand dryer don busar da gashin kanta da ya jike.
Ya turo kofar ya shigo, idanun shi suka yi kyakkyawan gani, shi kadai ya san abin da ya tsirga daga yatsar kafa zuwa zuciya da kwakwalwar sa, ashe model yarinya ce a cikin HIJABI?
Kallon second biyu ya yi mata ya dauke kansa, sannan ya juya da sauri cikin kakkausar murya ya ce,
“Mukhtar ke kiran ki”.
Ta zubo doguwar rigar shadda ‘dark-bluesenegalese’ ta dora da matsakaicin hijabi, ta tadda su a falon.
Ai kuwa su Munib suka yo tsalle suka yo kanta, har suna kokarin kada ita. Itama ta rungume su, suka soma jero mata tambayoyi.
“Anti Fati, Mummy ba ta dawo ba har yanzu? Ina kika tafi muka daina ganin ki? Nana tana ta kuka idan bakya nan, don Allah kar ki kara tafiya ki barmu…..”.
Ta ce, “Ba zan kara ba”. Ta kamo hannun Muniba, “Ba inda zan je muna tare kun

2 Comments On YAKANAH
avatar
rabiatu-2

1 year ago

Reply

Thanks

avatar
fatima-2-7-5

1 year ago

Reply

very nice book

Please Login or Register in order to submit comment