Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

idanun su cikin na juna, wadannan kwayan idon na Sulaiman suka birkita ta, kamar yadda suke birkita zuciyar duk wata lafiyayyar macen da ta san cewa akwai tsokar zuciya a tare da ita. Amma ga shi Sulaiman, gani yai ta rikide mishi ta koma Dr. Hadizah……

“Wannan yankar sai an yi dinki”. Ya fadawa Alti.
Cikin sanyin murya ta ce, “Ai shi ya sa na ce muje asibitin”.
Ya ce, “Ba damuwa bari in dinke mata”.
Ya fara da yi mata allurar ‘anaesthesia’, sannan ya fara dinkewa. Idanunta a rufe ba ta bude ba har ya gama.
Bayan ya gama ci gaba ya yi da rike hannun bai saki ba, ita kuma ba ta sani ba cewa ya gama ko bai gama ba.
Alti ta yi saurin fita ta bar kitchen din. Ya soma samun wani sassanyan sauyi a tare da shi, ya dinga hango rashin kyautatawar sa na tsanar jinin Hadiza da ba ta tsare mishi komai a rayuwa ba.
Auren su da aka yi ya tabbata ita ma ba da son ranta a kai ba, soyayyar Hadiza da ta yi mishi yawa, ita tasa yake kin kowacce mace. Ita kuwa Fati ba zai ce ga dalili ba.
Ya danganta hakan da rashin haduwar jini kawai, ina ruwan shi da tsarin rayuwar ta? Tunda ba a goshi zai lika ta ba? Ya soma kokarin goge muguwar kiyayyar da yake yi mata ta hanyar baiwa zuciyar shi uzuri iri daban-daban ga duk muguwar hujjar da ta kawo.

Sai dai muhimmin abin da iyayensu suka hada wato AURE da mu’amalan auratayya, baya jin zai taba iya yin shi da wadda ta zamo kanwa ga Hadiza. Duk da ba haramun bane shi kam ya haramtawa kansa, an halicce shi kadai don Hadiza, kuma har ya koma inda Hadiza take ba zai kara mallakawa wata diya mace soyayyar shi ba, babu gurbin da zai iya jogana son wata.
Sai dai shi kansa yana mai kalubalantar tunanin sa na cewa zai iya dauwama a haka ba tare da mace ba, kasancewar ta wani bangare na rayuwar dan adam, da kuma ganin tun ba a je ko ina ba ya fara kwana cikin halin ha’ula’i. Dole ya dau matakin da zai kawo karshen duk wannan, wato ya yi nisa da Fati, tun YAKANAR ta, kyautatawar ta, hakurin ta da juriyar ta basu ciwo galabar tattaurar zuciyar sa ba.

Jin ya yi shiru ba ya dinkin kuma bai saki hannun ta ba, Fati tayi saurin bude idon ta, suka yi ido hudu da Sulaiman dan Sulaiman da Inna Halima. Ashe haka Baban Munib yake da kyau? Ban taba sani ba? Fati ta ce a zuciyarta.
“Ina ma a ce yanda yake da kyan nan haka zuciyar shi take da kyau?”. Zuciyar ta kara tambayarta. Ta samu kanta cikin wani sabon yanayi da ba ta taba tsintar kanta a ciki ba.

A wannan daren mai dimbin tarihi a rayuwar kowannen su, daga Fati har Sulaiman babu wanda ya runtsa, soyayyar junan su ke neman samun muhalli a zuciyar kowannen su.
Amma sun sa kafa suna fatali da ita da gan-gan, don a ganin kowannen su bai dace ba. Sannan ita Fati ta riga ta yiwa Dr. Sulaiman mummunar fassara zuwa na makiyinta, mai nuna mata kiyayya karara, kiyayyar da babu wani mahaluki da ya taba nuna mata a rayuwar ta.
Don haka a kan me za ta so shi in ban da sharrin zuciya, don haka take ta ciccijewa, ita lallai karya zuciyar ta take yi ba son shi take yi ba.
Shi kuma a can nashi bangaren, Sulaiman, ya kasa sukuni, ya kasa runtsawa ne a dalilin abubuwa da dama na yarinyar a yau da suka fizge shi.
Ga dai kamannin Hadiza, sannan ga wasu (extraordinary qualities) da ya lura dasu a dan zaman watannin da ya yi tare da yarinyar. Don haka ya kwana cikin yiwa kai da zuciya hisabi, don tantance al’amarin da ke shirin faruwa da shi a kan Fatima Ja’afar Mai-Yadi.
Sakamakon ba mai saukin fadi bane a gare shi, halayen ta da yakanar ta da juriyar ta wajen yin abubuwan ta don Allah ba don ya yabe ta ko ta burge shi ba, sun taimaka kwarai wajen sayo mata soyayyar dole, wanda ke nufin Fati ta yi nasara kenan a kansa? Shi kuma ya fadi game din da suke bugawa. (He is the loser, and she is the winner!
Idan ya yi sake hakan ya bayyana gare ta shikenan za ta raina shi, GIRMA YA FADI! Ya manta cewa a magana ta aure babu raini tsakanin mace da mijinta.
To amma ina zai kai jin kan? Na tunanin kankanuwar yarinyar da yake rainawa ta yi winning a kansa? Don haka tunanin sa na ya yi nisa da Fati, don gudun RAINI ya kara kamari a tare da shi.
A kwanakin da suka biyo baya, duk hanyar da ya san za ta hada shi da Fati a gidan yana kauce mata. Ita ma Fatin hakan, tun daga ranar da ta yanke hannu, ga shi har ciwo ya kame.

****















Basu Kano ba su Abuja shi da wasu daga cikin likitoci ‘yan uwansa, suna fafutukar ‘visa’ zuwa jami’ar Chicago domin halartar wani kwas na shekaru biyu a kan dashen zuciya (heart transplantation) da ‘federal government’ ta tura su.
Ko Inna ba ta sani ba, sai da ya gama dukkan shirye-shiryen sa, shi lallai dole yana yaki ne da zama da Fati kada soyayyarta ta rinjaye shi, shi ya sanya ya sanya kanshi cikin ‘yan tafiyar, don da babu yadda shugaban su bai yi ba ya shiga cikin tawagar amma ya ce a’a, duk da matukar bukatar shi da kwas din da asibitin ke yi, don haka da ya zo da kansa ya ce zai tafi, ba karamin jin dadi shugaban su ya yi ba.
Suka fara shirye-shirye, har zuwa yau da Allah ya nufa suka kammala, sai tafiya kwanaki uku masu zuwa.
Ya cimma su ita da Alti a kicin don su nan ne ofishin su, suna ta suyar dambun nama. Ya hada giran nan sama da kasa lokacin da idanuwansa su kai arba da na Fati, ita ma ta hade tai murtuk kamar ta ga mala’ikan daukar ranta, wannan gigicewar da take yi in ta gan shi yau ba ta yi ba, sakamakon jimawa da ta yi ba ta sanya shi a idon ta ba.
A can wani gefe daga karkashin zuciyar ta, wani sanyi ne ya sauka a zuciyar ta wanda ba ta san dalilin shi ba. Hakika ta azabtu da rashin ganinsa a dan tsakanin, saboda yadda ganin sa ya zame mata SANYIN IDANIYA, yake gusar da duk wani bacin ranta, yake rage mata zugin rashin ‘yar uwarta da ke cin zuciyar ta, duk da rashin alherinsa gare ta kuwa.
Babu ko tantama ta fada a ‘soyayya,’ a inda take da yakinin cewa ba za a taba son ta ba, in haka ne zuciyar ta ta gingimo mata babban aikin da ba ta san ya za ta yi da shi ba.
Yana duban sashin da Fati take kasa-kasa ya gaida Alti, sannan ya dauke kanshi a sashin Fatin, ganin yadda ta yi murtuk da fuska. Ya yi murmushi ya ce da Alti,
“Ku yi shiri zan je in watsa ruwa mu wuce Bakori yanzun nan”.
Alti ta ce, “Allah ya sa lafiya?”
Ya yi murmushi ya ce, “Lafiya kalau Goggo Alti, yara sun kwana biyu basu ga Inna ba, suna ta tambaya ta”.
Ta ce, “To bari mu yi sauri mu karasa”.
Taso ta ce da shi, “Har da Fati?” Ta ga wannan ba abin da ya shafe ta bane sun fi kusa, wai harshe da hakori.
Ita ma Fatin da ba a ce da ita ba kawai sai ta hau shiri, domin tana son ganin Inna ainun. Ta zuba Abaya kirar Kuwait, ta kawo katon hijabin ta har gwiwa ta zuba.
Bayan ta shirya yaran dukkanin su, ta fi son ta goya Nana, maimakon ta yi ta rike ta a hannu ko a kafada.
Har Sulaiman kan yi mamaki ya ce a ransa, ita wannan ba ta gajiya da goyo ne? Duk sanda zai ganta goye da Nana zai ganta. An ce mai da wawa, kulawar da take yiwa ‘ya’yan shi ya taka rawa ba kadan ba, wajen sayo mata soyayya ta kwarai a zuciyar shi.
Kafin wani dan lokaci sun kimtsa tsaf suna falo suna jiran shi, ya fito cikin wagambari shudiya mai hasken sararin samaniya, wato navy blue, hannun shi na hagu daure da agogon RADO na bakar fata, haka takalmin da ke kafar shi wanda ya kasance budadde na fatar damisa.
Babu gilashi a idon shi sai fararen idanun shi ke sheki da daddadan kamshin ‘Chris Adams’ da ya baibaye su.
Yaran suka nufi jikin shi, ya kama hannun kowannen su suka nufi harabar adana motoci, ita kuma ta koma kitchen ta juye dambun naman da suka yi gaba daya ta taho da shi don ta kai wa Inna.
A wajen shiga mota ne ake dirama, yana son ganin in da za ta zaba don zama don son sanin matsayin da ta aje shi, tunda ‘yar gaisuwar da ta ke mishi ma a darare ta hakura ta daina, tunda baya amsawa.
Ta bude gidan gaba su Munib suka shiga, sannan ta sunto goyon ta shiga baya ita da Alti.
Har suka hau titin Kabuga babu wanda ya yi magana, sai yaran da ke ta rigima a tsakanin su a kan jirgin sama mai batir na Munib da Muniba ta dage sai ta amsa.
Ita dai Alti shiru ta yi tana nazarin su, ga dukkan alamu kowannen su ya sauya, ya yi sanyi, amma an rasa wanda zai sauke ya bi dan uwansa. Tana son ganin wanene zai yi jarumtakar tsaga billensa ya bi dan uwansa?
Wadannan ma’aurata suna ba ta dariya, ganin har ta cikin mudubi satar kallon juna suke, amma in daya ya kama daya sai a yi maza a fuske, a dauke fuska, wato babu shiri babu alaka.

Tafiya ta yi nisa a kan kwalta, barci ya fara daukar Alti, yaran tuni sun yi barci har Nana, ya mika hannu ya rage musu karfin na’urar sanyaya mota.
Kawai Sulaiman ya faka motar a tsakiyar daji, ya wani irin juyo ya dube ta, an yi sa’a ita ma a lokacin ta dago daga madara da take bai wa Nana, idanunsu cikin na juna, wani miracle ya yi aiki cikin ‘yan dakikai, ya haifar da wani al’amari mai GIRMA a zuciyoyin su.
Ji yake kamar yana yi mata kallon karshe ne, ya tuhumi kanshi da rashin sauke wani nauyi mai girma da Allah ya ce ya yi, ga shi har zai tafi, tafiyar da babu tabbacin zai dawo ko ba zai dawo ba, tunda rayuwar ba a hannunmu take ba.
Ya samu kansa da son tausasa mata, ko babu komi yana son goge mugun tabon da ta yi mishi a zuciyar ta. Ya tabbata idan Inna ta san har zuwa yanzu bai kula ta ba, la shakka za ta dauki mataki, duk da ya san da wuya Fatin ta gaya mata, tunda ba ta da magana.
Amma in Inna ba ta sani ba ai Allah ya sani, kuma ba zai kyale ba.
Ya mika mata hannu, “Kawo ta in taya ki rainon”.
Ta galla mishi harara, sannan ta kara kankame ‘yarta. Ya yi murmushi ya ce,
“Ko ‘yar gaisuwar da kike min kin daina, why Fati?”
Wannan karon ma ba ta yi mishi magana ba, amma ta tsuke baki ta juyar da kai.
Ya yarfar da hannu, “Tunda kin ki mu yi hirar bari mu karasa gaban Inna, watakila ita za ki yi mata bayanin dalilin ki na daina gaishe ni a matsayina na mijin ki da kuke kwana gida daya ku wayi gari cikin gida daya, zan gaya mata ‘ya’yan ki kawai kika sani, amma ni kin daina shiga sabgata, kin mai dani saniyar ware, dan gyaran dakin da ake min tun daga ranar da kika yanke hannu kin daina.
Haka nan zan iya tunawa cewa, tun daga ranar ne kika daina gaishe ni”.
Nan ma shiru, kamar da dutse yake magana. Haushi ya ishe shi ya fizgi motar. Bai kara tsayawa ba sai a kofar gidan su cikin garin Bakori.
Malam Sulaiman na alwala a kofar gida lokacin da suka isa, ya soma maraba da ‘yan jikokin shi. Suka dunguma suka shiga gidan tare, Inna na sallah lokacin da suka shiga falon ta, sai da ta idar ta shafa addu’a, sannan ne ta karvi Nana a hanun Fati, tana yi musu sannu da zuwa.
Alti tana daga waje, yaran ma Khalid ya shigo sun bishi shagon sa, falon ya rage daga Inna sai Malam, Fati da Dr. Sulaiman, hira ce suke sosai a junan su, ba ta tsoma musu baki ba.
Can anjima ya dubi sashen da take ya yi mata wani irin kallo da ya sanyaya gangar jikinta, ya ce,
“Na kawo karar Fati Inna, ta daina gaishe ni, ga shi ban san laifin da na yi mata ba, na tambaye ta ta yi min banza”.
Kunya ta kama ta, ta mike za ta fita Inna na ganin yadda ya bita da kyawawan idanun shi kamar ya fasa kuka, ta yiwa Allah godiya cikin zuciyar ta, ta tabbata Sulaiman ya fara son matarsa, addu’ar da ta ke kwana da yini tana yi ba ta fadi a banza ba.
Ta ce da Fati, “Koma ki zauna”. Ba musu ta koma ta zauna, amma ba ta kara hada ido da kowa ba, ji take dama kasar ta tsage ta shige saboda kunyar da Baban Munib ya bata.
Inna ta ce, “Wai haka Fatima?”
Malam kuma ya ce, “A’ah! Fatima ba za ta yi haka ba haka kawai, kai dai ka san laifin da ka yi mata”.
Bai yi magana ba. Inna ta ce,
“Me ya yi miki Fati? Na san ba shi da kirki”.
Da kyar ta ce, “Ni bai yi min komai ba, bana ganin sa ne”.
Inna ta ce, “Koma ya yi, ki yi hakuri kin ji Fati, komi na duniyar dan hakuri ne da yafiya (afuwa), kowa hakuri yake da abokin zaman sa, ta hakan ne za a ci ribar zama amma ba ta kullaci da rashin afuwa ba”.
Sai ta ga kamar Inna ta shiga zuciyar ta, da gaske ta kullaci Dr. Sulaiman kullata mai yawa a kan abin da yake yi mata, duk da ta fahimci shi ma ya sakko yana son a shirya, amma ba za ta yarda a shiryan haka (so easy) ba. Ya kuntata mata, ya cuzguna mata yadda harshenta bazai iya bayyanawa ba.
Wanda tun farko ya riga ya ce ba ya son ka, daga baya ya dawo ya ce yana son ka akwai dalilin shi na yin hakan. Change happens only on reasons.
Amma ba za ta iya yin musu da Inna ba, don haka ta ce, “Na yi hakuri Inna. Shima Allah ya huci zuciyarsa”.
10/15/21, 11:47 AM - Buhainat: Munib da Muniba suka shigo, sai suka tsaya saroro suna kallon sa, sannan suka tafi da gudu suka rungume shi suka soma zubo masa hira.
Inna ta kawo mishi waina da taushe ta ji tantakwashi da lemukan zobo da na Aya da ta ke siyarwa cikin firjin da ya saya mata.
Fati ba ta shigo ba, tana gama wankinta ta shanya ta dau mayafinta jikin igiya ta gudu makota gidan wata makociyar Inna Goggo mai gyada. Ba ta shigo gidan ba sai bayan azahar, lokacin shi da Malam suna kofar gida suna sallah da mutane. Ta zaga ta bayan su ta shiga gidan ta shige uwar dakin Inna.
Ya dawo dakin Inna suna hira, shiru-shiru bai ga Fati ba. Ya ce,
“Wai yarinyar nan Inna gudu na take yi?’
Ta ce, “Ni ina na sanar muku, ai kun fi kusa”.
Ya ce, “Tana ina ne?”
Ta nuna mishi uwar dakin ta da dan alinta, ita kuma ta fita don ta dora sanwar dare.
Tana jin shi zai shigo ta yi linkim a gadon Inna, ita a dole barci take. Ya karaso ya zauna a saitin kanta yana kallon kyakkyawar fuskarta ta dan hasken tagar Inna da ya ratso, babu wadatar haske a dakin don haka ya fiddo wayar shi yana haskata sosai.
Ta soma rikide mashi tana komawa Hadiza! Kanshi ya dinga zagayawa jiri ya soma diban shi, a lokacin da ya soma romancing din ta da fuskar Hadizahh……...
Ta yi wani irin juyi ita a dole barci take, kamin wani dan lokaci al’amura suka rikice musu, tun tana pretending har al’amarin yafi karfin kawaicinta da juriyar ta. Jin maganar Inna a falo ya sa ta daddage ta kwaci kanta, jikinta babu inda ba ya rawa saboda firgici da sabon al’amarin da ba ta taba tsintar kanta a ciki ba.
Idanun shi a galabaice ya ce, “Haba Hadizah! Don Allah Hadizahh.....!!”

Wani haushi ya kama Fati, karona farko a rayuwarta da kishin Hadiza ya darsu a ranta, wato ma da sunan Hadiza yake alakanta ta, sannan ne zai iya auratayya da ita?
Za ta fita ya cafke hannun ta, ta wani irin juyo tana hararar sa. Wai an ce aikin banza, harara a duhu. Don kuwa bai gani ba.
Shi ma ya juyo kukan Nana da maganar Inna, don haka ya yi saurin sakin hannun ta, ta fita amma shi bai fito a lokacin ba, sai da ya daidaita kansa tukunna. Sai dai fa shaddar Ghanilla baka wul duk ta yamutse.
Yana tsaye a falon Alti ta shigo suka gaisa, ya ce,
“Goggo Alti sai ku shirya tafiya zamu yi”.
Ta ce, “To ranka ya dade”.
Fati ta kwakkwabe fuska ta ce,
“Nifa Inna sai gobe zan tafi”.
Inna ta ce, “A’a, ga mijin ki ya zo tun daga wata uwa duniya ai wurin ki ya zo, yana bukatar kulawar ki, tashi ku tafi idan ya koma sai ku dawo, mu kullum muna maraba daku”.
Ba da son ranta ba ta tattara kayan su suka tafi. Wannan karon ma a baya ta zauna ita da Alti, duk yaran har Nana suna gaba.
A ranshi ya ce,
“Tunda na rasa Hadiza ai ba abin da ba zan gani ba, ga shi na zama direban Fati ina ji ina gani…..”.

Har suka isa gida babu wanda ya ce da dan uwansa uffan, don babu fuska a wurin Fati, fushi take sosai kan biris din da ya yi da ita tsayin shekara guda da doriya.
Sai shi da Munib suke ta hirar su, Alti na mamakin wadannan ma’aurata da ba ta san yaushe za su saduda su san Annabi ya faku ba. Ba ta san kuma laifin na wane ne a tsakanin su ba.
Suna zuwa gida ta dauko makullin dakin sa ta shiga ta soma gyara, duk da dama a gyare yake, domin duk bayan sati biyu take shiga ta share ta gyara ta wanke toilet.
Shi kuma da ya ajiye su fita ya yi, bai dawo ba sai karfe goma na dare. Ya yi wanka ya yi excercise ya zuba pajamas da turaren shi na kullum, amma a yau sai ya samu kansa da karawa da ‘Boss-Intense’, ya cakuda da ‘far away’. Sannan ya kara da ‘Gio-Gio Armani….’ Ango sosai. Mai ji da koshin lafiya da kuruciya, wanda Allah yayiwa duk wata ni’ima ta rayuwa.
Ya tadda Fati a dakinta, ita ma lokacin ta yi wanka tana busar da gashin ta da hand dryer, cikin wasu tausasan nighties, masu shara-shara, ya kashe dirayar ya ajiye a gefe, cikin kunnuwan ta yake rada mata.
“…..Ki yi hakuri mana Fati…..don Allah ba don ni ba”.
Ta ce, “Da aka yi me fa?”
Ya ce, “Rashin kiran ki a waya, ba haka kawai bane ina da hujjoji na”.
Cikin raunin murya ta ce,
“Kana da hujja sosai, hujjar baka damu dani ba, kana kiran kowa ban da ni, ba sai ka yi haka zan san cewa baka so na ba, lika maka ni aka yi. Tuni na kwana da sanin wannan......” Hawaye suka balle mata.
Ya juyo ta da sauri suka fuskanci juna, sanyin numfashin su na dukan fuskar kowannen su. Ya ce,
“Ni na ce da ke bana son ki?”
“Baka fada ba amma ka nuna mini, ka nunawa zuciyata. Tunda har ka iya ka yi shekara baka nemi jin lafiya ta ba, saboda ni kadai ka tsana a duniya, a kan laifin da ban sani ba”.
Ya yi murmushi sosai ya ce, “Dole sai ta bakin ki zan ji lafiyar ki? Ina ji a bakunan da ba za su yi min karya ba.
Maganar lika min ke aka yi, sai in ce MADALLAH da wadanda suka lika min ke, yaa ke ma’abociyar YAKANAH!.
Domin na hadu da alhairori da yawa a tare da auren ki. Ki yi min afuwa Fatima kamar kullum, ban san ki da kullaci ba, saboda ke na jingine komi dake gabana na zo, kada ki sagar min da gwiwa, saboda in gyara zaman mu, in gyara kurakurai na.
Na tabbata Hadiza ta tafi;

She is my past…... and you are my present.....!!!”

Haka ya ci gaba da kalallame ta da kalami masu dadi, har ya samu ya karbi abin nan mai matukar daraja daga gare ta. Ya rungume ta tsantsan yana fadi a ranshi,

“Yaya, (Sa’adatu) ta haifi ‘ya’yan baiwa”.

Albarka da addu’a, hadi da godiya mara iyaka Fati ta samu daga Dr. Saiman har ta gode Allah. A bisa yanayin daya risketa. Idan aka ce mata wani abu mai kama da MAFARKI to wannan ranar ce. Ranar da bata taba mafarkin gani cikin mafarkanta ba. It’s a dream that comes true. Bata jin akwai wani sauran buri da ya rage mata a rayuwa bayan na cikawa da imani da dorewar wannan ‘indescribable moment’ har karshen rayuwarta.
****







Kwanaki biyar din nan da yayi bai zuwa ko’ina sai barzar amarci, har Fati ta saba, duk da tana matukar cin kwakwa, tana galabaita matuka da wannan sabuwar rayuwa data samu kanta. To abin ne an tara shi fal, tsawon shekaru biyu ba kadan.

Albarka kam tana shan ta, ya soma tunanin yadda zai iya komawa ya bar Fati, saboda yadda ta zamo wani bangare na gangar jikinsa, zuciyar sa da ruhin sa gabadaya, ga shi suna tsaka da karatu balle ya yi mata visa in ya so yaran a kai su wajen Yaya.

A gobe ne zai tashi zuwa Lagos, daga nan ya bi jirgi mai zuwa Chicago. Fati tana hada mishi kaya, duk jikinta ya yi sanyi saboda mugun sabon da suka yi cikin kwanaki shidda kacal, sannan ga wata iri kewa na cin zuciyarta mai wuyar bayyanawa.

Ya fito daga wanka yana tsane kanshi da karamin tawul, jin kansa yake wani sabo, fresh, kamar yanzu aka bare shi a leda. Tunda ya samu ya sauke al’amuran da suka takurawa zuciyar shi da lafiyar shi. Inda zai iya maida Fati ciki, da watakila ya yi hakan ya sanya ta cikin ya gudu da ita.

Abin alfahari ce ga duk namijin da Allah ya baiwa, ya gode Allah da bai bi son zuciyar shi ya bijirewa iyayen shi ba. Ya tabbata da tuni yazo yana nadama. Nadama mara amfani kuwa.
Ta mika mishi wasu kayan barci ‘yan Indonesia marassa nauyi, ta ci gaba da hada sauran. Ashe hawaye take zubarwa shi bai sani ba, ya sanya kayan barcin, ya zauna a gabanta ya janye jakar kayan da ta ke hadawa, ya kamo dukkan hannuwanta biyu ya rike cikin nashi.

“Haba Fati! Ai sai ki karya min gwiwa, ku yi shiri ke da Nana ku raka ni har Lagos, sai in sanyo ku a jirgi ku dawo. In kin yi kuka ke da kike da ababen debe kewa (‘ya’ya) ni kuma in yi ya ya?
Kamar yau ne za ki ga na je na dawo, mai da hawayen nan maza-maza bana son ganin su”.
Ta ja shessheka tana kokarin mai da hawayen, daga nan kuma aka koma aikin lada, mai gigitarwa.

Karo na farko da Fati ta taka matattakalar jirgi a rayuwarta. A Lagos sun jima suna tsimayen lokacin tashin jirgi me zuwa Chicago, yana ta tausar ta da kalami masu dadi kamar ba Dr. Sulaiman ba, da cewa; ta kula da kanta, karatunta, da ‘ya’yanta. Suna daga mishi hannu ita da Nana ya bi matattakalar jirgin da sauri, ba tareda waiwaye ba, ya tabbata zai yi kewar su.

Karfe biyu na rana nasu jirgin (Bell-View) ya dawo dasu gida (Kano). Malam Habu ya debe su a Airport.

Tun tana damuwa da rashin Sulaiman har ta saba, ta sanyawa ranta salama, musamman kuma da yake duk dare suna tare a waya, ta maida hankali kan karatun

2 Comments On YAKANAH
avatar
rabiatu-2

1 year ago

Reply

Thanks

avatar
fatima-2-7-5

1 year ago

Reply

very nice book

Please Login or Register in order to submit comment