Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

shi kamar yadda ta ga Hadiza na yi.
Da gudu ta koma daki ta kulle, yana fitowa zai fita rike da ‘brief case’ ya yi tozali da sabbin warmers, sai kamshi ke tashi bisa dining din shi. Da gaske yunwa ta gallabe shi, hanjin cikinsa har rawa yake. Sai dai yana ganin idan ya ci ya zama sakarai tunda ga abin da ya ce da ita jiya, kuma raini zai gitta.
Don haka ya hadiye azababbiyar yunwar shi ya fice. yana shiga AKTH ya nufi gun cin abincin manyan likitoci na asibitin, can ya yi kalacin sa. Sai dai a bakinsa babu dandano, don Hadiza ta riga ta sangarta shi da cimar Fati mai dadin da ba ya misaltuwa, ya kuma fi na Goggo Alti wadda a da yake ganin babu wadda ta kaita iya sarrafa abinci, musamman na Hausawa wanda ya fi kama mishi ciki kasancewar shi ma'abocin tara yunwa kafin ya yi quenching din ta.

Da ta tabbatar ya fita, ta fito ta bude ma’adanan abincin, babu abin da aka taba. Bata ji haushi ba, ta tattara ta mikawa Malam Ilu bayan ta dibi iya wanda take ganin za ta iya ci, ta koma daki ta yi wanka sannan ta zauna cin abinci.
Tana kammalawa wayarta da ta sa a caji ta yi kara, ta amsa cikin kamilalliyar muryar ta, Inna ce. Suka gaisa, sannan ta mikawa Malam Sulaiman shima suka gaisa.
Ya yi mata addu’a sosai, ya kara da cewa, ta jure duk wani rashin jin dadi da za ta fuskanta daga mai sunan shi, nature (halittar shi) kenan, fara nuna kiyayya ga abu kamin ya so shi. Da yardar Allah watarana za ta tashi da riba.
Ranta ya yi fari, zuciyarta ta yi haske, a kalla ta san ta samu surukai na gari da ke son ta. Ta kara jin karfin gwiwar son ci gaba da kyautatawa Sulaiman, ba don ya yabe ta ko ya so ta ba. Ita ma ba son na shi take yi ba, sai dai ba za ta iya yin watsi da al’amarin shi kamar yadda ya bukata ba, saboda alkawarin da ta daukar wa Hadiza, ta tabbata sakayyar ta na wurin Allah.
Don haka ta mike ta nufi dakin shi don ganin ko akwai gyararrakin da za ta iya, cikin sa’a rufe kofar kawai ya yi amma bai sa key ba.
Ta murda ta shiga cikin sallama duk da babu kowa, wannan tarbiyya ce mai kyau sabida mala’ikun rahma. Dakin babu kintsi, ko ina takardu baja-baja, gado a yamutse, kayan wanki a toilet fal cikin kwando.
A jikin bed side ta yi tozali da ‘yar uwarta tana murmushi. Ta karasa ta dauki ‘frame’ din hoton tana shafawa a hankali tana murmushi itama, hawaye fal idanun ta.
Ta maida shi mazaunin shi ta nade hannun riga ta soma gyara komai neatly, ta cire bed sheet ta canza wani. Ta kunna A.C don dakin ya yi sanyi.
Ta koma toilet ta hau wankin da ya dauke ta har zuwa azahar, ta fito da kayan inda suke shanya ta shanya, ta wanke bandakin sosai da parazone, sai daukar ido yake, ta jawo kofofin ta fito ta soma aikin falo wanda babu datti sosai don su Inna sun tsaftace ko ina kamin su tafi.
Zuwa la’asar kayan sun bushe, sai tashin kamshin Dr. Sulaiman suke kamar yanzu aka fesa turaren gidan (Chris Adams) ba’a sanya su a omo ba.
Ta yi shimfida a falo ta soma goge su da dutsen guga, ta kammala cikin dan lokaci, ta je ta jera mishi a wardrove ta kunna burner ta turare dakin da bandakin da touch me, sannan ta fita ta koma dakinta ta yi wanka ta kwanta tana hutawa.
Bai dawo gidan ba sai goma na dare, nan ya soma shakar daddadan kamshin amarcin da gidan ke yi, ya kara cin karo da sakon Fati a kan dining cikin wasu flasks din asu zabar kyau ba na dazu ba.
“Wato yarinyar nan ba ta jin magana”.
Ya fadi a zuci.
Ya danna kai dakin shi, kamar ya sume don daddadan kamshin da dakin ke yi, da wata ni’ima ta musamman dake fita, wanda ya gauraye da rabar split mai sanyaya zuciya da kasalantar da gangar jiki.
Ya bude wardrove don ya sauya kaya, nan ma ya cimma sakon Fatima Ja’afar Mai-Yadi. Ya girgiza kai ya ce,
“Na san maganin ki tunda baki da zuciya”.
Washegari ma Fati ta kara yin kalacin kunun tsamiya dan leda, da poncake ta aza dining. Yau ma da ya gani wucewa yayi yana girgiza kai, cikin ransa yake fadin.
“Lafiya ce ta yi miki yawa kike losing energy din ki a banza!”.
‘Surely’ yana bukatar abincin, amma girman sa da yake tattali a idanun ta ya hana shi. In ya ci girkin ta ashe tana da amfani cikin gidan kenan, shi kuma so yake ya nuna mata da ita da babu duk daya. Babu wani amfani da mace za ta yi masa tunda ya rasa wadda yake so, ya jure rashin Hadiza ma balle rashin cin abincin da yake so?
Haka suke ta gangarawa har tsayin sati guda. Ranar lahadi yana gida, Mukhtar ya yi sallama ta hanyar danna kararrawa.
Ya tashi daga kan computer ya je ya bude, Mukhtar Ja’afar ne rungume da Baby Nanah, Munib da Muniba na biye da shi, suka rangada da gudu suka rungume mahaifin su.
Shi ma ya rungume su yana bin kowannen su da sumba, idon shi a lumshe. Suka karasa cikin falon shi da Mukhtar, Mukhtar ya mika mishi Nana, ya karbe ta ya rungume yana sunsunar ta. Sannan ya tsaya yana kallon ta, kamannin shi da ita har sun yi yawa.
Suka yi musabiha da Mukhtar, yake gaya mishi Inna ce ta yi waya ta ce a kawo su wajen babar su. “Ina Fatin ne? Ko barci take?”
Cikin dauriya ya ce, “Bari in duba”.
Ta fito daga wanka ke nan tana rufe kofar bandaki, karamin towell ne ta daura daga kirji zuwa cinyoyin ta, kanta cikin hular wanka, tana jona hand dryer don busar da gashin kanta da ya jike.
Ya turo kofar ya shigo, idanun shi suka yi kyakkyawan gani, shi kadai ya san abin da ya tsirga daga yatsar kafa zuwa zuciya da kwakwalwar sa, ashe model yarinya ce a cikin HIJABI?
Kallon second biyu ya yi mata ya dauke kansa, sannan ya juya da sauri cikin kakkausar murya ya ce,
“Mukhtar ke kiran ki”.
Ta zubo doguwar rigar shadda ‘dark-bluesenegalese’ ta dora da matsakaicin hijabi, ta tadda su a falon.
Ai kuwa su Munib suka yo tsalle suka yo kanta, har suna kokarin kada ita. Itama ta rungume su, suka soma jero mata tambayoyi.
“Anti Fati, Mummy ba ta dawo ba har yanzu? Ina kika tafi muka daina ganin ki? Nana tana ta kuka idan bakya nan, don Allah kar ki kara tafiya ki barmu…..”.
Ta ce, “Ba zan kara ba”. Ta kamo hannun Muniba, “Ba inda zan je muna tare kun ji my kids?”
Suka yi murmushi sannan ta karasa ta russuna ta gai da Yayanta, wanda suke ta hirar su shi da Sulaiman, ta nufi firjin kitchen ta kawo mishi lemon (Donsimon) da gorar ruwan (Eva) mai rangwamen sanyi.
Mukhtar bai dade ba ya yi musu sallama ya tafi. Bayan ya karbi lambar Fati. Tana so ta karbi Nana amma tana bisa cinyoyin sa, ta fara kuka don ta dade ba ta sha madara ba.
Dole ya mika mata ita, hannuwan su suka saka kara gogewa dana juna. Wasu irin hannuwa gareta masu bala’in taushi kamar auduga, wadanda suka tada tsigogin jikinsa. Ita kuma suka haifar mata da kasala irin wadda ta ji a ranar da hannun ta ya fara shafar nasa.
A hanzarce ya mike, “Oya kids! Muje mu sha (Ice-cream)”.
Suka yi tsalle suka dane kafadun shi, Munib ya ce,
“Amma har da Anti Fati za mu je?”
Ya yi kamar bai ji shi ba, ita dai jakar kayan su ta dauka ta yi ciki da Nana a hannun ta. Ya sunkuci yaran shi duka biyun a kowanne hannu daya du girmansu, suka yi waje.
Dama tana da tafasasshen ruwa cikin filas a kitchen, nan da nan ta dama madara ta soma baiwa Nana bayan ta sha iska.

****Kayan cefanen su sun kare, ba ta san ya za tai ta gaya mishi ba, saboda irin yadda yake bi ya daure fuska kamar wani soja idan ya ganta.
Fati na mamakin wannan wace irin kiyayya ce Sulaiman yake mata ta babu gaira babu dalili?
Kamar ita ce ta kashe Hadiza?

Yana da wata kima a idon ta kasancewar shi wanda ya auri ‘yar uwarta da ba ta da ya ita a duniya, ya zauna da ita, ya rayu da ita cikin so da kauna da kyautatawa har ta koma ga mahaliccin ta, ba ta taba fadan laifin sa ko aibunsa ba, ko wani abu da ya yi mata na rashin dadi.
Sannan da kasancewar shi Baban ‘ya’yan da take so sama da komi a duniya. Idan ba zai so ta ba ai ta ci albarkacin Hadiza.
Amma yadda yake nunawa kamar ko a hanya basu taba hada wata alaka ba, idan ta biyewa wulakancin da yake mata ta ce za ta dinga bata ranta a banza, ita ce za ta cutu, ta dorawa kanta ciwon zuciya da hawan jinin da ko duba ta ba zai yi ba, balle ya rubuta mata magani.
Don haka ta debe tsoro da shakku, bayan sun dawo yana kwance a falo yaran shi sun baibaye shi suna ta yi mishi tadi, shi kuma yana aiki cikin kwamfutar da ke bisa ruwan cikin sa.
Ta lallabo ta fito uwa munafuka, tana goye da Nana ta rabe a gefe, Muniba ta taho ta zauna a cinyar ta. Sai a lokacin ya ankara da shigowar ta falon, ya juyo da sauri kamin ta yi magana ya mike, ya aje computer a fusace.
Ta runtse ido tana jiran saukar mari a lallausan kumatun ta, ya ce,
“Don’t I warned you? Idan ban neme ki ba ki daina zuwa inda nake?”
Cikin makyarkyatar murya da gigicewa ta ce, “Ka yi hakuri, kayan cefane ne suka kare, sannan babu kayan abincin makarantar su Munib”.
Ya yi tsaki “Tsuuu!” Kamar ya tsinke harshen sa, ya ce, “Na ji shikenan ko?” Ta mike a salube gwiwa babu karfi ta koma daki, don ita ba abin da ta tsana a rayuwarta irin a yi mata tsawa.
Su kansu yaran sun tsorata da tsawar da Baban su ya yiwa Antin su, sun yi zuru-zuru, suma ya nuna musu hanya ya ce su bita. Da gudu suka tafi har suna faduwa, ya kashe komai ya fice daga gidan.

Washegari Alti ta dawo, ba karamin jin dadin dawowar ta Fati da yara suka yi ba, ko ba komai ta samu mai taimaka mata da debe mata kewa, don Goggo Alti mutum ce mai barkwanci da ban dariya.
Sai ga Malam Ilu yana shigowa da kayan abinci nau’i-nau’i. Suka zaun ita da Alti suka gyara komai suka adana na adanawa a firij, suka markada na markadawa suka adana a ‘freezer’
Washegari ta tashi da wuri da taimakon Alti suka kammala komi da wuri, suka shirya yaran da abincin su, karfe bakwai da rabi Babansu ya kwashe su ya wuce dasu, sannan ya dangana ga ofishinsa.
Kuma ranar ne su Yaya Haulatu kanwar Yaya da wasu daga aminan arzikin ta suka zo suka yi mata jeren kayan gado dai-dai karfin iyayen ta da dan uwanta Mukhtar.
Falon ba ya bukatar komi, masu gidan sun riga sun tsara abin su dai-dai da rayuwar su ta masu murza tsinin biro, sai ba’a taba komi ba, iyakacin su dakinta.

A kwanaki bakwai da Alti ta yi tare dasu, ta fahimci irin zaman kare da kyanwar da ake tsakanin Fati da maigidanta Dr. Sulaiman. A ranta ta ce,
“Yarinya kyakkyawa kamar Hadiza, ga hankali da addini, ko meye nakasunta da Dr. Sulaiman ya kasa son ta?”

Ta ce, “Ko da yake so ba’a nan yake ba, abune wanda ke faruwa kawai a duk sanda ya so, ga duk wanda ya so, cikin iko da kudurar Allah.

A yau suna yankar alayyahu ita da Alti, domin yin miyar wainar masar dare. Suka jiyo motsin shi yana shigowa kitchen din, tuni Fati ta soma makyarkyatar jiki, kan ka ce meye wannan wuka kakkaifa ta shiga cikin naman hannun ta.
Don ita ko gyaran muryar shi ta ji gigicewa take ta fita hayyacinta kada ya yi mata tsawar nan tashi mai dimauta ta.
Jini ya soma bulbula a dai-dai lokacin da ya idasa shigowa kitchen din. Alti ta ce, “Ya salam! Kin gani kin yanke, na yi na yi ki daina amfani da wannan wukar kin ki, ta fiye kaifi da yawa, sannan gaki da saurin gigicewa”.
Ya ji hankalinsa ya tashi ganin yadda jini ke gudu amma ba ta dago ba. Ta dukar da kai ko motsi ta ki yi. Ya basar Ya ce, “Babu sauran ruwan roba ne Baba Alti? Firjina babu komai, sannan ina jin kishi”.
Ta mike zuwa store ta dauko mishi katon na FARO ta dawo, ta kama hannun Fati ta ce, “Babu kananzir balle in sanya miki, bari a daure da tsumma”.
Ta tsaga zanin ta tana kokarin daure mata. Ya kalle ta a kaikaice ta kasan ido ya fita, zuciyar shi babu dadi, don ya tuno yadda ta nuna damuwa ranar da ya yanke nashi hannun.
Mamaki ya kama Alti, ashe Baban Munib ba shi da kirki? Matarka ta yi irin wannan yanka amma ko kallo ba ta ishe ka ba?
Tana daure mata Fati ta fara kuka yankar ta fi karfin daurewa da tsumma. Alti ta biyo shi, ba ya falon yana dakin sa. Ta tura Munib wanda ke ta wasan game cikin computer ta ce ya kirawo Baban shi.
Jim kadan suka fito tare shi da Munib, yana rike da gorar ruwan yana sha. Cikin takaici ta ce,
“Zan kai Fati asibiti ne”.
Ya sunkuyar da kai duk jikin shi ya yi sanyi, ganin bacin rai kwance a fuskar tsohuwar da bai taba ganin bacin ran ta ba tsayin shekaru shida da suka yi tare da ita, ya dukar da kai sosai ya ce,
“Bari in diba ciwon nata”.
Ya koma daki ya dauko first aid box ya same su a kitchen din, jinin na ta zuba har yanzu.
Sanye yake da brown getzner ta sha dinkin Mohammed wanda shi ne dinkin sa kawai, ya russuna dai-dai inda take sunkuye, ya kama hannun ta. Wani sanyi ya tsirga a zuciyar ta. Dago idon nan da za ta yi sai idanun su cikin na juna, wadannan kwayan idon na Sulaiman suka birkita ta, kamar yadda suke birkita zuciyar duk wata lafiyayyar macen da ta san cewa akwai tsokar zuciya a tare da ita. Amma ga shi Sulaiman, gani yai ta rikide mishi ta koma Dr. Hadizah……

“Wannan yankar sai an yi dinki”. Ya fadawa Alti.
Cikin sanyin murya ta ce, “Ai shi ya sa na ce muje asibitin”.
Ya ce, “Ba damuwa bari in dinke mata”.
Ya fara da yi mata allurar ‘anaesthesia’, sannan ya fara dinkewa. Idanunta a rufe ba ta bude ba har ya gama.
Bayan ya gama ci gaba ya yi da rike hannun bai saki ba, ita kuma ba ta sani ba cewa ya gama ko bai gama ba.
Alti ta yi saurin fita ta bar kitchen din. Ya soma samun wani sassanyan sauyi a tare da shi, ya dinga hango rashin kyautatawar sa na tsanar jinin Hadiza da ba ta tsare mishi komai a rayuwa ba.
Auren su da aka yi ya tabbata ita ma ba da son ranta a kai ba, soyayyar Hadiza da ta yi mishi yawa, ita tasa yake kin kowacce mace. Ita kuwa Fati ba zai ce ga dalili ba.
Ya danganta hakan da rashin haduwar jini kawai, ina ruwan shi da tsarin rayuwar ta? Tunda ba a goshi zai lika ta ba? Ya soma kokarin goge muguwar kiyayyar da yake yi mata ta hanyar baiwa zuciyar shi uzuri iri daban-daban ga duk muguwar hujjar da ta kawo.

Sai dai muhimmin abin da iyayensu suka hada wato AURE da mu’amalan auratayya, baya jin zai taba iya yin shi da wadda ta zamo kanwa ga Hadiza. Duk da ba haramun bane shi kam ya haramtawa kansa, an halicce shi kadai don Hadiza, kuma har ya koma inda Hadiza take ba zai kara mallakawa wata diya mace soyayyar shi ba, babu gurbin da zai iya jogana son wata.
Sai dai shi kansa yana mai kalubalantar tunanin sa na cewa zai iya dauwama a haka ba tare da mace ba, kasancewar ta wani bangare na rayuwar dan adam, da kuma ganin tun ba a je ko ina ba ya fara kwana cikin halin ha’ula’i. Dole ya dau matakin da zai kawo karshen duk wannan, wato ya yi nisa da Fati, tun YAKANAR ta, kyautatawar ta, hakurin ta da juriyar ta basu ciwo galabar tattaurar zuciyar sa ba.

Jin ya yi shiru ba ya dinkin kuma bai saki hannun ta ba, Fati tayi saurin bude idon ta, suka yi ido hudu da Sulaiman dan Sulaiman da Inna Halima. Ashe haka Baban Munib yake da kyau? Ban taba sani ba? Fati ta ce a zuciyarta.
“Ina ma a ce yanda yake da kyan nan haka zuciyar shi take da kyau?”. Zuciyar ta kara tambayarta. Ta samu kanta cikin wani sabon yanayi da ba ta taba tsintar kanta a ciki ba.

A wannan daren mai dimbin tarihi a rayuwar kowannen su, daga Fati har Sulaiman babu wanda ya runtsa, soyayyar junan su ke neman samun muhalli a zuciyar kowannen su.
Amma sun sa kafa suna fatali da ita da gan-gan, don a ganin kowannen su bai dace ba. Sannan ita Fati ta riga ta yiwa Dr. Sulaiman mummunar fassara zuwa na makiyinta, mai nuna mata kiyayya karara, kiyayyar da babu wani mahaluki da ya taba nuna mata a rayuwar ta.
Don haka a kan me za ta so shi in ban da sharrin zuciya, don haka take ta ciccijewa, ita lallai karya zuciyar ta take yi ba son shi take yi ba.
Shi kuma a can nashi bangaren, Sulaiman, ya kasa sukuni, ya kasa runtsawa ne a dalilin abubuwa da dama na yarinyar a yau da suka fizge shi.
Ga dai kamannin Hadiza, sannan ga wasu (extraordinary qualities) da ya lura dasu a dan zaman watannin da ya yi tare da yarinyar. Don haka ya kwana cikin yiwa kai da zuciya hisabi, don tantance al’amarin da ke shirin faruwa da shi a kan Fatima Ja’afar Mai-Yadi.
Sakamakon ba mai saukin fadi bane a gare shi, halayen ta da yakanar ta da juriyar ta wajen yin abubuwan ta don Allah ba don ya yabe ta ko ta burge shi ba, sun taimaka kwarai wajen sayo mata soyayyar dole, wanda ke nufin Fati ta yi nasara kenan a kansa? Shi kuma ya fadi game din da suke bugawa. (He is the loser, and she is the winner!
Idan ya yi sake hakan ya bayyana gare ta shikenan za ta raina shi, GIRMA YA FADI! Ya manta cewa a magana ta aure babu raini tsakanin mace da mijinta.
To amma ina zai kai jin kan? Na tunanin kankanuwar yarinyar da yake rainawa ta yi winning a kansa? Don haka tunanin sa na ya yi nisa da Fati, don gudun RAINI ya kara kamari a tare da shi.
A kwanakin da suka biyo baya, duk hanyar da ya san za ta hada shi da Fati a gidan yana kauce mata. Ita ma Fatin hakan, tun daga ranar da ta yanke hannu, ga shi har ciwo ya kame.

****















Basu Kano ba su Abuja shi da wasu daga cikin likitoci ‘yan uwansa, suna fafutukar ‘visa’ zuwa jami’ar Chicago domin halartar wani kwas na shekaru biyu a kan dashen zuciya (heart transplantation) da ‘federal government’ ta tura su.
Ko Inna ba ta sani ba, sai da ya gama dukkan shirye-shiryen sa, shi lallai dole yana yaki ne da zama da Fati kada soyayyarta ta rinjaye shi, shi ya sanya ya sanya kanshi cikin ‘yan tafiyar, don da babu yadda shugaban su bai yi ba ya shiga cikin tawagar amma ya ce a’a, duk da matukar bukatar shi da kwas din da asibitin ke yi, don haka da ya zo da kansa ya ce zai tafi, ba karamin jin dadi shugaban su ya yi ba.
Suka fara shirye-shirye, har zuwa yau da Allah ya nufa suka kammala, sai tafiya kwanaki uku masu zuwa.
Ya cimma su ita da Alti a kicin don su nan ne ofishin su, suna ta suyar dambun nama. Ya hada giran nan sama da kasa lokacin da idanuwansa su kai arba da na Fati, ita ma ta hade tai murtuk kamar ta ga mala’ikan daukar ranta, wannan gigicewar da take yi in ta gan shi yau ba ta yi ba, sakamakon jimawa da ta yi ba ta sanya shi a idon ta ba.
A can wani gefe daga karkashin zuciyar ta, wani sanyi ne ya sauka a zuciyar ta wanda ba ta san dalilin shi ba. Hakika ta azabtu da rashin ganinsa a dan tsakanin, saboda yadda ganin sa ya zame mata SANYIN IDANIYA, yake gusar da duk wani bacin ranta, yake rage mata zugin rashin ‘yar uwarta da ke cin zuciyar ta, duk da rashin alherinsa gare ta kuwa.
Babu ko tantama ta fada a ‘soyayya,’ a inda take da yakinin cewa ba za a taba son ta ba, in haka ne zuciyar ta ta gingimo mata babban aikin da ba ta san ya za ta yi da shi ba.
Yana duban sashin da Fati take kasa-kasa ya gaida Alti, sannan ya dauke kanshi a sashin Fatin, ganin yadda ta yi murtuk da fuska. Ya yi murmushi ya ce da Alti,
“Ku yi shiri zan je in watsa ruwa mu wuce Bakori yanzun nan”.
Alti ta ce, “Allah ya sa lafiya?”
Ya yi murmushi ya ce, “Lafiya kalau Goggo Alti, yara sun kwana biyu basu ga Inna ba, suna ta tambaya ta”.
Ta ce, “To bari mu yi sauri mu karasa”.
Taso ta ce da shi, “Har da Fati?” Ta ga wannan ba abin da ya shafe ta bane sun fi kusa, wai harshe da hakori.
Ita ma Fatin da ba a ce da ita ba kawai sai ta hau shiri, domin tana son ganin Inna ainun. Ta zuba Abaya kirar Kuwait, ta kawo katon hijabin ta har gwiwa ta zuba.
Bayan ta shirya yaran dukkanin su, ta fi son ta goya Nana, maimakon ta yi ta rike ta a hannu ko a kafada.
Har Sulaiman kan yi mamaki ya ce a ransa, ita wannan ba ta gajiya da goyo ne? Duk sanda zai ganta goye da Nana zai ganta. An ce mai da wawa, kulawar da take yiwa ‘ya’yan shi ya taka rawa ba kadan ba, wajen sayo mata soyayya ta kwarai a zuciyar shi.
Kafin wani dan lokaci sun kimtsa tsaf suna falo suna jiran shi, ya fito cikin wagambari shudiya mai hasken sararin samaniya, wato navy blue, hannun shi na hagu daure da agogon RADO na bakar fata, haka takalmin da ke kafar shi wanda ya kasance budadde na fatar damisa.
Babu gilashi a idon shi sai fararen idanun shi ke sheki da daddadan kamshin ‘Chris Adams’ da ya baibaye su.
Yaran suka nufi jikin shi, ya kama hannun kowannen su suka nufi harabar adana motoci, ita kuma ta koma kitchen ta juye dambun naman da suka yi gaba daya ta taho da shi don ta kai wa Inna.
A wajen shiga mota ne ake dirama, yana son ganin in da za ta zaba don zama don son sanin matsayin da ta aje shi, tunda ‘yar gaisuwar da ta ke mishi ma a darare ta hakura ta daina, tunda baya amsawa.
Ta bude gidan gaba su Munib suka shiga, sannan ta sunto goyon ta shiga baya ita da Alti.
Har suka hau titin Kabuga babu wanda ya yi magana, sai yaran da ke ta rigima a tsakanin su a kan jirgin sama mai batir na Munib da Muniba ta dage sai ta amsa.
Ita dai Alti shiru ta yi tana nazarin su, ga dukkan alamu kowannen su ya sauya, ya yi sanyi, amma an rasa wanda zai sauke ya bi dan uwansa. Tana son ganin wanene zai yi jarumtakar tsaga billensa ya bi dan uwansa?
Wadannan ma’aurata suna ba ta dariya, ganin har ta cikin mudubi satar kallon juna suke, amma in daya ya kama daya sai a yi maza a fuske, a dauke fuska, wato babu shiri babu alaka.

Tafiya ta yi nisa a kan kwalta, barci ya fara daukar Alti, yaran tuni sun yi barci har Nana, ya mika hannu ya rage musu karfin na’urar sanyaya mota.
Kawai Sulaiman ya faka motar a

2 Comments On YAKANAH
avatar
rabiatu-2

1 year ago

Reply

Thanks

avatar
fatima-2-7-5

1 year ago

Reply

very nice book

Please Login or Register in order to submit comment