Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta da rainon ‘ya’yan ta.


Shekara kwana ga mai yawan rai, Dr. Sulaiman-Sulaiman Bakori, ya gama course din shi cikin nasara da shi da sauran likitoci ‘yan uwansa. Aka yi mishi sauyin aiki da karin girma zuwa babban asibitin koyarwa na Abuja, a lokacin Fati na mataki na uku a jami’a, dauke da tsohon ciki na haihuwa yau ko gobe.

Zuwa wannan lokacin Fati ta gama mallake komi na Sulaiman, da da’arta, halayen ta da addinin ta. Ita ce matar shi mafi kusanci da shi, sannan kawar shi abokiyar shawarar shi. A gefe abin so da kaunar shi.
Iyayen na matukar alfahari da wannan aure da suka hada a bayan ran marigayiya Hadiza, wadda har gobe, jibi, har gata basu daina yi mata addu’a ba. Kuma tunaninta bai taba gushewa daga zuciyar kowannensu ba.

Dr. Sulaiman yana Abuja, sai week end yake zuwa musu, sai ko in duk sun samu hutu suma su ke bin shi Abujan.

Ranar wata litinin kwana daya da tafiyar Sulaiman nakuda ta kama Fati, suka nufi asibiti ita da Alti, yaran duk suna Karkasara.
Kafin magariba ta haifi sankacecen danta mai kama da Baban shi har farcen kafa. Sai waya Dr. Surayyah ta yi mishi cewa baby ya iso. Sai ga shi a washegari kamar an jefo shi, ya tadda Fati da baby a ‘aminity’, sai dai dakin cike yake da ‘yan uwanta. Sai daga nesa yake jifanta da murmushin
‘bani da abin da zan gode miki’.
Ita ma murmushin take masa da su kadai suka san ma’anar abin su.
Ba da son ranshi ba Yaya ta wuce da ita gida inda za ta yi wanka, don Alti an aiko mata rasuwar danta a kauyen su Kukawa, don haka za ta tafi a washegari.

Dakin ta na da Yaya ta gyara mata suke wankan, Munib dan kankanba ya kasa sukuni saboda ya yi kani namiji dan uwan sa. Bini-bini zai ce a ba shi ya dauke shi, ita kuma Fati ba ta gajiya da mika mishi shi.
Kawarta Fa’iza ta zo mata barka wadda ita ma an yi auren ta tuni, suka wuni sur suna hirar bayan rabo, don Fati ta zamewa Fa’iza abin sha’awa ganin yadda ta yi kyau ta kara girma, yanda duk wanda ya dube ta duba daya zai tabbatar tana da kwanciyar hankali a gidanta.
Sabanin ita da kishiya ta sa ta gaba, ta hana ta zaman lafiya. Fati na tausar ta tare da ba ta shawarwari na gari.

Ranar suna yaro ya ci sunan Malam, wato Ja’afar. Malam ya roke su kar su boye mashi suna su kira shi da Jafarun shi.

Juma’a yamma lis, Dr. Sulaiman ya iso Kano daga Abuja, kai tsaye gidan surukan sa ya fara dosa. Bayan motar shi dankare da himilin tsaraba, Yaya ta yi mishi shimfida da sabuwar tabarma, ta sunto baby da ke bayan ta ta mika mishi.
A lokacin Fati ta fito daga bandaki, ta yi daurin kirji ta rufu da tawul, ta sha dukan ganye, jikin nan ya kara zama fresh, fatar nan ta kara zama mai taushin gani a ido.
Ta kasan ido ya dube ta, sai ya ga duk ta canza mishi, ta kara zama yarinya danya sharaf. Da alama ba ta da damuwa, sun barshi da kadaici, sai fama yake da biro da takarda.

Yaya ta shige kitchen ta barsu, ai kamar jira yake ta tashi ya yi ma dakin Fati tsinke. Tana tsane gashin kanta da tawul ya bude mata dukkan hannuwan sa bayan ya aje babyn a cikin katifar sa. Ta rufe ido tana dariya, shima ya san bazata iya ba, har a gobe halayenta na kawaici da alkunya basa canzawa, sai shi ne ya karaso ya rungume ta tsantsan a hankali, yana fada mata kalaman da suka zama sirri ne a tsakanin su tana ta sakin murmushi. Cikin ranta addu’a take Allah ya barta da SULAYMAN dinta, ya dorar da rayuwarsu cikin daukaka da soyayya, kamar yadda ta faro, har zuwa ranar da suka daina numfashi.

*** ***












SHEKARU GOMA SHA BIYAR A GABA!

Taron rantsar da sabbin ministoci da mai girma shugaban kasa President Umaru Musa ‘Yar Aduwa zai gabatar a yau a hotel din NICON NOGA, har da babban likitan zuciya da kasarmu Najeriya ke tanka how
da shi, wato Dr. Sulaiman Sulaiman Bakori, wanda aka rantsar a matsayin Ministan Lafiya na kasa baki daya. Ranar Litinin, ashirin da shida ga watan Maris, na wannan shekarar.

Dr. Fatima Ja’afar, H.O.D Islamic, a jami’ar Abuja, cikakkiyar mace ‘yar kimanin shekaru talatin da bakwai da haihuwa, uwar ‘ya’ya biyar a halin yanzu, in ka hada da manyan ‘ya’yan ta Munib, Muniba da Nana Khadija sun zama su takwas kenan.
Tana sanye da bakar abaya kirar Bahrain da mayafinta, hannunsu sakale dana juna suka isa ga mazaunin su, daukacin Ministocin da ake shirin rantsar wa suna tare da matansu da rakiyar ‘ya’yansu, to haka suma, Muniba, Nana Khadija, da Ja’afar. Ya yin da suka baro Mufida, Mufid da Ibrahim da dan autan su Abdulhak a gida, cikin kulawaar tsohuwa Alti.

Bayan mai girma shugaban kasa ya rantsar da Ministocinsa, aka zarce da gagarumar walima. Ba su baro dakin taron ba sai dare, suna kan hanyar isowa gida wayar Munib ta shigo, wanda ke can kasar ‘Srilanka’ yana karatun harhada magunguna.


Munib Ya ce,
“Daddy kun manta dani, ko waya an fi sati ba wanda ya yi min.
Yanzu nake jin abin alheri a BBC, congratulations Daddy!”
Ya ce, “Kwantar da hankalin ka Munib, zirga-zirga ta hana mu neman ka. Ina mai yi maka albishir da cewa, muna tafe dukkanin mu cikin satin nan, sai ka tanadar mana better”.
Ya yi ihu ya ce, “Allah Daddy da gaske?”
Fati ta amshe wayar ta ce,
“Amma sai in point din ka na wannan semester ya kai CGPA 4.00, if not, babu wanda zai zo”.

Ya ce, “Wallahi 4.60 ma na samu Mummy”.
Ta ce, “Ah, lallai Babban Yaya ka gama min komai, zuwan kowa ya zama dole, tunda duk muna cikin hutu”.

Ja’afar ya amshe wayar ya ci gaba da ba shi labarin duk shagulgulan da ake yi a yau. Munib ya ciji yatsa ya ce,
“Ayya! Na yi missing….”.
Daga nan sai Muniba, ita kuwa Nana ta ce, ba za ta yi magana da shi ba tunda baya yi mata waya sai budurwar sa kawarta Naina.
Daddy ya harare ta ya ce,
“Bana son sakarci, shi ba shi da wata budurwa dan makaranta ne”.
Ta ce, “Amma yake yi mata waya yake yo mata tsaraba in zai zo?”.
Ya ce, “Ba kanwar shi ba ce? Ke ba ya yi miki?”
Ta ce, “Wallahi Daddy nata ya fi yawa, har da kati an rubuta I LUV YOU”.

Fati ta tintsire da dariya, shi kuma Dr. Sulaiman sai ya rasa ta cewa, yaran zamani sai a barsu, da wayonsu ake haifar su.
Ya dubi Fati da wani irin sassanyan kallo, “Momin yara, wai da gaske ne Munib yana da budurwa?”
Ta rausayar da kai ta ce, “Shirmen Nana ne, Naina Bunza, tana da shiga ran kowa sosai ba Munib kadai ba, suna shiri da Munib sosai sabida kokarinta.”. (Diyar Dr. Surayyah).
Ya ce, “Ba zan yi mamaki ba in son nata yake, ai jin kanshi yake matured (balagagge) kamar kowa”.
Dariya ta kama Fati, sai da ta murmusa sosai.
Sun isa gida yara kowanne ya kama harkar gabansa, ya cacumi Fati su kai sama ana biyan bashin soyayya, wadda hidimar kwana biyu ba ta bari ba. Suka ci gaba da amsa sakonnin taya murna da fatan alheri daga ‘yan uwa da abokan arziki, har tsayin sati daya.

Ranar juma’a jirgin MEA International ya tashi dasu zuwa Srilanka, har filin jirgi Munib yaje ya taro su, ya dauki Abdulhaq ya rungume suka karasa zuwa makarantar su bayan sun yi booking din hotel din da za su sauka.

Farin cikin Munib ba sai an fada ba, ya rasa inda zai sa iyayen shi da ‘yan uwan shi. Dr. Sulaiman ya yi bincike sosai kan karatun shi, ya yaba sosai da hazakar da yaron ke nunawa. Kwanan su uku suka wuce Saudiyyah suka yi Umarah, sannan suka dawo gida.

Da albashinta da ta ke tari, da kuma taimakon Dr. Sulaiman, Dr. Fatima Ja’afar, ta bude makarantar Islamiyya ta yara maza da mata a nan Abuja, da aka sanyawa suna NANA HADIZAH ISLAMIYYAH. Haddar Alkur’ani mai girma ake yi tsantsa, sai sauran littattafan addini irin su Ishmawi, Bulugul Maram, Sirah, Hadith, Al-Akhdari, Fikh da koyar da harshen larabci. Ana zuwa daga karfe biyu na rana zuwa shida na yamma.
Ba ta da abin da za ta ce da Dr. kuma Minista, Sulaiman dan Sulaiman, sai godiya da addu’ar alheri, domin ya gama cika mata burinta na son yada ilimin Alkur’ani da hadisi, kamar yadda ta ke buri.
Ya lullube ta da duk wasu alhairori na rayuwa, ya lullube ta da so da kauna. Gaskiyar Babanta ne; Alqur’anin ta ba zai bari ta tozarta ba!!!

Ta san Sulaiman ba ya son ta ya aure ta, kuma ba zai taba son wata diya mace kamar yadda ya so Hadiza ba, amma tana tantama a halin yanzu, idan son da yake mata baiyi kunnen doki da wanda ya yi wa Yayarta Dr. Hadiza ba.

A alfarma ta soyayyah, ta san ba ta cancanci Dr. Sulaiman ya so ta a wancan lokacin ba, amma ya so ta saboda hakuri, juriyar ta da YAKANAR ta. Ya so ta sabida kyawawan halayenta.
“Mene ne YAKANAH?”
Nayi tattaki har gidan Dr. BAKORI na tambayi Malamarmu, Dr. Fatima Ja’afar Mai-Yadi.
Ta yi murmushin ta mai motsa zuciya tace.
“Takori ba ki san Yakanah ba?”
Na ce, “Ina zan sani Fati? Sai ku malaman addini”.
Ta yi murmushi ta ce,
“Nima daliba ce SUMAYYAH! Sai dai in sanar da ke dan abin da na sani a dalibtaka ta”.
Na ce, “daure ki sanar dani Aunty Fati, komi kankantar sa. Domin al’umma zasu so su san me ita wannan kalma ta YAKANAH take nufi?”.
Faty ta yi murmushi tana dubana ;

MECE CE YAKANAH???

Ita YAKANAH ba kasaifai ake ganin ta a wajen yawancin mutane ba, YAKANAH ita ce take daukaka darajar mai yin Ibadah, ta kai shi wani matsayi na daukaka a wajen Allah. YAKANAH ita ce tushen dukkanin aiyuka na gari, wato daukacin ayyukan kirki suna fitowa ne daga cikin ta.
Mutum mai YAKANAH shi ne mai yin babban jihadi ko gwagwarmaya da kansa wajen watsi da abubuwan da rai da zuciya ke so, saboda neman yardar Ubangiji, da neman dadin falalar sa, tare da nuna biyayya a gare shi.
An ambaci irin wadannan mutane a cikin Alkur’ani mai girma, kamar cikin suratul Al-Imran (3:17) Al-Nisa’i (4:25, 127-128), Fussilati (41:34) da sauran su.
Irin wannan babban jihadi da kai ana yin sa ne tsakanin mutum da zuciyar sa (Nafs Al-Ammara), domin sauya ta ya zuwa (Nafs Al-Lawwama), sannan ya zuwa zuciya madaukakiya (Nafs Al-Mutma’innah).
Saboda haka madallah da ita wannan baiwa ta YAKANAH, domin tana kai masu yin Ibadah zuwa ga matakin shiga cikin rukunin salihai wadanda a koyaushe suna masu yin godiya a kan dukkanin abin da ya zo musu daga Allah.
YAKANAH it ce kololiyar taqwa wato tsoron Allah. Takwah kuma ita ce mai kore tsoron haduwa da Allah (wanda ba ya jin kunyar ubangijinsa kuma mai sabon sa, shi ne mai zama cikin fargabar haduwa da Allah).
Daya daga cikin ma’anar YAKANAH ita ce, ka dinga kallon kanka a matsayin kai ba kowa bane a cikin jama’a, kuma kowa ya fi ka, saboda haka YAKANAH tana nuni da rashin kasancewar mutum cikin halin GIRMAN KAI!
Misalai: Idan ka kasance mutum ne kai mai YAKANAH ta gaske, a duk lokacin da ka gamu da wani mutum wanda baka san shi ba, komi lalacewar sa, sai ka ce da kanka a cikin zuciyar ka.
“Watakila matsayin wannan mutum a wajen Allah ya fi nawa”.
Idan kuwa ka gamu da yaro kankani, sai ka cewa kanka, “Ka ga wanda ba ya sabon Allah, ni kuwa ina yi”.
Idan kuwa ka gamu da wanda ya girme ka, sai ka ce, “Ka ga wanda ya jima yana bautar Ubangiji tuntuni kafin ni”.
Idan kuwa ka yi kicibus da mutum mai dimbin ilimi, sai ka ce, “Ga wanda aka yiwa baiwa da abin da ni bani da shi, domin ya fi ni ilimi, kuma yana aiki da ilimin sa, amma ni ko ya ya dai?”
Idan kuwa ka yi karo da jahili, sai ka ce, “Dubi wani yana sabon Allah cikin rashin sani, ni kuma ina yi cikin sani. Ga shi kuma ban san yanda karshen sa zai kasance ba, kuma ban san nawa karshen ba. Ko me zai zama a nan gaba? Allah shi ya fi kowa sani”.
Idan kuwa ka gamu da kafiri, sai ka ce da kanka, “Wa ya sani? Watakila nan gaba ya musulunta kafin ya mutu, kuma wa ya sani ko ni kuma in mutu a kafirce?”
Ire-iren wadannan maganganun gaba daya suna nuni da halin mutumin da YAKANAH da tawali’u suka baibaye shi, yake kuma cikin hali na binciken kansa a koyaushe.
Dalilin irin wannan tunani a zuciyar wannan bawan Allah shi ne, yana cikin yanayi na rashin yarda da kansa. Tare da rashin tabbas game da abin da zai abku wajen haduwar sa da Allah.
Ire-iren wadannan tunani kuwa suna nuna karfin imani ne da dogaro da Allah madaukakin sarki wanda shi ne tushen kaskantar da kai.
A kowanne lokaci idan bawa ya kaskantar da kansa, Allah zai kare shi daga masifu, kuma ya ba shi sirrin “Ikhlasi” Wato nacewa da son bin hakikar gaskiya a dukkannin al’amuransa na yau da kullum. Daga wannan mataki ne mutum zai kasance cikin mutane ‘yan kadan wadanda suka samu yardar Allah tare da kusanci da shi.
YAKANAH ita ce kofar da ake bi ta cikinta zuwa wurin da baiwar Allah da rahamar sa suke muhimmancin YAKANAH ga musulmi kamar kwatankwacin bargo ne a cikin kashi.
YAKANAH tana a matsayin bargo na Ibadah, kuma sauran ayyuka suna a matsayi na kashi. Bayin Allah wadanda ake kira ‘zahideen’ masu cike da da’a da tsantsenin duniya, tare da ‘nasiqeen’ masu sadaukar da rayuwar su domin bautar Ubangiji, dukkannin su suna ji da wannan baiwa ta YAKANAH.
Bayin Allah masu YAKANAH basa yin maganganu barkatai, basa yin tsegumi ko wata muguwar magana a game da wani a bayan idanun sa, su kan fadi abin alheri ne a game da shi. Ba sa shiga sharo ba shanu, kuma zuciyar su fes take. Ta kuma nisanta da miyagun dabi’u, kamar hargowa da JI DA KAI. Wato kirjin irin wadannan bayin Allah garau yake.
Duk maganar da irin wadannan bayin Allah masu YAKANAH suka fadi, ta dace dai-dai da abin da suka yi, suka kuma yi imani da shi.
Basu da wani abu da za su boye a zuciyar su domin kada wani ya sani, wato basu da wani mummunan abu a tare dasu.
Bayin Allah ne masu zallar gaskiya da rikon ta, wanda duk ya yi hulda da irin su zai ga cewa basa fafutukar neman kuskure a kan wani, maimakon haka, a shirye suke wajen neman kuskure daga wajen su, wato a kan kansu.
Basa yarda su zauna tare da (marada) (masu kawo tsegumi). Don haka ‘yan uwa musulmi mu yi damara da kokarin kasancewa cikin bayi masu YAKANAH, mu rike addininmu, mu kama Alqur’anin mu, mu suturce jikinmu, mu tsayar da sallah domin samun dacewa a duniya da lahira. Kamar jarumar wannan littafi, Allah ya bamu iko amin summa amin.
Takori
10/15/21, 11:47 AM - Buhainat: Yakanah
10/15/21, 11:47 AM - Buhainat: Tana ganin sanda sulaiman ya saki wata boyayyar ajiyar zuciya.
Inna ta ce, “To Allah ya yi muku albarka”.
Ya gyara zamansa cikin nutsuwa yace,
“Inna dama na zo in yi muku sallama ne….”.
Cikin mamaki ita da Malam suka hada baki suka ce, “Zuwa ina?”
Fati kuwa zuciyar ta ce ta buga, irin bugun da ba ta taba yi ba. Ya soma yi musu bayanin course din da aka zabe su su goma shi da abokan aikinsa na shekaru biyu a cikin jami’ar Chicago din Amurka.`
“Amma tare za ku tafi da iyalinka bakidaya ko?” Malam ya tambaya.

Ya ce a ransa, “An yi ba’a yi ba kenan! Fatin yake gudu, Fati yake son tserewa, Fatin yake so yayi nisa da ita, Fatin yake son yiwa kandagarki daga son kutsowa cikin rayuwarsa da karfin gaske, bai shiryawa hakan ba, bai taba mafarkin kasancewar hakan ba, kada ta rushe masa plan din rayuwa, in ya dauke ta suka tafi me aka yi ke nan? Bonono rufe kofar da barawo?
Duk da shi ma ya soma kalubalantar kansa da ganin wautar sa na tsallake abinda rai da zuciya suka soma so da gangan, wai don kada GIRMA YA FADI!”.
Ya ce, “A’a, za su zauna ita da Alti saboda yara suna zuwa makaranta”.
Malam ya ce, “Kun yi shawara ne ta yarda za ta zauna?”
Bai iya karya ba, kai tsaye ya ce, “A’a, bamu yi zancen ba”.
Ya ce, “To sai ku yi shawara a tsakanin ku can, in ta yarda za ta zauna din shikenan, mu ‘yan sanya albarka ne”.

Ba su taho ba sai yamma lis, kamin su iso gida har an yi kiran isha’i, kasancewar duk a koshe suke, Inna ta cika musu ciki da dambun shinkafar ta mai dadi, basu shiga kicin ba kowacce ta nemi makwancin ta, yaran ma sun nabba’a a dakin su, shi kuma ya juya asibiti.

Fati tana shiga daki ta kwanta rub da ciki, da filo a karkashin ta cikin wani mawuyacin hali na soyayyar Baban Munib da ke cin zuciyarta. Ta kai hannu ta dafe kirjin ta wanda ke bugawa da-sauri-da-sauri da haruffan SU-LAI-MAN a kowacce dakika, zai tafi ya barta, bayan ya gama da farauto zuciyarta, ya kimsa mata soyayyar da ba ta san iyakacin ta a zuciyar ta ba.
Ya warware duk wata nutsuwa da tunanin da ke tare da ita, ya mamaye 80% na zuciyarta. Ya haifar da wasu al’amura masu girma a gare ta da ba ta san ya ya za ta yi dasu ba.
Jin tafiyar shi take har ruhi da bargon jikinta, Fati tace wai maiyasa wasu mazajen suke haka ne? Idan sun san sun kimsa maka soyayyarsu, sai su nemi gudu su barka da jibgin abar ka?
Wasu hawaye suka zubo, maimakon ta share sai ta tara hannu tana tarar saukar su a kan tafukan ta. Ba ta ji motsin bude kofa ba sai alamar zaman mutum a gefen ta, kafadunsu suka gogi na juna, ta yi hanzarin juyawa, Dr. Sulaiman ke kallon ta da murmushi.
Ya sanya hannu cikin aljihun bakin jeans da ke jikinsa, ya zaro hankicin sa ya mika mata, ta jima ba ta karba ba, daga karshe ta karba ta share ambaliyar hawayen ta.
Ya mika mata hannu alamar ta ba shi abinsa, sai ta kalle shi sannan ta sunkuyar da kai ba tareda ta bashi ba.
Ya ce, “Bani mana? Ko kukan bai kare bane?”
Ta tsuke fuska, ta tsuke baki, ta hade girar sama da ta kasa.
Ya yi murmushi ya sa hannu cikin hannunta ya dauke hankicin sa, kadan ya rage ta sume da hucin sassanyan numfashin sa ya doki fuskar ta, kamshin jikin sa na fizgar ta, da wata itin fizga mai karfi, kamin ta farfado daga shidewar da ta yi na wucin gadi ya fice a dakin.

Zuwa can kuma ya dawo da takardu a hannun sa, sai dai wannan karon ya janye murmushin da ke kan fuskar shi, ya zauna dab da ita cikin kakkausar murya ya ce,
“Me ya sa ki kuka?”
Shiru ta yi masa ba ta amsa ba, zuciyarta na ci gaba da azalzala da azabar soyayya, wadda ke linkuwa a bayan kowacce dakika. Jikinta ya soma rawa, tana son cewa ya tashi ya ba ta waje ta samu iska amma ta kasa. Kallon ta yake yana (observing) da ido, da zuciya. Gaba daya yanayin ta ya sauya, ya nuna wata mace da ke azabtuwa da soyayya da sha’awar mijinta mai yawa.
Amma kawaici da kau da kai ya rinjayi komi, ya tabbata idan ya tafi ya bar ta cikin wannan halin, Allah ba zai yafe mishi ba, amma tunanin Hadiza ya danne komi. Tattalin girmansa da mutuncinsa a idanun yarinyar ba zai bar shi ya aiwatar da abinda zuciyoyin su da gangar jikin su ke so ba, idanun shi a juye yake kallon ta, gangar jikin shi babu inda bai kaduwa. Ya soma kokarin saisaita kansa, in azabar soyayya ce ai ya fita dandana, ba tun yau ba.
Ya janyo brief case ya fiddo daurin kudi masu tudu ‘yan awolawo ya ajiye a gefen ta, sannan ya mika mata form din JAMB Online.
Ta dan ware ido tana kallon sa da alamar jin dadin hakan sosai a kwayan idanun ta, ya kawar da fuskar shi gefe ya ce,
“Zan bude maku account da skyeBank in Allah ya kai mu gobe, in na wajen ki sun kare kuna da bukata sai ku je ku diba. Akwai sabon direba na aje muku duk inda kuke son zuwa ki kira shi a waya ki gaya masa, ni zan tafi jibi insha Allahu sai Allah ya nufe mu da dawowa.
To amma Fati, ba zan samu ko da kalmar Allah kiyaye hanya ba, daga Fatin da ba zan kara gani ba, sai bayan wasu shekaru har guda biyu?”

Hawayen ya kara zubo mata, ta yi saurin sharewa da bayan hannun ta. Ya tsura mata ido analytically, can kuma ya ce,
“Girl, ina so in san damuwar ki….., Akalla ko ban yi miki maganin ta ba, ina da shekarun da zan ba ki shawara a kanta. Ta bangare na dai duk hanyar da nasan zan bi in gyara kuskure na nabi, amma kin ki bani hadin kai I do not your thoughts. Not even a single word from you, you are indeed a nice person! Duk wanda ya zauna da ke na lokaci kankani, zai so ci gaba da zama da ke muddin rayuwar shi!!”

Ta yi hanzarin dagowa ta dube shi, kallon ta yake ta cikin kwayar idon shi, da wani lallausar murmushi makale a gefen bakin shi.
“Gaya min mene ne damuwar ki Fatima?”
A hankali ta ce,
“Babu”.
“Ba kya bukatar komai?”
Nan ma ta ce,
“Eh, Allah ya kai ku lafiya!”.

Ya ji dadin addu’ar da ta yi mishi, sai dai ba irin wannan rabuwar yake so su yi ba, ta rashin dadin zuciya. Ta ki sakin jiki dashi ko yaya ne.
Ya kama tafin hannun ta ya rike cikin nashi, “Ba za ki gaya min abin da ke sanya ki kukan ba?”
Ta ce a ranta, “Za ka yi min magani ne?”
Magana ta yi a zuci, ba ta san ta fito, ta shiga kunnuwan sa ba.
“Idan ina da shi me zai hana in yi miki?”
Ta ce, “Bani da damuwa, ba sai mutum yana da damuwa yake yin kuka ba, wani zubin mutum yana yin kukan, don ya ji dadin ransa”.
Ya yi murmushi a kaikaice ya lakaci kuncin ta da dan alinsa,
وتتاىاMu kwana lafiya, amma ina rokon ki duk wasu inconveniences ki yafe min su!!!”.
Ta lumshe ido kafin ta ce, “Babu wani inconvenience game da kai a tare dani, kada ka manta ka ce ni kanwar ka ce. Idan Yaya Mukhtar ya yi min laifi zan kullace shi ne, ko zan kasa yafe mishi?”
Ya yi kirr! Da ido yana duban ta da wani irin sassanyan kallo. Kalmar “Yayan” sai yau bata yi mishi dadi ba kamar ba shi ya jaddada ta ba. Tattausar muryar ta da nutsuwar ta na burge shi har bai son a daina hirar, ita kuma so take a gama, saboda yadda yake kara ruruta wutar son shi a zuciyarta
Nana ta yi motsi za ta soma kuka, dukkan su suka juya gare ta, suka mika hannu a tare don su dauke ta, nata hannun ya riga sauka a kan Nana, don haka nashin sai ya sauka a kan nata. Dukkan su babu wanda bai ji a jikin shi ba. Ta yi saurin sakar mishi Babyn, ta dunkule hannun ta.
Ya dauke ta ya kai kafadun shi ya mike tsaye yana safa da marwa da ita a dakin don ta koma barci, ya kasa fita a dakin Fati, mai wani irin sihirtaccen kamshi da ba zai ce na kowanne turaren wuta ne ba, haka nan gauraye da rabar A.C mai kwantar da hankali. Dakinta ko tsinke babu saboda masifar tsafta. Bai ki ba su kwana a hakan, yana jin sassanyan sautin ta mai motsa zuciya, ta yi mata rahma ko da ba da son ran mutum ba.
Ya kwantar da Nana cikin dan gadon ta dake kan gadon Fati, ya mika mata hannun

2 Comments On YAKANAH
avatar
rabiatu-2

1 year ago

Reply

Thanks

avatar
fatima-2-7-5

1 year ago

Reply

very nice book

Please Login or Register in order to submit comment