Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

take it easy......." Ya shiga rattabo mata al'amarin da ya samu rayuwarta, ya kare da cewa, "Wannan shi ne ya dagawa Sulaiman hankali, amma kamar yadda Baba ya ce ne, ki yi tawakkali, ki zamo mai YAKANAH! Wannan ba shi ne karshen rayuwar ba!"

A matsayinta na cikakkiyar likita, ma’abociyar sani a fannonin kiwon lafiya, tuni ta hararo mummunan nakasun da ya samu rayuwarta rana tsaka wanda babu wani likitan duniya da zai iya maganin shi. Ta nemi hawaye a kwayar idonta ta rasa, ta nemi miyau don ta hadiya a kan harshen ta ya kafe karaf! Kamar bai taba gudana a cikin bakinta ba.

Ta runtse idonta da karfi, tsawon mintuna biyar ba ta bude ba. Ita kadai ta san radadin da take ji a zuciyarta, ita kadai ta san azabtuwar da ruhinta ke yi, al'amarin ya shallake tunanin ta. Ba ta yi tsammanin al'amarin ya yi kamarin haka ba, bata taba kawowa ba, spinal cord injury! A gareta ita Hadiza. Lallai dan adam ba a bakin komai yake ba.
Yau ne kake mai rai, gobe ne kake gawa. Yau ne kake da amfani, idan Ubangiji ya so, gobe ne ka zama tarihi. A rayuwar Hadiza ba ta taba tsammanin wata kaddara makamanciyar wannan za ta taba shafar rayuwar ta ba. To ina ruwan Allah!

Ta bude idon a hankali daga runtsewar data yi musu, tana kallon iyayen ta da 'yan uwanta wadanda dukkanin su ke sharar hawaye, sai ta soma lallashin su cikin muryar ban mamaki, tamkar ba ita ba. Ta fi su karfin zuciya, ta fi su tawakkali, ta fi su YAKANAH. Ta karbi kaddarar ta da hannu bibbiyu, tana fatan Allah ya sa hakan ya zamo kaffara a gare ta, in kuma jarrabawa ce ya sa ta cinye jarrabawar ta.

****
Dole kanwar naki, Sulaiman yana ji yana gani, da hannusa da kudinsa ya sayo ma Hadiza wheel chair ana i gobe za a sallame su daga asibiti. Wani bigire na karshe da ko makiyinsa baya yiwa fatan ya hau. Don duk raunin dake jikinta ya kame sai karfin jiki da dan abin da ba a rasa ba.
Yaya ta so Sulaiman ya ba ta Hadiza ta wuce da ita gida inda za ta fi samun kulawar iyaye da 'yan uwa, amma sai ya sa musu kuka. Da me zai ji ne? Da lalurar da ta kashe masa rayuwa, ko da rashin Hadiza a cikin gidan, wadda ta zamo wani bangare na rayuwar sa, kundin farin cikin sa, sannan barin jikinsa?
Dole suka kyale shi da matar shi, amma sun ce Fati ta koma gidan ta zauna tare dasu, don ta dinga taimaka masa kula da Hadiza, musamman kasancewar sa ba mazauni ba.
Sulaiman bai so ba, don shi tun fil'azal Allah bai sa mishi son Fati ba, saboda son da Hadiza ke mata. Yana kishin Fati, a ganin sa Hadiza ta fi son Fati a kanshi. Sannan zubin ta na zuhudu (gudun duniya) ya yi yawa, bai fiya son mutane irin ta ba, kasancewar shi (sociable).
A tsarin halittar dan adam (personality), tana cikin rukunin al'ummar da ake kira (introvert). Ba ta iya hada ido da shi, kai da kowa ma, saboda kunya. Da wuya ka ga hakoranta, sai dai in guri ya kure ta yi murmushi, ‘dimple’ din da ‘cleft’ su lotsa, wanda shi ne muhimmin al'amarin da ke daukar hankalin dubban maza a kanta, sai dai kuma bai isa ya tsallake hukuncin da Yaya ta yanke ba.

Haka Fati ta hado kayan ta tsaf, ta dawo gidan 'yar uwarta da zuciyar 'yan uwantaka. Zuciyarta cike fal da so da kaunar 'yar'uwar ta da tausayinta, karatun da ta taso shekara da shekaru da burin yin sa, gashi ta samu, amma a yau ta sallama shi, ta jingine shi ta sadaukar da rayuwarta kacokam da lokacinta ga rayuwar, 'yar uwarta Hadiza.

Sulaiman ya ciccibo Hadiza ya fito da ita daga mota, Fati ta bude (boot) ta fiddo wheel chair a nade, cikin sauri ta warware, Sulaiman ya sanya ta a ciki ya tura a hankali zuwa cikin gida.
Fati ta fiddo kayansu daga cikin motar ta rufe motar, ta soma diban kayan daya bayan daya tana shiga dasu cikin gida.
Malam Ilu maigadi, ya yi sallama a falon, a lokacin Sulaiman na kici-kicin aza Hadiza a daya daga cikin kujerun falon, ba tare da ya juyo ba ya amsa masa.

Ya zube har kasa yana jajantawa iyayen gidansa kaddarar da ta same su. Yana magana yana sharar hawaye, saboda yadda yake matukar kaunar Hadiza, saboda karamci da kyautatawar ta gare shi.
Haka Goggo Alti ta fito daga kitchen, ganin Hadiza yau nade cikin kujera sai ta fashe da kuka, Sulaiman ya yi saurin ficewa a falon ya dau mota ya fita don dauko yara a makaranta.
Hadiza ta dubi Alti ta yi dan murmushi, "Alti wane ne ya halicce mu?"
Ta ce, "Allah (S.W.A)".
Ta ce, "To kinga in haka ne ke nan bamu da iko da kanmu sai abin da ya ga damar hukuntawa a gare mu, mu kuma dole ne mu zamto masu godiya idan har muna so imanin mu ya cika".
Alti ta jinjina kai tana mai jinjina karfin imani irin na uwargijiyarta.
Hadiza ta juya ga Fati ta ce ta kai kayanta dakin ta, kasancewar a tsarin gidan likitocin babu wani extra room, ita za ta yi amfani da na Sulaiman.
Fati ta ce atafau ita dakin su Muniba za ta zauna tare dasu, ta kada ta raya amma ta ki, ta ciccibi jakarta ta yi dakin su Muniba d ita.
Fitar ta daga falon ke nan su Munib suka dira a falon, Baban su na biye dasu yana rike da jakunkunan su da food flasks din su. Suka tafi da gudu suka rungume Mamarsu, Munib da yake shine mai wayo ya ce,
"Mummy yaya jikin ki? Daddy ya gaya mana kin yi accident kin ji ciwo kina asibiti ana yi miki allura?"
Ya kai hannu ga tabon ciwon goshinta, "Sannu Mummy, kin ji?". Ta shafa kansa ta yi masa murmushi bata ce komai ba.
Ita kuwa Muniba bin jikin Mummyn ta yi ta lafe kamar mage, dama ita ba ta fiya magana ba. Zuciyarta kal da ganin mahaifiyarta da ta jima ba ta gani ba.
Munib ya soma jan hannunta wai ta taso suje su yi kwallo (ball) kamar yadda suka saba, Sulaiman ya kau da kai, bai son ganin wannan abin tausayi, ya mai da hankali ga lallatsa wayar sa, baya son su ga hawayen sa.
To ita ma Hadizar duk dauriyar ta sai da hawayen suka tsatstsafo, ta sa yatsun ta biyu ta dauke su, ta kama dukkan 'ya'yan biyu ta rungume a kirjinta. Kukan zuci take wanda ya fi na fili soya zuciya. Ta ce,
"Ku tafi wurin Anti Fati tana dakinku ku yi kwallon tare, har yanzu bani da lafiya".
Da gudu suka mike daga jikinta suka nufi dakin su suna murnar zuwan Antin su da suke tsananin so. Alti ta yi sallama dauke da tray kanta a sunkuye, idonta cike fal da hawaye, muryarta a sanyaye tace da Hadiza,

"Na ce sai na daina daura abinci a tebir?”

Hadiza ta yi murmushi mai hade da wani irin radadi a zuci, ta ce,
"Idan maigidan yana son hawa tebir din fa?"
Ta fada tana kallon Sulaiman.
Bai dago ya kalle su ba, haka bai tofa musu ba, duk da ya lura ta bakinsa suke son ji. Alti ta ajiye katon tray a gaban Hadiza ta juya ta fita.
Tana ba da baya ya suri Hadiza a kafadar shi sai dakin barcin su. A hankali ya sauke ta a makeken ‘family bed’ din su, ya koma toilet ya cika baf da ruwa mai dumi, ya zuba dettol kadan ya dawo ya soma warwarewa Hadiza kayan jikinta, ya nade ta cikin towel ya sake sungumar ta ya yi toilet ya sanya ta cikin ruwan da ya hada. Ita karfin Sulaiman mamaki yake bata. Ya yi mata kyakkyawan wanka da kamsassan sabulun Zest, ya nado ta ya fito da ita.
Yawancin kayanta a dakin suke dama, don haka ya shirya ta cikin riga da wandon pakistan ruwan goro (orange), ya dauki (kumb) ya soma sharce mata gashin kanta da ya wanke da (head&shoulder) wanda rashin gyara kwana biyu ya sa shi duk ya cukurkude.
Ta ce, "Da ka bari Sulaiman Fati za ta yi min gyaran kan".
Bai saurare ta ba ya ci gaba da abin da yake, amma da a ce ta kalli fuskarshi a lokacin, data lura da yadda ya dan hada rai, saboda ambatar Fati da ta yi, wato ta fi son Fati ta kula da ita fiye da shi.
Ta yi murmushi ta ce, "Amma tunda ka hada ruwan wanka ka yi mai wuyar, zan iya wanka da kaina, sai Fati ta shirya ni koda yake ma zan iya shiryawa da kaina.......".
A hassle yace .
"Is o.k Hadizah, very o.k, ba tun yau ba na san kin fi son kanwar ki fiye dani. In ba haka ba ni amfanin me ke gare ni? Da ba zan kula dake ba a lokacin da kike cikin lalura?"
Ta kama baki, don ba ta ji dadin maganar shi ta farko ba, amma sai ta share ta ce, "Yau da gobe ne sai Allah Sulaiman…….". Can kuma ta yi rau-rau da ido kamar hawaye za su zubo,
"Me ya kawo maganar na fi son Fati a kanka? Ban ji dadin nagetive response din ka ba".
Ya ce, "To ai ke ce Hadiza da wani irin batu, amma ina so ki yarda da cewa, idan zan gaji da hidimar ki Hadiza, to zan gaji da hidimar kaina……".
Ta ce, "Amma Sulaiman......"
Ya kai hannu ya toshe mata baki, "Kina shakka da abin da na ce miki?"
Ba ta son jan zancen da nisa, har ya yi tsayin da zai zamo bacin rai, sai ta ce,
"Bana shakka Sulaiman, Allah ya bamu rai da lafiya".

Ya turo ta cikin kujerar ta suka dawo falon don cin abinci. Munib da Muniba suka shigo, fes dasu cikin kaya 'yan kanti (pink colour) har Fati tayi musu wanka ta shirya su ta feshe su da turare.
Suka saki baki cikin mamaki, ganin Daddy yana tura Mummy cikin kujera mai tayoyi, abin ki da yaro, sai ba su kawo ma ransu komai ba, ko wani abu ne ya faru da Maman nasu, sun dauka haka nan dai yake tura ta don bata da lafiya. Sai suka sa rigimar ta tashi suma Daddy ya tura su.
Haka Sulaiman ya sauke Hadiza a seater, ya dauke su su duka biyun ya aza a kujerar, ya yi ta zagaya falon dasu suna jin dadi, sai kyalkyatar dariya suke.
Hadiza ta juya ta dube su, ganin abin nasu ba na kare bane ta ce, "Oya! Food is ready, maza ku zo ku ci kafin malamin lesson ya zo, ko kuna so ku yi latti ya yi muku bulala?"
Suka diro daga kujerar suka nufo abincin, Sulaiman ya zauna tsakanin Hadiza da Muniba, kafadun su na gugar na juna. Ta sa murya ta ce,
"Fati!"

Ta fito sanye da hijab, da alama sallah ta idar, kallo daya Sulaiman ya yi mata ya dauke kansa, ya ci gaba da cin abincinsa. Daga can bakin kofa ta tsaya ba ta karaso cikin falon ba, son addini irin na Fati yana matukar burge Hadiza ba kadan ba.
Ta ce, "Taho mu ci abinci in kin idar da sallar".
Ta yatsina fuska ta ce, "Na ci tun dazu, Alti ta zuba mini".
Don jikinta ya yi sanyi da hararar da Sulaiman ke zabga mata, bayan ita ko da gida da mota aka hada ta dama ba za ta ci abinci da shi ba, don ta ki jinin mutum mai halin GIRMAN KAI.
To a ganin ta halin Sulaiman kenan, babu wanda ke ganin walwalar shi sai 'ya'yan shi da matarshi, duk ilimin da ya ke takama da shi a ganin ta girman kai ba hali ne da ya dace da likita ba. Ba ta san cewa shi ma bekenta yake gani ba.
Hadiza ta ce, "Don me ba za ki bari mu ci tare ba? Kada ki sake yin haka".
Fati ta ce, "Haka nan na saba, ba zan iya cin abinci da mutane ba".
Sulaiman ya balla mata harara, ya dago a sukwane.
"Su waye mutanen? Bakauya kawai, saboda ni ne ba za ki ci ba. Na yi kama da rubabben saurayin ki ne? Dube ta da Allah kullum da zumbulelen hijabi kamar takari, gara ma ki rage wannan zuhudun ko kya samu mashinshini, don duk mijin d aka bawa ke ko da sadaka ne an cuceshi wallahi wallahi, ko mata sun kare a duniya".
Fati ta harare shi ta zumbura baki kamar ta yi kuka, ta ce da Hadiza,
"Kina jin shi ko?"
Hadiza ta yi dariya ta ce, "Rabu da shi Fati na, ko shi din me zakiyi dashi? Allah na tuba ko mutuwa nayi ai ya yi miki tsufa, me za ki ci da dan late thirty? Sai yaro sabon jini kamar ki".
Daga Fati har Sulaiman, kalmar “mutuwa” da Hadiza ta ambatawa kanta, ta taba zuciyar su. Sulaiman ya tsame cokali daga plate ya aje gefe yana bin Hadiza da wata irin harara da ita kadai ta san ma'anar ta.
Ita kuwa Fati ba ta kara tofawa ba, ta koma daki tana cewa cikin ranta;
“kada Allah ya nuna min wannan ranar…., Yaya Hadiza sai dai ki yi min makoki, ba dai in yi miki ba”.

Kwana bakwai cif Sulaiman yana gida cikin iyalinsa bai je ofis ba, yana kula da lafiyar Hadizar sa. Ta fuskar shan magungunan ta a kan lokaci, hidimar ta da walwalar ta, tare da ba ta karfin gwiwa na karbar rayuwa a duk yadda tazo, yana nuna mata kaddarar da ta same ta ba ta shafi ko kankani na daga soyayyar da yake yi mata ba.
Ta yarda, ta amince Sulaiman mai son ta ne, kuma irin mazan da da wuya a samu kamar su a wannan zamanin wajen rike alkawarin soyayya da sanin darajar diya mace.
A 'yan kwanakin ta kara samun karfin jikinta, don haka ta kirkirowa kanta abubuwan debe kewa da dama, wadanda a da ba ta da lokacin su, kamar karatun jaridu da mujallu, ‘Internet browsing’ da kuma kasancewa full-time house-wife da 'ya'yanta suka kara shakuwa.
Abu na hudu da take ganin zai taimaka ainun wajen debe mata kewa shi ne, rubuta tarihin rayuwar ta a matsayin story-writing cikin harshen Hausa. Wanda take so ta sanyawa suna “YAKANAH!”

Da Sulaiman ya fahimci damuwar Hadiza ta ragu da 80%, sai ya samu kwarin gwiwa da jarumtakar fuskantar aikin sa. Ya koma aiki ranar monday cike da tausayin Hadiza, yana mai tuno lokutan zirga-zirgar su cikin asibitin don ceton rayukan al'umma, da matsalar ta mai magantuwa ce ba ya tsammanin in zai rasa duk abin da ya mallaka zai gaza wajen nema mata magani.

A wani bangaren kuma yana tunanin shawarar su Dr. Ruth ne da suka ce Hadiza za ta iya komawa aikin ta a haka. Da ya tuntube ta, ta nuna ba ta yi na'am da wannan shawarar ba, don ba ta yanke kauna da rahmar Ubangiji ba, za ta zauna a gida ta yi zaman aure, wanda a da ba ta yi ba. Ta ga shi kuma yaya yake? Wace irin riba ce a cikin sa, tunda ta yi aikin, ta ga ribarsa da rashin ribar sa?
A wautar Hadiza, tunda wannan lalura ta same ta shikenan Sulaiman ya daina sha'awar ta, wato ya daina mu'amalar aure da ita, tunda ta nakasa, ba ta da abin da za ta ja hankalin sa. Ba ta yi la'akari da cewa soyayyar ta a cikin jinin Sulaiman take ba, ba’a abun jan hankali ba.
Kwata-kwata sati biyu cur da fitowar ta daga asibiti, sai labari ya sauya, Sulaiman soyayya har ta fi ta baya, kamar wanda ya je ya kara yin course a kan (love-making) ga masu lalura. Watakila da da hali da ya tsaga kirjinsa ya sanya ta a ciki, mai yiwuwa sannan ne zai zamo (contented).
Sai da komai ya lafa ya fahimci Hadiza kuka take, ba kuma kukan komi take ba,
….kukan rashin yarda da kai ne.
Amma shi duk sai ya rikice, kukanta da hawayen ta ba karamin daga mai hankali ya yi ba.
Ya tarairayo ta ya dora a kan kirjin shi yna mai shafar bayanta, cikin sassanyar murya yake tambayar dalilin kukan,

"Did I hurt you Hadizahh?'”

Ta girgiza kai, cikin shesshekar kuka ta ce,
"Sulaiman kai ne???"
"In bani bane wane ne?"
Sai ta yarfar da hawaye da hannun daman ta, ta ce.

"Ni dai don Allah na rokeka, kayi min alfarma ka kara AURE!"

Sai ya janye jiki daga jikinta a hankali cikin mutuwar jiki da sagewar gwiwa,
"Kafin in baki amsa Hadiza, ko in bi umarnin ki, ina so in san mene ne dalilin ki na cewa hakan?"
Kai tsaye ta amsa.

"Saboda Hadizar da, ba ita ce yanzu ba, wannan nakasasshiya ce, ba ta cancanci wannan dimbin soyayyar ba".

Ya dade yana kallon kyakkyawar fuskarta a dan hasken asubahi da ya soma keto shara-sharan farin labulen dakin, kamin ya yi murmushin takaici ya zauna sosai ya bata baya.
"Hadiza tafiyar ki ce ta sa na aure ki? Ko ko yanga da kwarkwasa kika yi min na ji ina son ki?"
Ta girgiza kai, wasu tawagar hawaye na biyo idanunta.
"Babu ko daya. Amma son da nake maka Sulaiman, ba zai barni in kware ka ba, idan ka ci gaba da zama dani ni kadai, na kware ka; a matsayin ka na lafiyayye kuma cikakken namiji. Idan ka kara aure zan ji dadi, zuciyata za ta sake. Akalla ina da tabbacin baka cikin kwaruwa, amma yanzu sai nake ganin, na kware ka........ I'm nothing but a burden to you.....".
Ya daga mata hannu ya ce, "Ya isa, ya isa Hadiza...." Ya ma rasa me zai ce don takaici, sai ya karkada kai ya fita ya bar mata dakin.
Kwanaki uku suna kan wannan takaddamar. Hadiza ta dage ta ja tunga a kan bakanta, in ya yi fushi sai kuma ya sauko ya yi dariya don mamaki. Yau Hadiza ke neman kai dashi. Hadizar da ko kallonsa bata so mata su yi in ba bisa dole ba. Ba ya son duk wani abu da zai bata ranta a dai wannan lokacin da yake angwancewa bayan shan jinya ta lokaci mai tsaho, da kuma yin la'akari da halin da take ciki.
Don haka a rana ta biyar da ya ga ba zai iya jure wannan horon da ta tsiri yi mishi ba, don ba shi da juriyar a wannan fannin ta inda take samun weakness din sa kenan. Sai ya kama hannayen ta ya langabar da kai kamar karamin yaro, idanuwan nan sun juye sun rikide zuwa damuwa tsantsa.
Ya ce, "Hadiza na baki wuka da nama, ke ce mijin ke ce matar, ki zabo min duk yarinyar da kika ga ta dace dani, don bani da idon kallon wata diya mace, tun daga lokacin da Allah ya mallaka min ke......".
Ta cira kai a hankali ta dube shi, sai ya bata tausayi, don numfashi kanshi a wahale yake furzar da shi da sauri da sauri. Ganin yadda jidalin ta ya ramar da shi kwanaki biyar kacal, sai ta kara jin tausayin sa.
Amma jan ajin mu na mata, sai ta balla masa harara wadda in ka lura ba komi ne cikin ta ba face tsananin son mijinta da matsanancin kishin sa, ganin daga karshe din kuma ya sauko ya bi ra'ayinta kamar yadda take so.
Kamar ta yi kuka ta ce,
"Nice ma zan nemo maka matar? Ashe you are not serious…!"
Ta juyar da kai, sai ga hawaye sharrr! Sun zubo a kan kundukukin ta.
Kiris ya rage dariya ta kubce masa, amma ya danne kada ya kara laifi. A gicciye ba tare da ya dube ta ba ya ce, "Wai ko a cikin student din ward din ku, irin 'yan yara-yaran 'yammatan nan? Ko rikakkun 'yammatan likitoci irin su Dr. Surayyah".
Haushi ya kama Hadiza, don ta lura ya mai da abin zolaya. Ta yi shiru ba ta ba shi amsa ba.
Ya rungumota ta baya, ya dora kan shi a kafadun ta, yana sakin ajiyar zuciya mai nauyi. A sanyaye ya ce,
"Ko kin daina sona ne Hadizahh? Kike neman kai dani? A da ko kallo na wata ta yi, kallon da bai yi miki ba, sai kin kwana bakya yi min magana, amma yanzu duk kin daga hankalin ki wai in yi aure. Which means...... na gundire ki…. kina neman mataimakiya don ki huta…..
Ni ina ruwana da wasu kafafun ki tunda ba su nake aure ba? Inda nake aure zam-zam yake. Da aka yi accident din ma, kamar an kara masa armashi. Kafafu? Ni ba ina da su ba? Kuma ba ina daukar ki dasu ba? To meye damuwar ki?
In gaya miki gaskiya, ba zan iya sharing kaina ba, saboda ina da kyama, ba kowacce mace zan iya hada jiki da ita ba. Babu, ban taba ba, bana fata, kada ki tursasa ni, don ba zan iya ba, ba zan iya adalci ba. An ce kuma in ba za ku iya adalci ba, to ku zauna da daya.
Amma in kin gwammace ranar kiyama in tashi da shanyayyen barin jiki, all the same, sai in auri Surayyah! Kinga daga nan sai ku kara dankon zumunci........".

Ta ture shi da sauri, duk da jikinta ya yi sanyi da maganganun sa, ta tabbatar iya gaskiyar shi yake fadi, don shi bai fadin abin da ba haka bane a zuciyar shi. Don kaji dadi, ko don ya faranta maka.
“In haka ne kenan Sulaiman da gaske za ka iya auren Dr. Surayyah?" Sai hawaye suka zubo.
Magana take a zuci, ba ta san cewa a fili ta yi ba. Ya sauka daga gadon ya zauna dabas a kan kafet a gabanta, ya dauki hannu ya rafka uban tagumi, "Ni Sulaiman na shige su, duk yadda na yi, ban iya ba. Duk yadda nayi ban fita ba. To ki fadi yadda kike so, ni kuma mijin ta ce ne!"
Idon ta fal hawaye ta dube shi cikin ido, abin da bata yi sai rana ta kure,
"Ka gaya min gaskiya Sulaiman, Surayyah kake so?"
Ya yi murmushi ya shafi siraran lebbansa,
"Ya ya ba zan so ta ba tunda tana son ki, tana son 'ya'yana?"
"Ni ba wannan son nake nufi ba........".
Ya mike tsaye ya bata baya zai fice, "Koma wanne kike nufi shi ne, yarinyar nan rikicinki ya ishe ni, son ta nake na soyayya, soyet. Kin gane yanzu ko? Ki yi kuli-kulin kubura dani, ko ki yi ta kuka, har hawayenki ya kare........!!! "
Duk da kuka take ba ta san sanda ta yi dariya ba, ganin kuma ya dawo ya cafko ta yana son a sauya hirar da irin wacce ya fi so ayi, mai ma'ana da tsayawa a zuci, hadi da dimbin lada.
Ba ta da zabi (she have no choice) ban da ta rungumi mijinta, mai son ta, mai kaunar ta da gaskiya. Ta nuna mishi nashi son kawai ya sani, bai san nata ba. Duk abubuwan da take yi kan ya kara aure hasashe take, dauriya take don kada ta zamo mai son kanta, amma ita ma ta san ba za ta iya raba Sulaiman din ta da kowa ba.

***Da wannan Sulaiman ya kashe bakin Hadiza da maganar ya kara aure, saboda ita ta nakasa. Don ta san cewa zai yi zai auri Dr. Surayyah, ita kuma in da abin da ta tsana ya fito daga bakin sa, to bai wuce wannan furucin ba.
Surayyar ba ta watsar da Hadiza ba, ta kan zo in ta samu sararin aiki kuma suna yawan yin waya. Tayi-tayi Hadiza ta koma aiki in ya so sai Fati ta dinga kula da zirga-zirgar ta amma ta ki. A ganin ta ita Fatin zaman ta kenan ba za ta yi nata auren ba? Ko ko haka za ta karar da rayuwar ta wajen hidimar ta alhalin bata kai ga cimma komai a rayuwa ba?
Gara ita ta kai ga matakin da duk dan adam ke burin samu; tayi ilmi, tanada kwali, tayi aure, ta hayayyafa. Don ta zauna gida a halin yanzu babu komi. Amma Fati fa?

Ta ce, "Surayyah mune bamu gane ba, ko da yake mu namu aikin mai tushe ne daga addini. Amma ba abin da ya kai mace ta zauna a dakin mijinta ta yi biyayyar aure dadi da kwanciyar hankali, amma ina amfanin da auren ki da mijin ki da 'ya'yan

2 Comments On YAKANAH
avatar
rabiatu-2

1 year ago

Reply

Thanks

avatar
fatima-2-7-5

1 year ago

Reply

very nice book

Please Login or Register in order to submit comment