Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

asibitin.
Tun safe yau kanta ke damun ta da ciwo, gida kawai take so ta je ta huta. Amma dole sai ta fara ganin Sulaiman tukunna, akwai wasu kudi da take son karba a wajen sa za ta biya ta kai ma Fati tayi (registration).
Ta bude motar ta kenan ta zuba shirgin hannun ta, wata Nurse ta karaso da gudu tana haki tana kiran ta,
"Dr. Hadizah!"

Ta juya tana kallon ta har ta karaso. "…….Don Allah ki taimaka, wata ce aka kawo yanzun nan da alama ba za ta iya haihuwa da kanta ba, sai bleeding (zubar jini) take".
Ta kama kanta dake sarawa ta ce, "Lokacin tashina ya yi, yanzu Dr. Surayyah za ta zo.........”
Nurse din ta katse ta,
"Ki ceci rai kamar yadda kika saba, sakayyar ki na wajen Allah! Daga matar har Babyn suna cikin hadari, ga shi babu likita ko daya duk sun shiga meeting. Sannan Surayyah babu wanda ya san lokacin da za ta karaso".
Hadizah mai sanyin zuciya, matar ta kashe mata gwiwa da tausasan kalamanta. A take ta manta da ciwon kanta, ta rufe motar ta koma gun mai haihuwa.

Wannan halayyar ta ce da ta sha banbam da ta sauran likitocin labour room da kowa ke kuka dasu. Zuciyarta mai laushi ce, shi ya sa daga likitocin har Nurses zuwa labourers ke son ta, suke jin dadin aiki da ita. Hadiza is simple, komi nata a saukake yake.
Da gaske ne matar ba za ta iya haihuwa ba. Ta kai matuka wajen galabaita, ta soma ba ta dukkan taimakon da ya dace. Tana cikin aikin Dr. Surayyah ta iso, suka tsaya tare a kan matar nan.
Cikin dan lokaci sun yi nasarar fitar da jaririn amma ba rai. To alhamdulillahi an samu uwar. Tana zare safar hannunta ta ce da Surayyah,
"Ko da ban zo gobe ba, don Allah ki kular min da matar nan, haka kawai nake jin tausayin ta, dube ta yarinya karama, ga dukkan alamu ba ta isa auren ba suka yi mata. Allah ne ya taimake ta sun zo asibiti da wuri, da babu mamaki VVF ya same ta, wannan stitches da me yayi kama!".
Surayyah ta ce,
"Matsalar mutanen karkararmu kenan, ban san yaushe za su hankalta ba. A kullum fadakarwa ake a radio da talabijin, amma kamar ana kara zuga su. Allah ya kyauta. Balle ma me zai hana ki zuwa idan da rai da lafiya?"
Ta girgiza kai ta yi dan tsaki, ta ce,
"Bana jin dadi ne".
Surayyah ta ce,
"To Allah ya kawo sauki, a shafa min kan Munib":
Da haka suka yi sallama ta fita.

Da yake yau kowa a motar shi ya zo, wato itada Sulaiman, kasancewar lokutan ayyukan nasu sun banbanta. Akwai tazara sosai daga inda ta yi parking zuwa cardiology. Tana tukin tana duba agogon ‘gucci’ da ke daure a damtsen hannun ta na hagu. Yau Dr. Sulaiman aikin kwana gare shi, kudin Fati sun tsaya mata a rai, ga shi jakarta (is empty). Sannan is too late ta je banki ta fitar da kudi (lokacin ba ATM).

Ba al'adar ta ba ce tambayar Sulaiman kudi ba, saboda duk wata yana cika mata account ba tare da la'akari da albashin ta ba. Ita da kudin ta sai dai ta yiwa iyayen ta da 'yan uwanta hidima, amma duk wani nauyin rayuwar ta Sulaiman ya dauke shi.

Sau tari, ta kan ji kawayen ta da ba suyi aure ba irin su Dr. Surayyah, na tattaunawa a kan abinda ya hana su yin aure, su kan ce da ka yi aure shi ke nan ka shiga matsalar da namiji (wulakanci, rashin tsayawa ga mace daya, rowa da sauran su).
To ita dai yau shekaru biyar cif, ba ta ga ta inda nata da namijin ya kuskuro ta ba;

Matakin iliminsa bai sa shi ya zamo cikin kowanne irin aikin ashsha ba. Bai sa shi ya zamo mai tauye mata hakki ba, bai sa shi ya zamo mai girman kai a gare ta ba. Kullum tambayar shi,
"No problem Haddizah (babu matsala Hadiza)?"

Ta kan tambayi kanta, yadda neman mata ya zamo ado ga akasarin mazan wannan zamanin, masu matakin rayuwa irin nashi, mai ya sa ban da Sulaiman? Duk da kasancewar shi cikin rukunin mazan data ke da tabbacin suna bukatar mace fiye da daya. Ta yadda duk juriyar ta wani lokacin har ta kan nuna gazawar ta. Allah ya halicce ta da rauni a fannin auratayya. Ta taba tambayar shi a wani dare cewar,

"Don me ba zai kara aure ba?"

Sai ya kankame ta. Ya ce,
"Haddizah you are okey for me, in dai ba za ki yi min rowar ni'imtaccen jikin ki ba........." Ta ce,
"Baban Munib gani nake ina kwarar ka, you seem not o.k........"
A hanzarce ya ce,
"Ni na gaya miki?"
Ta girgiza kai. Ya ce,
"To kar ki kara yi min wannan zancen, silly girl kawai".

Ta yi murmushi, da tunanin ta ya zo nan. Dai-dai lokacin da ta iso cardiology, ta yi parking a inda aka tanada don adana motoci ta fito rike da jakarta. A nutse ta karasa (male ward) inda office din Sulaiman yake, ta tura kofar bayan ta murda tare da sallama.

Da alama aiki ya kacame masa, yana ta rubutu cikin file-file dake gabansa, ya daga kai yana duban ta duba na so da kauna, kuma na nutsuwa kamar yana son karanto ainihin damuwar da ke fuskarta.
Ya mike ya baro kujerar sa ya zauna a masangalin kujerar da ta zauna, wato ta ganawa da patients, ya zare mata gilashi, ya goge gumin dake tsakanin hancinta yace,
"Ya ya ne Dr. Hadiza, you look exhausted!" (Da alama kin gaji likis).
Ta lumshe zara-zaran gashin idonta ta ce, "Migraine ke damuna (ciwon kan barin kai guda)".
Ya kai lallausar tafin hannun shi goshinta, har sai da ta ji wani shock kamar yau ya fara taba ta. Ta yi saurin ture hannun sa, za ta yi magan Dr. Abdullahi ya turo kofar ya shigo, da sauri ya koma yana “excuse me plzzz.......!" Duk suka yi murmushi.
Ya ce,
"Kin sha magani?"
Ta girgiza kai,
"Ina so in je Karkasara ne".
"Amma lafiya na gaba da komai ko?'
Ta ce,
"Zan biya emergency in amsa kamin in wuce".
Ya kai hannu cikin rigarta wai zai ji temperature na jikin, ta yi saurin rike hannun ta ce, "Haba Sulaiman......."
Shi ma ya ce,
"Haba Hadizahhh….! Ni kadai zan kwana fa, babu dumin jikin ki Hadizah…..?"
Ta yi murmushi ta rusunar da kwayar idon ta cikin jin kunyar furucinsa, domin dai ita mace ce mai tsananin kamun kai a gaban mijinta da jin kunyar sa, kai ka ce basu haihu tare ba. Kullum girmansa da kunyarsa da kimarsa karuwa suke a idanun ta. Yace.

"Ke kwanta in duba ki, ban yarda dake ba, har yanzu ba ki cire wannan loop din bane (IUCD)". Ya soma laluben ta. Ta rike hannun shi ta marairaice tace,
"Wallahi na cire".Ya ce,
"To ko ke fa?
'Ya'ya nake so Haddizah, ki yi ta cika min gida dasu. Bamu da wani sauran abinyi a gaba banda rainonsu da tara su. Bani da harshen da zai iya bayyana hakikanin son da nake miki, you are my life Hadizah….., kada Allah ya rabamu.......". Ya shiga nuna mata son, practically (a aikace) irin yadda bai taba yi ba. Murmushi tayi. Ta ce,
"Sulaiman naka son ka sani, amma baka san nawa ba.
Sannan ban san yaya zan yi in fassara ba. All I can say (abinda zan iya cewa shine) ina son ka Sulaiman, son da nake yiwa raina......”.
Ya kai hannu ya toshe mata baki, wayar shi ta yi kara ya juya yana amsa call din amma bai saki hannunta ba. Ya gama ya kashe ya maida aljihun shi, yana yi mata wani sassanyan kallo ya ce,
"Ki yi min alfarma ki taya ni kwana ko hira ce ki dinga yi min ina aikin".
Ta ce, "Ka yi min afuwa Baban Munib, Fati zan kai ma kudi za ta yi registration gobe".
Da sauri Ya ce,
"Registration din Fati ya fini?"

Ta bude baki ta rufe da hannun ta, ta kasa cewa komai. Ya tsare ta da sexy eyes din sa, masu kassara ta, ba shiri ta sunkuyar da kai, don ba ta iya jure kallon idanuwan nan na Sulaiman din ta, masu rikirkita kowacce lafiyayyar diya mace, balle ita matarshi ta sunnah, data fi kowa sanin sirrinsa na zahiri da badini. A raunane ta ce,

"Ban so ka yi min wannan fahimtar ba".
"Sai wacce kike so in miki?"
"Irin wadda ka saba, understandable (ta fahimta)".
Ya yi murmushi ya mike daga kujerar ya koma mazaunin shi, duk ya shafa mata mayataccen kamshinsa na turaren ‘Chris Adams’. Nutsuwar matarshi da haibarta na burge shi, magana take cikin nutsuwa da haiba, kamar ba daga bakinta furucin ke fitowa ba, dauke da matsananciyar kauna a cikin kwayar idanun ta. Son ta da kaunar ta na kara kwarara a zuciyarsa, ya rasa inda zai sa kansa. Ya kama kanshi da hannuwan shi biyu.Ya ce,

"Hadiza bana so ki tafi ne, sai in ji ni lonely kamar maraya........!"

Ta ce,
"Alfarma za ka yi min Sulaiman, muna tare muddin rayuwar mu".
Ya mika mata hannu ta kama, ta isa gare shi. Ya miko mata kumatun shi ya ce, "Kiss me plzzzz……???".
Ta ji kunya sosai, ta boye kanta a kafadun shi, ita ba ta iya wannan keke-da-keken ba.
Ta ce,
"Kudin da zan kai mata za ka bani Sulaiman, ba kudi a waje na".
Ji yake in zai iya ba ta ranshi, to zai ba ta. Balle duniyar da abin da ke cikinta. Bai tambaye ta me za ta yi dasu ba, ko adadin da take so, ya kwaso duk abin da ke cikin aljihun shi ya zuba a jakar ta.

Allah sarki! Kamar ba za su rabu ba, a lokacin har duhun dare ya shigo, likitoci uku ne da ke karkashin sa suka kwankwasa suka turo kofar suka shigo. Dole Hadiza ta dau jakarta da lab-coat hadi da gilashinta ta fita, yana kara jaddada mata ta yi tuki da kula.

Dan banzan go slow ne ya tare ta a titi, ba ta isa gidansu ba sai tara da rabi, Maman su da suke kira Yaya, tana zaune a tsakar gida da rediyo a hannun ta tana sauraron Jakar Magori. Autan su Abdulyassar yana gefe yana hada motar kara.
Yaya Babar su Hadiza ba wata tsohuwa ba ce cancan, don irin auren wurin nan aka yi mata, shekarun ta arba'in kenan.
Hadiza ta yi sallama Yaya ta amsa, Abdulyassar ya watsar da kayan wasan shi da gudun shi ya kwaso ya rungume 'yar uwar shi, kasancewar ta mai jan su a jiki tare da nuna musu kauna. Yana tambayar ta ina Munib?

Daga can dakinta na 'yammatanci, wanda a yanzu ya zan mallakin Fati, sautin Abdurrahaman Sudais ke tashi a hankali cikin suratul Al-Imran, wannan ya tabbatar mata Hafiza FATIMA JA’AFAR na gida.
Ta samu gefen Yaya ta zauna, Yaya ta mike daga kwanciyar da ta yi bisa tabarma. Kai da ganin kyakkyawar fuskarta ka san ta ji dadin ganin diyar tata, ta ce,
"Da daddaren nan Hadiza? Shin ba Sulaiman ya hanaki tukin dare ba?”
Ta ce, "Wallahi Yaya, Dr. ne ya tare ni da magana, tun dazu na tashi, aikin kwana zaiyi shiyasa bamu zo tare ba, na kawo ma Fati kudin ne".
Ta ce, "Amma kin kyauta, don da ta yi ma Yayan ku maganar ta waya ya ce ba zai samu zuwa Kano wannan satin ba, ga shi baban ku kwanan nan kasuwar ta ja baya, kuma ta ce daga wannan satin za a rufe".
Ta ce, "Baba bai dawo bane?"
Yaya ta ce, "Ya dawo tun yamma, ya tafi dubiyar dan gidan Malam Abdu ne babur ya buge shi dazu".
Ta ce, "Allah ya sauwake, Fati na ciki ko".
Yaya ta ce, "Yanzu ta gama cin abinci ta shige ciki tana rehearsal, jibi za su yi musabakar jiha kuma ita za ta wakilci jihar Kano, kin san Fati ba daga nan ba".
Cikin alfahari da kanwar tata a zuciyarta, Hadiza ta tura kofar dakin cikin sallama ta danna kai, Fati ta diro daga gado ta rungume 'yar uwarta tana yi mata oyoyo.
Hadiza ta dubi Fati sama da kasa, yau sai ta ga ta zame mata cikakkiyar budurwa sosai. Ta kama baki.
"Fati girma haka?"
Fati ta yi murmushi, kumatunta duka suka lotsa gwanin sha'awa, wushiryarta ta fito siririya da ita.
Hadiza ta ce, "Wane course aka samu?"
Ta ce, "Course din da na nema ne (B.A Islamic Studies)".
Ta ce, "Masha Allah, da an je kuma sai a samo saurayi, irin wannan girma haka Fati?"
Ta ji kunya, ta boye fuskarta cikin tafukanta, ta ce,
"Ai hijabi zan ke zumbulawa irin mai hannun nan, kada a ce ana so na".
Hadiza ta ce me za ta yi ba dariya ba, duk girman Fati baka raba ta da wauta.
Ta kirgo kudi a jakarta naira dubu ishirin ta ba ta, Fati ta yi godiya ta ce,
"Allah Yaya Hadiza kwana biyu ba’a kawo su Munib ba".
Ta ce, "Makaranta ta boye su, amma da anyi hutu suna nan tafe insha-Allah". Sai sannan ne ta ga hakoran Fati. Ita shaida ce kan cewa ba abinda Fati ke so a duniya irin ‘ya’yanta Munib da Muniba.
Ta ce, "Ashe kuma musabaka za a yi Fati ba labari? To Allah Ya ba da sa'a".
Ta yi murmushi ta ce,
"Ameen".
Tana shirin fita Baban su na shigowa, ya ce,
"A'ah, manyan likitoci ne yau a gidan namu? Ina matas da abokin?"
Ta yi murmushi ta tsuguna har kasa ta gaida tsohon ta, ta ce, "Suna nan lafiya basu samu hutu bane, da sun samu za su zo".
Ya ce, "Kinga kafar nan tawa kwanan nan bana jin dadin ta, har na gaji da hadiyar magani".
Ta ce, "Wane magani ne Baba? Likita ne ya rubuta?"
Ya ce, "A'a, maganin ciwon kashi ne kawai nake saya a wajen masu talla".
Ta kama baki cikin gigicewa,

"Baba irin wadannan magungunan ba masu kyau bane, yawanci ma sun yi expiry don Allah ka daina sha. Baba meye amfanin mu nida Sulayman? Da har zaka sayawa kanka magani? Yanzu bari in rubuta maganin in bawa Fati ko Hamza su je su siyo".
Ya ce, "To na gode".

Ta baro Karkasara karfe goma dai-dai na dare, dauke da tazbihi a bakinta domin ba abu ne da ta ke so ko ta saba ba, abu ne da mijinta ke matukar ki, wato (night driving) tukin dare.
Ta biyo ta titin Court Road ta hawo titin Gandu, ta yi kwana ta hau titin B.U.K Road. Ta iso Kabuga ta dau titin sabuwar jami'ar Bayero, wanda zai sadata da Janbulo. Babu wadatar motoci a titin.
Daga gefen ta wayarta ta yi kara, sunan Sweetypie ya soma yawo a screen din. Ta yi murmushi ta mika hannun damanta ta dauka, ta rike sitiyari da hannun hagu cikin sanyin sauti ya ce,

"Yaya dai D.Z? Hope for now kina gida???"
Ta yi ajiyar zuciya cikin karyayyar murya ta ce,
"Na kusa dai, ina kan hanya.........".

Iya abin da ya ji ke nan sai wata irin kara da ta fi kama da fashewar taya, ya yi kira "Hello!.....Hello....Hadddizah!" Amma ba amsa.
Motar ta hantsila ta shige karkashin wata trailer da ke cike da buhunhunan abinci, duk da kokarin da direban ya yi wajen kauce mata hakan bai samu ba, motocin da ke gabansu da bayan su duk suka yi birki cikin salati, tsirarun mutanen da ke gefen titi suka runtumo don kawo agaji.

*******Ta hanyar katin shaida (ID Card) jami'an tsaro suka gano ko wacece Hadiza. Don haka ba su sha wahalar samun nombar wayar mijinta ba, wanda ke can cikin gigicewa. Nan asibitin aka taho da ita cikin jinni kaca-kaca, rai a hannun Allah.

Likitoci biyar ne a kan Hadiza, sai Sulaiman cikon na shida, wanda ya manta wani abu wai shi karatun likita, komawa ya yi tamkar bai taba halarta aji ba. Shi da Hadiza da ke kwance babu maraba, illa shi a tsaye yake, sai dai jingine da garu (bango), wanda ya taimaka masa wajen daukar nauyin gangar jikinsa. A lokacin da za ka tsaga ba za ka samu ko digon jini a cikin jikinsa ba.
Tashin hankali ba a sa maka rana! Haka wannan mummunan labari ya iske iyayen Hadiza da 'yan uwanta ta hanyar Dr. Surayyah.
A daren Mukhtar ya baro Kaduna zuwa Kano, a daren suka dungumo baki dayan su suka taho, sai dai basu samu ganin Hadiza ba. Har zuwa lokacin likitoci na tsananta bincike a kanta, haka suka kwana a barandar asibiti cikin tsananin sanyi. Amma babu mai jinsa. Fati sai kuka take kamar ranta zai fita tunda suka taho, Yaya na lallashin ta.
Sai washegari da safe result din Hadiza ya iske Sulaiman da iyayen ta, bayan raunuka da ba za su kirgu ba, babu karaya ko daya a jikinta. Babban tashin hankalin wanda ya girgiza kowa shi ne, jijiyar bayanta wadda ta hada daga wuya zuwa bayan ta (spinal cord) ta tsinke, wanda ke nufin Hadiza ba za ta kara iya mikewa ba, ba za ta kara iya tafiya ba a gaba daya sauran rayuwar ta.

Dr. Sulaiman ya mike tsaye ya nuna Dr. Samson da dan yatsa, "Ka san abin da kake fada, ban san cewa baka san aikin ka ba sai yau. Kuma shi ke nan daga yin accident sai ka nakasta min mata? Uwarka ce ba za ta kara iya mikewa ba, amma ba Hadiza ba......"
Kai da ganin yadda yake maganar, kwayar idanun shi a juye, ka san ba a hayyacin sa yake wannan furucin ba.
Samson ya sunkuyar da kai, duka likitocin babu wanda ya kara magana. Tausayi ne fal a zukatan su. Dr. Hadiza abar so ce ga kowa, suna jin dadin tarayya da ita, marasa lafiyan ta na yaba kokarin ta. Wannan accident da ya yi mata karan tsaye da kuruciyar ta, ya zamo nakasu ga dimbin taimakon da take bai ma al'umma.

Malam Ja'afar mahaifin Hadiza da ke gefe shi ya soma tausar Sulaiman da kalami masu dadi da sanya imani, yana tuna masa muhimmancin yarda da kaddara.
Sulaiman ya yi shiru, ya koma ya zauna a kujerar sa. Ya kifa kai cikin cinyoyin sa, amma har yanzu ya kasa yarda da abin da kunnuwan sa suka jiye masa.
Wai Hadiza ta zama sai dai a kwantar a tayar ba za ta kara amfanuwa ba, ba za ta kara moruwa ba. Balle ta amfanawa kanta komai. Ita da 'ya'yanta da mijinta sai dai gani da ido. Abin da suke gani kullum yana faruwa da al'umma yau Allah As-Samadu ya juyo da shi kansu. Dimbin ilimin su, karfin aljihunsu da tunanin su babu abin da zai iya a kai, domin ita wannan jijiya ba ta doruwa. Sai ya fashe da kuka.

Malam Ja'afar ya mike daga kujerar sa ya isa ga Sulaiman, ya mikar da shi tsaye ya rungume a jikinsa.
"Haba Sule! Kamar ba namiji ba? Namijin ma, likitan likitoci. Ba ka yi kuka a kan sauran al'umma da kuke kwana da yini kuna fama dasu ba sai a kan matar ka kadai? Su Allah ba ya son su ne yake dora musu lalura? Allah da ya halicci Hadiza ya fi mu son ta, shi kadai ya san dalilin sa na hukunta hakan a gare ta.
Yau in Hadiza mutuwa ta yi me zamu iya ban da mu yi mata addu'a? Amma tana raye, a kalla muna ganin ta muna jin dadi, ka yi tawakkali ka barwa Allah, ka zamo mai YAKANAH, sai ya yi maka tukuici da abin da baka zata ba.
Kai za ka ba ta kwarin gwiwa, ta rungumi kaddarar da Allah ya dora mata. Amma idan ka fita karaya, wane ne zai karfafa wani?"

Ya mika hannu yana share masa hawayen da suka kasa daina ambaliya daga kyawawan idanun sa.
Dr. Ruth ta yi gyaran murya, ta dubi Dr. Sulaiman ta sunkuyar da kanta, kana ta dago ta ce,
"Ina ganin idan Dr. Hadiza ta ji sauki, raunikan jikinta sun warke, za ta iya ci gaba da aikinta ta hanyar amfani da wheel chair, idan har za’a samu wanda zai juri kawo ta da mai da ita".
Kiris! Ya rage ya lailayo ashar ya antaya mata, ko ya faska mata mari, amma da ya tuna Malam na wajen sai ya balla mata harara, a zuciyar shi ya ce,
"Uwar ki za a sa a wheel chair ba uwar Munib ba!!!".

Samson ya ce,
"Shawarar Ruth abar dubawa ce, hakan zai debe mata kewa fiye da ta zauna a gida ba abin da take yi. Ko ba don zuwa aiki ba dole za a nema mata wheel chair ko da a gida ne".
Ba shi da abin cewa, don duk likitocin abin da suke cewa kenan. (They cannot afford to lose HADIZA in the Nigerian medical practition). Malam dai baya ji saboda cikin harshen turanci suke maganar. Shikadai ne ba likita ba a ofishin. Wannan na jefo tasa wannan na jefo tasa kai kace a gaban ofishin Barrack Obama kake. Da zancen ya ishi Sulaiman sai ya tashi ya fita cike da jin zafinsu. Ta amfanin ta ga Nigeria da asibitin su suke, bata gurguncewar rayuwarta bakidaya ba. Ya nufi ICU inda aka kwantar da Hadizah.

A bayan kofa ya tsaya ya rabe, yana leken ta, ya kasa karasawa, ya kura mata ido yana ta'ajjibin yadda kwana daya rak! Allah ya jirkitar da kyakkyawar fuskar Hadiza, ko ina a jikinta rauni ne, nan plasta can plasta. Barci take sadidan, sai dai da gani ba na Allah da Annabi bane (na karfin allurai ne).
Rabin fuskarta nade cikin bandeji, wadda ta kumbura ta yi sumtum kamar an hura (baloon). A hankali ya soma taku ya isa ga gadon da take kwance, ya ja kujera ya zauna dai-dai fuskarta yana fuskantar ta.
Ya kai hannu bisa goshin ta wanda ke nade cikin bandeji, kamar an ce da ita bude idon ki. Suka yi ido hudu da Sulaiman din ta, ta dubi dakin ta dubi kanta, ta tabbatar a kwance take a gadon asibiti. Ta maido duban ta ga Sulaiman wanda ke binta da ido da zuciya, ta ce cikin kankanuwar murya,
"Sulayman Accident na yi ko?"
Ya daga mata kai. Ta dora hannunta mai rangwamen raunika bisa nashi dake goshin ta, ta sauke, don ji take kamar ya dora mata Dala da Gwauron Dutse.

Ta yunkura da niyyar ta tashi zaune amma ta ji kamar ba jikinta ba, ya mike ya kama ta ya mikar da ita zaune. Ya janyo pillow ya tusa mata don ta ji dadin jinginar, ya tabbatar dai da gaske ne Hadizar shi ta zama disabled (nakasasshiya), sai jikinsa ya soma kyarma.

Duk dauriyar da yake yi abin ya ci tura, da sauri ya rungume ta, cikin shesshekar kuka ya ce,

"Cikin kowanne hali, INA SON KI HADIZAH!"

Kuka suke dukkanin su babu mai rarrashin wani, don ita Hadiza ta tabbatar abin da zai sa Sulaiman kuka, to tabbata ba karamin abu bane, wannan shi ya gigita ta, ita ma ta fashe da kuka.

Fati a gaba, Yaya, Malam, Hamza da babban Yayan su Mukhtar suka shigo, daga Hadiza har Sulaiman babu wanda ya san da shigowar su, shessehekar kukan Fati ne ya ankarar da Sulaiman cewa akwai mutane a dakin.
A hankali ya zare jikinsa daga na Hadiza ya juya ya fita daga dakin ba tare da ya iya hada ido da surukansa ba.
Malam Ja'afar ya karasa jikin gadon Hadiza ya kama hannun ta inda babu ciwo, ya ce,
"Ki yi tawakkali Hadiza, ki zamo mai YAKANAH a dukkanin al'amuran ki, ki zamo mai godiya ga Allah a duk yanayin da kika tsinci kanki. Wannan ba shi ne karshen rayuwar ba, yarda da kaddara dole ne ga duk musulmin kwarai".
Cikin kuka mai tsanani ta ce, "Na ji Baba, amma don Allah ku fada min me ke faruwa dani? Sulaiman bai gaya min komi ba, sai kuka yake yi, kukan shi ya daga min hankali, ku fidda ni a duhu. Wani abu ne ya faru dani?"
Malam ya sa habar babbar rigar sa ya share hawayen da suka ciko mishi ido cikin dabara wai kada Hadiza ta ga shi ma kukan yake kamar Sulayman din, amma ta ganin. Hadiza ta musamman ce ko a cikin 'ya'yansa, yana son ta son da bai yiwa su Mukhtar, ta kama duka hidimar gidansa ta rungume, kafin Yayanta Muktar ya Kawo sau daya ta kawo sau goma. Ta sha cewa don su take aiki. Ganin Babanta yana kuka wiwi sai ta kara tsananta kukan ta.

Cikin tausasawa Mukhtar ya ce,

"Cool down Hadiza,

2 Comments On YAKANAH
avatar
rabiatu-2

1 year ago

Reply

Thanks

avatar
fatima-2-7-5

1 year ago

Reply

very nice book

Please Login or Register in order to submit comment