Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yana nuna masa yadda ciwon ya ci karfin ta a yanzu, da irin taimakon da ya ba ta. Shi kan sa Bunza sai da ya yi hawaye balle gogan, wanda gudun jini ya katse a jijiyoyin jikinsa.

****









Karfe shida na safe Dr. Surayyah ta fito da jaririyar da aka cirowa Hadiza, kamar ta daya da Baban ta kamar ya yi kaki ya tofar, har duhun kalar nashi ne.
A lokacin ne jama'ar gidan su Hadiza suka iso, Dr. Surayyah ta sanar da su. Fati karfe bakwai na safe ta iso asibitin, ta baro yaran da Alti ta zo a (keke-napep). Dai-dai lokacin da aka turo Hadiza za a mai da ita ICU, ya yi dai-dai da sanda Surayyah ta mika mishi jaririyar ya ki amsa, sai Fati ce ta amsa.
Za a wuce da Hadiza ta rike hannun sister Magajiya ta rada mata cikin nishi,
"Ina son yin magana da su…..".
Don haka sister ta dakata. Sulaiman da Fati suka garzayo gareta, kowanne ya fita hayyacinsa. Fati rungume da jaririya tsantsan tana ta tsala ihu.
Itama Fatin Kukan take. Hadiza ta runtse ido hawaye na zirara, ta ce,
"Fati ina alkawarin mu?"
Cikin Kuka ta ce,
"Yana nan Yaya Hadiza".
Ta kama hannun Sulaiman ta hada da na Fati, duk su Malam Ja'afar na kallo, ta ce,
"Fati har da shi a alkawarin fa.........."
Ta yi sharbe ta yarfar da majina da hawaye ta ce, "In kula da shi kika ce? Yaya Hadiza ai shi babba ne?”

"Babba ba ya bukatar kulawa Fati……?"
Ta ce,
"Ban sani ba".
Ta ce,
"To yana bukata, shi ma kamar Munib ne, bambancinsu shine shi Munib kulawar UWA yake nema, shi kuwa Sulaiman kulawar MATA yake nema..........".
Ta yi murmushi ta runtse idonta, cikin azabar da take dandana a kwakwalwarta. Sulaiman ya russuna ya sumbaci goshinta, hancinta, bakinta da idanunta. "You will get well soon Hadizah……, bana bukatar kulawar kowa sai taki, in ba taki ba na yafe, zafin ciwo yake sa ki yin irin wannan magana.........".
Ta girgiza kai tana kara manne hannun su cikin nata ta ce,

"Sulaiman-Fati............".

Dr. Bunza ya karaso ya tura gadon da kanshi yana ta yiwa sister Magajiya fada. Yaya ta karaso ta karbi 'yar da ke hannun Fati ganin tana neman kwala ta da kasa.

Dr. Sulaiman ya mai da hannun shi cikin aljihu, yana so ya yi kuka amma idanun sun bushe kamar soyayyar gyada marau-marau. Sai Malam Ja'afar ya iso gare shi ya kamo hannun sa suka zauna tare, yana cewa,
"Karbi 'yar ka sa mata albarka".
Amma Sulaiman ya ki, sai kirjin shi da ke ta kai kawo kamar zuciyar ta ballo allon kirjinsa ta fito.
Ana shigar da ita cikin computer don a yi hoton kwakwalwar ta kamin likitocin su san me za su yi a kai, ta soma wata irin jijjiga mai ban tsoro, kamin ta yi salati rai bakon duniya ya yi halinsa.

"Allah ya ji kan Dr. Hadizah!"

Abin da dukkanin likitocin suka furta kenan, a lokaci guda suna share ambaliyar hawaye daga idanuwan su, tare da kai hannu su rufe mata idanun ta.

****
10/15/21, 11:47 AM - Buhainat: Washegari da yamma sai ga Inna ta kara dawowa, Dr. Sulaiman ya kawo ta, Hamza da Abdulyassar suka shigowa Fati da katon na madarar SMA, katon na diapers da himilin shopping na kayan masarufi da kayan biskit da choculate da su Indomie wanda su Munib ke zuwa makaranta da su. Ta adana kowanne a inda ya dace, Inna ta ce ya je sai dare ya zo ya dauke ta.
A lokacin Malam Ja'afar ya iso da shi da Inna da Yaya suka kule a daki, suka sakayo kofa, me suka ce me suka ce oho, sun dai dade suna magana kafin ya dawo ya dauki Inna su wuce, kasancewar a gobe zata koma Bakori, ya biya ta Jifatu ya yi mata sayayya mai yawa kamar yadda ya saba, ita da Malam da sauran kannen shi, suka wuce gidan sa.
Inna ta tuka mishi tuwon semovita da miyar ganye ya ci, ta takura mishi ya bude wayoyinsa. Yana budewa sakonnin ta'aziyya daga likitoci 'yan uwansa da sauran abokan arziki ya soma tittidowa cikin wayar. Sannan ana neman shi a ofishin (Chief Medical Director) na AKTH ranar litinin.
Don haka yana kai Inna Bakori suka gaisa da mahaifin shi bai tsaya ba. Da zai tafi Inna ta ce,
"Ni kuwa akwai wata magana muhimmiya da nake so mu yi, ga shi na ga alamar kana sauri".
Ya ce,
"Gaskiya kam ina cikin sauri, sai ko idan na dawo". Ta ce,
"Shi ke nan Allah ya kiyaye hanya, ya kara maka hakuri da YAKANAH, ya shige maka gaba a kan al'amuran ka, ya yi maka musayan alheri".

Har ransa ya ji dadin addu'o'in Inna, wata nutsuwa ta kara shigar shi, son mahaifiyar shi ya kara shigar shi. Ta ce,
"Ina so zuwa sanda za ka dawo in ga canji, kamar yadda ka yi min alkawari, in ganka a likitanka ba mai sunan Malam ba".
Murmushi ya yi, wanda rabon shi da yin shi tun wani karni can da ya shude.

****










Litinin, ya isa ofishin CMD, sun dade suna tattunawa a kan wani aiki na dashen zuciya da za a yiwa ministan lafiya. Yana daya daga cikin likitocin da zasu gabatar da aikin. Ya koma office dinsa ya daidaita komai ya ci gaba da aikin sa, cikin karfin zuciya da neman rinjaye a kanta.

Sai ya zamto yana jin dadin aikin sosai, don yana debe mishi kewa, yana hana shi zama shiru har maraicin matarsa ya gallabe shi. Ya tarar da tulin ayyuka da yawa, don haka ya zamo busy a satin gaba daya.
Ranar alhamis ya saci jiki ya je yayowa 'ya'yan shi siyayya ya biya ta makarantar su ya gansu, lokacin da aka fito cin abinci, a karkashin wani benci ya zauna ya rungume su suna ta labari, ya bude ‘kit-kat’ yana basu suna ci suna yi mishi hira. Tun suna damuwa da rashin Momin su har sun hakura sun dangana sun daina tambayar ta.
Munib ya ce,
"Daddy ba ka zo (prize giving) din mu ba, kowa Baban shi ya zo banda mu".
Ya kama kunnen shi cikin nunawa yaron amsa laifin sa, ya ce,
"I am very very sorry..... aiki ne ya yi min yawa. To wa ya kawo ku?"
Suka ce, "Aunty Fati, ta yi mana kwalliya ta kawo mu".
Ya ce,
"Aunty Fati ta kyauta!".
Suka yi murmushi. Ya ce,
"Next year ba zan sake ba".
Aka kada kararrawar komawa aji, suka fella da gudu suka nufi ajinsu, ya bisu da kallo yana murmushi cike da kewar su.

Hakan yake yi duk sanda ya samu sararin aiki, ya daina zuwa gidan don kar ya ga Fati, tana tuno mishi da wasu al'amura msu yawa a kan Hadiza. Sannan ba ya son wata alaka take shiga tsakanin su, shi ma kuma bai san mai ya sa ba, ya danganta hakan da rashin haduwar jininsu na tuntuni.

Ita kuma ta danganta hakan da wulakanci da raina mata wayo, yana ganin ta kamar ba ta san abin da take yi ba, bayan in da wanda ya san ciwon kansa a duniya to ita ce.
Sai dai tsarin rayuwar su da ya banbanta, kowa da irin nashi tsarin rayuwar, sun dauki rayuwar bature mai zafi sun yafa shi da Hadiza, ita kuwa Lahira ta sani ita take wa tanadi, shiyasa yake mata wani gani-gani, don haka ita ma ta yi kamar ba ta san yana zuwa makarantar yaran ba, bayan kuma suna gaya mata.
10/15/21, 11:47 AM - Buhainat: Ana i gobe sadakar arba'in din Hadizah, Malam Sulaiman, Inna Halima da Baffanin Sulaiman guda biyu, Malam Surajo da Alhaji Umar suka iso gidan Sulaiman a Kano, a daren suka bukaci ya kai su Karkasara. In da ya ajiye su da daddare ya wuce asibiti, da cewar zai dawo ya dauke su.

Manya sun kule a falon Baban Hadiza, wato Malam Ja'afar suna magana ta gemu-da-gemu har da Yaya da Inna. Yaya ta ce,

"Ni bana jin Fati sai shi Sulaiman, anya zai yi na'am da al'amarin nan?"

Malam Sulaiman ya yi murmushi ya ce, "Kune baku san Sule ba har yanzu, yana da wani hali tun yana yaro, abin da zai so sai ya fara kin shi tukunna.
Ga yadda mahaifiyar shi take bani labari, babu jituwa ko ya ya tsakanin sa da Fati, ita kuma ta kama kanta ba ta shiga shirgin shi. Mu dai burin mu ku bamu hadin kai, Allah ya gani muna son zuri'ar gidan nan, muna son zumunci ya ci gaba da gudana kamar yadda aka faro.
Fati ita ta fi cancanta da ta rike 'ya'yan 'yar uwar ta, don a wannan zamanin da wuya a samu macen da za ta rike maka 'ya'ya har uku duk son da take maka. Sannan mun yaba da hankali da tsarin rayuwar Fati, muna sa ran yara za su tashi da kyakkyawar tarbiyya har zuwa girman su.
Fati ba za ta dauwama a gida tana bautar 'ya'yan 'yar uwarta ba, dole watarana za ta yi aure. Ranar da hakan ta faru ya ya Sulaiman zai yi da yaran nan?
Ga shi suna karatun su mai kyau a nan balle mu tafi dasu Bakori. Fati ita ta fi cancanta da ta maye gurbin 'yar uwarta a zuciyar Sulaiman.
Don haka muna neman hadin kanku, yardar ku da amincewar ku Malam Ja'afar. Shin an bamu Fati? Da karfin mu muka zo, da sadakin mu a hannu, gobe muke so bayan an shafa addu'ar Hadiza a daura auren Sulaiman da Fatima".
Malam Ja'afar ya ce,
"Tun kafin ku yi wannan tunanin na riga ku yin sa, kun dai riga ni furtawa ne. Tabbas duk matar da Sule zai aura nan gaba ta rike mishi marayun shi ba kamar Fati ba, wadda ta san ciwon su, tasan ciwon 'yar uwarta.
Sannan Hadizah ta yi wani abu a ranar da za ta koma ga mahaliccinta, wanda ya tsaya min a rai kwarai, ta kama hannun Sulaiman ta hada da na Fati, sai dai ban ji me suke cewa ba.
Fati yarinya ce mai biyayya, ba za ta tsallake umarnin mu ba, amma kamar yadda Sa'adatu ta ce ne, da kyar idan shi Sulaiman din zai amince. Sannan ya wuce matsayin da za a ce za a yi mishi aure ba tare da sanin shi ba".
Alhaji Umar ya ce, "Ku bar wannan a hannun mu, kamar yadda Fati take mai biyayya, shi ma Sulaiman mai biyayya ne, iyayen shi basu taba saka mishi kara ya tsallake ba. Ina da yakinin zai yi biyayya ga mahaifin shi, kuma a daren nan zamu sanar da shi ba sai gobe ba.
Ga sadaki naira dubu ishirin ga goro, daga aljihuna ni waliyyin sa. Jikina ya bani alheri ne zamu kulla, don irin wannan auren na son zuciyar iyaye ba karamar falala ake samu a cikin shi ba".

Kowa ya jinjina kai. Yaya ta ce,

"Nima a daren nan zan sanar da ita insha Allahu".

Da haka taron ya tashi, ya yi dai-dai da sallamar Sulaiman a falon, dukkanin su suka amsa fuskar kowannen su cike da walwala da annuri.
Malam ya ce,
"Faduwa ta zo dai-dai da zama kenan, ita ma Fatiman a kirawo ta".
Yaya ta tashi ta fita don kiran Fati.

Tana yiwa su Munib shimfidar kwanciya goye da Nana, Yaya ta yane labulen dakin ta ce,
"Fati kin kwanta ne?"
"A'a, ina harama dai".
"To biyo ni dakin Malam yana son magana da ke".
Ta sauke goyon ta zurma hijabin ta, ta bi bayan Yaya har dakin Malam.
Ta sha mamakin ganin taron dakin har da Baban Munib, wanda ke can sunkuye da kai a gefe. Ta yi sallama cikin sassanyar muryar ta dukkan su suka amsa, ban da Sulaiman wanda ya fara shan jinin jikinsa kan wannan taron domin shi aka yi. Jikinsa ya yi sanyi, gaban shi ya soma faduwa, haka nan gwiwoyinsa ya jisu kamar an rarrade su da murfin kwano.
Ta samu gefen Inna ta zauna, ita ma jikinta ya soma kyarma don ba ta son a tirke ta a cikin mutane.
Iyayen dai na duban su suna nazarin kowannen su, sun fahimci dukkan su a firgice suke, amma firgitar ta fi karfi ga Sulaiman. Wannan taro na mene ne? Malam Sulaiman baya shiga kankanuwar magana.
Sai da suka tabbatar sun dan samu nutsuwa sannan Malam Sulaiman ya dubi dansa ya ce,
"Mai sunana wani abin alheri ne za mu yi maka, da fatan za ka karba hannu bibbiyu".
Bai yi magana ba, amma ya dago ya dubi mahaifin sa. Ya ci gaba da cewa,
"Muna kara yi muku ta'aziyya, sannan muna so ku sani cewa, duk abin da Allah ya tsara akwai hikimar yin hakan a cikin sa.
Mun zauna mun yi tunani, mun yi shawara mun yanke cewa, Fati za ta maye gurbin 'yar uwarta a gare ka, ku ci gaba da raino da tarbiyyar 'ya'yanku kamar yadda mahaifiyar su ta fara yi musu, kuma 'yar uwarta ta karbe ta.
Allah ya riga ya hada mu, zuri'a ta hada mu. Don haka Sulaiman bana son ka da wani aure in dai ba jinin gidan nan ne ya kare ba. Za mu yi alfahari daku idan kuka taushi zuciyoyin ku kuka yi mana biyayya. Allah zai nunawa Hadiza har cikin kabarin ta cewa, ke Fati kin rungumi iyalinta, kin rungumi mijinta baki bar rashin ta a rayuwa ya tagayyara su ba.
Sannan kai Sulaiman Hadiza za ta yi farin ciki idan har ya zamto ka rungumi amanar rayuwar 'yar uwarta ta hanyar aure, wadda kowa shaida ne kan bata da kamarta, muna neman hadin kan ku, shin za mu samu Fatima da Sulaimanu?"

Da a ce Malam Sulaiman ya lura, da ya ga irin jibin (zufar) da ke ambaliya a fuska da jikin Sulaiman, yayin da gudun jini ya katse a jikin Fati, idanuwanta suka juye suka kada suka yi jazur, hanjin cikinta ya dunkule waje daya ko dan yatsanta ta kasa dagawa balle ta motsa bakinta. Tana addu'a cikin zuciyarta idan mafarki take Ubangiji Allah subhana ya yi gaggawar farkar da ita.
Sai dai a bangaren shi Sulaiman, ya so a ce shi da iyayen shi ne kadai su kai wannan maganar, da a take zai ce dasu idan kasa da sama za ta hadu bai amince ba. To an ce wai ko mutuwa tana kunyar iyaye, balle iyayen Hadiza? Ya zai yi ya iya ya budi baki a gabansu ya ce baya son jinin Hadiza?
Shi tunda ya rasa Hadiza bai kara tunanin nan gaba zai kara yin aure ba, bai kara tunanin wai yana da future ba, balle ya yi tunanin yin aure. Kuma a rasa wadda za a aura masa sai wannan yarinyar da bai san a matsayin da ya ajiye ta a zuciyar sa ba.
Duk da yadda take hidima da 'ya'yansa, Fati ba ta taba burge shi ba, Allah bai sa masa kaunar ta a zuciyar sa ba, sannan kuma wai auren ma daga yin arba'in din Hadiza? Sannan da shakikiyar ta?
Fati ba ta taba burge shi ba balle ya so ta, bai taba tunanin irin ta a matsayin matar shi ba. Ya ya ma za ai wannan kidahumar yarinyar 'yar sakandire ta maye gurbin Hadiza? Ta ya ya mahaifan shi suke tunanin zai iya rayuwa da kanwar Hadiza? Ya yada girman sa ya yi mu'amalar aure da ita?
Kwarai ya fahimci abin da Hadiza ke nufi tsakanin shi da Fati a ranar da Allah zai dauki ranta, amma (he is sorry to say) ba zai iya cikawa Hadiza burinta ba.
In don 'ya'yan shi ne a ba shi abinsa ya rike ko ya bai wa Inna, karatun nasu a birnin Kano ba dole bane, ba sai an makala mishi auren da bai san ya ya zai yi da shi ba.
Malam Ja'afar ya ce,
"Duk kun yi shiru, ko da yake shirun alamar amincewa ne, To ku tashi ku je Allah ya yi muku albarka, dama mun sanar daku ne kada sai gobe ku ji an daura aure ku ce ba a sanar daku ba. In kuma akwai mai magana to ya yi, a shirye muke da mu bai wa kowannen ku hakkin sa".
Inna tana murmushi ta dubi Sulaiman ta ce,
"Ni na san mai sunan Malam ba zai ki abin da muke so ba".
Jikinsa ya yi sanyi kalau, ya nemi duk wata hujja da zai bayar ya neme ta ya rasa. Zuwa lokacin Fati ta mike za ta fita, juwa na kwasar ta, da dafa bango ta samu ta bar falon.
Ta yi dakinta ta dauki 'yar jaririyar ta wadda ke ta tsala kuka a dalilin ta manta ba ta sa mata gidan sauro ba ta fita, sauro ya hana mata barci.

Shi ma bai yi magana ba yana jin su suna ta kida suna rawar su na addu'o'i, sa albarka da fatan alheri a gare shi. Gwiwa a salube ya fito jikin mota ya baro su suna ta sallama.
10/15/21, 11:47 AM - Buhainat: Yaya ta yi murmushi irin na manya wadanda suka san cewa ciwon 'ya mace na 'ya mace ne, sarai ta gane abin da Fati ke nufi; Hadiza 'yar gayu ce, kuma wadda ta gogu cikin zuzzurfan ilimin boko, ita kuwa 'yar Islamiyyah ce, wadda Allah da Annabi sune kawai a gabanta, wato dai ita 'yar Arabiyyah ce wadda ta horu ta goge cikin ilmummukan addini daban-daban da fadin Allah da manzonsa. Wadanda 'yan bokon irin su Sulaiman ke wa kallon 'yan kauye, wannan banbancin a farrake yake.
Ta ce,
"Fati kowacce mace da kika gani da kissarta aka haife ta, sannan kowacce da yadda Allah ya halicce ta. Sai dai ra'ayi da akida sun banbanta. Amma fa duk sunan su daya (MACE), kuma abin da ke jikin wannan shi ne a jikin waccan, ba wadda ta fi wata a matantakar sai dai ko kazama da mai tsafta.
Fati ke mai tsafta ce, har a makaranta tun daga firamare har sakandire an fahimci tsaftar ki an kuma sha baki kyauta a kanta. Wannan kadai kika rike jigo ne a gidan aure, kuma ya ishe ki ki yaki zuciyar kowanne da namiji ba Sulaiman kadai ba.
Kamar yadda kika ce baki da abin da za ki burge Sulaiman sai in ce a'a, Fati kina da shi, HANKALI da sanin CIWON KAI sune manyan halayen da ke burge namijin da ya san ciwon kansa irin Sulaiman ba kyale-kyalen mace ba.........".
Fati ta dago ido tana kallon mahaifiyar ta,
"Yaya kina nufin Baban Munib bai fi karfina ba?"
Yaya ta yi murmushi a karo na uku, ta ce, "A doke kam idan za ku gabza ai ya fi karfin ki, amma a zaman aure bai fi karfin ki ba. Tunda kema mace ce kamar Hadiza, kuma a hakan da kike ba sai kin yi wata kwarkwasa ko kwalisa Sulaiman zai so ki ba. A'a, maintain your own qualities (rike taki sigar) kada ki aro wadda ba taki ba don ki burge.
Kwalisa, kwarkwasa da yanga ba sa burge namijin da ya san ciwon kansa, sai hankali, nutsuwa, kamewa, ilimi da sanin ciwon kai. Wadanda dasu ne Hadiza ta samo zuciyar Sulaiman ba appearance (kamantuwar ta ba).
Saboda haka Fati ki kwantar da hankalin ki, ki yi biyayya ga mahaifin ki, Alqur’anin ki, ba zai bari ki tozarta a rayuwa ba…..!!".

Ta mike ta na murmushi cike da jin dadin kalaman mahaifiyarta, ko ba komi ta bata kwarin gwiwa cewa, itama mace ce kamar sauran mata ba mata ta rako duniya ba kamar yadda Sulaiman ke cewa.
Ta cire mata inferiority complex din da ya bi ya addabe ta, har ta ji za ita iya jure duk wani hali da za ta tsinci kanta ko da a ce hasashen Yaya ba su zamo gaskiya a kan nata al'amarin rayuwar ba.
Da kanta Yaya ta zaunar da ita a gabanta, ta sa kibiya ta tsefe mata gashin kanta da ya yi masifar dauda ya duddunkule saboda rashin gyara har tsayin kwanaki arba'in da biyar. Fati sai yawan gashi amma babu tsayi irin na asalin Kanawa, sannan ga shi da karfi kamar reza, sabida ba ta taba shafa mishi relaxer ba, da za ta shafa mishi din da ya mike ya zama mai ban sha'awa.
Fa'iza ta yi sallama ta shigo tana cewa, "Wai da gaske ne abin da nake ji?"
Ta tsuguna ta gaida Yaya ta amsa. Fati na hararar ta ta sake cewa,
"Don Allah Yaya da gaske ne? Yau an daurawa Fati aure?"
Yaya ta yi murmushi ta ce,
"Eh, haka Allah ya nufa". Ta ce,
"To, Allah ya sanya alheri". Yaya ta ce, "Amin".

Fa'izah kawar Fati ce, tare suka yi makarantar kwana a G.G.C Kano, kuma gidansu nan cikin layinsu yake babu nisa zuwa gidan su Fati.
Yaya ta ce dama yanzu zan tura Abdulyassar ya kirawo ki, ki zo ki raka ta wajen wankin kai, na san in na bar ta a haka za ta tafi gidan mijin. Daga nan ku biya ayi mata kunshi".
Fa'iza ta ce, "Gaskiya kam, kawo in karasa mata tsifar".
A daren sai ga kannen Dr. Sulaiman da wata kanwar Inna sun kawo akwatuna hudu shake da kaya, ga shi ba su gayawa Yaya za su kawo ba balle ta tara masu karba.
Ta kama baki ta ce, "Yanzu Allah sai da aka takura Sulaiman da yin lefen nan yana fama da halin da yake ciki?"
Ruma ta ce,
"Ai babu komi, abune da idan ba mu yi ba, ba zamu ji dadi ba".
Yaya ta ce,
"To Allah ya amfana, ya sa an yi a sa'a, ya kuma tabbatar da alherin da aka kulla, amin".

Fati kwana ta yi sallah, in 'yar ta yi kuka sai ta dakata ta kula da ita har ta koma barci, sannan ta ci gaba, Cikin sujjadarta tana mai rokon Allah koma mene ne zai zo cikin rayuwar ta ya zo mata da sauki.

Washegari ko tsakar gida ba ta leko ba, don gidan ya cika da 'yan uwan Yaya da dangin Malam, saboda kowa da Hadiza a zuciyar sa babu wanda yake yin hayaniya.
Karfe uku na rana Fa'iza ta kawo mata kayan da za ta sanya, wani leshi mai taushi ruwan zuma da kananun stones da ta kai Diallo (Zoo Road) aka yi mata dinki express, amma ya yi kyau sosai, ya amshi dan karamin jikinta.
Fati siririya ce, kuma ba ta kai tsayin Hadiza ba, komi na halittar ta (natural) kamar fata, gashi da hakora yiri-yiri, kuma farare kal wadanda ba ta wasa da kuskure su da listerine (mouth wash) a duk lokacin da ta goge su. Shiyasa suke farare tas, kamar kankara
A can gidan Sulaiman shi ma cike yake da nashi 'yan uwan, suna ta gyare-gyare, suka gyara gidan tsaf, dama tuni an kwashe kayan Hadiza har gadaje da (wardrove) an balle an fitar dasu an kai gidansu.
Malam Ja'afar ya ba da daki guda aka kulle su, Inna tasa aka sayo katuwar katifa aka aje a dakin da a yanzu ya zama mallakin Fati kamin a yi mata jere.

Kai! Rayuwa!! Ran dan adam ba a bakin komai ba, kowa ganin al'amarin yake kamar almara, masu yiwa Hadiza addu'a na yi, masu kokawa na yi, masu korafin anyi gaggawar yiwa Sulaiman wani aure na yi. Amma a bayan idon Inna, don kowa ya san irin son da Sulaiman yake yiwa Hadiza.
Shi kam bai ma gidan yana asibiti tun safe, ya kama wayoyin shi ya kulle kada Inna ta neme shi. Don a daren jiya ta shaida mishi wai shi zai je da kanshi Karkasara ya dauko Fati da yara, shi kuma ya kudire in har shi zai yi hakan, to wallahi sai dai idan ba za ta zo gidan ba.
Zuwa karfe hudu ran Inna ya soma baci da rashin samun Sulaiman a waya, sai dai ta yi mishi uzri. Ta sani sarai sun takura shi, wanda su sun tabbatar abin alheri suka yi, sun gyara zumuncin su da iyayen Hadiza, sun kawo wadda za ta rike 'yan jikokin su da gaskiya, sannan sun aura mishi mai kama da Hadiza, kuma shakikiyarta.
Akwai gatan da za su yi mishi da ya wuce wannan? Ta kudurce a ranta za ta tsayawa Fati da addu'a da yakin zuciyar Sulaiman har sai ya so ta kamar yadda yake son 'yar uwarta.
Don haka sai Inna Talatuwa kanwar Malam da su Ramatu ne suka taho dauko amaryar a motar mijin Ruma, don motar shi da ita ya fita, ta Hadiza tuni an sayar sai ta amfanin gida rufe cikin tampol. Cikin girma da mutuntawa aka basu amarya. Yaya ta ce a bar mata

2 Comments On YAKANAH
avatar
rabiatu-2

1 year ago

Reply

Thanks

avatar
fatima-2-7-5

1 year ago

Reply

very nice book

Please Login or Register in order to submit comment