Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE


DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register
DOWNLOAD

gefen gado, cikin doguwar rigar barci mai santsi mara hannu ruwan madara, kyawawan kafafunta da cinyoyin ta a mike sambal, a haka sai ka rantse lafiyar ta kalau ba ta tare da wata lalura.
Son matarshi da kaunar ta na kara girgiza zuciyar sa, yana hargitsa gangar jikinsa. Ta kure fanka da A.C amma ba ta daina zufa (gumi) ba. Da sauri ya karasa zarga igiyar pyjamas din shi ya yiwa kanshi kyakkyawan matsuguni a bayan ta, ya daura hannu a kan goshin ta, zafi rau! Dole ya hadiye nashi bukatan ya soma ba ta kyakkyawar kulawa ta hanyar sanya karamin towell a ruwa yana goge mata kanta don zafin kan ya ragu. Sannan ya soma bin gabban jikinta da message don ta ji dadin kasusuwan ta. Ya juyo ta ya rungume ta ganin wani irin gumi na tsatsafowa daga cikin kanta, a yau ma ya sake cewa,
"Cikin kowanne hali, INA SON KI HADIZAH!"
Ta bude idanunta a hankali, wadanda suka kankance suka yi jawur don azabar data ke dandana, tana kallon abin son ta, shi ma kallon ta yake kallon yaya zan yi da raina? Me zanyi in sama miki lafiya? Ya ce a galabaice,
"Gobe zan dauko Dr. Bunza ya duba ki".
Gabanta ya yi wani irin faduwa, ta runtse idon ta da karfi ta ce,
"Bana so, kada ka dauko shi, idan kuma har ka dage sai ka dauko shi to zan koma Karkasara".
Ya girgiza ta da karfi ya ce, "What do you mean (me kike nufi)? In barki a gida kina ciwo ban nema miki magani ba? Bansan hakikanin me ke damunki ba? Allah sai ya tambaye ni, iyayen ki da suka danka min amanar rayuwarki su tuhume ni. Wannan ciwon kan bana wasa bane yana bukatar bincike".
Ta ce, "Ai ba yau na fara ba ka sani, kuma da na sha magani shi ke nan yake lafawa".
"Ina maganin? Dauko min in gani".
Ta ce, "Ya kare dazu, da safe nake shirin in aiki Fati ta siyo wasu".
Ya ce, "Wane magani ne?"
Ta yi shiru.
"Tambayar ki nake yi, ina maganin? Ya ya sunan sa?'
Ta ce,
"Panadol".
A mamakance ya maimaita
"Panadol?"
'Eh".
Ya ce,
"You are silly, ko in ce you are a nonsense Doctor! I did not trust you.........". (kina shirme, ke shashashar likita ce, ban yarda dake ba).
Ya tashi a fusace ya fizgi waya ya kira Dr. Bashir, ‘consultant’ na ‘neurology’, Surayya ce ta dauka, bai ko amsa gaisuwar da take mishi ba ya ce,
"Ina mijin ki?'
A ladabce ta amsa.
"An kira shi a ‘emergency’ kuma ‘he is on call’ yanzu ya fita, ya manta wayar".
Ya kashe wayar ya cillar ya zauna a gefen gado ya dafe kai, Hadiza na kuka a hankali tana kara hargitsa shi, ya ce a fusace,
"Enough.......is enough Hadizah! Ki gaya min fisabilillahi mene ne babbar matsalar ki?"
Ta ce,
"Nifa na gaya maka laulayin ciki ne, sai migraine wanda ba yau na fara ba, kuma ka san shi dama ina da magungunan da nake sha a kan shi, wannan zazzabin da haraswa laulayin ciki ne irin wanda na saba, zan gaya maka karya ne? Yau da bakin ka Sulaiman kake cewa baka yarda dani ba?"
Jikinsa ya dan yi sanyi, ya rage sauti ya ce, "To ta ya ya zan ce zan kira likita da ya san matsalar ki ya duba ki ki ce a'a? Sai in dauka wani abu ne daban kike boye mini".
Ya yi mata wani irin murmushi da har abada ba zai gushe daga zuciyarta ba, ta dauke kai alamar ta yi fushi. Ya bi bayan ta a hankali ya kwanta, suna raba zazzabin tare. Akwai wani abu wai shi 'hot kiss' da Hadiza ba ta sani ba daga Sulaiman sai a yau, ya mantar da ita rashin lafiyar ta, ya dauke ta ya jefa a duniyar soyayya, ta manta cewa ita nakasasshiya ce, ta manta damuwar ta na cewa lafiyarta na hannun Allah, ta dauka cewa, tana a matsayinta nna Dr. Hadiza ne ta baya. Ba za ta mance da wannan ranar da Sulaiman ya zubar da hawayen shi a karo na biyu a kanta ba.
Na farko saboda ta nakasa, na biyu na dimbin soyayyar da yake yi mata. To wanne ne zai kasance na uku???

****
10/15/21, 11:47 AM - Buhainat: Ta hanyar katin shaida (ID Card) jami'an tsaro suka gano ko wacece Hadiza. Don haka ba su sha wahalar samun nombar wayar mijinta ba, wanda ke can cikin gigicewa. Nan asibitin aka taho da ita cikin jinni kaca-kaca, rai a hannun Allah.

Likitoci biyar ne a kan Hadiza, sai Sulaiman cikon na shida, wanda ya manta wani abu wai shi karatun likita, komawa ya yi tamkar bai taba halarta aji ba. Shi da Hadiza da ke kwance babu maraba, illa shi a tsaye yake, sai dai jingine da garu (bango), wanda ya taimaka masa wajen daukar nauyin gangar jikinsa. A lokacin da za ka tsaga ba za ka samu ko digon jini a cikin jikinsa ba.
Tashin hankali ba a sa maka rana! Haka wannan mummunan labari ya iske iyayen Hadiza da 'yan uwanta ta hanyar Dr. Surayyah.
A daren Mukhtar ya baro Kaduna zuwa Kano, a daren suka dungumo baki dayan su suka taho, sai dai basu samu ganin Hadiza ba. Har zuwa lokacin likitoci na tsananta bincike a kanta, haka suka kwana a barandar asibiti cikin tsananin sanyi. Amma babu mai jinsa. Fati sai kuka take kamar ranta zai fita tunda suka taho, Yaya na lallashin ta.
Sai washegari da safe result din Hadiza ya iske Sulaiman da iyayen ta, bayan raunuka da ba za su kirgu ba, babu karaya ko daya a jikinta. Babban tashin hankalin wanda ya girgiza kowa shi ne, jijiyar bayanta wadda ta hada daga wuya zuwa bayan ta (spinal cord) ta tsinke, wanda ke nufin Hadiza ba za ta kara iya mikewa ba, ba za ta kara iya tafiya ba a gaba daya sauran rayuwar ta.

Dr. Sulaiman ya mike tsaye ya nuna Dr. Samson da dan yatsa, "Ka san abin da kake fada, ban san cewa baka san aikin ka ba sai yau. Kuma shi ke nan daga yin accident sai ka nakasta min mata? Uwarka ce ba za ta kara iya mikewa ba, amma ba Hadiza ba......"
Kai da ganin yadda yake maganar, kwayar idanun shi a juye, ka san ba a hayyacin sa yake wannan furucin ba.
Samson ya sunkuyar da kai, duka likitocin babu wanda ya kara magana. Tausayi ne fal a zukatan su. Dr. Hadiza abar so ce ga kowa, suna jin dadin tarayya da ita, marasa lafiyan ta na yaba kokarin ta. Wannan accident da ya yi mata karan tsaye da kuruciyar ta, ya zamo nakasu ga dimbin taimakon da take bai ma al'umma.

Malam Ja'afar mahaifin Hadiza da ke gefe shi ya soma tausar Sulaiman da kalami masu dadi da sanya imani, yana tuna masa muhimmancin yarda da kaddara.
Sulaiman ya yi shiru, ya koma ya zauna a kujerar sa. Ya kifa kai cikin cinyoyin sa, amma har yanzu ya kasa yarda da abin da kunnuwan sa suka jiye masa.
Wai Hadiza ta zama sai dai a kwantar a tayar ba za ta kara amfanuwa ba, ba za ta kara moruwa ba. Balle ta amfanawa kanta komai. Ita da 'ya'yanta da mijinta sai dai gani da ido. Abin da suke gani kullum yana faruwa da al'umma yau Allah As-Samadu ya juyo da shi kansu. Dimbin ilimin su, karfin aljihunsu da tunanin su babu abin da zai iya a kai, domin ita wannan jijiya ba ta doruwa. Sai ya fashe da kuka.

Malam Ja'afar ya mike daga kujerar sa ya isa ga Sulaiman, ya mikar da shi tsaye ya rungume a jikinsa.
"Haba Sule! Kamar ba namiji ba? Namijin ma, likitan likitoci. Ba ka yi kuka a kan sauran al'umma da kuke kwana da yini kuna fama dasu ba sai a kan matar ka kadai? Su Allah ba ya son su ne yake dora musu lalura? Allah da ya halicci Hadiza ya fi mu son ta, shi kadai ya san dalilin sa na hukunta hakan a gare ta.
Yau in Hadiza mutuwa ta yi me zamu iya ban da mu yi mata addu'a? Amma tana raye, a kalla muna ganin ta muna jin dadi, ka yi tawakkali ka barwa Allah, ka zamo mai YAKANAH, sai ya yi maka tukuici da abin da baka zata ba.
Kai za ka ba ta kwarin gwiwa, ta rungumi kaddarar da Allah ya dora mata. Amma idan ka fita karaya, wane ne zai karfafa wani?"

Ya mika hannu yana share masa hawayen da suka kasa daina ambaliya daga kyawawan idanun sa.
Dr. Ruth ta yi gyaran murya, ta dubi Dr. Sulaiman ta sunkuyar da kanta, kana ta dago ta ce,
"Ina ganin idan Dr. Hadiza ta ji sauki, raunikan jikinta sun warke, za ta iya ci gaba da aikinta ta hanyar amfani da wheel chair, idan har za’a samu wanda zai juri kawo ta da mai da ita".
Kiris! Ya rage ya lailayo ashar ya antaya mata, ko ya faska mata mari, amma da ya tuna Malam na wajen sai ya balla mata harara, a zuciyar shi ya ce,
"Uwar ki za a sa a wheel chair ba uwar Munib ba!!!".

Samson ya ce,
"Shawarar Ruth abar dubawa ce, hakan zai debe mata kewa fiye da ta zauna a gida ba abin da take yi. Ko ba don zuwa aiki ba dole za a nema mata wheel chair ko da a gida ne".
Ba shi da abin cewa, don duk likitocin abin da suke cewa kenan. (They cannot afford to lose HADIZA in the Nigerian medical practition). Malam dai baya ji saboda cikin harshen turanci suke maganar. Shikadai ne ba likita ba a ofishin. Wannan na jefo tasa wannan na jefo tasa kai kace a gaban ofishin Barrack Obama kake. Da zancen ya ishi Sulaiman sai ya tashi ya fita cike da jin zafinsu. Ta amfanin ta ga Nigeria da asibitin su suke, bata gurguncewar rayuwarta bakidaya ba. Ya nufi ICU inda aka kwantar da Hadizah.

A bayan kofa ya tsaya ya rabe, yana leken ta, ya kasa karasawa, ya kura mata ido yana ta'ajjibin yadda kwana daya rak! Allah ya jirkitar da kyakkyawar fuskar Hadiza, ko ina a jikinta rauni ne, nan plasta can plasta. Barci take sadidan, sai dai da gani ba na Allah da Annabi bane (na karfin allurai ne).
Rabin fuskarta nade cikin bandeji, wadda ta kumbura ta yi sumtum kamar an hura (baloon). A hankali ya soma taku ya isa ga gadon da take kwance, ya ja kujera ya zauna dai-dai fuskarta yana fuskantar ta.
Ya kai hannu bisa goshin ta wanda ke nade cikin bandeji, kamar an ce da ita bude idon ki. Suka yi ido hudu da Sulaiman din ta, ta dubi dakin ta dubi kanta, ta tabbatar a kwance take a gadon asibiti. Ta maido duban ta ga Sulaiman wanda ke binta da ido da zuciya, ta ce cikin kankanuwar murya,
"Sulayman Accident na yi ko?"
Ya daga mata kai. Ta dora hannunta mai rangwamen raunika bisa nashi dake goshin ta, ta sauke, don ji take kamar ya dora mata Dala da Gwauron Dutse.

Ta yunkura da niyyar ta tashi zaune amma ta ji kamar ba jikinta ba, ya mike ya kama ta ya mikar da ita zaune. Ya janyo pillow ya tusa mata don ta ji dadin jinginar, ya tabbatar dai da gaske ne Hadizar shi ta zama disabled (nakasasshiya), sai jikinsa ya soma kyarma.

Duk dauriyar da yake yi abin ya ci tura, da sauri ya rungume ta, cikin shesshekar kuka ya ce,

"Cikin kowanne hali, INA SON KI HADIZAH!"

Kuka suke dukkanin su babu mai rarrashin wani, don ita Hadiza ta tabbatar abin da zai sa Sulaiman kuka, to tabbata ba karamin abu bane, wannan shi ya gigita ta, ita ma ta fashe da kuka.

Fati a gaba, Yaya, Malam, Hamza da babban Yayan su Mukhtar suka shigo, daga Hadiza har Sulaiman babu wanda ya san da shigowar su, shessehekar kukan Fati ne ya ankarar da Sulaiman cewa akwai mutane a dakin.
A hankali ya zare jikinsa daga na Hadiza ya juya ya fita daga dakin ba tare da ya iya hada ido da surukansa ba.
Malam Ja'afar ya karasa jikin gadon Hadiza ya kama hannun ta inda babu ciwo, ya ce,
"Ki yi tawakkali Hadiza, ki zamo mai YAKANAH a dukkanin al'amuran ki, ki zamo mai godiya ga Allah a duk yanayin da kika tsinci kanki. Wannan ba shi ne karshen rayuwar ba, yarda da kaddara dole ne ga duk musulmin kwarai".
Cikin kuka mai tsanani ta ce, "Na ji Baba, amma don Allah ku fada min me ke faruwa dani? Sulaiman bai gaya min komi ba, sai kuka yake yi, kukan shi ya daga min hankali, ku fidda ni a duhu. Wani abu ne ya faru dani?"
Malam ya sa habar babbar rigar sa ya share hawayen da suka ciko mishi ido cikin dabara wai kada Hadiza ta ga shi ma kukan yake kamar Sulayman din, amma ta ganin. Hadiza ta musamman ce ko a cikin 'ya'yansa, yana son ta son da bai yiwa su Mukhtar, ta kama duka hidimar gidansa ta rungume, kafin Yayanta Muktar ya Kawo sau daya ta kawo sau goma. Ta sha cewa don su take aiki. Ganin Babanta yana kuka wiwi sai ta kara tsananta kukan ta.

Cikin tausasawa Mukhtar ya ce,

"Cool down Hadiza, take it easy......." Ya shiga rattabo mata al'amarin da ya samu rayuwarta, ya kare da cewa, "Wannan shi ne ya dagawa Sulaiman hankali, amma kamar yadda Baba ya ce ne, ki yi tawakkali, ki zamo mai YAKANAH! Wannan ba shi ne karshen rayuwar ba!"

A matsayinta na cikakkiyar likita, ma’abociyar sani a fannonin kiwon lafiya, tuni ta hararo mummunan nakasun da ya samu rayuwarta rana tsaka wanda babu wani likitan duniya da zai iya maganin shi. Ta nemi hawaye a kwayar idonta ta rasa, ta nemi miyau don ta hadiya a kan harshen ta ya kafe karaf! Kamar bai taba gudana a cikin bakinta ba.

Ta runtse idonta da karfi, tsawon mintuna biyar ba ta bude ba. Ita kadai ta san radadin da take ji a zuciyarta, ita kadai ta san azabtuwar da ruhinta ke yi, al'amarin ya shallake tunanin ta. Ba ta yi tsammanin al'amarin ya yi kamarin haka ba, bata taba kawowa ba, spinal cord injury! A gareta ita Hadiza. Lallai dan adam ba a bakin komai yake ba.
Yau ne kake mai rai, gobe ne kake gawa. Yau ne kake da amfani, idan Ubangiji ya so, gobe ne ka zama tarihi. A rayuwar Hadiza ba ta taba tsammanin wata kaddara makamanciyar wannan za ta taba shafar rayuwar ta ba. To ina ruwan Allah!

Ta bude idon a hankali daga runtsewar data yi musu, tana kallon iyayen ta da 'yan uwanta wadanda dukkanin su ke sharar hawaye, sai ta soma lallashin su cikin muryar ban mamaki, tamkar ba ita ba. Ta fi su karfin zuciya, ta fi su tawakkali, ta fi su YAKANAH. Ta karbi kaddarar ta da hannu bibbiyu, tana fatan Allah ya sa hakan ya zamo kaffara a gare ta, in kuma jarrabawa ce ya sa ta cinye jarrabawar ta.

****
Dole kanwar naki, Sulaiman yana ji yana gani, da hannusa da kudinsa ya sayo ma Hadiza wheel chair ana i gobe za a sallame su daga asibiti. Wani bigire na karshe da ko makiyinsa baya yiwa fatan ya hau. Don duk raunin dake jikinta ya kame sai karfin jiki da dan abin da ba a rasa ba.
Yaya ta so Sulaiman ya ba ta Hadiza ta wuce da ita gida inda za ta fi samun kulawar iyaye da 'yan uwa, amma sai ya sa musu kuka. Da me zai ji ne? Da lalurar da ta kashe masa rayuwa, ko da rashin Hadiza a cikin gidan, wadda ta zamo wani bangare na rayuwar sa, kundin farin cikin sa, sannan barin jikinsa?
Dole suka kyale shi da matar shi, amma sun ce Fati ta koma gidan ta zauna tare dasu, don ta dinga taimaka masa kula da Hadiza, musamman kasancewar sa ba mazauni ba.
Sulaiman bai so ba, don shi tun fil'azal Allah bai sa mishi son Fati ba, saboda son da Hadiza ke mata. Yana kishin Fati, a ganin sa Hadiza ta fi son Fati a kanshi. Sannan zubin ta na zuhudu (gudun duniya) ya yi yawa, bai fiya son mutane irin ta ba, kasancewar shi (sociable).
A tsarin halittar dan adam (personality), tana cikin rukunin al'ummar da ake kira (introvert). Ba ta iya hada ido da shi, kai da kowa ma, saboda kunya. Da wuya ka ga hakoranta, sai dai in guri ya kure ta yi murmushi, ‘dimple’ din da ‘cleft’ su lotsa, wanda shi ne muhimmin al'amarin da ke daukar hankalin dubban maza a kanta, sai dai kuma bai isa ya tsallake hukuncin da Yaya ta yanke ba.

Haka Fati ta hado kayan ta tsaf, ta dawo gidan 'yar uwarta da zuciyar 'yan uwantaka. Zuciyarta cike fal da so da kaunar 'yar'uwar ta da tausayinta, karatun da ta taso shekara da shekaru da burin yin sa, gashi ta samu, amma a yau ta sallama shi, ta jingine shi ta sadaukar da rayuwarta kacokam da lokacinta ga rayuwar, 'yar uwarta Hadiza.

Sulaiman ya ciccibo Hadiza ya fito da ita daga mota, Fati ta bude (boot) ta fiddo wheel chair a nade, cikin sauri ta warware, Sulaiman ya sanya ta a ciki ya tura a hankali zuwa cikin gida.
Fati ta fiddo kayansu daga cikin motar ta rufe motar, ta soma diban kayan daya bayan daya tana shiga dasu cikin gida.
Malam Ilu maigadi, ya yi sallama a falon, a lokacin Sulaiman na kici-kicin aza Hadiza a daya daga cikin kujerun falon, ba tare da ya juyo ba ya amsa masa.

Ya zube har kasa yana jajantawa iyayen gidansa kaddarar da ta same su. Yana magana yana sharar hawaye, saboda yadda yake matukar kaunar Hadiza, saboda karamci da kyautatawar ta gare shi.
Haka Goggo Alti ta fito daga kitchen, ganin Hadiza yau nade cikin kujera sai ta fashe da kuka, Sulaiman ya yi saurin ficewa a falon ya dau mota ya fita don dauko yara a makaranta.
Hadiza ta dubi Alti ta yi dan murmushi, "Alti wane ne ya halicce mu?"
Ta ce, "Allah (S.W.A)".
Ta ce, "To kinga in haka ne ke nan bamu da iko da kanmu sai abin da ya ga damar hukuntawa a gare mu, mu kuma dole ne mu zamto masu godiya idan har muna so imanin mu ya cika".
Alti ta jinjina kai tana mai jinjina karfin imani irin na uwargijiyarta.
Hadiza ta juya ga Fati ta ce ta kai kayanta dakin ta, kasancewar a tsarin gidan likitocin babu wani extra room, ita za ta yi amfani da na Sulaiman.
Fati ta ce atafau ita dakin su Muniba za ta zauna tare dasu, ta kada ta raya amma ta ki, ta ciccibi jakarta ta yi dakin su Muniba d ita.
Fitar ta daga falon ke nan su Munib suka dira a falon, Baban su na biye dasu yana rike da jakunkunan su da food flasks din su. Suka tafi da gudu suka rungume Mamarsu, Munib da yake shine mai wayo ya ce,
"Mummy yaya jikin ki? Daddy ya gaya mana kin yi accident kin ji ciwo kina asibiti ana yi miki allura?"
Ya kai hannu ga tabon ciwon goshinta, "Sannu Mummy, kin ji?". Ta shafa kansa ta yi masa murmushi bata ce komai ba.
Ita kuwa Muniba bin jikin Mummyn ta yi ta lafe kamar mage, dama ita ba ta fiya magana ba. Zuciyarta kal da ganin mahaifiyarta da ta jima ba ta gani ba.
Munib ya soma jan hannunta wai ta taso suje su yi kwallo (ball) kamar yadda suka saba, Sulaiman ya kau da kai, bai son ganin wannan abin tausayi, ya mai da hankali ga lallatsa wayar sa, baya son su ga hawayen sa.
To ita ma Hadizar duk dauriyar ta sai da hawayen suka tsatstsafo, ta sa yatsun ta biyu ta dauke su, ta kama dukkan 'ya'yan biyu ta rungume a kirjinta. Kukan zuci take wanda ya fi na fili soya zuciya. Ta ce,
"Ku tafi wurin Anti Fati tana dakinku ku yi kwallon tare, har yanzu bani da lafiya".
Da gudu suka mike daga jikinta suka nufi dakin su suna murnar zuwan Antin su da suke tsananin so. Alti ta yi sallama dauke da tray kanta a sunkuye, idonta cike fal da hawaye, muryarta a sanyaye tace da Hadiza,

"Na ce sai na daina daura abinci a tebir?”

Hadiza ta yi murmushi mai hade da wani irin radadi a zuci, ta ce,
"Idan maigidan yana son hawa tebir din fa?"
Ta fada tana kallon Sulaiman.
Bai dago ya kalle su ba, haka bai tofa musu ba, duk da ya lura ta bakinsa suke son ji. Alti ta ajiye katon tray a gaban Hadiza ta juya ta fita.
Tana ba da baya ya suri Hadiza a kafadar shi sai dakin barcin su. A hankali ya sauke ta a makeken ‘family bed’ din su, ya koma toilet ya cika baf da ruwa mai dumi, ya zuba dettol kadan ya dawo ya soma warwarewa Hadiza kayan jikinta, ya nade ta cikin towel ya sake sungumar ta ya yi toilet ya sanya ta cikin ruwan da ya hada. Ita karfin Sulaiman mamaki yake bata. Ya yi mata kyakkyawan wanka da kamsassan sabulun Zest, ya nado ta ya fito da ita.
Yawancin kayanta a dakin suke dama, don haka ya shirya ta cikin riga da wandon pakistan ruwan goro (orange), ya dauki (kumb) ya soma sharce mata gashin kanta da ya wanke da (head&shoulder) wanda rashin gyara kwana biyu ya sa shi duk ya cukurkude.
Ta ce, "Da ka bari Sulaiman Fati za ta yi min gyaran kan".
Bai saurare ta ba ya ci gaba da abin da yake, amma da a ce ta kalli fuskarshi a lokacin, data lura da yadda ya dan hada rai, saboda ambatar Fati da ta yi, wato ta fi son Fati ta kula da ita fiye da shi.
Ta yi murmushi ta ce, "Amma tunda ka hada ruwan wanka ka yi mai wuyar, zan iya wanka da kaina, sai Fati ta shirya ni koda yake ma zan iya shiryawa da kaina.......".
A hassle yace .
"Is o.k Hadizah, very o.k, ba tun yau ba na san kin fi son kanwar ki fiye dani. In ba haka ba ni amfanin me ke gare ni? Da ba zan kula dake ba a lokacin da kike cikin lalura?"
Ta kama baki, don ba ta ji dadin maganar shi ta farko ba, amma sai ta share ta ce, "Yau da gobe ne sai Allah Sulaiman…….". Can kuma ta yi rau-rau da ido kamar hawaye za su zubo,
"Me ya kawo maganar na fi son Fati a kanka? Ban ji dadin nagetive response din ka ba".
Ya ce, "To ai ke ce Hadiza da wani irin batu, amma ina so ki yarda da cewa, idan zan gaji da hidimar ki Hadiza, to zan gaji da hidimar kaina……".
Ta ce, "Amma Sulaiman......"
Ya kai hannu ya toshe mata baki, "Kina shakka da abin da na ce miki?"
Ba ta son jan zancen da nisa, har ya yi tsayin da zai zamo bacin rai, sai ta ce,
"Bana shakka Sulaiman, Allah ya bamu rai da lafiya".

Ya turo ta cikin kujerar ta suka dawo falon don cin abinci. Munib da Muniba suka shigo, fes dasu cikin kaya 'yan kanti (pink colour) har Fati tayi musu wanka ta shirya su ta feshe su da turare.
Suka saki baki cikin mamaki, ganin Daddy yana tura Mummy cikin kujera mai tayoyi, abin ki da yaro, sai ba su kawo ma ransu komai ba, ko wani abu ne ya faru da Maman nasu, sun dauka haka nan dai yake tura ta don bata da lafiya. Sai suka sa rigimar ta tashi suma Daddy ya tura su.
Haka Sulaiman ya sauke Hadiza a seater, ya dauke su su duka biyun ya aza a kujerar, ya yi ta zagaya falon dasu suna jin dadi, sai kyalkyatar dariya suke.
Hadiza ta juya ta dube su, ganin abin nasu ba na kare bane ta ce, "Oya! Food is ready, maza ku zo ku ci kafin malamin lesson ya zo, ko kuna so ku yi latti ya yi muku bulala?"
Suka diro daga kujerar suka nufo abincin, Sulaiman ya zauna tsakanin Hadiza da Muniba, kafadun su na gugar na juna. Ta sa murya ta ce,
"Fati!"

Ta fito sanye da hijab, da alama sallah ta idar, kallo daya Sulaiman ya yi mata ya dauke
DOWNLOAD
DOWNLOAD

2 Comments On YAKANAH
avatar
rabiatu-2

8 months ago

Reply

Thanks

avatar
fatima-2-7-5

7 months ago

Reply

very nice book

Please Login or Register in order to submit comment