Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta fito daga bandaki, ta yi daurin kirji ta rufu da tawul, ta sha dukan ganye, jikin nan ya kara zama fresh, fatar nan ta kara zama mai taushin gani a ido.
Ta kasan ido ya dube ta, sai ya ga duk ta canza mishi, ta kara zama yarinya danya sharaf. Da alama ba ta da damuwa, sun barshi da kadaici, sai fama yake da biro da takarda.

Yaya ta shige kitchen ta barsu, ai kamar jira yake ta tashi ya yi ma dakin Fati tsinke. Tana tsane gashin kanta da tawul ya bude mata dukkan hannuwan sa bayan ya aje babyn a cikin katifar sa. Ta rufe ido tana dariya, shima ya san bazata iya ba, har a gobe halayenta na kawaici da alkunya basa canzawa, sai shi ne ya karaso ya rungume ta tsantsan a hankali, yana fada mata kalaman da suka zama sirri ne a tsakanin su tana ta sakin murmushi. Cikin ranta addu’a take Allah ya barta da SULAYMAN dinta, ya dorar da rayuwarsu cikin daukaka da soyayya, kamar yadda ta faro, har zuwa ranar da suka daina numfashi.

*** ***












SHEKARU GOMA SHA BIYAR A GABA!

Taron rantsar da sabbin ministoci da mai girma shugaban kasa President Umaru Musa ‘Yar Aduwa zai gabatar a yau a hotel din NICON NOGA, har da babban likitan zuciya da kasarmu Najeriya ke tanka how
da shi, wato Dr. Sulaiman Sulaiman Bakori, wanda aka rantsar a matsayin Ministan Lafiya na kasa baki daya. Ranar Litinin, ashirin da shida ga watan Maris, na wannan shekarar.

Dr. Fatima Ja’afar, H.O.D Islamic, a jami’ar Abuja, cikakkiyar mace ‘yar kimanin shekaru talatin da bakwai da haihuwa, uwar ‘ya’ya biyar a halin yanzu, in ka hada da manyan ‘ya’yan ta Munib, Muniba da Nana Khadija sun zama su takwas kenan.
Tana sanye da bakar abaya kirar Bahrain da mayafinta, hannunsu sakale dana juna suka isa ga mazaunin su, daukacin Ministocin da ake shirin rantsar wa suna tare da matansu da rakiyar ‘ya’yansu, to haka suma, Muniba, Nana Khadija, da Ja’afar. Ya yin da suka baro Mufida, Mufid da Ibrahim da dan autan su Abdulhak a gida, cikin kulawaar tsohuwa Alti.

Bayan mai girma shugaban kasa ya rantsar da Ministocinsa, aka zarce da gagarumar walima. Ba su baro dakin taron ba sai dare, suna kan hanyar isowa gida wayar Munib ta shigo, wanda ke can kasar ‘Srilanka’ yana karatun harhada magunguna.


Munib Ya ce,
“Daddy kun manta dani, ko waya an fi sati ba wanda ya yi min.
Yanzu nake jin abin alheri a BBC, congratulations Daddy!”
Ya ce, “Kwantar da hankalin ka Munib, zirga-zirga ta hana mu neman ka. Ina mai yi maka albishir da cewa, muna tafe dukkanin mu cikin satin nan, sai ka tanadar mana better”.
Ya yi ihu ya ce, “Allah Daddy da gaske?”
Fati ta amshe wayar ta ce,
“Amma sai in point din ka na wannan semester ya kai CGPA 4.00, if not, babu wanda zai zo”.

Ya ce, “Wallahi 4.60 ma na samu Mummy”.
Ta ce, “Ah, lallai Babban Yaya ka gama min komai, zuwan kowa ya zama dole, tunda duk muna cikin hutu”.

Ja’afar ya amshe wayar ya ci gaba da ba shi labarin duk shagulgulan da ake yi a yau. Munib ya ciji yatsa ya ce,
“Ayya! Na yi missing….”.
Daga nan sai Muniba, ita kuwa Nana ta ce, ba za ta yi magana da shi ba tunda baya yi mata waya sai budurwar sa kawarta Naina.
Daddy ya harare ta ya ce,
“Bana son sakarci, shi ba shi da wata budurwa dan makaranta ne”.
Ta ce, “Amma yake yi mata waya yake yo mata tsaraba in zai zo?”.
Ya ce, “Ba kanwar shi ba ce? Ke ba ya yi miki?”
Ta ce, “Wallahi Daddy nata ya fi yawa, har da kati an rubuta I LUV YOU”.

Fati ta tintsire da dariya, shi kuma Dr. Sulaiman sai ya rasa ta cewa, yaran zamani sai a barsu, da wayonsu ake haifar su.
Ya dubi Fati da wani irin sassanyan kallo, “Momin yara, wai da gaske ne Munib yana da budurwa?”
Ta rausayar da kai ta ce, “Shirmen Nana ne, Naina Bunza, tana da shiga ran kowa sosai ba Munib kadai ba, suna shiri da Munib sosai sabida kokarinta.”. (Diyar Dr. Surayyah).
Ya ce, “Ba zan yi mamaki ba in son nata yake, ai jin kanshi yake matured (balagagge) kamar kowa”.
Dariya ta kama Fati, sai da ta murmusa sosai.
Sun isa gida yara kowanne ya kama harkar gabansa, ya cacumi Fati su kai sama ana biyan bashin soyayya, wadda hidimar kwana biyu ba ta bari ba. Suka ci gaba da amsa sakonnin taya murna da fatan alheri daga ‘yan uwa da abokan arziki, har tsayin sati daya.

Ranar juma’a jirgin MEA International ya tashi dasu zuwa Srilanka, har filin jirgi Munib yaje ya taro su, ya dauki Abdulhaq ya rungume suka karasa zuwa makarantar su bayan sun yi booking din hotel din da za su sauka.

Farin cikin Munib ba sai an fada ba, ya rasa inda zai sa iyayen shi da ‘yan uwan shi. Dr. Sulaiman ya yi bincike sosai kan karatun shi, ya yaba sosai da hazakar da yaron ke nunawa. Kwanan su uku suka wuce Saudiyyah suka yi Umarah, sannan suka dawo gida.

Da albashinta da ta ke tari, da kuma taimakon Dr. Sulaiman, Dr. Fatima Ja’afar, ta bude makarantar Islamiyya ta yara maza da mata a nan Abuja, da aka sanyawa suna NANA HADIZAH ISLAMIYYAH. Haddar Alkur’ani mai girma ake yi tsantsa, sai sauran littattafan addini irin su Ishmawi, Bulugul Maram, Sirah, Hadith, Al-Akhdari, Fikh da koyar da harshen larabci. Ana zuwa daga karfe biyu na rana zuwa shida na yamma.
Ba ta da abin da za ta ce da Dr. kuma Minista, Sulaiman dan Sulaiman, sai godiya da addu’ar alheri, domin ya gama cika mata burinta na son yada ilimin Alkur’ani da hadisi, kamar yadda ta ke buri.
Ya lullube ta da duk wasu alhairori na rayuwa, ya lullube ta da so da kauna. Gaskiyar Babanta ne; Alqur’anin ta ba zai bari ta tozarta ba!!!

Ta san Sulaiman ba ya son ta ya aure ta, kuma ba zai taba son wata diya mace kamar yadda ya so Hadiza ba, amma tana tantama a halin yanzu, idan son da yake mata baiyi kunnen doki da wanda ya yi wa Yayarta Dr. Hadiza ba.

A alfarma ta soyayyah, ta san ba ta cancanci Dr. Sulaiman ya so ta a wancan lokacin ba, amma ya so ta saboda hakuri, juriyar ta da YAKANAR ta. Ya so ta sabida kyawawan halayenta.
“Mene ne YAKANAH?”
Nayi tattaki har gidan Dr. BAKORI na tambayi Malamarmu, Dr. Fatima Ja’afar Mai-Yadi.
Ta yi murmushin ta mai motsa zuciya tace.
“Takori ba ki san Yakanah ba?”
Na ce, “Ina zan sani Fati? Sai ku malaman addini”.
Ta yi murmushi ta ce,
“Nima daliba ce SUMAYYAH! Sai dai in sanar da ke dan abin da na sani a dalibtaka ta”.
Na ce, “daure ki sanar dani Aunty Fati, komi kankantar sa. Domin al’umma zasu so su san me ita wannan kalma ta YAKANAH take nufi?”.
Faty ta yi murmushi tana dubana ;

MECE CE YAKANAH???

Ita YAKANAH ba kasaifai ake ganin ta a wajen yawancin mutane ba, YAKANAH ita ce take daukaka darajar mai yin Ibadah, ta kai shi wani matsayi na daukaka a wajen Allah. YAKANAH ita ce tushen dukkanin aiyuka na gari, wato daukacin ayyukan kirki suna fitowa ne daga cikin ta.
Mutum mai YAKANAH shi ne mai yin babban jihadi ko gwagwarmaya da kansa wajen watsi da abubuwan da rai da zuciya ke so, saboda neman yardar Ubangiji, da neman dadin falalar sa, tare da nuna biyayya a gare shi.
An ambaci irin wadannan mutane a cikin Alkur’ani mai girma, kamar cikin suratul Al-Imran (3:17) Al-Nisa’i (4:25, 127-128), Fussilati (41:34) da sauran su.
Irin wannan babban jihadi da kai ana yin sa ne tsakanin mutum da zuciyar sa (Nafs Al-Ammara), domin sauya ta ya zuwa (Nafs Al-Lawwama), sannan ya zuwa zuciya madaukakiya (Nafs Al-Mutma’innah).
Saboda haka madallah da ita wannan baiwa ta YAKANAH, domin tana kai masu yin Ibadah zuwa ga matakin shiga cikin rukunin salihai wadanda a koyaushe suna masu yin godiya a kan dukkanin abin da ya zo musu daga Allah.
YAKANAH it ce kololiyar taqwa wato tsoron Allah. Takwah kuma ita ce mai kore tsoron haduwa da Allah (wanda ba ya jin kunyar ubangijinsa kuma mai sabon sa, shi ne mai zama cikin fargabar haduwa da Allah).
Daya daga cikin ma’anar YAKANAH ita ce, ka dinga kallon kanka a matsayin kai ba kowa bane a cikin jama’a, kuma kowa ya fi ka, saboda haka YAKANAH tana nuni da rashin kasancewar mutum cikin halin GIRMAN KAI!
Misalai: Idan ka kasance mutum ne kai mai YAKANAH ta gaske, a duk lokacin da ka gamu da wani mutum wanda baka san shi ba, komi lalacewar sa, sai ka ce da kanka a cikin zuciyar ka.
“Watakila matsayin wannan mutum a wajen Allah ya fi nawa”.
Idan kuwa ka gamu da yaro kankani, sai ka cewa kanka, “Ka ga wanda ba ya sabon Allah, ni kuwa ina yi”.
Idan kuwa ka gamu da wanda ya girme ka, sai ka ce, “Ka ga wanda ya jima yana bautar Ubangiji tuntuni kafin ni”.
Idan kuwa ka yi kicibus da mutum mai dimbin ilimi, sai ka ce, “Ga wanda aka yiwa baiwa da abin da ni bani da shi, domin ya fi ni ilimi, kuma yana aiki da ilimin sa, amma ni ko ya ya dai?”
Idan kuwa ka yi karo da jahili, sai ka ce, “Dubi wani yana sabon Allah cikin rashin sani, ni kuma ina yi cikin sani. Ga shi kuma ban san yanda karshen sa zai kasance ba, kuma ban san nawa karshen ba. Ko me zai zama a nan gaba? Allah shi ya fi kowa sani”.
Idan kuwa ka gamu da kafiri, sai ka ce da kanka, “Wa ya sani? Watakila nan gaba ya musulunta kafin ya mutu, kuma wa ya sani ko ni kuma in mutu a kafirce?”
Ire-iren wadannan maganganun gaba daya suna nuni da halin mutumin da YAKANAH da tawali’u suka baibaye shi, yake kuma cikin hali na binciken kansa a koyaushe.
Dalilin irin wannan tunani a zuciyar wannan bawan Allah shi ne, yana cikin yanayi na rashin yarda da kansa. Tare da rashin tabbas game da abin da zai abku wajen haduwar sa da Allah.
Ire-iren wadannan tunani kuwa suna nuna karfin imani ne da dogaro da Allah madaukakin sarki wanda shi ne tushen kaskantar da kai.
A kowanne lokaci idan bawa ya kaskantar da kansa, Allah zai kare shi daga masifu, kuma ya ba shi sirrin “Ikhlasi” Wato nacewa da son bin hakikar gaskiya a dukkannin al’amuransa na yau da kullum. Daga wannan mataki ne mutum zai kasance cikin mutane ‘yan kadan wadanda suka samu yardar Allah tare da kusanci da shi.
YAKANAH ita ce kofar da ake bi ta cikinta zuwa wurin da baiwar Allah da rahamar sa suke muhimmancin YAKANAH ga musulmi kamar kwatankwacin bargo ne a cikin kashi.
YAKANAH tana a matsayin bargo na Ibadah, kuma sauran ayyuka suna a matsayi na kashi. Bayin Allah wadanda ake kira ‘zahideen’ masu cike da da’a da tsantsenin duniya, tare da ‘nasiqeen’ masu sadaukar da rayuwar su domin bautar Ubangiji, dukkannin su suna ji da wannan baiwa ta YAKANAH.
Bayin Allah masu YAKANAH basa yin maganganu barkatai, basa yin tsegumi ko wata muguwar magana a game da wani a bayan idanun sa, su kan fadi abin alheri ne a game da shi. Ba sa shiga sharo ba shanu, kuma zuciyar su fes take. Ta kuma nisanta da miyagun dabi’u, kamar hargowa da JI DA KAI. Wato kirjin irin wadannan bayin Allah garau yake.
Duk maganar da irin wadannan bayin Allah masu YAKANAH suka fadi, ta dace dai-dai da abin da suka yi, suka kuma yi imani da shi.
Basu da wani abu da za su boye a zuciyar su domin kada wani ya sani, wato basu da wani mummunan abu a tare dasu.
Bayin Allah ne masu zallar gaskiya da rikon ta, wanda duk ya yi hulda da irin su zai ga cewa basa fafutukar neman kuskure a kan wani, maimakon haka, a shirye suke wajen neman kuskure daga wajen su, wato a kan kansu.
Basa yarda su zauna tare da (marada) (masu kawo tsegumi). Don haka ‘yan uwa musulmi mu yi damara da kokarin kasancewa cikin bayi masu YAKANAH, mu rike addininmu, mu kama Alqur’anin mu, mu suturce jikinmu, mu tsayar da sallah domin samun dacewa a duniya da lahira. Kamar jarumar wannan littafi, Allah ya bamu iko amin summa amin.
Takori..

: Agogon ‘alarm’ da ke gefen makeken gadon ya buga karfe shidda dai-dai na safe, Dr. Hadizah wadda ke kwance a gadon doguwa ce ba can ba, irin tsayin nan gare ta mai tsari da ban sha'awa. Tana sanye cikin rigar barci mai santsi fara sol. Ta yi mika a hankali tare da koro addu'ar (Alhamdulillahil lazee ahyana, ba'ada ma amatana wa ilaihin nushour). Ta mika hannu side din da maigidanta ke kwance, wayam! Tayi hanzarin mikewa daga kwanciyar don a zatonta, ta makara.
Daga can kitchen ta jiyo motsin mai aikinsu Goggo Alti tana karakaina da kwanuka. Tana shirin mikewa ta ji motsin maigidanta Sulayman a shower, don haka ta yi ajiyar zuciya mai sanyi, a kalla ko ta makara kadan ne. Ita ma ta fada bandakin don ta taimaka mishi wajen wanka kamar yadda yake a al’adarsu.
Wasu ma’aurata ne wadanda samun masoyan da suka shaqu da juna suka kuma yarda da juna, suka aminta da juna, suke matukar kaunar junansu kamarsu a wannan zamanin zai yi wuya.
Suka fito kowane daure da towell, shi iya kugun shi ita iya cinyoyin ta. Jiki ne da ita lukui-lukui kamar atafa. Jiki ne da shi na MANYA, kuma kasaitattun maza, wadanda suka dama, suka kutsa cikin manyan ilimummuka daban-daban.
Yana da duhu, amma duhun mazan Marocco ne. Dogo ne sosai ma'abocin karfi da kyawun sura ta ko’ina. Idan baka san asalin shi ba, za ka yi tsammanin ya fito ne daga Sirreleone, amma a zahiri Bakatsine ne dan asalin garin Bakori. Wanda Bakorin ta bi sunan shi, ta boye Sulayman-Sulayman din, ake kiran shi Dr. Bakori.
Ta bude wardrove ta dauko mishi bakaken Spanish-Suit mai hade da farin tie mai santsi. Ita kuma ta fiddo wata atamfa super shudiya mai ratsin rowan hoda da hasken sararin samaniya, riga, zane da kallabin su, ta dora da farar rigar su ta likitoci. Tuni ta fito a Dr. Hadizarta. Tana tsuke mishi tie ya ja zankalelen dogon karan hancinta in appreciation din (cike da jin dadin) irin kulawar da take mishi. Ya ce
"Allah ya bar min ke Dr. D.Z". Ta ce
"….Ya bar min kai nima, likitan zuciyata…..". Ta manna mishi kyakkyawar sumba a kirji, kasancewar ya kere ta a tsaho, ita iya kirjin shi ce. Ta dauko tashi rigar likitocin ta zagaya ta bayan shi ta rufa mishi, ya zura hannun shi kana a hankali ya janyo ta ya rungume ta. Sun dau tsawon lokaci a hakan, suna sakin ajiyar zuciya mai sanyi cike da matsananciyar kauna wadda biro ba zai iya rubutawa ba, kamin su saki juna ba don sun so ba, sai don tunanin dimbin al'umma masu larura da suka yi sammako suke jiran su.
Sai da suka gama kammalawa tsaf sannan suka fito, tana rike da gilashin idonta a hannu, yayin da shi yake rike da jakarta da brief case din shi. Kai tsaye dakin yaransu suka nufa, inda suka tarar tuni Alti ta shirya su tsaf, kasancewar yau garin an tashi da lullumin sanyi mai tsanani ya sanya ta sanya musu rigar sanyi mai kauri a ciki, ta sanya musu fararen socks ta rufe musu kafafu cikin farin cambas.
Yaran su biyu ne mace da namiji, namijin dan kimanin shekaru hudu, macen 'yar kimanin shekaru biyu da kadan. Dole in ka gansu sai ka sake marmarin kallon su, sun kuma baka sha'awa.
Munib sak Babansa, yayin da Muniba komi nata na Dr, Hadiza ne. To ba Mamin ba, ba Daddyn ba, kowanne ji yake da kyau tamkar shi ya yi kansa. Akwai shakuwa, fahimta da soyayya mai yawa a tsakanin wannan family.
Hadiza ta rage tsawo ta russuna ta rungume diyarta Muniba,
"Gud morning my dear......."
"Morning Mummy….".
Munib ma ya ce
"Gud morning Daddy…..".
Ya amsa da
"Morning my Munib, an tashi lafiya?"
Su dukka suka nufi tebir domin yin kalaci.

Goggo Alti ta fito daga kitchen za ta wuce bangaren ta, daga Hadiza har Sulayman suka gaishe ta, kamin ita ta gaida su. Wannan dabi'arsu ce da ke karawa dattijuwar jin dadin zama dasu, saboda yadda suke ba ta girma kamar ba a karkashin su take ci ba. Hakan ne yake kara mata himmar kula musu da yaransu saboda Allah.
Hadiza ta bude ma'adanan abincin ta soma serving kowannen su da abinda yake so. Sinasir ne da miyar ganye, sai farfesun kayan ciki, sai kuma soyayyen dankali da kwai domin su Munib da bazasu iya cin mai nauyin ba.
Ga al'adarsu sun fi cin abinci mai nauyi da safe, don ba za su kara ci ba sai dare in sun dawo aiki, sai 'yan ciye-ciye da ba a rasa ba a office.
Hankalin Dr. Sulaiman yana kan 'ya'yan shi, sai da ya tabbatar sun koshi sannan ya ci nasa. Zuwa bakwai da rabi sun gama komai sun fito, suka yiwa Goggo Alti sallama suka wuce rumfar adana motocin su.
Akwai motoci har guda uku, daya ta Sulaiman, daya ta Hadiza, daya ta amfanin gida. Sai da suka aje yaran a makarantar su (Maitama Sule) da ke dab da asibitin da suke, wato (AKTH) sannan suka karasa cikin asibiti, kowanne ya nufi bangaren sa.

Dr. SULAIMAN-SULAIMAN BAKORI shi ne consultant na (cardiology), yayin da Dr. Hadiza Ja'afar Mai-Yadi take likitar mata wato (gynaec) a labour ward take. Sai da ya fara sauke ta sannan ya wuce ofishinsa, ya soma attending dimbin cases din da ke gabansa.
Karfe sha biyu na rana ya zame ya je ya debo yara ya kai ma Goggo Alti, sannan ya dawo. Wannan shi ne tsarin rayuwar su a kullum.
***







Shekarun su biyar kenan da aure, amma har zuwa inda yau ke motsi, babu abinda ya canza na daga soyayyar da suke yiwa juna, sai ma abin da ya karu.
Hadiza dalibar shi ce irin yaran likitocin nan da ake koyarwa a (teaching hospital). Ya fahimce ta yarinya ce mai matukar kwazo a tsakanin tsararrakin ta. Wani abin mamaki da ya fara bincike a kanta 'yar talakawa ce likis, amma iyayenta sun tsaya tsayin daka wajen daukar nauyin karatun ta, duk da tsadar shi kuwa, da dukkan iyawarsu.
Soyayya ce mai tsabta irin ta wadanda suka wadata da ilimi suka gudanar kamin aure. Ga Hadizah ba karamar sa'a ba ce, kuma ba karamin abin alfahari bane samun mutun kaman Sulayman (as a husband). To haka shi ma.
Hadiza ta tara duk wasu qualities da yake nema ga diya mace, ga dai kyau ga kyan hali, ga addini da kyakkyawar zuciya, sannan uwa uba ta samu ingantacciyar tarbiyya daga iyayen kwarai.
Iyayenta suna nan a unguwar Karkasara dake cikin birnin Kano, sana'ar mahaifinta shi ne yadiddika yake sayarwa, yana da shago a nan kantin Kwari.
Hadiza ita ce ta biyu a cikin 'ya'yan gidansu, akwai Yayanta Mukhtar wanda ke aiki da (Zenith Bank) a Kaduna, kusan da tallafin shi ne Hadiza ta samu ta kammala karatun ta.
Duk da haka shi ma mahaifinsu a tsaye yake a kan karatun su, don yaga amfanin da karatun yayiwa Mukhtar. Sai kanwar ta Fati, budurwa ce 'yar kimanin shekaru sha bakwai, a bana ne ta kammala karatun sakandire. Sai Hamza da Yusuf, da dan autan su Abdulyassar.
Duk cikin kannenta Hadiza ta fi son Fati, wata irin yarinya ce mai sanyin hali, sanyin kyau da sassanyar zuciya. Akwai wata irin shakuwa ta musamman tsakanin Hadiza da 'yar uwarta Fati. Jininsu ya hadu sosai ta yadda Hadiza ba ta iya shawara da kowa kan al'amuranta kamar Fati saboda hankalin ta.
Fati yarinya ce mai tsananin son addini da nutsuwa, ba ta da rawar kai ko kadan irin na 'yammatan zamanin nan, komi nata cikin hankali da nutsuwa yake. Ita da Hadiza kamar an tsaga kara, sai dai Hadiza fara ce sol, yayin da Fati ta kasance wankan tarwada. Amma hatta yanayin tafiyar su da murmushin su iri daya ne.

****


Sulaiman – Sulayman Bakori, mutumin garin Bakori ne ta jihar Katsina, daga kallo na farko mawuyaci ne ka bambance daga kabilar da ya fito, wani mutum ma'abocin cikar zati da kamala da duk wani nau'in daidaito na rayuwa, ga dimbin ilimi a cikin fannonin kiwon lafiya daban-daban. Ya ci sunan mahaifinshi ne don haka a gidan su ake kiran shi mai sunan Malam.
Mahaifin shi Malam Sulaiman, Malami ne mai karantarwa, yana baiwa magidanta anguwar su karatun buzu. Duk wani da ya kwana ya tashi a garin Bakori ya san Malam Sulaiman Mai-Gafaka. Mutum ne da al'ummarsa ke matukar ganin girman sa, kuma ya yi fice a garin Bakori baki daya saboda ilimin da Allah ya ba shi, kowa yana daraja shi.
Shi ne da na biyu a gidansu, yayar shi Jummai ta rasu wajen haihuwar fari, sai kannen shi Ramatu, Saude da Ruma, duk suna gidan aure. Sai Khalid wanda ke karatun sakandire a halin yanzu.
Sulaiman ya yi dukkan karatun shi ne da taimakon gwamnati da mahaifiyar shi Inna Halima, wadda duk lokacin da hidimar karatun ta tashi take fitar da kadararta ta siyar ta yi masa. In dan ta Malam ne sakandire ma kawai ta isa. Burinsa Sulayman ya zauna a gida ya tallafa mishi kasuwancin shi na fata, ya yi aure ya haifa mishi jikoki shi kuma zai yi masa komai.
Amma Sulaiman ya ki, ya dage ga son cimma burinsa na son zama likita. Ba abin da yake so a rayuwar shi irin yau a ce ya zama likita yana yiwa mutane allura.
Irin yaran nan ne gifted tun suna kanana, wato 'yan baiwa. Wata irin kwakwalwa gare shi da ba duk mutane Allah yake baiwa ba, duk inda yayi karatu malaman shi sai sun san shi, sun kuma ja shi a jiki, sun so shi saboda hazakar shi.
Ya yi gaba dayan karatun shi daga jami'ar Najeriya (NSUKKA). Bayan ya kammala MBBS din shi ya yi nasarar samun scholarship zuwa jami'ar (Manchester) inda ya yi specializing a kan zuciya da duk abin da ya shafe ta. Bayan kammalawar shi da dawowar shi ya soma aiki da federal Government, hakan ne ya sa ake yawan canza mishi wajen aiki. Daga wannan gari zuwa wancan cikin jihohin Najeriya.
Ya fara ne da aiki a babbn asibitin koyarwa na Ibadan, daga baya suka mai da shi ABU Teaching Hospital. Nan din bai dade ba suka dawo da shi nan AKTH na Kano, inda Allah ya hada shi da Hadizah.


HADUWAR SULAIMAN DA HADIZA
Haduwar su haduwa ce special kuma haduwa ba ta dadi ba. Yana tare da patient da ya yiwa aiki satin da ya wuce, Hadizah Ja'afar, da wasu abokan karatun ta suka shigo domin daukar lacca kamar yadda suka saba. A matsayinsa na consultant dinsu, basu samu kallo daga gareshi ba, balle ya tantance kamannin su, kasancewar Allah bai dora mishi lalurar yiwa mata kallon kurilla ba. Tsakanin shi da kowacce diya mace, kallo daya ne, da kau da kai. Wannan a jinin Sulaiman yake.
Suka samu kujeru suka zauna, kowacce da jotter din ta da biro a hannu. Yana ta yi musu bayani cikin lafiyayyen turancinshi na Birtaniya mara surki, wani zubin ya yiwa mara lafiyar tambaya ta ba shi amsa.
Wata amsa da patient din ta bayar ta sanya su murmushi dukkanin su (ban da Hadiza), cikin kalaman ta za ka fahimci kwakwalwarta ta tabu sakamakon bacin zuciya da damuwa.
Ta ce,
"Likita nifa 'yar sarauta ce ba mara lafiya ba!".
(Wannan ne ya sanya su yin murmushi). Ya ce,
"Wacce sarauta gare ki don mu fara girmama ki?"
Gaba daya daliban suka yi dariya don yadda yake biye ma shirmen matar dole ya baka dariya. Ta ce,
"Sarautar Kano gare ni".
Ya ce, "Wacce ke nan?" Ta ce,
"Nice 'yar ruwatan Kano".
Gaba daya suka yi murmushi, wannan karon ma ban da Hadizah, wadda a lokacin hankalinta baya tare dasu, yana ga halin da ta baro Mamansu a ciki na rashin lafiya mai tsanani.
Ba zato Dr. Bakori ya jefo tambaya, "Mene ne delusion?" Ya kuma nuna Hadiza da ya lura hankalinta ba ya tare da shi matsayin wadda za ta amsa mishi tambayar shi.
Ya yi mata magana ya kai sau uku ba

2 Comments On YAKANAH
avatar
rabiatu-2

1 year ago

Reply

Thanks

avatar
fatima-2-7-5

1 year ago

Reply

very nice book

Please Login or Register in order to submit comment