Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ji my kids?”
Suka yi murmushi sannan ta karasa ta russuna ta gai da Yayanta, wanda suke ta hirar su shi da Sulaiman, ta nufi firjin kitchen ta kawo mishi lemon (Donsimon) da gorar ruwan (Eva) mai rangwamen sanyi.
Mukhtar bai dade ba ya yi musu sallama ya tafi. Bayan ya karbi lambar Fati. Tana so ta karbi Nana amma tana bisa cinyoyin sa, ta fara kuka don ta dade ba ta sha madara ba.
Dole ya mika mata ita, hannuwan su suka saka kara gogewa dana juna. Wasu irin hannuwa gareta masu bala’in taushi kamar auduga, wadanda suka tada tsigogin jikinsa. Ita kuma suka haifar mata da kasala irin wadda ta ji a ranar da hannun ta ya fara shafar nasa.
A hanzarce ya mike, “Oya kids! Muje mu sha (Ice-cream)”.
Suka yi tsalle suka dane kafadun shi, Munib ya ce,
“Amma har da Anti Fati za mu je?”
Ya yi kamar bai ji shi ba, ita dai jakar kayan su ta dauka ta yi ciki da Nana a hannun ta. Ya sunkuci yaran shi duka biyun a kowanne hannu daya du girmansu, suka yi waje.
Dama tana da tafasasshen ruwa cikin filas a kitchen, nan da nan ta dama madara ta soma baiwa Nana bayan ta sha iska.

****
10/15/21, 11:47 AM - Buhainat: 2
Karfe goma sha dayan dare garin Kano ya yi tsit, sai iskar hunturu da ke kadawa. Malam Ja'afar ya dauko tabarmar sa ya shigo cikin gida daga soron kofar gida.
Zai gifta ta dakin Fati ya jiyo shesshekar kukan ta, ya dakata ya daga labulen yana kallon ta, tana zaune a kan darduma ta kunshe fuskar ta cikin hijabi sai kuka take.
Ya karasa shigowa cikin dakin ya ce,
"Fadimatu kukan me kike yi?"
A razane ta cira kai ta dube shi idanunta jawur, sun yi luhu-luhu alamar ta yi kuka har ta gode Allah. Malam Ja'afar ya zauna a wata 'yar kujera da ke dakin yana fuskantar diyar sa. Nanah ta soma motsi alamun za ta tashi daga barcinta, ta soma rirriga ta.
Ya jima bai yi magana ba sai da Nana ta koma barcin ta ya ce,
"Gaya min damuwar ki Fadimatu, ni mahaifin ki ne".
Ta share idon ta da hankici, ta ja shessheka kafin ta ce,
"Baba babu komi".
Ya jima yana kallon ta, sannan ya yi murmushi ya ce,
"Kina tuhumar mu da yi miki auren da baki so, auren mijin 'yar uwar ki. Ki yi hakuri, alheri muke nufin ku da shi, ba za ku gane ba sai nan gaba, idan kun gano gatan da muka yiwa rayuwar ku".

Fati ta yi shiru tana sauraron Baban su, ta ga cewa wannan ita ce damarta ta karshe, daga gobe za a zarga mata igiyoyin wanda ta tabbatar ba ya son ta. Ta kai kanta kasa tana kuka sosai, ta ce,
"Ku yi min alfarma Baba, Baba baka taba sani in yi wani abu na shallake maganar ka ba, amma a wannan karon, ina so ka duba hujjojina.
Baba Dr. Sulaiman ba ya sona, Baba Dr. Sulaiman ya fi karfina, bani da ilimin da zan jera da shi a matsayin matarsa. Baba Sulaiman ba zai taba son wata ba, bayan son da yake yiwa Yaya Hadiza. Baba kune baku sani ba, amma Dr. Sulaiman tun fil azal ya tsane ni, ban san laifin da na yi masa ba.
Ban taba gaishe shi ya amsa ba, haka bai taba duba na a matsayin jinin Hadiza ba, balle ya yi la'akari da wannan ya kaunace ni. In dai don 'ya'yan shi ne ai nima 'ya'yana ne, zan ci gaba da rike su ba sai na zama matarsa ba".
Ya ce,
"Amma za ki zama matar wani ko? Kuma babu wanda zai aure ki da zugar 'ya'yan Yayar ki? Da ‘yar uwarki ta damka miki amanarsu?
Na ji hujjojin ki Fati, na kuma yarda bazaki yi mun karya ba, amma nima ina so in tambaye ki.
Wane abu ne Hadiza take da shi wanda ya kaita ga matakin zama matar babban likita irin Sulaiman? Tana 'yar talakawa kuma mace kamar ki?"
Babu dogon tunani ta ce,
"Ilimi".
Ya ce,
"A ina ta samu?"
Ta ce,
"Fita ta yi ta nema".
Ya ce, "In haka ne ke mai zai hana kema ki fita ki nema?'
Ta ce,
"Ba zan iya irin nata ba!"
Ya yi murmushi ya ce,
"Duk ilimi sunan sa ilimi, balle ilimin ki ya fi na kowa, yafi na komai, ilimin Alkur'ani ne da ke wanda ya kunshi dukkan rayuwar duniya da lahira baki dayan ta, ke din nan ba abar wulakantawa ba ce 'yar baiwa ce, mahaddaciyar Alkur'ani, wallahi-wallahi a rayuwar duniya da lahira ba za ki tozarta ba.
Sannan don kina gaishe shi bai amsa ba, sai ki ce ba ya son ki? Me kika yi masa? Mutum ne mai kyakkyawar zuciya, shekaru dai-dai har bakwai da nayi tare da shi ban taba ganin wata halayya ta banza a tare da shi ba.
Tunda ya auri 'yar uwar ki ba’a taba jin kansu ba, ba ta taba yin yaji ba, ba ta taba kawo karar shi ba. Sai ki yi tunanin me Hadiza ta yi ta samu wannan mafificiyar soyayya a zuciyar mijinta, tunda kin zauna da ita, kema ki kwatanta ko ba duka ba, ki gani idan ba za ki samu ba?".
Ta share ido ta ce,
"Baba ai ni gani na yake 'yar kauye, ga shi ni kuma ba zan iya yin irin rayuwar su ba. Mai ya sa ba za ka gane ba? Banida abinda zan burge shi da shi. Don Allah Baba ka aura min ko wane ne, komi yawan matansa da yawan shekarun sa, na rantse zan zauna da shi, amma kada ka kai ni inda ba zan yi kwarjini ba, inda za a wulakanta ni, inda ba za a so ni ba….".

Ya yi murmushi ya ce, "Babu inda zan kai ki sai gidan SULAIMAN! Na kuma tabbatar miki ko a yanzu bai son ki, watarana na zuwa da za ya so ki. Kamar, ko ma fiye da yadda yake son 'yar uwarki.
Daina kukan nan kada ya haddasa miki ciwo, a duk sanda ki kai sujjada cikin sallolin farilla ki ce, "Allah ka sanya soyayyata a zuciyar mijina". Za ki sha mamaki Fadima, ki sanyawa zuciyar ki salama, shi da yake namiji bai bijirewa iyayen shi ba sai ke? A'a kada mu yi haka da ke Fadimatu, na san ki, na san halin ki, na tabbata ba za ki bani kunya ba.
Ki yi min alkawarin za ki zauna lafiya da mijin ki, ki yi min alkawarin za ki yi mishi biyayya, ki yi min alkawarin za ki ba shi soyayya irin wadda shakikiyar ki ke ba shi, ki yi min alkawarin ba za ki taba kai karar shi wani waje ba, ke ko mu din nan ban yarda ki kawo karar shi gare mu ba, balle iyayen shi.
Duk abin da ya yi miki na rashin dadi ki yi hakuri, ki yafe mishi cikin zuciyar ki, ki yi mishi uzuri. Wannan halin YAKANAH kenan! Sakayyar ki na wurin Allah!!".
Tana kuka sosai ta ce, "Na ji Baba, kuma na yi maka alkawari".
Ya dora hannu a kanta,
"To Allah ya yi miki albarka, ya ba ki juriyar rike 'ya'yan ki, ya sa suma mahaddata alkur'ani ne kamar ki. Tashi ki dauro alwala ki ci gaba da neman yardar Allah da yardar mijin ki".

****









Dr.Sulaiman yana tuki amma hankalinsa ba ya jikinsa, in banda tafasa babu abin da zuciyarsa ke yi, amma kamar wanda aka dinkewa baki ya kasa ce da iyayen shi komi wadanda ke ta hirarrakin su a kan karamcin iyayen Hadiza.
Har suka iso gida ya kai su bangaren da ya tanada don bakin kwana, wanda ke daga wajen gidan. Inna kuma ta wuce dakin da yake na Hadiza.
Ya fada toilet ya yo wanka, yana alwala cikin sink sai jini ya balle mishi ta hanci. Haka ya tsaya yai ta kwararar da habon (nasal bleeding), yana bin shi da ruwa yana wucewa. A duk lokacin da yake cikin takurar zuciya habo yake yi, ya soma yiwa kanshi taimakon gaggawa har jinin ya tsaya. Ya fito ‘bed room’ din su wanda ya zama kaca-kaca saboda rashin gyara, ya dauko wata rigar barcin Hadiza ya kwanta rigingine, ya dora rigar a kan fuskar shi yana shakar kamshin Hadizah na dindindin na turaren 'escada-sentiment'. So da kaunar matar shi ke dawainiya da shi. Ya lumshe ido ya shafo makwancin ta, katon fili ya yi mishi sallama, wasu irin dumammun hawaye, suka mirgino ta gefen idon sa.

A sannan ne tunanin shirmamman auran da za a yi mishi a gobe ya dawo mishi cikin kwanya, Eh! Shirmamme mana, don bai dauki wannan auren da sunan aure ba.
Amma a yadda Inna da Malam suka sanya ransu da zuciyar su a auren nan in ya ce baya yi ya tabbata zai bata goma ne daya ba ta gyaru ba, don za su yi fushi da shi, sannan kuma ba za su fasa ba. Don Malam bai yin magana biyu, sannan ransu za ya baci, kuma ba za su taba shiryawa da shi ba.
Don haka maganar ya je ya ce da Inna bai yarda ba, ko bai amince ba, kamar yadda zuciyar shi ke ta kimsa mishi ba ta ma taso ba. Illa ya zuba musu ido su yi yadda suke so.
Sai dai ya san yadda suka kawo yarinya, haka za su zo su dauki abar su. Shi mijin mace daya ne a duniya da lahira (Hadizah). Bayan ita bashi da sauran bukatar komi daga kowacce diya mace, balle kanwarta duk da Allah ya halarta, amma ai da kunya, ya hada rayuwa da kanwar Hadiza, balle wannan yarinyar da bai san irin ta ba, sannan Allah subhana bai halicci zuciyar sa da kaunar ta ba.
Ba kilin (clean) ba isasshen wanka a jikinta, balle aje ga ado irin na 'ya'ya mata. Kullum cikin tsummokara! Yo tsummokara mana? Kyawun surar ta ya tashi a banza tunda ba ta san yadda za ta yi ta gyara kanta ba.
Shi duk ma ba wannan ya dame shi ba, kawai ranshi baya son Fatima Ja'afar, duk da kasancewar ta kanwar Hadiza. Jikinsa ya sha ba shi akwai wani al'amari mai GIRMA tsakanin shi da yarinyar, tun daga sanda ya fara ganin ta, cikin kwayar idanunsu wani ‘chemistry’ mai girma ya afku rana ta farko da ya ganta matsayin kanwar Hadiza, amma bai taba kawowa cewa aure ne ba.

Yadda Fati ta kwana ido biyu, haka Dr. Sulaiman ya kwana ido biyu, kowannen su zuciya na zugi. Sai dai ita Fati ba ta kin al'amarin musamman in ta tuna da alkawarin da ta daukar wa 'yar uwarta. Damuwar ta shi ne Sulaiman ba ya son ta, da dan karen tsoron zama dashi dankare a zuciyar ta.
Shi kuwa tunanin yadda zai yi ya tsallake auren yake ba tare da ya batawa iyayen shi ba, ya san a sake dai bai isa ya ce ya saki ba. Daga karshe ya yanke wa kansa shawarar da yake ganin ita ce za ta fissheshi. Don haka ya dan samu sa'idar da ya kwanta ya runtsa idon sa.
Kwanciyar sa ke da wuya aka soma kiraye-kirayen sallar asubahi. Ya dauro alwala ya gabatar da raka'atainil fijri, kamin ya dora da farillar. Ya yi addu'o'in shi ya koma ya kwanta.

Zuwa bakwai ya tashi ya feso wanka ya debi koriyar Getzner sabuwa kar sai sheki take, ya fesa turare ya zuba hular kube, ya fito kamar saurayi dan shekaru ashirin da bakwai, ba za ka ce shi ne ya aje su Munib ba, zuciyar shi wasai da hukuncin da ya yankewa zuciyar shi.
Ya fito ya janyo kofar ya iso falo, nan ya tarar da Inna ta hada musu kalaci, kunun gyada da dafadukan taliya, kasancewar a gurguje ta yi don dai ya samu ya ci wani abu kafin ya fita. Ya je ya shigo da su Malam suka yi kalacin gaba daya. Daga nan suka nufo Karkasara.

Kofar gidan Malam Ja'afar ya cika makil da jama'a wadanda suka zo addu'ar arba'in din Dr. Hadiza, aka rarraba pieces *na alkur'ani aka yi mata sauka, aka yi addu'o'i na musamman.
Daga nan kafin mutane su watse, waliyyai suka gabatar da daurin auren Dr. Sulaiman Sulaiman Bakori, da Fatima Ja'afar Mai-Yadi, a kan sadaki naira dubu ishirin kacal. Mutane suka yi ta mamaki tare da sanya albarka, domin an yi koyi da fadar ma'aiki (S.A.W).

Malam Ja'afar ya dubi Inna Halima ya ce, "Babu bukatar wata bidi'a, gobe Sulaiman ya zo ya dau matarsa da 'ya'yan shi su tafi, Allah ya yi musu albarka".
Fati da ke uwar dakin Yaya tana jin duk abin da ke faruwa a gidan, ta takure a bayan labule sai gursheken kuka take, goye da 'yarta sai makyarkyata take. Ta rasa inda za ta sa ranta ta ji dadi, shin rayuwarta da wadda za ta je ta tarar wace irin rayuwa ce? Shin meye makomar rayuwar ta?
Ta tabbata, kuma a ko’ina za ta yi rantsuwa a kan cewa Sulaiman bai son ta. Takura mishi aka yi. Yaya Hadiza ta dora mata nauyi, da kananan shekarun ta ba za su iya saukewa ba. Amma in ta tuno nasihar da Baban su ya yi mata a daren jiya, sai ta ji sanyi a ranta.
Jin Inna na neman ta, ta yi saurin shigewa toilet. Inna ta daga labule ba ta ganta ba, ta ce da Yaya “bata nan, watakil ta shiga bayi”.
Daga nan suka ci gaba da hira ita da Yaya a kan maganar lefe, ta ce za ta sa su Ruma su hado ko gidanta ne a kai mata.
Yaya ta kafe a kan cewa wallahi sun yafe, ko tsinken Sulaiman ba za su karba ba. An riga an zama daya sai dai su bi yara da addu'a. Amma Inna ta kudire a ranta sai an yiwa Fati lefe irin wanda ake yiwa kowacce yarinya budurwa.
Sai da su Inna suka bar gidan sannan Fati ta fito daga maboyar ta, makota na ta shigowa suna yiwa Yaya ta'aziyya da Allah ya sanya alheri. Ta nufi dakinta ta shimfidar da Nana, sannan ta kwanta a gefen ta ba laka a jikinta.
Yaya ta shigo rike da kwanon silba da damammiyar fura mai sanyi, ta zauna a gefen ta tana kallon yadda duk ta zuge kwana daya kacal.
Ta ce, "Ungo fura tashi shanye ki bani kwanon".
Ta girgiza kai, "Bana son cin komi".
Yaya ta ce,
"Haka za ki daure ki dura, zama da yunwa da bacin rai ba naki bane, tunda dai auren nan an riga an daura ya kuma dauru, sai ki saki ranki ki watsar da duk wani tunani wanda zai hana miki kwanciyar hankali. Karbi na ce".
Ta tashi zaune ta amsa, ta kafa kai tana sha tare da kokarin maida kukan da ya taho mata a dalilin furucin Yaya,
"Aure ne an riga an daura kuma ya dauru….". Wato dai da gaske ta zama matar Dr. Sulaiman mijin Yayarta.
Sai da ta shanye furar ta share hawaye da 'yan yatsunta, Yaya ta ce, "Kukan dai? Sai ki yi ta yi tunda kin ga shi zai fisshe ki. Haba, ayi yarinya da shegen kuka kamar Muniba? Yanzu ki tashi ki je ki yi wanka, ki sa kaya masu kyau ki je a wanke miki wannan dankararren gashin naki da yau kwana arba'in ba ki tsefe shi ba. Ko ni uwar Hadiza ban takura rayuwata yadda kika takura taki ba. Gobe za su zo su dauke ki, don Allah ki dan gyara kanki yadda za ki yi kyan gani, ki aje hijabin nan haka ki yiwa mijinki kwalliya.......".
Ai kuwa sai ta balle da kuka, "Ni wallahi ba inda za ni, ni wallahi bana son sa...........".
Yaya ta bige mata baki ta ce,
"Don Allah in an kaiki ki sha poison kema ki mutu, ba zan kasa rayuwa ba!!!".
Ta juya ta fita.

Ta tabbatar ran Yaya yai matukar baci tunda har ta yi wannan furucin, tana kuka ta taso ta biyo ta dakinta, tana zaune a kujera ta yi tagumi. Ta zube a gabanta ta kama kafarta cikin rishin kuka ta ce,
"Don Allah Yaya ki yi hakuri ki yafe min, wallahi ba zan kara ba".
Ta ce, "Ni me ki kai min da za ki bani hakuri? Ke aka yiwa laifi ke za a bawa hakuri. Me kika fishi ko me kike takama da shi da za ki ce bakya son sa?
Ban da Allah ya kashe ya baki ai Sulaiman ba tsaran ki bane, ba za ki gano gatan da aka yi muku dukkanin ku ba sai nan gaba. Wannan shi ne karshen kauna da za ki nunawa Hadizah, ki rungumi iyalinta a bayanta, sai dai in dama ba son ta kike yi ba........!"
Ta kara sautin kukan ta,
"Na tuba Yaya, na bi Allah na bi ku, na yarda zan zauna da Baban Munib ko ba ya so na.......".
"Shi ya ce miki ba ya son ki? Bana son mummunar fahimta, ko bai miki son soyayya ta aure ba, yana yi miki son 'yan'uwantaka, wadda a hankali in kin sadaukar da kanki gare shi za ta rikide ta koma soyayyah!.
Sanda aka aura min mahaifin ku ban san shi ba, ban taba ganin sa ba. Haka aka lullube ni aka kawo ni, ko sunana bai sani ba nima ban san nashi ba. Amma kyautatawa da sadaukar da kai ya sa a yau ba abin da muke so da kauna sama da junan mu, har muka kai ga haifar ku daya bayan daya. Kina gani har yau bai taba yi min kishiya ba, bai taba bata min rai ba sai bisa kuskure.
Bacin raina na nufin tashin hankalinsa, fushina na nufin tabarbarewar al'amuransa. Ki yi auren BIYAYYA ba SOYAYYA ba ki ga wacce irin riba za ki samu a cikin sa? Idan mun san babu riba ba zamu ba ki jarin ba".

Fati ta share hawayen ta, cikin zuciyar ta tana cewa, mazan da dana yanzu ai ba daya bane Yaya! Balle wadannan da suka hantse cikin ilmummukan zamani masu gigitarwa, suka saba ganin mata iri-iri dai-dai da tsarin rayuwar su. Ina zan iya burge shi balle har ya kaunace ni? Ina zan iya mai da kaina irin Yaya Hadiza?
10/15/21, 11:47 AM - Buhainat: Kayan cefanen su sun kare, ba ta san ya za tai ta gaya mishi ba, saboda irin yadda yake bi ya daure fuska kamar wani soja idan ya ganta.
Fati na mamakin wannan wace irin kiyayya ce Sulaiman yake mata ta babu gaira babu dalili?
Kamar ita ce ta kashe Hadiza?

Yana da wata kima a idon ta kasancewar shi wanda ya auri ‘yar uwarta da ba ta da ya ita a duniya, ya zauna da ita, ya rayu da ita cikin so da kauna da kyautatawa har ta koma ga mahaliccin ta, ba ta taba fadan laifin sa ko aibunsa ba, ko wani abu da ya yi mata na rashin dadi.
Sannan da kasancewar shi Baban ‘ya’yan da take so sama da komi a duniya. Idan ba zai so ta ba ai ta ci albarkacin Hadiza.
Amma yadda yake nunawa kamar ko a hanya basu taba hada wata alaka ba, idan ta biyewa wulakancin da yake mata ta ce za ta dinga bata ranta a banza, ita ce za ta cutu, ta dorawa kanta ciwon zuciya da hawan jinin da ko duba ta ba zai yi ba, balle ya rubuta mata magani.
Don haka ta debe tsoro da shakku, bayan sun dawo yana kwance a falo yaran shi sun baibaye shi suna ta yi mishi tadi, shi kuma yana aiki cikin kwamfutar da ke bisa ruwan cikin sa.
Ta lallabo ta fito uwa munafuka, tana goye da Nana ta rabe a gefe, Muniba ta taho ta zauna a cinyar ta. Sai a lokacin ya ankara da shigowar ta falon, ya juyo da sauri kamin ta yi magana ya mike, ya aje computer a fusace.
Ta runtse ido tana jiran saukar mari a lallausan kumatun ta, ya ce,
“Don’t I warned you? Idan ban neme ki ba ki daina zuwa inda nake?”
Cikin makyarkyatar murya da gigicewa ta ce, “Ka yi hakuri, kayan cefane ne suka kare, sannan babu kayan abincin makarantar su Munib”.
Ya yi tsaki “Tsuuu!” Kamar ya tsinke harshen sa, ya ce, “Na ji shikenan ko?” Ta mike a salube gwiwa babu karfi ta koma daki, don ita ba abin da ta tsana a rayuwarta irin a yi mata tsawa.
Su kansu yaran sun tsorata da tsawar da Baban su ya yiwa Antin su, sun yi zuru-zuru, suma ya nuna musu hanya ya ce su bita. Da gudu suka tafi har suna faduwa, ya kashe komai ya fice daga gidan.

Washegari Alti ta dawo, ba karamin jin dadin dawowar ta Fati da yara suka yi ba, ko ba komai ta samu mai taimaka mata da debe mata kewa, don Goggo Alti mutum ce mai barkwanci da ban dariya.
Sai ga Malam Ilu yana shigowa da kayan abinci nau’i-nau’i. Suka zaun ita da Alti suka gyara komai suka adana na adanawa a firij, suka markada na markadawa suka adana a ‘freezer’
Washegari ta tashi da wuri da taimakon Alti suka kammala komi da wuri, suka shirya yaran da abincin su, karfe bakwai da rabi Babansu ya kwashe su ya wuce dasu, sannan ya dangana ga ofishinsa.
Kuma ranar ne su Yaya Haulatu kanwar Yaya da wasu daga aminan arzikin ta suka zo suka yi mata jeren kayan gado dai-dai karfin iyayen ta da dan uwanta Mukhtar.
Falon ba ya bukatar komi, masu gidan sun riga sun tsara abin su dai-dai da rayuwar su ta masu murza tsinin biro, sai ba’a taba komi ba, iyakacin su dakinta.

A kwanaki bakwai da Alti ta yi tare dasu, ta fahimci irin zaman kare da kyanwar da ake tsakanin Fati da maigidanta Dr. Sulaiman. A ranta ta ce,
“Yarinya kyakkyawa kamar Hadiza, ga hankali da addini, ko meye nakasunta da Dr. Sulaiman ya kasa son ta?”

Ta ce, “Ko da yake so ba’a nan yake ba, abune wanda ke faruwa kawai a duk sanda ya so, ga duk wanda ya so, cikin iko da kudurar Allah.

A yau suna yankar alayyahu ita da Alti, domin yin miyar wainar masar dare. Suka jiyo motsin shi yana shigowa kitchen din, tuni Fati ta soma makyarkyatar jiki, kan ka ce meye wannan wuka kakkaifa ta shiga cikin naman hannun ta.
Don ita ko gyaran muryar shi ta ji gigicewa take ta fita hayyacinta kada ya yi mata tsawar nan tashi mai dimauta ta.
Jini ya soma bulbula a dai-dai lokacin da ya idasa shigowa kitchen din. Alti ta ce, “Ya salam! Kin gani kin yanke, na yi na yi ki daina amfani da wannan wukar kin ki, ta fiye kaifi da yawa, sannan gaki da saurin gigicewa”.
Ya ji hankalinsa ya tashi ganin yadda jini ke gudu amma ba ta dago ba. Ta dukar da kai ko motsi ta ki yi. Ya basar Ya ce, “Babu sauran ruwan roba ne Baba Alti? Firjina babu komai, sannan ina jin kishi”.
Ta mike zuwa store ta dauko mishi katon na FARO ta dawo, ta kama hannun Fati ta ce, “Babu kananzir balle in sanya miki, bari a daure da tsumma”.
Ta tsaga zanin ta tana kokarin daure mata. Ya kalle ta a kaikaice ta kasan ido ya fita, zuciyar shi babu dadi, don ya tuno yadda ta nuna damuwa ranar da ya yanke nashi hannun.
Mamaki ya kama Alti, ashe Baban Munib ba shi da kirki? Matarka ta yi irin wannan yanka amma ko kallo ba ta ishe ka ba?
Tana daure mata Fati ta fara kuka yankar ta fi karfin daurewa da tsumma. Alti ta biyo shi, ba ya falon yana dakin sa. Ta tura Munib wanda ke ta wasan game cikin computer ta ce ya kirawo Baban shi.
Jim kadan suka fito tare shi da Munib, yana rike da gorar ruwan yana sha. Cikin takaici ta ce,
“Zan kai Fati asibiti ne”.
Ya sunkuyar da kai duk jikin shi ya yi sanyi, ganin bacin rai kwance a fuskar tsohuwar da bai taba ganin bacin ran ta ba tsayin shekaru shida da suka yi tare da ita, ya dukar da kai sosai ya ce,
“Bari in diba ciwon nata”.
Ya koma daki ya dauko first aid box ya same su a kitchen din, jinin na ta zuba har yanzu.
Sanye yake da brown getzner ta sha dinkin Mohammed wanda shi ne dinkin sa kawai, ya russuna dai-dai inda take sunkuye, ya kama hannun ta. Wani sanyi ya tsirga a zuciyar ta. Dago idon nan da za ta yi sai

2 Comments On YAKANAH
avatar
rabiatu-2

1 year ago

Reply

Thanks

avatar
fatima-2-7-5

1 year ago

Reply

very nice book

Please Login or Register in order to submit comment