Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Hadiza yake yana nuna masa yadda ciwon ya ci karfin ta a yanzu, da irin taimakon da ya ba ta. Shi kan sa Bunza sai da ya yi hawaye balle gogan, wanda gudun jini ya katse a jijiyoyin jikinsa.

****









Karfe shida na safe Dr. Surayyah ta fito da jaririyar da aka cirowa Hadiza, kamar ta daya da Baban ta kamar ya yi kaki ya tofar, har duhun kalar nashi ne.
A lokacin ne jama'ar gidan su Hadiza suka iso, Dr. Surayyah ta sanar da su. Fati karfe bakwai na safe ta iso asibitin, ta baro yaran da Alti ta zo a (keke-napep). Dai-dai lokacin da aka turo Hadiza za a mai da ita ICU, ya yi dai-dai da sanda Surayyah ta mika mishi jaririyar ya ki amsa, sai Fati ce ta amsa.
Za a wuce da Hadiza ta rike hannun sister Magajiya ta rada mata cikin nishi,
"Ina son yin magana da su…..".
Don haka sister ta dakata. Sulaiman da Fati suka garzayo gareta, kowanne ya fita hayyacinsa. Fati rungume da jaririya tsantsan tana ta tsala ihu.
Itama Fatin Kukan take. Hadiza ta runtse ido hawaye na zirara, ta ce,
"Fati ina alkawarin mu?"
Cikin Kuka ta ce,
"Yana nan Yaya Hadiza".
Ta kama hannun Sulaiman ta hada da na Fati, duk su Malam Ja'afar na kallo, ta ce,
"Fati har da shi a alkawarin fa.........."
Ta yi sharbe ta yarfar da majina da hawaye ta ce, "In kula da shi kika ce? Yaya Hadiza ai shi babba ne?”

"Babba ba ya bukatar kulawa Fati……?"
Ta ce,
"Ban sani ba".
Ta ce,
"To yana bukata, shi ma kamar Munib ne, bambancinsu shine shi Munib kulawar UWA yake nema, shi kuwa Sulaiman kulawar MATA yake nema..........".
Ta yi murmushi ta runtse idonta, cikin azabar da take dandana a kwakwalwarta. Sulaiman ya russuna ya sumbaci goshinta, hancinta, bakinta da idanunta. "You will get well soon Hadizah……, bana bukatar kulawar kowa sai taki, in ba taki ba na yafe, zafin ciwo yake sa ki yin irin wannan magana.........".
Ta girgiza kai tana kara manne hannun su cikin nata ta ce,

"Sulaiman-Fati............".

Dr. Bunza ya karaso ya tura gadon da kanshi yana ta yiwa sister Magajiya fada. Yaya ta karaso ta karbi 'yar da ke hannun Fati ganin tana neman kwala ta da kasa.

Dr. Sulaiman ya mai da hannun shi cikin aljihu, yana so ya yi kuka amma idanun sun bushe kamar soyayyar gyada marau-marau. Sai Malam Ja'afar ya iso gare shi ya kamo hannun sa suka zauna tare, yana cewa,
"Karbi 'yar ka sa mata albarka".
Amma Sulaiman ya ki, sai kirjin shi da ke ta kai kawo kamar zuciyar ta ballo allon kirjinsa ta fito.
Ana shigar da ita cikin computer don a yi hoton kwakwalwar ta kamin likitocin su san me za su yi a kai, ta soma wata irin jijjiga mai ban tsoro, kamin ta yi salati rai bakon duniya ya yi halinsa.

"Allah ya ji kan Dr. Hadizah!"

Abin da dukkanin likitocin suka furta kenan, a lokaci guda suna share ambaliyar hawaye daga idanuwan su, tare da kai hannu su rufe mata idanun ta.

****An bawa Malam Ja'afar da Sulaiman gawar Hadiza cikin mota ambulance, zuwa nan unguwar Karkasara. Inda daruruwar jama'a suka yi jana'izar ta. Mijinta da Mahaifinta suka sanya ta a kabarin ta, suna masu yi mata addu'ar fatan alheri, yafiya, afuwa da addu'ar Allah ya yi mata masauki da aljanna, Annabi ya san da zuwan ta. Su kuma ya basu imanin jurewa.

Sulaiman ya baiwa kowa mamaki, saboda yadda ya tsaya a kan jana'izar Hadizah, babu ko digon hawaye a idanunsa. Ba su san shi kansa kukan na zuwa ne idan an san abin da ake yi ba. To bai san me yake yi ba, bai san halin da kwakwalwarshi ke ciki ba.
Ya san dai kawai Hadizar sa ta rasu, sun kaita makwancin ta na gaskiya, bayan wannan bai san komi ba, bai san kansa ba, bai san a ina yake ba.
Ya dai bude ido ya gan shi a gidan su Hadizah, dakin Mukhtar, ba ya rintsawa, yadda ya ga rana haka yake ganin dare, ya wuni yana karbar ta'aziyyar 'yan uwa da abokan arziki. Tun a ranar Inna Halima, Malam Sulaiman da sauran kannen shi suka zo Kano, da su ake karbar gaisuwa har zuwa kwana uku.
Ranar lahadi suka juya Bakori cike da juyayin halin da Sulaiman ke ciki. Malam ya ce zai dinga aiko mishi da rubutu tsayin kwana bakwai. Ya ce, "To". Wadda ta zama kalma mafi saukin fada a bakinsa, sai kuma bin kowa da ido, amma abinci da ruwa wannan kwanan shi uku bai dandana su ba.
Alti ma tana gidan ita da yara wadanda suka damu kowa da tambayar ina Momin su? Alhamis aka yi sadakar uku, Alti ta koma kauyen su tana kuka da hawayen ta, ta ce sai ranar sadakar arba'in za ta dawo.

Tambaye ni ina baiwar Allah Fatima Ja'afar Mai-Yadi?

Tana can dakinta tana kuka, inna ce kuka ina nufin kuka, mai futa daga karkashin zuciya da ruhi, tana kuma fama da jaririya, bini-bini ta hada madarar (SMA) ta dura mata, ta ba ta ruwan zam-zam. Ba ta barin ta tayi kuka, idan ta bata madarar da ruwan sai ta sa ta a baya ta goye, ta zauna ta yi ta jijjiga ta, har sai ta samu barci, ta sakko ta ta sanya ta a gadon ta, ta zauna a gabanta ta yi ta girka kuka. Idan kukan ya ishe ta sai ta bude littattafan addu'o'in ta, ta yi ta karantawa tana rokon Allah ya kai ladan makwancin rabin jikin ta Dr. Hadiza Ja'afar Mai-Yadi.

Mutuwar Hadiza ta girgiza kowa a gidan nan, haka duk wanda ya santa ya koka ya gode Allah. Kada Dr. Surayyah ta ji labari, to ina ga wanda farin cikin rayuwar sa ya ta'allaka ne kacokam a wuyan ta? Ya ke kwana da ita yake tashi da ita, yake yi mata son da ko iyayen ta sai dai su ce su suka haife ta?
Don haka Doctor Sulaiman-Sulaiman Bakori, yana cikin wani irin hali da duk masoyinsa dole ya koka masa, in har yana da imani, ya bishi da addu'ar Allah ya ba shi dangana da YAKANAH!

Tuni Mukhtar ya koma Kaduna, ranar da aka yi bakwai shi ma Malam Ja'afar ya ce ya koma bakin aikin sa. Ya bishi da "To". Kamar yadda yake bin kowa da ita.
Ya tattara ya koma gidansa, shi kadai kwal kamar maye. Sai da ya gwammace da bai dawo ba, a lokacin da ya ci karo da wheel chair din Hadiza da kayan ta dake watse a dakin barcin su, a nan ne komi ya dawo masa danye, karo na uku da ya soma kukan da ya tabbatar har abada ba zai daina ba.
Haka ya kulle kansa, ba shi da abinci sai ruwan lipton wanda yake dafawa a kettle ya dura a flask ya wuni yana sha, babu ko tunanin sa sukari.
Cikin kwanaki ashirin da mutuwar Hadiza ya zama babu kyawun gani, kasumba ta cika fuskar sa. Duk wannan gayun ya daina shi, wanka ma ba kullum yake yi ba sai ya ji alamar jikin shi na dan wari-wari, ya kashe wayoyinsa gaba daya, ya yi sallama da aikin sa, amma bai fasa kwana yana yiwa Hadiza addu'a ba.

Uwa, mahaifiya, duk ta rasa sukuni, tana can Bakori, hankalinta na Kano, ta san cikin kowanne hali Sulaiman yake yana cikin halin da yake neman matallafi. Kuma cikin halin da yake bukatar mai tausar sa, da nuna masa kauna da kulawa.
Don haka yau ta tambayi Malam Sulaiman cewa za ta taho Kano wajen Sulaiman. Ya ce hakan ya yi.
Yana zaune a falo, daga shi sai wata dukunkunanniyar jallabiya ruwan makuba, da kofin ‘tea’ a hannun shi da ‘remote’ yana kallon tashar Saudiyyah, inda suke gabatar da sallar magariba. Aka danna kararrawa wajen sau biyar kamin ya yunkura ya aje kofin a kan side table ya bude kofar.
Inna Halima ce tsaye cikin atamfa holland ta sha lullubi da koren mayafi kalar atamfar ta, har ranshi ya ji dadin ganin ta, ya ba ta hanya ta wuce cikin falon, ya tsuguna ya gaishe ta.
Ba ta amsa ba sai kallon shi take cikin al'ajabi, "Haka ka lalata kanka Sulaimanu saboda Allah? To wannan rashin tawakkalin da kake shi zai dawo da Hadiza duniya ko me?
Ka sani Hadiza ta riga ta koma ga mahaliccin ta, ba za ta taba dawowa ba, ka fuskanci rayuwar da take jiran ka a gaba, ka zamo mai YAKANAH cikin duk halin da ka tsinci kanka.
Tsakanin ka da Hadiza yanzu addu'a ce, ba wannan lalata rayuwar ba. Idan Hadiza tana raye, ba za ta so ganin ka haka ba, ka yi hakuri mai sunan Malam. Shin yaushe rabon ka da cin abinci?'
Ya sunkuyar da kai bai yi magana ba. Ta jawo ledar da ta shigo da ita ta fiddo ma'adanan abinci guda biyu, ta bude ta tura masa, tuwon shinkafa ne lafiyayye da miyar taushe ta ji nama zuku-zuku, ta ce,
"Cinye maza ka bani kwanon".
Ba musu ya dauka ya soma ci kamar Allah ya aiko shi.
Inna ta mike ta soma tattare bolar falon, ta share shi tsaf, ta shiga dakunan ta gyare ko ina, ta wanke masa toilet. Sanda ta gama ya dade da yin barci a carpet, ta zauna a gefen kansa tana tofa masa addu'a.
Yana tashi ta ba shi rubutun da ta zo da shi cikin jarka ya sha, ya mai da kai kan tuntun ya koma barci. Bai tashi ba sai la'asar, ta je bandaki ta hada mishi ruwan wanka cikin kwami, ta dawo falon ta same shi ya idar da sallar la'asar, ya mike kafa yana kallon ceiling, ta tsuguna a gabansa ta ce,
"Tashi ka je ka yi wanka, ka shirya muje mu ga mai sunan Hadiza".
Wannan karon ma bai yi musu ba, ya mike ya je ya yi wankan, ya zubo farar shadda dinkin Mohammed, ya dora hula fara sol amma bai fesa turare ba, ya fito ya tadda Inna ta idar da sallah tana lazimi. Ta yi addu'a ta shafa, ta mike suka fito harabar adana motoci, duk motocin sun yi kura futuk! Alamar an dade ba a taba su ba.
Ya sa key ya fiddo motar dai-dai inda Inna take, Malam Ilu ya karaso da sauri ya gaida Inna, ya sa ‘duster’ ya karkade motar cike da jin dadin ganin yau Ubangidansa ya fito, wanda yake kwana cikin wannan gida shi kadai ransa, sai dai yana tausaya masa, don ya san rashin matar kwarai kamar Dr. Hadiza ba karamin abu bane.
Inna na baya shi kuma yana tukin suka nufi unguwar Karkasara. A dai-dai titin asibitin AKTH kamar an ce da Inna ta juya, ta hango Fati rike da hannun Munib da Muniba cikin kayan makaranta tana tare tasi, da alama ta dauko su ne daga makaranta.
Da sauri Inna ta ce,
"Ka ga Fati can tana tare mota, yi kwana mu dauke su". Ya yi kamar bai ji ba, ya karawa motar shi gudu. Inna ta yi salati ta ce, "Baka ji ni bane? 'Ya'yan ka fa ta dauko daga makaranta!".
Sai a sannan ya juya, tuni ta tare tasi suna kokarin shiga. Ya ce, "Ai sun shiga mota ma hadu a can". Inna ta yi shiru tana mamaki, har suka iso gidan su Fati ba su shigo ba, don ba za ka hada motar gida da ta haya da ke yin tsaye-tsaye ba.
Tun daga soron gidan yake jiyo kukan Baby Nana Khadijah. Ya rintse ido tsigar jikinshi na tashi. Inna ce ta yi sallama ya biyo bayan ta. Yaya suka tarar tana ta fama da Baby Nana, wadda ke ta tsandara kuka kamar ta tsaga gidan ta ki karbar madarar da take bata.
Ta amsa musu sallama cikin sakin fuska da walwala, ta shimfida musu sabuwar tabarma, sannan ta mikawa Inna Baby Nana. Yaya ta dubi Sulaiman ganin yadda ya rame ya yi kasumba, sai ta ji hawaye sun ciko idon ta.
Ta ce,
"Me nake gani haka ni Sa'adatu? Sulaiman me ya yi zafi? Hadiza ba ta yi gaggawa ba, muma jiran namu wa'adin muke. Karbi 'yarka tunda ta zo duniya baka taba daukar ta ba, ita kuma laifin me ta yi? Ka zamo mai YAKANAH, wannan ba shi ne karshen rayuwar ka ba!!".

Inna ta mika mishi yarinyar, ya fi karafin mintuna uku kamin ya karbe ta, ya kura mata ido yana mamakin kamannin shi da ita har sun fi nashi da Munib.
Dai-dai sanda Fati da yaran suka shigo cikin sallama, tana sanye da katon hijabin ta har kasa mai hannaye, rike da lunch box din yara da jakunkunan su.
Cikin nutsuwa ta tsuguna har kasa ta gaida Inna, ba tare da ta kalli Sulaiman ba ta ce, "Ina wuni?' Bai amsa ba, ita ma ba ta tsaya sauraron ya amsa ba ta wuce ciki.
Ai Munib da Muniba suna ganin Baban su suka fada mishi suna ta tsallen murna, ya mikawa Inna Baby ya zaunar dasu duka a cinyoyin sa, suka soma ba shi labari iri-iri, duka rabi ‘AUNTY FATI’ ta yi mana kaza, ta yi mana kaza. Yana jinsu bai ce komi ba.
Malam Ja'afar ya shigo hannayen shi rike da manyan ledoji yayo cefane ciki har da madarar SMA da Nana ke sha, ya kwalawa Fati kira ta fito ya bata.
Sai a sannan ya lura da bakin takalma har da na namiji a kofar dakin Yaya, ya ce da Fati, "Waccan madarar ta kare ne?" Ta ce, "Eh, saura kadan". Ya ce, "To ki dinga gaya min kafin ta kare ba sai ta kare kaf a barta tana kuka ba".
Ta ce,
"Ai masassara take shi ne take kuka, amma dama gobe zan kaita asibiti". Ya ce, "To Allah ya sauwake, ke kuma Allah ya ba ki ladan hidimar da kike yi da 'ya'yan ki, ya sa suji kan ki kamar yadda kika ji kan su, ya kai rahama kabarin mahaifiyar su".
Ta ce,
"Amin Baba".
Shi ma Sulaiman da ke can daki yana jin su ya ce "Amin". A zuciyar shi.
Malam ya daga labulen ya ce, "A'a! Ashe Inna ce, barka da zuwa kin sha hanya, ya ya aka baro Malam?"
Ta amsa, suka ci gaba da gaisawa suna hirar 'yan jikokin su, tare da kara yiwa juna ta'aziyya. Malam Ja'afar ya dubi Sulaiman sosai ya ce,
"Ina maganar aiki ta kwana?"
Ya yi shiru kanshi a sunkuye, can kuma ya ce,
"Zan koma gobe insha Allahu".
Malam ya ji dadi, ya kara mishi da nasiha mai sanyaya zuciya.

Ba su baro gidan ba sai karfe biyar na yamma, bayan Inna da Yaya sun yanke shawarar yaran za su ci gaba da zama a nan saboda ya fi kusa da makarantar su.
Har za su tafi ya dubi Yaya fuska ba walwala ya ce,
"Duk abin da ake bukata Yaya, don Allah a gaya min".
Yaya ta yi murmushi ta ce, "Me ake bukata ban da madara? Bayan ita babu abin da zai gagara da izinin Allah".
Ya ce,
"Duk da haka ina son sanin sauran abubuwan da ake bukata, ai ragi-ragi ne".
Ta ce,
"To ka tambayi Fati".
Ba don ranshi ya so ba ya nufi kofar dakin nata. Ta goya Nanah tana jijjiga ta, wannan karon babu hijabin a jikinta, kwayar idanun su ta hadu, ya yi saurin dauke kansa don gani ya yi kamar Hadiza, hatta digon tauwadar Allah da ke kan tsinin hancin Hadiza akwai shi a tsinin hancin Fati.
Zuciyar shi ta yi wani irin mummunan bugu, don gani ya yi tana rikide mishi Hadiza sak, kasancewar bai taba ganin ta babu hijabi ba. Ya tsaya daga bakin kofar hannun shi duka biyu zube cikin aljihu. Da kyar yake magana kamar an tilasta mishi, ba tare da ya kara kallon ta ba.
"Na tambayi Yaya abubuwan da yara suke bukata, ta ce in tambaye ki?"
Kanta a kasa ta ce,
"Sai ko pampers da madara".
Ya ce,
"Bayan su ba wani abu?"
Ta ce, "Eh, amma malamar su ta ce akwai prize giving day ranar asabar kuma ana son iyayen yara su je".
Sannan ta dauko report card na yaran na wannan zangon ta mika masa.
Garin karba hannayen su suka gogi juna, sannan suka kara hada ido a lokaci daya babu wanda bai ji a jikin sa ba. Ita tsoro ta ji, shi kuma ji ya yi kamar hannun Hadiza.
Bai ce komi ba ya karba ya sanya a aljihun shi ba tare da ya duba ba, bai kuma ba ta amsar zai je ko ba zai je ba ya fita. Ya tadda Inna har ta fito suka tafi, ya bar Fati cikin tunani.

Ta zauna a gefen gadon ta, ta sauko Nanah wadda ta samu barci ta rungume cikin hannayen ta, tana tunanin me Hadiza ke nufi da ta ce ta kula da Baban Munib???

"…..Munib kulawar Uwa yake nema, Sulaiman kulawar MATA yake nema….".
Ta tuno kalaman Hadiza.
To ai ita ba matar shi ba ce, ba gidansu daya ba, ta ina za ta kula da shin kada rashin Hadiza ya tagayyara shi?
Wannan baudadden mijin nata dake yi mata kiyayya maras dalili? In har Hadiza na nufin ta auri mijinta ne wanda ba ta fito baro-baro ta fada ba, sai hannunka mai sanda da ta yi mata, ta hada ta da wani al'amari da ba zai taba yiwuwa ba.
Ba ta fata, kuma kada Allah ya tabbatar ta yi tarayya da Hadiza a kan abin da take so, ta tafi ta bari ba don ba ta so ba, sai don hukuncin Allah wanda ya fi karfin dan adam ya yi jayayya da shi. Hakika ta dauki alkawarin da ba ta san yadda za ta yi ta sauke shi ba.
****Washegari da yamma sai ga Inna ta kara dawowa, Dr. Sulaiman ya kawo ta, Hamza da Abdulyassar suka shigowa Fati da katon na madarar SMA, katon na diapers da himilin shopping na kayan masarufi da kayan biskit da choculate da su Indomie wanda su Munib ke zuwa makaranta da su. Ta adana kowanne a inda ya dace, Inna ta ce ya je sai dare ya zo ya dauke ta.
A lokacin Malam Ja'afar ya iso da shi da Inna da Yaya suka kule a daki, suka sakayo kofa, me suka ce me suka ce oho, sun dai dade suna magana kafin ya dawo ya dauki Inna su wuce, kasancewar a gobe zata koma Bakori, ya biya ta Jifatu ya yi mata sayayya mai yawa kamar yadda ya saba, ita da Malam da sauran kannen shi, suka wuce gidan sa.
Inna ta tuka mishi tuwon semovita da miyar ganye ya ci, ta takura mishi ya bude wayoyinsa. Yana budewa sakonnin ta'aziyya daga likitoci 'yan uwansa da sauran abokan arziki ya soma tittidowa cikin wayar. Sannan ana neman shi a ofishin (Chief Medical Director) na AKTH ranar litinin.
Don haka yana kai Inna Bakori suka gaisa da mahaifin shi bai tsaya ba. Da zai tafi Inna ta ce,
"Ni kuwa akwai wata magana muhimmiya da nake so mu yi, ga shi na ga alamar kana sauri".
Ya ce,
"Gaskiya kam ina cikin sauri, sai ko idan na dawo". Ta ce,
"Shi ke nan Allah ya kiyaye hanya, ya kara maka hakuri da YAKANAH, ya shige maka gaba a kan al'amuran ka, ya yi maka musayan alheri".

Har ransa ya ji dadin addu'o'in Inna, wata nutsuwa ta kara shigar shi, son mahaifiyar shi ya kara shigar shi. Ta ce,
"Ina so zuwa sanda za ka dawo in ga canji, kamar yadda ka yi min alkawari, in ganka a likitanka ba mai sunan Malam ba".
Murmushi ya yi, wanda rabon shi da yin shi tun wani karni can da ya shude.

****










Litinin, ya isa ofishin CMD, sun dade suna tattunawa a kan wani aiki na dashen zuciya da za a yiwa ministan lafiya. Yana daya daga cikin likitocin da zasu gabatar da aikin. Ya koma office dinsa ya daidaita komai ya ci gaba da aikin sa, cikin karfin zuciya da neman rinjaye a kanta.

Sai ya zamto yana jin dadin aikin sosai, don yana debe mishi kewa, yana hana shi zama shiru har maraicin matarsa ya gallabe shi. Ya tarar da tulin ayyuka da yawa, don haka ya zamo busy a satin gaba daya.
Ranar alhamis ya saci jiki ya je yayowa 'ya'yan shi siyayya ya biya ta makarantar su ya gansu, lokacin da aka fito cin abinci, a karkashin wani benci ya zauna ya rungume su suna ta labari, ya bude ‘kit-kat’ yana basu suna ci suna yi mishi hira. Tun suna damuwa da rashin Momin su har sun hakura sun dangana sun daina tambayar ta.
Munib ya ce,
"Daddy ba ka zo (prize giving) din mu ba, kowa Baban shi ya zo banda mu".
Ya kama kunnen shi cikin nunawa yaron amsa laifin sa, ya ce,
"I am very very sorry..... aiki ne ya yi min yawa. To wa ya kawo ku?"
Suka ce, "Aunty Fati, ta yi mana kwalliya ta kawo mu".
Ya ce,
"Aunty Fati ta kyauta!".
Suka yi murmushi. Ya ce,
"Next year ba zan sake ba".
Aka kada kararrawar komawa aji, suka fella da gudu suka nufi ajinsu, ya bisu da kallo yana murmushi cike da kewar su.

Hakan yake yi duk sanda ya samu sararin aiki, ya daina zuwa gidan don kar ya ga Fati, tana tuno mishi da wasu al'amura msu yawa a kan Hadiza. Sannan ba ya son wata alaka take shiga tsakanin su, shi ma kuma bai san mai ya sa ba, ya danganta hakan da rashin haduwar jininsu na tuntuni.

Ita kuma ta danganta hakan da wulakanci da raina mata wayo, yana ganin ta kamar ba ta san abin da take yi ba, bayan in da wanda ya san ciwon kansa a duniya to ita ce.
Sai dai tsarin rayuwar su da ya banbanta, kowa da irin nashi tsarin rayuwar, sun dauki rayuwar bature mai zafi sun yafa shi da Hadiza, ita kuwa Lahira ta sani ita take wa tanadi, shiyasa yake mata wani gani-gani, don haka ita ma ta yi kamar ba ta san yana zuwa makarantar yaran ba, bayan kuma suna gaya mata.Ana i gobe sadakar arba'in din Hadizah, Malam Sulaiman, Inna Halima da Baffanin Sulaiman guda biyu, Malam Surajo da Alhaji Umar suka iso gidan Sulaiman a Kano, a daren suka bukaci ya kai su Karkasara. In da ya ajiye su da daddare ya wuce asibiti, da cewar zai dawo ya dauke su.

Manya sun kule a falon Baban Hadiza, wato Malam Ja'afar suna magana ta gemu-da-gemu har da Yaya da Inna. Yaya ta ce,

"Ni bana jin Fati sai shi Sulaiman, anya zai yi na'am da al'amarin nan?"

Malam Sulaiman ya yi murmushi ya ce, "Kune baku san Sule ba har yanzu, yana da wani hali tun yana yaro, abin da zai so sai ya fara kin shi tukunna.
Ga yadda mahaifiyar shi take bani labari, babu jituwa ko ya ya tsakanin sa da Fati, ita kuma ta kama kanta ba ta shiga shirgin shi. Mu dai burin mu ku bamu hadin kai, Allah ya gani muna son zuri'ar gidan nan, muna son zumunci ya ci gaba da gudana kamar yadda aka faro.
Fati ita ta fi cancanta da ta rike 'ya'yan 'yar uwar ta, don a wannan zamanin da wuya a samu macen da za ta rike maka 'ya'ya har uku duk son da take maka. Sannan mun yaba da hankali da tsarin rayuwar Fati, muna sa ran yara za su tashi da kyakkyawar tarbiyya har zuwa girman su.
Fati ba za ta dauwama a gida tana bautar 'ya'yan 'yar uwarta ba, dole watarana za ta yi aure. Ranar da hakan ta faru ya ya Sulaiman zai yi da yaran nan?
Ga shi suna karatun su mai kyau a nan balle mu tafi dasu Bakori. Fati ita ta fi cancanta da ta maye gurbin 'yar uwarta a zuciyar Sulaiman.
Don haka muna neman hadin kanku, yardar ku da amincewar ku Malam Ja'afar. Shin an bamu Fati? Da karfin mu muka zo, da sadakin mu a hannu, gobe muke so bayan an shafa addu'ar Hadiza a daura auren Sulaiman da Fatima".
Malam Ja'afar ya ce,
"Tun kafin ku yi wannan tunanin na riga ku yin sa, kun dai riga ni furtawa ne. Tabbas duk matar da Sule zai aura nan gaba ta rike mishi marayun shi ba kamar Fati ba, wadda ta san ciwon su, tasan ciwon 'yar uwarta.
Sannan Hadizah ta yi wani abu a ranar da za ta koma ga mahaliccinta, wanda ya tsaya min a rai kwarai, ta kama hannun Sulaiman ta

2 Comments On YAKANAH
avatar
rabiatu-2

1 year ago

Reply

Thanks

avatar
fatima-2-7-5

1 year ago

Reply

very nice book

Please Login or Register in order to submit comment