Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ki koma makaranta ki samu Ilimi,Ido na zaro nace no bana so da girmana godai godai Primary Kawai nayi ta Kauye shekaruna ashirin da biyu ba wata makaranta da zani,ba a girma da karatu Rabi Ilimi ilimi ne ko wanne irine,to ni dakikiya ce nan daka ganni kasurgumar jahila ce ni bana ganewa katuwar jahila ce ni ba uwar da na sani ilimin addini ma Dan na dage ne amma ba abinda da Zan sani,Kai baka ga alama ba jahila ce ni shi yasa nace maka ni abinda zakayi ka birgeni Kawai ka kwanta dani dan Allah ka....wata mahaukaciyar tsawa ya buga min yace baza a kwanta dake ba din karki sake min zancen nan bana son ji sai na tashi na bar Miki gidan bana son zancen banza bana so kinji na fada Miki watch your tongue Inshaallah bazan kwanta dake ba Kuma sai dai na ci abinci badai ke ba,dariya ya mugun bani nace to naji yi hakuri ci abincin ni na hakura ba sai ka c...bakina na rufe yace yanzu kiyi kuka yanzu sai aga kina dariya ke haka kike ne?nace ae Mana ai dan Kaine na koma kusa dashi na zauna yace ki kyaleni naci abincina in Peace dan Allah,na kyaleka ci abincinka in peace not in pieces,dariyarsa ya danne ya kyaleni Yana ci,Hannu nasa a ciki tunda naga da hannu yake ci,nama na dauka nace baka cin naman bude bakin na saka maka ha bakin haaaaa....dariya yayi ba shiri na saka Masa da sauri ya rufe bakin da katon nama a ciki,Murmushi nayi na dauka daya naci Nima na tashi tare da haurawa sama na sake karkade Masa bed din na gyara bed din sosai duk da ba abinda yayi,kayan bacci na zabo Masa na ajiye a gefen gadon na fito

Har ya gama cin abincinsa Ina Fitowa na iskeshi Yana kallon ball ya lankwashe kafafunsa a Kan kujerar kwanciya nayi na dora kaina a cinyarsa tsokanarsa nayi amma yasan maitata da naci sai ya rabu dani,dagowa nayi Muka hada Ido yace mene kike kallona? baka yi fada ba ya zanyi dake to tunda kin zama mayyata ba kya Jin magana,ki bani tarihinki kinki fada min nayi nayi kinki da nayi magana zaki fara min kuka shike nan gobe bazan dawo ba ai sai nayi kwana biyar baki ganni ba,kayi hakuri Zan fada maka ai nan gaba,Allah ya kaimu yace na koma na kwanta nayi matashi da cinyarsa ban ma San nayi bacci ba,Ina yin bacci ya zame kafarsa ya barni nan ya tashi tsam ya koma dakinsa,Shirin bacci ya Fara Yana Fitowa daga wanka yaga kayan baccin akan gadon da guntuwar takarda a Kai,takardar ya dauka ya karanta WANNAN KAYAN ZAKA SA, SU NA ZABO MAKA ZASU MAKA KYAU, PLEASE KARKA SA WASU IN BA WANNAN BA
DAGA KARUWARKA, .
dariya ta bashi Wai karuwarsa tana so ta dinga ikirarin ita karuwa ce kayan ya saka data zabo Masa ya kwanta abinsa adduar bacci yayi ya kwanta sai bacci.

Dagaci Katsam shugabannin gidan marayu Suka zo duba yarsu yar tsuntuwa Rabi, tsoro ya kamashi sabo da dama Indai gomnati tasan ka karbi dan tsuntuwa to Dole sai da shedu da kotu da hukumar marayu,sai ka cike takaddu sosai anyi a rubuce sannan jefi jefi sukan leko duba yaransu a ka'ida, ai Kuwa rabon da suzo tun Rabi tana karama sai yau, Dagaci karya yayi yace ai ta tafi Hutu gidan kanwarsa dake Abuja,Suka ce ba damuwa suna ganinsa babban mutum Kuma Dagaci shugaba a kauyen sai basu damu ba Suka tafi abinsu, Dagaci Yana Jin dadi gashi Rabi ta tafi sun huta za ayi auren yarinya ya zauna a dakin Gwaggo ya fashe da dariya yace Kinga Yan Iska na musu karya sun tafi,Gwaggo ta sheke da dariya tace Ina tsoro fa Kar Yarinyar nan taje ta kaiwa hukuma Kara watarana kasan suna da gata a gomnati,dariya ya saki yace tun yaushe na Gama da shafinta ai wajen malamina na koma nace tunda ta tafi to duk inda take ta fada Neman maza,dabara bata fado min ba sai data yi wata biyar da barin gida na garzaya nace a sata tafiya Neman maza ta kangare ta zama fitsararriya duk inda taje Kar tayi kunya shike nan Kinga ta fada duniya ta gaji iyayenta da Suka jefar da ita ai na bawa Amarya labarin komai,Gwaggo ta sheke da dariya tace muyi Shuru da bakin mu Kar Wanda ya sani bye bye Rabi zaki ga Kudurar Allah.
Gaji Shirin biki Kawai suke babu Kama hannun yaro.

Sabreen ce ta fuskanci Nawwar baya kwana a gida watarana,yau ma taje har dakinsa ta duba ba kowa har 3am tace kut wato dama mutumin nan dan bariki ne ai Kuwa wallahi sai ubansa da uwarsa sun sani zai gane kurensa Kuma Iyamami sai taji tasa danta ya dauki mataki,Tsaki taja tace ta tabbata Yana can tare da karuwarsa dole na saka Jamcy ta fara bibiyar min shi sai anga Ina yake zuwa zai sani ta mike ta koma dakinta ta kora barasarta me karfi ta kwanta abinta,washe gari da sassafe ta kira Jamcy tana fada Mata mijina fa baya kwana a gida yanzu aiki ya sameki kawata ki Fara bibiyar min shi,Jamcy farin ciki ya kamata a ranta tace Allah ya Kara a fili tace to yanzu duk Sanda Kika ga zai fita da dare sai ki min waya na fito Nima kin gane,ae ba damuwa Zan fada Miki dan Allah ki gano min Ina yake zuwa cewar Sabreen,Karki damu kawata an gama jamcy ta kashe wayar tace Zaki ga aiki Ina nan a kwance yayi abinda ma zaiyi ke Kika ja Mata baki San ma me mijinki ke ciki ba sai shaye shaye taja Tsaki ta kwanta.

Washe gari kamshin girkina ne ya tashe shi bayan yaje masallaci bacci ya koma,Ni Kuwa tunda nasan Yana gidan Dana koma baccin ma banyi na kirki ba na Fara gyara gida Ina girki kuma a haka na gama komai da komai nawa dakinsa ne ban gyara ba,wanka nayi na shirya cikin wata buba doguwar riga ta material pink dama ni ba kwalliya nake a Fuska ba iyakaci powder da lipgloss pink na shafa na haura sama na nufi dakinsa da kayan gyara dakin, knocking na Masa Shuru na bude na shiga ba kowa karar ruwa naji nasan wanka yake yi ai Kuwa na fara gyarawa kenan ya fito,Yana ganina ya koma ciki tare da zuro Hannu ta cikin toilet din ya ja kofar hannunsa ne Kawai a waje yace bani Kaya da lotion dina,kayansa na bude duk kusan Jallabiya ne a nan gidan baida Kaya a nan,yace banda Kaya a nan na kirki duk suna gidan matata Miko min Jallabiya Kawai,na zabo Masa gajeren wando na fito da wata Jallabiya ruwan zuma na Mika masa,ya karba na Mika masa lotion din ya karasa rufe kofarsa,sai da ya shirya tsaf a ciki sannan ya fito,Yana Fitowa ya iske na gyara ko Ina room freshner nake fesawa yace sarkin Aiki sannu ya furta yana kallona yanda nayi kyau,Murmushi nayi na shiga toilet na wanke komai Kal Kal sannan na fito na karasa komai,a dining na sameshi yana Danna wayarsa cike da nishadi.

Ina kwana nace yace da ban kwana ba kya ganni,nace ka tashi lafiya to? Lafiya Alhmdllh ya furta,serving dinsa nayi yaga wani Kalar soye soyen ba irin na jiya ba Kuma ba tea nayi ba kunun gyada nayi me kyau ya zauna yaci ya cika cikinsa nima haka,nace da yau ka kainmu joint tunda naga Saturday ne ba aiki,ke da wa da zaki ce na fita da ku? Kawayena mana sai na fada musu a waya da time su zabi inda zamu hadu kowacce taje kawai sai mu samesu a can,yace anya Kuwa? please Kamar zanyi kuka Ina rokonsa,yace to ba damuwa,nayi murna nace mutum biyar Wanda Muka fi mutunci ko? Yace yanda Kika gani, wayata na dauka na Kira Seraline nace ku shirya keda star,wise,yarzabil,sai Santana zamu hadu saurayina yace zamu je outing,Ihu Seraline tayi da murna nan take ta fitar da wani joint na cin nama da shawarma Yana da tsada tace nan za a kaisu,nace karki damu saurayina akwai kudi karku ci komai anjima zamu hadu 6pm Kawai kuje can zamu Zo mu same ku tace an gama,tana kashe waya ta fadawa sauran Suma sai Murna.

Yace sai Yamma ya mike ya fice tashin motarsa naji,Yana fita gidansu ya nufa ya samu Maminsa a zaune a palonta tayi tagumi,tagumim ya cire da hannayensa,juyowa tayi ta kalle shi tace yaushe ka shigo? Yace Ina ta sallama baki ji ba Mami lafiya dai ko? lafiya tace Kawai yasan ba lafiya ba Kawai baza ta fada Masa bane,yace Mami ki Kara hakuri kinji,tace Inshaallah tana Murmushi,Ina yaran?
Sultana tana gidan Kanwata Rahma,Nasira da Hamra suna Islamiyya,shi kuwa sarakin buga ball Nawaf ya tafi Wai yau suna da ball tsakanin su Yan Jss 3 da Yan Ss1 shine ya tafi,shi ba zaije islamiyyar ba sai ball,yaune Kawai kayi hakuri karka taba min yaro nasan halinka,Ina Sabreen din tana lafiya ko? Lafiya take...sallama Sultana tayi ta shigo tana cewa laaaa Yaya Sannu da zuwa yace yawwa sarkin yawo haka ake Yi daga yin candy shike nan Islamiyyar ma an daina,Ina zuwa wlh Yaya Aunty ce tace naje bata da lafiya,Mami tace ya jikinta nata tunda nasan laulayi take,Nawwar yace ciki fa ita Ina zata Kai Yara ya har bakwai,to Allah ya bata sai taki,Ina Baffanmu? Ya fita tare da Yar gwal din tasa,Murmushi Nawwar yayi yace Allah ya kyauta komai zai wuce Mami na,tace ga abinci fa,yace naci a gida ya mike tare da furta na tafi sai zuwa Yamma watakil,tace Allah ya kaimu a gaishe ta,Yana tafiya Sultana tace wlh in Allah ya yarda Yaya sai ya Kara aure wlh Kinga irin abinda matarsa take Yi a gidan hmm Yaya wahala Kawai yake Yi,Mami tace na San komai ai Rannan na gani da idona Dana je gidan sai hakuri,ke Mami komai kice hakuri ni wlh Rannan ma naso na nadawa shegiya duka Kinga wani wulakanci data Mana da kawayena,ku dinga hakuri Yar uwarku ce dai ato kije kiyi Sallah,tace to ta mike ta haura sama.

Nawwar gidansa ya shiga ya iske shi kaca kaca ba gyara tsallakewa yayi dakinsa ma gashi nan duk sai yaji ya kasa samun nutsuwa babu tsabta sam, Fitowa yayi ya leka ko Ina matar tasa bata nan,dakinta ya leka ya isketa tana shara uban bacci tayi shaye shaye har munshari take zabgawa kwarrrr...kwarrr...sisi....fi..fifi...ya juya a gidan ya yini sai 5pm ta farka ba Sallah ba salati sai da ta tashi ta hada azahar da la'asar tayi a gurguje ba nutsuwa mayen bai gama sakinta ba ta fito kitchen ta dan tafasa indomie ta cinye abarta tana Shan ruwa ya fito cikin shirinsa ya hade cikin wata farar shadda dinkin zamani na zaratan matasa yayi mugun kyau Kamar a sace shi, ta ganshi ba zato yace kin tashi,yanzu baza kiwa kanki fada ba wannan wanne irin bacci ne ko dai shaye shaye kike ne ban sani ba? kame kame ta Fara tace jiyane na raba dare Ina kallon film,yace uhm ai ko ba kallo haka kike yi,bacci bacci hakkina ma bakya bani ba abinda ya dameki da ci na da Sha na,gyaran gidan,kiyi kwalliya duk ba ruwanki komai na zaman aurenki zero,a Haka Zaki samu ciki ki Haifa min yara, Ina ta baki chance kinki gyarawa Wai me yasa ke bakya ganin yanda yaran zamani masu aure ke kula da mazajensu ba,inda karuwan nan Suka Yi yawa a duniya da karuwan gida dana waje ga Yan kwalta suna ta kwacewa Mata mazaje ke ko a jikinki,ai Sabreen kuka ta saki tace Allah ya kamaka Allah ya Isa dama cin amanata kake yi kana can kana bin karuwai ai dama yanzu baka kwana a gida kullum kana bariki,ya Bude baki yace dama zargina kike yi? to naji Ina zuwa bariki ki gyara halinki ki kwato mijinki,harara ta watsa Masa ta juya ta Shige dakinta ta gyara iya dakinta kal kal Yana shining tayi wanka abinta tayi kwalliyarta sannan ta fito ta Kira shi a waya lokacin ya shiga wata bakar motarsa me arnen tsada ya rubuta wifey ya daga yace ya dai madam ko na dawo ne akwai harka? Wai haushi ya bata ta kashe wayarta ma ta fasa tambayar unguwar Kun San me Shan Coccaine sai a hankali daga yace haka sai haushi ya kamata ta yafa mayafinta a saman atamfarta me tsada ta fito ta Shige motarta ta fisga abinta ta fice ba izininsa tace to shima fita yake baya Zama Nima me zanyi masa.

Ni Kuwa na gama cakarewa cikin wata English fitted gown ta wani silver din material nayi kyau gashina na Tara a tsakiya na dan Dora siririn mayafina black na saka takalmi Baki da jakata baka,har maroon jambaki na dan shafa sama sama nayi kyau na karshe ana ganina an San wayayyiya ce,Ina shafa turaren da Muka siyo a wajen Mazarkwaila kamshinsa ya Isa gashi da saukar da nutsuwa,shigowa yayi ya min knocking,Fitowa nayi jakata a hannuna tsayawa yayi Yana kallona yanda na Zama wata Queen na diga ruwan kyau dama gani kyakyawa dani, a ransa yace a haka fa maza duk sun gama da ita zancen ya kautar yace let's go,nace bakace nayi kyau ba,kinyi kyau mana Murmushi nayi nabi shi Muka jera Muna fita yasawa palon key,motar na bude masa da sauri ya shiga na rufe nima na zaga na shiga gefe,nace na iya driving fa,yace ai dama Yar bariki idan bata iya mota ba waye zai iya,nace wlh kuwa.

Muna Hanya Sera ta min waya suna can jiranmu suke Yi kawai,Muna zuwa yayi parking muka fito hannunsa na rike Muka shiga ciki,sai kallonmu akeyi munyi kyau sosai arna sai yabawa suke,Su Saratu ma abin ya birgesu sosai kana ganinsa ba karya akwai Naira hutu da wanka yabi jiki,kujeru suka Kara Mana mu bakwai Muka zauna mamaki ya Kama Nawwar ganin Santana Dan daudu Namiji ya tira sumarsa ta koma red,Suka ce good Afternoon sir ya jinjina musu Kai kawai yau sunga Isa da gadara a wajensa, mu Kuwa dama bama yanga abinmu,Santana Yana karairaya ya furta su Saratu anga banza ta Fadi anzo kwasar gara,Star tace yo Saratu Ina taga saurayi ai karuwanci ya shiga jikinta sosai,Wise tana ji tace abeg a kawo mana nama da shawarma,kafadar Nawwar na dafa Ina gefensa dama nace kuci kome kuke so wannan Saurayin nawa Dan Albarka ne akwai kudi komai zai biya karku daga kafa Enjoy your life,Saratu da karfi ta kwalawa masu bada abincin tace Juice please tana daga hannu kowacce cikinsu sanye take da matsiyatan Kaya kusan tsirara suke,aka Fara kawo musu gasashen nama,aka kawo shawarma,ga Ice cream,ga lemo,ga wani farfesun kifi a gefe da chips,suna ta ci suna Santi,Yar zabil ta dauki nama ta jefa a baki ihu ta kurma tace heee sweet oooo...Kai yau Ina Jin dadin rayuwata Wise ta furta suna ta ci Nima Ina ci Ina cewa muji dadinmu Karuwai mun samu me kudi,na kalli Nawwar da baya cin komai shi nace ka shiga Uku ka fada hannun karuwai taka ta kare,Murmushi Kawai yake suna bashi dariya,kifin na Fara ci nace ga inda dadi yake, Santana ya furta water Yana yiwa masu wajen magana aka kawo,Saratu ko magana ta daina sai aikin duri Kawai take yi, nace a gama kowa yayi take away abinda yake so,Star sai ihu da wata mahaukaciyar dariya tace yau Muna gwangwajewa,Dan daudu yace ba abinda zamu ce sai muce Allah ya barku tare ke Kuma ki dinga bashi dadi sosai a sakar Masa jiki banda rowa,Yar zabil tace fada Mata dai ko tafi ji irin wannan ba a musu rowa,Wise kallon Saratu tayi tace ke baki da saurayi me kudi Wanda zai kashe Miki kudi haka sai shegen ci duk kinfi kowa ci sai kace saurayinki ne ya siya,Nace ku kyaleta taci sai a Karo karku damu akwai kudi me kudi ne karku tausaya Masa,Saratu tace karku isheni Jin dadina nake yau,karuwanci yabi jini cewar Star,Kai Karuwai Muna shanawa Karuwanci yayi a rayuwa a buga bariki kunji ta daga juice tana korawa tace Muna cin darajar karuwanci,Ke dai bari cewar Santana Dan daudu,shi dai Nawwar saidai yayi Murmushi Kawai Yana kallon ikon Allah na wani tale kafafu Kamar yanda su Seraline Suka zauna Suma kowacce Kamar tana palon uwarta bama Jin kunya duk abinda Muka ga dama fada muke Muna ta shewa ga wajen kida masu Dadi suna tashi,Star tana koshi ta mike a wajen tayi Mika ta koma ta zauna,mikewa nayi Nima Nawwar ya fisgoni na zauna da sauri na kalle shi nace mika zanyi,wani kallo ya min nayi shuru,Saratu ita dama bata da kiriniya akwai dan aji kadan,sai da Muka koshi Kamar cikinmu zai fashe Suka Yi take away ya biya komai sannan Muka fito farkan Yarzabil yazo da katuwar mota ya dauke su Suka tafi Muka fita muma dauke da take away dinsa bai ci a wajen ba,Muna mota yace hankalinki ya kwanta yanzu? Nace ae yace sai me nace gida akwai film din da zasu haska yau Zan kalla,gida ya kawoni Ina fita yaja motarsa ya koma gidansa ya samu ba kowa ya tambayi me gadi yace ai Sabreen ta fita bayan fitarsa, yasan Bata yawo ta tafi ba baza ta wuce gidansu ba,waya ya kirata tace gani ma Zan shigo gidan,Yana kashewa ta ja tsaki tana cewa shi Papa ya matsu nayi ciki bari na lallaba shi dai na samu cikin,tana shigowa gidan Yana Palo a zaune rungume shi tayi ta baya tace na dawo,ledar take away din ya Mika Mata ta karba tana murna Kamar kasan yunwa nake ji





Masu bukatar sauraren Audio na wasu books dina kuje S ZARIA TV







AsmaBaffa
08061929616
[7/15, 5:49 AM] +234 912 082 5656: 🌼'YAR AIKIN KARUWAI🌼
LITTAFIN KYAUTA NE



31-35



SADAUKARWA NE GA DUK YARAN TSUNTUWA




Official

By
AsmaBaffa



*AL-KUTUBIYYA ISLAMIC MEDICINE*
_Jama'a kada ku bari wannan garabasa ta wuce ku,muna da nau'i magungunan gargajiya masu kyau da inganci_
_Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda inganci da sahihancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai-dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_

_nfection_
_Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace *SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI💯☑️*_

_Muna sayar da supplement gangariya irin wadanda ba su da matsala sai da su gyara garkuwar jiki da inganta lafiya, muna bayar da sari duk wani supplement muna da shi, kuma muna sayar da daya muna bada sari akan farashi mai sauki, muna tura kayanmu ko wane gari domin neman karin bayani a tuntunbi wannan lambobinmu dake kasa._
*08089965176*
*07084653262*





Page naki ne
AUTARESS







A wajen ta zauna ta bude tana ci tana Santi duk ta gigice sabo da dadin naman harda cewa dan Allah a Ina ka siyo? Sunan wajen ya fada Mata,bata San Yan bariki da sanin waje iri iri ba ko Ina sun sani komai na manyan Yara sun San da zamansa sabo da gantalinsu, sai data gama ci sannan yaci nasa ya koshi ya koma dakinsa yayi Shirin bacci yana kwanciya ta shigo dakin cikin matsiyatan kayan baccinta yasan me tazo nema dama ya gaji da kulata suna hayaniya tana kwanciya ta Fara murza shi biye mata yayi Kawai sabo da ya bata hakkinta haka ta samu abinda take so wannan karon a ciki ta bari ya zuba Mata sperm dinsa ciki take so ta samu, shi bai sani ba yana saduwa da ita yajita a wangale ba gyara Kuma yasan farko ma haka ya ji ta,dannewa yayi kawai ya zaiyi da kaddara tunda ta same shi,badan Yana tsoron Allah ba da tuni ya fada neman Mata sosai, Yana wannan tunanin bacci ya dauke shi yau itama a jikinsa ta kwana bata Sha komai ba, sai da safe tana yin wanka ta tsarkake jikinta taje ta dafa zallan ruwan zafi empty ta zuba a cup ta hada Madara da Milo ta Sha tea dinta da bread da ragowar naman jiya,sai da ya fito Sunday ba aiki zai fita sanye cikin 3qrt da riga me gajeren Hannu marasa nauyi ne sosai,Wai a tunaninta ta bashi abinci tace ga ruwan zafi kazo ka hada tea in zaka Sha,ko kulata baiyi ba ya fice daga gidan,Yana fita tace kai kaga duhu tana gamawa ta maida kwanikan kitchen anci sa'a ta dan gyara gidan sama sama gashi nan dai ta koma dakinta ta Fara shaye shaye ta fada saman bed tana shakar hanci idonta nan take yayi jajir da shi Ido ta lumshe Kamar zata Yi bacci sai ga su Sultana kannen znawwar sun zo gidan su ukun,Sultana,Nasira da Hamra sallamar duniya gidan Shuru ba kowa,ita Kuwa ko motsi ta kasa tana jinsu sama sama har bacci ya kwashe ta,dakinta Sultana ta leka ta dawo tace Kai kuzo mu koma yau ma baccin asara take fa,baki suka tabe suna kallon gidan Suka fice driver ya maida su gida suna ta bawa Mami labarin gidan,Mami tace oh wannan yaro Yana hakuri Allah ya bashi mace ta gari an hadashi da kaddara Ni dama tun farko hadin nan bai min ba amma ba yanda zanyi sai hakuri.

Yau ni kuwa na gama karyawa na bar Masa nasa a dining na gyara ko Ina kwanciya a kujera da Niyyar hutawa bacci ya kwasheni har yazo ya karya a gidan ban sani ba baccina nake yi,bai tasheni ba ya fice ya tafi gidan abokinsa Khaleel,Yana zuwa ya sameshi zaune tare da matarsa da yaransa biyu,,matar Khaleel Sufia tace na Sabreen Ina kwana ya amsa Yana cewa ya kamata na Miki kyautar kirarin nan,dan Khaleel ya dauka yana Masa Wasa sannan ya ajiye shi Suka koma part din Khaleel suna palonsa,Khaleel yace Wai Dan Allah wace wacce na ganka da ita? Nasan abinda ya dameka kenan dan sa Ido labarin Rabi ya bawa Khaleel bai boye Masa ba,Khaleel yana gama ji yace haba Ina ganinta nasan ban santa ba, ba yar uwarku bace,Amma fa tana da kyau ba karya inda kasan itace tayi kanta,sai dai bata da kunya ashe karuwa ce Kuma bata yi kala da karuwan ba,ita Kuwa karuwancin bai nunata ba ashe Yar kwalta ce,amma Kai tunda harka bata yuwu ba Allah ya tsareka Ina ruwanka da ita ka rabu da ita Mana,Nawwar yace ni so nake ta daina ta koma gaban iyayenta,Yarinyar ta lalace da yawa yarinya karama tausayi ta bani so nake ta shiryu,dariya Khaleel ya dinga shekawa yace ko dai sonta kake Yi? Haba Khaleel amma baka kaunata wlh me zanyi da karuwa,Khaleel yace kaga Wanda ya kangare sai Allah shi yake shirya bawansa a Sanda yaso kaga tun bata jawo maka masifa ba iyayenka

5 Comments On YAR AIKIN KARUWAI
avatar
asmau-7

1 year ago

Reply

T

avatar
sadiya-9

1 year ago

Reply

Wonderful and nice novel

avatar
diaabdourahamane

1 year ago

Reply

Nice novel

avatar
bashar

1 year ago

Reply

Don Allah ina cikon labarin nan?

avatar
taskar

1 year ago

Reply

Replying to bashar

Dole fa sai dai ku siya a cigaban labarin a wurin marubuciyar, ga nambarta 08061929616

Please Login or Register in order to submit comment