Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

me kyau sunyi kyau daga nan aka dora da kida da rawa tare da sabon liki, babu Wanda zai so ya bar wajen nan,sai lokacin muka raba waina da miya aka sake ci da ruwa da lemo, bamu Ankara ba har 5:30pm sai Inna ce tazo tace Yan Kai Amarya sun shirya,sannan Muka tashi daga kida,masu kida Suka hada kayansu da motarsu suka tafi abinsu suna murna sun Sha kudi.
A gurguje nayi wanka sabo da zafi na canja cikin Net less fari yasha hadadden dinki na Sha takalmi da jaka fari aka min dauri na yafa mayafi me kyau fari da adon silver,turaruka na shafa Wanda kayana komai an tattara su tuni sunyi gaba Angwayen da Suka Fara tafiya su aka bawa Suka tafi da komai dama kayan lefe ne, Wanda na cire Kuma Sera ta ninke ta tattara komai a jakata da na zubo kayan sawa na biki suna wajenta tsinke namu bamu bari ba, Jangudo ne yace tunda Kai Amaryar ba addini bane iya kawayen ma sun Isa ga angwaye ai sun Isa Kai Amaryar

Ba sai an sake wahalar da Ango ba Watarana idan ta haihu sai aje Mata,Inna tace hakan ma shawara ce shike nan aka fasa a Raina nace da ace Ina da iyaye Dole sai an rakani dakin miji amma ya zanyi haka Allah ya tsara min wannan yasa zuciyata ta karye na fashe da kuka,duk sun zaci kukan Kai Amarya nakeyi Suka dinga dariya Yar bariki da kuka za a kaita dakin miji suna ta tsokanata, Nawwar ganin Ina kuka dariya ta Kama shi yace Amma Yarinyar nan ba karamar Yar rainin hankali bace lallai Ina ganin Yar duniya,ki gama tikar rawa gata dama zaman kanta takeyi ta Gama sanin da Namiji me yayi Saura.

Muna jikin Motar da Ango yake tsaye mu da kawayena kaf Inna tana cewa Allah ya tsare kinji Allah ya kade fitina,a zauna lafiya kinji dai nasiha ta to Allah ya bada sa'a ya bada zuria dayyiba na manta ma kuka nakeyi nace Ameen Ameen Allah ya bani me hankali,Inna sai da tayi dariya da su Star ana ta dariya har angwaye, Inna tace aure sai hakuri kiyi hakuri da mijinki komai yace to banda musu da gardama da taurin Kai,ba a jayayya da miji,Miji yafi Gaban Wasa,Nawwar Yana gefe yace dama ta rainani Kuwa Inna,Inna tace wallahi idan kina so ki gama da duniya lafiya kibi Allah kibi mijinki yanzu ba da bane baki da kamarsa,yanzu mulkinki ya Kare shi zai haye karaga shi zai Fara nasa mulkin sai yanda yayi dake,Nawwar yace ai tuni ma na fara Inna,Inna tace lokacinka ne banga laifinka ba dan nan kayi abinka,Amma mace dai ki sani Rabi bata da wani yanci Matukar a gidan miji take,ta kalli Nawwar tace wallahi kai Kuma idan ka zalunci marainiya ubanka zaka ci a wajen Allah yo Allah ba ruwansa,ka kula da ita ka Zama gatanta ka Zama mijin marainiya,kaga Allah Kai ya damkawa amanarta Amana fa aka baka banda banbanci tsakanin matanka ka kamanta adalci, Kar kaji Daya tafi daya iya kwanciyar aure ka wulakanta daya,su Star suka kaure da shewa, Nawwar ya kalli Inna da sauri,Inna tace ae zaka zuba min Ido ku maza imaninku a nan yake da kunji ba bayani to mutunci ya Kare abinda kuka iya kenan soyayyarku kwanciya da mace ba uwar da kuka iya a nan kuka iya soyayya musamman hausawa sai a lokacin za a fara Ina sonki bani da kamarki,kece gwanata,jarumata,dausayin raina, kece tekun zuciyata,ya turmin dakan dake lugude a zuciyata Nawwar ya sheke da dariyar da bai shirya ba,kowa dake wajen motar dariya yake su Seraline harda ihu,Inna tace yo ai mun sani muma zamaninmu munyi soyayyar nan tsiyar maza wacce ce bamu gani ba,sai kana haihuwa shike nan an juya ma baya sabuwa ake nema Allah yasa kai a kudu kake Allah yasa dai ka koyi halin arziki,dariya na dinga Yi a boye cikin mayafi,Nawwar ma Dariya ta kume shi Khaleel dake Gaban mota da Driver sai dariya suke Kamar ba gobe,Nawwar yace mun gode Inna za a kiyaye,Inna ta furta ato kun girma dai idan Kun gyara ruwanku idan baku gyara ba ruwanku Inna tana gida tana baccinta.

Zamu Shiga mota tace ban Gama ba ke Rabi na sanki da zafi yanzu ba a wa miji Fushi,ba Kuma a juyawa miji baya ke gaki Allah ya albarkace ki da Ido kamar Madara ki dinga sanyaya Masa zuciya da kallo,ke bakisan da kallo ma idan mace ta Isa sai tayi juya Miji ba,Nawwar Yana ta dariya yace banda ni Inna,Inna tace wane mutum karya kake yaro baka hadu da tsohon Hannu bane mu irinmu muka sa Namiji a gaba ai ya shiga Uku,Muka sake kwashewa da dariya kaji tsohuwa wa zai kalleta ma harda yabon kai, Rabi nace Na'am tace kuka bazai fishshe ki ba sai kin tashi sosai gidan kishiya zaki, ba a kishin fada,duka ko zagi gasa ake a wajen me gida,idan ta bashi Onga Kinga kayan Miya ne dai ko to karki sake kuyi abu iri daya a'a ke karki bashi Onga ki bashi Madara,Idan ta bashi Milo ke ki bashi farfesu,haka akeyin tsere Nawwar kunya ta kamasu Ni Kuwa ko a jikina nace to Inna tace yawwa dare nayi kuje sai munyi waya,muka shiga mota kowa ya shiga Driver yaja mota dariya Kawai muke Yi Kamar me,Allah sarki Inna na bata Atamfa da leshi da sabulai cikin kayan lefena,sannan na bata kudi su Wise ma sun bata kudi akwai dadin Zama.

Sauran duk sun rigamu zuwa airport muna zuwa dama jirgi na kasa Muka shiga da kayan mu Nan ma an Mana pics duk an watsa a media,har Muka sauka lafiya na Kira Inna nace mun sauka ta Mana fatan Alheri na rufa mayafina a Kai Amarya sosai,Mami da kawayenta su Uku da Maman Khaleel da Sufia a Airport suka tarbemu cikin shigar su ta Alfarma, sauran abokan Ango da Ango bayan an sake pics suka tafi kowa sai Khaleel da Nawwar Suka shiga mota driver ya ja su zuwa gidan Khaleel can suka Yi wanka a part dinsa Suka canja Kaya sannan suka Yi Sallar magriba da Isha suka zauna suna kallon pics suna Hira da labarin irin dadin da bikin yayi.

Mu kuwa Mami tana gefe na a mota da sauran kawayena a wasu morocin Muka nufi gidan Sabreen,Mami a mota tana ta min Nasiha sosai akan zaman aure karshe tace dan Allah ki kiyaye ki farantawa Nawwar shima ya samu farin cikin da duk wani da Namiji ke samu karki biyewa rudun duniya da kawaye ki kula da aurenki ba abin Wasa bane shine darajar duk wata mace, rayuwar waje da Kika Yi wannan ya wuce da ba yanzu bane a manta da waccen rayuwar a Kama wannan kinji Rabiah dan Allah kiyi hakuri da halin kowa ku zauna lafiya,Kar naji ba daidai ba,nace Inshaallah,Mami tace ke ba yarinya bace Rabia kin San komai a kiyaye,Nawwar ya nuna Miki gatan da ba kowane zai iya ba,nace na sani Mami karki damu Inshaallah tace yawwa Yar Albarka Allah ya muku Albarka a haka Muka karasa gidan an canja tsarinsa gaba daya komai anyi sabo abin ya bada citta, Sabreen ta tashi a bacci tayi wanka ta fito Palo tana kallon furniture din da aka canja komai na gidan an canja an gyara ko Ina Yana kamshi mamaki ya kamata tace nasan dai anyiwa gidan nan gyara to waye yayi shara da mopping ko Ina na kamshi,wayarta ta tuna da ta kashe yau kwana kusan biyu bata tuna kowa lokacin ta sha kwaya da yawa,wayarta ta kunna ta kunna Data ta shiga WhatsApp Kawai taga wasu duk sun cire status din wasu sun saka bikin sabo da an kashe kudi musamman Dinner din,taga pics farrrr jamcy ta turo da videos ta bude nan ma Nawwar ta gani da Rabiah da kawayenta kamar ango da amarya,Pics din maza ta gani a masallaci alamar wajen daurin aure,sai ga pics din Amarya da ango a wajen daurin aure ga kawaye sai rawar Dj,tana bude wani taga Nawwar yayiwa Rabi Kiss a filin rawa suna ruwan kudi an ci uwar Naira,ihu ta saki tare da mikewa tsaye Zumbur tace na shiga Uku na,guda taji a gidan motoci suna ta shigowa,da gudu ta fada dakinta ta cire atamfar da ta saka ta canja Riga da wando tace yau za a kwashi bala'i kafin na sanar da Baffa da Iyamami,dama ba samu damar daukan Baffa a pics ba shi Yana daura aure ya fice ya bar kauyen daga nan ma kasar ya bari ya wuce US Dan karma a dame shi,yace wa Iyamami da Yan Uwa da matansa ya tafi Us su basu San ma daga wajen daurin aure ya wuce ba yayi haka ne Dan ace ai baya gari ma aka daura.

Sabreen wuka ta dakko a kitchen ta rike tana huci Yan kawo Amarya Suka shigo Mami ce a gaba sai kawayenta da Kuma su Sera,ai Sabreen tana ganin gayyar su Sera sunfi ashirin suna guda suna cewa wata tara a zubo Mana twins,Wise tana shewa tace a bawa ango local government sosai,yau Ango zaiji banbanci ya samu GRA masu kirji fanko a ja baya,Allah ya taimaki ango an kawo masa me kirji a cike,Mami kunya ta kamasu gashi sunki yin Shuru sai fitsara suke suna cewa ayi magana mu naushi bakin mutum, da sauri Sabreen ta wayance wukar data dakko ta ajiye a Center table tace daga kitchen na fito Ina girki ashe kune ta juya salin alin ta maida wukar inda ta dakko,sai ta zagaye ta bayan kitchen ta fice waje tare da tare taxi ta fada motar ta bar gidan a million, tana fita a gidan ta fashe da kuka sai gidansu tana yiwa me taxi bala'i yayi sauri.

Mami tace Sabreen fito Ina da magana da ku,Shuru shuru,Sera tace ta gudu fa ta bar gidan Naga fitarta,Mami tace Allah ya kyauta to,Sama aka haura da ni cikin hadadden dakina nima,sabo da a saman ma part uku ne,part din Nawwar,Nawa sai na Sabreen,kowa sai kallon gida yake ana yabawa,dukkan kayan lefena da tarkacen kayana har na gidan Karuwai da kayan gyaran jikina duk an kawo suna part dina su Misha su Muka bari tunda baza suje kauyen ba su suka shirya min komai na part dina har kayan Suka goge Suka gyara gidan ko Ina Kal Kal dama dakin ogan yasa key,Basu shiga part din Sabreen ba,sun Sha mamaki irin yanda suke karaf karaf a gidan amma bata tashi a bacci ba,ko Ina kamshi yake na musamman sunyi aiki babba na gyara gidan.

A gefen bed dina na zauna komai nawa na dakin milk and brown ne,Ina zaune mayafi a kaina,sauran Suka ce to Amarya sai munzo nan da sati asha amarci lafiya,na dinga musu godiya Suka tafi,su Mami ma da Sufia tafiya sukayi ya rage daga ni sai Sera,Star da Wise,na cire mayafin Muna ta hirar bikin Muna kallon pics,nace in ya bari na siyi waya Zan tura please ,Sera tace wallahi Indai sun tabaki ki Kira mu,nace ya zama dole,ki kula sosai Kinga ta Fara daukan wuka Kar ta shammaceki cewar Wise Nace Allah dai ya tsare, Sallah nayi abina, Suka Shiga kitchen Suka Sha Madara da lemuka Suka dawo Muna zaune har 10pm sannan Suka min Sallama zasu tafi nace zanyi kuka karku tafi,Muka kwashe da dariya har ni, nace sai na biku ni Muna ta dariya,nace wayyo first night ya zanyi tsoro nake ji,Muka fito tare Muna ta dariya sai ga Sabreen ta dawo a compound ta ganmu har Amarya tace Yan bariki tayi ciki da gudu,shareta Muka yi Amarya ce da rakiya har waje kofar gida,Nawwar ne ya karaso da motarsa da mamaki glass ya sauke ya musu godiya sosai yace a fadawa sauran Yana godiya Suka ce zasu ji Suka Shige Napep din da Suka Kira sai gidan bariki, kirji na dafe nace Allah sarki Kwalta,Stree ohh duniya Ashawo work me Dadi da yanci ai Zan dawo ne soon ana sakina Zan dawo Yan Uwa Ina nan zuwa ba da dadewa ba nace bye bye Street Ina daga hannu,Nawwar Yana kallona Yana ji tunda a saitina yake glass dinsa a sauke yake,Kai ya girgiza yace in kin gama sai ki koma ko,ciki na shiga na koma dakina da sauri na rigashi shiga na zauna saman bed na jawo mayafina na rufe kaina zuwa fuskata na nutsu,ya shigo lokacin tsaki ya ja ya ajiye min ledata cike da nama da abin dadi,Daya ledar hannunsa dakin Sabreen ya nufa.

Ya isketa ta dora Kai a jikin mudubi tana rusa uban kuka,shi dariya ma ta bashi yaushe ta Fara kishinsa,Kafadarta ya dafa tare da furta Babyna lafiya bai taba kiranta da Baby ba sai yau,mikewa tayi tsaye Zumbur tare da daga masa Hannu tace dakata Malam me zaka ce dani zakayi aure ka fada min baza ka fada min ba sabo da cin amanarka sabo da zaka auri Karuwarka ai ka Dade kana cin Amanata tun kafin ayi aure ka Gama da ita dole ka boye min Kuma kaje gobe Iyamami tana nemanka,Murmushi yayi yace karki sake Kiran matata da karuwa ya Zama last idan ba haka ba Zaki ga abinda Zan Miki Kuma Iyamami ta Isa dani ne bazan je ba ki fada Mata kice nace baza a zo ba duk abinda zakiyi kiyi, aure kuma na kara ke kin Isa wace ke da sai na fada Miki tunda bacci Kika zaba kije ya isheki yaja tsaki tare da jefar mata ledar namanta ya fice abinsa.

Part dinsa ya shiga ya kalli ko Ina kaca kaca duk dirty babu me gyara Masa shi kyankyaminsa ma yaji a haka yayi wanka ya fito ya shirya cikin kayan baccinsa ya kwanta sai bacci,ni kuwa ganin yaki shigowa na bude naci abinda zan iya na ajiye sauran nayi wanka da brush nayi Shirin bacci cikin gown Yar guntuwa ko cinya bata rufe ba peach nayi adduoi sannan na kwanta baccin gajiya ko farkawa banyi ba sai asuba,na tashi Ina saman Sallaya ya dawo daga masallaci ya bude kofata a hankali tare da lekowa ya ganni saman Sallaya juyawa yayi ya wuce abinsa ban ma San ya leko ba,part din Sabreen yaje ya duba tana ta bacci tashin duniya yayi taki tashi hakura yayi ya koma dakinsa ya koma baccinsa.

8am na tashi na gyara ba garena Kal Kal Yana kamshi,fitowa nayi na gyara ko Ina har Palo dama ba dirty sabo da jiya an gyara,masu kula da compound sunyi nasu,part dinsa na shiga Yana bacci, toilet na fara wankewa sosai sai da ta dawo tana shining ko Ina,sannan na kunna turaren wutan na turiri Wanda ba hayaki yake ba da ruwa ake hadawa a kunna sai turiri Kawai, na fito a toilet na hau gyara Palon tunda na dawo palon ya farka a bacci amma bai nuna min ya tashi ba,gadon nasa na turawa na tura Yana Kai na kaishi gefe sai da na gyara side din sannan na dawo da shi inda yake dake ko waye akai kana danna Abu a jiki zai matsa da kansa,sai da nagama gyarawa shima dakin na hada turaren na turiri,na fesa room freshner me kamshin turaren wuta na, nazo na tattara kayansa kaf na koma toilet na zuba su a washing machine na wanke su tas naje na shanya a waje ta wajen garden,na dawo na iske ya shige toilet nace hmm ya tashi,haka na gyara bed din na canja bedsheet din sabo me kyau wancan na kwashe na kaiwa yaron gidan nace ya wanke a injin wanki idan sun bushe ya hada da kayan Nawwar dake shanye ya goge yace an gama.

Kitchen na shiga bayan na Gama duk wani gyarana ko Ina sai kamshi, na gaji Kawai tea na dafa na soya dankalin turawa da kwai na kawo dining na shirya komai,na leka Zan kirashi na same shi Yana shafa lotion a bakin kofar nace na gama breakfast na koma dakina wanka nayi na shirya cikin atamfata super me tsada Riga da skert nayi kyau sosai Kamar zanje biki.

Fitowa nayi na iske sai lokacin ma ya fito ya zauna a dining,Ina karasowa na Masa gaisuwar Yan Jagaliya nace yane ya akayi ne? Kallona Kawai yayi na furta ina kwana ka tashi lafiya,ya amsa min da lafiya,sanye yake cikin kana nan Kaya wasu grey Riga da wando marasa nauyi,tea din na hada Masa na zuba Masa komai sannan na tura Masa gabansa,na hada nawa Ina Sha
Yana mamakina duk surutu na yau banyi magana ba bance komai ba,ya bude baki zaiyi magana wayata ta dauki ruri,Murmushi nayi na daga tare da cewa Seraline,tace Amarya ya aka kwana nace lafiya lau ku fa tace lafiya sumul,ya gajiyarku?sai godiya ya amarcin fa an Sha kauna buri ya cika ko ta furta murmush na saki hade da dariya nace ae Kinga dake virgin ce da yanzu sai mun Zo gashi wannan dariyar baki Isa kinyi shi ba nace to ya za ayi,Ina ogan naku,Ogana dai ko, dariya Sera tayi tare da furta to ki gaida shi nace zai ji,Yana zaune yana Shan tea nace Seraline tace a gaisheka Ina amsawa yace,ya na ganki yau haka haka? Mika nayi da hamma nace gajiya ce kawai,rawar da kuka Yi ma ta Isa ta sa muku ciwon jiki,nace mun Sha aiki fa mijin Sabreen,Murmushi yayi yace mijin Sabreen ko ,nace ae ai nata ne ni da nazo temporary,hakane ya furta,nace na bar Mata kwanana gaba daya har na bar gidan nan na bar mata, jiya na kwana daya Ina ta irgawa kwanakin barina gidan nan kaga dai jiya aka daura kwana daya kenan, yace ke kin Isa kice Wai kin bawa wata kwananki ni fa Kinga ba abinda zanyi dake Hajiya,nace ai na sani nima ba so nake kayi wani abu dani ba yawwa ehe,Sabreen ce ta fito ta Sha wanka cikin kana nan Kaya tayi kyau tana zuwa sabon salo kujera ta ja ta zauna itama tare da furta Ina kwana Sweetheart, shi Kansa mamaki yayi bata taba gaisar da shi ba,sabo da Kar ya disgata yace lfy,ta ja cup ta hada tea dankalin gabana tasa Hannu ta janye da kwai sabo da tsokana,ban kulata ba na daure na share, Tsaki ta ja Wanda ya jawo Nawwar ya kalleta ya kamata tana kallona tana hararata, tace Yar tsuntuwa ma an iya girki ko a barikin Kika koya? Ko da yake ance karuwai sun iya girki fa,gashi kinci Sa'a kin auri daduronki,Nawwar ya Mata wata uwar tsawa, Murmushi nayi nace kyaleta ai gaskiya ta fada,Yar tsuntuwa ce Karuwa a da amma yanzu Kuma matar Nawwar dadiro na, na auri mijinki yanda ya narka kudi ya aure ni ke ba haka aka Yi ba,kyauta aka bashi ke lika masa akayi baya so aka Masa auren zumunci,kasa rike shi Kika Yi ya fita daukan karuwa Kuma ya sameni ya makale min da Kansa ya gani yace yaji a haka Yana so na sabo da idan bani to rayuwarsa tana cikin garari,ke ai kishin banza kike tunda baki San ma mene aure ba, da wata ce ke jiya a gidan nan baza ta iya bacci ba yanda muke zunduma ihun dadi daren amarci na tabbata da bakiyi bacci ba jiya to yau gidanku zaki tafi amma kina ta shaye shaye taya zaki sani Yar kwaya,Yar giya Yar Coccaine irinki dama wanne zaman aure zaki iya ai sai bacci...ya Isa haka bana son shirme Nawwar ya fada cikin fushi,na daki table da hanuna nace badai haka take so ayi ba to mu zuba mu indai fada ne harda na siyarwa dan kutmar...Dan me......shut up ya rike Hannu yace muje bana son rashin hankali,Yana Jana Ina tirjewa Ina wutsil wutsil Ina furta Dan babanki Yusuf da Uwarki Zuwaira munafuka Wanda basu iya tarbiya ba sai naci....Jana yayi muka haura sama da ya gaji ma Ina faman tirjewa sai ya daukeni cak,Sabreen ta saki kuka tana furta yanzu ta zageni haka a banza uwata fa Zuwaira tace yanzu Ina magana ta nada min uban duk ko ta gayyato karuwai suyi min jina jina to zata ci ubanta wlh nasan yanda zanyi tunda a fili tafi karfina.




*AL-KUTUBIYYA ISLAMIC MEDICINE*
_Jama'a kada ku bari wannan garabasa ta wuce ku,muna da nau'i magungunan gargajiya masu kyau da inganci_
_Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda inganci da sahihancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai-dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_

_nfection_
_Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace *SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI💯☑️*_

_Muna sayar da supplement gangariya irin wadanda ba su da matsala sai da su gyara garkuwar jiki da inganta lafiya, muna bayar da sari duk wani supplement muna da shi, kuma muna sayar da daya muna bada sari akan farashi mai sauki, muna tura kayanmu ko wane gari domin neman karin bayani a tuntunbi wannan lambobinmu dake kasa._
*08089965176*
*07084653262*





AsmaBaffa.
08061929616

An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number

5 Comments On YAR AIKIN KARUWAI
avatar
asmau-7

1 year ago

Reply

T

avatar
sadiya-9

1 year ago

Reply

Wonderful and nice novel

avatar
diaabdourahamane

1 year ago

Reply

Nice novel

avatar
bashar

1 year ago

Reply

Don Allah ina cikon labarin nan?

avatar
taskar

1 year ago

Reply

Replying to bashar

Dole fa sai dai ku siya a cigaban labarin a wurin marubuciyar, ga nambarta 08061929616

Please Login or Register in order to submit comment