Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tace yar nan ni baku bari ma nayi aikin ba a matsayina na Yar aiki kuka hanani aikin kuka ce ni babarku ce na zauna na huta,ai na gode muku 'yata,nace Hmm Baba kulu karma ki dauki kanki a Yar Aiki ki dauki kanki a Mamana kawai,Baba kulu tace na gode Yar nan Allah ya Miki albarka,Ameen na furta ta mike ta shiga dakinta sai da ta kalli dakin sosai sannan ta shiga toilet,Nima wanka nayi na kwanta dama bana Sallah yau na Fara period.

Auren Gaji Yana ta matsowa har Saura sati Daya duk wani Abu anyi lefenta akwati hudu su a kauyen gani suke tafi kowa har yanga suke,Kaya masu kyan gaske,Amarya ta Sha gyara Aunty Amarya da Gwaggo kullum hudubarsu suke ma Amarya,yau ma da Yamma suna zaune Gwaggo tace kinji dai Gaji Muna fada Miki kina da ilimin zamani kin waye duk kauyen nan wa yayi makaranta ta gaba da sikandire sai ke da Mairo to kiyi amfani da bokonki ki nunawa kishiyar nan ke ba jahila bace,idan ta Miki karki ragawa shegiya ki taka ta,Kuma bance ki dagawa kowa kafa ba duk Wanda yace zai taka ki a Dangin miji,Aunty Amarya tace miji Kawai shi Zaki rike Kam da kissa da kisisina irin tamu ta Mata sannan ko shi yazo da rainin hankalinsu na maza karki yarda ki dora shi a tsarinki,Gaji tana ji tace ai Inshaallah ma Ina shiga za a saki uwar gidan ko tayi zaman bakin ciki,Gwaggo tace shaallahu Kuwa rubutun nan kinyi amfani da shi yanda aka saki ko? gaji tace da gudu ma ai duk abinda kuka bani ba Wasa,Aunty Amarya ta dakko sabon pillow din Amarya ta farke Kan dinki ta cusa laya a ciki ta mayar ta dinke da zare da allura tace Kinga babu me sanin akwai wani Abu ciki idan aka saka yadin gado ki cire pillow din da ya zuba Miki a gidan ki saka Masa wannan kullum ya dinga kwana akan laya, tace to,Gwaggo ta irga wake guda dari ba daya ta dakko kwai Wanda an gama rubuce jikin kwan da ayoyi ta hada tsubbunta aka dafa aka bawa Gaji ta cinye,Cikin lotion din da gaji take shafawa na gyara fata nan ma wani rubutu aka dan zuba aka cakude a cikin man,tozalin gaje na musamman ne da wani siddabaru a ciki Haka turare duk da sunan gyaran amarya ne, kafin biki sai da aka gama tsuma Gaji,Bangaren uwar gida Kuwa tunda ta tabbatar Alhaji Kabirunta Danbinni aure zai Kara itama iyayenta Suka tashi tsaye dama bata da uwa bata da uba a hannun kakarta ta girma kakarta itace ke karbo Mata magungunan tsubbu wajen Malamai itama tana ta tsuma kanta gashi gida daya zasu zauna da Gaji,tace in Banda Kabiru ma dabba ne ni Zayyanatu ai shike nan ayi mu gani wlh idan tazo ma Sai ta fita ta bar min gidana a shirye nake, Saura kwana uku daurin aure Zayyanatu tun kafin ayi jere ta shiga bangaren Gaji ko wanne kusurwa ta yarfa ruwan rubutu da tsintsinya ta fito ta rufe.
Bangaren su Gaji iyayenta sunyi sunyi suje suga gida tunda yace ya zubawa Gaji furniture ba sai sun siyi ko cokali ba komai akwai amma sai hanya hanya yake musu karshe ma yace shi yafi so idan an Kai Amarya a Yaba Masa da irin bajintar da yayi ya nuna musu hoton katafaren gidan a waya sai Murna suke yi yace sauran idan anje za a gani yasan sai sun gode Masa,daga Jin Haka sai hankalin su Gaji ya kwanta abinsu dama yace shi Dan Izala ne baza ayi Masa party ba albarkar aure yake nema,ranar daurin Aure 11am mutane Suka taru sosai da Dangin ango dana Amarya harda abokai aka sheda auren Fatima Usman da Alhaji Kabiru Danbinni Kan sadaki dubu talatin da biyar ko ganin Amarya baiyi ba Suka koma birni abinsu sai waya ya Mata.

Amarya kuwa an hade cikin leshi fari da Golden ga jaka da mayafi cikin Yan school kawaye da Suka zo wata tana make up itace ta tsara Mata kwalliya da dauri ba karya Gaji tayi kyau dama kuma ta kara haske sabo da man da take shafawa me kyau,Gaji ango Yana sheda Mata an daura ta tambayi wasu Yara da Suka shigo gidan maza,ko kunya a gaban mutane dangi da kawaye tace Kai Sadakina Nawa? Yara Suka ce dubu talatin da biyar Gaji tace Kai dalla ku rufe mana baki jahilan banza bakwa zuwa makaranta ta ya zaku gane lissafi,wata tsohuwa ce ta shigo tana guda Amarya tayi goshi dubu talatin da biyar Sadaki ayiririir...wasu ma yan matan Suka shigo Sadaki talatin da biyar,kowa yazo sadaki dubu talatin da biyar, ai jikin Gaji yayi sanyi ta tsaya sororo tace naji masifa yanzu Danbinni ko waliyyai na ne Suka yanke Masa haka ai yasan na wuce ajin dubu talatin da biyar sai kace kudin kajin turawa guda biyar ko tinkiya karama ta kiwo,da ilimina da komai ubana ya kashe min kudi naje birni nayi karatu makaranta ta gaba da secondary sabo da Allah,ubana ya sakani a primary na Gama ya biya min secondary na gama bai gajiya ba ya sake Nemo min admission na shiga college na karanta Hausa English na gama aiki Kawai nake jira amma duk a dubu talatin da biyar Zan Kare,eyye Ni ba mummuna ba mashaallah dani, gani da hankali,Ina da burin bawa yarana tarbiyya wani wawan Tsaki taja ta fige daurin dankwalinta da aka mata ta zauna duk kowa sai jinta ake ana kallo,waya ta dakko a jaka ta Kira Danbinni bugu daya ya daga kafin yayi magana ta lullube shi da masifa

Haba Danbinni a matsayinka da kudinka ka kalleni Kamar ni zaka biya Sadakina dubu talatin da biyar ko waliyyai na ne Suka yanke haka a matsayina ai ka kara yanzu dan wulakanci ma ka cike biyar din Mana su cike dubu arba'in amma Wai wani talatin da biyar mece dorin biyar din,da ilimina da komai ko yara Muka haifa kasan fa ABCD da sauransu duk Zan koya musu su Alif,ba'un,ta'un duk a dubu talatin da biyar nufinka Zan zauna na koya musu to wallahi ka shirya iya kudin daka bayar iya abinda zaka gani a gidanka,Danbinni yayi Murmushi yace ke me Kika dauki aure ne?Ashe ilimin da kike ikirari Baki da shi to an fada Miki siyen mutum ake a aure shi,Ibada ce fa Zaki yi, ke yanzu Indai har kina da tunanin akwai Dan Adam da zai iya biyan kudinki to lallai baki San me kike ba,ai ko silin gashinki Dan Adam Bai iya siyansa a duniya bare sauran jikinki da komai ma,domin silin gashinki daya idan ya cire duk duniya babu me iya fito Miki da shi sai Allah to akwai Wanda zai iya biyan wannan kudin ke kina tunani? Tsaki ya ja tare da kashe wayarsa,Gaji tace ka gama dani Kawai tun daga nan Gaji ta daina shagali.

Sai Yamma ana Shirin Kai Amarya Dagaci ya shigo gidan ransa a bace ya Kira Gaji ta fito daga cikin kawayenta ya irga dubu talatin da biyar cas yace Gaji gashi kudin sadakinki sai ayi hakuri,Gaji tace Wai Baba da gaske talatin da biyar idon Gaji ya ciko da kwalla,Dagaji yace Hmmm Gaji yaron nan yau ya gama kunyata mu a idon duniya ki godewa Allah ma da aka daura auren Saura kadan a fasa
Gwaggo ta dafe kirji sunja gefe suna ta kuskus Yan biki suna kallonsu kowa yasan ba abu me dadi suke tattaunawa ba

Dagaci yace Danbinni da Suka zo da danginsa Muka yanke sadaki dubu dari mu a tunaninmu mun Masa sauki da karamci sai kuwa danginsa Suka Yi tsalle Suka dire Suka ce ai su dansu baida halin haka mamaki ya kamamu Suka ce a musu ragi,Gaji Zo ki ganmu inda kisan an jika biri a ruwa haka na koma na zaci karya ne, ke yo ba sai aka Fara ciniki ba wallahi Gwaggon Mairo inda kisan na kai Akuya kasuwa haka a bainar mutane Muka dinga cinikin yarki Gaji,Muka sakko dubu tamanin Suka ce Albarka,Muka dawo dubu sittin Suka ce Albarka,dubu hamsim, arba'in duk Albarka a talatin dinma sai da Liman yasa baki yace wallah idan basu Kara ba bazai daura aure ba Taya zasu Zo Masa da zancen radio da kullum ake fadar farashin Sadaki Suka ce Basu da ciko da kyar aka samu wani a wajen cikin abokai ya cika musu dubu biyar sannan aka daura aure,duk garin nan labarin mu ake Yi yanzu Maganar muce take trending inji yan media Suka ce trending, Dagaci ya kalli Gaji yace da alama akwai karya a lamarin Danbinni duk yanda akayi Danbinni ko airport bai sani ba shi da kanshi ya sawa Kansa Alhaji Danbinni makaryacin banza,Dagaci ya sake kurawa Gaji Ido dake Hawaye yace Gaji ta Yan kudu Suka ce you are in Soup,gaji ba Miya Kawai ba Hot Soup me zafin bala'i sai dai Allah ya tsare yanzu za a kaiki mu Kuma Muna nan Muna jiran tsammani muji me zai faru a can gidan Danbinni,Gwaggo tace na shiga Uku ni Gwaggo Anya ba mafarki nake ba,Dagaci yace bude idonki tar yamma ce karfe Uku da minti goma biki akeyi na Yar mu Gaji Muna cikin tararrabi,Gwaggo tace ba Danbinni ba ko Dan Madina ne Gaji in kinji wuya ki dawo gidan ubanki karki zauna bance kiyi hakuri ba karki sake kiyi hakuri a zaman aure a wajena ba hakuri kina Jin ba dadi ki gudo,Dagaci yace af da kaina zanje na dakko 'yata.

Gaji tunda ta koma wajen kawaye take faman rusa kuka an zaci kukan rabuwa da gidane basu San abinda Gaji taji ba shike damunta,Mairo ma taji labari Gwaggo ta fada mata itama sai da tayi hawaye,Aunty Amarya Kamar yaranta sabo da su zamansu da Gwaggo lafiya sukeyi basa kishi basa fada sai bacin rana matsalar kowa ta kowa ce Kamar Yan Uwa sabo da tsiyarsu tazo daya halinsu yazo daya rashin Imaninsu daya,Yamma nayi motoci biyu kanana kacal Danbinni ya turo Daya ta Amarya da kawayenta Daya ta dattijai Amarya tayi wanka ta canja wani material me kyau ta Sha kyau aka tafi kaita dakin miji Nasihar Gwaggo da Gaji Kawai idan taji wuya ta gudo gida,Shima Dagaci yace ni da kaina zanzo na taho da abata,Aunty Amarya kuwa tana kusa da Gaji itace zata kaita daki da wasu dattijai sai Mairo da wasu kawaye su hudu.

Mu Kuwa washe gari da asuba bayan munyi Sallah bacci Muka koma sai 9 karar wayata ta tashe ni Ina dubawa Naga Saurayina wato Nawwar dagawa nayi cikin muryar bacci sallama nayi masa ya amsa cikin muryarsa me dadin saurare sannan yace hope dai kinyi Sallah,Murmushi nayi ba kunya ba komai nace a'a wallahi diga nake a bule nake yau Jini nake ka gane,na rasa dalili sometimes Kawai sai naji magana fit ta fito daga bani ko bana so na fada sai na fada Ina so na dinga Jin kunya amma na rasa dalili na kasa,Ina so ko Yaya na nuna cewar ni ta gari ce amma abin yaki, yace naji to ko kunya bakya ji,nace ai magana ce ta gaskiya kaga ma yanzu...katse ni yayi yace anjima kadan Zan kawo muku breakfast,nace to kayi sauri yunwa nake ji, wayarsa ya datse,wanka na shiga nayi da brush na fito na shirya cikin wata Yar Riga Yar kanti har kasa wata me hannun vest daga sama Tasha roba ta same kasa ta dan bude kadan,nayi kyau shape dina ya fito sosai,Baba Kulu na samu ta fito ta dakko tsintsiya zata fara shara,da sauri na karbi tsintsiyar nace haba Baba ga yarki yaushe zaki shara Ina nan ki zauna ki huta zanyi komai,Baba kulu baki ta saki tace Yar nan Nifa Yar aiki ce,nace ba dai tare dani ba akwai abinda dai zan iya baki ki tayani amma banda me wahala,tace ayi haka Kuwa nace gashi ma anyi ki zauna zai kawo Mana abinci tace to Yar Nan Allah ya Miki Albarka , ina ta share Palo naji knoking tare da turo kofar gaba daya wani kamshi na musamman ya daki hancinmu,dagowa nayi na kalli bakin kofar sai da gaba na ya Fadi ganinsa da wani irin kyau na daban ka rantse balarabe ne Kuma a haka ba wani gayu yayi ba 3qtr ne a jikinsa da rigarsa me gajeren Hannu rigar tana da jerin botin a gaba da rigar da wandon irinsu daya irin kyan da Suka Masa ya baci sai kallonsa nayi baki ya turo gaba nayi sauri na dawo hayyacina sannan na karasa gabansa na rada Masa a kunne irin wannan kyau sai ka jawo na maka fyade, Ina kwana na furta ka tashi lafiya ya amsa da lafiya sannan Suka gaisa da Baba Kulu ledojin na karba a hannunsa kaina ba dankwali na gyara gashina me tsayi da kyau, nace ka zauna mana,kujera ya samu ya zauna Baba kulu na bawa nata ledar tana karba tayi godiya ta Shige dakinta ni Kuma na zauna a kujera Muna facing juna,na shiga kitchen na barshi Yana latsa waya plate na wanko har biyu da cokula na fito,yace sai dai kuyi manage fa ba tea, wani chips ne da Naman kaza sai wata Kalar fried rice da pepper meat,sai fresh Madara da ruwa da lemo juice,glass cups na kwaso mana na juye abincin a plate biyu sabo da Leda biyu ne ya bani Banda na Baba kulu,Fresh milk din na zuba Masa a glass cup tare da Mika masa Ina cewa gashi,kallona yayi kadan yace kin iya abin masu aure why baza ki samu Miji kiyi aure ba,Fuska na bata nace ni dai bana so, shi dai shanyewa yayi na Mika Masa plate din chips and chicken ya karba Yana ci da fork da wuka ni kuwa Hannu na wanko na zauna Ina cin nawa,Ina ci Ina Santi nace Karuwanci wato duniya ne na kurbi ruwan juice nace badan Karuwanci ba Ina Zan tsinci kaina a nan yanzu kuwa dalili yasa sai Dadi nake ji wayyo Dadi zai sa nayi kuka ai duk Wanda yace nayi aure na bar karuwanci to ba karamin makiyi na bane,magana kike fada min ni makiyinki ne ko? Lemon dana kurba na hadiye da sauri nace haba ai duk duniya bani da kamarka kasan me na tsura Masa Ido nace I love you sha'awarka nake yi ka kara lalatani don Allah,baki ya saki yana kallo na a ransa yace wannan kuwa zata shiryu Anya, Fuska ya murtuke sosai tare da ajiye min abinci ya mike da sauri na rungume kafafunsa da hannuna biyu tare da furta kayi hakuri dan Allah bazan sake ba sai kana min Uzuri ni Jahila ce ka sani ba boko kasan rashin zaman aji, kafafunsa ya kwace zai fita nayi sauri na mike tsaye tare da Shan gabansa nace kayi hakuri please nima Watarana mamakin kaina nake yi ban San Sanda nake furta irin wannan maganganun ba Ina so na daina na kasa,wallahi da ba haka nake ba idan kaga Saliha Shuru Shuru to nice,Indai kina so in hakura sai kin yarda Za kiyi aure,Nan take idona ya ciko da kwalla nace wlh ni bana son aure idan ana min zancensa ma ji nake zuciyata Kamar zata fito,Salati yayi a ransa a fili yace sunnar kike adawa da ita lallai bariki ta Miki illa ya taka zai fita,da sauri na riko hannunsa Yana juyowa ya kasheni da mari yana huci idonsa ya canja Kamar wani zaki,tsoronsa ya kamani na dafe kumatuna na tsaya na zaci akan auren ya mareni sai na fada kirjinsa na fashe da kuka wani wawan hankadarwa ya min Kamar me Aljanu ya fisgo Wayar Tv ya Fara zuba min Yana masifa yace sa'anki ne ni Ina daga Miki kafa bakya ji ko muharraminki ne ni ko an fada Miki ni Dan kwalta ne irinki, ihu nake yi na zube a kasa Ina bashi hakuri,Baba kulu tana ji tace lallai ba shakka zaman bariki suke in ba Haka ba wacece Namiji na dukanta tana bashi hakuri haka,Fitowa tayi ta rike wire din dake hannunsa tana cewa haba Alhaji kayi hakuri Mana,shi kuwa sai kokarin fisge Wayar yake yi yace kyaleta bata Sanni bane dan Ina kyaleta,da yatsa ya nuna Ni yace duk ranar da Kika sake min Maganar banza wallahi sai kin gane kurenki Kuma Allah yasa na dawo gidan naji kin fita wani wajen nonsense ya furta tare da dungure min kai ya zuba min rankwashi kwasss....Ina kuka ban San Sanda nayi dariya ba yanda ya dungure min kai ne ya bani dariya,ganin Ina dariya ba karamin daure Masa Kai yayi ba yace Yar nan ba kalau take ba Rukiyya Zan kaita wata rana, Tsaki ya ja ya juya ya fice Ina cewa abincinka fa? Bai kulani ba na mike da sauri na Bude kofa har ya kai jikin mota nace Zan turo maka list din abinda muke bukata na kayan abinci,ko kallona baiyi ba ya shiga motarsa benz baka ya bar Estate din.

Sabreen Kuwa ganin bata ganni ba tasan na bar Mata gida sai Murna har da Kiran kawarta Jamcy ta fada Mata suna murna Jamcy tace Saura ke sai na hada Miki masifa a fili kuwa tace Ina tayaki murna kawata,Haka Sabreen ta sanarwa Mamanta na bar gidan Mama tace shege aka ce baya ji ai duk wani Namiji dole yaji tsoron matarsa yanzu dai ki rage shaye shayen nan dan Allah ki lallaba ki samu ciki kinji Sabreen Mama tayi Maganar da lallashi Sabreen tace an gama Mama.
Baffa ne ya samu Mamin Nawwar yake balbala Mata masifa ta ya Auta Nawaf zaizo na uku a ajinsu,tace yaro a ajinsu yazo na uku ai yayi kokari

Tsawa ya Mata ke dalla rufe min baki ke dai baki iya tarbiyya ba bakya nuna musu Abu yanda ya kamata kin jawo Ina asarar kudin tara ni ga me kudin banza, duk yaranki basu da kokari dakikai ne,Amma ai yaran amaryarka masu kokari ne tunda naga Haidar yazo na 10 amma ita nata kokari Suka Yi Nawa yazo na uku kazo kana min fada ita ka kyaleta har murna kake yi ni sabo da baka so na ka tsaneni,in Banda ma ka rainani da nuna banbanci mene Nawa a position na yaro ita Ummyn Haidar bata laifi a wajenka kullum nice sabo da yanzu na girma na tsufa ga matashiya wallahi kaji tsoron Allah hakkina sai ya kamaka kwanana ma da kake tauye min ka bata sai dai na dafa na Kai maka itace da kwanan Miji Allah sai ya saka min inyi girki wata katuwa da kwana da miji bazan yafe ba,Mari ya zabgawa Mami dai dai Sanda Nawwar ya shigo Marin nan me karfi sai da fuskar Mami ta tasa yatsunsa reras a kumatunta abinka da fara,Ido Nawwar ya runtse hannunsa ya nutsa a cikin sumarsa me yawa da santsi ya hangitsa,nan take idonsa ya canja kamanninsa Suka sauya ransa ya Matukar baci amma ba abinda ya Isa yayi dagowa yayi yace Baffa....ba ruwanka muryar Mami ta ratsa kunnuwansa,bai hakura ba yace amma...shut up ta furta cikin karaji Shuru yayi,Baffa Yana muzurai Yana wani cin magani ya bige babbar rigarsa tare da furta da kayi magana Mana, uwarku ko ba mahaukaciyar bace dabba ce bata da hankali Kuma Watarana idan bata taka a Sannu ba sai na tsinke ragowar igiyar rubbish ya sake bige babbar riga fat ya fice a fusashe,domin shi ba sai Mami taje bangarensa ba da Kansa yake zuwa yaci mutuncinta ya Kara gaba,Yana fita Ummyn Haidar ta cakare matar so kenan ta sa Kaya na gagara ta kwama glass dinta tayi kyau itama kyakyawa ce amma bata Kama kafar Mami ba a kyau,Baffa Murmushi ya saki ya karasa inda take tare da furta sorry my love I keep you waiting,tace ba komai ka dinga dan sassautawa Mamin Sultana kasanta ballagaza ce duk da bata da nutsuwa ka dinga binta a hankali har Sanda zaku rabu lafiya,yace ai ba karamin hakuri nake da ita ba,Hmm na sanka sarkin hakuri ne ka Kara akan Wanda kake da,yace Inshaallah ya rike hannunta tare da furta muje ki rakani meeting din nan ni ake jira ya rike hannunta Suka shiga rantsatsiyar motarsa driver ya ja suna baya.

Bangaren Mami Kuwa Samanta ta haura Kawai ta Shige bedroom dinta,Nawwar ya bi bayanta Idonsa yayi ja da gani kasan Yana cikin tashin hankali,Mami ya iske a tsaye ta juya baya hawaye Yana sintiri a kumatunta bakin cikinta yanda yake zaginta a gaban yayanta, Nawwar gabanta ya zagayo ya tsaya ya rungumeta kokari tayi irin na iyaye ta danne kukanta ta maida shi ta shanye abinta hawayen dake kumatunta yasa hannu ya goge Mata tas ta kalle shi Suka hada Ido tayi murmushin karfin hali,a hankali ya furta kiyi hakuri Mami ko ki muje ki koma gidana ki huta tare da su Sultana,ko kin tafi Kinga yace ko Ina Zaki ba ruwansa karki sake tambayarsa unguwa baki da amfani a wajensa yace idan ma sama Zaki tashi ki tashi,Ki taho mu koma ko Zaki samu sauki,Mami ta kalle shi tace da wata me hankali ka aura sai na koma amma Sabreen ce Nawwar sai ta karasani,yace to ga sauran gidajen nawa Mana ciki ki zabi Wanda yafi Miki,Mami tace na zabi gidan nan na can nesa inda ba mutane sosai is better amma kasan bazai bari na daukar Masa Yara ba ko Daya Kuma idan na barsu za a gallaza musu ne gwara na zauna kusa da Yara na sadaukar da farin cikina ga yarana duk tsiya gwara na bawa yarana tarbiyya da kaina idan na tafi ma hankalina Yana kansu,to idan sakin ki yayi fa sannan da yaran da su ya auro ki ba sai a bar Masa abinsa ba,no Nawwar uwa daban take ba irinku uba bane kayi hakuri Kawai Zan dai iya zuwa gidanka nayi sati biyu idan na huta sai na dawo,Yace Alright wancan gidan dai na wajen gari inda ba mutane? Mami ta daga Kai inda ba Wanda zai dameni,yace an gama gobe zan kaiki bari a zuba Masa Kaya wani part dinma ba a Gama ba ginawa akeyi na
sani Dan Albarka Allah ya muku Albarka,yace su Hamra suna school Kai Kawai Mami ta daga masa yace to yaje ya kawo Mata ruwa me sanyi yace Dan Sha ta karba ta sha sannan ya fita ya bar gidan yasan tana bukatar a barta ita daya, hankalinsa bai kwanta ba sai da ya Kira company na wata masu tsara gida a zuba furniture da komai na buka ko cokali baza ka nema ba,suka je Suka ga gida ya Fadi yanda yake son komai ya biya kudi washe gari da wuri aka hada komai da yace yanda ya dace na Yan gayu,abinci ma Mami baza tayi ba shi zaina kawo Mata Kawai hutawa zata yi ga gidan daf da bakin ruwa.

Tunda ya dakeni ya tafi bai dawo gidan ba sai kayan abinci Naga an kawo a mota an shigar da komai store na shirya kitchen Muna zaman mu da Baba kulu tana bani hakuri akan dukan da na Sha duk da bata San me nayi Masa ba,ranar girkinmu mukayi ban ganshi ba sai washe gari da rana 2pm Ina dakina a kwance Ina sauraron audio na novel Wanda S Zaria Tv ta karanta a YouTube channel a wayata sabo da na gaji da kallo,Sallamarsa naji a hankali cikin muryarsa me dadi,Fitowa nayi sanye nake cikin doguwar Riga kasancewar kaf kayana na gidan da ya Fara kaini ya Aiko min da su,Fitowa nayi a nutse ya Saba ganin Ina gaishe shi yau yaga na zauna a kujera nayi mirsisi yace baki iya gaisuwa ba,Ina yini nace Kawai na shiga harkata shi sai yanzu ma ya tuna ya zaneni,ya sake furta haka akeyi,banyi musu ba na durkusa nace ka yini lafiya tsaki ya ja ya zauna duk na ganshi wani iri ba yanda na Saba ganinsa

5 Comments On YAR AIKIN KARUWAI
avatar
asmau-7

1 year ago

Reply

T

avatar
sadiya-9

1 year ago

Reply

Wonderful and nice novel

avatar
diaabdourahamane

1 year ago

Reply

Nice novel

avatar
bashar

1 year ago

Reply

Don Allah ina cikon labarin nan?

avatar
taskar

1 year ago

Reply

Replying to bashar

Dole fa sai dai ku siya a cigaban labarin a wurin marubuciyar, ga nambarta 08061929616

Please Login or Register in order to submit comment