Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sun gano ka rabu da ita,kasan Baffanka baida hakuri tam Kai Ina Kai Ina Yar bariki,Nawwar yace tab ai ka fada a banza ma Sai ta shiryu Inshaallah gidana ma Zan kaita ta zauna a can sabo da gudun shedan Kar ya shiga tsakani,Ashe zaka hada yaki,ai a matsayin Yar aiki Zan kaita ko me na ce zata yi bata da matsala ita Indai zaka biyata kudi,Khaleel yace bana goyon baya wlh Kuma duk abinda ya faru Ka kuka da kanka,ae naji cewar Nawwar ya canja zancen ma don Kar Khaleel ya dame shi.

Haka naci gaba da Zama a gidan Nawwar Kamar wata matar aure na gaji ji na nake Kamar a kurkuku yau da yamma ya kwana biyu bai zo ba,sai na gudu daga gidan tare da kashe wayata tunda yanzu Yana da number ta Kar ma ya sameni na gaji yanci nake so,Saratu ta ganni katsam bayan Sallar Isha ta dinga min dariya,nace na gaji wlh bazan iya ba,Kinga bari nayi Sallar Isha mu fita yau Zan fita titi abina bazai hanani yanci ba,Sera tace har yau fa ke kina Sallah nace sosai ma,Ina yin Sallah na dakko wata sabuwar gown dita da kadan ta haura duwawu na saka na saka takalmi me tsini naci kwalliya tare da saka hular gashi wata sabuwa me kitson twisting Wanda tsayinsa ya wuce duwawu Muka gama shiryawa Muka fice titi inda muke tsaiwa, a daren Nawwar yazo gidan amma ya samu bana nan,Ilu ya tambaya Ina Rabiah fa? yace ai ta fita gaf da Sallar Isha,da fada yace me yasa baza ka fada min ba ka barta ta fice,ai ni ganin bata fita shi yasa kuma tace abu zata siyo a chemist,Tsaki ya ja ya shige mota hankalinsa tashe ya duba bai ganni ba direct gidanmu ya wuce na karuwai,motar yayi parking ya fito ransa a bace Kamar zaiyi duka ba kowa a gidan sai wani Dandaudu,yace Miracle fa tana gida? Dandaudu shewa yayi Yana tafa Hannu yace karuwai dama suna Zama da dare ne? Ehehe ai baka sani ba ai karuwai basa bacci da dare sun fita aiki zauna nan kana jira baza ka gansu ba sai da safe ai suna street nima yau hutawa nake shi yasa ka ganni a gida ni kaga nayi nan yayi tafiyarsa,Shuru yayi ya tsaya Kamar gunki sai da ya gaji ya shiga motarsa ya fito daga layi ya nufi inda yasan muna tsayawa,tun kafin ya karasa ya hangoni da tsinannun Kaya a tsaye, a gabanmu yayi parking ya bude mota ya fito,ina ganinsa haushi ya kamani na zumburo Masa baki.

Tsawa ya buga min Shiga mota muje,harara na watsa Masa Ina dire diren kafafu nace ni Allah bana so na gaji kamar Ina prison ni ko kudin ne bana so ka barni nayi rayuwata kaje kayi taka,mota nace ki Shiga ya furta Kamar zai dakeni sauran karuwan suna kallonmu baki bude, hannuna ya fisga ya jani na tirje ni ka kyaleni bazan je ba,Ina tirjewa harna zube a kasa Ina ta burburwa Ina Shure shure,Tsaki ya ja ya sakar min hannu,sai ya daukeni cak Ina wutsil wutsil ya bude gaban mota tare da jefa ni ciki ya rufe ya Shiga mota yaja muka wuce gidan dai da ya ajiyeni,Yana yin parking ya fito na fito Zan sake guduwa tsawa ya buga min na tsaya cak tare da juyowa yace come karasawa nayi gabansa Ina Kunkuni mari ya kwada min na dafe kumatuna da sauri na kalle shi cikin karaji yace Ina alkawarin da Kika min Zaki zauna? Mene a cikin karuwanci,karuwancin ma na titi ke bakya Jin kunya musulma dake hausa Fulani mene birgewa a karuwanci,bance Miki Zan biyaki kudi ba,har albashi na saka Miki duk wata,nace Zan maidaki school dan Kawai na inganta rayuwarki ba sonki nake yi ba karki Raina min hankali wallahi Kika sake barin gidan nan ba izinina sai Kinga abinda zan Miki useless girl baki San ciwon kanki ba kina yamace kalleki karuwanci bai dace dake ba,kuka zanyi Masa nace ai ni Kawai so nake nayi Ina so ne sai naji Ina son Karuwancin,shut up ya buga min tsawa shashasha wacce bata San darajar kanta ba wuce ciki,tsayawa nayi ya buga min tsawa shiga nace ya furta a tsawace, da gudu na fada ciki,Yana shigowa ya matso kusa dani ihun tsoro na saki na ja baya Kar ya dukeni, yace karki sake karki sake, kika sake zaki ga ba daidai ba yaja tsaki ya koma wajen me gadi yace idan ka sake barinta ta fita a bakin aikinka,Ilu yace Zan kiyaye, ciki ya koma Yana shiga yace tashi ki canja Kaya wannan yan iskan kayan sai na Kona su mijinki Kawai Zaki sakawa,tashi nayi Sadaf Sadaf na koma na canja silk material marar nauyi na fito,Ina Fitowa Kamar ba nice ya gama zazzagawa ba nace abinci fa a dafa,shi da Kansa a ransa yace bata da zuciya ya tabbata da wata ce ranar ko kulashi baza ta sake Yi ba ko matarsa ai sai suyi watanni tana gaba da shi,yace kin bani ne abincin,sum sum na Shiga kitchen na Masa jullof din taliya ta Sha kifi da kayan lambu, kawo Masa nayi har gabansa nayi serving dinsa Nima na zuba tawa Muna ci muna kallo,yace baza ki fada min wace ke ba I mean tarihinki,Ina cin abincina Ina bashi labarina komai ban boye Masa ba,yaji tausayina da yaji bani da kowa a duniya Yar tsuntuwa ce Ni,yace Kuma shine baza kiwa maraicinki gata ba ki Zama ta gari sai ki lalace,Shuru nayi Ina jinsa yana ta min fada ni dai bance komai ba, yace gobe ki shirya gidana Zan maidaki, kallonsa nayi nace matarka fa ni kasan bani da kunya Kar nayi abinda zata ji haushi in ta min ba kyaleta zanyi ba kasan halinmu,ai yar aiki Zaki zama aiki Zan daukeki tunda kince ke baza ki aure ba baza ki makaranta ba Mene amfaninki Kawai na kaiki can kiyi aiki ki gyara gida kiyi girki,nace yanzu Yar aiki zan koma haka gaskiya tace? Cutar dani zaka yi,ko baza ki abinda nace ba? Kamar zanyi kuka nace zanyi,Kuma kina kwalliya zata ce kwace Mata miji Zaki Yi ta Miki dukan tsiya,Nace wlh sai dai na daketa Kai kasan karfina kuwa hmm amma tunda kace nayi zanyi ai zaka biyani ko? Yace kudi ma Zan Kara miki, ihu na saki nace wane ni nace bazan Yi ba ai ya Zama dole,yace Good girl Kinga mun huta da tsoron shedan,ka huta dai Amma Ni kaina ai shedaniyace me zaman kanta na furta,yace to babu kyau dai kebewa mace da Namiji shi yasa Zan maidaki a matsayin Yar aiki sabo da dangina da iyayena da matata ce za a dameni amma idan a Yar Aiki Kika je sai kiyi zamanki a haka dama aikinki kenan aikin gida da girki,nace rashin yanci dai ya Kara tabbata a kaina ka bari sai jibi to na Kara hutawa,yace Allah ya kaimu.


Washe gari a gidan ya kwana Sai ga su Sera su bakwai sunzo gidan da kyar Suka gane gidan sabo da na taba fadawa Sera address,da masifa Suka shigo suna kwala min Kira, miracle...Miracle.. na fito Suka hauni da masifa Zaki tafi baza ki dinga fada Mana ba sai mu dinga tunanin saceki akayi,Nawwar ne shima ya fito a tsaya a gefena tare da harde hannayensa a kirjinsa, ni Kuwa nace yarinya ce ni da zan bata kunzo Kuna min ihu a gida,Nawwar sanye cikin kayan baccinsa Yana jinsu suna cewa Kai karfa ka rabamu da yarinya abin ya isheka haka,da sauri nace Sera zanyi diban albarka a nan wlh ki tsaya haka, Kar wacce ta zagi saurayina yarinya ce ni da zaku zo Kuna min ihu,wannan ba Kalar Yan iskanku bane ku Shiga hankalinku,Au haka Kika ce? Nace ae kuje gida idan na gaji zanzo ai Kun ganni kalau nake,Sabo da haushi juyawa sukayi Suka tafi suna masifa, suna tafiya ni Kuma na juya Muna facing juna Ilu dai tana kallo,nace karka damu dasu kayi hakuri ko me kake so zanyi Kai mutumin kirki ne,Shuru ya min na shafa gemunsa nace inya.... inya... inya....dariya yayi ba shiri nace muje ciki na ja hannunsa muka shige ciki,Muna shiga na rungume shi nace kayi hakuri kaji,jikinsa ya janye da sauri yace naji na hakura ki daina tabani nace fa bakya ji, kasan me na furta Ina gabansa a tsaye muna facing juna nace kana da kyau,idanuwa ya lumshe tare da furta ba kya ji,dariya nayi Ina kida baki na shima dariya abin ya bashi yace kin haukace maybe.
Yau ma da dare cewa nayi sai mun fita haka na dau wanka Muka fita wajen Shan ice cream Muka je nan ma ya kashe kudi,daga nan muka wuce wani wajen na shakatawa.

Sabreen ce ta Kira Jamcy tace har yanzu fa bai dawo ba dan Allah ki Dan duba wuraren shakatawa ko Zaki ganshi da wata,Jamcy tana Dariya a ranta tace to,yau dai ta shirya a motar mamanta ta fito tana bi duk wajen joint tana zuwa Wanda Nawwar muke Kawai ta hango shi tare dani mun fito da ledoji ga wani ice cream din a hannuna Ina Sha Muka shiga mota,Jamcy ta saki ashar tace cab Sabreen Kinga ta kanki amma sai ta bugawa Sabreen waya,tana dagawa tace kin ganshi Jamcy? Jamcy tace ke dalla banza kin cika zargi to na ganshi yanzu ma Yana ma unguwar taku Yana masallaci makarantar da magidanta ke daukan darasi Yana ciki karatu yake a can makarantar Malam maikudi, Sabreen tace dama nayi tunanin haka ai shi akwai addini,Jamcy tace ke dai bari tsaurin addininsa da tsoron Allah dinsa har tsoro yake bani kin ganshi rike da Fiqhu, Sabreen hankalinta ya kwanta abinta mijinta karatu yake dauka a masallaci.

Washe gari Kuwa Maminsa ya fadawa ya samo sabuwar Yar aiki me hankali,yaje ya fadawa Maman Sabreen,Mama tace ai Sabreen ta huta dama aikin ya Mata yawa har tausayi take bani Kamar ba me kudi take aure ba,itama Sabreen din yace Mata Maminsa ta samo Masa Yar aiki sabo da Kar ta zargi komai ma,tace sai ta zo tunda ita bauta ta zaba tazo tayi,ya kalleta yace dan Allah karki wulakantata ki zauna da ita lafiya,bata ce komai ba,ni kuwa tunda yace a yar aiki zai kaini gidansa sai na zabi wata Atamfa wacce ya dinka min dinkin ba wani na kuzo ku gani bane,na dauki wata atamfar sai Rigar material kayana kala biyu na hada da komai na bukata na zuba a jaka,makwaftanmu na shiga na samu wata me aikinsu budurwa na roketa akan ta bani kayanta kala uku ga sababbi nawa masu kyau,da gudu ta bani ta karbi nawa masu kyau ta bani wata kodaddiyar Atamfa Riga da zani dinkin kauye,sai wani tsohon leshi doguwar Riga da dankwali Wanda ake cewa disco tsoho,sai wata Atamfa ta ji jiki sosai Riga da katon skert marar fasali,sake wanke su nayi na goge washe gari ranar da zan koma can na shirya cikin rigar da zanin na tsohuwar atamfata sauran kala biyun Kuma na zuba a Leda Viva da sauran tarkacen bukata,dankwalin Disco na daura a kaina nan take na dinga yiwa kaina dariya irin watsewar kayan danma ni Fara da bazan ganu ba,Yana shigowa ya kalleni dariya ta kamashi yace gaskiya kina da kwakwalwa muje,na dauki ledar kayana Muka fita na Shiga gaban mota sai gidansa

A hanya sai dariya yake min wai yayi winning bai taba zaton zan yarda naje gidansa a Yar Aiki ba,bai san duk abinda yace zanyi ba bai san yanda nake ganin girmansa ba,juyowa yayi kadan ya kalleni Yana Murmushi yace a Ina Kika samo kayan nan? baki na turo gaba tare da dora kaina a kafadarsa sannan na furta a wajen wata Yar aiki a makwaftanmu na bata masu kyau cikin nawa,Okay ya furta banda fitina da fada a gidana Kawai kiyi aikinki Zan biyaki ko nawa ne,yanzu nawa ma zan baki? kallonsa nayi lokacin ya juyo Muka hada Ido nace kana tunanin kudinka zasu sa na Zama yar aiki a gidanka? Karuwa ce ni fa kasan abinda muke siyarwa mu samu kudi wlh badan kudinka na yarda ba Kawai Ina ganin girmanka ne Ina Jin kunyarka Ina girmamaka shi yasa,Murmushi ya saki tare da furta a haka kina Jin kunyata Hannu na tafa Ina Dariya nace kasan Kuwa nifa ba karamar cikakkiyar Yar duniya bace,Yar duniya ce ni ta gaske ai nan daka ganni na Kama mutunci na ne ba karamin hakuri nake Yi ba,Allah? ya tambaya nace hmm yanda nake jina ko Namiji Zan iya Masa fyade,dariya yake sosai yace ya baki min ba ni? ai da kin sani kin min,karka cika baki Zan baka kunya a gaban matarka,karki Fara ya furta zamu bata bana so,daga min kafada,kafada ta na noke Wai naki,kyaleni yayi har Muka je katafaren gidansa na aure,sai Naga duk haduwar guess house dinsa da nake ciki ashe ba gida bane Yar Kauye na dawo sabo da tsabar tsaruwar gidan,Fitowa nayi da kayana a leda yace behave yourself,na nutsu tare da sadda kaina kasa Ina Wasa da yatsu na,dariya ce ta kule shi yau farin ciki ya isheshi yayi winning,Fuska na shagwabe,tun daga kofa Muka ji kida na tashi a hankali na furta zanyi loosing control rawa na kirana,yace dan Allah karki yi Yana rokata,nace wannan shine gidan Zama ai nan yafi mim dadi Matukar da wannan kida haka ai akwai nishadi,ciki Muka shiga Yana gaba Ina baya,Kannensa ne Ashe a gidan Suka kunna kida suna ta rawa gidan Suka zo Suka gyara ko Ina har dakinsa,Matar gidan Sabreen sanye take cikin kana nan Kaya tana zaune tana wani bata rai kannen Miji sun Zo Mata gida,suna ganinsa Suka kashe kidan tare da zuwa suka rungume shi dukansu suna Yaya Oyoyo tun dazu muke jiranka.

Yace sannunku Hamra ce idonta ya Kai kaina Dana shigo Ina tafiya salo salo ta furta wow kaga wata me kyau Suka juyo gaba daya yace me aikin da aka samo min ne sunanta Rabi,Suka ce Masha Allah suna cewa ai gwara daka samo Yar aikin, Sabreen sai lokacin ta juyo ta min wani kallon wulakanci da kaskanci tare da cewa baki iya gaisuwa bane ko ba a koya Miki ba a gidanku,nan take raina ya baci na harzuka Nawwar ya girgiza min kai,labbana na cije na daure nace Ina kwana tace yanzu ne kwanan Kuma haka ake gaida masu gida,Please karki fara bana so kina takurawa Yan aikina dukkansu Yan Adam ne kamarki,tashi Sabreen tayi ta wuce abinta,Raina a mugun bace Sultana tace kiyi hakuri Zama da ita sai hakuri muje na nuna Miki dakinki, yace bafa bangaren masu aiki Zaki kaita ba a nan zata zauna ga room a kasa wancan ki kaita can,Sultana ta kaini hadadden daki ne harda nuna min yanda ake amfani da toilet din ta fito dani ta nuna min komai na kitchen da store sannan ta zuba min abincin da Suka dafa nace Mata yanzu na koshi anjima na ci,tace okay,Ina jinsu Suka ce zasu tafi gida Suka Mana sallama ya basu kudi suka tafi,dakina na shiga Raina a bace da abinda matarsa ta min,shigowa yayi dakin Ina zaune a bakin bed yace kiyi hakuri kinji,nace ba komai amma kasan inda ka dakko ni ko wlh in bata Yi Wasa ba sai na canja Mata kamanni gwara ka tsawatar mata,yace naji to mene na fushin zamana kike fa ke Ina ruwanki da ita,Murmushi nayi nace Okay wooo.... karka damu ya furta good girl,bani kudi ni yau kifi zanci ko kaje ka siyo min,yace a siyo Miki dai ai baza ki Fara fita yanzu ba,Kinga dai nan yafi safe sabo da gudun shedan amma idan kina nan ba wata matsala ai bai dace mu dinga kebewa waje daya ba,naji Ustaz Kar dai ta shigo ta ganka,yace to mene ne nifa bana tsoron kowa da Kika ganni nasan Allah Yana tare da me gaskiya akan me Zan tsorata,karka cika min baki ai Ina gidan nan Zan gani watarana,fita yayi Kawai Yana Fitowa ya haura sama,Sabreen tana jinsa ta share ta fito Palo ta zauna tare da hakimcewa ta kwala min Kira Rabi kike ko wa zo fito dan burar...ta duro min ashar,na fito nace gani Hajiya,tace wacce tarkacece ke? Nace tarkace Kuma Kamar ya? Wacece ke to daga wanne kauyen aka fito? nace Kano kauyen Zaria,tace shi yasa na ganki wata shawaragi, na daure na danne tace Shiga kitchen ki min girki sauri,nace Allah sarki ai ba kawoni akayi nayiwa wata katuwa girki ba ko uwarki nafi karfin na Mata girki,a gigice ta juyo ta kalleni nace ba zamanki nake Yi ba ke baki Isa kisani aiki ba sai abinda Naga dama sai Kuma abinda Ogana me gidan nan yace shegiya me kafar agwagwa,zata bude baki nace Kinga baki San wace ni ba Zan iya sassaba Miki kamanni ba abinda ya dameni bane sai na nada miki mugun duka wlh Zan iya canja ki yanzu,ke kin San wace ni kuwa na nuna kaina nace kin ganni kina tabani bala'i sai ya sauka a gidan nan yau,dariya tayi tace Allah Sannu waliyya,nace yawwa ki kiyayeni ba baiwarki bace ni baki Sanni ba tantiriyar takadariyar yar iska ce ni bani da mutunci Sanda aka Yi rabon mutunci Ina bacci digo ban samu ba Ina bala'i harda zufa Ina nunata da yatsa Tsaki na ja na juya dakina,Wata ashar ta dura tace tab ai Kuwa sai Yarinyar nan tabar gidan nan Kamar yanda na kori wancan, Yar aiki a gidana idan ta sa min Ido ta gano Ina shaye shaye ta fadawa Nawwar fa shi yasa fa nake korar duk wasu Yan aiki a gidan nan.

Nawwar Yana Jin hayaniyar mu bai leko ba yace Sabreen ta samu dai dai ita ke baza ki gyara gida ba Kuma kin Hana masu aikin ma da ake kawowa suyi...kafin ya rufe baki Sabreen ta banko Masa cikin daki tace wannan Yar aikin ta bar gidan nan bana sonta Ni a canja min wata idan ba jaka ba kuwa za ayi yaki,ransa a bace yace ba inda zata je aiki Kuma sai abinda na sata ba Yar aikinki bace tawa ce ta gyara min gida ta min girki na ci ke kiyi naki yawwa,daga nan ka aurota Mana ai Kuwa da balbalin bala'i a gidan nan Kai da zaman lafiya ya Kare,ya Kare Miki dai ni kullum lafiya Zan zauna,Haka kace to wallahi na baka sati ta bar gidan nan idan ba Haka ba Baffanka da Iyamami sai sunji yace kije ki fada musu ki gani,Fitowa tayi fuuuu ta koma dakinta ta kwanta tana cewa wlh baza ta yuwu ba Ina sam Yan aiki munafukai Ina siyen kwayoyina a sirri Insha a sirri yanzu a kawo wata ta sa min Ido dole ta bar gidan nan.
Sabreen ko ta samu ciki ba Zama zaiyi ba sabo da shaye shaye ita Kuma baza ta iya hakuri ba Dole sai ta Sha yabi jininta,kusan ko yaushe Yana biya Mata bukatarta ta aure yanzu baya danne Mata hakki itace ma Watarana duk Sanda take son shaye shaye to baza ayi ba ko Yana so baza ma ta kwana a dakinsa ba,yayi bincike ya kasa gane dalilin baccin nan nata na masifa.

Yau banyi aikin komai ba sai washe gari na tashi da wuri na gyara ko Ina a gidan banda dakinta da nasa,breakfast na shirya na ebi nawa na ja gefe na karya sai gashi ya fito da Shirin Office,nace Ina kwana ya amsa ya zauna nayi serving nasa asararriya tana can tana bacci, sai da ya gama karyawa zai fita nace Banda pad Kuma maybe anjima zan Fara period ba kunya na fada,sannan yace kije ki siyo Mana ya zaro dubu biyu ya bani na karba nace na gode ya fice abinsa na kwashe kwanikan ragowar abincin ma na tattara na bawa masu aiki maza na wanke komai na gyara kitchen na koma dakina nayi karatun Qur'ani sannan na saka katon hijab har kasa na fita na siyo pad dita na dawo gida Shuru Shuru bata tashi ba tana bacci har na dawo palo Ina kallo 11:30 am ta fito sanye da rigar baccinta ko wanka bata Yi ba,Ina kallonta na Gane tana shaye shaye Indai kasan me Shan kayan maye to zaka iya ganewa, ke me Kika dafa ta furta nayi shuru,tace dan ubanki ba dake nake ba shegiya mayya,waka ma na Fara na bawa banza ajiyarta,kwafa ta ja ta Shige kitchen ta dafa indomie ta fito ta wuce dakinta Ina kallonta.

Tunda ya kawoni gidan bana ganinsa baya dawowa da wuri sannan kafin na tashi ma ya fita da sassafe aikine ya Sha Kansa har wurin sati guda itama Sabreen ta gaji bata kulani bana kulata ganin mijinta baya ko saurarena sai hankalinta ya kwanta,ni kuwa na shiga tsananin takura da damuwar rashin ganinsa sabo dan shi nake zaune ban San me yasa ba idan na ganshi sai naji sanyi a Raina naji nishadi marar misaltuwa,idan Ina ganinsa duniyar tana min dadi,gaba daya kewarsa nake yi so nake na ganshi Sam gidan bai min dadi,har Fitowa nakeyi da wuri ko zamu hadu amma bana ganinsa ganin haka Raina ya baci Banga amfanin zamana ba Kawai na saci jiki cikin dare da ledar kayana na fece sai unguwar mu ta Yan bariki, Ina komawa Allah yasa duk sun tafi ashawo nayi sauri na canja kayana masu kyau na kwanta a saman gadonmu sai bacci dake dama tana da key din dakin Nima Ina da key a hannuna duk wacce tazo zata bude Kawai.
Kwanciya nayi da Niyyar bacci amma na kasa sai tunanin Nawwar nakeyi a haka har bacci ya kwashe ni.

Washe gari Sabreen Bata ji kamshin girkina ba Kuma ko motsina bata ji ba,gidan ta hau dubawa ko Ina bani babu kayana,Sunday yau Nawwar bazai fita ba hutawa zaiyi,Sabreen ta Shiga dakinsa Yana bacci tana ta kwasar dariya,dariyarta ce ta tashe shi ya bude kyawawan idanunsa a hankali ya kalleta yace kina lafiya Kuwa? tace ahayee dama an fada maka Yan aiki ba Yan goyo bane Yar aikin taka ta gudu tuni bata gidan nan tun jiya banji motsinta ba babu ita ba kayant...wata uwar zabura da yayi sai da Sabreen ta firgita Kamar ance uwarsa ta bace,ya dirgo daga saman bed dinsa,Jallabiya ya zura ko wanka ya figi key din mota ya fito,sai da ya duba ko Ina bana nan sannan ya shiga mota ya nufi unguwar mu,wayata ma bata shiga, yana zuwa ya hadu da star Suka gaisa yace Miracle fa? tace dazu na ganta ta fito tayi wanka ma maybe tana dakinsu,Dan Allah Kira min ita,star ta juya ta tafi dakinmu,tana zuwa ta samu bacci na koma duk da nayi wanka na sanye nake da vest peach sai dan wando gajere fari, Saratu ce ta fito daga dakin Wise ta hango Nawwar a tsaye,wajensa ta karasa Suka gaisa yace Rabiah fa?bacci ta koma ka shigo Mana dakin,Star ce ta dawo tace Masa tace baza ta zo ba,okay ya furta yabi bayan Saratu ta nuna Masa dakin ya shiga ita Sera tayi wani wajen ta tafi gantalinta

Baccina nakeyi ba bata lokaci ya Shiga tashina ke ke....ko jinsa nayi,jikina yabi da kallo ya Dan ja tsaki tare da aza hannunsa Kan kafata ya rike tare da girgiza kafar na farka a hankali na Shiga bude idona Ina kallon mutum sama sama yana tsaye yayi folding hannayensa a kirjinsa mukullin mota na hannunsa tar na saka idona cikin nasa,idanuwansa masu Matukar tasiri ya lumshe tare da danne lip dinsa na kasa da hakoransa kadan,Naga fa lallai shine a zabure na mike zaune nace yaushe kazo? bai kulani ba yace tashi mu tafi,nace nidai na shiga Uku ka takura min ka damu rayuwa ka kyaleni nayi rayuwata kayi taka,me kake nufi Dani wai kayi rayuwarka na by force,ke bari kiji dole ki daina bariki ya Zama Dole ki daina ko kina so ko ba kya so sai kin bar gidan

5 Comments On YAR AIKIN KARUWAI
avatar
asmau-7

1 year ago

Reply

T

avatar
sadiya-9

1 year ago

Reply

Wonderful and nice novel

avatar
diaabdourahamane

1 year ago

Reply

Nice novel

avatar
bashar

1 year ago

Reply

Don Allah ina cikon labarin nan?

avatar
taskar

1 year ago

Reply

Replying to bashar

Dole fa sai dai ku siya a cigaban labarin a wurin marubuciyar, ga nambarta 08061929616

Please Login or Register in order to submit comment