Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yaji tunda ba Wanda ya sani to muyi shuru, yace to nayi shuru,Sabreen masifar papa yasa ba shiri ta tattara ta dawo,Papa da Kansa ya dakkota a airport,tana shigowa part din Mami a Palo ta iske Nawwar Yana dining Yana cin abinci
Mami tana ta zuba Masa surutu,dake Allah yayi ba me son magana bane Kuma shi bai fiye fara'a ba ga kafirin Isa da mallaka da son girma sai ya Mata shuru sai jefi jefi yake furta uhm hakane, har Sabreen ta kwala sallama ta shigo ta Sha tsadaddijar gown golden ga takalmi da Haka tayi kyau matuka,Mami ko murna bata yi da dawowarta ba ,Nawwar ko kallonta baiyi ba yaci gaba da uzurinsa itama bata kulashi ba sai da Mami tace ga yayanki Nawwar ku gaisa,sai lokacin tace Ina yini ta Kara gaba bai ko amsawa.

Itama sai bayan ta cika sati biyu da dawowa sannan Papa ya kirata ya sanar Mata cewar ya hadata aure da Nawwar ita Kuma Saurayinta Dan Italy take so Lorenzo,Zata Yi Musu papa ya dakatar da ita yace wlh idan baki yarda da auren nan ba sai na tsine Miki muna so muci arziki kina hauka kudi ne fa da shi kina gani arzikina ya Kare shi yake mana komai yanzu ci Sha sutura idan Kika aure shi ai dukiyar ma zai mallaka Mana wata Kuma mun samu damar Shiga jikinsa tunda shi Sulaiman busy ya Masa yawa, Mama tace ana Neman arziki kina hauka idan kika aure shi ai kinyi dace, Sabreen ba yanda ta iya haka ta amince Kawai,sannan Baffa ya samu Nawwar har dakinsa ya zauna yace Nawwar magana nake so muyi Jin haka Nawwar ya gyara zama sabo da shi mutum ne me biyayya, sune Suka kula da shi Suka dauki nauyinsa har ya zama abinda ya zama yanzu,Baffa yace dan Allah na rokeka Nawwar ka auri 'yata Sabreen sabo da Kaine kadai na yarda zaka riketa da Amana ko bayan ba raina dan Allah karka ce a'a ka amsa min,Murmushi Nawwar yayi yace ni ai bance bana son Sabreen ba na amince Baffa bani da abinda zan biya ku iyayena,sannan na gama gina gidana na gama komai sanda kuka shirya ayi bikin,Yusuf Papa yana gefe a zaune shima ya dinga murna yace an gama dan albarka Allah ya baku zaman lafiya Kamar gaske bayan a ransa yana ta saka tsiyar da zai hadawa Nawwar ya gaje wannan kudin nasa da ya tara.

Baffa tunda ya auri Amaryarsa Ummin Haidar gaba daya ya tsani uwar gidansa Mami haka su Iyamami ma Suka tsani Mami basa sonta kullum sai zagi da cin mutunci,duk abinda danta yayi to ita zasu Zo su zage tasss bata da iko tayi magana Baffa sai ya sake ta gaba daya igiyar auren Saura daya jal,bai bata kwananta sai dai ranar girkinta tayi girki ta Kai Masa part dinsa amma Kuma Ummin Haidar ce zata kwana da miji,tun Mami na zuwa Yana wulakantata ya koreta har yace ta daina zuwa Masa da dare,a gidan daga ita sai yaranta su Nawwar da su take rayuwa,Abu na gaba gaba ma abinci ya daina zuba Mata a part dinta ganin haka Nawwar ya koma siyen komai a gidan na abinci Watarana ma har bangaren Iyamami da Papa, basa kaunar Mami ko kadan a gidan,Ko bata je wajen Baffa ba idan yaga dama har bangarenta zai Zo ya zazzageta ya fita,tayi kuka har ta Saba ma da rayuwar.

Bikin su Nawwar wata daya kacal aka saka sabo da gaggawa nan da nan biki yazo ba wani shagali Kawai aure za a daura a Kai Amarya cewar Sabreen tunda ba auren soyayya bane ana gobe daurin aure Yan Uwa da abokan arzuka sun ciga gida, ga kawayen Amarya sai Nawwar Wanda bai kaunar auren Sabreen baya sonta Sam haka suka raba Iv,Hajiya Binta da Rukayya kannen su Papa sun iso da yaransu samari wasu Kamar Nawwar wasu Kuma kasa da haka,akwai ma Mus'ab babban dan Binta ya girmi Nawwar,Washe gari aka daura auren Sabreen Yusuf Raj da Nawwar Sulaiman Raj Kan sadaki dubu dari, kudi dama ya basu da kansu Suka je kazar waje suka hada lefe, bayan Sallar Isha Papa da Mama suka Kira Ango da Amarya,Baffa,Mami,Ummin Haidar suna gefe Papa ya fara Nasiha me shiga jiki kamar gaske har zuciya sannan Suka ce su tashi su tafi shine Suka tafi gidan aurensu yayin da Ango ya dandana Amarya yaji ba kanta.

Ci Gaban Labari

Karasawa nayi a nutse Ina zuwa nayi sallama ya amsa,nace Ina yini ya amsa min Yana kallona yana zuba Murmushi ni dai daga haka bance komai ba,da Kansa naji ya fara magana yace Rabi na dago da kaina a hankali na maida kaina kasa Ina Wasa da yatsuna yace ba Wasa ne ya kawo Ni ba,kamar yanda na fada Miki sunana a farko to hakane Ina da mace guda Daya da yarana uku ,da gaske nakeyi wallahi harga Allah sonki nakeyi da aure bada Wasa ba,Amma bance sai kin Soni yanzu ba Sanda Kika ji kina so na sai ayi komai,nace to kawai,yace Ina Harkar shigo da Kaya da zannuwan gado daga kasashen waje Zan dinka baki bedsheet kamar guda ashirin zuwa sama ki dinga Kara ribarki kina siyarwa Kinga kin samu Sana'a ko tunda naga da shekarunki,Mamakinsa ya kamani na zaci karya ne ashe da gaske yake haka Muka rabu,sati Daya ya sake dawowa Allah bai sa Yan gidanmu sun San me kudine ke zuwa wajena ba har sai da Muka shaku sosai na fada son Alhaji Kutama,muka tsunduma a soyayya daga nan ya Fara min Wasa da kudi a haka ma Ina kin karba,har dai yace zaizo ya gaisa da iyayena,wani zuwa na fadawa Gwaggo Saurayina zaizo ya gaishe su sai dariya suke min tunannsu talaka ne Yana zuwa Gaji ta leka taga irin motarsa ta koma gida tace jama'a kuzo kusha kallon Saurayin Rabi,dukkan matan gidan Suka leka waje abin ya tsorata su Mairo tace tab ko mu da mukayi ilimi bamu samu irin wannan Saurayin ba ko me lifan bamu da shi sai Rabi wlh da sake,Dagaci ya gigice yace Kar Wanda ya damu Kansa Rabi baza ta aure shi ba Amma a kyale shi muyi amfani da damar mu sai mu samu kudi,Haka ya lallaba su Basu nuna min komai ba na Masa iso har ciki Suka gaisa sun Sha Alheri na kudi Dagaci ma dubu dari biyu ya bashi ya bawa su Gwaggo dubu ashirin ashirin,Gaji da Mairo dubu goma goma sannan yace za a kawo kayan abinci, a ranar ya siya min waya me tsada Ranar murna ta cika gida sai basu kulani ba Muka ci gaba da soyayya da Alhj Kutama ya dinga kashe min kudi kamar hauka kayan sawa masu tsada iri iri takalma jakankuna,mayafai etc,Dagaci ne ya kwace iPhone Dina ya siyar ya siya min Tekno keypad Yar dubu bakwai yace baza ki rike babbar waya ba, Haka kayan kwalliya duk su Mairo da Nawa suke amfani da turaruka,gashi ya Fara kawo min yadin gado Ina siyarwa iri iri a garin,Dan ma a Kauye muke ban waye ba tunda ni ba ilimi nayi ba iyakata primary a Jss1 Dagaci ya hanani zuwa,Dagaci ya fada Masa gaskiya cewar Ni Yar tsintuwa ce duk da haka Alhj Kutama yace yaji ya gani yana so, Haka Dagaci yace ya kamata Kutama ya turo da manya,ba Wasa ya turo manya Suka kawo kudin aure aka tsaida aure wata hudu.

Abu Yana ta karasowa Ni Ina ta Shirin biki Kutama Kuma ya tafi Dubai business dinsa yace bazai dawo da wuri ba sai dai a daura aure baya nan idan an daura zai min visa na bishi kasar waje can Dubai Haka akayi magana da Dagaci.
Haka biki yazo komai ya turo danginsa tunda baida iyaye kanin babansa da sauran Suka Zo da yawa aka taru aka daura Aurena da Kutama akan sadaki dubu dari biyu,ga lefe an hada na gani na fada,to bayan an gama ba wani shagali akayi ba tunda bani da gata ba Wanda ke shiga lamarin auren nawa idan ba Dagaci ba,Ina jira muji me Ango zaice Muna waya kullum har sati daya da biki, Gwaggo tana zaune tare da Dagaci Ina dakina Basu San Ina Jin hirar tasu ba sun manta Ina dakina Kuma a jikin dakin Nawa suke,yace karku damu kanku Gwaggo na Gama daukan mataki malamin yace bazai taba Zama tare da ita ba kwana nan zamu ji labari me Dadi,Gwaggo ta rangada shewa tace Alhmdllh ai nafi so Gaji da Mairo ta suyi auren su Allah dai ya kawo musu Miji me kudi Wanda zamu huta cewar Dagaci, Ni dai bance komai ba Ina zaune a gida Ango Shuru Shuru tun Yana kirana har ya daina kirana idan na kirashi ma bazai daga ba,gashi a gari sai gulmata akeyi Ango yaki zuwa an daura aure har wata guda Shuru,kayan lefen Nawa ma duk su Mairo sun kwashe sai kadan Suka barmin,kullum nayi kuka har na gaji Addua nake Yi ba dare ba rana.

Ango Nawwar da Amarya gaba suke da juna baya kulata bata kulashi komai na gyaran gidan masu aiki keyi da girki ma tunda ya hanata yi,kullum sai dai taci ta Sha taci uwar gayu tayi shaye shayenta ta kwanta bacci bata free kullum a make take cikin maye,tsabar shaye shaye muryarta har ta koma ta Yan maye a slow take magana tana lumshe idanu tana wani babbasarwa Watarana Kuma ita kadai zaka ga tana ciccijewa shi dai Ango aikinsa yake fita yana uzurinsa ko kararsa bata kaiwa harkarta take yi dama ita bata da kawaye a nan kasar rayuwarta takeyi kawarta guda daya ce Yar gidan wani Minister Jamila suna ce Mata Jamcy tare Suka lalace a Italy tare suka dawo kasar tare suke shaye shayensu asalima Jamcy ita dake bata Yi aure ba ita ke kawowa Sabreen kayan mayen a boye su zauna su Sha hira duk sirrin Sabreen Jamcy ta San komai,har kwanciyar aurensu first night ta bata labari yanda abin ya wakwana,Jamcy tace ashe duk kyan nan nasa da Izzarsa na banza ne ba lafiyayye bane,Sabreen tace dan wofi ma sai iya sarrafa mace da romance baya aiki,ga Banana katuwa tsayi da kauri kin ganta Kuwa Jamcy tab

Nawwar yau sai bayan yayi Sallar Isha ya shugo gidansa,Sabreen tana zaune a Palo tana kora lemo ta zubawa lemon kwayoyin maye,harda mikewa ta dakko glass cup ta zubawa Nawwar ganin shi take tsiyaya tana Sha bai zaci da kwayoyin maye ba a ciki bai disga ta ba ya karba ya shanye sannan ya haura sama,abinka da ba a saba ba sai yaga dakin ya fara juyawa yana hajijiya da shi,kafin kace me ya fadi tim a kasa ya mike ya sake tangal tangal ya fada saman bed Idonsa ya rufe Kuma shi ba bacci yake ba Kuma ba Idonsa biyu ba bai san a Ina yake ba, a haka ya kwana ya yini idonsa a bude yana magana a hankali yana furta Mami Mamina na mutu ne ko a raye nake? a lahira nake ko a duniya nake ne.

Sabreen bata ko kalli dakinsa ba kuma tasan bai taba shan komai ba,sai yamma likis taci wanka tare da haurawa sama ta ganshi a kwance shanana kamar gawa kuma idonsa a bude yana magana da kyar yana Kiran Mami,Sabreen ta sheke da dariya tana tafa hannaye,saman gadon ta haura ta samu kumatun Nawwar yana ji Yana gani ta kwada Masa Mari tasan baya hayyacinsa idan ya dawo dai dai bazai San ta mare shi ba,ai duka ta rufe shi da shi sannan ta sake kwada Masa mari,baya ko motsi ko mintsininsa akayi bazai ji ba,kayan jikinsa ta cire masa ta masa zigidir sai da ta gaji sannan tayi ficewarta ta barshi timbur a saman bed Yana sambatu,wayarsa ana ta Kira ba a daga ba

Mami tana cikin masu kiransa taga danta ta kira kwana daya Shuru ba a daga ba Kuma bai biyota ba Kawai kasa daurewa tayi a daren ta shiga lafiyayyar motarta da kanta tayi driving zuwa gidan Nawwar, Sabreen tana dakinta a kwance tana latsa waya sallamar duniya tana Jin muryar Mami taki amsawa har sai da Mami ta gaji ta bude kofarta ta ganta tana danna waya,Mami ranta a bace tace amma Sabreen kina jina Ina sallama sai kace ba musulma ba,sai lokacin Sabreen tace banji ba Ina yini,sabo da bacin rai Mami bata ma amsa ba tayi gaba zuwa dakin Nawwar, ta kwankwansa Shuru haka ta kutsa ciki sai da ta tsorata ganin danta tsirara a kwance shanana yana surutai da gani kasan ba lafiya,da gudu ta karasa tana Nawwar tana girgiza shi,cikin maye ya furta waye...dan Allah a duniya nake ko na mutu? Mami kuka ta saki ta furta Maminka ce Nawwar me ya sameka? Ita Sabreen din bata da hankali ne? Nawwar dai ba ganewa yake ba tambaya Kawai yake na mutu ne ko Ina Ina duniya,da sauri ta nemo sutura ta saka Masa ta fita ta Kira masu gadi Suka taimaka aka sashi a mota sai asibiti,Sabreen tana ta dariya tana kallo ya window Samanta, ana zuwa asibiti likita yace ai kayan maye ne ko aka bashi ya Sha ko ya Sha bai taba sha ba, Nan take Mami tace Sabreen ce itace take shaye shaye naji labarin,wata Allura likita yayi Masa 15mnt sai ga Nawwar ya dawo hayyacinsa babu abinda ya tuna sai Sanda ya sha lemon da Sabreen ta bashi,sunan Mami ya kira, ta dinga murna tace Sannu Nawwar kalli kumatunka yayi ja Kamar an mareka dama gashi fari,yace ni ban sani ba muje gida salloli zanyi Naga kamar tunda na Sha lemon Sabreen banyi Sallah ba,Mami tace Allah ya saka maka ranar aka basu sallama.

Yau Kuwa ya Sha bacci harda makara sai washe gari 12pm sannan ya iya bude Idonsa a hakan ma ya dade kafin ya fara ganin daidai ya mike yaje yayi wanka da Alwala ya fito Sallar asuba yayi da tsakar rana ya hada da azahar sannan ya fito Neman abinci,Sabreen tana kallonsa dariya ta kwace Mata, bai ko kulata ba yasan tabbas a lemo ta saka Masa wani abu abincinsa yaci ya koshi Ladidi me aiki tace ranka ya dade Ina yini yace yawwa barka da asuba an tashi lafiya,Ladidi tace ai Yamma tayi karfe daya na rana ma ta wuce,sai lokacin ya tuna.

Sabo da baya shiga harkarta komai ma ta daina Yi a gidan in Banda bacci ba abinda tasa gaba, shima harkarsa yake Yi da Kansa yake gyara dakinsa, ganin shi yaki kulata har tsawon wata guda ta gaji ta Kira Mama,Mama daga Wayar tayi tana dagawa ta fashe da kuka,Mama gigicewa tayi ta saki Salati tare da furta na Shiga Uku Ni Zuwaira Sabreen lafiya dukanki yake? Sabreen cikin kuka tace Mama wlh bashi da lafiya baya iya saduwar aure sai ta Kara da sharri tace ai kullum Mama sai dai yayi min da yatsansa yanzu gashi dalilin haka na hadu da ciwon Mara kullum sai ciwon Mara,Mama ta dafe kirji tace kardai bata tashi? Sabreen tace inda kisan an jika Tsumma a ruwa Mama,firgita Mama tayi tace da sake,katon saurayi Kamar Nawwar ko ta babanki da yake dattijo ai tana aiki, to ya batun kudi baiyi yunkurin baki ajiyar takardun gidajensa da filaye ba ko wasu kadaran? Sabreen tace tab ai komi nasa na takardu babu a gidan nan mutumin nan a shirye yake,kin San Papa yace nayi kokari na binciko Masa takardun filaye da gidaje amma wallahi dakinsa ba komai sai takardun Office dinsa sabo da Haka tunda aka kawoni nake gyara Masa dakin sabo da na samo takardun Amma ko Daya,Mama tace bar shege dan iska idan nan gaba ba a samu komai ba sai kiyi Masa abinda zai sakeki mu huta,Sabreen tace an Gama Mama amma kuyi Maganar da Papa aji me zai ce a haka suka rabu.
Mama Kuwa Papa yana dawowa ko hutawa baiyi ba ta same shi da labarin yace tayi hakuri taci gaba da Zama haka Muga abinda Allah zaiyi ko za a samu takardun domin yanzu bani da komai a kasa kudadena babu kadarata Saura kadan.

Mama yarta ta sake Kira a Karo na biyu,Sabreen tana dagawa tace yawwa munyi Maganar yace ki Kara hakuri dai a gani, sannan ni Wai baya ajiye makudan kudade ne a gidan? Sabreen tace Yana ajiyewa har da daloli ma kuwa,Amma Sabreen anyi sakarai Baki Fara dan ebowa a ciki ba ai bazai gane ba,mutumin nan Mama bashi da mutunci kullum Fuska a murtuke Kar nazo ya kamani Ni kaina Ina son daukan kudin amma Ina tsoro wlh,ke dalla shashasha sakarai in Zaki bude idonki ki bude idan kin ebo ai ko fili ma mallaka ni da ke karki fadawa Papa wannan daga Ni sai ke, Papa shi ta takardu yake yi muma muyi kokari mu samu rabon mu,Sabreen tace to dama kadan take jira tana so ta dinga kashe kudi tana siyen kayan mayenta masu tsada kudinta sun Kare kaf ga Papa complain yake Mata baida kudi,fada da cikawa suna gama Wayar ta mike tare da lallabawa sadaf sadaf har bedroom dinsa dama baya gida tana zuwa ta bude inda kayan sawarsa suke tasan a gefe guda akwai inda yake zube kudi,tana budewa ta gansu wannan karon da yawa bai Kai bank ba, rapa daya ta dauka na dollars ta duba a kudin Naira na Nigeria ta kwashe dubu dari uku lokaci guda ta fice da abinta tana Fitowa Mayafi ta yafa ta dauki key din motarta ta fice daga gidan ba tare da ya sani ba,banki ta wuce a direct ta Kai kudin nan harda zuba dalolin a dollar account dinta ta fito da dubu dari data rage,waya ta sake yi da kawarta cikin kankanin lokaci ta kawo Mata yar mitsilar cocaine da kayan mayensu masu karfi ta biya kudin Suka shiga shopping mall ta siyo giyarta ta fito.

Jamila tace ya kamata kawata ki nemi Sana'a ki fara Kinga Zama haka bazai kaiki ba karki dogara da miji ki nemi aikin gomnati ko company,Kallonta Sabreen tayi tare da furta Jamcy kenan ni business nake so na Fara nasan zanyi ciniki idan na Fara siyar da su Coccaine,wiwi,kwayoyi,su codeine da sauransu,Jamcy tace wlh da Kuwa kin samu kudi kinga Yan wannan da nake siyarwa kalli katon mansion dina Dana kera,ki Fara wlh zaki samu kudi idan Kika Yi karfi sai mu Fara shigo da dawar nan Yar Cameroon wacce ake yin giya da ita kamfanin giya da tsada suke siyarwa Zaki hadu da manyan masu kudi,yanzu fa wannan shigo da dawar giyar ita masu kudinmu suke shiga Dan danan zaki ga mutum da tarin milliyoyin kudi to ya Fara mu'amula da kamfanin giya dare Daya ake kudi Kamar na yankan Kai,tafawa sukayi Sabreen tace Haka za ayi Zan sa mijina ya bani jari,Ae ko million Daya ya Baki ya Isa ki Fara da kadan Sabreen motarta tayiwa key tace bari na wuce gida Kar ya dawo bana gida,kowacce motarta ta ja ta Kama gabanta,ko da ta koma gida Ogan bai dawo ba.

Bayan watanni ni Rabi Ina gida Alhj Kutama ya Aiko Yaronsa ya kawo min takarda, gabana ya fadi Ina shigowa gida na bude na karanta Kawai naga ya rubuta min Saki har uku lokaci guda,hawaye Suka zubo min na fashe da kuka na mike Ina Jan kafa da kyar na kaiwa Dagaci,yana karba ya duba sai naga Murmushi ya subuce masa sai Kuma ya hade rai yace haka Allah ya tsara sai ayi hakuri Allah ya kawo wani ko me yasar masai ne,kallon Dagaci nayi Kawai wasu hawayen masu dumi suka gangaro min na fita na koma dakina naci kuka na koshi,tun Ina damuwa har na hakura ba'a dade ba na hadu da wani manager na gidan Mai me kudi Yana mugun sona Amma ni Sam ba shi nake so ba nafi son Kutama,su Gwaggo bakin ciki Kamar su mutu sai masu kudine suke zuwa wajena su Kuwa yaransu talakawan ma basu zuwa..

Yau Juma'a Ina gida sanye cikin vest da skert dina dan kanti brown me digon fari nayi kyau sai ga babbar Aminiyata Saratu taci wanka na gaske ta Zama gogaggiyar Yar gayu Yar birni sanye cikin rantsatsiyar Shadda Maroon jaka da takalmi komai me tsadar gaske,da murna na tashi na tareta nace Saratu kece Wai dan Allah? Gwaggo da sauran yan gida suka saki baki galala suna kallon Saratu ta cakare,Gaji ce ta dawo daga kasuwa tace Wai Saratu ba dai kece da mota ba haka? Saratu tace wlh Allah ya nufa na siyi kwano,ke Kuwa wanne aiki Kika samu a kudu? tace ai kin San Onitcha bakin ruwa ne akwai business ba karya da naje can na Fara dan zamarwa wata Nkeci a restaurant Ina Mata wanke wanke da idona ya bude na gane yanda ake kasuwanci sai na Fara sana'a inje a bani takalma da jakankuna masu araha akan sari sai na dora ribata idan na siyar na Kai kudi na karbi wasu ana haka na Fara samun jarin kaina Ina Sara da kudina Allah ya sa min Albarka nazo na bude katon restaurant na zuba yara...Gwaggo ce ta katseta tace ke ki bari Dan Allah kice kinyi kudi,Saratu taci gaba da cewa gefe daya Kuma Ina ta kasuwancina a Haka yanzu na siyi katon gida na gani na fada ga mota na siya,Mairo tace cab kekam kin tsallake,Ina murna nace sai naji kamar na biki ki bani aiki a restaurant dinki ko nima ki min hanya,Saratu tace tashi muje dakinki mu zanta,su Gwaggo suka tabe baki,muna Shiga dakina Saratu tace bari na baki Address dina idan Zaki kawo min ziyara Watarana idan Kika je tashar da ake hawa motar Anambra zaki samu masu zuwa Onitcha ma idan kinje ki hau Napep ko taxi kice Odimgbe Street kina zuwa wajen ko wa Kika gani kice gidan Seraline za'a nuna Miki nice Seraline a can a haka ake kirana,nace uhmmm to zanzo Watarana na shakata Kinga yanda Kika hadu Kuwa Masha Allah haka Muka Sha hira na fita tare Muka dinga yawo a Kauye Muna ta labari cike da nishadi,tunda kaf garin sai kallon Saratu akeyi ana sha'awarta,dama Bata da uba ya rasu tun tana karama daga ita sai babarta sai kanin Babanta Wanda ke daukan nauyinsu ita Kuma babarta bata da kowa sai sai wata Yar uwarta da suke zaune tare,Saratu tana zama budurwa Kanin mahaifinta Kawu ya Mata wayo idan ya kaita dakinsa sai bata kwayoyi a cikin lemo ya bata ta shanye hankalinta ya fita daga jikinta sai yayi amfani da ita,Kuma idan ta dawo hayyacinta sai yace Indai ta fadawa wani sai ya kashe ta,kullum Yana mata haka wata da watanni ba Wanda ya sani Sai Katsam ciki ya bayyana a jikin Saratu,da Innarta ta matsa Mata da duka ta fada Mata abinda Kawunta ke Mata,Kawu Yana Jin asirinsa ya tonu ya hada kayansa ya gudu ya bar garin har yau ba a San inda yake ba,matarsa tana gidansu da yaranta hudu,Inna ganin ana ta cakaki a kauyen sai ta tura Saratu Lagos wajen wata Yar uwarsu Hajiya Kattime,a can Kuma sai waya Saratu ta bugowa Inna Wai cikinta ya zube shine sanadin barin kauyen Saratu.

Yanzu Saratu itace take ci da mahaifiyarta tana turo musu da kudade,sanadin zuwan Saratu Onitcha daga tafiya Lagos wajen Yar uwarsu shikenan akaji ta koma Anambra ta samu aiki a can,Maman Saratu tana Jin dadi sosai komai tana turo da kudi ana bata shi yasa kullum cikin sawa Saratu Albarka take.
Washe gari cikin dare na sake fitowa wajen da muke Alwala jikin dakin Dagaci ne ina tsugune Ina Alwala naji Aunty Amarya tana sheka ihu kasancewar Dagaci yau a dakinta yake,tana furta....Zan mutu...kana haukatani....Ido na zaro na mike tsaye a fili na furta a'a wai me yake musu ne wannan wacce irin mugunta ce

5 Comments On YAR AIKIN KARUWAI
avatar
asmau-7

1 year ago

Reply

T

avatar
sadiya-9

1 year ago

Reply

Wonderful and nice novel

avatar
diaabdourahamane

1 year ago

Reply

Nice novel

avatar
bashar

1 year ago

Reply

Don Allah ina cikon labarin nan?

avatar
taskar

1 year ago

Reply

Replying to bashar

Dole fa sai dai ku siya a cigaban labarin a wurin marubuciyar, ga nambarta 08061929616

Please Login or Register in order to submit comment