Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kullum sai ya zalunci matansa,ihu naji Aunty Amarya ta saki ...Dagaci naji yace karki haihu kinfi min a haka...baki bude na harari dakin Dagaci nace sabo da Kai azzalumi ne akan bata haihuwa kake Mata mugunta gashi tana ta cewa zata mutu

Muryar Aunty Amarya tana tashi ta sake yin wani nishi tana zaka halakani....ka barni haka...na tuba....zan mutu....wani gurnani naji tayi Wanda na gaza hakuri nayi Sauri na hau dukan kofar Ina cewa kayi hakuri Baba dan Allah ka kyaleta karka kasheta duk da cewar naga Gwaggo ranar nan bata mutu ba Watarana tun kana dukansu suna tashi to wataran mutuwar zasuyi,kofar na shiga duka da karfi Ina cewa wayyo jama'a ku fito ku kawo agaji wayyo zai kashe Aunty....Gwaggo ce kawai ta fito sauran yaran bacci yayi nisa,Gwaggo tana Fitowa tace laaaaa yanzu yau ma laben kike yi musu wannan wacce jarabar 'ya ce ta dakko tabarya,butar dake hannuna na saki na gudu dakina na kulle sannan naji Dagaci da Aunty Amarya sun fito suna ta zage zage,Ni Kuwa tausayinsu nake ji a raina Dagaci zai kashe su kasancewar bani da kawaye a garin basa barina na shiga cikin jama'a bare nasan wani Abu na rayuwa.
Washe gari da safe Dagaci ya fito na dinga zuba Masa harara Ina Masa kallon azzalumi me dukan matansa Yana musu mugunta zai kashe su,ranar yini nayi Ina hararar Dagaci.

Satin Saratu daya a Kauye ta koma,Ni Kuwa Ina zaune sai samari nakeyi masu kudi ban taba saurayi talaka ba,Gwaggo hakan Yana bakanta Mata rai har daki ta samu Aunty Amarya tace Amarya ki bani shawara mu San yanda zamuyi da Yarinyar Nan Rabi Nifa har ga Allah na gaji kina ga ta Hana yarana samun samari masu kudi kowa yazo Rabi Matukar Yarinyar nan bata bar gidan nan ba mu da ganin ci gaba sai dai in Muna Saduwar aure da Dagaci,Rabi ta sheke da dariya tace ai da kin dauki shawarata da tuni shegiyar ta bar gidan nan tunda dagaci shima ba kaunarta yake ba,Gwaggo tace Wai shawarar da Kika bani kwanaki? Kwarai kuwa,shewa sukayi tare da tafawa Gwaggo tace an gama,Shuru Shuru ni dai Ina ta Shan wahala ta iri iri a gidan har aka kwashe wata biyu yau Gwaggo girki ta sani ban sani ba Gaji ta faki idona bana kusa ta watsa min gishiri me mugun yawa a Miya sai da na gama an zubawa dagaci nasa ya baje ya balla ya Kai loma Daya bakinsa ai a gigice ya tofo tuwon waje yace wacece take so ta halaka ni a gidan nan? jikina ya hau rawa nan take na fara karkarwa Ina rabewa a bango,Gwaggo ta dandana miyar ihu ta saki da karfi,Aunty Amarya ta lasa itama tace Ashe da babbar makiyar mu muke zaune Zaki kashe mu

Tuni na Fara kuka nace wallahi Allah gishirina dai dai na zub...saukar mari naji Dagaci ya hau jibgata Aunty Amarya ta Miko Masa wata Sanda ya dinga makamin tun Ina tsaye har na zube a kasa,Ina kuka har na daina motsi ma na kasa sai da ya gaji Dan Kansa sannan ya rabu dani,azaba tasa na kasa tashi a nan yashe tsakar gida har Suka Dora wani girkin ban tashi ba babu Kuma Wanda ya kulani sai da na samu sauki sannan na iya yunkurawa na tashi da kyar Ina daura zanina Daya kwance Ina sheshekar kuka na fada dakina zazzabi da ciwon Kai Suka lullubeni haka na kwana ko lekowa ban iya ba sabo da azabar zazzabi da ciwon kai, Sallah ma Sai da Isha tayi na lallaba na fito da rarrafe na dafa jikin banko naje nayi wanka da sabulun wanki dama Ni a gidan ba'a barina nayi wanka da sabulun me kamshi sai dai sabulun wanki ko omo ake bani a wulakance tunda na taso a haka na taso a hakan ma idan na tambaya sai an zageni anyi min gori sannan Dagaci ya bani da kyar.

Bayan na fito nayi brush da Alwala duk da zazzabin Yana jikina haka na canja Kaya wankanku sabo da Ina da tsafta ni,Sallolina na rama a zaune sannan na fita wajen Gwaggo dake zaune a dakinta sallama nayi tasa yaranta gaba suna ta hira sun baje tsire suna ta ci itama Aunty Amarya ita da Dagaci suna cin nasu a dakinsa yau ita ke da girki,Gaji tace to mayya anji kamshi anzo dan a sammiki,Ko ma mene wannan tsiren haramiyarta ko barbade shegiya mayya haihuwar kwararo Yar shege cewar Gwaggo,Mairo tace dan Allah ku kyaleta haka ke dalla marar zuciya me za a baki? Na kalli Mairo a haka itace me sauki,nace abinci za a bani yunwa nake ji,Audu da Imrana Suka ce anzo gidan ubanmu sai cinye Mana abinci akeyi ki tafi gidan ubanki Mana ko uwarki data haifeki ta jefar ta baki,Ido na runtse sabo da bacin rai ga zazzabi na cina,Tsaki gaji ta ja tace muje ni na zuba Miki,Gwaggo tace ki kula a cikin miyar akwai nama karki manta ki sa Mata nama ko yanka daya,mikewa nayi bayan Gaji ta zuba min tuwon Dan kadan da Miya ta bani a wulakance ko almajiri baza ayi Masa haka ba,na saba da haka shi yasa na karba Kawai na koma dakina na cinye na Sha ruwa sannan na koma na kwanta bani da kudin siyen magani ko kwandala babu inda zanje Kuma a bani,haka Wasa Wasa na kwashe kwana hudu Ina zazzabi kullum a kwance nake yini,Ina wannan hali naji Gwaggo da Amarya sun leko dakin Gwaggo ta fasa ihu da kururuwa ta Fara wayyo jama'a ku kawo Mana a gaji,jama'a kuzo bala'i ya same mu mun shiga Uku yau ya zamuyi,mamaki ya kamani na bude idona da kyar kafin kace me Dagaci ya fado dakin mutane makwafta sun cika damkan a gidan ana tambaya lafiya,Aunty Amarya ma tace shike nan ta tona Mana asiri ta gama damu dama ance tsintacciyar mage bata mage,Dan tsuntuwa kwai masifa,Dagaci yace menene Wai tace Gwaggo dakko takarda ayi a gaban kowa ya gani, Gani mukayi Rabi kullum tana ta zazzabi da amai gashi duk ta dashe tayi fari tas sai tofar da yawu takeyi,shine Gwaggo tace ita tana zargin ko Rabi cikine da ita Muka tafi chemist din garin nan muka Kira Tijjani Dafta yazo da abin gwaji Yana gwada fitsarinta yace ciki ne da Rabi nan take nace ban yarda ba yarinya kamila,sai ya zuki jininta a sirinji ya hau machine da wuri ya Kai asibitinsu na garin nan aka gwada har sau uku ciki ne da ita har na wata biyu,Gwaggo ta zaro takarda tare da mikawa Dagaci tace dazu Tijjani ya kawo idan Baku yarda ba a Kira Tijjani zaiyi bayani,Dagaci ya duba yaga tabbas Rabi Muhammad,makwafta sai aka Fara salati abinka da Kauye kinyi asara Rabi kin bata wayonki,kin cuci kanki wallahi baki kalli maraicinki ba sam Allah ya shirye ki,wasu na zagina haka Suka gama Suka tafi mamaki ya kasheni gaba daya na nemi zazzabin na rasa babu,Dagaci ne ya dakko wuka na mike tsaye da sauri abinka da me cuta Nan na kasa tsaiwa na zube kasa sharaf, Yace Dan ubanki wa ya Miki ciki? kuka na saki me tsuma zuciya nace wal..wal..hi bani... d..da ci...Mari ya hau kwada min ta ko Ina,yasa kafa yayi ball dani na bugu da jikin bangon dakinmu na fasa ihu me tsanani yaci gaba da dukana yace baza ki fada min wa ya Miki ba,na dage akan gaskiyata ni ban san kowa ba,sai da ya gaji da dukana sannan yace na Baki sati ko ki fadi Wanda ya Miki ciki ko ki bar min gidana shegiya tsinanniya tambadaddiya,wacce Allah ya kwashe Mata Albarka azzaluma,Yar iska fasika,Ni dai kuka nake wiwi har ya gama ya fita a dakin,su gaji Suka shugo Suka duddugure min Kai,Gwaggo murna suke Kamar zasu kashe kansu ita da Aunty Amarya.

Gani nayi Zan mutu a daki na lallaba Ina kuka na fice na nufi chemist din Bala banje ma Chemist din Tijjani ba,Bala ya ganni Ina kuka jikina duk rauni Yana jini,yace Rabi lafiya Kamar kinyi hatsari na sake rushewa da kuka na bawa Bala labarin komai Bala ya jinjina Kai yace Allah zai saka Miki Rabi kiyi hakuri kinji haka Allah ya kaddara Miki Haka ya wanke min raunin ya bani magunguna na dawo gida na balla na Sha,abinci ma Dagaci yace Kar a sake bani dole nake Shiga gari inda muke mutunci Ina rokon abinci a taimaka min,to gashi zance ya baza gari nayi cikin Shege duk inda na zaga sai zagina akeyi ana ci min mutunci,abincin ma kafin a bani sai an ci min mutunci a haka har sati ya zagayo,Ina idar da Sallar asuba lokacin na warke ma naji bugun kofa kamar za a ballata,Ina Budewa Dagaci yana min magana kasa kasa dan Allah Rabi nima ki yarda dani ki bani hadin Kai naji dadi,ko kina da cikin ba komai zanyi haka Indai zanji dadi, gida bai koshi ba a kaiwa dawa,harda lallabani sabo da Allah Rabi gani a gida ai gwara ni mu dinga Yi a boye sai na kaiki asibiti a zubar da cikin ki zauna a gidana kinji Rabi,idan ta Kama ma Sai na aure ki,Kallonsa nayi shekeke kawai,nace wlh baka Isa ba babu ni ba kai Allah ya kiyaye ni Kuma bani da ciki ehe,bazan taba yarda ba babu Wanda ya taba min wajen Iskanci na Kuma bazan yarda wani ya taba min wajen Iskanci na ba.

Fusata Dagaci yayi yaji haushi naki yarda da shi sai ya dawo da masifarsa dan uwarki fada min waye yayi cikin eyeeee waye yayi cikin? nace wallahi kaji na rantse ban taba sanin wani da Namiji ba wallahi Allah ko Qur'ani ka bani zanyi Alwala na dafa ko Kuma ka kaini asibiti da kanka ka gani,Dagaci yace karya kike munafuka akanki kwandala bazan kashe ba wajen gwaji,maza kwaso kayanki ki bar min gida,hankalina ya tashi na durkusa har kasa Ina kuka nace dan Allah kayi hakuri idan na tafi Ina zanje bani da kowa ku kadai na sani Dan Allah.....tashi nace tun kafin na karyaki,kuka nake wiwi amma babu Wanda ya kulani ma,ganin baza su hakura ba na dakko ledar Yan tsummokara na,Ina Fitowa Gwaggo tace yo kya tafi tsaya a Sanmiki koko ki kurba ta gama dama koko yana tiriri tana min dariyar wulakanci ta Miko min a kofi karba nayi na kalli kokon na kalli Gwaggo na juye Mata kokon a kirjin gaba daya,ta kwalla uwar Kara ta Fadi tana birgima sabo da zafin Kokon nasan sai ya kone Mata kirji na fice da gudu,Yan gidan Suka Yi Kan Gwaggo ni kuwa Ina tafiya gudu gudu sauri sauri Allah yasa garin ba kowa kasancewar sassafe ne,Bala me chemist ne ya ganni ya fito yace Kudirar Allah Ina zuwa haka? nace ai ya koreni,Bala yace wannan wanne irin azzalumi ne yanzu to Ina Zaki je? nace Ina da kawa a Kudu can wajenta zanje,kina da kudin mota ne? Kai na girgiza Masa Ina goge kwallata nace bara zanyi a hanya,yace Allah sarki ya zaro dubu daya yace ga wannan ko ruwa kya Sha,Hannu biyu nasa na karba Ina ta godiya,yace ki tsare mutuncinki kinji Rabi karki bari a lalata Miki rayuwa Allah ya baki Miji na gari me share Miki hawaye.

Idona ya kawo sabon hawaye muryata tana rawa nace Ameen ba komai Mahaifiyata ce ta jawo min da bata jefar dani ba da babu me wulakantani Ina fadar haka kuka me karfi ya kwace min Malam bala yace kiyi hakuri kinji ai kina da waya bani number dinki idan da wata matsala ki nemi layina kinji zan iya bakin kokarina bani da inda Zan ajiyeki Rabi Amma da kin zauna a gidana amma kin San gidana daki dayane ma,nace ba komai na karbi number Bala na shigar a karamar wayata shima na sa Masa tawa na juya da sauri na bar garin na shiga motar cikin birnin Kano inda zanyi bara na samu kudin zuwa wajen kawata Saratu dake Anambra Onitcha, ita Kuwa Gwaggo tana ta kururuwa Dagaci ya samo Zuma ya shafa Mata a kirjinta inda kokon ya kone Mata,tace da gani Rabi daga tsatson yahudawan larabawa ta fito Wanda basu da Imani.



SADAUKARWA NE GA DUK YARAN TSUNTUWA

A dinga sharhi please



AsmaBaffa
08061929616
[7/15, 5:48 AM] +234 912 082 5656: 🌼'YAR AIKIN KARUWAI🌼
LITTAFIN KYAUTA NE


11-15


Official

By
AsmaBaffa
08061929616



SADAUKARWA ZUWA GA DUK YARAN TSUNTUWA






Page naki ne
MARYAM T BALIYA







Nawwar a gurguje ya fito cikin shiri yasha wankan wani danyen yadi milk shara shara,gashinsa yaci gyara na gogaggun matasa kamar wani bature Yana zuba kamshi,agogonsa me azabar tsada yake daurawa yana sakkowa daga steps wani Yaronsa ne ya fito Masa da Yar karamar jakarsa wacce ya shirya kayansa da sauran abin bukata ya wuce Masa da ita ya saka a boot din mota,Sabreen tana dining tana breakfast sanye cikin kayan bacci tana ganinsa ta dauke Kai Wai ita me aji, kallo ma bata isheshi ba,har yanzu bai duba inda ya ajiye kudinsa ba bare yasan ta ebi wasu ba,Zama yayi ya hadawa Kansa tea yana Sha Yana cin chips sai da ya koshi sannan ya dauki wayarsa yace na wuce Kano Ina da meeting a can har na 2weeks,shekeke ta kalleshi ko a dawo lafiya babu tace to Kawai ta mike tare da haurawa sama,baki Nawwar ya tabe ya daga Kiran wani abokinsa Khaleel suna waya Yana fada Masa ya tafi kano,fita yayi ya shiga mota ya kame a baya securities a mota uku suna take Masa baya,gidansu ya fara zuwa tare da yiwa Maminsa sallama sai yaje ya samu Papa Yana gida har dakinsa ya shiga bayan sun gaisa Mama tace kaga dana ga iya wanka ga kyau,Murmushi Nawwar yayi ba shiri,Papa yace ai Yar mu ta dace,Sumarsa Nawwar ya shafa sannan yace Papa dama Kano zanje Ina da meeting da wasu turawa sunzo daga Finland akan business dinmu zanyi sati biyu,Papa yace a'a to Allah ya bada sa'a ubangiji ya ida nufi,Mama ta furta Allah ya tsare hanya yace ameen ya mike yace na tafi sabo da jirgi ya musu sallama ya fito direct part din Iyamami ya nufa kakarsa kenan,zaune ya isketa a kujera ta tasa katuwar tv gaba tana kallo tana tauna goro,Dan Nema sai yau aka ga damar zuwar min dama nasan ni ba kaunata kake Yi ba sai kayi sati ban ganka ba auren ma bana Yi na sake ka,Murmushi Nawwar ya saki yace dama ni me zanyi da tsohuwa ga matata sabon jini dama sallama nazo na Miki zanje Kano Ina da wani meeting, Iyamami tace aikin kenan to Allah ya tsare na zaci da matarka zaka tafi ma,ai ba dadewa zanyi ba,to Allah ya bada abinda ake Nema yace ameen tare da zaro kudi da yawa ya bata yace ga kudin cefanenki tunda na bawa Amarya karki ce na zalunce ki,dariya ta dinga Yi tayi godiya ya wuce Suka wuce airport.

Bangaren su Mama Kuwa Yana tafiya Papa yace bar shege ya gama tara Mana mu gaje dukiyar,wani ma yaji cewar Mama.
Nawwar yana zuwa Kano wani Yaronsa yazo da mota ya kaishi green palace hotel inda aka sauki turawan kuma a nan hotel din zasuyi meeting din kullum har a Gama,bai ko zauna ba kayansa Kawai ya ajiye yaje inda zasuyi meeting din dama shi ake jira,Yana zuwa suka Fara basu gama ba sai bayan Sallar Isha,wanka yayi da Sallah sannan ya zari motar da aka bar Masa ya fita dan zaga gari sanye cikin farar jallabiya me tsada.

Rabi ina sauka a Kano ban San inda nake ba haka na samu wani lungu na fito da yagaggen Hijab dina ja,ya gama fatattakewa haka na saka nace Neman Sadaka yo ai sai anyi Kalar tausayi sosai a kasar nan basa ba da Sadaka sai anga mutum ya kusa mutuwa sabo da wahala,ni Rabi ina maganganuna ina canja kamanni nace gani jajir ai dole na Zama Yar dukununu na nemo gawayi a hanya da kyar na samu na dandaka da dutse na dan shafa kadan a fuskata Kamar me shafa powder nayi wani duhu,hakorana ma duk na goga musu bakin sukayi Kamar sunyi tsatsa in ka kalli Rabi Kamar ba ni ba,tafiya nayi me uban nisa ga rana tayi sosai sai da na samo wata makaranta wacce babu gate ta gomnati ce na shiga na samu saman baranda na ajiye kayana a nan sannan na fito gefen titi tare da shanye hannuna Daya ya dawo Kamar me shanyayyen hannu ina tafiya ina cewa a taimaka min sabo da annabi a taimakeni na samu abinci, na koma dai dai wajen danger inda motoci ke tsayawa jiran a basu hannu su wuce ina bi ta tsakiyar motoci ina a taimakeni sabo da Annabi,dan me Mana ruwa da iska abinci ya gagare mu,wani ya sauke glass zai siyi charger naje wajen ina Alhaji adubi girman Allah Allah ya kaika gida lafiya canjin ishiri ya mika min ni Rabi na karbe ina Allah shi Albarka,matarsa dake Gaban mota tace na tsani almajiran Nan duk su damu mutane wasu ma sunfi ka kudi da gatansu sabo da mutuwar zuciya sai su fito bara,mijin yace ai baka San wa zaka taimakawa ba a haka wasu ne Suka bata wasu,wasu da kike gani dole ce ta sasu bara baki San mene dalili ba.

Na hada uwar zufa sosai amma daga goma sai biyar sai ishirin yinin ranar gaba daya kudin abinci naci dasu zuwa Yamma na koma makarantar inda kayana suke naci sa'a Kuwa lokacin Yan makaranta suna hutu sai na fito wasu gidaje dake kusa da makarantar na lallaba na leka wani gida na talakawa sosai ai Kuwa a zaure na iske wani dan baho karami na dauke shi na gudu tare da komawa makarantar na ebi ruwa a tuka tuka din na duba jakar kayana na dakko sabulun wankina na zaga bayan aji tunda ajujuwan a rufe suke me gadi ma ya tafi hutu abinsa a can a tsorace nayi wanka na canja Kaya sannan na Kara Nemo gawayi na mulke Fuska ta na kwanta a barandar Ina hutawa bacci ya sace ni sai bayan Sallar Isha na farka,a gurguje nayi Alwala tare da Sallah sannan na sake Fitowa cikin dare ko zan dace,ko da na fito ban iya bara ba sai yawo Ina ta kallon birni ko Ina haske Kamar Rana Yan Mata da samari da Yan gayu ana ta lailaya Kan mota gaba Daya kallo ya dauke min hankali Ina ta yawona har nazo bakin wani hamshakin Hotel na tsaya Kawai Ina kallon haduwa motoci sai parking suke wasu a ciki wasu a waje,Yan Mata Kuwa Subhannallahi ana ta shiga dasu da manyan Alhazawa wasu ana sauke su a napep,wasu sunyi gayu suna zaga wajen masu so suna samu suna Shiga dasu ciki,sai zare Ido nakeyi Ina kallo.

Ina nan tsaye wani kamshi ya daki hancina Wanda ban taba Jin irinsa a duniya ba,kafin nayi motsi wani azababben matashi ya wuce ta gefena,Nawwar kenan hannunsa dauke da ledojin take away,wayarsa ce tayi Kara ya Fara lalubota ya zaro Wayar ya daga tare da shigewa cikin Hotel din, Wallet dinsa ce ta Fadi bai kula ba sabo da ga waya ga ledoji a hannunsa har ta Fadi bai sani ba,Ina kallo da sauri na karasa kanta na dauka tare da budewa ATM card ne kala sun Kai biyar a ciki sai wasu kudin Amurka dollars amma dake ni Yar Kauye ce ban San Mene ba sai na tabe baki nace aikin banza babu abin arziki a ciki ma bari na jira ko zai fito ya amshi abarsa,waje na samu nesa da wurin na zauna a jikin wata bishiya,shi Kam bai San ma ya jefar da wallet dinsa ba wanka yayi ya kwanta bacci abinsa,Ni Kam a jikin bishiyar bacci ya kwashe ni sai farkawa nayi Naga rana a kaina,tashi nayi da sauri na koma makarantar da masaukina yake Alwala nayi nayi Sallah wallet din tana wajena,itacen bishiya na balla na zauna na goge bakina tas na kuskure da ruwa,Fitowa nayi Ina dubawa har naje wajen da mutane suke sosai da manyan shaguna ga me kosai a wajen na siyo cikin kudin barata na jiya,na siyo bredi da shayina ba Madara aka zuba min a Leda na dawo makarantar na zauna naci na koshi,na sake shafa bakina a Fuska duk nayi Mata dabbara dabbara da bakin gawayi na saka yagaggun kayana na bara na fito rike da wallet a hannuna

Ina tafiya Ina kalle kalle Ina zare idanuwa wani ne ya tare ni a hanya ganin Kamar ko zararriya ce ni,yace ke...a gabansa na tsaya Ina kalle kalle,gashina na sosa na kasa tsayawa kyam,kana ganinsa kaga kamili yace Ina Zaki je? nace ai Almajira ce ni,kai ya jinjina yace kina zuwa makaranta Kuwa? Murmushi na saki nace tab ai ni Jahila ce bani da ilimin komai yanzu ma littafi da karatu bazai Shiga kaina ba,galala ya kalleni yace kina so ki iya? da sauri nace ae,yace Okay da zaki iya zuwa dakina da na koya Miki dole sai karatu ya shigeki da yatsansa ya nuna kirjina yace idan bai shiga ta kanki ba dole zai shiga ta nan idan bai shiga ta nan ba to Dole zai shiga ta nan ya nuna gabana da yatsa,nace har ta nan karatu Yana shiga kaji karya,to Malam Iskanci aka ce ana yi da wajen,Kai baka sani ba Iskanci fa akeyi da wajen ba ruwana wajen Iskanci ne,na ja tsaki na juya nayi tafiya ta abina Ina masifa ya dauka bani da wayo zai taba min wajen Iskanci na Allah ya kiyaye.

Direct hotel din nan na koma ko zanga mutumin jiya gashi bazan ma ganeshi a Fuska ba sai dai ko idan naji kamshinsa na dade Banga alamar shi ba na bar wajen na tafi barata yau ma iya kudin abinci na tara, Wasa Wasa kullum Ina zuwa Hotel har da dare ban sake Jin me irin kamshinsa ba har na kwashe kwana biyar,shi Kuma Nawwar bai ma duba wallet dinsa bata nan ba,yau da dare na sake komawa nace wallahi daga yau Matukar ban ji me kamshinsa ba bani sake zuwa, ranar Kuma Nawwar ya nemi wallet dinsa ya rasa musamman atm card dinsa sune Suka dame shi, Fitowa yayi ko zai iya gani a cikin motarsa Nan ma ya gama dubawa babu, Fitowa yayi dake da duhu a wajen ko fuskarsa ban gane ba nidai naga hadadde ya wuce,Yana wucewa wani kamshi ya dakeni naji Kamar irin kamshin Wanda ya jefar da wallet dinsa jiya,Ina juyawa Naga ya Dan min nisa da karfi nace Malam....tsayawa yayi ba tare da ya juyo ba da gudu na fyalla naci wawan birki a gabansa Ina haki na zaro wallet din tare da Mika Masa nace t...taka..ce? Yau sati guda kenan ka jefar da ita na ganta kullum sai nazo ko zan ganka,kasan irin hatsarin da na Shiga a hanya sabo da zan kawo maka abarka ai Saura kadan wani ya taba min wajen Iskancina,wai dan Allah karatu ai baya Shiga ta wajen,Nawwar bai gane me nake nufi ba ko saurarar zancen nawa baiyi ba, farin ciki ya Kama Nawwar cikin muryarsa me dadin saurare yace ta ya Kika ganeni? Nace kamshinka yasa kawai danni ko yanzu in za a kasheni bazan ce ga fuskarka ba sabo da duhu,karbar wallet din yayi Ina kallo ya duba komai nasa Yana ciki inda suke ya fito da dalolin masu yawa ya irga ko wacce dala dari dari ce a ciki ya zaro guda Uku yace gashi na gode

Baki na turo nace Hmmm uhm jam ni me zanci da wannan takardar ai gwara ka bani dari biyar,dariya ta kamashi yace kudine fa idan Kika canja sunfi dubu dari nace wallahi bana so kaji mutum dama can baka yi Niyyar kyautata min

5 Comments On YAR AIKIN KARUWAI
avatar
asmau-7

1 year ago

Reply

T

avatar
sadiya-9

1 year ago

Reply

Wonderful and nice novel

avatar
diaabdourahamane

1 year ago

Reply

Nice novel

avatar
bashar

1 year ago

Reply

Don Allah ina cikon labarin nan?

avatar
taskar

1 year ago

Reply

Replying to bashar

Dole fa sai dai ku siya a cigaban labarin a wurin marubuciyar, ga nambarta 08061929616

Please Login or Register in order to submit comment