Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

nan which kind nonsense be this,tashi karki bata min lokaci ya furta a Matukar hasale cikin tsananin fadan da sai da na tsorata kina wasting time dina get up,me yasa kike sa min ciwon kaine har waje Yan gidan suna Jin bala'in da yake zazzaga min,Star ta rike baki suna gulma lallai Miracle ta dakko ruwan dafa kanta,Har Kara labewa sukeyi suna manna kansu a jikin kofar dakinmu sabo da suji me ake cewa,Ni bazan koma gidanka ba bana so matarka ta dinga min masifa tana min kallon banza ba dama mu hadu sai ta dinga hararata,ba sai ki rama ba kema,to idan na rama ba Kaine zaka ce bani da hakuri na furta Ina share hawaye,Murmushi ya saki yasan yanda na dinga cin uban Sabreen a gidan sai da Sabreen ta gaji ta daina kulani amma yanzu nace itace take min,yace bana son dogon surutu tashi mu tafi,bazan je ba,Ina magana kina min musu Zan iya janki fa har mota,Ni dai bazan je ba,na daina sa kayan Yan aiki ba daga yau,Mamana da kannena fa idan Suka ganni,to su gani mana basai su rabaka da ni ba ka kyaleni,Tsaki ya ja ya shiga karewa dakin kallo ya hango kayan aikin Dana watsar a daki ya kwaso su harda ledar kayan ya zuba a ciki ya jawo wani Kato hijab yace saka mu tafi,Ina so in Masa musu amma bazan iya ba ya tsareni da Ido kwarjininsa ya min yawa,sai naki sakawa Kuma nayi shuru,durkusawa yayi yace abinda Ina da Hannu ya dauki hijab dina tare da saka min da Kansa yace tashi,kin tashi nayi na Fara kuka,daukana yayi cak ya sabani a kafada da ledar a hannunsa ya tafi duk Yan barikin wajen suna kallo mu bama Jin kunya suma a wajensu wannan Abu ne karami bai Kai a kalla ba ma,a mota ya jefani ya zaga ya shiga shima tare da tuka motar Muka bar layin.

Tunda Muka tafi nake sharbar kuka bai ko kulani ba,ya wuce dani gidan da na Fara Zama a ciki ya kalleni kadan tare da maida hankalinsa Kan tuki yace gidana ne bakya so? Ina shesheka nace ae,a ransa Yana so ya kaita wajen Maminsa Amma bata da kunya zata iya kunyata shi a gaban Mami ko taje tayi wani shirmen,ko ta dinga guduwa irin wannan za a San da matsala bai so Kuma a San me take yi,shi Kuma baya son kebewa da ita waje daya ita Kuma taki gane nufinsa dole ya koma wajen Khaleel ko zai samu shawarar ya zaiyi da ita.

Yana parking a gidan na fice na shiga ciki Ina Jin Dadi bana son gidansa,Zama yayi a kujera tare da dafe kansa da hannu yayi Shuru Yana tunani,gefensa na karasa na zauna gaf da shi nace meke faruwa? hannuna na sakalo ta wuyansa yace Kinga abinda bana so Kinga abinda kike Yi bana so shi yasa nake kaucewa kebewa dake,dariya nayi na cire hannun nace Ustazu,hijab dina na cire surata ta bayyana yace kinwa kanki wlh sai kin koma gidana baza ki sani a gaba ki dinga Iskanci ba tashi ya fisgi hannuna ya min tsawa sa hijab jikina na rawa na dauka na saka ya fincikeni har sai da na Fadi amma hakan bai sa ya sake ni ba Kawai jana yaci gaba da Yi a kasa kiiiiiiiii ......na mike da kyar a haka ya sake jefani a mota ya wullo min ledar kayana saka kayan aikinki,na zaro Ina rawar Hannu na saka Riga na saka skert akan kayana na maida hijab din jikina ya ja mota Yana uban Tsaki.









AsmaBaffa
[7/15, 5:49 AM] +234 912 082 5656: 🌼'YAR AIKIN KARUWAI🌼
LITTAFIN KYAUTA NE


36-40


Official

By
AsmaBaffa



SADAUKARWA NE GA DUKKAN YARAN TSUNTUWA



*AL-KUTUBIYYA ISLAMIC MEDICINE*
_Jama'a kada ku bari wannan garabasa ta wuce ku,muna da nau'i magungunan gargajiya masu kyau da inganci_
_Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda inganci da sahihancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai-dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_

_nfection_
_Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace *SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI💯☑️*_

_Muna sayar da supplement gangariya irin wadanda ba su da matsala sai da su gyara garkuwar jiki da inganta lafiya, muna bayar da sari duk wani supplement muna da shi, kuma muna sayar da daya muna bada sari akan farashi mai sauki, muna tura kayanmu ko wane gari domin neman karin bayani a tuntunbi wannan lambobinmu dake kasa._
*08089965176*
*07084653262*



Page naku ne

Ruky
Kukuwa
Maman Khadija Abj
SummynDaddy
Fatimalawan600
Maman Twins
Ammey laylah
Umminnas
Serdieycute
Wuta(Golda)
Hafsat I Atiku
Khairiyya Ahmad
Darlin Queen
~Umme

Gingina ga
BINTA UMAR ABBALE
UMMIN SADDIQ
MHIZ AWWAL





Sabreen tana Jin Dadi na gudu da kaina sai ganinmu tayi ya dawo dani tace wlh baka Isa ba bazan zauna da Yar iska ba ni da kaina zanyi maganinta,ban kulata ba shima bai kulata ba ya shirya ya bar gidan ya wuce gidan Khaleel,Ina zaune zuwa yamma ban San komai ba wasu kartai su biyu Suka fado min daki,hannayensu dauke da manyan bulalai,Sabreen ce ta shigo tace Na'alhaji ku cika Mata aiki yanda nace kudi Zan biya,Ina zaune Ina kallon ikon Allah,mikewa nayi tsaye,Sabreen tace ke ba Yar iska ba wlh baza ki zauna min a gida ba ai ba gidan ubanki bane,Cikin kartin nan Daya ya kamani da igiya a hannunsa Muna kokawa Ina cewa ka sake ni zanci uwarku shegu tsinannu Allah ya Isa a Haka Suka daureni da igiya Kamar goro kowanne a cikinsu da bulala Suka Fara zubaba min ita Kamar daga sama aka basu umarni,Ina ihu amma Sabreen cewa take ku karawa shegiya sai ta daina motsi gobe ai baza tazo gidan wata ba,tunda Naga zasu cuceni yanda tace sai na daina motsi ai Ina Jin haka da Suka sake tsula min uku sai nayi suman karya na daina ko motsi tare da dauke numfashi na, Sabreen ta tuntsire da dariya tare da cewa ku barta haka ta Suma muje na biyaku,Suka juya Suka fice sannan na saki numfashi na amma dukansu dukane bana Wasa ba gadon bayana yayi rudu rudu ya farfashe,na fashe da kuka nace wlh sai na rama,Ita Kuwa biyansu tayi Suka tafi Ina nan kwance a kasa sun daureni sun tafi,inda Allah ya taimakeni na dinga ihu ban daina ba cewa nake wayyo Allah azo a taimakeni har Nawwar ya dawo yaji ihuna a daki da gudu ya shigo ya ganni a daddaure da igiya,na saki kuka me karfi,yace waye ya Miki haka nace Sabreen cikin kuka,reza ya dakko ya yayyanke igiyar na tashi zaune da kyar nace kalli bayana na zuge Masa zip yaga yanda bayana yayi rudu rudu bulala Uku kawai wani wajen har da jini abinka da Fara dama,waiyazubillah ya furta ya fita a fusace,Ni Kuwa wayata na jawo na Kira Seraline tana dagawa na fashe da kuka nace ku taho za a kashe ni matar saurayina tasa Yan Iska sun min dukan tsiya sun fasa min jiki kuzo gidan na fada Mata Adress,Seraline Wayar ta ajiye daure take da guntun towel daga wanka ta fito ma taji wayata da ihu ta fito tana kwalawa karuwan Kira harda Yan daudu su biyu,matan Suka zo su wurin goma tace an taba Mana Yar uwa,Yar uwar mu tana can Rai a hannun Allah matar Saurayinta ta kawo Yan Daba sun Mata mugun duka.

Santana dan daudu yace ahayye an tabo jarabar duniya yau za aga bala'i ya rike haba yace oh Kinga star ku dakko makamai,Nima ga Nawa ya suro wani dogon ludayin juya miya,Daya dan daudun yace yau nake Jin jaraba shike nan sai a nemi illata Mana Yar uwa laifinta ko na mijinta ita Miracle sabo da Allah Ina ruwanta service fa aka dauketa ya tafa hannaye biyu yace kuzo mu kaddamar musu ke Yar uwa kiji samun waje dan Allah ya dakko almakashi yace aski zanwa shegiya a local government dinta sai na samu tsuliyar shegiya na aske ta kwal kwal Zan Mata muje,Star tace yau idan na dinga zubawa Yarinyar mari sai ta tafi gidansu a kafa, Wise ma daga wanka ta fito,itama Yarzabil haka,Manduwa da Star sune da wata matsiyaciyar shiga domin manduwa mini skert ne a jikinta sai half vest,ita kuma,da sauran karuwan duk ba me shigar mutunci su goma cif Suka hadu zasu je,wasu Suka taho Suma Suka ce ai dole Suma suje su kwatowa Yar uwarsu yanci,mutum biyar harda yare Suka karu,kananan mota uku taxi uku Suka cika su Sera dukkansu daure da towel su uku a haka Suka tafi sauran Kuma Babu me shigar mutunci ga Yan daudu mutum biyu.

Suna zuwa kofar gidan masu taxi dinma nasu ne Yan duniya ne harda zana kwabo a kofar gidan Suka danne horn ba dagawa fiiiiiiiii suna zaga wajen da mota wasu da makamai wasu babu,Kuma sunci sa'a ba securities yau a gidan sai me gadi Kara da hayaniya tasa Sabreen data buya a daki gudun Kar Nawwar ya daketa ta fito Jin ihun da karadin tasan ba lafiya ba,har compound ta fito taga an banko kofar gate suna dukan gate karaf kararaf...wata Igbo a ciki tace who is she da karfi,Seraline daure da dan towel tace gata can Suka rugo gidan gaba daya suna durawa Sabreen ashar tsoro da firgici yasa Sabreen ta kasa motsi da kyar take daga kafarta tana ja da baya,Seraline ba jira tana zuwa ta cakumi wuyan Sabreen ta kwada Mata mari,ta sake kwada Mata mari tace dan uwarki Yar uwarmu Zaki sa a daka ta sake wanke ta da mari,Star tazo ta hankada Sabreen ta timata da kasa Suka Zo dukkansu Mata Suka dinga jibgarta,Yan daudu ihu Kawai da zage zage sukeyi suna shewa da tafi, Sabreen ihu babu damar Yi sai ta Fara basu hakuri tace wlh bazan sake ba babu ruwana da Yar uwarku daga yau,Wise ta make Mata Baki sai da jini ya fito ko a jikinsu Yarzabil harda fisgowa Sabreen nono ta kurma salati tace ko a bariki shegiya baza ki samu kudi ba,wannan a kwalta ba me zabarta bata da nono,Seraline ce tace ku kyaleta haka Naga jikin Yar uwarmu da sauki ganina na fito Ina dingishi,Sai lokacin Nawwar yaji hayaniya yaki karewa ya zaci ma securities dinsa ne suka dawo ya leko ta sama ya hango Sabreen kwance a kasa jina jina da ita ba Dan kwali rigar ma ta yayyage,jini ta baki na fita,jikinta duk rauni,Me gadi ma yana kwance a kasa Yan daudu sunci ubansa sun kwantar da shi a kasa Santana ya Dora kafarsa daya a ruwan cikin me gadi yace da dayan Miko min mudubi a jakarka na duba fuskata ko ta baci,Nawwar ne ya fito da sauri ya daka musu tsawa wannan wanne irin haukane zaku zo min gida ku daki matata,wanne irin hauka ne haka,Seraline tace Matukar za a taba Mana Yar uwa to wlh baza mu Bari ba, ba a taba irinmu a kwana lafiya,baiwa ce ka dauka wallahi duk ranar daka bari aka sake dukanta wallahi abinda zamuyi sai yafi wannan,tsawa Nawwar ya daka musu ya nuna musu hanya yace get out ko yanzu nasa a kamaku gaba daya,Wisa tana gyara daurin towel dinta tace dama ai ba Zama zamuyi ba dole zamu tafi mudai aka taba Mana Yar uwa baza mu kyale ba ko sojoji ka zuba gidan nan wallah sai mun tarewa ko waye Hanya mun Saba Masa kamanni,Ina ji nace ya Isa haka Wise kuje tunda Kun rama min ana Kara tabani zan kiraku kuje,Suka tafi abinsu Suka sake tashin motocinsu Kamar zasu kashewa mutum dodon kunne,Suna barin kofar gidan ya juyo ya kalleni yasan Yana masifa Zan gudu can bariki yace me yasa bakya ji? Me yasa kike da taurin kai? Lokacin Sabreen ta bude idonta tana kuka wiwi tana kallonmu, nace ya za ayi tasa karti maza su min duka daya ya rikeni ya daureni,Ido ya zaro yace ya rikeki nace ae sai da ya rungumo kirjina sau uku Yana taba min nono Kuma itace tace su taba na banza ne na karasa da kuka na fada jikinsa na rungume shi nace shi yasa nace gwara kai ka dinga tabawa tunda kana biyan kudi,Tsaki yaja ya janye jikinsa da sauri ganin Sabreen tana gani, tana daga kwance tace ta tabbata wallahi Karuwarka ce yau gidan ubana Zan kwana,duk dukan da taci haka ta mike Yana tsaye taje ta hado kayanta ta fito tana tafiya da kyar ta shiga motarta,ihu nayi Ina dariya nace bye bye,Me gadi da ya tashi tuni Yana uzurinsa ya bude Mata gate ta fice a tsiyace, Nawwar ya kalleni yace kinji dadi shike nan? dariya da farin ciki ya kamani nace ae mu indai za a taba mu to fa uwarsa baza tayi bacci ba ko waye in ka gaji ka maida ni bariki na ka huta ni banga abin takura ba a nan duk inda Naga Sabreen sai ta San fada damu ba dadi.

Ido ya lumshe a hankali tare da juyawa ya koma Palo ya fada saman kujera Yana huci zuciyarsa tana Masa zafi ciki na koma nima na zauna Muka Yi shuru ni da shi,ba a fi 15mnt ba sai ga Kiran Baffansa,sai da yayi tunani dama ya daga Yana dagawa yaji ashar sabo da shi babban mutum ne amma Babu Kalar zagin da baya yiwa yaro sai da ya kutuntuma Masa ashar iri iri karshe yace to Dan uwarka Dan ubanka kazo gida Ina nemanka,to kawai yace ya tashi bazai iya driving ba yau driver dinsa na ya tukashi zuwa gida.

Kowa ya zauna yayi Shuru Yana saurare Nawwar yana kusa da Maminsa, Iyamami itace ta Fara magana tace wallahi Nawwar ka bani mamaki ka bani mamaki tirrr da hali irin naka,Mami a ranta tace ba tirr ba ban haifi dan tirr ba wlh Allah yayiwa dana Albarka Inshaallah sai yaga dai dai,Iyamami tace dama wannan lusarar uwar taku ai ita ke zuga ku wato Kai ka girma mace daya ta maka kadan sai ka Kara da karuwa,to bari kaji ko zaka Kara aure sai dai a dangi a samo maka wacce aka sani aka San iyayenta da asalinsu,Muna wannan gari Wanda ya tara baki garin kazo nazo ace ka hadu da wata ka aura bazai yuwu ba ko bana raye Matukar da sauran yarana a duniya baka Isa ba,idan Karin aure kake so ka koma can danginmu Shuwa ka Nemo Yar dangi idan Kuma baza ka iya ba ka bamu zabi,Kuma ba yanzu ba sai Sabreen ta tara iyali,Mamin Nawwar ce tayi magana tace idan Allah ya rubuta ya zakuyi wannan fa hurumin Allah kuke shiga,laaaaaa......Iyamami ta dafe kirji kunji Salamatu abinda take fada min wato ke ba a Isa ayi magana akan yayanki ba sai kin shiga kin tare musu shi yasa Suka taso basu da tarbiyya basa ganin kowa da mutunci
Papa ne yace dan Allah ku kalli jikin Sabreen 'yata Daya tilo tace gaba daya matan tsirara Suka Zo da Yan daudu sunfi su talatin Suka Mata dukan tsiya,Sabreen da bakinta yake a kumbure da idonta daya ya kumbure tace ai iya Yan daudu sunfi sunfi su goma,Nawwar ya kalleta tare da furta kiji tsoron Allah lokacin dai kin ji jiki bakya gani dai dai,Baffa ne yace rufe min baki yanzu kalli Yar uwarka kalleta matarka wata banza ta Mata haka idan baka Yi Wasa ba sai na tsine maka,Mama tana gefe tace ato a dauki mataki wallahi idan wani Abu ya samu yata tilo baza aga dai dai ba duk da nima Yar uwa ce amma ai Da baifi 'Ya ba,Sultana ce tace wlh Namiji yafi 'ya ko a gado ba daya bane,Baffa ne ya kifa Mata Mari ta dafe kunci yace uwata tana magana kina magana,Iyamami kuka ta fashe da shi tace dama yaran Salamatu basa ganina da mutunci sun tsaneni ta gama zuga su,Amaryar Baffa Yar gaban goshinsa sai yanzu tayi magana tace ato gwara ku gani da idonku nima da yarana biyu ne rak basa kaunata basa kaunar yarana Kuma jini daya muke dadin abin dai mijin ko kwana baiyi a dakinki sai dai ki dafa Mana a matsayin baiwa kike shi yasa ban damu ba,Iyamami tace ita take jawa kanta da kuturun iyayinta,Baffa ya kalli Nawwar yace ka tabbatar ka gyara kuskurenka idan ba haka ba ga shedu kar ku ce ban fada ba duk abinda na maka kaika ji,Kuma ka tababbatar ko wacece ta bar gidan nan Kuma Kar najita a Daya daga cikin gidajenka Zan dinga bincikawa Kuma Kar a kawota gidana ko bangaren uwarka ta koma barikinta kaji me nace? Nawwar yace naji,Sabreen tace Saura Maganar dazu Baffa,yace Ina sane ai tace dama baka kwana tare da ita Kuma kana da lafiya,idan da kana muamular aure da ita ai da mun ganta da ciki,Nawwar ransa ya Fadi da Sabreen har wannan zancen ta iya fada kwafa yaja a ransa,sai da Suka gama fadansu sannan Suka sallami kowa,Mamice ta Fara mikewa yaranta kaf Suka tashi Iyamami ta furta idan aka zagemu aka ci Naman mu Allah ya Isa munafukai duk kin lalata yara Anya Kuwa wannan jinin mu ce,tafiyarsu Suka Yi Suka barsu suna ta magana akan Mami da yaranta.

Mami sama ta haura bedroom dinta,yaran gaba Daya Suka shiga Nasira da Hamra ta Fara Kora tace kuje kuyi Assignment dinku ayi Sallah Kuma,Sultana ta kalla tace kije kiyi Sallah ki shiga kitchen kiyi girki tace to ta wuce shi kuwa Autan nasu sarkin ball ya wuce dakinsa tuni,Nawwar kwanciya yayi a gadon Mami ita Kuma tana zaune a gefe a hankali tace wacece? Nawwar yace Mami ba fa wata bace,bana son karya me yasa baka ji Nawwar me yasa kake son sani a masifar mutananne? tunda kasan halinsu Kawai kabi umarni a zauna lafiya,Mikewa yayi ya zauna yace Mami kin san fa tsarin Allah dole haka rayuwarka zata bi,Kuma wlh ni nayi Niyyar taimakonta bazan fasa ba,Ido Mami ta zaro tace sonta kake Yi? da sauri yace haba Mami so Kuma Allah ya kiyaye bata layin Kalar matan Dana ke son aure ma,ni da nake son Ustaziya kullum a hijab Yar Shuru Shuru saliha bana son mace Yar duniya,nafi son me addini da hankali, Murmushi Mami tayi tare da cewa Allah ya baka to,yace Ameen,to fada min tunda kace ba sonta kake Yi ba me zakayi ka taimaketa Kuma wacece ita? yace ni so nake Kawai ta sanadina ta shiryu yanzu dalilin kawota gidana so nake na raineta na bata tarbiyya sannan na aurar da ita,au ashe yarinya ce ma shekarunta Nawa? Mami ta tambaya,yace 22yrs take,dariya Mami tayi tace Dan Allah Nawwar bana son Wasa 22yrs sabo da rainin hankalinka kace Wai zaka raineta ka bata tarbiyya ka aurar da ita,to ki bari Mana kiji labarinta Mami ba kya cin ribar zance

Kunne Mami ta Miko Masa tace to Ina ji,Murmushi yayi yace to ki daina kallona ma kunyarki nake ji,yau kuma,dariya yayi yace I'm serious,Ina ji,yace Kinga Mami bana boye Miki Abu karki ce nayi rashin kunya, lokacin Sabreen tana min wulakanci Ina nemanta bata yarda ko naje na iske tayi bacci Kuma baza ta tashi ba,lallai maganin Iyamami yayi aiki,idonsa ya rufe Wai kunyar Maminsa yake ji,tace uhum Ina ji,shine naji haushi na gaji Kuma a lokaci Ina cikin yanayi na bukata,Mami tace Allah sarki My son Sannu,dariya ya sake saki yace Mami kunyarki fa nake ji,to na daina Ina jinka,yaci gaba sai nace bari ma na fara Neman Mata na dinga bin titi shine na ganta,a lokacin ta Yi maka ka dakko ta ko? Mami ta tambaya yace ae,Amma ba abinda ya faru banyi komai ba,Mami Hannu ta daga sama tare da furta ya Rabbi na gode maka Ina Addua Inshaallah yarona bazai lalace ba na sani,daga nan ya bawa Mami labarina kaf da komai har labarina dana bashi cewar Ni Yar tsintuwa ce da labarin Dagaci inda na taso,Mami tana gama ji tace ya sunanta? Rabiah,tace duniya kenan idan kaji halin da wani ke ciki sai ka godewa Allah Kai.

Abinda mutum zai Fara godewa Allah akai da aka Yi auren sunna aka haife shi ya taso cikin asali da dangi,idan aka jefar da Kai ko akasi yasa kazo a Dan tsuntuwa baka San kowa ba shike nan Kai baka da asali da nasaba,Babu dangi bare uwa da uba baka San kowa ba a duniya sai Kai kadai wannan kadai ya Isa a tausayawa yaran tsuntuwa da Wanda ke gidan marayu Allah sarki kaga rashin iyaye da dangi shi ya taba wannan yarinya da ace ta fada Hannu na gari da shikenan, idan aka samu akasi baka fada Hannun na gari ba to fa ka shiga Uku,a wannan Zamanin wa Yana zina da kanwa,Kani yayi da yayarsa,kanin uba ya Nemo Yar Kaninsa ko Yar yayansa ana samu uba me Neman yarsa to bare mariki Dagaci Wanda ya rike yarinya ganin bata da kowa irinsu Kuma Allah Yana musu baiwa da ba kowa ke samu ba sabo da Allah baya hadawa mutum biyu

Wannan marikin nata yaci Amana matuka Kuma na tausaya mata,yanzu kaga Wanda ya riketa yaci amanarta ya koreta amma karuwai sun karbeta har fada suke akanta suna daukar Mata fansa,suna kiranta da Yar uwarsu su basu kyamaceta ba Zama ya hadasu na banza Amma sun dauki kansu Yan uwan juna ne,ga masu hankali Wanda basa shashanci sun tsani junansu Kuma suna Yan Uwa musulmai,wani ya taba musu ita sunzo sun daukar Mata fansa Allahu Akbar,kaima gashi Allah yasa maka ita a ranka,a'a Mami nifa ba so ne ba Kawai naga ta lalace ne da yawa shi yasa nake kokarin taimaka mata,Mami tace ka taimaketa da duk abinda zaka iya da karfinka da dukiyarka ka taimaka mata amma kayi da iyawa sabo da mahaifinka idan ya gane Kuna tare zai dauki matakin da baka zato kasan halinsa ita Kuma matarka bata da hankali ka sani Sarai zata sake fada musu,Amma yau Zan bika naje na ganta ashe itace Hamra take cewa kazo da wata ziza kyakyawa Sam bata Yi Kalar Kauye ba,yanzu kaje kayi Sallah in yaso sai muci abinci muje,no Mami bazanci abinci ba nasan ta dafa yanzu Yarinyar fa tana da Yar biyayya abinda nace tana Yi she is so caring, Sabreen bata bani abinci tunda na aureta naci banci ba babu ruwanta amma ita har rokona take yi sai naci dole,Mami kin gani har durkusawa fa,a haka tasan idan Ina Fushi kiji dan Allah dan lokaci kadan ta karance ni she is so brilliant,Mami tace kaji Yar baiwa Kudirar Allah,yace dama sunanta ne Kuwa Kamar kin sani Miracle ake ce Mata,ya sake furtawa, Mami ki tashi kiyi Sallah tace to ko bakya Yi yau ne? Slifas din dake kafarta ta dauka tare da jefa Masa ya fita da gudu,Tsaki Mami

5 Comments On YAR AIKIN KARUWAI
avatar
asmau-7

1 year ago

Reply

T

avatar
sadiya-9

1 year ago

Reply

Wonderful and nice novel

avatar
diaabdourahamane

1 year ago

Reply

Nice novel

avatar
bashar

1 year ago

Reply

Don Allah ina cikon labarin nan?

avatar
taskar

1 year ago

Reply

Replying to bashar

Dole fa sai dai ku siya a cigaban labarin a wurin marubuciyar, ga nambarta 08061929616

Please Login or Register in order to submit comment