Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da, waje ya hadu dama na manya ne, 8:30pm an gama min make up, munsha kayan namu Kalar decoration din wajen da aka yi Fari da dark pink sai Silver gaba Daya wajen walwali yake, ni rigar Amaryar tawa gown ce daga kasar waje yayi order online dark pink tana Jan kasa daga baya,sama ta kamani me dogon Hannu Net,sai gogoron da aka daura min Silver da takalmi da jaka silver Kalar shaddar jikinsa,hularsa da takalminsa duk Kalar shaddarsa Yar gaske an Masa babbar riga ta matasa dai dai shi, Khaleel ke driving dinsa a bayan sabuwar motarsa ta bugawa a news fara duk ta Sha adon flower da zare pink kana gani kasan ta Amarya da ango ce, daga wajen makeup din na fito wacce ta min ta rike min kasan rigar har motar na shiga ta rufe tana mana murna Khaleel yaja Muka wuce,hannuna wata a layinmu bahaushiya ta iya lalle tana yiwa hausawa karuwai, ita ta zana min ta gani ta fada ja da baki hannu da kafa nayi kyau abin ba a cewa komai, Khaleel yace Amarya kinyi kyau sosai wlh dama me kyau ce,nace na gode Friend

Nawwar yace mu ganki na juyo sosai harda fari na lumshe Ido dan Wai yaga gashin idon da aka saka min sosai, hannayena da ya Sha lalle da abin hannu na amare na daga Masa ya gani na juya Masa tafin hannun ya gani,Khaleel yace kaiiiiii gaskiya lallen yayi,Nawwar yace Wai mene haka bana son munafunci,dariya yayi yace to sai ka bari a daura sai mu daina fada amma yanzu bata zama taka ba,Murmushi nayi na zare takalmin kafata tare da dago kafar daya nace ka gani, Khaleel ya leko da Kansa ya maida Kansa wajen tuki,Nawwar yace Allah ya kyauta maka Khaleel,kafar ya gani tayi kyau yace good, maidata dan Allah kin dameni,sai da na maidata yace muga hannun naki na Miko na dama,yace na hagu,na Miko masa hannunsa yasa a aljihu ya saka ya zaro gidan zobe ya bude naga zoben gold me tsada Dan karami hannuna ya rike ya saka min zoben a yatsana na kusa da karamin yatsan da kyar ya shiga yayi min cif cif,na washe baki nace yayi kyau thanks gidan zoben ya saka min a jaka tare da kudin liki masu yawa Yan dubu dubu sababbi,Khaleel yace gulmamme abinda kakeyi kenan,Bai kulashi ba, tun kafin mu karasa wajen event din muke jin kida na tashi Kamar hauka Yan gayu ana ta Shiga Su Sera Amarya suke jira suna waje wajen su goma sauran Kuwa an gama cika ana cashewa rawa suke ta rashin kunya ta fitsara Amma da aji ake yinta ba hauka ba yau ranar nutsuwace da yanga da aji, Yar zabil tana ciki itace MC ma,akwai wasu masu rawa a gidan karuwai ba rawar da basa Yi Mata da maza Yan rawar Solo ne ai kuwa sune suke takawa gwanin nishadi ana ta kallo suna mimimg wakokin hausa, a ciki Mc tayi magana da turanci Amarya da ango sun iso tayi da hausa kuma,kowa Zama yayi aka nutsu, mu Kuma muna mota me camera ya Mana pics iya Amarya da ango,Muka fito aka Yi mana harda frnds a wajen sannan a waje abokan ango sunfi su goma ga Mata kawayena Sufia ma tana cikin ayari mun gaisa da ita,Fara tafiya mukayi zamu shiga ango ya rike min hannu, Sera da wise suke rike min riga ta baya,Muna zuwa bakin kofa aka canja kidan Amarya da Ango muna tafiya ana fesa Mana snow da golden burzer kanana har sit dinmu na musamman.

Dinner ta Matukar kayatar duk da an zubar da daraja a wajen amma yanda muka tsara anyi abin da iyawa a tsari da birgewa kowa zaice wayewa ce tayi yawa a wajen, anci an Sha an zubar da liki,Ango har daloli ya lika ana ta sawa a tiktok da sauran media, Allah yasa Sabreen tana ta bacci Jamcy ta watso Mata pics da videos Amma tana ta baccin asara ta kashe wayar gaba daya an Sha kwaya, sai da aka gama Dinner angwaye a guess house dinsa aka sauke su komai a gidan Su Khaleel akayi Mami ma tana can duk da ba Wanda ya sani.

Washe gari Sunday Muka Yi Shirin tafiya Kano kauyen mu ai a ranar da yawanmu Mata munfi ashirin Muka dira a kauyen ango ya biya jirgi Muka zo Kano Muka shigo a taxi, angwaye sai da safe zasu zo a jirgi su ma da Iyayen Ango,Sabreen an manta da waya ana ta bacci in ta tashi ma wanka take taci abinci tayi Sallar da Zata iya ta koma bacci,gamu iya karuwan da yawan mu Muka dira Wise tace dole Dagaci yasan mun shigo gari.










AsmaBaffa
08061929616
[7/15, 5:49 AM] +234 912 082 5656: 🌼'YAR AIKIN KARUWAI🌼
LITTAFIN KYAUTA NE



56-60


Official

By
AsmaBaffa



SADAUKARWA NE GA DUKKAN YARAN TSUNTUWA


Page naku ne

Khadija Dandume
Mrs Mukhtar
Maman Afrah Ik
Fairdausi m Sani oum Meenal
Mrs Aminullah
A'eesha
Aisha S Maibankeey
Mom Islam
Khadeeja Sageer(Umee)


Gaisuwa gareki
Aida Maman Tasnim





Anga rida ridan yan Mata ai ni yarinya nake tashi cikinsu,damasu Dj dinmu Muka dira speakers manya manya sun Kai goma Sha biyu kida suke badawa kamar zasu fasa gari,Inna har Yan matan kauyen ta rabawa alawa, dama mu mun Saba ba abinda ya dame mu da Kauye katon dakin da Inna ta gyara ta bamu Muka baje dayan dakin Kuma kayanmu Muka ajiye,sai da Muka tsara komai akan ba shaye shaye duk me Shan wani abu tayi hakuri zuwa kwana daya, Yan matan Kauye kasa zuwa cikinmu suka Yi dama Yara ne gidan Dagaci ne Kawai da Mairo ita Kuma Bata zo ba, komai mun siya na abinci, tun kafin muzo na turawa Bala kudin ya siyo ya Kai gidan Inna,Wani abin Kuma da abinmu Muka zo,amma Muna zuwa Inna da matar Jangudo an dafa Mana shinkafa da miyar,salat Kawai Muka yanka Muka ci Muka barta ga lemukan biki Muna ta sha,akwai abincin Kuma da Muka bayar a cikin birnin Kano za ayi Mana fried rice sai waina da miya,alala,da tuwon shinkafa miyar Agushi har na angwaye su fried rice ce da pepper chicken sai waina da miya, har fura mun bada ayi ta Yan gayu munyi order duk kudin Nawwar ne Wanda ko waya bamu yi sai da dalili,Yara sun zo gidan Inna sun tsaya Mana a Kai suna kallo sabo da Muna zuwa duk kana nan Kaya Muka saka a jikinmu ko wacce sura a bankade wani yaro ne zai Kai 13yrs ya tsurawa Wise Ido sanye da half vest da dan guntun wando gashin nan yaji gyara gata itama fara Kuma ta Kara da Mai tayi Kal Kal,wise ta kalli yaron ta Mika Hannu wuf ta kamo shi tace Dan ubanka zo na baka nono ka sha,ihu ya saka zaiyi kuka yana wutsil wutsil tace ai sai ka Sha nono shegen yaro ka tsura min ido,zuwa nayi Ina dariya na kwace shi ya fice da gudu, Star tace gobe fa sai an kawo Mana motoci biyu sabo da zirga zirga,nace karku damu za a kawo ai na fadawa Ango yace Already an kawo motocin ma har Wanda zasu kwaso angwaye daga airport Kun San Yana da mutane a nan, Inna kuwa da makwafta suna ta Shirin abincin da zasu bawa Yan Kauye mutan kauyen, Bluetooth speaker muka kunna a gidan muna ta rawa,sai dare bayan munyi sallar Isha nace wai Mandula baza ta zo bane,kin manta a cikin Kano fa gidan kawarta ta zauna itace zata taho da abincin idan an hada,sai Kuma me Make up da zata taho da ita,nace ai sai ku fada min yanzu ita za a kaiwa mota? Sera tace ae mana nace ai to an huta ma mota daya tayi ko wacce zamuyi amfani da ita? Wise tace yeah ku tashi mu dan zaga garin Mana mu gani tunda gobe ba time,wasu Hijab Muka saka wasu abaya Muka fito kamar mutanen kirki dake da wutar nepa ko Ina haske ana ta hada hada a kauyen mun fito duk inda Muka yi sai kallo harrrrrr samari ana ta cacar baki,wani me tsaurin Ido Sani ya turo yaro wai Ya nuna Yar Zabil tazo,nace inji wa? yace Sani na gidan Sale me Alewa dariya nayi nace sisi baza ki samu ba ubansa ma Alawar Dinya Madi yake siyarwa,Yar Zabil tace kut ni a kauyen nan ai duk sai dai na aike su ta ja tsaki Kai muje,Sera tace Sani guy na taba tsinka Masa Mari tana Dariya.

Gidan Dagaci Muka shiga nace a nan na girma,Dagaci suna tsakar gida suna gulmata na kawo karuwai, sai gamu da yawan mu mun shigo dama tsokana nazo ba gaishe su nazo Yi ba,Dagaci Yana ganinmu ya mike da masifa ku fitar min a gida Kar ku lalata min tarbiyyar iyali ku tafi can gayyar tsiya,Star ce ta kalle shi da hularsa tasa Hannu tayi fatali da hular Dagaci tayi fatali da ita na sa kafa na take hular, tace Kai dalla rufe mana baki,nace tunda ka Mana you must collect nayiwa kirjin Dagaci kwass na rankwashi kirjinsa ,yace kuyi abinda zakuyi shegu tambadaddu sai nasa hukuma ta Kamaku ,Malika ta furta da kuwa ka taro bala'i wallahi da sai na sa an kwace sarautarka karka cika Mana baki muke da masu fada a kasar nan,nace ni da kaina sai nayi maganinsa mark my words,Mairo ce ta mike tace iyyeee anje birni anyi clean an tsinci turanci a kwalta to wallahi ke baki Isa ba ke din banza banzaye karuwai an zo ana mana burg....Mari taji tas tas tas har uku tuni Wise ta Gama da ita,hawaye ta saki da kuka, Star tace kina sake magana wallahi sai mun tara Miki gajiya baki san waye mu ba,ta nuna Dagaci tace Kai Kuma Muna nan zuwa kanka yanzu gidanka Muka zo amma nan gaba zaka ji mu karka manta bama gaggawar daukan fansa, Azzalumi an baka amanar marainiya kaci tunda kaci amanar Rabiah you must see shege, Gwaggo ce ta taso da bala'i Yar Zabil taci kwalarta ta hankadeta ta fada Kan Aunty Amarya tace yanzu biki Muka zo zamu dawo Kun tabo bala'i sai mun hanaka Shan ruwa a garin nan wlh wannan Dagacin sai an kwace zaka ga masifa,na kalli Gwaggo na furta idan Gaji ta dawo kuce ta shirya nace muje dan Allah dama kawoku nayi mu isar da sako,Wise ta dinga foli foli da tukane da kwanika a gidan da kafa,na nuna Dagaci nace dan gyatimarka akan na hanaka local government dina cikin dare kake zuwa gabanka a dage ya kalli samaniya kana rokata na baka hadin Kai shine kuka min sharri kuka bata min suna wallahi Allah sai ya bimin hakkina Kuma sai na ci takashin uwarku Dan me dirkawa uwarka ciki Ina bala'i harda hawaye naci gaba me chemist din da kuka sa ya rubuta Ina da ciki sai Kun karyata kanku na karasa Gaban Gwaggo da Amarya nace sai kun bada sheda a gaban kowa kafin ku bayar a lahira,Aunty Amarya na tugewa dankwali na wullar da shi nace ubanki ne yayi min cikin Yar gidan Ubale me tsire,ubanki Ubale shine ya min cikin? Aunty Amarya ta mike ita ga marar kunya nace wallahi kina magana sai nayi tsirara naci ubanki a nan sai na miki tsirara,komawa tayi baya tayi mukus,Gwaggo ta mike ta cakumoni nace ku barni da ita na dauki Gwaggo dama ba kiba nayi sama da ita na watsota waje Dagaci ya kasa motsi bai taba ganin jaraba irin wannan ba,Mero ta fito tana zagina Sera ta kamata ta dinga jibgarta Kamar ta samu jaka,Gwaggo ta mike ta rukuma kokawa dani ita ga Yar bala'i tana cewa Yar tsuntuwa Yar cikin Shege

Dama munzo da Santana mutane da makwafta an cika ana kallo,Santana ya falfalo Yana ihu ya dora Hannu a ka Yana cewa na shiga Uku za a kashe Mana Yar uwa Yana gyara daurin zaninsa a saman Jallabiya ya kalli Su Wise yace kun tsaya za a kashe Mana Yar uwa ya dakko dutse wani Dan karami Yana yarfe Hannu Yana furta wash nauyi ya jefawa Gwaggo a hankali ya rike hannunsa da sauri Yana fari Yana karairaya ya furta na Shiga Uku zata min illa hannuna wooo, su Wise ne Suka hadarwa Gwaggo Muka lakada Mata duka,wasu Kuma Suka tafi wajen Aunty Amarya ta fada dakinta tana ihu Suka bita ciki Santana yace ko karkashin gado ta shiga ku kamota,Dagaci abin yafi karfinsa yasan shi kanshi Yana magana Karuwan zasu ci ubansa,Santana Yana ta ihu Yana Karuwai in action wlh an taro Barcelona da Madrid Dole a caskale wuuuuuu yau ana batakashi da kyar makwafta Suka kwaci Gwaggo Amma duk da haka zage zage take tana haki,Aunty Amarya suna fitowa ta sawa dakinta key,Dagaci Kansa buya yayi a dakinsa yaga shima zamu iya dukansa, mu kuwa ficewa Muka yi mun Gama kullawa dagaci yanzu kam,Dagaci yace ayi auren mu gani idan Zaki ji dadinsa gobe Kuma iya yina saina rusa auren nan kwafa ya ja ya tafi Yana lallashin matansa,Mero ta fara kuri tace ai sun tafi da su tsaya Mana su gani Ina ma Gaji tana nan yau da sai dai a mutu.

Sai da Muka gama yawonmu sannan Muka koma gida 11pm Muka kwanta bacci, a ranar Mairo ta Kira Gaji ta fada Mata abinda muka Yi musu,ita ga yar masifa tace gobe da wuri zanzo zasu ga inda ake masifa. washe gari tea Muka Sha harda harda kwai aka soya Mana duk kudi Muka bada aka siya, su Inna sun gama tuwon daurin aure da akeyi a kauyen tuwon danyar shinkafa miyar taushe duk an kwashe a Leda an adana a manyan cooler, 11:30am ne daurin auren,sabo da haka 11am angwaye Suka zo,duk munyi wanka ko wacce ta saka sabon kayan data dinka na kece raini Malika ta iya make up itace ke musu tana musu dauri,ni kuwa Amarya tsadajjen leshi na saka white and golden takalmina golden da jakata da mayafina,wata gown aka dinka min fitted amma a tsakiya an yanke rabi anbi wajen da adon abu,ta gaba sai kace riga da skert ne amma ta baya kuma fitted gown ce nayi mugun kyau, dake mulmul nake dai dai dani ga mazaunai manya sai na fito wata Queen,Mandula ce tayi parking da mota a gaban angwaye dake sanye cikin manyan shaddoji abokan ango da Yan uwan Baffa na can maiduguri da shi Kansa Baffan suna cikin hadaddiyar mota Baffa Kamar ya fasa ihu Yana ta kunci dansa zai auri bare marar asali Kuma ga Kauye ma abin ta ko Ina ba kyau, Nawwar da rukunin abokansa sun Kai su ashirin da wani abu harda Auta Nawaf kanin Nawwar, ango ya sha wata farar shadda da babbar riga ta zamani ya coka Yar hula kalar takalminsa farare komai fari,motar ma da aka dakko shi daga airport Fara,irin kyan da ya zuba ba a cewa komai kowa shi yake kallo a wajen,Ni Kam me Make up tana ta tsarani tsaf,Mandula ce ta murzo motar da Nawwar yasa aka Kai Mata a cikin birnin Kano taci wankanta itama cikin wani danyen material peach ta Sha make up light,takalminta me tsini ta fito gasu dama da kibarsu ba rammiya sakamakon supplement na yanzu da Mata ke dannawa cikinsu,Fitowa tayi tare da bude bayan motar komai an shirya shi na musamman take away dinmu ma da aka zuba abincin na daban ne,har lemuka duk an zuba a jakar take away din,su Sera ne Suka fito Suka tayata shigar da kayan ciki,ta Kira Khaleel ya bude bayan motarsa ta zuba musu nasu abincin na angwaye,aka bude mota Daya cikin na Iyayen Ango aka basu nasu da yawa, Suma aka ware nasu aka saka musu a mota sai da Mandula ta sallami kowa Saura na Yan daurin aure mutan kauye za a karasa basu,sun ware nasu Dana bakin su,tana gamawa ta kulle motar ta tako zata wuce Nawwar tace ango tana Murmushi yace sannunki kirjin biki,Auta ne yazo da sauri yace Ina Amaryar Yaya,Nawwar yace ga kawarta nan bita ta kaika wajenta,Mandula ta rike hannun Auta,tace ya sunanka yace shi Auta Kawai ake fada masa tace to,ya zama dan saurayi suka shiga gidan da shi, Kawai yaga Yan Mata iya Yan manta ya rasa wace Amaryar ma, an Gama kwalliya dauri ake min Yana ganina yace wannan ce ma amaryar naga tafi kowa,gabana ya tsaya Ina ganinsa na gane kanin ango ne domin sunyi kama,yace Amarya nace Auta ne naji ai Mami tana zancen Autanta yace ai duk tafi so na,nayi dariya yace yunwa nake ji Aunty,nace a bashi abinci ya zabi waina da miya yaci yasha lemo da ruwa yaci ya koshi yace anjima zanci fried rice nace to Allah ya kaimu,masallaci ana shirye shiryen daurin aure Dagaci yazo aka nuna Masa uban Ango da Ango Kansa

Bakin ciki ya kusa kashe shi yace da gaske masu kudi ne ai larabawa ne cab ai sai yaje wajen Baffa ya Mika Masa hannu Suka gaisa yace bawan Allah mutum me Kamala irinka ka yarda danka ya auri Yar tsuntuwa tsintarta fa akayi,Baffa a ransa yace wallahi nima dole ce ta sa,amma a fili sai yace ae ai mun sani ita Yar tsuntuwa ba mutum bace? Iyaye ne suka haife ta sabo da Haka yaro Yana so Allah ya nufa wa ya Isa ya ja da ikon Allah,jikin Dagaci yayi sanyi matuka yace Babu riba Kawai na koma wajen malamina yafi min a daura kawai sabo da bacin rai zamewa yayi bazai ji an daura a gabansa ba ya koma gida,Liman sai Neman Dagaci yake a matsayinsa na Babba a gari Kuma Wanda ya rike yarinya amma an neme shi an rasa ashe dan kar ma aje nemansa gona ya tafi ya samu bishiya yayi shimfida ya kwanta Yana bacci abinsa.

Mutanen garin sunyi Kara sun cika kamar kasa cikar da ba'a taba Yi ba a garin a daurin auren wata sai akan Yar tsuntuwa kaf garin nafi kowa tara dan Adam,wasu ma kallo ya kawo su,dubban jama'a ne Suka sheda daurin Auren Rabiah ta daina amfani da sunan Dagaci a matsayin Uba tuni ta koma Rabiah Muhammad Nawwar tunda bata da kowa a duniya ta zabi Muhammad Nawwar,Jin sunan da Liman ya kira ya sa Nawwar Jin dadi harda sunansa a sunanta Rabiah Muhammad Nawwar,shi Kuma Nawwar Ibrahim, Baffa shine waliyyin Amarya,Nawwar ya karbi Aurensa yanda yace babu Kara,ga masu uban Dj sun shirya tsaf,Sadakina dubu dari biyu,Jangudo da yaransa su Suka dinga raba goro a wajen da alawa sannan suka fitar musu da abinci tuwon da su Inna sukayi,Fitowa mukayi gaba daya kallo ya dawo kanmu,Nawwar ya tsaya a gabana nace to an daura? ya furta uhm,Nan aka Fara zuba ruwan pics ta ko Ina wayoyi ne ke tashi,ana haka me Dj suka saki ganga kida Kamar zai fasa kunnen mutane, Wise ce ta fara bude rawa a gaban dattijai Yan daurin aure Basu watse ba ta fara takawa kowa ita yake kallo,Abokan ango an baza Ido ana kallo wani Sabeer a cikinsu yace wannan tsagera ce ta kirki,Murmushi muka Yi mun San bai ga komai ba,Kafin mu rufe baki Malika taje tana mata liki farrrrrrrr da Yan dari dari tana gamawa tabi sahu tana cashewa,dariya ta Kama angwaye dan Kuwa Malika gwana ce a rawa yanda ta duka ta tana wargaza mazaunai tab,Wasu su Sera Suma suka shige suna zuba liki suna rawa,Angwaye ai sai Suka gyara tsaiwa Suka ce sun fasa tafiya yanzu Suka fito da take away dinsu,fararen kujerun da Muka aro haya aka jera musu da yawa Suka zauna a gaba sauran Yan kallo Mata da maza suna baya mu Kuwa iya kawaye Muna ciki,Mc yace Amarya kadai ake son gani a fili ai Nawwar yasan ya Zama dole nayi rawar nan ya sani ma shi yasa Bai ce ma komai ba.

Duk fili suka bani na shiga aka canja min kida tun Ina Yi kadan kida Yana ratsani na karbi speaker nace Ango ka yafe min Zan tsokani shari'a da Speaker a hannu nake rawar Ina Jin kunya Wai a haka amma yanda nake Cashewa,Auta kanin Nawwar ya shigo Yana min liki hannayensa na rike da hannayena biyu Muna facing juna a haka muna rawa kasa ai Kuwa kawaye Suka rufe ni da ruwan Naira Dj yana caskar kudi,suna fita Angwaye Suka shigo Kai an zubar da Naira Kan uba,gajiya nayi na fita sabo da make up dina,Nawwar ko daya bai ma tashi ba tukun yace zaiyi nasa, Kawayene Suka shiga su Uku Malika da Wise tare da Manduwa yau ana Shan kallo Yan kauyen sai ihu suke ana kallon iya shege karara a haka ma munyi da sauki,suna fita aka Kira Ango da Amarya Muka mike muka shiga sabo da iyayin Nawwar Wai a filin rawar za a sa Masa kujera kamar wani sarki ya zauna a tsakiyar wajen Yana Shan ruwan roba,ni kuwa rawata na dinga yin cin koshi ka rantse ba Amaryar bace,mikewa yayi ya dinga zuba min ruwan Yan dubu dubu, ana ta dauka a wayayi,Sera ce tazo ta min rada kuyi kiss zamu dauka a waya nace bazai yarda ba,sai kace ba mace ba ai karuwancin Zaki tuna,dariya nayi Ina dan takawa yana min liki,na dora hannuna daya a kafadarsa na maida dayan ma a kafadar na dora yace ta ya Zan Miki likin Wai bakya Jin kunyar mutane ne fa abokaina zasu ce baki da tarbiyya nace sai yanzu suka sani kiss zamuyi dauka za ayi zai zame nace Allah kana guduwa sai na kunyataka a wajen nan ka sanni, ai Kai kace kaji ka gani ka aureni, mu bama Jin magana ka bani hadin kai,yace to kiyi sauri na gaji,Yatsa na dagawa su saira su dauka haushina yaji Yana ta fada bai Dace ba wannan a musulunci Wanda yanzu ya Zama ruwan dare mutane da yaran masu kudi gani suke birgewa ce wayewa ce,a hankali nace kaine fa zaka min Ido ya zaro tare da furta na shiga Uku nidai,please karka kunyata ni Zan kunyataka wallahi, Ido ya rufe aka canja slow music a hankali na dora bakina a saman nasa ya min kiss a nutse ana dauka na rungume shi sai aka dauki tafi da ihu yeeeeeeee Yan kauyen Suka Fara cewa yeee ya tsotsi bakinta alquran,billahillazi bakinta ya lasa kunga sun rungume da gani sun Saba tun a waje,Yan matan kauyen shewa Suka dauka yau Muna ganin bariki yehoho ahayye chasss...,Khaleel bai taba zaton abokinsa ya fetse haka ba sai yau dariya ya dinga yi, sai da Muka gama likawa juna kudi Yana min Ina Masa sannan Muka fita,Khaleel yace Lover boy,Nawwar ya hade rai tare da Zama,abokai su abin ya birge su sosai dama duk gasu Yan gayu yaran masu kudi,Wise bata gajiya sake shiga tayi tana yiwa kanta da kanta liki tana cashewa,Autan su Nawwar yaga duwawuka sai tsalle suke yace wow ya radawa Nawwar irin wannan Zan Aura nima Yaya idan na girma da wuri za a min aure,Nawwar yayi dariya a ransa a fili yace sai kaci ubanka wlh ni ban San ma ya akayi ka biyo mu ba,Mami ce tace nazo yaci gaba da cewa Auren Kauye za a min da wuri ni wallahi ba sai na girma ba,na daina kula Yan class dinmu wajen Aunty Rabiah zanzo ta hadani da kawarta,Nawwar yace sai na zaneka bari mu koma gida tunda baka kunya,Shuru yayi bai sai sake magana amma ya zurawa Mata ido.

A wajen muma muke cin take away dinmu har Yan Kauye Suma sun samu da yawa sun samu, tare zamu tarkata da angwaye mu koma can Anambra, duk munfi yin rawar wakokin Yan kudu su Muka iya Kamar kannen Naira merly, 2pm aka tafi Sallah wanka Muka sake tare da canja Kaya wannan karon ba make up Kawai dauri mukayi kowa tayi wacce zata iya, muka fito na sha shadda dark purple nayi kyau, su Kuma ankon Atamfa Suka saka

5 Comments On YAR AIKIN KARUWAI
avatar
asmau-7

1 year ago

Reply

T

avatar
sadiya-9

1 year ago

Reply

Wonderful and nice novel

avatar
diaabdourahamane

1 year ago

Reply

Nice novel

avatar
bashar

1 year ago

Reply

Don Allah ina cikon labarin nan?

avatar
taskar

1 year ago

Reply

Replying to bashar

Dole fa sai dai ku siya a cigaban labarin a wurin marubuciyar, ga nambarta 08061929616

Please Login or Register in order to submit comment