Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kasa,dining ya nufa nayi serving nasa yaci yaji wani shegen dadi ai sai da yaci da yawa ya koshi yana Shan lemon dana hada, let's go ya furta Yana Shan ruwa tare da kuskure bakinsa da ruwa ya hadiye,na rataya jakata babu ko dankwali sai hular gashina babu mayafi a gidan haka Muka tafi ko a jikina.

Gaban mota na bude na shiga shi Kuma ya zauna a mazaunin driver Yana tashin motar na kunna Mana kida ya kalleni yace malamar kida horn yayi me gadi ya bude gate muka fice zuwa katafariyar shipping mall.

Parking yayi ya fito Nima na bude na fito Muka jera da jallabiyata yace Dora hular rigar taki a kanki yanda yace nayi na saka hannuna cikin nasa Muka shiga a haka Yana ta so ya kwace hannunsa amma naki yarda a hankali yace ba kyau fa, kukan shagwaba na fara masa, yace zaki tara min jama'a fa naji muje,Shuru nayi muka tafi a haka.

Dogayen rigunan ya siyamin ready-made masu tsadar gaske wasu Yan Egyft,wasu Turkish,wasu Yan Saudi sai namu irin materials kala kala da ake musu digayen riguna masu kyau buba gasu nan dai,takalma da jakankuna ya siya min iri iri da mayafai irin na Yan Mata inner wears gasu nan da yawa iri iri,kayan bacci sai kayan makeup Suma na zaba,Muka koma layin sarka da Yan kunne,ribons etc,ya kashe kudade sosai muka kwaso kayan ya kwaso wasu nima na kwaso wasu Muna zubawa a bayan mota sai ga abokinsa Khaleel,yayi mamakin ganinsa da wata da bai sani ba amma ya share ya karaso inda muke

Khaleel sallama yayi Muka amsa ya kalleni ya kalli abokinsa yace Nawwar daga Ina haka? Nawwar gabansa ya Fadi baya so kowa ya sani ya ganshi tare da ni,Ni dai nace da Khaleel Ina yini ya amsa Yana min wani kallo, Kawai yaci gaba da magana da abokinsa suna hirar Office,gajiya nayi na dafa kafadar Nawwar nace na gaji mu tafi gida,wani harara ya zabbaga min na tona Masa asiri Wai,Khaleel yace akwai magana kuje kawai yayi gaba,muma mota Muka shiga Yana min fada wai sai kin tona min asiri a ko ina,nace nifa kaga karka dameni in ka gaji ka rabu dani na koma inda na fito baza ka takura min ba,shut up baza a barki ki tafi ba din,Shuru nayi naji tsoro baki na turo masa tare da dora kaina a kafadarsa yace daga min jiki bana so babu kyau fa Kuma ke musulma ce Allah yana kallonki, to sai hakuri ka hadu da balagaggiya,sabo da ya gaji yace nafi karfinsa ya barni na tafi nace na tara ruwa dan Allah yau ka dan nausa cikin ae...na kalleshi na daga Masa gira, a ransa yace na shiga Uku da kaddararriya yarinya ta isheni da Iskanci a fili kuwa ko kulani baiyi ba,na sake cewa dai dai da Kai ce ni Allah Harija ce ni zaka ji dadi,Ina da Mata fa yarinya nace ni Ina ruwana da matarka mu babu abinda ya damemu,a ransa yace ni ya zanyi da ita karfa jarabarta tasa taje wajen wani ya biya Mata bukata to yau dole na kawo securities gidan nan suyi gadinta.

Ina jinsa Yana waya da securities yace Yana son mutum biyar, Muna komawa gida ya tayani Muka kwashe kayan tas har dakina na zube naje nayi Alwala yaga na dakko wani hijab dan madaidaici na saka,yace dama kina da hijab Amma Kika ce ba komai da zaki sa Muka fita a Haka? Nace na Sallah ne duk inda naje idan zani aiki da shi nake tafiya sabo da Sallah,mamaki ya kashe shi yace kina Sallah? Nace sosai ai Sallah bata wuceni,yace to ba a karba da ana karba da baza ki lalace haka ba,me yasa Kika lalace da yawa haka? kallonsa nayi nace burina nane tare da tada sallah,na tafi sai da safe ya furta abinsa ya wuce.

Securities ya kawo gidan yace Kar a sake a barni na leka ko bakin gate Suka ce an gama ya tafi,suna ta tsaron gida ai Kuwa yau na ayyana zanje can gidanmu na sanarwa Kawata Seraline Ina gidan saurayina dan Ni tuni ma na sa Masa suna saurayina,na saka kananan kayana da nazo dasu jiya na fito Zan tafi naga sojoji a gidan mamaki Ina takowa tsakar gida Suka daka min uwar tsawa,na kalle su sojoji ne ba raini salin alin ban sake gigin lekowa ba,haushi da Takaici ya kamani.

Dagaci Yana zaune suna hira da Aunty Amarya Suka sako zancen Rabi,Dagaci yace shegiya tana can karki fadawa kowa bakinki kanin kafarki tunda na koreta da wata shida na kasa hakura sabo da karma ta hadu dana gari ko me kudi sai na koma gidan malamina Malam ya'u nace ya sake cillata Kar tazo garin nan ko da wasa sai ya bani shawara ko a sa ta fada duniya lallai ta koma bariki duk inda taje kawai ta zama yar duniya karuwa zata je a sa Mata son karuwanci lallai ta fada cikinsa tsundum ai Kuwa nan take na yarda ba karamin kudi na kashe ba kafin ayi aikin,ni Sam bana kauna Yarinyar nan ta nuna ta Sanni ma,Yar tsuntuwa yo ai Yar shege ce gwara ma daka Kara cilla shegiya bariki cewar Amarya, Dagaci Yana dariya Yana Jin dadi,Shi a duniya haka yake da hassada a garin kowa ya sanshi,Hassada ce tayi Masa yawa yafiso Kawai ace daga shi sai Yaransa sune zasu ci gaba a rayuwa kaf garin haka yake wa mutane hassada Indai Allah ya daukaka ka baya kauna,idan talaka ne Wanda yake cikin wahala to Inshaallah shine abokinsa,Amma da ka samu kudi to ya daina kulaka wannan har yaransa da matansa haka suke a kauyen kowa taka tsantsan yake dasu.







AsmaBaffa
[7/15, 5:49 AM] +234 912 082 5656: 🌼'YAR AIKIN KARUWAI🌼

LITTAFIN KYAUTA NE



26-30



SADAUKARWA NE GA DUK YARAN TSUNTUWA



Page naku ne

Bellomaryam581
Maryammkhalid2
Dr Suhailat Hussein Armai
Mrs Idris
Ummy M
Oumm Yasmin
Hafsa Abdullahi
Aesha
Hauwa Kasim
Momyy Hibbah
Hadizahamidu369gmail.com.


Masu Sharhi Ina godiya ko da wasu zasu Yi suga banyi reply ba suyi min afwa ban gani bane ban kula ba.





Washe gari bayan na gama gyara ko Ina na gidan na karya yau bai zo ba har Yamma sai magriba Ina ta kallon film yinin ranar gaba daya, da Magriba ya shigo bayan ya dawo daga masallaci,Ina ganinsa na fashe da kuka nace Allah ni tafiya zanyi gida na gaji da nan bana so ka ajiyeni a prison ni gidanmu Zan tafi Ina can cikin nishadi ka ajiyeni a nan ni bazan iya ba na nuna doguwar rigar da nasa me tsada cikin kayan da ya siya min tayi min mugun kyau nace kalli Riga har kasa gashi ni rigar ta dameni bana so,sai da na gama Ina tsaye a gabansa yace wannan aikin da kike ikirari kina fita Wai Dan me kike Yi? nace kudi yace to biyanki zanyi ba kyauta nace ki zauna ba,Ina goge hawayena na koma na zauna tare da turo baki gaba,kudi ya zaro dala dari dari guda uku ya Mika min Yace gashi,kallonsa nayi nace wata fa bai cika ba kace Kuma sai wata yace ae baki nayi ki Kara hakuri ya furta tare da Zama,mikewa nayi da murna na kasa magana ma nace wannan Kawai na roko ne akan na zauna Kuma idan wata yayi zaka bani albashi? Yace ae,nace yau ana burar....na dura ashar nace la'ilahaillahu Wai Kai to me kake amfana dani,baka taba ko nono na Kawai ka ajiyeni ka dinga biyana kudi every time money ehhhhheheh nayi wata mahaukaciyar dariya Ina tafa hannaye nace bafa ka amfanuwa da ni a Zamanin nan,na nuna kaina nace ni Kuma banza Rabi wai ni ka bawa Elizabeth, nace yehoho kai Nawwar zan iya maka bauta,Kai mutumin kirki ne Kawai gani ka bautar dani kayi abinda kaga dama dani,ko wuta ka fada Zan iya binka nima na wulla ciki,ah'ah ikon Allah,kallona yakeyi Yana ta dariya yanda na haukace akan kudi,gabansa na durkusa nace Alhaji dama dazu ban gaisheka ba Ina yini ya iyalin? ya kwashe da dariyar da ban taba ganin yayita ba,nace Dan Allah kunyarka nake ji kana ta min kyauta baka tabani bana Jin dadi wlh uhm Sana'a nake uhm haba dan Allah yanzu ko Yan nono baza ka taba ba,yace ae nace dan Allah da girmansu wlh Allah ya bani akwai auki hiiim suke,yace na gode,mikewa nayi nace shike nan Allah yasa dai matarka tana baka nata,a ransa yace ko ta bani ma Yan karamaye ne ko saurararsu banyi a fili yace Ina samun halak dina nace ai Kuwa ta kyauta amma idan ta maka hauka Kawai ka fada min naje naci babbar burar....,Wai karuwai ma irinmu muke badawa bare mace da mijinta mene amfaninta idan ba a ragargajeta ba shi yasa fa nayi hips kugu na ya bude to yau da gobe taki Wasa ana ta iban harka,yace Wai ke in tambayeki,nace Ina jinka na nutsu sosai yace bakya Jin kunyata? Kai na daga masa nace ae bana ji,sabo da me? ta gudu ai ni bani da kunya na gantalar a titi bana Jin kunyar uban kowa yau da gobe taki wasa,numfashi ya ja yace to idan nazo ki dinga kokarin Adana kalamanki na banza bana so ki daina Yi a gabana bana so tunda kince duk abinda nace kiyi zakiyi bana son kalaman banza,nace to zanyi Inshaallah na daina, better ya furta nace to mu koma karatu Mana,yace me Kika sani a addini da kina da ilimin addini ai da baki abinda kike ba sabo da a wani Hadisi Manzon Allah (SAW) yan acewa

kullu ummati yadkulunar jannata....kafin ya rufe baki na karbe Hadisin naci gaba da karanta Masa Ina fassarawa nace wato ka gane annabi (SAW) yace dukkan alummata zasu shiga aljana,sai yace illa man aba sai dai Wanda yaki kaga irin mu kenan munki mu tunda Muna karuwanci to Allah ya shirye mu,sai sahabbai Suka ce kalu ya rasulillahi,Suka ce ya ma'aikin Allah wa yam aba?waye zai ki? Sai ya basu amsa Wa man asani Wanda ya Saba mini faqat aba hakika yaki,Allah ya shirye mu na furta yace ameen,nace na kusa fa sauka nan daka ganni da ilimina ko a karatun Qur'ani baza ka kureni ba sannan Ina da littafa da dama a kaina sabo da Ina zuwa Islamiyya a kauye Kuma na dage a lokacin.

Wato kin sani kike take sani nace mu bar zancen kaga Ina so na sanarwa Kawata Seraline ta San Ina nan Kar tazo hankalinta ya tashi bata ganni ba har kwana biyu yace ki kirata a waya Mana ga wayarki nan, wayata na jawo na Kira Seraline tana dagawa tace Ina ta kiranki wayarki a kashe Ina Kika shiga duk mun damu su Wise sai gwada wayarki ake bata shiga? nace sorry dama Kira nayi na fada Miki Ina gidan Saurayin nan nawa da ya bani daloli to shine yace na zauna a gidan zai biyani na Dan tayashi kwana na wani lokaci shine nace bari na fada Miki ki fadawa mutanenmu kafin na dawo, Seraline ta Yi dariya tace kice kin Zama Yar Hannu nace ae Kawai Muka danyi surutun mu na Yan duniya sannan na kashe Wayar, nace ko Watarana baza kayi sex dani ba? ganin na dameshi sai yace sai Watarana Kawai Sanda naga dama zan iya ki kwantar da hankalinki ko yaushe Zan iya,ya tashi zai fita nace Ina zakaje daga shigowa zaka fita ni baza ka bani lokacina ba wai ni Allah Zan gudu gida na koma inda na fito,karamin Tsaki ya ja ya dawo ya zauna na kamo Mana Nigeria film Muna kaiwa suna saka sabo Muka ci gaba da kalla tare Muna sharhi a kai,cikin Raina Kuwa tunani nake Yi yace ko yaushe zai iya sex dani gashi ni ba taba Yi nayi ba,na dai Saba da maza arna da Yan daudu zamu rungume juna Babu batun mace ko Namiji har zama muke a cinyar Namiji Kamar mace Yar uwarka,a raina nace idan yazo ko yaushe banyi gyaran jiki bafa yazo ya jini ba Dadi ai dole na Kira Sera ya Zama idan bani ya kusanta ba bazai ji Dadi ba tunda dai nasa ran Zan Fara Ashawo work idan ma zai na biyana ko yaushe ai ba matsala sai na dinga Yi da shi Kawai mutum daya,Ina ta sake sake a raina har ya Fara Jin bacci a nan yayi Sallah ya mike yace matata tana jirana,nace to Goodnight,rakoshi nayi har mota securities suna nan suna gadina,da kaina na bude masa motar ya Shige mota na rufe Masa glass ya sauke yace sai gobe nace Allah ya kaika lafiya ka kula da tuki na juya Ina cewa banda ganganci matarka zaka yiwa asara ni ba ruwana,Murmushi yayi kawai ya murza Kan motarsa ya bar gidan.

Ina komawa na Kira Seraline na fayyace Mata komai dake bama boyewa juna sirri,Sera tace to ai Kuwa zai iya zuwa bakatatan ya nemeki Kuma Kinga dai yanda muke kashewa Gomnatinmu kudi Kinga yanda muke Shan gyara uban kowa ya dandanaka bai iya barinka sai ya dawo,kina da kudi ki kawo a fara kashe dubu dari biyu haka a tsumaki karuwai basa Wasa da gyara Kai kusan kudinmu a gyaran jiki ke tafiya da haka muke samun riba jari muke zubawa ki kawo kudi a zubawa jikinki jari,in kana da kyau ka Kara da wanka karki kalli kina da kyau Wai kice baza ki Kara da wanka ba,nace ai shine na gani nima gobe Zan rokeshi ya barni nazo sai muje Sera ta kwashe da dariya naji dariyar su Wise ma a Wayar hahaha Sera tace kin gammu dukanmu yau Muna gida Hira akeyi suna jinki munce kin dakkowa kanki masifa,Star ce ta kwace Wayar tace Yar wanke wanken karuwai haka Kika jefa kanki a masifa sai kace mijinki zai wani hanaki fita baki da yanci ma wato sai ma ya baki izini zaki fito mene amfanin barikin da Kika shigo daga farawa shike nan sai ki tsaya kina bin Maganar katon banza,nace Kinga star ba katon banza bane karki sake zagar min saurayi,harkarki daban tawa daban kiyi naki inyi tawa,abinda naga dama shi zanyi ko ke kike daukan nauyina,hehehe Suka furta gaba dayansu lallai namijin bariki zaki biyewa zai kaiki ya baro,nace ae naji ke Sera sai nazo tace to suna ta min dariya Ina jinsu...

Duk da haka zugar tasu ta danyi tasiri a zuciyata amma na danne washe gari da Yamma yazo 5pm,na shirya cikin wata doguwar rigar nayi rolling da mayafinta na fito a gabansa na durkusa nace dan Allah ka barni naje na dawo wlh bazan dade ba wajen Sera zanje matsala ce ta taso a dakin da Muka Kama karya na sharara Masa,yace hour nawa Zan baki? Nace 3hrs ma yace karki wuce 9pm Baki dawo ba nace to Ina murna na fita ya kwanta Yana jirana,Ina fita na shiga taxi,a ciki na cire Abayata kana nan kayana da nazo dasu gidan Suka bayyana na saka hular gashi na Kar ma su Sera su ganni da manyan Kaya suyi min Dariya,a cikin jaka na saka su,suka ganni nazo Sera tace ya barki kenan nace ae tare da kwanciya a saman gadon nace tsakani da Allah na gaji da mutumin nan Sera,ya takurani ya hanani lekawa ko kofar gida gashi dole sai na sa manyan Kaya na rufe jikina,Kinga takura komai nayi zai ce ba kyau,musulunci kaza kaza gashi mugun tsoronsa nake ji Yana da wani kwarjini kyansa kadai ya Isa ya rudaka gashi baya dariya sosai inda kisan ubana haka ya takura min na karashe da Tsaki,Sera ta dinga dariya tace ke Kika ga Zaki iya ta jawo sigarinta ta kunna Mata wuta,Ina mita nace gida ba nishadi ba kida ba shanawa Ina cikin wahala ai wlh kwana nan na kusa gudowa barikina bazan iya ba,Sera tace maybe sonki fa yake dama kina son aure sai kiyi abinki,nace wa ai da ne nace Ina son aure yanzu Kam rabani da wahala bazan iya ba aure baya tsarina a dinga takura min bada ni ba amma daga ganin mutumin zai iya love,zabura nayi nace tashi mu tafi 3hours ya bani idan na wuce ba mutunci,Sera dariya Kamar ta kasheta tace maganinki kenan yanzu gwara ki hada kanki zo mu tafi gidan Hajiya Mazarkwaila,dariyar sunan ya kamani nace hala itama tsohuwar karuwa ce domin daga Jin sunan bana kirki bane,Sera tace ai muguwar tsohuwar karuwa ce har yanzu ma Kuma yanzu ta koma kawalci manyan masu kudi take kaiwa Mata gata uwar karuwai kayan maye ba Wanda bata siyarwa ta tara arziki da bariki attajira ce ta gaske Kuma tana gyaran jiki na Mata gyaran skin gyaran Gomnati in and out amma akwai kashe kudi amma fa ba karya da kayan kasar waje take amfani idan Namiji ya dandanaki wlh ko a gaban uwarsa in zai ganki sai hankalinsa ya tashi bai iya kusantar wata yaji nutsuwa sai ke,nace iceko ba shirka bace? Tsaki taja tace ance Miki maganin kasar waje na gargajiya kina shirme,kin San karuwai muma ba tsafin da bamayi idan Muka hadu da me kudin gaske wlh in Muka Masa wani tsafin shi da iyalinsa har abada kullum Yana bariki wajenmu, jira nake Allah ya hadani da wani gagararren me kudin uwarsa ma Sai ya juya Mata baya,baki na saki nace nidai ba ruwana wallahi bazan je ko gun Malam ba bare shirka Allah ka tsareni,Sera tace ameen karki isheni Karuwar banza Karuwar wofi,dariya nayi nace karuwai dai Sera har yau dadin sex din nan ban ji ba ban taba yi ba Ina ta ikararin karuwanci amma Abu ya gagareni,ganin dama Kika Yi kin biyewa Dan iskan farkanki Muna tafiya muna hira Muka shiga napep nace Sera nifa yanzu kin San me? tace Ina jinki nace sha'awa ce ta dameni kullum da ita nake kwana nake tashi,to kin cuci kanki kin zauna a gidan dan banza babu me dan saitaki ba dole ba Kuma kina bariki kullum dare da rana a maganganun batsa muke dole a dinga taso Miki da sha'awa Kar aje ayi gyaran jiki Kuma abin yayi Miki yawa Kawai a hakura da gyaran a siya Miki na infection da Wanda zai dai dan dawwamar Miki da niima Kar kizo ki afkawa maza,dariya nayi nace ai Kuwa da ce Masa zanyi idan yasan baya son sex to ya dinga saka wandon karfe dama naji Yana cewa kwanan nan da wandon karfe zai dinga zuwa gidan,dariya mukayi har Muka je gidan Mazarkwaila,gidane na gagara gidanta abin kallo ne Muka shiga tana Palo ita kadai tana kallo kana ganinta ba sai an fada maka ba kasan shedan ya gama fitsare Mata Kai muguwar Yar duniya ce.

Da murna da karramawa ta karbe mu me aiki ta kawo Mana Kayan ci da sha Muka ci Kuwa Muka Sha sannan Sera ta mata bayani tace amma yanzu yace bazai Yi sex da ita ba sai Watarana Kuma tana cikin wani hali Kar a bata Wanda zata gaza hakuri, Mazarkwaila tace karki sake Kiran kanki da karuwa Kuwa Indai hakane ke Kuwa me ya kaiki wahalar da kanki haka ki zage kiji dadi mene a duniyar dole sai ana hutawa Kinga Ina da Wanda zasu iya baki million biyar ma lokaci guda idan sun sameki gaki Kalar da suke nema ce ni kin San ba kowa nake kaiwa Mata ba sai ka cika me kudi,ke Kuma irinki suke nema akwai arziki a tare dake za a samu alheri dake sosai,nace nidai a'a tsoronsa nake ji ba ruwana Kawai ki bani magani mu tafi yace idan na wuce 3hours akwai matsala Kinga gashi har lokaci ya kusa ni dai yau na shiga Uku wayyo Allah na 8:30pm yanzu kafin naje gida ma 9 ta wuce,Sera da Mazarkwaila Suka bude baki ta mike ta kawo min magungunan infection masu mugun kyau da tsada, ta bani kayan gyaran skin ta gwada min yanda Zan dinga Yi kafin na shiga wanka Dana shafawa, ta bani wasu kayan kamshi tace Kinga wannan karki Wasa da su duk inda kika je sai kin bar kamshi a wajen bazai so ya dinga nisa dake ba sabo da kamshin da kike yi na musamman ne daga Dubai nazo da su,na karba nayi godiya na biya dubu dari da ashirin a iya Yan kayan kala kadan,a gidan na bar Sera na shiga taxi da sauri Ina shiga na maida abayata nayi rolling Kamar yanda na bar gida,9:40pm na shiga gidan da gudu na fada Palo Ina haki,Yana Palo sai da ya tsorata,sake fita nayi na dawo na Masa sallama ya amsa sannan na shiga ransa a bace yace Ina Kika zauna? Ina haki nace bamu gama da wuri bane Kuma mun hadu munyi hira kayi hakuri na furta tare da turo Dan bakina gaba Ina Kunkuni nace ni duk anbi an takura min sai kace babana,yace magana kike? Nace no Ina satar kallonsa na mike na shiga bedroom na boye tarkacena sannan na dawo palo,kinci abinci? ya tambaya nace ae,a ina? a can mana Seraline ce ta bani,baza ki girki ba kenan? Yunwa yake ji bazai iya cewa na dafa Masa ba,nace na koshi ni sai dai in dafa maka naka,me zaki dafa min? abinci mana ba kana cin komai ba sai nayi tunani na dafa, alright tunana naji, tunani na Shiga yi daga baya nace yawwa na dafa maka sakwara da miyar kwai Muna da garin sakwara na gani kaga ba wahalar daka da Zan sha,yace ai girkin ya Miki wahala da yawa da dare haka, tab ai ni bana Jin wahalar girki da aiki ma na Saba mufa ba Hutu Muka zo duniya ba bare ma Kaine mene bazan maka ba sai in baka so, Murmushi yayi kadan yace to zanci Ina so kiyi a nutse a nan gidan Zan kwana yau,yeeeeee na furta Ina ihun murna nace shi yasa naga securities sun tafi,cewa zaka Yi yau kwananki ne Miracle,ka Fara raba Mana kwana kenan,Fuska ya bata,nace sorry wlh yau Ina farin ciki,mamaki yayi yanda yaga Ina ta murna Kamar Zan tashi sama,matarsa Kuwa tab banza wofi ne shi a wajenta.

Kitchen na Shiga na tsara miyar kwai taji nama sannan na tuka sakwarata lafiyayya,na gama na gyara kitchen din na kawo dining yace kawo min nan ban iya tashi na kawo gabansa na jera nayi serving nasa na zuba Masa juice sannan nace Ina zuwa naje na zubawa Ilu me gadi na fito yace Ina zakije? Nace Ilu Zan kaiwa nasa yace oh har shi kike bawa? Nace ae ai tunda na Fara girki Ina kaiwa Ilu,yace da kayanki fitsararru kike zuwa Gaban Ilu ki Kai Masa abinci? nace ah mene a ciki Allah na tuba ko da bra da pant Zan iya zage garin nan kaf bare zuwa wani Gaban Ilu da damammun Kaya Sanda ka dakkoni farko baka ga a yanda ka dakkoni bane to ai wannan shigar mutunci nayi,yace jeki dan Allah karki sa na mareki,gaskiya na fada maka ni dai na fice na kaiwa Ilu na dawo,yace daga yau ko compound Zaki leka sai da mayafi,takurar da yake min ta min yawa abin ya isheni Kawai nace to idona ya ciko da hawaye akan Kawai ance na saka mayafi,yace kuka zakiyi? Kaina na sadda kasa Ina girgiza kaina Ina bude baki da Niyyar cewa a'a sai kuka yazo min na Fara shesheka Ina kuka sosai nace k...ka...k..ka..sh..shiga...hakkina...k...ka...takura..min...bana..ba..bana...bana...jin..dadi...ba..bana son..wannan rayuwar taka....ka...kyaleni na tafi....kallona yayi yace baki San ciwon kanki ba Rabiah ki daina karuwanci ki daina ba kyau,mace kyakyawa kamarki musulma mene abin so a bariki,Ina amfanin irin wannan rayuwar kiyi aure ki bautawa Allah ki samu lada ki huta mijinki zai Miki komai,sex idan kunyi lada Zaki samu mene a wannan rayuwa,nace ni bana son aure bazan yi ba karuwanci zanyi ni karuwa ce bani da asali gadon Iyayena zanyi,Tsaki yaja yace okay fine Zan saki a school

5 Comments On YAR AIKIN KARUWAI
avatar
asmau-7

1 year ago

Reply

T

avatar
sadiya-9

1 year ago

Reply

Wonderful and nice novel

avatar
diaabdourahamane

1 year ago

Reply

Nice novel

avatar
bashar

1 year ago

Reply

Don Allah ina cikon labarin nan?

avatar
taskar

1 year ago

Reply

Replying to bashar

Dole fa sai dai ku siya a cigaban labarin a wurin marubuciyar, ga nambarta 08061929616

Please Login or Register in order to submit comment