Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da wani uffan ,itace ma dataji shirun yayi ,yawa ta fara magana "likita wancen pic d'in Ummi ne da dadyn ka dakai lokacin kana jariri ?"...

Murmushi yayi ,yace "A'a matatace da ,d'ana " matatace da, d'ana saida ta maimaita yakai sau ,uku a zuciyar ta ,yanzu dama Samir yana da mata harda, d'a 'amman ban tab'a sani ba ,yanzu dama duk haukar banza nakeyi , wata zuciyar ,tace tow ke ,meya sani game dake ,kema 'ai kina da yar amman be sani ba , "abun ya baki mamaki ne ,naji kinyi shiru" ta, tsinci muryar shi yana magana, Dariyan yak'e ta saki tace "ae abun da mamaki ace duk zamana dakai ban tab'a sanin kana da mata harda ,d'a ba kaga kow dole nayi mamaki" Hmmm labarin yana da tsaho Doc...bana son ina tuna labarin ,nan yana tayar min da ciwo na , amman zan baki labarina yau da kuma ,koni waye ,wannan matar da ,d'an da kike gani sun jima da barin duniya ,Arayuta na kasance.................kinji cikaken labari na , Hajar tsabar hawaye har idanunta,sun cenja kala daga fari zuwa ja tausayin shi duk taji ya kama ta haka nan taji ziciyar ta ya k'ara kwanciya dashi ,"tun daga wannan lokacin ,na kamu da matsanancin ziwan zuciya dalilin da kikaga yasa ina zuwa ,wurin Dr Aiman kenan bawai wani abu ,bane ,Arayuwa ta yanzu bani da kowa sai mahaifiya ta ," Hajar kam ,kuka ya hanata iya cewa komai, ..

"Allah sarki Doc....kaga rayuwa kaga jarabawa ko nace kana kan gani ,duk irin jarabawan da nagani arayuwa ta naka yafi nawa ,Allah ya baka mace me irin halin marigayiya Allah yayi musu rahama ita da prince"....

"Ameen ,nagode yanzu yanda na zage na baki labarin rayuwata da kuma waye ni ba tare dana b'oye miki ,komai ba nima ina so kiban ,naki don ko nasan akwai abunda ke damun ki tun randa nace ki shirya mu fita kika ce A'a nasan akwai wani abu a k'asa ina so yau kisanar dani damuwar ki ,idan har kinyarda, dani "..

Lokaci guda taji zuciyar ta ya fara bugu da sauri ,da sauri Ba ta da niyyar yi masa k'arya 'a labarin rayuwan ta 'amman idan yasani yaya ze d'auki abun ze cigaba da 'abota da ita koko zai gujeta , bazatyi k'arya ba zata fad'a ma sa komai koda hakan zeyi sanadin rabuwan su.

Saida tad'anja wani gauron ,nufashi sannan ta fara magana" zan sanar dakai wacece ni da kuma tarihin rayuwata har zuwa lokacin da 'Allah ya had'ani dakai a matsayin abokina 'Amman ,ina so kasani labari na babu wani abun farin ciki, ciki sai tarin kuncin rayuwa da bakin ciki da tsantsar yaudara irin ,na d'a 'namiji, nasan idan kasan labarina ba lalle bane mucigaba da 'abota dani dakai amman ina so labarin da zan baka ya zama 'amana ban yarda ka sanar da kowa ba idan har bada izinina ba, kadai san nauyin amana kuma labarina dogon labari ne zamu iya kaiwa gobe anan ba tare da mun gama ba , kaine mutun ,na farko aduniya da zan fara bawa labarin rayuwa ta , zan bayana maka' abunda nakai shekaru ina danewa ciwan daya jima yana damu na"...

"Insha 'Allah nad'auki alk'awarin bazan fad'ama kowa ba ,kuma bazan tab'a gujen kiba, duk da bansan labarin ,naki akan me ya kunsa ba"..

murmushi da iya kacinsa fatar baki tayi "tow nagode saida tad'an nisa sosai , sannan ta 'ajje jakarta kan table ta cire gilashin idon ta ma ta 'ajje ta zaro wani farin towel k'arami daga jakar ta ,tafara goge hawayen dake bin fuskar ta, zu ciyar ta na mata zugi...

"Sunana Hajara wacce akafi sani da Dr Hajar ,ni cikakiyar bafula tanace gaba da baya................."





*BY DIJA_WAZIRI*💉
[18/12 7:32 pm] Dija Waziri: 💉💉💉💉💉💉💉
*DOCTOR HAJAR*👩🏻‍🔬
💉💉💉💉💉💉



Chapter 23

Wannan shine labarina, kuma har yau da nake baka wannan labarin ,ban kuma saka 'Akram cikin idanuna ba ,hasali ma wai abokin sa yace baya ma k'asar ya gudu ,tana maganar tana kuka me tsuma zuciya,hankiy d'in dake hanunta ya jik'e sherk'af kamar ansa masa ruwa,

Dr Samir ko kura ma ta ida yayi lokacin da ta kifar da kan ta, tana wani sabon kukan mai tsima jiki. Bai san abun da ya dace yayi a lokacin ba don tausayin ta ya gama kama shi, ji yake da zega 'Akram babu ,abinda zai hanashi harbe shi, idan ko be harbeshi ba to dole ze masa ila, don aduniya 'idan akwai abunda ya tsana be wuce ,cin mutuncin da maza keyiwa mata ba tare da keta musu haddi, ya tsani cin amana da yaudara ..

Lokaci guda Doc... Ya ji kan sa na wani irin sarawa kamar zai rabu gida biyu ,zuciyar sa kuwa sai buga k'irjin sa takeyi, Hak'ika taga rayuwa taga tashin hankali mara misal tuwa ta tsinci kanta cikin watarayuwa mara dad'i ,ba ko wani d'a namiji bane zeji labarin ta ya, yarda hakan shine gsky kuma ba ko wani d'a namiji bane ze iya 'auren ta har idan yaji tana da ,d'iyar da bata da uba ,Amman shikam harga 'Allah ya ,yarda ,da ita kuma ya ,yarda ,da labarin data bashi da zata 'amince ta 'aure shi da zaiso hakan , amman ze jaraba hakan ya gani koba yanzu ba...

D'agowa tayi ta kalli agogon dake manne jikin bangon office d'in taga har shida saura minti biyar na yamma , d'aukar jakar ta ,tayi ta kalle shi da idon ta dayayi jawur kamar gauta "barin tafi gida ,kar magriba tamin 'anan".

Cikin kunci take, ya lura da hakan. Ta na buk'atar waraka, ko ba 'alokaci d'aya ba ne.sake tuna labarin ta ya na matuk'ar rugurguza ta. Ji yayi yana son taimaka mata wajen sa mun sassaucin in har zata yarda, dashi.

Don haka ya ,yanke shawaran ze meni yardan ta ,ze aureta baze tab'a jure ganinta cikin damuwa ba ,tun ba yauba yake dakon son ta don haka labarin ta baze iya janye wannan kwauna daya dasu cikin zuciyar saba..

"Tow Dr Hajar labarin ki yana cike da ban tausayi na jinjina maki wajen danne zuciyar ki da hakurin da ,kikayi kan abunda ya sameki , kaddaran kice hakan dama tuncen me sama ya rubuta faruwan hakan, wayon ki ,ko dabaran ki basu isa hana faruwan hakan ba , abunda na fahimta cikin labarin ki ,ki dena cewa laifin kine ba laifin ki bane laifin iyayen kine ,kema kina da naki laifin (wato yanzu ankai wata gab'a da idan yaro nason yarinya ba ko wasu iyaye bane masu tsaurara bincike ,kan yaron da sun d'anyi kadan shikenan anwuce gurin basa tsayawa suyi bincike dakyau ,tow yanzu ma 'a wannan zamanin da muke ciki an tsaurara binciken ma ba'a kubuta ba ,bare kuma ba'a maida hankali gurin yin ba , Allah kasa mudace ka, kuma karemu da, dukkan ,kariyan ka 'Ameen) kiyi hakuri da 'abunda na fad'a ban fad'a ,don cin fuska ba , kuma wannan labarin bazesa na guje kiba, ina tare dake zanyi kokarin ,naga kin maido ,da farin cikin ki, kin samu ingataciyar ,rayuwa kamar yadda ko wace mace take mafarki, kuma zanyi kokarin fahimtar da, duk wanda yazo neman auren ki cewar wannan abunda ya faru dake ,kaddara ce ni dake mun tashi daga 'abota mun koma yan uwan juna, zanyi kokarin share maki hawaye kamar yanda yaya da k'anwa kewa keyi , Jawahir kuma daga yau ta dena kukan rashin hamaifi insha 'Allah, Abunda nake so dake shine kiyi hakuri kamar yanda kika sabayi ubangiji ya baki miji nagari me sonki tsakani da 'Allah"...

Dukda tana cikin damuwa hakan be hanata tsintar kanta cikin farin ciki ba dashin furucin Doc...Amman wani tashin hankalin shene ya zatayi tace da Jawahir ba Captin bane ,baban ta bayan tariga da tace mata shine ? Shin idan ta dawo tace bashi bane hakan baze jawo matsala ba? Haka ta d'inga tsak'e sak'e daga bisani ta kawar da zance , "Ameen Dr Samir nagode ,da kulawar ka 'Allah ya saka barin tafi ". Tare suka fito dashi har bakin mota ya rakata, ta shiga sannan shima ya shiga nashi....



Indian

Yau ne Maman akram ta cika sati biyu a gidan kaso , duk ta rame tayi bak'i duk da ,dama bak'ar ce ta kuma bak'an cewa , da safiyar ,yau asabar wani ba indiye ,yazo yayi belin ta , tare da biyan wannan mutumin kud'in da yake bin su, wannan ba indiyan ,ya shaida mata cewa Akram ne ya turo shi ,Amman be sanar da ita ko ina yake ba, babu yanda batayi dashi ya kaita gun Akram d'in ba yak'i daga baya ma tafiya, yayi ,ya barta gurin taci kuka ,kamar ba gobe takumayi nadamar rayuwan ta , daga caji office bata wuce ko ina ba sai filin jirgi, a ranar ta gama komai kawai jira take ta shiga jirgi ,basu suka shiga jirgi ba saida suka, k'ara kwana da ini k'arfe bakwai na dare jirgin su ya d'aga zuwa najeriya...


A b'angaren Talatu kuwa ,koda taje gurin boka da basu a raba Captin da Hajar idan ,da hali ma 'a kashe ta ,boka babu yanda beyi ba don yaga hoton Captin dana Hajar ya fito kan Allon tsafin sa 'amman ina sunfi k'arfin sa ,haka ya shaida mata cewa baze iya dasu ba wannan karon Captin yayi masa nisa don ko baya iyawa dashi ,sun rik'e karatun kur'ani da 'azkar tare da addu'on tsari ,kuma sun rik'e salan dare dana farillah don haka, babu wani bokan duniyar da ze iya dasu, hakan yasa ta hakura ta koma gida tare da 'Alwashin baza ta b'a bari suyi aure ba.

****-*

"Abokina Hanzar ta pls kar magrib tayi nafiso idan ma magrib d'in zatayi tow tayi mana 'a gidan su , Dr Samir dake ,kokarin b'ale botuns d'in rigan shi yace" kwantar da hankalinka,na gama yanzu zamu tafi, ni wlh haka, kurum jikina keban akwai abunda ze faru idan mukaje"..

"Kamar ya kana ,nufin bazamu samu nasara ba?" No bana fatan haka ,kawai bana jin dadin yau d'inne ,wlh don ,kawai nayi maka 'alk'awari ne dase nace na fasa ", tow nidai mutafi tunda ka gama "....

Mota suka shiga sai k'amshi suke suka d'auki hanya..

Tow fa me kuke ganin ze faru?😳


Muje zuwa 🏃‍♀🏃‍♀🏃‍♀🏃‍♀🏃‍♀


Banyi editing ba yau sai kuyi hakuri da typing errors da zaku samu gajiya nayi

*By Dija_waziri*
[18/12 7:32 pm] Dija Waziri: 💉💉💉💉💉💉💉
*DOCTOR HAJAR*👩🏻‍🔬
💉💉💉💉💉💉

*Tabbas duk wata d'aukaka bata zuwa ma bawa babu jarabawa 'a cikin ta*

*duk halin daka tsinci kanka na farin ciki, kona bakin ciki, ka gode ubangijin ka*.


*idan ka samu ci da sha da gurin da zaka rufawa kanka 'asiri kayi hamdala ga 'Allah ,koda ace a rana so d'aya tak zaka samu abunda zaka sawa bakin ,ka ,kad'au hanu ka godewa ubangijin ka ,wasu ,sau d'ayan ma suke nema basu samu ba*

*ina jin mamakin mutanin da sunsan ,sunfi k'arfin abu amman bazasu iya d'auka suyi kyauta dashi ga wanda basu dashi ba ,sai dai su ,siyar masa ,saboda suna ganin ,idan sun bashi kyauta sunci baya ,*

*yan uwa ku sani cewa idan kayiwa na k'asa dakai Alkairi Allah ze baka lada kuma shima wannan mutumin baze tab'a mantawa dakai ba, barin ma 'ace yana cikin buk'atar abun ka bashi, kullum idan ya kalli abun koya tuna da 'abun zeji dadi kuma zeyi maka 'addu'a da fatan Alkairi, me yafi wannan dad'i..*

*Amman yanzu mun shigo wata gab'a wanda idan talaka yaje neman taimako , wajen wanda yasan yana da 'abunda ze iya taimaka ,masa dashi dede gwargwadon yanda ze iya, Amman ,mutun sai ya dinga nuna shifa bayi da 'abunnan kuma 'Alhalin yana dashi bayar wance kawai bazeyi ba saboda idan ya bada yayi asara*.

*Yanzu munkai wani zamani da mekud'i bazeyi cud'anya da talaka ba sai mai dukiya irin shi , saboda yana ganin wannan talakan bashi da 'abunda ze bashi sai dai shi yayi ,taci a jikin sa yan uwa ku sani cewa ubangiji shike bada wannan dukiyar, ba wayon mutun ba ko dabaran sa ,baka tunani a kowani lokaci Allah yaga dama ze iya kwace wannan dukiya taka ya bawa shi wancen da kake tunanin bashi da ,Amfani a cikin rayuwan ka, idan hakan ta faru ya zakaji , shi talauci ba mutun bane yake d'auka ya k'ak'abawa kansa ubangiji ne yake bashi ,haka 'arziki ma, kuma wani me kud'in Allah yakan bashine don ya jarabashi kuma ya ga k'arfin imanin shi ,shin ze iya tafiyar dasu yanda ,ya kamata*..

*Naga wani abuda ya bani mamaki ,wata baiwar Allah ce taje tallan ged'a wani gidan me rufin asiri, tunda basa rasa ci basa rasa sha kuma basa rasa, suturan da zasu ,saka bakuma sa rasa kud'in da zasu b'atar , wannan tsohuwa da taje gidan matar, gida ta ,tambayeta nawa nawa ne gyad'ar tsohuwa ta fad'a sai matar ,ta nemi arage mata ,tsohuwar tace wlh idan ta rage mata zata kwaru don yanzun ma tafito neman yanda zasuyi ne tabar yara babu abinci tun safe, Amman ta d'au ged'an kwano d'a idan yaso ,sai ta bata hatsi dede ged'an , ae ko babu kunya matar ta karb'a tako bata gero mudu d'aya geron ma irin k'asa ne wanda suka 'ajeye bazasu iya 'amfani dashi ba , najima ina jimamin abun ,abunda kasan kafi k'arfin shi meyasa bazaka iya badawo kyauta ba har sai kun fanshe ,wannan tsohuwa yau koda ba talle ta kawo ba 'ae abar tausayawa ce idan kasan kafin k'arfin abu meyasa zaka ,dunka ,k'ask'antar da kanka ,kana ,nuna baka dashi wannan shi ake ,kira da rashin wadatar zuci baka tunanin Allah ze iya hanakan....*


*Allah ubangiji kasa mudace masu irin wannan d'abi'a 'Allah yasa, su gane Ameen*🙏


Chapter 24


"Wai , ya sunan uguwan tasu ne?" Samir ya tambaya, "bata ma uguwar su d'azu Khadee tace min tana gidan Kakar ta, tarauni zamuje " Samir ne ke driving k'ara bawa motar wuta yayi ,suna isa unguwar aka ,kira sallah magrib ,saida suka tsaya ' sukayi sallah a wani masalaci sannan suka ,k'arasa cikin layin ,suna isa horn sukayi get man yazo ya bud'e masu kofa suka, k'arasa da motar , shidai Samir tunda suka shiga ,gaban shi ke fad'uwa , Captain , ne ya fita yace da megadi yaje ciki yace ana salama da Hajjo, me gadi be jira wata ,wata ba ya fad'a cikin gida Inna ya samu a ktichin tana yanka ,kub'ewa me aikin kakar su Hajar kenan , ganin shigowan shi yasa inna washe baki" a'a idi ya 'akayi ko yinwa ce ?"..

"A'a Inna kinsan ido dayawa ni shikenan bazan shigo ba sai naji yinwa ,sai kace wani acici naga ban, jima dacin ,na rana ba ma "...

Dariya Inna tasa tace"tow ae naga babu abinda ze higo dakai cikin ,ne".

"Tow yanzu dai bashine ya kawo niba ,kije ki sanar da likita wai ,wasu ,sunzo gurin ta , suna waje suna jira" yana gama fad'a ya wuce sauri sauri don yabar kofar gida'a bud'e ...

Inna kuwa falo ta shiga ta iske Hajar na karansa jarida Hajiya kuma da Jawahir suna kallo suna d'an hiran su , rusu nawa tayi tace" Barka da, dare Hajiya Maman Jawahir wai kinyi bak'i suna waje "..

Hajar taji abunda inna tace sarai, sai tayi kamar bataji ba ,taci gaba da karatun jaridan ta, "Hajjo bakiji abunda 'akace bane?" Hajiya ta ,tambaya.

Sai a lokacin Hajar ta d'ago ta ,kalleta "me akace Hajiya banji ba, ni hankali nama yana kan wannan jaridar " zaki iya jid'in ma ki share don ,nasan hali cewa 'akayi kinyi baki don Haka sai ki tashi" wasu bak'i kuma ni babu wanda mukayi zezo gurina don haka babu inda zani halama ba gurina suka zo ba, b'ata sukayi ,Inna kije kice musu bananna gidan bane .

Har Inna zata Mik'e Hajiya ta dakatar da ita da cewa ,"Inna kice da me gadi 'injini ya kaisu falon bak'i, ke kuma ki had'a ruwa da lemo kikai masu"..

Yanda Hajiya tasa Inna tayi hakan tayi, "don Allah kiyi ta zama Hajjo kar kije don bakisan ,suwaye ba sai shikenan bazaki fita kiga ko suwaye ba tow kuma idan mijin auren kine fa shikenan kinwa kanki asara kow, tow karki tashi kije " Hajar na tura baki ta zari hijabin Hajiya tasa ,ta cire gilashin dake idon ta, ta ajje shi kan Tv sand ,har tazo ,zata fita Jawahir tace"Mommy nazo na raka ,ki?" Kafun tayi magana har Hajiya ta riga ta, "A'a babu inda zaki muna hiran zaki tafi ki barni, ni kuma na zauna dawa...

Zaune suke suna d'an shawaran yanda zasu shawo kan Hajar , suna cikin Haka wayan Dr Samir yahau k'ara ganin Ummi yasa shi d'aukar wayan tare da fita.

Fuskar ta babu ko fara'a ta shigo cikin falon k'amshin turaren da taji ne yasa ta ,saurin d'agowa taga ko waye don ko mutun d'aya ne wanda take jin k'amshin turaren a jikin shi ,da mamaki taga bashi bane Captin ta gani zaune yana murmushi, k'ara hade rai tayi ta zauna ba tare da tace uffan ba ,tana wasa da yan yatsun hanun ta ...

"Barka da ,dare Hajjo ya kike ya Jawahir?".

Fuskar ta 'a d'aure ta 'amsa da "lfy qlau ".

"Masha 'Allah kwana biyu laifin me nayi kika dena kulani?".

Shiru tayi batace komai ba zuciyar ta na suya ita haka, nan jininta bezo d'aya da nashi ba..

"Duk abunda ya faru naji Khadee ta sanar dani ,kuma ita wacce ta ,turo maki wannan lettar wlh ba ,budurwa ta bace , hasali ma ba yarinya bace don ashekaru zata iya kaiwa 45 cousin d'ina ce, kuma naje nayi mata ,magana don haka ina rok'on ki da kiyi hakuri "...

Ita dai Hajar tunda ya fara zancen shi bata ce dashi uffan ba , da murmushi ya shigo falon hanunsa d'auke da wayan shi ganin wacce ke zaune a kan ,kujera ne yasa shi fad'in ,"innalilahi wa inna ilaihin raji'un" besan ,sanda wayar hanunshi ta subuce ta fad'i ba ,gefen zuciyar shi ya rik'e yana wani 'irin numfashi nan danan fuskarshi ta juya ta koma jazur babu abinda ke tashi cikin falon sai sautin ,nufashin sa dake fita, sama sama , da gudu Captin yaje ya tareshi dede lokacin da yake shirin zubewa k'asa , "innalilahi wa inna ilaihi rajiun" Dr Samir meya kawoka ,nanna gidan ? Waya maka kwatance? "Hajar tazo da gudu tana ,tambaya...


Captin kanshi yayi mugun d'aurewa dayaga Yanda Hajar ta rud'e,kar dai ,tasan shi tow miye halak'an su ? Shi kadai yake ta ,wasu tunani cikin zuciyar shi...

"Sashi mota barin sanar da Hajiya sai nazo mu wuce hospital , nanna ta sanar da Hajiya sannan suka d'auki hanya basu jima ba suka isa Hajar Hospital suna zuwa 'aka shigar dashi wani d'aki , Dr Aiman takira takoyi sa'a yana 'asibitin nan suka rufu kan Dr Samir aka fara saka masa wasu na'urori wanda zasu taimaka wajen sevin life d'in shi , daga nan Dr Aiman yayi wasu yan binciken shi , kallon Hajar yayi ,yace "akwai matsala fa Dr Hajar idan ,da hali ki ,kira mana Dr Khadee pls Samir ze iya rasa ransa at any time ,Hajar da jikinta ke wani 'irin kyarma tayi saurin d'aukar waya ta kira khadee ta kuma sanar da ita cewa tazo Hospital yanzu akwai matsala ...

Shiko Captin kanshi ya gama d'aure wa yana so yasan menene dalilin fad'uwar Doc....kode an fad'a masa wani abunda ya girgiza shine a waya , shi yanzu mezece da su Ummi kuma yasan dole su ,sani don abun bana b'oyewa bane , Salma ya kira ya sanar da ita 'abun dake faruwa Salma cikin Fargaba da tashin hankali ta sanar da Ummi koda ta gaya ma Ummi kuka sata, sukayi asibiti




Shiko Dr Samir har a lokacin be farka ba, Ummi ko idan banda kuka babu abinda takeyi dak'er Hajar ta shawo kanta, tayi shiru ,suna cikin Haka ne Hajar taga Khadee ta fito daga d'akin da 'aka ,kwantar da Samir babu walwala, "lfy dai kow Khadee ?" Hajar ta, tambaya girgiza mata kai Khadee tayi ,tace Muje office d'in Dr Aiman.....

"Dr Aiman akwai babban problem ,Hajar gsky zan gaya maki 'idan ,nace zan karb'i aikin Dr Samir zan wahala tun daga kan wannan yarinya na dena daukan irin wannan cuta, "nifa ban gane abunda kike nufi ba meke damun sa ,shi nike son ji?" Cewar Hajar...

"Tow binceke ya nuna cewa Dr Samir yana d'auke da ciwan daji na huhu wato kidney cancer disease kuma cutar tariga da tafara cin jikin sa ' a nawa shawaran kawai shine gara 'a fitar dashi waje ,cox idan ba hakaba ze sha wuya daga k'arshe ma ya rasa rayuwan sa, kinga ita dama wannan cuta bata bayyana sai taci jikin mutun , shi kansar huhu ba'a cika yinshi ba don ,nikam ma tunda nake ,karb'an cancer patients ban tab'a haduwa da me kedney ba gsky tunda na fara 'aiki a rayuwa ta " innalilahi wa innailaihi raji'un jarabawa da yawa take aduniya daga wannan sai wannan ,Allah ka bamu sa'ar cinyewa ,wannan bawan Allah yana cikin matsala ga ciwan zuciya ga cancer ubangiji kayi masa, sassauci a rayuwan shi" Ameen Dr Hajar yanzu haka halin da 'ake ciki sai munyi masa wanki zuciya " cewar Dr Aiman. "Tow Dr Aiman idan hakan zesa muceto rayuwan shi ae sai ayi"...

"Tow Allah yasa muyi a sa'a wai miye musababin tashin ciwon ,nashi ne?" Dr Aiman ya tambaya "wlh nikam ban sani ba Ina gidan Hajiya Muna tare Da Junaid kawai naga ya shigo ban ma san waye ,yayi nasa kwatance ba ,shigowar da yayi mukaga ya fara kalmar shada yana wani 'irin nishi", tow Allah dai yasa lfy cewar Khadee






*By Dija_waziri*
[18/12 7:32 pm] Dija Waziri: 💉💉💉💉💉💉💉
*DOCTOR HAJAR*👩🏻‍🔬
💉💉💉💉💉💉







*Hakika kyakkyawan amfani da lokaci wani al'amari ne mai matuk'ar muhimmanci a cikin rayuwar mu domin kasancewar lokaci wani haja ne mai tsada wadda ke saurin kubucewa ko shudewa a cikin rayuwa.*

*Zamu iya daukar ma'anar lokaci a matsayin duk wata gusawa da 'aka samu tsakanin wani zango zuwa wani a cikin rayuwar dan adam kamar gusawa daga dazu ,yanzu, jiya zuwa yau, gobe zuwa jibi ko dare zuwa rana da dai sauran su.*

*idan muka duba fadin Allah a cikin littafin sa mai girma, suratul nisa'a 'aya ta dari da cesain ,inda yake cewa, lalle ne a cikin halittar sammai da kasai da sabawar dare da yini akwai ayoyi ga ma'abuta hankali (nisa'i) zamu fahimci muhimmancin tunani akan juyawan lokaci wadda ke zuwa saka makon sabawar dare da rana ,a cikin rayuwar dan 'adam.*

*Akwai wasu ni'imomi guda biyu wadanda mutane da yawa ,suke tozarta su wadannan ni'imomi sune lafiya da kuma lokaci wadannan abubuwan suna daga cikin ni'imomin da Allah yayi wa dan adam wadda kuma yake bukatar su gode masa ta hanyar kyakkyawar amfani da su.*

*yadda zamu ribanci dukkan lokutan mu sune kamar haka, mutun zai ribanci lokacin da mutane suke cikin kunci da wahalhalun rayuwa wajen maida hankali akan taimakon masu rauni da ,dukiyoyin sa'a maimakon ya takaita kansa wajen hidimar yayan sa da iyalin sa kawai ,Alhalin alummar dake kewaye da shi suna cikin matukar bukatuwa da taimakon sa. Monzon Allah (SAW)yana cewa duk wanda ya kuranye wa dan'uwan sa musulmi wata damuwar duniya Allah zai kuranye masa damuwar ranar alkiyama. Duk wanda ya kawo sauki a rayuwan dan 'uwansa musulmi, Allah zai kawo masa sauki anan duniya da kuma lahira .kuma Allah na cikin taimakon bawan sa matukar bawa na cikin taimakon dan uwan sa*

Chapter 25


4:30Am

A hankali yake bude idon shi yana motsa kafar shi alamun yana son tashi , da sauri Salma ta k'arasa kusa dashi tana "sanu Yaya" dede lokacin daya k'arasa bude idon shi dede lokacin Dr Hajar ta banko ,kofar d'akin ta shigo,

Be sauke idon shi kan kowa ba sai kan ta, ita ma shid'in take ,kallo saurin kauda idon shi yayi daga ,gareta, tare da maidashi kan Captian daya shigo shima....

"Dr Samir sanu ya jikin ,naka hope da sauk'i kow? Ya kakeji yanzu ?" Dr Hajar ta, tambaya..

Bece da ita komai ba sai girgiza mata kai da yayi ,yaja pillo da taimakon Salma yad'an jingina.

"Likita ya kamata kad'an ci wani abun tunda 'Allah yasa ka tashi lfy" cewar Ummi ,kallon Ummi shi kawai yayi

Please Login or Register in order to submit comment