Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

,nufanshin ,sa tare da tunanin wannan yarinyan wacece ita da yake mafarkin ta, kuma metake nufi dashi?, kamoshi da yaji anyi ne yayi saurin ,k'ara ,razanar dashi don yayi tunanin ko itace ganin Hajja yasa shi jin dad'i..

"Akram, magana fa nake maka ,kamin banza " don Allah Hajja ki rabu dani duk halin danake ciki, kece sila kece kika jefani kuma wlh ,nafada miki ,idan har baki gayamin waye niba zan gudu na barki ,kuma bazaki sake ganina ba"

"Ya 'Allah "shine abunda ta futa cikin k'asan zuciyar ta , wasu zafafan hawaye taji ya zubo mata , nadama ce fal cikin zuciyar ta. Kud'i basuyi mata ,rana ba yanzi 'ina zata saka ,kanta ,tajefa d'anta ,tilo guda ,d'aya da 'Allah ya bata cikin gurb'a taciyar ,rayuwa ,wanda ita kanta 'ayanzun bata isa futar dashi ba kuma itama ,tajefa kanta cikin halin ,nadama da kuma dana sani ,da tasan haka rayuwan ta zai kasance ayanzu da tunfarko, bata 'aikata 'abunda tayi ba yanzu gashi tasa kanta cikin tsaka me wuya , kuka me sauti ne ya sub'uce mata wanda shine dalilin ficewar ta daga d'akin..

Akram ,ko ajikinsa be damu da fice warta daga d'akin ba kuma be damu da kukan ,taba tashi yayi ,ya d'auki ,kwalbar giyar dake girke ,kan tabal d'in d'akin ya fara kwan -kwad'a saida yasha me isarsa, sannan ya koma ya kwanta yana rik'e da kanshi daya fara juya ma


NIGERIA

Dr Samir a gsky ni mebaka shawara ne da ka ,fita k'asar waje tun da sauran k'arfin ka ,ka fara jinya 'a gsky bamu da kayan aiki sosai kamar k'asar turai barin ma irin wannan cuta nake da baya bayyana da wuri sai yaci jikin mutun, sanin kanka ne kafun mu gane abunda ke damunka, munci bak'ak'ar wuya wurin ganowa, kuma koda muka gano abun yaci jikinka saboda haka gsky abunnan gaba ,gaba yake ,k'arawa gara tunda sauran k'arfinka ,kaje k'asar waje su d'auraka, kan magani tare da treatment me kyau "..

Murmushin dabekai zuciya ba Dr Samir ya saki"likita sauk'i daga 'Allah yake yau kona fita ko karna fita, duk sanda 'ajalina yayi dole na tafi babu wanda ya isa ya magance min abunda me kowa me komai ya d'aura min ,Addu'a itace komai da fatan cikawa da imani ,idan babu damuwa kacigaba da ,d'aurani kan magani kamar yanda kasaba 'da taimon Ubangiji zan samu waraka"..

"Haka ne Samir Amman karka manta ,Allah yace tashi na taimake ,ka ,Amman babu komai ,insha 'Allah zanyi ,iya k'ok'arina ,kuma zanci gaba da yi maka 'addu'a Allah ya baka lfy".

"Ameen likita nagode ,da taimakon da kake min".

"Babu godiya tsakanina dakai Dr Samir dukkan mu ,muna taimakon yan uwanmu ,musulmai fatan mude Allah ya k'ara mana basira da fasaha kuma yasa mucika dakyau da imani ".

"Ameen Likita"nan sukayi salama Doc... Samir ya koma office d'inshi..

***

"Hajjo niko ina son magana dake " tow Mami 'ina jinki"..

Gyara zama ,Mami tayi ta fuskanci Hajar sosai "Hajjo meke damun ki? Idan nina haifeki kuma na isa dake, tow karki min k'arya "..

Duk yadda Hajar tayi da b'oye damuwata, takasa kallon Mami tayi idonta na zubda hawaye "Mami haryau na kasa mance rayuwan baya ,narasa ina zansa kaina Mami wlh Gabaki d'aya bana jin dad'in rayuwata'a yanzu "

"Kallon Harjar Mami kawai takeyi tare da tausayin ta , yanda taga d'iyar tata ,tarame tayi wani 'iri yasa ta zubda kwala batare da Hajar d'in ta gani ba, "Hajjo Allah maji rokon bayinsa ne haka zalika babu wanda ya kaishi nuna kauna da soyayya ga bayinsa. Duk abunda kikaga ya samu bawa tow muk'adari ne dama yana rubuce ,kuma bawai sonkine bayayi ba wlh yafi kowa sonki don komu iyayenki baza mu tab'a had'a soyayyar da muke muki dana mahalicin kiba ,Allah yana jaraftar bawanshi tako wace hanya kuma 'aduk sanda yaso alokacin dayaso don haka, kiyarda ,dani lokaci yana zuwa da zakiyi dariya wanda ya zalun ceki ,kuma yayi kuka ,kuka nahar abada ,don haka lokaci yayi da zaki manta da komai a yanzu ,ki maida komai ba komai ba 'Allah ya baki miji nagari ".

"Ameen Mami ,insha Allah zanyi kokarin cire komai cikin zuciya ta zanyi, yanda kikace " yawwa 'Allah ya miki albarka" Ameen Mami"

Koda Hajar ta koma d'aki, tunani take kan yadda zata gina rayuwarta, ta inganta, ta kuma mori sauran kuruciyar da tayi mata saura dolenta, ta shafe babin rayuwan baya tasan abunyi arayuwa yanzu bata da wacce tafiso tafi k'auna sama da Jawahir da kuna iyayen ta kodon ganin farin cikin su dole ne yanzu ta janye kudurin ta, tare da k'arb'an soyyar Captin Junaid ,badon tana son saba sai don ginawa d'iyarta rayuwa me inganci ,wanda ko bayan ranta, tasan bazatayi kuka ba,

Ajiyar zuciya ta saki tare da wani murmushin da iya fatar baki ya tsaya , azahiri tana buk'atar kunnan wayan ta 'amman bataso tayi karo da kiran Dr Samir, yau kwana biyu kenan rabonta da kunnan wayanta, a zahirin gsky tana son takunna kodon taji muryan shi amman tana tsoron abunda zai biyo baya ,tasan dole da tambayoyin da zaiyi mata, haka dole ta hak'ura ...

Ban d'aki ta fad'a tayi wanka ta fesa kwaliya kamar ba itaba rabon da tayi ,irin kwaliyar da tayi ,yau shekara biyar kenan da suka wuce , yaune tafito a 'asalin Hajar sarkin gayu ,wani material tasa ruwan ganye da launin ja d'inki buba ,ta yane kanta da jan mayafi tafeshe jikinta da turaruka masu k'amshi ....

"Wow Hajjo gsky kinyi kyau yau ,wlh kamar bake ba "cewar Basmad ,datashigo d'akin sanye da bak'i da farin kayan ta ga dukkan Alamu daga ,gurin aiki take.

"Thank you sister "Hajar ta fad'a tana fari da ido "nifa ban gane ba Hajjo wannan irin kwaliya haka, wanda rabon da naga kinyi tun shekarun baya da suka wuce, kode yayan ,nawane zai zo yau?"..

Nan danan Hajar ta had'e rai duk fara'an da take ta dena"haba Sister bana so yau ina cikin farin cikin shine kike son samin damuwa ina ruwana dashi meya shafeni dashi aiki zani kuma ganin damanane yasani yin kwaliyar yau " fuuu da ja ,jakarta zata fice..

"Tow adawo lfy idan ,nab'ata miki rai sorry"..

Ko, kulata Hajar batayi ba tafice taje tayi wa Mami Salama ta ,tafi, gudu take shararawa kan titi sauri take, taisa don ta ,sameshi ,dukda tasan bazata yarda su had'a ido ,dashi ba , minti 30 ya sadata, da 'asibitin tundaga haraban asibitin kowa sai binta yake da kallo ,shiga ciki tayi tana zuwa direct office d'in Khadee ta shiga...

"Wow Masha 'Allah ,Hajar kece koko idona kimin gizo ?" Cewar Khadee tana nunata da yatsa "miye kuma hakan sai kace yar k'auyen datashigo birni yau " Hmmm badole na tmby ba Hajar yaushe rabon da kiyi kwaliya irin haka gsky kinyi kyau wlh Allah nagode maka daka dai-dai tamin k'awata ka dawo da ita kan hanya 'Allah kaine abun godiya, wlh Hajar ganinki cikin walwala yau ba k'aramin sani farin ciki yayi ba ,harcikin zuciya ta ".

Murmushi Hajar tayi "nagode K'awata " Hajar kwana biyu meya hanaki zuwa 'aiki ?" Wlh ,hutawa nakeyi Mami ce tahanani zuwa tace yakamata nad'an samu nahuta na kwana biyu".

"Kaji yar gatan Mami tow meyasa kika ,kashe wayoyin ki Captin ma saida ya kirani wai baya samun ki, yauma zai dawo"..

Daure fuska Hajar tayi kamar bata, tab'a dariya ba "ni bawannane ya Kawoni ba ke duk randa muka hadu baki da magana sai nashi,tow Allah ya kawo shi lfy nikam kinga tafiya ta "..

Tana fita office din Dr Aiman ta wuce ,shikad'ai ta ,tadda shi kanshi kasa ganeta yayi saida ya kura mata ido sosai"kai Doc..wlh kinyi kyau yau Gud morning? " morning how are you? " I'm fine and u? "Same to you "tow masha 'Allah kwana biyu munjiki shiru Allah yasa dai lfy?" Lfy qlau fa yau abokin ,naka bezo bane ?" Wlh yayi tafiya ne bama ya k'asar " har cikin zuciyar ta bataji dad'in rashin samun shiba duk wata walwala da farin ciki taji sun gushi mata, dak'er ta iya cewa Dr Aiman ok ,sanan dai tadan tsaya sukayi dan hiran da ,duk rabi ,baganewa takeyi ba donta tsunduma, duniyar tunani...

Koda ta koma offce d'inta saita fara tunani ,wai meyasa ma tadamu da taganshi miye ruwanta dashi da zata sawa kanta da muwa,da haka takauda tunani tacigaba da 'aikin dake gabanta .....



******

Tun sanda sukayi wayan k'arshe da ita yakasa samun nutsuwa kullumsaiya kira number dinta amman akashe shi karan kanshi ayanzun yasan soyayyar hajar tayi zurfi cikin zuciyar sa amman yana tsoran sanar da ita yayi alk'awarin bazai sanar da itaba harsai ya koya mata sonsa.

SATURDAY

"Basmad wai ina Hajjo ? Nifa idan bazata zoba zan tafi " cewar Khadee "la sorry Khadee dama baki lek'a d'akin Mami bane ae nayi tunanin kun had'u da ita, tana cen tana gyarawa Mami kaya "eyyah wlh ban shiga ba dana shiga ban ganta falo ba kawai na shigo d'aki banaje na sameta "...

Tashi Khadee tayi taje D'akin Mami, Basmad kuma taci gaba da shafawa Jawahir mai suna wasa da, dariyan su, "Aunty " Na'am Jawahir menene? " tsayawa da, dariyan Jawahir tayi ta d'an had'e rai sanan tafara magana "Aunty kin tab'a ganin babana? "Eh natab'a ganinshi Jawahir menene ?" Hawaye Jawari ta fara zubdawa ,wannan shine karo nafarko da Basmad ta ,tab'a ganin Jawahir tayi kuka batare da ko ta fad'i ba ko ando keta"ki nuna min hoton shi Aunty ina so naga Babana ,Mummy tak'i ,kaini gurin shi " tausayin tane ya kama Basmad tayi saurin rungume ta ,Hajar da Khadee na bakin ,kofa suna jin duk abunda ya faru ,gefen gado ,ta nema ta zauna jikinta 'a mace tajuyar da kanta ,tayi tan kwala ,Khadee ce ta k'arasa inda Jawahir take ,ta janye ta daga jikin Basmad "fuskarta d'auke da murmushin yak'e tace"Jawahir my Beby Babanki ,kike son gani kow?" Jawahir na hawaye ta girgiza wa Khadee kai Alamar eh" tow karki damu yau nayi miki Alk'awari yanzu ,zakiga Baban ki ,kow" cigaba da kuka Jawahir tayi "kiyi shiru yanzu keje Aunty Basmad tacigaba da shirya ki ,amman sai naga dariyan ki " nan danan Jawahir ta saki ranta, ta fara k'elk'ela dariya..

"Hajjo "Khadee tazo kusa da ita ,tana kiran sunan ta , Juyowa Hajar tayi tana kallon ta batare da tace komai ba, "ki tashi ki shirya kar bak'on ki yazo yayi ta jira kinsan yakusa isowa " babu musu Hajar ta ,tashi ta fad'a toilet zuciyar ta 'a jagule ,saida ta kusan kaiwa mintuna talatin sanan ta fito ,tana fitowa ,wayan ta yahau ruri fargaba da fad'uwar gaba taji sun riski zuciyar ta, dak'er ta iya furtawa Khadee ta d'auki wayar,

D'auka ,Khadee tayi banaji me aka ce da itaba, kawai tace tow tana zuwa sannan ta tsinke wayar, ta maida kallon ta kan Hajar da shafa mai "bok'on kine ya iso wai yana waje, bari muje nida Jawahir mu shigo dashi falon bak'i, kafun ki gama shiryawa " kama hanun Jawahir Khadee tayi zasu fice Hajar tayi saurin dakatar dasu zuciyar ta, na mata wani irin suya



Ku biyoni yanzu Aka fara buk ⛹⛹⛹⛹⛹⛹





*By Dija_Waziri*💉
[18/12 7:32 pm] Dija Waziri: 💉💉💉💉💉💉💉
*DOCTOR HAJAR*👩🏻‍🔬
💉💉💉💉💉💉



Chapter 18

Yanzu dai tsakanin Captain Junaid da Hajar ta fara d'aukan wayar shi har sud'an yi hira, cikin raha , kuma lokaci lokaci yana zuwa gurinta su gaisa ,ita dai har yanzu ba sonshi takeyi ba kawai dai babu yanda ta iya ne bata da zab'i sai wanda 'Allah ya zab'a mata , batun Dr Samir kuwa ,kwata kwata ya dena kiran wayan ta ya hasali ma ita rabon da taganshi tun sanda suka had'u a Hospital d'inta ranar wata jumu'a da yaje gurin Dr Aiman check up, tun abun baya damun ta yanzu harya fara damun ta 'aduk lokacin data, tuna shi 'idan da, dare ne tow bata iya bacci sai tayi ,ta ,tunanin shi ita ,tara dalilin haka ta ,rasa meyake shirin faruwa da ita karfa ta koma gidan jiya ,tawa kanta 'alk'awarin bazata kuma soyyah ba , tow amman meke damun ta da yawan tunanin Dr da kuma idan ta ,tunashi take jin fad'uwar gaba ko sabone yasa hakan ,karfa maganar Khadee ya zamo gsky, kai wannan ma 'ai wasa ne daga kan Akram na gama so kuma na gama yarda don haka 'Allah ya sawak'e naso shi nidai nasan kawai shakuwa ce, ita kad'ai take ta magana da zuciyar ta


******
Kwance yake kan sofa ya jingina wayan shi k'an k'irjin sa ya d'aura hanunsa bisa kansa idanunsa 'a lum-lumshe ,ringing d'in da yaji wayarsa nayi ne yayi saurin dawo dashi daga duniyar tunanin daya lula, ganin lambar Ummi ce yasa shi saurind'agawa, daga b'angaren Ummi ta fara magana.

"Hello Dr ya kake ya kuma jikin ka hope babu matsala kow?".

"Lfyna qlau Ummi Jikina kuma 'Alhamdulillah sai godiyar uban giji, ya kike ya Salma?".

"Tow masha 'Allah ae hakan akeso akoda yaushe fatan sauk'in muke son ji, lafiyan mu qlau, ya batun abunda ya kaika?".

Tab'e baki yayi kamar tana kusa dashi yace"wlh mami ba'a dace ba ,babu neman da banyi ba daga k'arshe ma kaini gurin da yan Naija sukafi yawa 'akayi Amman babu kowa don ance shekarun baya da suka wuce duk mazauna gurin sun mutu saka mako wata gobara data faru 'a yanki duk saida taci guri babu wanda 'aka fito dashi a raye ".

"Subhanallah yanzu d'an uwanka ya tafi kenan tow Allah yasa cen d'in yafi masa nan, yanzu yaushe zaka juyo ?".

"Tow ina tunanin gobe zan dawo Amman ina son ,naje k'asa me tsarki ,idan ban dawo gobe ,ba tow zan kira na gaya maki zan wuce ".

"Tow Allah ya kaimu ae gara kaje d'in karok'i Allah buk'atun ka, kuma kawa d'an uwanka da mahaifinka da matarka da ,d'anka 'addu'a".

"Tow Ummi abunda kika ced'in hakan zanyi shawaran ki zanbi "

Nandai sukayi salama ya katse wayar yana katsewa ,riganshi ya d'auk'a yasa ya shiga ,gari



Kuci gaba da hak'uri dani pls wlh abubuwa ne sukamin yawa, ga ciwan kai dake damuna kwana biyu insha 'Allah komai na dawowa nomal zaku dinga jina 'akai akai ,kuma zan k'ara yawan rubutun ,nawa, nagode da kulawar ku a gareni🙏




*Dija_Waziri*💉
[18/12 7:32 pm] Dija Waziri: 💉💉💉💉💉💉💉
*DOCTOR HAJAR*👩🏻‍🔬
💉💉💉💉💉💉



Chapter 17

Da sauri Khadee ta juyo tana kallon ta,

"Hajjo lafiyan ki ,kuwa yau?"cewar Basmad "Hajar dake faman shafa mai tace "me kika gani Basmad lfy ta k'alau " tow meyasa zaki hanasu zuwa ?" Shiru tayi batace komai ba taci gaba da 'abunda takeyi..

Khadee dake tsaye na kallon su ,batace komai ba taja hanun Jawahir suka fice , ganin tahowar su Khadee yasa shi saurin fitowa daga cikin mota shima ya nufosu yana murmushi sanye ,yake cikin shadda d'inki tazarce tasha 'aiki hanunsa ya wara yana Kalon Jawahir ,tsayawa Jawahir tayi ,tak'i k'arasawa kusa dashi saida Khadee ta kaleta tace taje sanan tayi saurin zuwa ta rungushe shi d'aukan ta yayi ,yana shafa gashin kanta da suka zubo, Khadee tayi masa iso daya k'arasa ciki babu musu ,suka wuce , ciki ,saida suka gaisa, sanan takawo masa 'abun motsa baki ta, koma ciki tabar shi da Jawahir dake mafan dariya,


Khadee na shiga ciki yanda tabar Hajar haka tazo ,ta ganta zaune ko motsawa batayi ba, murmushi kawai tasaki, tasan Yanzu tace zatayi mata magana sai ,suyi fad'a ran kowa ya b'aci gara ta bita'a hankali ,saida ta k'arasa dabda ita sanan tace "tow Hajjo nikam nagama bak'on ki na jiran ki" ,Hajar batace da ita ufan ba ta mik'e ta zura wata doguwan riga me k'aramin hanu sanan ta zura wani zunbulelen hijabi har k'asa, ko powder bata shafa ba haka ta fice...

"Hajjo uwar masifa wlh tana da matsala" cewar Basmad "ae Basmad wannan cousin d'in taki akwai tsatsauran ra'ayi ,yanzun mafa kafun ta yarda yazo saida Mami tasa baki shigar da nayi nasamu ,Mami nayi mata fad'a ne" Uhmm inde Hajjo ce zata iya fitan kuma tak'i ,kula shi inda kika san me jinu haka take ,ni fad'a ma ,mukayi da ita jiya" haba ke kuwa Basmad dukda bansan meya had'a kuba ,bedace ba kuna yan uwa kinsan Hajjo da sauri k'uluwa abu kad'e ke bata haushi ,ke ,kuma 'akwaiki da zolaya" tow Khadee gara ke ina da 'aiki bana shirya ,yau insha 'Allah zan gama komai jibi zan koma 'abuja "tow Allah ya kaimu, nima Hajjo na dawowa zan tafi gida "


Da salama ta ,tura kofar falon ta shiga kanta 'a sunkuye ta daure fuska ,jawahir kuwa sai wasa ,suke da,dariya kamar bayau ta, tab'a ganin shiba"Dady ga Mummy tazo barinje na d'auko bebyna ,na dawa, "Jawahir ta fad'a yayin da ta sauk'a daga kan cinyar sa ta fice, itako Dr Hajar guri ta nema ta zauna tana wasa da yatsun hanun ta ,tace"ina wuni ciki ciki take gaisuwar kamar baza tayi ba shiko da fara'a ya 'amsa da lfy haka dai ya dinga janta da hira Amman tak'i sakewa jifa jifa nema take amsa masa haka dai har suka gama yaje mota, ya kwaso mata wasu ledoji guda uku manya biyu sai kuma wani d'an daidai guda ,d'aya ya bata manya biyun daya nata ne d'aya na Jawahir k'aramin kuma na Khadee batayi musu ba tasa hanu ta karb'a takumayi godiya ,sukayi salama ya tafi ita kuma tayo ciki .

Koda ta dawo d'aki kan gado ta watsa kayan ta nunawa Khadee nata sanan tahau gado tayi kwanciyar ta ba tare da k'ara kallon ledar ba ,Khadee ko tayi murna sosai takumayi godiya, bud'ewa tayi taga jaka da takalmi ne sai wani mayafi me kyau data bud'e na Jawahir kuwa wasu dogayen riguna, ne masu kyau da tsada kala biyar sai takalmi kala uku da ribbon ribbon masu kyau sai kuma sweet da bistcut, Hajar kuwa dogayen riguna ya siyo mata kala ,kala guda shida da takalmi da jaka da agogo mekyau da tsada "kai gsky cpt yayi kokari Hajjo ,juyo kiga kayan daya siyo miki ,Khadee ta ,tab'a ta "don Allah ki barni Khadee nagani Allah amfana "magana take ba tare data juyo ba "tow yau a tsinki ,kike nikam zan wuce gida "ta mik'e Hajar ma ,mik'ewar tayi ta raka ta har bakin mota sanan ta dawo ciki d'aki ta koma ta kwanta, tana kallo, Jawahir ko sai surutu , take mata ,tun tana biyewa Jawahir gar bacci b'arawo ya sace ta ,ba ita ,ta farko ba sai bayan sallar magrib , Basmad ta gani zaune kan durowan madubi tana shirya 'akwatin ,ta "ke ,kuma ina zuwa?" Dr Hajar ta, tambaya ,da murmushi dauke a fuskar ta" gida man gobe zan koma 'Abuja " cewar basmad "kai harkin gama 'abunda zakiyi Amman dai tare da Jawahir zaku tafi tunda ta samu Hutu taje tayiwa Aunty hutu" yp yanzu ma zan had'a mata kayan ta 'ae ban Isa natafi nabar uwata ba "dariya suduka suka Sa ,sannan Dr Hajar ta shige band'aki ta dauro alola tafito, sallah tayi data idar ,tace da Basmad ta ibi dogayen riguna guda biyu daga cikin Wanda Captain ya kawo mata har a lokacin bata kalle suba bare tasan ya suke Basmad taji dad'i sosai tako dibi masu kyau, a wannan dare Dr Hajar da Basmad har kusan asuba suka ,kai suna hira ,harma sun manta da sunyi fad'a,


K'arfe shabiyu da kusan rabi su Basmad suka tafi Hajar kuma ta wuce hospital


*By Dija_Waziri*💉
[18/12 7:32 pm] Dija Waziri: 💉💉💉💉💉💉💉
*DOCTOR HAJAR*👩🏻‍🔬
💉💉💉💉💉💉

*Ina k'ara baku hakuri da jina shiru kwana biyu ,abubuwa ne sukamin yawa ga wayar tawa yanzu hauka take min ,tow amman yanzu angyara komai ya dawo ,dai-dai ,insha Allah zaku fara jina yanzu akai -akai kamar yanda kuka saba ,nagode da kulawar ku*


*Na sadaukar da shifinnan ga dukkan masoyana na kusani 'ina k'aunar ku akoda yaushe*😍😍

*Ina jidaku Maman khairee Rabi'a haruwa rukky zainab matazu respectable da sauran ku ina jin dadin commentis d'inku sosai love you gus lodi lodi*😍😘

Chapter 19

Hajar ce zaune cikin offce d'inta ,tana duba wasu files ,fuskarta d'auke da farin gilashi ta maida hankalinta kan files d'in dake gaban ta jin kwan-kwasa k'ofar office d'inne ya sa ta d'agowa ba tare da ta ,tambayi waye ba ta bada izinin shigowa , wata nurse ce ta shigo hanun ta d'auke da wani farin envelop cikin girmamawa tace "Doctor gashi wata ,tace a baki, "sai alokacin Hajar ta d'ago ta kalleta ,tace "wata kuma wacece ita ?" Wlh nidai ban san taba hasalima gsky bata, tab'a zuwa asibitanan bama ,kawai ganin ta nayi kuma tana mik'o min takardan ta wuce ba tare da wani k'arin bayani ba" tow ita kuma wacece ,kiramin Dr Khadija 'a office d'inta Hajar tafad'a tana shirin bud'e takardan , rubutu ,ta gani dajan biro kamar haka...

*Ke Hajara kike ,ko wa ki fita daga harkan mijina don naji ance kece wacce ya mato akai tow ,wlh tun muna cikin salin alin kifita harkan Captin Junaid ,don kuwa nawa, ni kad'ai ne ,ke in banda ma shirme irin ,nasa me zeyi dake wacce ta gama zubar da mutuncin ta'a titi wadda tayi cikin shege ,koda yake shid'in duk besan hakan bane ,tow ina jaddad maki da babbar murya da kifita harkan mijina idan ba hakaba zan falasa 'abunda kike b'oye masa ki sani ,nasan duk wani sirrin ki ,kuma nasan duk wani sirrin gidan ku idan kina ,k'aunar iyayen ki da wannan shegiyar yar taki ,tow kifita hanyar mijina don ko ba sa'an yinki bane idan ko baki fita harkan shiba duk abunda ya faru da, d'iyar ki ,kece sila ,sak'o daga matar Captin wanda ze aura ko yak'i ,ko yaso nice matar sa ehee*....


Duk wanda ya ga hajar a wannan lokacin yasan ta shiga tashin hankali mara ,misal tuwa , kallon Khadee ta farayi da fuskar ta dake alamun hawaye, karb'an takardan Khadee tayi ,ta karanta, itama idan ranta yayi dubu toya b'aci, "Hajjo ita kuma wacece dabin diddigi haka ?" Hmmm ina zan santa Khadee idan tayi hak'uri niba, bakuwar zafi bace inde akan ,namiji ne dama ni bason shi nakeyi ba ,kuma insha 'Allah bazan sake ,kula shiba ,bana son wani abu ya samu shegiyar yar tawa kamar yanda ta fad'a haka nake son abata ,Khadee kinga babban dalilin dayasa nace bazan yi aure ba'a rayuwa ta don ko bajima koba dad'i duk mijin dazan aura koshi bemin goriba yan uwansa zasumin "tana maganar tana sheshek'ar kuka, Khadee ko dafe kanta kawai tayi don tama kasa cewa komai ..

Wannan wace irin rayuwa ce ,ya 'Allah kaika jarabceni da wannan abun Allah ka fiddani Allah idan ,nayi maka laifi ne ka yafe min ,natuba ya Allah duk wani me ,mugun ,nufi a kaina 'Allah ka, kareni daga sharrin sa 'Allah wannan jarabawa daka d'aura min Allah ka bani sa'ar cinyewa Allah natufa ,duk a zuciyar ta Hajar keyi tana kuka me tsuma zuciya.

"Kiyi hak'uri Hajjo Allah yana tare dake ,ki dena kuka " dole nayi kuka ,Khadee arayuwa ni shikenan bazanji dadi ba Khadee tun ina k'arama nake cikin bak'in ciki tun shekaruna basu kai na shiga damuwa ba, ko iyayena wlh basu kaini damuwa ba Khadee wannan wace irin rayuwa ce Khadee da wannan rayuwan dama 'Allah ya d'auki raina ,Allah na tufa" subhanallah haba Hajjo sai kace bakiyi 'imani da 'Allah ba 'ashe dama baki yarda, da k'addara ba ?kowa da tasa k'addaran aduniya ke ,kuma tak'i k'addaran ,ce haka mahakurci mawa daci ,komai nisan dare gari zai waye akwai ranar da zaki manta da wannan rayuwan da kike ciki ayanzu ,zai zamo tarihi ,saboda haka na kwab'eki da cewa Allah ya d'auki ranki akan abunda kike tunanin kobajima koba dadi dole zai wuce " gaba d'aya Hajar ji tayi jikinta yayi sanyi don aikin ma da 'alamun yau bazata iya k'arasa shiba dole ta koma gida"nagode Khadee kuma nagodewa Allah da ya kawoki cikin rayuwa ta samun k'awa tagari ,irin ki sai an tona ,ni zan tafi gida, don kuwa bana tunanin zan iya cigaba da 'aikin yau dinnan " Ahaka sukayi salama Hajar jiki babu laka ta fita


****
"Tali wlh baki da kirki ,baki san mutun ba

Please Login or Register in order to submit comment