Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tukun darai da lafiya".

"Ameen" tun daga Ameen d'in da yace be sake cewa komai ba ,sunfi minti goma 'a haka batare da wani yace da wani uffan ba, "Hajjo ya batun ,maganar mu?" Cewar Captian.

"Munyi magana da, Dady jiya ,yace wai ranar jumu'a kazo, ka sameshi bayan sallar jumu'a ...

Muje zuwa🏃‍♀🏃‍♀










*By Dija_Waziri*💉

Team CJ😊
[18/12 7:33 pm] Dija Waziri: 💉💉💉💉💉💉💉
*DOCTOR HAJAR*👩🏻‍🔬
💉💉💉💉💉💉



Chapter 34

Hajiya ce tayi saurin dakatar da Captian "anya Junaid bakayi hauka ba kuwa, yau har lalacewa takai haka ,Samir fa ko ,ka manta waye Samir ne ? Tow ka shiga taitayin ka na gaya maka, ko ance maka, kai kad'ai ne kake shiga irin wannan yanayin arayuwa idan kaji na wani zaka maida naka ba komai bane, kul, kakiyayeni duk wani abunda zakayi ban yarda kayiwa Samir ba ,don ko ya wuce haka'a gurin ka", ta juya da kallon ta kan Samir "kayi hak'uri Samir kaji ina jinka " murmushi Samir ya saki "babu komai Hajiya nasan abunda yakeji sai munyi masa uzuri baya cikin hayacin sa ". Guri Captian ya nema ya zauna zuciyar shi na suya ,don dai Hajiya Mahaifiyar sace babu yanda ya iya da ita da babu abinda zesashi gaya mata magana 'ahalin da yake yanzu don idonshi ya rufe baya ganin kowa sai Hajar.

"Hajiya Hajar macece me kamun kai da mutunci , batun yar kam wannan ba'ayi k'arya ba yar bata da uba Amman hakan ya farune a matsayin k'addara don zan iya cewa reping d'inta 'akayi " inalilahi wa inna ilaihi raji'un amman Samir meyasa, suka b'oye mana basu, sanar damu ba ?".

"Tow a gsky ban san miye dalilin su na b'oye war ba Hajiya ,Hakan da sukayi kuma gsky ba daidai bane". Wlh naga wautan su kaga yanzu Alhaji yace idan yana raye Captian be isa ya 'aure taba ranshi yayi masifar b'aci don ahalin yanzu ma yace Talatu ze aura masa, kuma kasan tsaf ze aikata don shi 'idan yayi magana guda ,d'aya baya kuma maimai tawa , kuma har idan yayi Alk'awari tofa saiya cika yake jin dad'i".

"Subhanallah gsky abu beyi dad'i ba 'amman da yafara zuwa yaji dalilin su kafun ya, yanke hukunci" tow kasan Alhaji da zafi an bashi, shawaran hakan yace bazeje ba ,Amman ,nikam gobe da safe idan yafita office zanyi kok'ari naje ,naji komai".

"Yawwa hakan ma yayi Hajiya 'Allah ya mana jagora " ameen ,ni bazan shiga daga ciki zanyi sallah".

Tashi ,tayi ta shiga ta basu guri, Captian da idon sa, suka cenza kasa zuwa jajazur kamar gauta, ya dubi Samir cikin kunan rai yace " Samir yanzu ashe duk ,kasan wannan zancen kak'i sanar dani ? Miye anfanin abotar mu ,yanzu dama 'akwai abunda zaka iya b'oye min aduniya? "

Samir ,rik'e gefen k'irjinsa dake masa wani 'irin suka ,yayi ,yau sati biyu kenan yana jin ,naman jikinsa nayi masa wani 'irin zafin daya rasa namiye gashi Doc...d'in dake duba shi na ciwan Cancer d'inshi ya fati abrod k'aro karatu, gurin Khadeen daya koma, ma tun ranar da 'aka saka ranar shi da Salma be sake zuwa hospital d'in ba ya dena zuwa k'arb'an magani , idan yaji zuciyar sa nayi masa zafi yakan ,kira Dr aiman gida yazo ya dubashi tow, duk yanzu ya watsar da komai maganin ma ba kasafai yake shaba , ciwo nata cin jikinsa be sani ba gashi yanzu ko abinci baya iya ci kullum sai ruwan shayi .

Karfin halin magana yayi, ya kalli Captian "haba Junaid wannan shine adalcin da zaka man, karfa ka manta yariyar nan buduruwar kace , ya dace ace lokacin da kuka fara deting ka tambayeta wasu yan labarin ta da kuma yanda 'akayi tarabu da mijin ta, tunda 'ae kaganta da yarinya , kuma sau nawa ina ce maka, ka tambayeta kana cemin tow ka tab'a tambaya? Wlh wannan d'in ma 'amana ta bani kade san girman amana babu yanda na iyane kawai yasa na furta kuma sena, nemi gafaran ta dalilin dayasa ban sanar dakai ba kenan ".

Dafashi Captian yayi da yaga 'alamun ranshi ya baci kuma, kamar shima yana da ,wata damuwar da yake b'oyewa "na gamsu abokina kayi hakuri abun da ya faru d'azu wlh bana cikin hayacinane shiyasa, wai meke damun ka nifa tun randa 'aka saka ranar ka ,naga kamar kana cikin damuwa kuma 'akwai abunda kake boyewa ,wanda baka san kowa ya sani gashi duk, ka rame " murmushi Samir yayi yace " ka gama ji da, damuwar ka tukun zan gaya maka, koma miye ni yanzu burina be wuce naga komai ya daidai taba, Hajjo naban tausayi kuma, nasan kai kad'ai ne zaka rik'eta da'amana ba tare da wata, rana ka goran ta mata ba, ni zan wuce gida bani da isashen lfy ".

Tare suka fita saida ya rakashi, har bakin mota sannan ya dawo gida...



Washe gari

Da misalin k'arfe shabiyu na ,rana Hajiya da Fadila sukayi shirin zuwa gidan su Hajar bayan fitan Abba.

Basu wani jima ba suka isa kofar gidan su Hajar , me gadi ne yazo ya bud'e musu k'ofa ,suna fita sukaci karo da kakar su Hajar itama shigowar ta gidan kenan, tana sanye da wata sufa ruwan ganye da ratsin blue tasa wani farin shijabi me hanu, ganin ta yasa hajiya Saurin fita daga motar har k'asa ta duk'a ta gaida ta sannan tayi mata bayanin kosu ,suwaye Kakar su Hajar da fara'a suka gaisa ,sosai sannan ta umarce su da sushiga 'a falon k'asa ,suka zauna duka harda Kakar Hajar d'in ta umarci me aiki data kawo musu lemo da ruwa, sannan tahau sama ta kira su Ummi,.

Jawahir ce ta sauko daga sama da gudu tayo falon ta rungume Kakar , Maman Junaid kuwa tsayawa kawai tayi ,tana ta kallon yarinyar me kyau da ita 'amman wai shegiya ce, ita ,tausayin yar cema taji ya kama ta, suna cikin Haka saiga Dad, da Mami sun sauko har k'asa suka duk'a suka gaida Kakar sannan suka nemi guri suka zauna bayan sun gaisa da Mahaifiyar Junad.

Falon tsi yayi Jawahir na cinyar Kaka tasa Alawuya ta ,kaita gurin Hajar "sanunku sunana Hafsat nice mahaifiyar Junad wanda yake, neman yar wurin ku, nasan zakuyi mamakin dalilin daya sa jiya ba'a zo ba ,nan ta kwashe lbr ta basu, shiru Dady yayi kawai ya tsaya ,yana ,nazari sai daga bisani kuma ya bud'e baki yayi magana " duk naji batun ki Amman da yayi hakuri yazo da kanshi, wa inda 'suka zo neman auren yarinyar nan duk saida nayi bayanin komai sannan daga bisani ,naja d'aya daga cikin su na sanar masa dakomai ,kuma nace ya sanar muku ,don wannan abu ba 'abin boye wa bane tunda harka ce ta 'aure".

"Tow nima dai abun ya d'aure min kai , gsky nasan babu yanda za'ayi ace baku fad'a ba shi Alhaji Samani ne be sanar damu ba," gsky tow sai dai shid'in ae nayi tunanin yaron ya sani ze iya sanar muku " wlh be sani ba duk muma jiya mukeji "

Dady ,yayi wa Hajiya bayanai sosai gome da rayuwan Hajar na baya kuma ta gamsu da ,duk abunda ya fad'a mata, takumayi Alk'awarin sanar da 'Alhaji komai duk abunda suka yanke zata sanar musu ,takuma ,matuk'ar tausayawa Hajar , sunyi magana sosai sannan daga bisani suka, tashi suka ,tafi....


******-

"Tow Alhaji kaji abunda ya faru yanzu miye abunyi , duk mahaifin ta yamin bayani kuma na gamsu, kasan k'addara tana iya fad'awa kan ,kowa kowa da tashi k'addaran tow ita natane yazo da hakan, don Allah kayi hakuri a 'aura wa yaronan yarinyar nan ,shine kawai kwanciyar hankalin mu ,tunda abunnan ya faru wlh duk ya susuce yana ,neman lalacewa ko abinci ma ya dena ci gashi baya samun bacci kullum cikin tunani , tunda kayi tafiya, yau satin ka biyu kenan ,naka sa, samun, nu tsuwa" Hmmm Hafsat kenan tow ni 'ina ruwana ya mutu ma, mana idan shi besan ciwan kansa ba tow ni sanani ,don haka ,ki sanar dashi na bashi nan da sati 1 idan be kawo min wata, matar ba tow ni zan aura masa, wacce naga dama na gama ,magana" fuuu ya tashi ya bar falon..

Sakin baki Hajiya tayi kawai tana kallon shi harya fice, cikin zuciyar ta, tace Allah ya kyauta


Kwance yake ,kan gadon shi duk ya rame yayi wani 'iri kamar bashi ba, wayan shine a hanunsa tun safe yake ,kiran Hajar amman tak'i d'auka yau sati guda kenan bata d'aga wayan shi tun randa yakira tace masa, surabu kawai tunda iyayen shi basa, son auren , har yanzu be hak'ura ba dad'a kira yakeyi dayaga bata da niyar d'agawa saiya tura mata test.

_ Hi Hajjo don Allah ki d'auki waya ta ,wlhi na son ki bazan iya rabuwa dake ba , so tamkar rayuwane, ba ko yaushe yake zamowa abu mai sauk'i ba haka kuma ba'a koda yaushe yake wanzar da farin ciki ba, to amma mene ne zai sa matsawar muna raye da, rai da lfy za mu yanke alak'ar soyayya a tsakanin mu? Har zuwa yau babu kamar ki a cikin zuciyata domin kuwa jin muryar ki a kullum na rubanya adadin soyayyar da na keyi miki a cikin ko wane dare ko safiya .karda ki rabu dani don Allah, domin hakan zai iya sanyawa na zamo mutum ,mai rauni a rayuwata. Ki sani 'ina sonki_

Ya tura, mata sannan ya mik'e ya shiga toilet don watsa ma kanshi ruwa kozai ji dadi cikin zuciyar shi..

Salma ce zaune Falo tana kallon zee word ,jin salamar Dr Samir ne yasata kashe Tv yayin data 'amsa salamar , shigowa cikin falon yayi, ya zauna bashi da wani walwala yana sanye da Jalabiya ga dukkan alamu daga bacci ya tashi wurin k'arfe Biyar "ina Hajiya?" Ya tambaya " tun wurin 4 ta, tafi gidan k'awar ta taje zatayi maka, magana ma tasamu kana bacci, tow bata d'agaka bane saboda tasan kayi aiki ,kagaji kana buk'atar hutu " ok ,kawo min Coffe " mik'ewa tayi, ta kawo masa, tana bashi ya mik'e zebar falon saurin tsaidashi tayi "yaya pls ina son magana dakai " fuskar shi babu walwala ya dawo ya zauna "ina jinki".

Saida ta d'anyi jim kad'an sanan ta kaleshi tace "yaya dama 'akan batun auren mune kaga 'abu sai matsowa yakeyi shiyasa naga ya dace nasanar dakai, wasiyar Aunty Jamila " tana fad'ar haka sai tayi shiru , sai alokacin ya 'ajje coffe d'in hanunshi ya dubeta sosai "ina jinki ".

"Dama Aunty Jami tunkan kuyi aure idan muna zaune agida, muna hira idan mun sako hiran aure sai tace min ita ko mutuwa tayi bata yarda ,wani k'aninta ya 'auri mijin taba , kuma ita har cikin ranta , take fad'i ni kuma tun alokacin ,na d'aukar mata 'alk'awarin hakan bazai tab'a faruwa ba insha 'Allah kuma ,kafin ta rasuma saida ta jadadamin cewar narik'e Alk'awari karnaci amanar ta, kaji dalilina yaya don Allah kasan yanda za'ayi ka fahimtar da Ummi , kaima nasan ba sona kake ba kawai biyayya zakayi pls Yaya don Allah katayani cika wannan alk'awarin dana d'auka ".

"Tow Salma tun farko meyasa baki sanar dani ba ? Ni yanzu bazan iya tunkaran Ummi da wannan maganar ba, gsky garama ke ,kisanar mata da kanki".

"Yaya kana ganin haka babu matsala kana ganin wani abu ,bazai iya faruwa ba gsky bazan iya fad'a mata ba ".

"Tow zan duba nagani zan san abunyi " ya mik'e ya fice , shi kad'ai yasan halin da yake ciki, don jikinsa na bashi ma zeyi wuya Salma ta zama ,matar sa


*By Dija_waziri*
[18/12 7:33 pm] Dija Waziri: 💉💉💉💉💉💉
DR HAJAR 👩‍🔬
💉💉💉💉💉


Chapter 35

Hajar ce zaune cikin lanbun gidan su tana hutawa ,tana sanye da riga da wando na kanti, sai ta d'aura wani boyfriend jacket akai ,kanta sanye da wani hula me kamar toban ,ta kishin gid'a kan wani kujera tana karanta wani ,inglish novel me suna happiness at last gefen ta wani d'an madai-daicin table ne ta 'ajje Apple da kilishi, tana karatu ,tana d'an ci a zahiri kowa ya ganta baze tab'a tsamanin tana da wani damuwa ba , amman cikin zuciyar ta,ita kad'a tasan me take ji.duk da 'acikin kaso100% na damuwar ta ,ta cire kaso 70 a ciki don Doc...yace ta rage sama kanta damuwa idan ba haka ba zai ,iya haifar mata da wani damuwa ,a kullum takan godewa 'ubangiji daya bata ,tawakali da yarda, da k'addara 'akan duk irin yanayin da zata, tsinci kanta , hakan yasa duk irin abunda ze sameta 'a rayuwa takan yi k'okarin ganin ta danne shi.

"Sister " Kalifa ya kira sunan ta ,da sauri ta d'ago ta kalle shi "na'am bro ya work d'in har ka dawo ne ?" Aiki gashi 'inata fama yanzu nakama o shigowata kenan ma, Naga wannan friend d'in, naki yazo shine nace bazan kira mishi ke don ,nasan kinanan gurin ke, dai lanbu ya 'aure ki, kullum idan baki zoba ,baki jin dad'i, ya naki aikin likita bokan turai, ae wannan aikin saike da Dady mukan muna office "ya fad'a 'a zolaye ,murmushi ta saki tace "Aiki Alhmdulh ae kai ragon, namiji ne shiyasa bazaka iya'aikin likita ba "Habawa ,wlh kinsan duk ,da ke yayatace idan 'an had'amu fad'a kin san kezan cuta ni kawai 'aikin likitanne banajin yi barin shiga daga ciki ,kije bak'on ki na jira " tow sai nashigo wai waye bak'on ,nawa ne?" Wannan likitan Dr Samir yake, kowa tow shine yazo" ok pls idan kafita kace yazo inanan ya sameni ?" Ok tam" ya wuce ita kuma, taci gaba da karatun littafin ta,

"Hajar " saurin firgita ,tayi ta juyo da sauri ,tana "wlh ka razanani " tow ba dole ba nafi mintuna ina maki magana kin maida hankalinki ,kan novel ke har kina ma da lokacin karatun ,novel?" Wlh ban tab'a karan tawa ba wannan shine firts tima d'ina da na fara karanta Novel shima wlh gurin Basmad na gani ,itace ma'a bociyar karatun novel ,shine fa ta ban dak'er na karb'a wlh " lokacinne dake ae ni fushi nakeyi dake yau wajen 1 month kenan rabona da naganki, kod'an gaisuwar da mukeyi awaya ma yanzu kin dena ko laifi nayi?"

"Hmm Dr Samir kenan ,ni bance nayi fushi daikai ba sai kai zakace kayi fushi dani, ko ka manta ranar ka' aka sa 'amman ko kabugo ka gaya min ,ni meyasa bance ina fushi dakai ba?" Murmushi yayi, yace "ae gani ,nayi na sanar da mijin ki kuma dama shiya dace ace ya sanar miki" nan da nan ta had'e rai tace "mijin wa 'an shafa mana fatiha dashi ne ko yaya da zakace mijina karka sake fad'an haka don kuwa ni ba mijina bane , kuma naga kafun ,na sanshi kai na fara sani don me sai shi ya fad'a min?" Tow Ran mata ya b'aci fa daga magana har kin wani cenza fuska ,ae idan be zama ba ze ,zaman, nan bada jimawa ba, "bata sake ce dashi komai ba tayi shiru taci gaba da karatun , ta da yaga bata da niyar magana shima sai yayi shirun , ya mik'e Ya nufi gurin wata bishiyar mangoro daf da inda suke a zaune, hannu yasa ya tsinko ganyen mangoron sannan , ya juyo ya fuskan ceta sosai yace "Hajar pls ina son ,magana dake ,kuma nasan bazakiyi min ,musu ba ina kuma fatan ki fahim ci abunda zan gaya mi...." Kafun ya k'arasa tace "idan akan abokin kane bana son jin komai , don munriga mun gama, magana dashi nace yayi hak'uri ya bi umarnin iyayen shi, tunda nid'in ce ba aso ya had'a zuri'a dani ,tow na fasa yaje su bashi wacce tafi dacewa dashi, mutuncina dana iyayena ,nike nema 'aduniya bani da tamkar yasu ,sune kad'ai zasu iya zama dani aduk irin halin da zan shiga'a rayuwa don haka bazan so naga 'anci mutuncin suba Doc... Ada na fara son abokin ka tow amman ayanzu gsky bana son shi kuma bazan iya 'auren shiba sai dai kuma ban san k'addara ba , don Allah idan har zancen sa zakayi ,kayi hakuri bana son ji" shiru Dr Samir yayi, ya kasa cewa komai don kuwa zancen zeyi mata komawa yayi, ya zauna ya fuskanci kujeran da take zaune "kiyi Hakuri Hajar kiyi masu 'uzuri wlh ba laifin iyayen shi bane duk wannan matar da take son shine take had'a komai, amman wlh ,harga 'Allah mahaifiyar Junaid na son ki don kuwa ita 'abunda ,d'anta keso shi 'itama take so , kiyi hakuri " kaga Dr Samir naface maka bana son maganar sa don Allah karabu dani, ae bakaga 'abunda sukayi ma iyayena ba ,dole kazo bani hakuri " kafun ya bud'e baki yayi magana yaji muryan Jawahir ta nufo gurin da gudu tana dariya, dalilin daya sa ya kasa magana kenan, jikin Hajar ta haye tana dariya "Mummy kinga Ancle Kalifa ko, ya tsorata ni " tunda ta shigo ,gurin Dr Samir yasa mata ido wannan shine karo na farko daya fara ganin ta, ya rasa dawa take masa kama don tunda yaga fuskar ta ya fara tunanin akwai wanda ya tab'a gani suna kama da ita 'amman ya rasa 'a ina ya tab'a gani, dukyanda yaso ya tuna ya kasa , kalon ta yayi ,ya kalli Hajar yaga itama suna mugun kama da ita hakan yasa ya gane cewa itace Jawahir lokaci guda yaji son yarinyar har cikin ransa har yana Jin inama shine mahaifin ta, yaji ta shiga ransa ,sosai wani b'an gare na zuciyar sa kuma ya fara jin tausayin yarinyar, idan tagirma tasan matsayin ta ya zataji? Gsky mahaifin ta ya gama cutar, ta'arayuwa 'ayau daze ganshi da saiya kwatar ma Hajar hakkin ta nacin zarafin da yayi mata, yanda yaga Hajar da yar tata suna wasa da, dariya sai yaji sun bashi shi'awa yaji ,inama 'ace Captian be ruga shiba da ya 'aureta ya kuma gina musu wata rayuwan wanda yafi wanda suke ciki jin dad'i amman hakan baze tab'a yuwa ba don kuwa ,ko mutuwa zeyi baze tab'a furta mata yana son taba, tunda har abokin shi kuma 'aminin shi ya riga shi, duk da yana da tabacin cewa koda basu samu, matsala da Captian ba yau ,yace ita yake so zata iya fasa 'auren Captian ta aure shi amman baze tab'a bari hakan ya faru ba, satar kallon su yakeyi suna d'an hiran su irin ,na Uwa da ya, "Hajar wannan itace Jawahir d'inki ?" Ya tambaya, sai alokacin ma ta ,tuna da ashe fa yananna da murmushi ta bashi amsa "Eh itace bama kama Kama kow" ita kuwa jawahir tsireshi da ido tayi tana ta kallon shi "A'a kuna mugun kama da ita sai dai tafiki ,kyau sosai yar tunda naganta naji tashi raina wlh ki barmin ita "dariya Hajar tasa, sosai rabon ta da 'ariya irin haka har ta manta "tow kar ka damu idan ka shirya kazo ka d'auke ta, amman fa bata ji" Jawahir fuska 'a daure tace "Mummy ni bazan bishi ba ni gurin Dady na zaki, kaini kince min ,munkusa komawa 'kuma haryau bamu koma wajen shiba " kallon ta Dr Samir ya tsaya ,yana yi ,yarinya k'arama 'amman sai wayo "zo Jawahir" ya kira sunan ta, tun da yashigo ta, tsireshi da ido taki saukewa "ni bazan zoba " Hajar ta ,tsani Halin Jawahir na tsayawa tana kurawa mutane ido ,dama ga idon manya manya tayi maganar tayi maganar har ta gaji Amman Jawahir bata denawa ita kuma 'abun yana k'ona mata rai wasu ma sai ,suyi tunanin bata mata fad'a ,daka mata, tsawa tayi "ke Jawahir dan gidan ku ban hanaki kallon mutane cikin ido ba ? Kuma sa'an kine shi da zai kira ki ,kice bazaki ba, zaki Wuce ko sai nai ball dake mara kunya kawai" Babu musu Jawahir ta ,wuce, taje gurin Dr Samir" Haba Hajar ki dinga mata uzuri mana yarinya ce fa sai da lallab'i" barni kawai Doc...sau nawa ina hanata irin haka she karunta nawa yanzu 10 fa take nema gara na dinga yi mata fad'an idan ta kama,ma harda, duka zata shiga hankalin ta ,sam yarinyar nan bata gudun b'acin raina duk abunda na hana ta nad'an kwana biyu ne zakaga taci gaba da 'abunta saboda ta rainani" haka zaki ci gaba da hak'uri komai ,mai wucewa ne ,wata rana baza tayi ba" Hajar batace komai ba tad'au ruwan faron dake gefen ta, tahau sha ,shiko ,kama hanun Jawahir yayi ,yace "sorry Beby kinji , ki d'inga jin maganar Mum d'inki kinji kow beby ne nima daga yau Dadyn kine ina kina sona?" D'aga masa kai tayi alamun eh , yayi murmushi yace "gud girl me jin magana , wane school kike zuwa ?" Lokaci guda taji ta sake dashi zama tayi kusa dashi tace "Turkish nike zuwa 'amman ,Mummy tace ,cireni zatayi "a shagwab'e tayi maganar "A'a meyasa Mummy zata cire ki?" Saboda banyi kokari ba nazo ta 3 don Allah Dad kace tayi hakuri Allah next ,tima zanyi kok'ari" tow karki damu zan gaya mata 'amman ki tabata zaki dena wasa, idan kika zo ta 1 nima 'zan baki wani abu amman bazan gaya miki, ko miye ba" tsale tayi ,ta rungume shi ,insha Allah na dena wasa kayan wasan ma ,Mummy ta b'oye su " tow yayi kyau ajinki nawa ?" Primary 5" gud ashe bebyn tamu babba ce idan kin gama karatu me kike son ki zama?" Da sauri tace "Barrister nake so irin ,na Aunty Basma" meyasa kike son zama Barrister?" Shiru tayi batace komai ba sai da ya sake tmby sannan fuskar ta babu walwala tace"saboda na kama ,mutumin da kullum nakeji mummy nayi masa 'Allah ya isa tana cewa ya cuceta kullum ,kuma idan dare yayi sai tayi kuka , shiyasa zan kama shi na kulle shi saboda ya dena zuwa cikin dare yana sa ,Mummy na kuka shiya sa nakeso na zama Barrister" Hajar dake ,karatun littafi kasa karatun tayi ,ta tsaya tana jin yarinya karama kamar Jawahir sai d'an banzan wayo Ashe tana kula da, duk abunda takeyi kenan ,abun na damun ta , kallon Dr Samir tayi suka Had'a ido ya girgiza mata kai, sannan ya koma, da kallon shi kan Jawahir " tow Beby zan tafi gida 'Amman gobe zan dawo na d'auke ki muje musha ice cream ina zaki bini" da saurin ta ,tace "eh zan biki " shafa kanta yayi ,yace "haka nake so Allah yayi miki Albarka " ya mik'e sukayi salama da Hajar ya tafi bai zarce ko ina ba sai gidan su Junaid d'akin shi ya shiga ya sameshi kwance kan gado shi ba ,bacci yakeyi ba ga dukkan alamu ya fad'a kogin tunani ,ne don Har Dr Samir ya k'araso cikin d'akin besan yazo ba, gefen daya zauna kayan abincin da 'aka kawo ma Junaid ne ,na rana be tab'a ko, kad'an ciki ba,"kai " Dr Samir ya tab'o shi, sai a lokacin yayi saurin dawo da hankalin shi " Junaid ka dena sawa kanka damuwa haka fa, ka tashi kaci abinci " Samir ya 'ake ciki bazan iya cin komai a yanzu ba matsawar banji me ake ciki ba ,bazan tab'a samun ,nutsuwa ba Samir ina son Hajjo ina k'aunar ta ,zan iya Mutuwa idan har na rasa ta ka taimakeni " zan taimake, ka Junaid Amman sai kaci abinci tukun " kayi Alk'awarin idan ,naci zaka taimaka min "yes nayi ak'awari" d'aukan abincin yayi ,yaci kad'an yasha ruwa sannan ya dawo ya zauna kusa da Samir "tow ya kukayi da Hajjon " duk yanda sukayi Samir ya kwashe ya fad'a masa , "ya ilahi duk Abba ne ya jamin yanzu ya za'ayi? " tow gsky mafita d'aya ce Junaid shine kawai hanyar da nake tunanin komai zai koma daidai, kuma shine hanyar da nake tunanin Hajjo taza iya komowa gareka ", tow ,wace hanya ce Haka Samir wlh zanbi matsawar bazan cutu ba" tow hanyar dai 'itace Zamu had'a plan ,ne da wani doctor a hospital d'in da nake aiki, ace ma su Abba kana cikin wani hali zaka iya rasa ,rayuwan ka cikin awani ishirin

Please Login or Register in order to submit comment