Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

isa ba na barki lfy "Khadee ta dauki jakarta, ta fice

****
Dr Aiman yanzu ya kake ganin za'ayi wannan abun tsakanina da kaine bana so kowa ya sani promise me bazaka fadawa kowa ba" hmmm Dr Samir kenan basai nama alkawari ba 'amman yanda muke dakai kasan bazan taba fada ma wani sirrin kaba ,ya jikin naka hope yanzu kana samu lfy sosai kow? "Alhmdulh jiki da sauki yanzu kam saidai some times nakanji gefen kirjina namun wani irin zafi da k'una " tow Dr Samir haryanzu baka dena tunane tunanen nakaba kenan kow? " haba ae kasan ina son mum bana son abunda zai tab'a lafiyar ta kuma inajin maganar ta, tunda tamin magana wlh narage ", ae kaji karage fa kace Doctor ya kamata ace kadena ne yanzu kwata kwata cox yanzu abunda ka fad'an tunanin ne ya saka jin haka kuma kana shan sugar sosai kow? " Yes ina shan suga "tow ka dena idan kana son lfyn ka sannan kuma kana shan nonon rak'umi da fitsarinshi kasha kamar na 40 days shima maganine sosai " tab'e fuska Dr Samir yayi yace" fitsarin rakumifa kace da nonon sa? " yes sufa har sunfi maganin da nike baka na hospital " kai gsky bazan iya shaba 'abokina "suna cikin magana, ne sukaji knocking da sauri ta shigo fuskarta ba walwala sosai ,

"A'a Dr Hajar mutuniyar kinanan abunki, kin manta da best friend d'inki "hmm Dr Samir kenan wai namanta dakai kaje ka duba chat d'inmu kaga nayi ma, magana ka share ni "lah sorry wlh bana chat yanzu aiki sunmin yawa Aminu kano ba sauk'i babu hutu " ae kai kaso hakan tun yaushe nace ma kadawo nan muna buk'atar Doctor d'in brin kak'i "cewar Dr Hajar.....

"No bazan dawo ba nafi jin dad'in hospital d'inmu "tow ae kaji dad'i wai meye ma yake kawoka nane naga duk Friday sai kazo? " murmushi yayi, yace "nothing gurin abokina nake zuwa " tow ae yayi kyau doctor Aiman muna da meeting 4:30 "cewar Dr Hajar, "ok Allah ya kaimu d'azu kuma Dr Khadee tace wai sai gobe "Eh da munbari gobe tow dad yayi waya yace ayi kawai " tow Allah ya kaimu "Ameen " hartazo fita taji muryan Dr Samir yana magana "aminiya sai nazo office d'inki yanzu idan na gama zan zo " tab'e baki tayi tace,

"Bana, neman ka "..

"Tow nidai sai nazo "...

"Tow ina jiranka "ta wuce ta, tafi

Dr Aiman ya bawa Dr Samir shawar wari sannan sukayi salama ya wuce office d'in Dr Hajar


Wurin k'arfe biyar da rabi na yamma Dr Samir ya gama abunda yake cikin Babban Asibinti Aminu kano ,fitowa yayi ya shiga motarshi yayi gida, wani k'aton gida ya shiga mention zubi da tsarin gidan yayi tsayawa fasaltashi bata lokacine ,sojojine kewaye a gidan daga get ya fita daga cikin motar yabar driver ya k'arasa fuskarshi babu wani walwala sosai ya shiga cikin wani dank'areren falo, wata jattijuwa ce zaune kan sofa fuskarta d'auke da glass tana karanta jarida gifenta kuma kayan fruit ne da drink masu sanyi daganinta bazata wuce shekara 59 ba, amman tsabar hutu ya ratsata wani ma yace yar shekara 40 ce...

Salamar Dr Samir ne ya k'aste mata karatun da takeyi da fara'a ta d'ago ta amsa...

"Doctor harka dawo how is work?"

"Fine gud afternoon ummi ya gida"

"Fine son gida lfy yanaganka haka wani iri kamar akwai abundake damunka ,kasha maganin ka?"


"Babu komai Ummi wlh kawai nagaji ne ,maganina kuma wlh yau mancewa nayi dasu agida 'amman yanzu ,zanje nasha" Son kafa dena wasa da shan maganin ka ,kaifa yanzu ba yaro bane kuma kafi kowa sanin wace irin ciwo kedamun ka 'amman saikayi ta wasa dashan magani ,kaje kaga Dr Aiman d'in ?"


"Eh d'azu naje ya dubani yakuma ce komai nomal" tow Alhmdul Allah ya k'ara maka lfy son Allah kuma ya baka mata ,tagari don ,nak'osa naga jikokina"...

Murmushi Dr Samir yayi ,yace"Ameen Ummi Barin shiga ciki nad'an watsa ruwa ,wai ina Salma ne ni ?" Salma na d'aki tana karatu exam zasu fara gobe " ok Allah ya bada sa'a" nan ya tashi ya shiga d'akinshi


"Mamana bazan lamuntaba, bazai tab'a yuwuwa ki kawomin wata wanda bansan ko ita waceba, yanzu ba'a yarda ,damutane mutun ba'abin yarda bane gara idan temokon kike sonyi ki temaketa kurabu lfy , ko ,kinmata abundaya faru dake ? Kin manta cewa yardan da kikayi yasa hakan?" Dr Hajar dake zaune kanta 'a k'asa tace mami wance lokacin k'addarace wannan kuma taimako zanyi Mami bana son kuna tunamin abundaya faru shekarun baya "

"tow nidai na fada miki ,karki yarda ki kawomin wata cikin gidana ban yarda ,da wannan ba" ranta 'a 6ace tayi d'akinta tabar Hajar gurin, itama ,mik'ewa tayi Ranta 'a b'ace ta fita daga falon tayi dakinta , tana tunanin mafita.....

Jawahir dake zaune kan bed tana wasa da kayan wasanta ,tayi saurin mik'ewa ta rungume ,mummyn ta tana dariya tace "welcome home mommy how is work? "

Murmushin k'arfin hali tayi "fine beby kinci abinci ?" Jawahir da dariya daga gani tana cikin farin ciki tace "yes mummy naci sosai " gud "Dr hajar tafad'a tana shafa kan yar tata, Shiru Jawahir tayi tana kallon maman, nata tace "Mummy ina dady na ?"

Dr Hajar dake kok'arin cire rigan jikinta ,tayi saurin juyowa ta kalli Jawahir a razane ,nan danan idanunta suka juya suka ,koma jazuri jikinta yayi sanyi , azuciyarta ,tafurta 'ranar da nake gudun faruwa yau gashi ya faru ni yanzu mezance wa Jawahir game da inda mahaifinta yake Akram! Inazan ganka? tab'ata da jawahir tayi shine ya dawo daita daga tunanin data lula....


"Mummy ,yanaga idonki yayi ja bakida lfy ne?" Murmushin k'arfin hali tayi tace"Eh bebyna kaina ke ciwo kibari' idan ,nasamu time zan kaiki gurin dadyn ki" tsale Jawahir tayi kan gadon tana murna zataje taga dadyn ta , Dr Hajar dake ,kallon Jawahir taji wani tausayinta ya kamata a zuciyarta ,tace dakinsan waye ubanki da kinyi regrating kasancewa cikin family dinshi koda yake balefin shi bane lefinane, hawayen daya zubo ta gefen idonta tayi saurin gogewa ba tare da jawahir tagani ba


Tow fa babbar magana waye Akram kuma?

Shin kun yarda Dr takawo, wannan matar cikin family d'inta? Meyi ra'ayunku game da hakan?



*BY DIJA_WAZIRI*🀞
[18/12 7:32 pm] Dija Waziri: πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰
DOCTOR HAJARπŸ‘©πŸ»β€πŸ”¬
πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰

*Ana sanin dad'in haduwane idan an rabu ,godewa ni'imomin Allah wanda ka sani da wanda baka saniba*

*zauna da jama'a lfy domain watarana sune zasuyi rakiyarka izuwa maqabarta*

*kayi tunani mai kyau ka dogara ga 'Allah duk da kuncin rayuwa da kake cikin*

*Ya ubangiji kayi mana tsawon rai mai amfani da, daukaka marar yankewa da lafiya mai dorewa 'Ameen*


Chapter 3

Mik'ewa Jawahir tayi tana dariya ta fita daga d'akin, ita kuwa Dr Hajar dama kamar jira take Jawahir tafice, batasan sanda ta 6arde da wani kuka me tsuma zuciya ba, wanda kowa yaga fiskanta yasan abubuwa sun mata yawa magana ta farayi a zuciya wanda batasan yafito filiba "yazanyi da rayuwata ni shikena haka zan dawama cikin bak'in ciki Akram kacuceni bazan ta6a yafe makaba ka yaudareni kaci amanata ka wargazamin duk wani farin cikina ka rabani.....

Jin Muryan Mami ne yasa ta kasa k'arasa furta abunda take da niyan furtawa" Haba Mamana kukan me kuma kikeyi? bafa nason ganinki cikin damuwa,kodon nayi miki fad'a ne?"

Girgiza kanta tayi alamar A'a "tow meya sameki?" kallon mamin tayi cikin kuka tace Jawahir ne tace tanaso tasan waye Babanta" saida jikin Mami yayi sanyi da taji furucin Dr Hajar. "Sai kika ce mata me?"cikin kuka tace "cewa nayi zan kaita"...

Kallon ta Mami tayi cikin tausayawa tace "abunda nake gude kenan tun baya danake ta binki ,kiyi aure saboda irin wannan ranar, mamana manema nawa sukazo gurinki amman kikayi k'irmisi kice ke ba'aure a ranki? ,da kinyi aure da wlh duk haka baze faru ba dama na gaya miki akwai wannan ranar kuma gashi tazo, yanzu ae , kinwa kanki fad'a kiyi aure Akram de bazaki tab'a ganin shiba don shekara biyar kenan mahaifinki na ,nemanshi amman anrasashi"....

Itadai Dr Hajar batace komaiba har Mami tagama ,mata nasiha ta fita tabar d'akin, ita kuwa wani sabon kukan ta dasa tasan cewa Mami tayi gsky...

Dole tayi aure dole tajanye kudurinta!! kodon saboda Jawahir ta samu rayuwa me kyau , tow tayaya zata kuma yarda ,da wani d'anamiji a rayuwanta ? Akram yariga daya 6ata kowani d'anamiji a gurinta gani take duk maza haka suke ,tow yanzu miye abunyi gashi bataso Jawahir tagirma tasan kow ita wace...hakadai tayi ta tunanin mafita da taga babu mafita dole ta kira Khadee don ita kad'ai ce zata iya taimakon ta kuma gashi sunyi fad'a yaya zatayi? Da wannan tunanin tashiga wanka...



*****

Kwance yake kan lallausar royal ded dinshi wanda yasha kwaliya idonshi a rufe ,fuskarta kawai yake hangowa yana tunanin yaya za'ayi ya malaketa , wayanshi ya zaro daga k'asan fillow yayi dailing number din Khadee bugu d'aya ta daga...

"Hello my dota ya kike?"

"Lfy qlau my father ya aiki? "

"Alhmdulh yasu mama da sauran su ina mutuniya ta? "

"Duk suna lfy tana gidan su "

"Tow masha Allah yanzu ya ake ciki kin mata magane? "

"Np bamuyiba tukun mutuniyar takace yar bori sai anbita a hankali so idan ,nasamu time inaso naje gidan sune sai muyi magana "

"Ok tow thank you so much ni gata zan tafi turkey duk yanda kukayi kin fad'an"...

"Ok Allah ya kiyaye "

"Ameen"...

Nan sukayi salama ya kashe wayan yana murmushi duk wanda yaga fice dinshi yasan yana cikin farin ciki....

*WANENE CAPTAIN JUNAID?*

Captain Junaid haifafen dan garin kano ne su biyar Mahaifinsu ya Haifa shine Babba dagashi sai Atika sai Musa kalamula, sai shabina, sai mina autarsu.


Atiki tana aure a kano musa kuma yana cairo yana karatu (computer science) Shabina kuma tana turkishi (jss 1) Mina kuma batakai zuwa school ba .

Mahaifin Captain ya dauki son duniya ya d'aurawa yaran nashi ,kuma hakan be hanashi basu tarbiyya me kyau ba...

Captain Junaid zaikai shekara 37 Amman haryanzu beyi aure ba babu yanda mahaifinshi beyi dashi yayi aureba yace shi haryanzu be samu wanda yake so ba

Wannan kenankenan

Yana gama waya da Khadee yayi dailing number din best friend nashi Dr Samir, (Dr Samir Abokin shine tun suna wasan k'asa kuma abokaine da Mahaifin Captin Junad da Mahaifin Dr Samin kafun Allah yayiwa Mahaifin Dr Samir rasuwa)....

Bugu d'aya ya d'aga daga bangaren Samirne yayi magana.

"Hello friend ka manta dani kow"...

"Haba dai wlh tunda nazo ban zauna bane ya gida da kowa da kowa ya jikinka hope kana samun sauki sosai?"...

"Hmmm jiki da Sauk'i Friead amman akwai magana kuma secret ne kasan bana b'oye maka damuwata "....

"Tow Allah ubangiji yasa 'Alkairine nima wani labarine dani kuma bazan iya beyema ba nasamu mata".

"Don Allah fa kai congrt gsky nama murna yar ina ce ? Hmmm yar kano ce amman fa tak'i saurarena bare na sanar da ita batuna hasalima sau d'aya na tab'a ganinta"

"Kai freiad wlh kai banzane harna fara hongo irin bidirin dazamuyi aiko baka samu mataba ,da sauran ka"...

"Hhhhh wlh kam da saurana nidai Allah yasa ta karb'eni kana gidane nazo?"....

"Ameen Eh ina gida kasan bani da isashen lfy tow yau jikin nawa babu dadi kuma banaso mum ta ,tada hankalinta...

"Gsky kam tow ganinan zuwa"...

"Ok saikazo ina jiranka "ya kashe wayar...

Wani pic naga ya d'auko daga cikin drow ya tsirawa hoton matar dake jiki kallo , yana kwala ,Allah ya miki rahama Jamila ,I love you so much Jamila nasan bazan samu mace kamar kiba kinmin komai a rayuwa , Jamila haryau kina cikin zuciyata aduk randa na tunaki nakayi kuka yanzune lokacin daya dace ku samu kulawata yanzune lokacin daya dace na saka miki da irin karamcin da kika min yanzune lokacin da yadace kiji dadin rayuwa 'Amman Allah beyi ba Allah yaji kanki keda prince ina matuk'ar jin zafin rabuwa daku shine abunda yake furtawa....


TUNA BAYA (RAYUWAN DR SAMIR)


"Rabi niba me nisan kwana bane nasan mutuwa zanyi wannan ciwan k'afan bakisan yanda yasani a gaba, ba gashi bamuda komai " haba Alhaji ka dena fad'an haka insha Allah zaka samu sauk'i ,karfa ka manta dukkan tsanani yana tare da sauki "Asalamu Alaikum" wa'alakum salam A'a samir harka dawo ina matar taka?" cewar Hajiya "wlh na barota gidan mamanta 'anjima zata dawo , sannu Abba ya jikin ?" Jiki da sauk'i samir " Tow Allah ya k'ara sauki ga kayan marmari na siyo maka "...

"A'a Samir hidimar ae tayi yawa kayi hidima da gida kuma kayi hidima ga d'awai niyar makaranta duk kai daya 'Amman harda hidimar siyomin wani abun kullum ka fita saika rik'omin wani abu " Tow Baba idan ban mukuba wazanwa ni duk abunda zan samu ku nake tunani da kuma ,matata " hakane d'ana Allah ya maka albarka "Ameen Baba Allah ya baka lfy "Ameen"....

Samir a duniya bashi da wanda yake so sama da iyayenshi duk wani abunda yaga zesasu cikin farin ciki tow yana masu daidai gwargwado kuma baya son abunda zai ta6a lfyn jikinsu gashi yanajin maganar su..

Samir be shirya 'aure da wuriba 'amman iyayenshi suka buk'aci had'ashi da Jamila yar k'anwar mahaifin Samir , saboda baya son yi mu ,su musu yasa ya 'amince da auren Jamila wanda ta zame masa tamkar jinin jikinshi takuma zama 'alkairi a rayuwan shi....mahaifin samir talakane yana 'aiki a company din saida taburma kuma ba wani babba bane duka duka Albashinsa naira dubu ishirinne duk wata dashi yake cida gidanshi dakuma biyawa Samir kudin makaranta, kwatsam wata rana aka kulla masa sharri , yayi sata kuma 'Alhalin besan komai ba tow tundaga lokacin suka koreshi daga wajen aiki ya zama bashi da 'aikinyi watarana abincin da zasucima gagaransu yakeyi.....

Suyan Asalin garin kano ne haifafun yan unguwar hausawa 'amman suna zaune a gadon k'aya shekara biyar kenan mahaifin Samir yake tare da laruran ciwan k'afa wanda yayi sanadin dena tafiyarshi kullum ana cikin magani gidan da suke zaune gidan hayane ,Shekarun Samir 19 Aka masa aure lokacin yana level 3 a B.U.K yana karantar medicine fannin kwakwalwa....

"Zaune suke cikin d'aki shida matarshiJamila da bakinta dukya bushi idanunta sukayi ciki ciki ga dukkan alamu yinwa takeji "Jami wlh rashin kud'i beyiba aduniya mutun sai yana da kud'i akeyi dashi kinga yanda nakeshan wulak'anci a school kuwa "hmmm ae sai hakuri rayuwance haka me arziki dashi akeyi" Jami wlh ina shi'awar inga kinyi karatu kin zama gainic dani me arzikine da babu abinda zai hana kiyi karatu "murmushi tayi tace" nasani mijina yanzu dai kai ,kayi din ka gama insha Allah ,Allah ya d'aukaka karatunka kayi kud'i inde muna tare ae zanyi" b'ata fuska Samir yayi yace "banason jin kalmar in muna tare bana hanaki fad'aba isha Allah muna tare har k'arshen rayuwar mu" murmushi tayi kawai tace "Ameen "...

"Kai kinga karna makara inada lecture 10 to 11 kinga kuma har 9 tayi kuma 'a k'afa zani gara na hanzarta karna makara " har bakin k'ofar gida Jami ta raka Samir saidaya k'ule sannan ta shigo gida tana hawaye ,don tana mugun tausayawa mijin nata beci komaiba ya kama hanyar school kuma a k'afa " Allah ka rufa mana 'asiri ta furta azuciyarta....

D'akin Baba ta shiga ta masa yajiki sannan ta fito ,tayi d'akin hajiya ta gaidata sannan taje ta gyara dakinsu tafito tsak'ar gida ta share tayi wanki -wanke, wani tsohon dawa ta dauko wanda kwari harsun fara lalatashi baze wuce kwano d'aya ba ta wankeshi tsaf tasa kayan kamshi ta bayar aka kaimata nik'a ,ta taceshi tayi gasaranta me kyau ta , karare tasa yara suka samo mata a waje tahad'a wuta ta d'aura ruwan zafi bata wani jimaba ta dama kunu me kyau ,

Mayafinta ta d'auka taje shagon kusa da gidan nasu tace ya bata suga na hamsin bashi kafun Samir ya dawo , Sule da yake yana ganin mutuncin Mahaifin samir yasa ya d'auka ya basu.

Dawowa tayi ta zuba sugan Tasawa su Malam nasu takai Hajiya kawai tagani d'akin "A'a Jamila Samir ya dawone?" A'a bedawoba Hajiya ae be jima da tafiya ba " ok ae nazaci ya dawo ya kawo abun karin kumallo ne tow ina kika samo gasara?" Murmushi Jamila tayi tace" wlh randa naje gidan Mamane naga wani gida sunfito da dawa zasu zubar wai ya lalace shine nace suban inaso " Allah sarki rayuwafa kenan abunda wasu ke ganin bashi da 'amfani a gurinsu wasu kuma shi suke gani me amfani Allah ya miki Albarka jamila yajik'an mahaifinki" Ameen Hajiya"....


Shiko samir tunda ya shiga makaranta babu wanda yake tunani sai iyayenshi da matarsa ya barsu babu abinci , karfe 4 suka gama lecturs Amman be koma gidaba har karfe shida na yanma ya tafi neman kud'i amman be samuba sai naira d'ari da yayi dako akasuwa , haka ya koma gida a tsakar gida ya iskesu suna hira nan ya tsuguna ya gaida iyayenshi sannan ya k'arasa ciki don cire kayan jikinshi yayi wanka biyoshi Jamila tayi tana masa sanuda zuwa ,haske fitilar dake dakin ma bakoina take haskawaba tsabar batter ya mutu...

"Sannun da zuwa Dr ya karatu" dama Dr take kiranshi....

"Alhmdul Jami wlh yau narasa yanda zanyi duk aikin danasan zanyi na samu kudi babu kinga d'ari na tsira da ita ,gashi tun safe bakuci komaiba"


murmushi tayi tace "karka damu Mijina da safe na dama musu kunu sunsha da rana kuma sauran tsakin dawan daya rage na tuk'a mana tuwo sai na ranto kayan mida da manja da magi gurin sule na sabain sugan hamsin nayi mana miyar kuka yanzu da dare kuma dama na cika palas da kunu saina iba musu ga naka cenma tare da tuwan ka, wani ajiyar zuciya ya sake yana me k'ara jin son Jamila cikin zuciyar shi.....

Jamila bawata babba bace shekarunta 14 amman idan tana wani abun hartafi wani babban "Jamila Allah ya miki Albarka Allah ya baki abunda kike so " murmushi tayi tace "Ameen Dr



Bayan kwana biyu

Yau Jamila ta tashi taji jikinta duk babu dad'i ga matsanacin ciwan ciki dake damunta da ciwan kai wanda takai sati tanayi da yawan zafin jiki fitsarinta ma ya cenza kala , Hankalin Samir a tashe ya dauketa sai asibitin murtala kafun suga likita duk Jamila tagama galabaita ,tafita hayyacinta ,sun shiga sunga likita yayi mata ,tambayoyi ta kuma amsa bayan ya gamane yace suje suyi gojin ciwan hanta (Hepatitis)..

Jikin Samir duk yayi sanyi sukaje sukayi suka kawo sult , kallon Samir Doctor yayi cikin tausayawa yace " matarka tana dauke da ciwan hanta kuma yaci jikinta sannan tanada juna biyu na wata biyu"...

Lokacin da Samir yaji furucin doctor ji yayi kamar an sara masa guduma akai ita kuwa Jamila hawaye ta soma fitarwa ita tasan bazatayi rayuwa da Samar kamar yanda ta tsarama kanta ba ,cigaba da bayanin doctoe yayi" sannan zaka iya diba idan har baka dena kusantar taba sannan shi wannan cuta ya kasu kashi biyar Hepatitis A Hepatitis B Hepatitis C Hepatitis D Hepatitis E cikinsu akwai masu b'acewa da kansu Bayan sun kama, mutun, wasunsu kuma sai anyi maganai .haka Nan wasunsu basa tsananta wasunsu kuma suna tsananta . Saidai bincike yayi nuni da cewa, Hepatitis A ,Hepatitis B da kuma Hepatitis C Sune sukafi wanzuwa tsakanin mutane .kowacce cikinsu Alamominta ,Abunda yake Haddasata, yanda Ake maganceta,Hanyoyin kamuwa da ita yanda ake kare Afkuwanta ya ban-banta da kowacce . sannan kuma kowanne cikinsu yana da alamomin shi Alamomin Hepatitis A :- mutun zainajin ciwon ciki (Abdominal pain) ,fiver (zafin jiki) , vomiting , tashin zuciya, kasala (fatigue) ,choluria, jaundice symptoms , da sauran su kwata-kwata bata tsananta bayan mutun ya kamu da ita .

Hepatitis B kuma yawan fever, kasala, jaundice symptoms, gudawa, da kuma wasu Alamomi masu kama da cutar flu wani Lokacinma bata nuna alama, tana iya tsananta dakaso goma cikin dari na mutanen da suka kamu da ita Hepatitis C iri dayane da Hepatitis B. Sai dai wannan tana iya tsananta da kaso 75-80 cikin dari na mutanen da suka kamu da ita.
Tsahon kwanaki daga lokacin shirgar kwayar cutar cikin jikin mutun izuwa lokacin bayyanar Alamominta (incubation period) Hepatitis A sati biyu zuwa bakwai .Hepatitis B 6-23 weeks Hepatitis C 2-25 weeks , Abubuwan da suke hadasa ciwan Hepatitis A 'abunda yake haddasata shine wani kwayar cuta da ido baya iya gani mai suna Hepatitis A virus (HAV) Hepatitis B (HVD) ma'ana Hepatitis B Virus ,Hepatitis C (HCV) sannan yawan shan giya ,guba ,(toxic substances) ,matsalar garkuwar jiki (Autoimmune diseases), yin Amfani da kwayoyin magani ba ,bisa k'ainda ba gado (genetic cause), da sauransu na iya haddasa ciwon hanta.

Hanyoyin kamuwa da cutar ,Hepatitis A gurb'atuwar abinci na ruwan sha Wanda ya gaurayu da kashin wani mai d'auke da cutar ,wanda kwaruna (flies) ke yad'awa ,da kuma had'a jiki (body contact) da sauransu , Hepatitis B idan aka sanyawa mutun jinin mai d'auke da ita (transfusion of infected blood ) , yin amfani da 'Allura ko razor na masu d'auke a cutar (use of infected sharp objects), daga uwa zuwa d'anta ,lokacin saduwa da mai d'auke da cutar (sexual contact) ,da sauransu. Hepatitis C sanyawa mutun jinin mai d'auke da cutar ,use of infected sharp objects ,sharing of parsonal hygiene implements, e.t.c nan dai docto ya fada musu abubuwan daya kamata tadingaci wanda ze kara mata lfy tanacin kayan fruit sosai sannan kuma tanashan rake sosai tana shan zuma shan abarba yakuma rubuta musu magani....

Salim bai k'ara shiga tashin hankali ba saida ya je gurin siyan magani yaji suna kira masa wurin dubu goma wanda ko naira biyar ta kanshi bashi dashi a lokacin ,kallon Jamila yayi cikin tausayawa kamar zeyi kuka yace "Jami kinji kudin maganinki kow?" Girgiza masa kai tayi tana hawaye tace"karka tada hankalinka Doctor sauk'i na Allah ne idan Allah ya rubuta zan warke ko babu magani zan warke " Hmm Jami amman ae Allah yace tashi in taimakeka yanzu ke kiwuce gida ni zanje neman kud'i ko wani irin aikine zanyi don naga nasamu kudin da zan siya miki magani"....

Koda Jamila ta koma gida ta sanar dasu Hajiya Abunda likita yace ba k'aramin tausaya mata sukayi ba, Samir kam daya fita aikin dakwan gawayi ya samu akace a kwashe buhu dari biyu yakai kuma gurin da zaikai danisa , idan ya gama za'a bashi dubu uku haka ya dinga jida yana kaiwa tsabar gajiya saida ya fasa buhu biyar a rashin sani mutumin ya dinga masa bala'i ya zaro dubu biyu ya watsa masa dubu dayan yace a bakacin asaran dayayi masa, salim Babu yanda ya iya haka ya kwashi dubu biyun ya tafi kamar zeyi kuka gayunwa da k'ishin ruwa dake damunshi, koda yabar gurin wani aikin yaje ya nema yayi saida ya tabatar ya had'a kudin maganin tukun ya je yasiya ya koma gida....

Rayuwa dai haka tayi ta ,tafiya musu babu dad'i babu walwala ,Jamila kuwa sai jinya takeyi gashi babu wani abu da takeci wanda ze kareta gaciki ya girma duk kayan d'akinta ,tasaida su don suci abinci yanzu bata da komai a d'akinta ko katifa babu....

Salim ko yana final year a b.u.k abubuwa duk sun tab'ar bare mai......

BAYAN WATA TARA

Jamila ce kwance cikin jini sai birgima takeyi tana ihu ,jin ihun tane yasa Hajiya saurin fitowa kwance ta sameta sai nishi take kan d'a ya fara fitowa nan dai hajiya ta taimaka mata har Allah ya sauketa lfy ta haifo san talelen danta fari tas me kama da ubanshi , saidai kuma wani babban matsalan shine Jamila tasuma ta dena motsi jikin hajiya a sanyaye ta gyarata ,takira Samir aka dauketa sai asibiti....

Salim ba k'aramin tashin hankali ya shigaba ,sintiri ya dingayi kofar dakin da aka kwantar da ita , bayan wasu yan mintuna wani doctor ya fito daga cikin dakin fuskarshi ba fara'a, da sauri samir yace "doctor ina fatan lfy" ,kallon shi yayi yace "ka biyoni office "

Suna shiga doctor ya kalli samir da masifa yace "matarka tana cikin matsala kunbar cuta yaci jikinta baku kula da ita yanda ya kamata , kuma gsky cutarnan taci jikinta da yawa hantarta ya dagargaje idan ba sa'a ba ma sai anyi mata tiyata ancenza hantar don zata iya Rasa santa a kowani lokaci, zamuyi admiting dinku harsai Allah yasa

Please Login or Register in order to submit comment