Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da hudu matsawar ba'a maka 'abunda kake so ba ita kuma hajar mukira ta muce gaka zaka mutu ,ta, taimaka mana ka gane?" Yes na gane amman kana ganin babu wata matsala ?" Insha Allah babu matsala " tow tashi muje bana so ma Hajiya ta lek'o ta..


*By Dija~Waziri*πŸ’‰
[18/12 7:33 pm] Dija Waziri: πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰
DR HAJARπŸ‘©β€πŸ”¬
πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰


Na sadaukar da wannan shafin gareki, k'awar arziki action beby tnx for ur love care and support Allah ya barmu tare 😘😘

Chapter 36

Bayan awa biyar

Hajiya ce ta fito daga cikin d'aki da sauri , a burkice, Abba ta samu zaune a falo yana karan ta wasu takardu ganin ta yasa ,shi saurin ajje takardun ya cire tabaron idon shi, "lfy Hajiya kika fito da wannan uban saurin haka?" Ba lfy ba 'Alhaji Junaid yana 'asibiti ba lfy ,yanzu samir ya kira ya sanar dani" dariya Abba yasa, yace "kai wlh kunban dariya wai ko ,kun manta nariga ku zuwa duniya, nifa ba yaro bane ,ni zaku had'a ma plan ba rashin lfy ,yakeyi ba k'arewa 'asibiti ya d'aura wa kanshi, ya mutu ni be shefeni ba " ya maida gilashin sa ya cigaba da, duba takardun sa, sakin baki Hajiya tayi tana kallon shi "yanzu dai Alhaji kana so kace min had'a baki, mukayi kow? Saboda gani mara hankali sai na bari a had'a baki dani ace d'ana bashi da lfy kow? Tow kar ,kaje asibitin ,ni zanje naga halin da, d'ana yake ciki, kuma ka sani wlh d'ana ya mutu ,ta dalilin ka bani bakai na fad'i maka , ta zari mayafin ta, ta fice .

Tana fita ya 'ajje takardan hanun shi ya fara, tunani tunda yaga Hajiya ta, tayar da hankalin ta yasan dole akwai matsala, kuma yasan babu yanda za'ayi a had'a baki da ita 'ayi masa k'arya dole ya tashi ya bita ,tun kafun ta pfice, ba shiri ya d'auki hulan shi ya fice yana fita , ya iske motar zata bar haraban gidan megadi har ya bud'e musu kofa, da sauri yasa 'aka tsaida Drive yaje ya shiga suka tafi.

Mintina kad'an ya kaisu Aminu Kano, basuyi wata ,wata ba suka nufi b'an garen da Samir yace musu an kwantar da ,Captian , suna isa Dr Samir ya nufo inda suke, hankalin shi a mugun tashi "Sannu Hajiya har kun iso?" Hajiya na kuka tace "Eh Samir ya jikin junaid ,d'in ?" Tow gashi nan dai likitoci na kanshi tun d'azu " subhanallah Allah ya bashi lfy zamu iya ganin shi?" Abba ya tambaya " gsky a halin yanzu bazaku iya ganin shiba 'Alhaji sai dai zuwa 'anjima " tow ,wai meyake damun shine " bari yanzu likita ze fito zeyi muku bayani" kafun Samir ya k'arasa maganar ma likitocin suka fito daga cikin d'akin da Junaid yake "yawwa 'Alhaji gama likitan ya fito, Dr Jalo kazo kayi musu bayani " Dr Jalo yana murmushi ya k'araso inda su Hajiya suke tsaye , yace "Dr Samir wainannan sune iyayen yaron ?" Eh suna Dr Jalo kayi musu bayanin komai ni banaje office na dawo" yana kaiwa nan ya wuce yabar su Hajiya da ,Dr Jalo "likita meke damun d'ana don Allah ka sanar dani ?" Abba ya tmby hankalin shi a tashe , hanunu Dr Jalo ya bashi suka gaisa ,sanan yace "kwantar da hankalin ka 'Alhaji muje office zan sanar daku ,komai " babu musu ,sukabi ,bayan shi har cikin office d'in shi ,suna shiga ya basu gurin zama shima ya nemi guri ya zauna yana fuskantar su ,sannan ya fara musu bayani"Alhaji d'an ku yana cikin wani hatsari zuciyar shi ta kunbura kuma zata iya fashewa cikin a wanin tara idan har baku bashi abunda yake so ba, don alamu sun ,nuna yana cikin damuwa ,wanda yayi sanadin kunburin zuciyar sa ,a lokacin da ,Dr Samir ya kawo mana shi ya kawo shine a sume ko nufashi baya iyawa , dak'er muka samu ,muka ceto rayuwan shi saboda haka zeyi wuya, ya rayu cikin a wanini tara nan gaba matsawar baku bashi abunda yake nema ba, ina ganin yakamata ,koda baku san me yake nema ba ya kamata ku bincika, kafun awa tara, idan kuna son rayuwan d'an ku" Abba yana sharara wani uban gumi ya cire hulan kanshi yana share zufar daya kwaranyo masa, Hajiya na kuka tace "ae kaga 'abunda nake gudu yanzu sai kasan yanda zakayi " kallon Doc..Alhaji yayi ,yace "mungode Doc...kuma insha 'Allah zamuyi abunda kace kafin lokaci ya cika " ya mik'e yaja Hajiya zasu fice Dr Jalo yace "Allah ya bada sa'a ya kuma bashi lfy "Abba yace Ameen suka fice ....

Hajiya wuri ta nema ta zauna tana sharan kwala 'Abba ko sai kaiwa da kawowa yakeyi mafita kawai yake nema, da wani 'idon zaije ya tunkari 'iyayen Hajar mezai ce musu, taya zasu yarda haka ya dinga sa k'awa da kwancewa yana ciki haka yaji an dafa shi da sauri ya juyo ,yaga Samir " Sannu Alhaji " Samir ya fad'a , Abba idanun shi sun kad'a sunyi jawur yace "yawwa Samir Doc.. Yamin bayanin komai yanzu ya kake ganin za'ayi , miya dace muyi?" Gyara tsayuwa Dr Samir yayi, ya saki murmushi, tare da farin cikin sun kusa, samun ,nasara .

"Alhaji ni a ganina 'abunyi shine kuje ku samu iyayen Hajar ku fahimci juna, ku basu hakuri, kuma ku fahim tar dasu halin da Junaid ya shiga, ina ganin shine kawai mafita" shiru Alhaji yayi, yana kallon Dr Samir be ce komai ba. Sai daya d'an jima sannan yace.

"Kana ganin iyayen yarinyar zasu amince kuwa ?" Kafun Dr Samir ya bashi Amsa Hajiya ta mik'e tana kuka tace " Alhaji Idan zakazo muje gidan su yariyar nan kazo muje ina Samir zesan da matsala ko babu shine iyayen, yarinyar ? Naga tun farko, kaine ka b'ata lamarinan , kabi abunda Talatu tazo ta d'aura ka'akai yanda ka b'ata sai kaje ka gyara nan gaba dai yanzu saura mana awanni bakwai , cikin sa kuma zamu iya rasa d'anmu idan bamu san abunyi ba".

Abba kallon agogon hanun shi yayi ,yaga saura 'awa bakwai ,kacal ya rage musu, kallon Dr Samir yayi, yace "bari muje mu dawo".

Gudu suke ,kamar zasu tashi sama cikin mintuna kad'an ya kaisu gidan su Hajar , Abba ko bari megadi ya bud'e musu get beyi ba, ya bud'e mota ya fice , ya shiga ,gidan shida Hajiya sunko yi sa'a 'Dady ,yana Haraban farfajiyan gidan yana zaune yana had'a wasu cemicals, ganin su yasa ,shi cire Safar hanun shi, ya umarce su da sushiga cikin falon bak'i, "Ina wuni Alhaji Galadan ci" Abba ya gaida shi ,da fara'a Dr Galadanci yace "barka da rana ya gida, da yaran ka?" Lfy qlau ya naka iyalan ?" Duk lfyn su qalau ince dai lfy na ganku da tsakar ,rana haka?" Kallon Hajiya Abba yayi sannan ya koma da kallon shi kan Dr Galadanci da, dariyan yak'e yace "lfy qlau " tow masha 'Allah barin sa'a kawo maka ruwa Hajiya ke, kuma ,muje ciki sai ku gaisa da Matar gidan" A'a Doc.. Karka damu nasha ruwa zauna kawai ,wata magana, nazo da ita " tow ae babu damuwa ina jinka " Doc.. Nasan banyi dai-dai ba ,ban kuma kyauta muku ba lokacin da yadace nazo ban zoba sai yanzu , ina ,neman alfarma da kuyi hak'uri lokacin abubuwa ne suka min yawa " murmushi Dr Galadanci ya saki yace" mu baka mana laifin komai ba 'Alhaji dena bamu hakuri ae ya wuce wannan zancen yau wata nawa Haka dama 'Allah ya k'addara ba laifin ku bane" , nidai 'ina k'ara baku hakuri Doc.. Duk da k'addara ce atemaka , ayi hakuri na gane komai kuma nafahimta, tunda Hajiya tamin bayanin abunda kace mata, kuma nagane cewa ,wannan abun daya faru da yarinyar ka ba son ranta bane kuma yana iya fad'awa kan kowa , yanzu ayi hakuri a dai-daita sai 'asa ranar ". Dariya Doc..yayi ,yace "ae kun makara ,kayi hak'uri kawai Malam gsky na jima da fasa baku d'iya ta, kuma itama tazo ta shaida min cewa ko ,kundawo ta fasa kuma bata son yaron kaga kenan maganar baiko be taso ba kuyi hak'uri kawai ku bashi 'ita wacce kace ka zab'a masa " innalilahi wa inna ilaihi raji'un Doc... Don girman Allah kuyi hak'uri ka taimakeni , na tabbata idan har ka 'amince itama zata janye pls Doc..." Alhaji Kayi hak'uri don Allah bazan iya baku d'iyata ba ,na fasa, bazan mata, tilas ba, bakuma zan musguna mata ba", Abba ,be sake cewa komai ba sai faman duba 'agogo da yakeyi awani biyar , ya rage musu.

Hajiya ce ta durk'usa gaban Doc.. Tana kuka tace "don Allah don Anabi Doc.. Ka taimaka, min duk wanda ya taimaki wani Allah ze taimake shi d'ana ze mutu awani biyar suka rage masa kacal idan bega yariyar nan ba ze iya rasa ransa don Allah ni ko bazata 'amince ta 'aure shiba don Allah ka, kirata muje asibitin da ita, doc ka dubi darajan haihuwa". Lokaci guda, gaba d'aya jikin Doc.. Yayi sanyi darajan Hajiya ,yasa ze ,janye batun sa don kuwa yana ganin mutuncin ta " tashi Hajiya ki ,koma ki zauna , na janye idan Alkairi ne zaman ta dashi Allah ya nuna mana, barin kira ta , sai dai gsky bazan mata ,tilas ba idan taga zata iya auren sa tow la ba'asa idan kuma tace A"a tow fa bazan tilasta mata ba" ya mik'e yashiga ciki, be jima ba ya dawo shida Mami da Hajar d'in duka, zama tayi gefen kujera, kanta sanye da himar ,cikin ladabi ta gaida su , da fara'a duk suka 'amsa.

Dady ne ya dubeta sannan yace "Hajjo ina fatan dai ko, kin gane suwaye " kanta 'a k'asa tace "Eh Dady na gane su Allah yasa dai lfy " ,yawwa lfy qlau ki ,kwantar da hankalin ki" nan yayi mata bayanin duk yadda sukayi "tow shine ,nike so naji daga ,gareki miye ra'ayin ki don,ni bazan tursasa miki ba, zaki yarda ki aureshi kow yaya ?" Shiru falon yayi ,kowa ya maida hankalin sa kanta, ita kuwa jikinta na b'ari bakin ta na rawa tace " Dady na hakura dashi gsky bazan iya 'auren shiba kuma bazan iya zuwa ko ina, na same shiba saboda" kafun ta k'arasa har Hajiya ta sauko daga inda take zaune ta durk'usa gaban Hajar idanun ta sun rune sun sauya sun koma ,kalan ja "Y'ata don Allah kiyi hak'uri ta dalilin ki d'anan ze rasa, rayuwan shi don Allah kiri hak'uri ki janye batun ki awa uku ,kacel ya rage idan har be samu abunda yake so ba zuciyar sa zata iya bagawa , a matsayina, na mahaifiyar shi 'ina me neman gafaran ki da kiyi hak'uri 'idan ma yayi mak'i wani laifine" gaba d'aya wani ,nauyi da kunyar Hajiya Hajar taji ya kamata, k'atuwar mace kamar ta, ace ta d'urk'usa tana, neman alfarma harda kuka, Haba Hajiya ki tashi wannan abu ,ko tsari babu ya zaki d'urkusa ma yar cikin ki haba ki tashi mana" Mami ta fad'i , tow me nema ,miye bazeyi ba Dole na k'ask'antar da kaina tunda nike ,nema kuma dama don kyautawa gsky ba'a kyauta ma yariyar nan ba " suna cikin maganar ne suka tsinci muryan Hajar tana magana "Hajiya ko baki , durk'usa min ba wlh zanyi hak'uri abunda kika min yanzu banji dad'in shiba naji wani 'iri kamar yanda bazan so uwata, ta durk'usa ma yar, yarinya kamar ni wai da niyar tana, neman alfarma ba haka, kema bazanso hakan ba mutuncin ki da ,darajan ki da k'imar ki da kuma ,karamcin kima sun isa na janye komai Hajiya ke suruka ce me ,mutunci me sanin yakamata, kuma ,me son duk abunda yayan ki ,keso na 'amince zan auri d'anki da zuciya d'aya " da gudu Hajiya ta mik'e ta rungume ta, tana shi mata 'albarka ,Abba ma 'albarkan yake zuba mata Dady da Mami duk sunyi murna kuma suna 'Alfahari da yar su , sun san tarbiyyar da suka bata ,ba'a banza ba..

Hajiya ce ta duba'a gogon hanun ta, taga saura minti d'aya , da sauri suka tashi suka wuce asibiti harda Hajar amman banda Dady da Mami


Muje zuwa


*By Dija_Waziri*πŸ’‰
[18/12 7:33 pm] Dija Waziri: πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰
DR HAJARπŸ‘©β€πŸ”¬
πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰

*INA KIKE MY JANNAT WANNAN PAGE D'IN ,NAKINE KEKE ,KAD'AI , KI SANI 'INAJI DAKE πŸ˜ƒ KED'IN TADABAN CE😘😘



Chapter 37



BAYAN WATA D'AYA

su Hajar sai shirye shiryen biki akeyi don tun sati uku daya wuce aka saka ranar ta da Captian ansa shine dede ,dana Dr Samir rana d'aya za'a d'aura 'auren Samir dana Salma da kuma Captian da Hajar yau saura kwana 60 bikin su wata biyu kenan..

Ta b'an garen Salma babu 'abinda take shiryawa don ita dama bason auren takeyi ba, haka shima Dr Samir Babu abinda yake shiryawa hatta 'akwati Ummi ce me had'awa don shi besan komai game da 'hidimar da 'akeyi ba, shi cikin kwanakin ma sam baya jin dadin jikin shi gashi sam yak'i zuwa 'asibiti , idan Ummi ta, tambaye shi sai yace yana zuwa , yanzu ko ,kaki yayi sai yaga jiki ,kuma kullum sai yayi aman jini guda guda 'amman yak'i sanar da kowa har Captian be gaya mishi ba gashi sai ya dinga jin cikin shi kamar an hura masa wuta, duk ya rame yayi bak'i , Ummi ta kula da ramar tasa, amman sai ta bari akan, kodon zeyi aure ne yasa haka.

***

Zaune suke d'akin Junaid , junaid na k'irga wasu kud'i da zebawa Hajar yayi fari yayi frish ya k'ara kyau da k'iba , sai jan Samir yake da hira 'amman Samir yak'i sakewa dashi suyi hiran kamar yanda suka saba" Samir wai meke damun kane kwana biyu kwata -kwata na kasa gane maka ? Kai ,naga kod'an murnan zakayi auren ma bakayi, ko aurene baka son yi ko, kuma Salman ce baka so?".

Murmushi Dr Samir yayi wanda iyakanshi fatar baki ne ,yace "duk abunda ka fad'a basu ,suke damuna ba Junaid , ni dama kaji na tab'a maganar aure na?" Gsky ban tab'aji ba " tow kagani 'ina ganin ma zance wa Ummi a d'aga bikin ,nawa " da sauri Junaid yace Akan me?" Saboda bana son barin yarinya k'arama cikin k'unci Salma bata sona 'a yanzu saboda wasu dalilai amman ,nasan da zaran, na 'aureta zata soni, tow bana so ,sai ta fad'a kogin sona kuma na barta kaga najefa rayuwan ta cikin hatsari , nafiso ta 'auri wanda zasu jima suna rayuwa kuma su hayyafa subar masuyi musu add'u".

Junaid cikin rashin Fahimta yace "Samir ban gane me kake nufi ba , kana ,nufin kace min zaka saketa kenan idan ka 'aure ta, koya 'abun yake" ba haka nake ,nufi ba Junaid abunda nake nufi shine mutuwa zanyi Junaid inaji a jikina bazan kuma wani dad'ewa 'a duniya ba 'Kuma ina rok'on Allah ya nuna min ranar auren ka da Hajar shine babban, burina , na k'arshe arayuwa naga kun zama, miji da mata ina da ,damuwa Junaid amman ,na barwa zuciya ta kuma ,koze kasheni wlh bazan furtashi ba dagani sai mahalicina mu kad'ai muka san miye shi" Haba Samir idan kana irin wainan magan ganun kana ,karya min zuciya, ka sani fa cuta bata kisa sai 'idan ajalin mutun yayi don Allah kadena irin wainan magan ganun ".

"Tow Junaid na dena 'Amman inaji ajikina kamar wani abu ze faru dani cikin, kwanakinan haka nakeji don ,nayi wani mugun mafarki jiya, wanda ina tsoron ya zama gsky " ina fatan kayi sadaka?" Eh nayi sadaka" tow insha 'Allah babu ,abinda ze faru sai alkairi " tow Allah yasa Junaid ni zan koma gida, gobe zanyi shirin tafiya Turkey sai nan da 1 month zan dawo" tow abokina 'Allah ya kiyaye ,ya kuma dawo dakai lfy ".


Su khadee itace babbar k'awar Amarya tunda 'aka saka rana dayake badayawa 'aka saka ba Khadee ta, tare gidan Su Hajar tare suke zurga zurgan su, Basmad ma kullum tana hanyar gidan,da tsohon cikin ta , Hajar ta saki jikin ta da Captian sosai soyayya suke zabgawa ita dashi, a yanzu har tana jin bazata iya rayuwa babu shi ba 'a kullum idan basuyi waya dashi da yawa ba tow shine sau goma , tsantsar soyayya suke nunawa junan su na gaskiya kuma, me tsafta, Hajar a yanzu ita har tamanta da rayuwan ta na baya, wanda takeyi ,yanzu shine kawai a gaban ta ,bama ta ,tuna wance.

****

"Mrs Jumaid Khadee ta Kira Hajar don da sunan take ,kiran ta , da murmushi Hajar ta 'amsa da "na'am Khadee na lfy nasan baki ,kirana da wannan sunan sai da, dalili ". Murmushi Khadee tayi ,tace dama tmbyn ki zanyi wai 'ina masoyin ki Dr Samir ne ko ,kin dena son shi yanzu?" Azolaye tayi maganar " ki ce min ango Samir dai ban dena son shiba gani, nayi ,yamin, nisa , kuma 'abokin shi naso na shiyasa na hak'ura dashi Amman wlh ,har yanzu ina son shi, ae Salma ta more don kuwa ta samu , miji me hak'uri da sanin ya kamata ,gashi da kawaici wlh ina tayata, murna , inama ace Junaid ne me irin halin shi wlh da bani da matsala" tow shi kuma Junaid me yayi ?" Beyi komai bafa ni matsala ta dashi abu guda biyu ne , wannan rashin yardar tashi da kuma d'an banzar kishin sa, kifa duba ranan ze taran jama'a 'a hospital don yaga Dr Aiman a motata " ki dinga masa uziri duk cikin sone, yanzu dai kina ,nufin kice kin fi son Samir akanshi kenan ,?saina fad'a masa".

"Ki rufa min asiri Khadee ni bance ba kibar ma zancen , kar uwar surutu Basmad tajimu , taje tayi sub'utar baki " dariya sosai Khadee tayi ,tace ba ruwana idan tajiyo ki..





Karfa ku shagala 'Akram yana hanyaπŸ€—




*By Dija_Waziri*πŸ’‰
[18/12 7:33 pm] Dija Waziri: πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰
DR HAJARπŸ‘©β€πŸ”¬
πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰

*Na sadaukar da wannan shafin gare ku dukkan masoyana ,na.*

*Kusani 'ina ji daku ,kuma ina k'aunar ku sosai, naji dad'i da irin k'aunar da kuka nuna min lokacin da kuka jini shiru da kulawar ku agare ni.*

*Dama baka gane masoyan ka sai ran da 'akajika shiru, bani da 'abunda zan ce muku sai godiya da fatan Alkairi*😘


*Masoyi duk inda yake baya b'uya so gamon jini , Action bazan gaji da mik'a godiya ta gareki ba, nagode nagode Allah ya barmu tare yabar zumunci, Ana tare sosai sosai*🀝❀❀


Chapter 38


Yau biki ya rage saura ,sati d'aya, Dr Samir ya kira Ummi ya sanar da ita cewa ,yau ze dawo gida najeriya , yanzu haka ma yana filin jirgi...



Istanbul
Tunda ya fito daga otal d'in shi yakejin fad'uwar gaba har ya isa filin jirgi , awan shi d'aya jirgin su ya d'aga daga istanbul zuwa najeri, yaso yabi k'asa me tsarki amman hakan be yuwu ba..

****

"Beby kwana biyu kin min horo da ganin fuskar ki ,meyasa? Ko wayar kima ya dena shiga, gaskiya idan haka wannan gyaran jikin yake a barshi kawai", dariya Hajar tayi da muryan ta me zak'i tace "sorry dear wlh Mami ce ta hanani fita ko ina yanzun ma bata, san ,nafito ba wayata, kuma Jawahir ta ,jefa min shi cikin ruwa yana gurin gyara Fadil ya kaimin , kayi hakuri kwana, nawa ya rage zakayi ta ganina harsai ka gaji dani" haba 'ae bazan tab'a gajiya dake ba ,kin tab'a jin masoyi ,ya gaji da masoyiyar shi?" Sunkuyar da kanta, tayi alamun kunya tace"dear barin shiga ciki ,kad Mami ta , nemeni "tam zan rabu dake ne ba'a son raina ba, don kar Mami tayi fad'a bana son b'acin ranki, hope babu abinda kike buk'ata ?" Eh ayanzu kam babu amman idan ma 'akwai zan gaya maka ta wayar Khadee, wai ni 'ina Dr Samir ne ?".

"Samir yau ,watanshi d'aya da sati uku a Turkey ,yau ,yana hanya halama ya kusa, isowa don yace idan ya iso ze kirani,naje na d'aukeshi a filin jirgi" lalle a gaida Yayana ,yana 'Angon ze kama hanya, ya wani tafi wata k'asa me nakon ya bari ayi auren tunda yakusa, sai su tafi ,tare" kema dai kin fad'a kibar Samir kawai na rasa meke damun shi, hatta kayan dazesa ,saini nakai masa d'inki na had'a da nawa baya komai akan bikin duk ni keyi masa" tow miye dalili, ko yana tuna matar shine don gsky ,yanda naji lbrn ta ba k'aramin so yake mata ba, " gsky ,yaso Jamila ko nace har yanzu yana son ta, yak'i cireta cikin zuciyar shi sam , don ma k'anwar ta ze aura " au kar ,kace min Salma k'anwar matar sace ?" Dama baki da lbr uwa d'aya 'uba d'aya ma kuwa " Allah Sarki wlh bani da lbr Ashe Sister d'in tane ,ae.yarinyar akwai kirki sau ,uku muna had'uwa da ita " ae Salma kam tana da kirki ,ga son jam'a kowa nata ne"gsky kam tow Dear Bye sai munyi waya " ok i love u " love u too" ta shige ciki shima yayi motar sa...


BAYAN AWA GOMA SHA UKU

UMMI ce kwance kan sofa tana kallon ,NTA ganin wani jirgin sama na hayak'i ne yasa, ta saurin mik'ewa ta k'ara volum d'in talabiJin d'in ta fara jin labaran kamar haka..

~innalilahi wa inna ilaihi raji'un ayaune da misalin k'arfe bakyau na dare, wannan babban jirgin me suna ******* ya samu hatsari a daidai ,inda ze sadashi da filin jinrgin saman, nan garin kano, wanda mutane kimanin guda d'ari biyu ne cikin wannan jirgi, duk sun rasa, rayukan su ,sai mutane biyu da suke da sauran, nufashi a duniya tow suma dai rai na hanun Allah Jami'an kula da lfy sun tafi dasu, Hajar Hospital ,tow jima'a sai a garzaya idan kayi sa'a da ,d'an uwan ka ciki tow ,wainan mamata kuma ubangiji yaji k'ansu da rahama labaran kenan~…

hannu Salma tasa 'akai tana kiran sunan Allah, Ummi kuwa mik'ewa tayi ,tana kiran ,number d'in Dr Samir akashe, han kalinta idan yayi dubu ya tashi , kiran wayan Captian tayi bugu d'aya ya d'aga da 'alamun tashin hankali a tare dashi, shima .

"Hello Junaid kana inane pls?".

Muryan shi ciki ciki yace "ina hanyar komawa gida Ummi lfy dai kow?".

Muryan ta da 'alamun kuka tace "Junaid ba lfy ba Junaid Jirgin su, Samir yayi hatsari yanzu muka gani a labarai, kuma duk yan cikin jirgin sun rasu mutane biyu ne kawai sukayi saura ".

"Innalilahi anya kuwa jirgin su , Samir ne Ummi ? Shifa sai 8 zasu ,sauka ".

A wannan karon Ummi kasa jurewa tayi ,kuka takeyi sosai tace "Junaid Jirgin su ,Samir ne don Allah kazo ka, kaini asibiti naga ko hardashi cikin wainda 'aka ,suke cen".

"Tow Ummi ki jira ni yanzu ,zan iso" ya kashe wayar ya juya kan motar sa zuwa gidan su ,Samir yana cikin far gaba da tashin hankali ,sai kiran wayar Samir yakeyi akashe..

******

Su Basmad ne zaune cikin d'akin Hajar tare da. Sauran yan uwan su Hajar yan mata suna kallo Khadee ,dataga hankalin su duk baya kan tibin yasa, ta d'auki remot ta cenja zuwa NTA dayake ita ma'a bociyar son labarai ce, tana kaiwai taga 'ana ,nuna yanda hatsarin ya faru..

Hajar kuwa shigowa d'akin tayi dede lokacin da labaran ya k'are ,amman taga dai jirgi naci da wuta, kallon Khadee tayi ,tace "Khadee lfy kuwa naga jirgi naci da wuta kuma ,kamar a kano ,nema nan d'in?" Sai a lokacin yan d'akin suma suka maida kallon su kan Tv.

"Hmmm kedai bari Hajjo wlh abun babu dad'in ji abun ma be jima da faruwa ba ,minti ,talatin kenan da faruwan Hakan , wai jirgin ya samu hatsari duk yan ciki sun rasu, mutane biyu suka tsira, Hospital d'inmu ,ma 'aka ,kaisu ,suma kuma rai na hanun Allah daya…"

Kafun Khadee ta k'arasa zancen ta har Hajar ta zube a wurin a sume, han kalin su Khadee yayi masifar tashi ,sukayi kanta ,suna ihu wasu kuma suka fita kiran Dady da Mami..



*BY DIJA_WAZIRI*πŸ’‰
[18/12 7:33 pm] Dija Waziri: πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰
DR HAJARπŸ‘©β€πŸ”¬
πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰


*YAN UWA MASU DAD'I , WANNAN SHAFIN GABAKI D'AYAN SHI SADAUKARWA CE , GAREKU YAN UWANA 'ABUN ALFAHARI NA*😍

*ADDA SADIYA WAZIRI, NANA WAZIRI, MIEMIE WAZIRI, WALIDA WAZIRI, UMMI SALMA, BEBY

Please Login or Register in order to submit comment