Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

jira mezatace ba yafice

"Happy birthday Hajar wlh na manta yau ne birthday d'inki " tnx Khadee ' tacigaba da rubutun da take tun d'azu don bata da niyar bud'e kwalin ma, suko su Khadee cigaba da hiransu sukayi, wayanta da yayi ring ne yasa ta 'ajje bairo dake hannunta, taga me kiran wayan....

Captin Junaid taga 'anrubuta kamar yanda Khadee tayi mata seving, babu wani fargaba ko tashin hankali ta d'auki wayen, daga b'angaren shine yayi magana...

"Hello my angel how are you? "..

Fusk'ata ba fara'a tace"I'm gud "..

"Masha Allah ya beby? "

Maganar ce tajishi wani ban barakwai ya 'akayi yasan tana da beby bayan koyan hospital d'insu babu wanda ya sani hasalima daga Khadee sai Basmad sai iyayen ta su kad'ai suka sani, sai cen tatuna ranar da ya kaita gida yaga Jawahir....

"Lfynta qlau " tana maganar kamar baza tayi ba ...

"Tow ashafa min kanta kafun nadawo nagan ta "..

"Tow zataji "...

"Nagode, dama nabugo naji muryan ki "....

Bata bashi amsaba tace sai anjima takashe wayar....

"Dawa kike waya Dr Hajar? " Khadee ta, tambaya "dawa kuwa zanyi waya in banda ,d'an nacin cen " murmushi Khadee tayi tace "kideyi hankali karki fara sonshi kizo kiji kunya" Hajar batace da ita komaiba tacigaba da 'abunda takeyi , "wai miye cikin kwalinan ne idan bazaki bud'eba ni barin bud'e " Basmad ta fad'a tana shirin bud'ewa..

"Wow "

Shine abunda ,Basmad ,da khadee sukace , birthday cake ne aciki red volved cake me shep d'in heart yasha kwaliya anrufeshi da red icen sai kwaliyan jiki fari anrubita Happy birthday my lovely friend a jiki abun gwanin ban shi'awa.

Ta gefen idon Dr Hajar ta 'akilli cake d'in ita kanta ya balain burge ta, amman tashare tacigaba da rubutun ta..

"Hajjo gsky friend d'inanan naki naji dake sosai wannan irin abu haka gsky ,yayi kyau " cewar Bersmed, ita kuwa Khadee ganin cake d'innan, ne ya k'ara tabatar mata da cewar Dr Samir yana son Dr Hajar....


Kuyi hakuri da wannan,

Nasan tamboyoyi ne mak'il cikin zuyiyan ku, kubini sanu ahankali zan amsa muku su


Shin kuna ganin Dr zata fara son captin?


Kuna ganin maganar Khadee zai ,zama gsky?

SAI NAJI AMSAR KU ZANCI GABA

*BY DIJA_WAZIRI*🤞
[18/12 7:32 pm] Dija Waziri: 💉💉💉💉💉💉💉
*DOCTOR HAJAR*👩🏻‍🔬
💉💉💉💉💉💉

this page goes to you may lovely sister Aisha Abbakar thanks for always supporting me, and encouraging me you 're a true friend and l want you to know how much l love and appreciate ur effort . You 'are the best ❤❤😍😍


Chapter 8


"Ummi shikuma wannan letter na miye shi ? Kuma pic d'in wacece wannan? Wacece ita? Meyasa kike kuka Ummi kinsan aduniya babu wanda nake so, sama dake bana son ganin hawayen ki "....

"Kafun mahaifinka ya rasu yabani yace nabaka Samir ka bud'e ka, karanta zakaga komai", shidai Samir be gane komai ba ya bud'e pepar ya karanta sannan ya dubi Ummi cikin tashin hankali yace...

"Ummi, ki kwantar da hankalinki kiyi shiru insha Allah zanje inyi "iya bakin kok'arina zan cikawa Abba burin shi " yawwa Doc... Don Allah duk yadda za'ayi kanemo d'an uwanka mahaifinka da bak'in cikin rashin d'an uwanka ya mutu be ta6a nuna maka bane soboda baya son ganinka cikin bak'in ciki".

"Insha Allah idan ,nasamu tima next week zani ijift d'in don ganin ,nagano inda suke...


******

Gida suka dawo Basmad tun a mota ,takejan Hajar da surutu amman Hajar fir tak'i sakewa suyi hira don bata buk'atar magana tana son keb'ewa ita kad'ai don tasamu damar bawa kanta 'amsoshin tmbyn ta. Suna shiga ciki, direct d'akin ta suka wuce kwance suka samu Jawahir daga ita sai pant tana gema cikin tab d'inta , ganin shigowan sune yasa tayi saurin ajje tab d'in tayi hugging Hajar tana oyoyo Mumy , itama Hajard'in ruguman ta ,tayi "my beby ya kike " lfy qlau Mumy i miss you so much" shafa gashin kanta ,tayi tace me two darling ina kayanki? " b'ata fuska Jawahir tayi tace "Mummy zafi nakeji shiyasa ban saba " sai alokacin Dr takula da ac d'anki ba'a kunne yakeba, d'aukan remot tayi tafara kunnawa...

"Aunty Basmard gud afternoon? ".

"Nayi fushi tunda sai yanzu kika tuna dani Mummy d'inki kawai kika sani ni kodan hugging d'inma baza'a min ba" Sorry Aunty tayi saurin rugumeta, tana dariya....

Jawahir yarinyace k'an k'anuwa duka-duka shekarunta 6 amman idan tana wani abun kamar wata babba, ga shegen wayo kamar dila, aduniya babu wanda takeso masa da mahaifiyar ta bataso taganta cikin wani yanayi, wataran idan taga maman, nakuka itama saita sata gaba suyi tayi tare, tunda take bata ,tab'a ganin baban taba ko'a hoto kullum mahaifiyar ta, take gani sai kakanin ta bata zuwa ko ina daga school sai gida sai kuma gidan Kakar su Hajar shikenan inda take zuwa..

Basmad ,data huta ,tayi wanka taci abinci d'aukan Jawahir tayi suka nufi BQ d'in gidan suna yan hiransu , ita kuma Dr Hajar wanka, kawai tayi tasa kaya marasa nauyi kasa cin abinci tayi sai ruwan Lipton data d'ansha, shima kad'an, kwanciya tayi tad'an kishingid'a tana kallon tv dake manne jikin bangon d'akin mbc Bollywood take kallah ammah ga dukkan alamu ba film d'in da 'akeyi take kallo ba ta, tafi duniyar tunani ...

K'aran wayan tane yayi saurin dawo da ita ganin, number d'in Doc... Yasa tayi saurin dagawa cikin muryanta me kwantar da hankali tace.....

"Asalamu'alaikum"..

Lumshe idonshi yayi don dukranda yaji muryanta sai yaji wani abu ya tsarga mishi

"Was'alaikum salam Doc.. Ya kike ya 'aiki? "...

"Lfy qlau aiki Alhmdulh ya jikin naka?, naga cake thank you "...


"Jiki da sauk'i gobe zanzo hospital d'in ae "...

"Tow Allah ya k'ara sauk'i wai me kake zuwa yi wurin Dr Aiman duk Friday ne? "....

"Babu komai zan gaya miki amman bayanzu ba "..

"Tow sai yaushe kenan baka yarda, daniba karfa ka manta I'm your friend yanzu akwai abunda zaka iya boyemin ?"....


"No karki dauka da wata manufa Allah i promise you zan fad'a miki, niko na yarda dake 100% amman ke haryau baki yarda, daniba don ban ta6a sanin wani abu nakiba duk shekarun da mukayi muna tare"...

Bezama wajibi kuma kasani ba kama dena saran zaka sani don think you know me you only know what i allow you to know cox ban yarda, dakuba tafad'a cikin zuciyar ta 'azahiri kuma tace...

"Ae bani da wata damuwa shiyasa 'amman da inadashi zan nemi shawaran ka "...

"Ban yarda ba Dr nifa ba k'aramin yaro bane wlh duk wanda ya tsaya, ya kalli cikin idonki sosai zaisan kina da damuwa sosai ae labarin zuciya 'a tmby fuska tafad'a "...

Some time abubuwan Doc... Suna d'aure mata kai duk abunda take yana kula da ita ya 'akayi yasan tana cikin damuwa? 'abunda sai wanda taga dama ya sani sannan yake sani...

"Bani da, damuwa Doc... Believe me "...

"Tow nayarda yanzu ki shirya zanzo mufita yau anjima wurin 5 o'clock "...

Yace mata ya, yardane don bayaso suja zance amman azahiri yasan tanada, damuwa


Wani yawu taji ta had'iya lokaci guda zuciyarta, tafara mata zafi da taji furucinsa na k'arshe sake maimai tawa tayi cikin zuciyar ta, ki shirya zamu fita karfe 5 ,shiru tayi batace dashi komai ba kuma bata kashe watar ba saida hawaye data fara zubda wa...

"Hello Doc.. yanaji kinyi shiru ko akwai wani abune? "..


Lokaci guda muryanta ya cenza

"Babu komai amman kayi hakuri bazan iya ba "...

Cikin tashin hankali dajin muyanta kamar maikuka yasa yace...

"Meyasa Hajar? Meyasa daga magana kuma naji muryan ki ya koma na kuka ranki, kamar ya b'aci? "..

"Bubu komai Doc.... Zamuyi waya letar " batajira mezai ceba takashe wayar.....

Shiko sai hello- hello yake wasu tunanuka ne suka fara zuwa ma,

Tow ko miye dalilinta nacewa 'a'a? Ko batayarda, dashi bane? hakadai ya ringa tunani kala kala...


Tana kashe wayar tayi cilli da ita, ta juya fuskarta jikin fillo tana wani irin kuma me cida zuci ..



TUNA BAYA


Dr Hajar macece mai adini tasan yakamata mace me kamun kai me tarbiyya, ita sam batasa love a rayuwan taba karatunta kwai tasa gaba...

Kwatsam saiga 'Akram yazo yashiga rayuwan ta shine ya ruguza mata duk wani burinta, tun bata 'amince da Soyayyar Akramba tsabar naci irin nashi sai da yasa ta yarda, da soyayyar sa...

Lokacin da takamu da son Akram tana final year a matakin karatunta 'ak'asar chaina, soyayya suke me ciki da 'abun shi'awa da tsafta wasu lokunta Akram ya kanyi, yinkurin ta6a wani sassa najikin ta 'amman saita nuna mishi bataso hakan badaidai bane..

Tow tunda Akram ya lura da bataso, ita ba irin matan daya saba kulawa bane watsatsu sai yake, kiyaye wa..

Akwana 'a tashi bawuya agurin Allah Dr Hajar harta kamala karatunta tadawo gida, wata rana Babanta ya kirata cikin ladabi taje "Dad gani" yawwa Hajjo kina lfy? " lfy qlau Dad" tow masha Allah"...

"Dama inaso na miki wata, tambaya ne " tow Dad Allah yasa nasani" saida ya d'anyi jim kad'an sannan yace "miye tsakaninki da wannan yaron da kullum yake zuwa? "...

Shiru tayi taji kunya ta kamata, tace "Dad shine wanda nake fad'awa Ummi " ok tow... Tow dama shine tow kiyi masa magana kice ina nemansa gobe da yamma " tow Dad insha 'Allah zan fad'a masa "...

Bayan da Dr Hajar tabar gurin Dad Akram takira ta sanar dashi abunda Dad ya gaya mata, shikuma ya 'amince zaizo goben...

Washe gari da 'Akram ya tashi zuwa gurin wani abokinsa yaje ya aro babban riga dahula yasa, yayi shigan mutunci ya b'oye gashin da yake tarawa da hula...

Dad na ganinshi yaji yaron ya kwanta masa 'arai rusunawa yayi har k'asa ya gaida, Dad " Barka da yamma Alhaji ina wuni? " fuskar Dad, d'auke da murmushi yace "Barka dai lfy qlau ya gidan naku? " Alhmdullh" tow masha Allah " kaine kake neman Hajjo kow? " Eh nine Alhaji " kanshi a sunkuye yake bada "Amsa..

"Tow yayi kyau, kai d'an wani garine yaya sunan mahaifinka? " shiru yayi, yashiga tunani don baitab'a zaton tmbyn da za'ayi masa kenan ba idan yazo ,"nidan, nan garin ne mahaifina kuma yajima da rasuwa saidan yanzu ina hanun kanin mahaifina Sunanshi Alhaji inuwa mai dala " ok yasunan unguwar ku " Akram jiyayi Dad ya fara bashi haushi donshi arayuwan shi baya son bin didigi kuma baya son tmby ,yacika yawa kuma yana ganin kamar wannan mutumin neman kureshi yakeyi, daurewa yayi, yace .

"gidanmu na lamid'o cresent"...

Daganan babu wanda yace komai shirune ya biyo baya sai cen Dad yace kaje zan nemeka, salama sukayi cikin ladabi da biyayya ,yatashi ya fita, yana fita ya d'aure fuska, koda Dr Hajar ta nufo inda yake, k'in d'aga ido yayi ,yakaleta "Akram, meyafaru naga lokaci guda ka cenza wani abun Dad yace maka? ".hankalinta 'a tashe tayi maganar,

Kollon ta yayi ranshi a b'ace yace "dama kinsan zancen da Mahaifinki zemin kenan shine baki sanar dani ba" wani zance kuma 'Akram ?wlh ni bansan komai ba " ni arayuwa ta bancika son tmby, tayi yawa na tsani bin didigi Haba sai kace wani wanda zai cutar dake za'a wani sani agaba 'anamin tambayoyi sai kace k'aramin yaro "...

"Haba Akram ae naga ba laifi bane don ansan asalinka miye abun tada hankali? " au hakama zakice " yaja tsaki yayi shigewar sa mota yana kok'arin tadawa, binshi tayi tana masa magana 'amman ina tuni yaja kan motarsa yabar haraban gidan .....


Shiga ciki tayi tana kuku don bataso ko, kad'an taga ran Akram ya b'aci ita jitake aduniya zata iya sadaukar masa dakomai nata inde be sa6ama 'adinin taba don taga farin cikin shi ganin kukanta ne yad'aga ma Mami hankali don bataso ko kad'an taganta cikin damuwa....


"Mamana meya faru naga kina kuka kunyi fad'a da Akram d'inne? "
Girgiza mata kai tayi Alamar a'a tak'i ta fad'a mata yanda sukayi da Akram..

"Mami pls don Allah kar arabani da 'Akram wlh ina sonshi zan iya rasa raina inhar ban aure shiba... " saurin rufe mata baki Mami tayi "dena kuka Mamana insha 'Allah kamar kin aure shi kin gama Dad ,d'in ,naki meyace da shi Akram d'in?" Wlh nima bansan meyace ba" nandai maman tayi ta rarashin ta hartayi shiru..

Tow tundaga wannan ranar Akram be sake ,kiran Hajar ba kota kira baya d'auka , ita kuwa 'abun namatuk'ar damun ta ,kwatsam rannan tana zaune taga shigowan text d'inshi kamar haka..

_idan kin damu dani kizo adobayaro mall ki sameni_

Agogon d'akinta, taduba taga karfe biyar harda minti biyu tunani tafarayi anyakuwa zata iya fita yanzu? Kuma tasan Mami bazata barta ba, Amman dole tasan k'aryan da zatayi kodon ganin Akram yadena fushi da ita, tashi tayi tasa rigan Abaya red tayi rolling black mayafi batayi wani kwaliya sosai ba ta d'auki hand back d'inta black da makullin motarta, tafito tayi d'akin Mami..

Zaune ta sameta, tana shan fruit da fara'a ta k'arasa inda take, ganin hannunta dajaka yasa Mamin b'ata fuska tace "ke kuma ina zuwa k'arfe biyar harda minti 9?" Murmushi ta saki tace "shoprite zani Mami yanzu, zan dawo, wlh bazan jimaba " mezakije yi shoprite? "..

"Mami cake zan siyo kinsan gobe birthday d'in Dad so inaso inyi masa suprise da safe yana tashi " hakane tow kin kyauta, kideyi sauri, kidawo kafun ya dawo gida kinsa dokar shice rashin fita at this time " tsale tayi tace"thank Mami insha 'Allah yanzu, zan dawo...



Muje zuwa fans

Shin me Akram kenufi dama antab'a aur ba'ayi bincike ba? Meyasa baya son ayi bincike? Meyake b'oye musu?

Yakuke jin buk d'in?

Sai naji comments d'inku zan cigaba





*BY DIJA_WAZIRI*🤞
[18/12 7:32 pm] Dija Waziri: 💉💉💉💉💉💉💉
*DOCTOR HAJAR*👩🏻‍🔬
💉💉💉💉💉💉


*Sakonki ya Iso gareni baiwar Allah nagode da soyayya 'Allah yabar zumunci ,kuma insha Allah zan k'ara yawan rubutun ,nima ina k'aunar ki*😊❤❤


*DAGA TAIMAKO*

*Sadnaf ina tayaki murnar kammala littafinki ubangiji Allah hasa mutane su amfana da'Abunda kika fad'akar, Ameen*

*Allah ya Kara miki basiri, muna jiran sabon, novel*

Chapter 10

next day

11:30am

"Hajjo! Hajjo!! Tashi Dad ,d'inku na ,neman ki" cewar Mami cikin bacci ta mik'e tana sosa idonta ,"na'am Mami good morning?" Morning Dear kiyi sauri kije Babanku na, neman ki" tawuce tafita..

Itako Hajar mik'a tayi tareda lumshe idanunta ,tna salati don yau baccin yayi mata sweet, wayarta ,ta duba taga Akram yakira harso 5 nan danan hankalinta ,ya tashi tayi sauri danna number d'inshi takira bugu d'aya ,ya dauka.

"Hello Bee how are you" cewar hajar

"Fine sweety ,meyasa nayi takira baki dauka ba?".

"Wlh bacci nakeyi sai yanzu natashi "..

"Ok tow ya kike i miss you kishirya zuwa anjima zamu fita "..

"Ina zamu? ".

"basai kinji ba kedai ki shirya kawai ".

"Tow zan tmby idan ,anbarni tow".

"Tow yanzu idan ba'a barkiba shikenan bazaki ba ke baki iya irin k'aryan nan taku ta mata bane?".

"Insha Allah ma za'a barni bye barin shiga toilet".

Nan sukayi salama takeshe wayar tana murmushi tare da tunanin k'aryan da zatayi don abarta ,tafita ita shef tamanta ma Mami tace Dad na jiran ta sai a yanzu ta , tuna hijabi ta zura tafita ,tana fara'a

A falon sama ta gansu tarusuna har k'asa tagaida su cikin girmamawa...

Dad ne yayi gyaran murya ,yace "Hajjo !!" Dagowa tayi takalleshi tana wasa da yan yatsun hanun ta "Na'am Dad" saida yad'an yi shiru sannan yace "kina son yaron nan?" Kunya ce taji ta kama ta ,tasunkuyar da kanta ,tana rufe ,fuska..

"Kinyi shiru"Dad ya fad'a yana murmushi "tana sonshi tunda kaga har tana kulle fuska" Mami tabashi amsa tana dariya "tow kice yazo yau ina son ganinshi zuwa bayan magrib", tow Dad zan gaya masa" sannan tamik'e tabar falon..

Koda takoma d'aki wayar ta, tad'auka takira 'Akram ta sanar dashi abunda mahaifinta yace beyi musuba ya 'amsa da zaizo yakuma shaida mata sunfasa fitar yau amman dai zasuyi..

Bayan salar magrib kamar yanda Dad yafad'a 'Akram yazo amman saidai yau shigan k'ananun kaya ,yayi sunyi magana ta fahimtar juna da, Dad sanan ya shaida masa da yaturo magaba tansa ya kuma 'amsa da tow (Tow fa wata sabuwa inji yan caca)..

Dad beyi wani bincike sosai akan Akram ba don shi dukya d'auka mutumin arziki ne daga ,ganin yanayin shigarsa da kuma ,magan ganun sa nanko besan duk siyasa bace...


"Musa kaji wata sabuwa kuma, mutaninan dagaske suke fa " meya faru kuma 'abokina ?" Wai naturo iyayena 'ayi maganar aure nida bani da kowa 'a k'asar nan " dafa kafad'ar Akram Musa yayi ,yace"kwantar da hankalinka wannan duk me sauk'i ne kana da kud'i?"..

"Yes inada kud'i ,inada ,dubu dari biyu ,tow zan maka hanyan wasu mutane su aikinsu shine suje suyi ,iyayen k'arya abiya su kud'i" tow ni cewa nayi maka 'auranta zanyi nifa ba sonta nakeyi ba jikinta kawai nake buk'ata".

"Tow idan ka aureta kabiya buk'atarka basai ka saketa ba" kai No bazan iyaba " tow zokaji inada shawara Musa yajawo shi ya rad'a masa ,tafawa sukayi Akram yace abokina ka iya plan yanzu yaushe zamuje wurin mutanen saimuyi ciniki muji nawa zamu biya su


*****
"Wannan ae me sauk'i ne karku damu dayaushe kuke so naje? Akwai abokan sana'ata su ukku zan d'ibesu ,suraka ni "..

"Jibi nake son kuje "cewar Akram "tow Allah ya kaimu jibin " .

"Ameen ,nawa zamu baka?" Cewar musa" kallon su mitumin yayi ,yana jijiga k'afa yace nera dubu d'ari shine kud'in aikina ,sannan kuma idan aiki yayi kyau zaku ,k'aran ,nera dubu sittin" zaro ido Akram yayi yace "dubu d'ari da sittin fa kenan zamu baka haba malam"..

"Gaskiya, yayi ,yawa inama laifin dubu d'arin ace duka" Musa yafad'a ,wani shi'umin ,murmushi mutumin ya saki yace"hakan shine sauk'i " Akram ne yace "kayi hakuri mubaka dubu dari " mek'ewa mutumin yayi ,yace "ba aikin ,kuke soba kuje kunemi dai-dai ,daku "harzai fita Akram ya tsaida shi.

Nan dai suka 'amince akan zasu bashi yanda yabuk'ata inde aiki zeyi ,yanda suke so,

Akram ya kira Hajar ya sanar da ita cewa magabatanshi zasuzo tasanar da iyayenta, bayan kwana biyu sukazo akayi magana ta fahimta ,tare da saka ranan aure wata d'aya da sati d'aya ,don sunce basu ,so asaka ranar dayawa...

Akram duk yayi 'iya buga ,bugan shi akan yasamu kud'in da zai sayi kayan lefe amman ina kud'i sunk'i shigo masa, haka daya rasa yanda zeyi gashi biki sai matsowa yakeyi sai ya ,yanke hukuncin gayawa Hajar abunda 'ake ciki ,koda ya sanar da ita bata wani tada hankalin taba, tace zata saida gwala- gwalan ta da aka siya mata ,tabashi idan yaso saiya bata daga baya, dama k'arya ,yayi mata 'akan yayi odaring kaya da kud'ad'anshi duk ,kuma basu isoba, ko za'a d'aga 'auren ,itakuma 'ayanzu bata da wani buri daya wuce taganta gidan Akram..

Koda 'Akram yaji tace zata bashi ba k'aramin farin ciki yayi ba ,bayan sun gama da 'Akram ne Khadee ke tmbyn ta "Amarsu mata ga Akram yau ko gobe wai me kuke tattau nawa da 'angon ,nakine?" Hajar dake faman kwaso gold d'inta batace da Khadee komai ba saida ta gama kwasowa ta ajje su gaban Khadee sannan tace"muje ki rakani bakin asibiti" bakin asibiti kuma Hajjo kije kiyi me?" Zan saida gwala-gwalai nane" tana fad'a tana shirin zura hijabin ta da nik'af don 'anfara mata gyaran jiki ,kuma bata son rana ya bigi fuskan ta, kamo hanunta Khadee tayi ,tace "meyasa zaki saida su Hajjo idan kud'i kike buk'ata kije gurin Mami ko Dad nasan bazasu hana kiba" hmm Khadee bazaki gane ba 'amman bana fad'a miki dalilin dayasa zan saida kuma wannan sirine tsakanina dake "nan takwashe duk yanda sukayi da 'Akram ta fad'ama Khadee ,ran Khadee a b'ace tace haba Hajjo ina kika bar hankalinki walahi karki ,kuskura ki fara wannan gangancin zakiyi rigreting nan gaba Hajjo namiji bad'an goyo bane kuma wannan zance kamata yayi ace Dad ,da Mami ya sanarwa bakeba wlh nifa tun sanda kuka had'u da 'Akram jikina be yarda ,dashi ba gani ,nike ,kamar akwai abunda yake son yi mik......"

"Ya'isa haka Malama kar kuma kiwuce gona da iri kin gane kow ,Wai saunawa zan gaya miki ,Khadee bana son abunda kike min ya zaki dinga fad'an magana son ranki akan mijin da nake fatan ya zama uban yarana wlh zan iya Rabuwa dake akan Akram inde bazaki so abunda nake so ba ,idan zaki rakani tashi muje".. Khadee sakin baki tayi ,tana kallon Hajar wai yau itace ke fad'i mata haka zata iya rabuwa da ita kan ,namiji lalle duk yanda 'akayi Akram ya mata wani abu amman zata jenyi jikinta daga duk wani abunda ya shafi Hajar kuma bazata sake mata zancen shiba zata zuba musu ido ,azahiri kuma tace "kije bazan jeba" tana hawaye don furucin Hajar yayi mata zafi ,Hajar batace da ita ufan ba tawuce tabar d'akin itama jakarta ,ta d'auka tayiwa Mami salama sannan tabar gidan titi ,tafita tana ,neman adai-daita har Hajar tazo tawuce....

tow ,tundaga wannan rana Khadee bata kuma kiran Hajar ba kuma bata sake zuwa gidan ba itama Hajar d'in haka bata kuma kiran Khadee ba ,dayake Basmad tazo ita ke tayata shirye shiryen biki..

2 million Hajar ta rantawa 'Akram tare da ita sukaje tazab'i duk abunda take so yabiya 'akwati dozin yayi mata(12) kowane anzuba kaya masu d'an tsada ,da kuma kyau , ko ranar da za'a kawo lefe saida Basmar ta ,tambayi Hajar ya bataga Khadee ba ,Hajar tace itama batasan dalilin dayasa batazo ba....

Hajar dai sai hidimar biki takeyi kud'in komai Akram ne yabada ,daga gyaran jiki ,kunshi kitso , lalle dadai sauran su ,

Yau saura sati d'aya bikin Hajar mahaifinta yayi ,tafiya London amman kafun bikin zai dawo gidan ba'a fara cika ba sai a wannan satin mutane ,nanesa zasu fara zuwa yanzu ,daga k'annen Mami sai yaransu sune kad'ai agidan....


FRIDAY

4:50PM

Hajar da Basmad ne zaune cikin gardin d'in gidan suna ,tattau nawa 'akan inda za'ayi bridel shawa, wayanta ya fara ,ruri da sauri taduba ganin Akram ne yasa tayi saurin d'auka ,daga b'an garan shine yafara magana...

"Hllo my wife how are you?"

Cikin shagwab'a Hajar tace "fine my husban i miss you 2 days bamu had'uba "..

Murmushi yayi tare da cije leb'en k'asan bakinsa yace "wlh aiki ne yamin yawa 'a kasuwa kinsan kayana next week zasu iso ,so muna ta shirye shirye ,yanzu kishirya zuwa k'arfe biyar zan kaiki gidanmu ,mama tun next week tace na kaiki wlh ban samu time ba sai yau"

Saida tad'anyi jim sanan tace "tow saikazo barin sanar da ,Mami" sukayi salama takashe wayar..

Kallon Basmad tayi ,tana murmushi tace ,ke Basmad kinji wai Akram yace nashirya zamu gidan su Maman shi tana son ganina zaki rakani?" Kai gsky ban zuwa 'anjima nima ,mijina zaizo kuje kawai" tab'e baki tayi tace karki raka d'in muje ki zab'an kayan sawa"..

Nan suka tashi suka shiga ciki ,koda Hajar tafad'a ma Mami cewan zasu gidan su Akram bata hanata ba 'amman tace karsu jima kuma tayi mata nasiha kan takama ,mutuncin ta, Hajar tana murna takoma d'aki tayi wanka tasa wani riga da zani ,na supar kayan sunyi mata kyau sosai batayi kwaliya ba powder da lipstick ,kawai tasa tayi kyau sosai ,k'arfe biyar da rabi Akram yazo suka tafi....



Kuyi hakuri da wannan




*BY DIJA_WAZIRI*🤞
[18/12 7:32 pm] Dija Waziri: 💉💉💉💉💉💉
*DOCTOR HAJAR*👩🏻‍🔬
💉💉💉💉💉

Chapter 9

wurin motarta, tanufa tana fita da k'arfi taja motar cikin sauri tabashi wuta ,don bata so tajima,

Bata wani jimaba ta isa cikin shoprite ,tashiga zaune tasameshi ,shida 'abokinsa suna hira ga dukan Alamu ita suke jira ganinta ne yasa ya tab'a 'abokin nasa ,sannan yayi masa nuni da ya kalle ta "kagani angaya maka nid'in, nawasa ne daga kiranta hartazo " Akram yafad'a yana shirin tashi, ita kuwa tahowa tayi tana murmushi me k'ara fito da 'ainahin kenta..

Hannu ya ware mata 'alumun tazo, ganin hakane yasa ta, tsaya turus tana kallon shi, takasa motsawa daga inda take, k'arasowa yayi har inda take ya rungumeta kamar wata, matarshi, kasa cemasa uffan tayi saida suka, kai kusan minti biyu a haka sannan tayi saurin kwace jikinta, tana "Beby miye haka, kuma karfa ka manta niba muhara marka bace" had'e rai yayi, yace "tow miye don kawai nad'an rungumeki yau kawai lalle ashe nikadai nayi missing d'inki ba komai "

Please Login or Register in order to submit comment