Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta samu sauki , nan yaje aka fad'a masa kudin gado da sauran abunda zai siya da yake Aminu kano sukaje .....


Dak'er samir ya samu ya biya kudin komai Hajiyace tazo tana zaune da ita da jaririn da ta haifa , Ranar suna yazo da yake bazasuyi bikin sunaba yaro yaci sunanshi Muh'd sunan mahaifin Samir sai kace da yaron prices shima tunda aka haifeshi bashi da koshin lfy kuma bayashan nono sai madara sabida uwar bata da ruwan nono, watan Jamila d'aya a hospital dukta kwanjame ta rame kamar ba itaba tayi wani fari fayau kamar bata da jini Salim ne ya shigo d'akin ya ganta kwance ita kadai sai hawaye takeyi tunda samir yayi mata kallo d'a yayi saurin dauke kanshi shima yana hawaye don tarame sosai duk me tausayi da imani ya ganta sai yayi mata kuka....

Gefen gadon ta ya samu ya zauna ya kamo hannun ta da suka mik'e sukayi fari alamun rashin isha shen jini" Jami meya saki kuka?" Mikewa tayi tad'an jingina da fillon da take kwance hawayen be dena zubaba tace"kukan rabuwa daku nake Dr nasan daga yau bazan kuma ganin kuba nasan daga yau zanyi bankwana da duniya nasan......

Saurin rufe mata baki yayi hawayen da yake ta danne wane suka zubo "ke dena fad'in haka Jami insha Allah zaki warke Allah yana tare dake " murmushin k'arfin hali tayi tace Dr kenan bakasan abunda nakeji ba da kasan me nakeji da bakace hakaba, Allah ya baka mata tagari wacce tafini Allah kuma ya had'amu a Aljanna Almdullh Allah nagode maka da ka bani danda zemin addu'a bayan raina , Samir prince amane agurin ka Allah ya raya mana shi samir sai wata rana sai munhadu a 'Aljanna "....

Samir na hawaye yace haba Jami pls ki dena fad'in haka insha Allah zaki warke" bud'e baki tayi zatayi magana taji hakorinta ya tsarke dak'er ta fara kalmar shahada tana ina lilahi wa inna ilaihi raju'un ,idanunta suka fara juyawa bakinta ya fara fitar da jini , da sauri Samir ya fice da gudu ya kira doctor....

Suna shiga ya sameta kwance idanunta suna kallon sama fuskarta dauke da murmushi , nufar gurin doctor yayi da sauri ya girgizata yaji bata motsi ya duba idanunta yaga basa motsi rufe mata ido yayi yaja zanin gadon ya rufe mata kanta.....

Samir da yayi tsuru yana kallon doctor ya kasa komai ,dafashi doctor yayi yace "kullu nafsin zaikatul maut Allah yayi mata rahama Allah ya baku hakurin rashi" Samir kasa gasgata abunda doctor ya fad'a yayi sai bayan fitar doctor ya nufi gawan Jamila yana hawaye Addu'a yayi mata ya kira Hajiya don sanar da ita abunda ke faruwa ,Abunda yaji hajiya tace ba k'aramin girgizashi yayi ba innalilahi wa inna ilaihi raju'un shine abunda ya iya furtawa kafun ya fad'i k'asa 'a sume....

Farkawan da zeyi Hajiya ya gani kusa da gadonshi tana rik'e da hannun shi fuskarta yayi luhu luhu alamun taci kuka harta gode Allah ,da sauri ya mik'e kamar zarare fuskarshi babu Alamun kuka ya fik'eta yana tmbyn d lfy meya sameshi kamar wani zarare dafashi tayi tace "Samir ka kwantar da hankalinka dama duk mairai mamacine Alhaji da Jamila abubu abinda suke buk'ata 'a gurinmu sai Addu'a da fatan dacewa , duk Alhaji kam ya tafi ta fashe da kuka don mutuwan Jamila da Baba ,ba k'aramin girgizasu yayi ba kasa kuka samir yayi donshi abubuwan sun masa yawa ga mutuwar mata ga mutuwan mahaifi ga danshi ba lfy gashi ze fara exam din gama school shi yanzu ina zesa kanshi?....

Tatara kayansu ,sukayi aka d'auki Jamila suka taxi gida, suna zuwa aka yi musu wanka kowa 'aka kaishi makwancin shi mu tanan unguwa babu wanda beji mutuwan Alhaji ba don mutune me iya zama da jama'a kuma mutunne me ilimin bok'o dana arabic haka zalika matarshi Hajiya itama yar bokoce kawai dai halin rayuwa ne yasa rayuwansu ta kasance haka......


Bayan rasuwan Firce tun lokacin da Allah yayiwa Jamila rasuwa Princes ya cigaba da rashin lfy Anyi magani anyi magani amman kamar ba'ayi da yake shi sikla ne haka dai har Allah ya d'auki kayan shi, tow tundaga lokacin Samir ya dena tsoran mutuwa don shi a yandu mutuwar mahaifiyar shice kawai ze kuma girgiza shi....

BAYAN SHEKARA SHIDA

Samir yayi kud'i sosai ya zama cikakken doctor na brin ya gina gidanshi me kyau a nasarawa G.R.A yana aiki a 'asibitin Aminu Kano....

Fad'uwa samir yayi yana tari bakinshi yana fitar da wasu gudan jini idanunsa ,suka juye suka ,koma jawur kamar gauta , Captin Junai de ya banko ,k'ofar dama sun saba haka 'a tsakanin su basa wa junansu knocking "innalilahi wa inna ilaihi raji'un meya sameke Dr? " hannu ya fara nuna masa yana tari alamar karya k'araso, shiko sai k'arasowa yake.............


*DIJA_WAZIRI CE*🤞
[18/12 7:32 pm] Dija Waziri: 💉💉💉💉💉💉💉
*DOCTOR HAJAR*👩🏻‍🔬
💉💉💉💉💉💉

*(P. M. L)*

*Duk wanda kaga ya zama wani a duniya tow yayi hakuri ne kuma yacire girman kai, lalle tabbas ni, nayarda cewa hakuri yana d'aga dara mutin, idan har kazamto mai Hakuri da dukkan abunda zai sameka 'arayuwa kuma ka mik'awa Allah saikaga cenji me cike da 'Alkairi*

*ya Allah ka bamu juriya da hakuri akan duk abinda zamu fuskanta narayu Ameen*



Chapter 4

Kama hannunsa yayi ,ya taimaka masa ya koma kan gadon ya kwanta yana wani ,irin ,nufashi har a lokacin jini bedena fita tabakinshi da hancin saba tissue Carpin Junaid ya zaro ya taimaka masa ya goge masa jinin dake zuba sannan ya bud'e fridge d'in dake d'akin ya dauko faro water ya zuba 'a cupe ya mik'a masa, girgiza kai Dr yayi ,yana tari alamar bazai ,iya shaba .

Cikin tausayawa Carpin ke ,kallon shi kamar zaiyi kuka ya ajje ruwan kan bedside drower, ya sauka k'asa, a falo ya samu Ummi tana kallo hankalinta kwance kowa ya ganta yasan tana cikin farin ciki da walwala bata da damuwa fuskarta d'auke da fara'a ta dawo da hankalinta kan carptin "lfy dai kow Junai ina Samir d'in yake? " Captin Junai fuskarshi ba yabo ba falasa kowa ya ganshi yasan hankalinshi baya kwance"Ummi wlh shigata naga Samir cikin wani hali...gsky ciwan shine ya tashi amman dai ,dasauki....

Kafun ya k'arasa furta mezai ce Mami hartakai bakin stairs tana kalmar shahada , shima bin bayanta yayi tana shiga ta zauna bakin gado kusa da inda yake kwance tana hawaye "Dr don Allah kamir rai karka mutu ka barni bani da kowa saika ,kaine farin cikina my Son idan kamutu inazansa kaina yazanyi darayuwa ta ?" tana maganar tana sheshek'ar kuka ta damk'e hannun shi murmushin k'arfin hali Dr yayi ,yace Ummi ki kwantar da hankalinki insha Allah ina tare dake har abada bazan barkiba "maganar dayayi ne yata d'agota tana kallon shi hakanne ma yasa tad'anji sanyi azuciyar ta.

Mik'awa Captin Junai waya ,yayi yace ya kira masa Dr Aiman, da rawan jiki Captin ya karb'a yayi dailing bugu d'aya, yad'aga daga b'angaren shine yayi magana "hello Abokina ya 'akayi? " bashi bane Abokin shine don Allah Doctor idan kana free kayi sauri kazo wlh ciwan shine ya tashi pls, "what!! ciwanshi fakace tow ganinan zuwa" yayi sauri ya kashe wayan.

Basufi minti 10 da wayaba saiga shinan yazo shigowar sane yasa Ummi tashi tabasu guri, "Abokina meya sameka bayan nasan munrabu dakai d'azu lfy?" Murmushi yayi idonshi a lumshe yace "Abubu komai Dr yau d'inne d'azu dana tuna Jamila kawai naji zuciyata namin kuna da zafi " OMG Dr haryau ka, kasa mance Jamila cikin zuciyar ka shekara nawa yanzu? haba Dr Samir kana so ka, kashe kanka ne? " Allah sarki Dr Aiman ae inajin bazan ta6a iya cire son dake tsakanina da Jami ba kuma bazan ta6a iya dena tunanin taba saidai zan rage "tow Allah yabaka lfy nidai taimakon dazan iya maka yanzu shine kadaure karinga shan maganinka sannan kuma kabi shawar -warin dana fad'a maka sai kuma nonon rak'umin da fitsarinshi dana fad'a maka, koda yake zan fad'ima ,Ummi nasan idan anbi ta, taka basha zakayi ba ,yanzu ga wannan maganin kasha kullum d'aya zakana sha ze rage maka zafin da kake yawanji "ya mik'a masa wani magani cikin leda sannan sukayi salama ya tafi...

Ruwa Captin ya mik'a masa yasha maganin sannan ya zauna kusa dashi yana k'ara masa, sannu "Friend kafayi hankali wlh gara ka daure ka cire tunanin Jami a ranka wandafa ya mutu yariga ya mutu bazai tab'a dawowa ba wlh ciwannan zai iya kaika lahira akan tunane- tunane dakasa wa ranka, yanzu kodon Ummi aika dena, kana ganifa yanda take tada hankalinta idan akace ciwanka ya tashi duk tabi ta gigice, kow sow kake hawan jini ya kamata? ".

"Hmmm friend dama nifa tunce nasan bame nisan kwana bane friend inada sirrin da babu wanda yasan dashi a duk fad'in duniyar nan sai Dr Aiman sai kuma mahalillci na su kad'ai suka sani saikuma kaida zan gayawa yanzu ina son abunda zan gayama yanzu yazama sirri tsakanina dakai duk rintsi duk wuya karnaji a wani guri "mik'ewa yayi yaje dede kunen sa ,sanan yafad'a masa .Captin tsabar rikicewa saida idanunsa ,suka juya zuwa ja besan sanda ya furta innalilahi wa inna ilaihi raji'un ba "yanzu Friend kana d'auke da wannan mugun ciwan shine kake b'oyewa why?" Junaid kafi kowa sanin cewa Ummi babu wanda takeso sama dani Ummi zata iya rasa, ranta sabodani haka zalika nima babu wanda nafi so sama da ita zan iya sadaukar da komai nawa saboda ita zan iya k'ask'antar da kaina saboda ita zan iya yin duk wani abunda nasan zesata farin ciki inde be sab'a addini ba kana ganin tasan halin da 'ake ciki bazata iya rasa ranta ba ? Koda ace bata rasa ranta ba kana ganin wani abu bazai faru da ita ba ?"....

"Lalle yau na sake tabatarwa kana balain k'aunar mahaifiyar ka Samir ,Amman dai ,ina fatan kana shan magani?" Yes akwai doctor d'in da nake gani hospital din danake aiki sow ya d'aurani akan magani" Tow Allah ubangiji ya yaye maka yasa kaffara ce ,Amman friend ga shawara mana ni aganina da kayi aure kaga ciwanka yakan tashi any tima kuma babu kowa kusa dakai kaga kuwa idan kayi aure matarka ,kullum tana tare dakai ita zatana sanin halinda kake ciki kuma zatana d'ebema kewa "...

"Nima nayi wannan tunani ,ni inaso nayi aurene ma saboda Ummi tanaso taga jikokin ta kuma kaga tajima tanamin magana ,tow haryanzu dai ban samu wacce tamin bane amman ahankali zan samu" tow Allah ya mana za6i mafi Alkairi nima dad yasani gaba 'nakawo mata inbahaka zeban da kansa yanamin gori wai duk kunyi aure kun barni ,nazama gauro"..

Dariya Dr Samir yasa yace"aishi aure rabone inde tima dinshi beyiba tofa baza'ayi shiba ,nifa bantab'a tunanin zanyi aure a age d'ina lokacin danayi ba " hakane kuma aure ba'ayi masa gaggawa kaga ni wlh nasamu yarinyar nidai ina 'addu'a Allah yasa ta k'arbeni "Ameen friend wai ya sunan ta?" Dr ya tambaya yana gyara kwanciyar shi "sunanta Hajjo" ok tow Allah ya daidai taku "Ameen ni barin tafi zan dawo gobe insha Allah jibi zan wuce "tow thank you freand kafun katafi nima zan shigo inaso na gaida dad" nan sukayi salama ya tafi

WASHE GARI

"Morning dad nd Mami? "Morning dear kin tashi lfy ? " suka had'a baki suka fad'a ,"lfy qlau "tow masha Allah ina Jawahir ?" Cewar Mami, "tana sama 'Alawuya na shirya ta ni na makara patient na jirana" ok amman dai saikinci abinci kafun kifice kow?" Mami ta ,tambaya tana shirin zuba mata chips da egg "no Mami karki damu idan najecen zanci " ok tow saikin dawo ki tabata kinci kuma" tow Mami insha Allah zanci bye" hartazo k'ofar fita daga falon taji muryan Dad," Mamana idan kin dawo inason magana dake ,Allah ya tsare take care of your self" ok Dad Allah ya kaimu by 2:30 zanbar Hospital so zanbiya gidan grany " tow kin kyauta saikin dawo "cewar Dad ,

Tana fita gurin motarta, ta nufa idi tagani yana goge motar yana ganinta ya durk'usa har k'asa yana gaisuwa "barka da safita Doctor antashi lfy? "Fuskarta d'auke da fara'a ta 'amsa da "lfy qlau idi ka gama ne? " Eh nagama Doctor barin bud'e miki yau mamanmu bazata makaranta bane ,naga baku fito tare ba? " zataje yanzu zatafito idan kakaita idan antashi gidan Hajiya zaka kaita," tana maganar tana kutsa kayai cikin motarta, "tam Doctor insha Allah yanda kikace haka za'ayi saikin dawo Allah ya tsare "Ameen " da gudu tafigi motarta, tabar harabar k'ofar gidan cikin mintina kad'an ta isa harabar asibitin, wurin da take parking ta nufa direct tayi parkin sannan tafito dauke da hand bag d'inta da kuma court d'inta a dayan hannun me d'auke da sunan hospital d'in tafiya take furkarta d'auke da murmushi sai d'agawa yan tsiranin mutanen dake yawo cikin haraban asibitin hannu takeyi tana musu murmushin ta me k'ara fito da kenta ,office d'inta, tashiga direct fale tagani guda 15 jirke kan table d'inta zama tayi tana maida nunfashi ta saka court d'inta , ta kira wata nurse ta zauna don tana taimaka mata da wani abun fara duba marasa lfy tayi sai da ta duba mutun 7 sannan taci Abinci tacigaba da dubawa saida ta dubasu duka wurin 3:45 tana shirin tafiya gida taji knowking da sauri tace "waye" jin munyar Attendant yasa tace "come in " shigowa yayi yace ma'am you have a visitor, yace wai yana son ganin ki sunanshi Dr Samir "6ata fuska tayi tace kace ya shigo " yana fita bejima ba Dr Samir ya shigo fuskarshi d'auke da murmushi sanye yake cikin black suit sun balain yi mishi kyau "afternoon K'awa ya aiki? " Alhmdulh ya naka aikin " ta 'amsa masa tana maida wasu file ma'ajin su "lfy dama wata magana, nazo maki da ita idan kina da time saina fad'a miki idan kuma kinada abunyi mayi waya " cewar Dr Samir duba agogon dake d'aure a tsintsiyar hannunta tayi taga hud'u saura minti goma, fad'ad'a murmushin ta, tayi tace ina jinka Dr Samir ae bazan iya k'in sauraran kaba har ka tako kazo "yawwa k'awa na gode da lokacin ki akwai wani da yake kawo matarshi hospital d'inmu ne so tanda problem da yawa kuma duk matsalar daya shafi matane so shikuma baya so namiji na tab'a masa mata shine yace idan nasan wata Doctor mace mana don Allah nahad'a su wlh mutumin yanada kirkine babu abinda zai iya nema ide zan iya ban masa ba yanzu na bashi number d'inki zasu dinga zuwa nan " eyyah ae babu komai Dr godiya muke " nan sukayi tahira suna fad'ace fad'acen su don duk randa suka had'u sai sunyi fad'a, tare suka fita kowa yayi wurin motarsa hadire ne sosai a garin keta had'uwa, tafiya take cikin k'warewa da iya tukin cikin nutsuwa take taka motar gari kuwa sai k'ara duhu yakeyi hadiri sai had'owa yake dede nasarawa G. R. A motarta ya fara yin abu kamar ze tsaya taji tafara yawo kan titi mutane sai hon suke dannan mata gashi tayi tsakiyan titi sosai hasbunalah shine abunda take ta furtawa cikin zuciyar ta...



Muje zuwa


*BY DIJA_WAZIRI*🤞
[18/12 7:32 pm] Dija Waziri: 💉💉💉💉💉💉💉
*DOCTOR HAJAR*
💉💉💉💉💉💉



chapter 5


Dak'er ta samu tayi parking gefen hanya tafito gashi anfara yayyafi yan tsirarin mutanen bakin hanya duk sun watse saboda ruwan ya soma k'arfi, motoci sai wucewa suke abunsu babu wanda ya tsaya tafi minti goma tsaye a bakin motar batare data shiga ba ruwan dayayi k'arfi sai dukanta yake ,kayan jikinta duk sun jik'e jak'af babu abinda take sai faman tsaki gashi tana so ta koma hospital 8 na dare , tana cikin tunanin hakan ne taji anyi mata hon wata black mota ce k'iran ferari tayi parking kusa da motarta, wani wawan tsaki ta kuma saki tare da zumar komawa cikin motar ta, don yanda take jin haushi bata, tunanin zata iya kula kowa, wani guy ne ya fito cikin motar sanye yake cikin dakaken shedda gezna ruwan toka ,k'arasawa yayi har inda take ya kwankwasa mata glass d'in mota da har bazata bud'eba wata zuciyar tace ki bud'e kika sani kozai taimaka miki motar ta tashi , saukewa tayi fuskarta 'a d'aure ta d'ago ta kalleshi, tunani ta farayi aina tasan wannan fuskar don ta ta6a karo da mutun me irin wannan fuskar amman ta manta "Hajjo ya 'akayi kika tsaya ruwa sai dukanki yake baki tunani ya saki mura" tsintar muryanshi yana magana ne yasa tayi saurin dawowa daga tunanin data shiga 'a firgice ta kuma d'agowa ta kalleshi da manya manya idanunta masu haske da 'Alamun tmby a tare da ita..

Fad'ada murmushin shi yayi yace nasan akwai ayar tambaya a kallon nan naki yanzu barin duba miki motar naga matsalar shi idan yaso zan maki bayani daga baya " itadai Dr Hajar kasa cewa uffan tayi don ita tasan babu wanda ke kiranta da Hajjo sai yan gidan su sai kuma k'awayen ta Khadee da basmard tow shi kuma waye aina ya santa meyi halak'anta dashi? tambayoyin da tayiwa zuciyar ta kenan wanda itama bata da amsar su, duk yanda taso ta tuno inda tasan fuskar shi amman ta kasa "Hajjo gwada tada motar muga ko zai tashi" ko k'arin tadawa tayi amman motar sam tak'i tashi, kallonta yayi yace ina tunani sai me gyara ya duba ta yanzu muje na kaiki inda zaki idan yaso daga baya idan angama ruwa na kai maki motar gurin gyara, "Dr batayi gardama ba ta bishi don tasan babu yanda ta iya tarauni tace ya kaita gidan grany ,tunda suka fara tafiya babu wanda yayi magana cikinsu, ita kuwa Dr Hajar kanta ya kulle ta shiga duhu jira take ,kawai ya fad'a mata ina ya santa ko taji dad'i ,kasa jurewa tayi ta fara magana da muryanta me sanyin dad'i "bawan Allah ina kasanni kuma har kasan sunana?" Murmushi Captin Junaid yayi ,yace" kin tuna wata rana keda k'awarki ,kun fito daga jufatu na ganku na tsaidaku ,ki kak'i tsayawa sai k'awar takice ta tsaya tow itace ta fad'an sunanki ", sai alokacin Dr Hajar ta ,tunoshi nan danan kuma taji kunya ta kamata ,tun daga haka bata kuma cewa uffan ba har suka isa d'an madede cin gidan granyi me kyau da tsari hon Captin Junaid yayi megadi yazo ya bud'e musu gate , suna shiga Jawahir Dr Hajar tagani kanta babu d'ankwali gashinta 'a sake daga ita sai pant tana wasa cikin ruwan sama ,ganin danowar motarne yasa tayi saurin k'ara sawa wurin tana "oyoyo Mummy ".

Fuskar Dr Hajar a d'aure cikin tsawa tace "wayace kiyi wasa 'a ruwa? Bana hanakiba ? Tafi ki bani wuri mara kunya kawai bazan kuma zuwa dake ,ko inaba tunda bakijin magana".Da gudu Jawahir ta koma cikin gida tana kuka , Sorry Hajjo Cool down naga kamar ,ranki ya b'aci sosai kinsan yara da son ruwa adunga hakuri dasu" ko kallon inda yake batayi ba don idonta ya fara zubar da kwallah fita ,tayi daga motar ko nagode batace ba tayi ciki...

Shiko Captin Junaid tambayoyine mak'il a zuciyar shi wanda bashi da amsar su ita kad'ai ce zata iya 'amsa masa su shin dama tanada 'aure? yake b'ata lokacinshi akanta kuma harda yarinya lalle tamasa nisa dole yasan abunyi ,tow Amman meyasa Khadee bata sanar dashi ba? Meyasa ta b'oye masa metake nufi dayin hakan? , buga kanshi yayi da jikin murfin motar ya furta 'a fili Khadee kece zaki amsamin tambayoyina jan motar yayi zai bar gidan kawai yaga wayan Dr Hajar kan kujeran inda ta zauna da sauri ya rubuta number d'inshi yayi sauri yayi dailing sannan ya mik'awa megadi yace yabata...


Zaune taga datijuwar matar da bazata wuce shekaru 85 ba, tana sanye da doguwan rigan abaya, ta mik'e k'asan carpet tana kallon Aljazeera jawahir kwance a cinyarta, tana kuka, k'ara sawa tayi fuskarta ba walwala ta zauna kusa da datijuwan "grany barka da yamma ya gida ?" A'a Hajjo harkin shigo ne lfy qlau gida Alhmdulh ya aikin hope komai nomal kow?" Aiki lfy qlau " gud yana ganki kamar baki da wata walwala waya ta6amin ke?" Tab'e ,baki tayi tace babu komai grany wlh Jahari ce kawai ta 6atan rai" tow me tayi kuma naga tashigo tana kuka ,kuma tak'i magana? "..

"Ruwafa taje tana shiga grany kalan idan dare yayi tahanani bacci tadameni da kuka " tow ae yaranne yanzu basaji hak'uri zakiyi kumafa haka 'akayi ta fama daku" tab'e baki tayi a shagwab'e tace "nidai banyi k'iri niya irin na yaran yanzu ba" dariya grany ta saki tace"sai kace lokacin kinada wayo "sun jima suna hira saibayan sallar isha' sannan suka tafi gida....

"Mummy kince zaki ,kaini gurin dady na kuma haryau baki ,kaini ba, ni ,inaso naganshi ne ,nima inaso Babana yana kaini school kamar yanda yan class d'inmu babansu ke kaisu, kuma inaso na dinga ganinshi kusa dani" Dr Hajar ji tayi kamar ansara mata guduma 'aka ,kasa driving d'in tayi ,tayi parking a gefen titi, taji kanta ya fara juyawa kalmar shi nak'arshe take tunawa...

~Hello my love kin yarda dani kamar yanda kika yarda ,da itayenki ,kin aminta dani ,ina sonkI Hajjo I love you so much Amman bazan iya zama dakeba domin bazan tab'a ganinki da daraja ba bazan ta6a ganinki da k'ima ba , ba kece mace tafarko dana gudu na bariba sunada yawa nariga na biya buk'atana don haka nakecewa dake nabarki lfy kije ki nemi wani mijin kiyi aure domin namiki nisa bazaku kuma jina ko ganina ba~

"Innalilahi wa inna ilaihi raji'un Allahuma ajirni fi musibatin" shine kalmar da take ta maimai tawa don aduniya bataso taji ,Jawahir ta ,tambayeta ina Babanta , danne hawayen dake k'ok'ari zubo mata ,tayi ta k'ak'alo murmushin dayafi yak'e ciwo ta kama hannun Jawahir "karki damu bebyna soon zan kaiki gurinshi banace miki saina samu hutu agurin aikina ba?" girgiza kai tayi tace"tow Mummy shi yana inane meyasa bazamu koma wurin shiba ?" Duk sanyi ac dake cikin motar be hana Dr Hajar jin zafiba ,zufane keta kwaranyo mata ,tako ina amsar da zata bawa Jawahir ta ,tsaya tana ,nazari cen kuma hikima ta fad'o mata, kama kumatun ta ,tayi tana dariyan dabekai zuciba tace" yana dubai yana 'aiki shiyasa bama tare Amman idanya tara mana kud'e zai dawo mukoma gidanmu "...

Matsawa tayi sosai ta rungume maman "yeeh zamu koma gidanmu idan dady na yadawo " shafa gashin kanta Dr Hajar keyi tana hawaye sunfi minti biyar ahaka sannan suka ,kama hanya saida ta ,tsaya tasiya ma Jawahir ice cream sannan suka wuce gida.....

Koda suka isa Jawahir tariga da tayi bacci ,d'aki ta kaita darect ta kwantar da ita sannan tadawo falon k'asa Dady ,da Mami ta gani zaune suna sauraron labarai a NTA "barkan ku da ,dare " barka dai Hajjo ya hajiyar?" Dad ya tmby ..

"Tana lfy tace nagaida ku". Muna 'amsawa "cewar Mami "tow yayi kyau Hajjo !! "Dad yakira sunan ta "na'am Dad "ta'amsa fuskarta 'a sake ,saida yayi shiru nayan mintuna sannan ya fara da "wai yaushe zakiyi aurene? Me kike nema yanzu da bazaki fidda mujiba ? nagaji da ganinki haka ".

Shiru tayi batace komai ba ita sam babu aure aranta hasalima batada wanda takeso don ita maza basa gabanta "kinyi shiru ko baki da kowane ,Nina kawo miki cikin yaran abokaina ?" Da sauri ta d'ago ta kalleshi tace "Dad zan kawo kad'an bani lokaci insha Allah zan kawo " tow ina zuba ido badai naso wannan shekaran yawuce kina gidana, nagaji da gorin da yan'uwa da ,abokai kemin " tow Dad insha 'Allah zanyi k'ok'ari " Tow Allah ya miki Albarka zaki iya tafiya "..

Tashi tayi tahau sama tayi d'akinta ,tana shiga ta fad'a kan gado tafashe da kuka ,tana ,nadamar haduwa da Akram a rayuwan ta, farkon had'uwanta adashi ta fara tunawa....

NAIL UNIVERSITY
Students ne keta zurga zurgansu a cikin haraban makaranta ,kowa harkan gabanshi yakeyi sanye take cikin English wears white T sheet da pink leggings sai ta d'aura

Please Login or Register in order to submit comment