Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

a razane Doc...ya kalli Mami yace bata da 'aure ?" Eh bata da 'aure meke faruwa?" Hajiya...." karka sanar da ita Doc..idan ma za'a sanar da ita bayanzu ba mubari saita nutsu"Aunty Asma'u tayi saurin tsaida shi tana hawaye , "ban gane sai na nutsuba? kufad'a min meke faruwa da ,diyata karkuce abunda nake tunani gsky ne ?"...

"A irin wannan zancen ba'a b'oyewa Hajiya 'sai dai kiyi hakuri Amman abunda kike tunanin shine dai" Doc...yafad'i yayi saurin barin d'aki "inna lillahi wa inna ilaihi rajooun Allah menayi maka ,kajarabceni ta wannan hanyar Allah na tu....."kafun ta k'arasa ,sai jinta sukayi luuu a k'asa nan danan kowa ya ,yo kanta....


K'arfe hud'un dare Mami ta farfad'o ,kasa had'a ido sukayi da Hajar don haushin Hajar d'in takeji ,gani take da saninta hakan yafaru ,ita ,tunanin yanda zata ,tunkari mahaifin su tasanar dashi tafara yi nadama ce far cikin zuciyarta ,da ,dana sani barin Hajar fita ,Mami takira mahaifin Hajar ta shaida masa cewa 'Akram ya fasa 'auren Hajar Amman bata sanar dashi abunda ya faru da ita ba ...

Dad ba k'aramin bak'in ciki yayi ba ,ya kira duk abokansa daya bawa Iv ya sanar dasu anfasa 'auren Hajar kowa beji dad'in hakanba , Hajar saida tayi kwana biyu a hospital sanan aka salamesu ,Khadee gidan su Hajar ta,tare wai sai tadawo dai-dai tukun takoma gidan su Aunty Asma'u ma tatafi ,tabar Basma idan yaso tazo daga baya, Mami kuwa babu abinda yake had'ata da Hajar Kakar su Hajar kam batasan komai ba itadai taji cewa 'anfasa 'aure..



*BY DIJA_WAZIRI*🤞
[18/12 7:32 pm] Dija Waziri: 💉💉💉💉💉💉💉
*DOCTOR HAJAR*👩🏻‍🔬
💉💉💉💉💉💉



Chapter 14

Cikin falon ta shiga ta zauna tana wasa da k'asan hijabin ta, su Mami kuwa yi sukayi kamar basu ganta ba, "Dady Mami barkan ku da yamma ina wuni" ta furta yayin da take kwala, Dad ne yayi k'arfin halin amsawa "lafiya" sannan ya mai da kansa ga tv, "Don Allah Mami kuyafe min ,natufa wlh ba laifina bane wlh ban san haka zata faru ba ,don Allah kuyafe min kudena fushi dani wlh bani da laifi , Dad kuyafemin kozan samu sassauci a rayuwa ta ko zan d'anji sanyi azuciya ta fushinku hatsarine a gareni ,kuyi hakuri " tana kuka me ci da zuci take rok'on iyayen ,nata 'amman ko juyowa su kalle ta basuyi ba ,bare suce wani abu. "Mami! Dady!! Don Allah kuce wani abu " kallon ta Dad yayi ,yace dama wayace muna fushi dake ? tashi kije ", Hajar mik'ewa tayi jiki babu laka ta fita sai k'ara wai gowa takeyi ,tana kallon su ,wannan shine kallon su nak'arshe da zatayi sai kuma idan sun had'u a lahira , duk-da tasan basu yafe mata ba idan tamutu zasu yafe mata, tana shiga d'aki peper da bairo ta d'auko ta fara ,rubutu tana kuka me cida zuci ,da wannan rayuwan da take ciki gara tamutu ,ta huta idan ta haifi wannan yar me zata ce mata ? ,tana gama rubutun ta 'aje kan gadon ,taje tayi alola tayi sallah raka'a biyu sanan ta d'auki hannun ta fara ,neman gafaran ubangiji..

Ya 'Allah ka sasauta min Dukkan wani kunci da ,damuwa ta, Allah ka yafemin Allah kasa iyaye na sugane gsky ba da sanina wannan abun ya faru ba, Allah natufa nasan abunda zan aikata yanzu babu kyau a 'addinin musulunci, Amman bani da zab'ine yasa zanyi haka ,hakan shizesa na samu kwanciyar hankali a rayuwata ,tana gamawa ta shafe addu'ar tana zubar kwallah..

Kamar kullum ,Kalifa idan zai kwanta barci sai yaje gurin yayarsa ,sunyi sai da safe yauma hakan ,akayi k'arfe takwas da kusan rabi ya gama duk ,abunda zaiyi ,yayo hanyar d'akin Hajar don yayi mata saida safe , yana shiga 'abunda ya gani ba k'aramin razanashi yayi ba ,da gudu yafita 'a dakin yana kwalawa su Dad kira , a tsorace suka zo be sanar dasu komai ba, sai jansu da yayi d'akin Hajar , Mami na ganin Halin da Hajar ke ciki ta kurma ihu tana kiran sunan Allah. Kwance suka sameta sai shure shure ,takeyi kamar me kakarin mutuwa ba kinta na fitar da wani kumfa , Dad a firgice yace Kalifa ya d'auko mukullin mota su tafi Hospital ,Dad ,da kanshi ya sungumi Hajar wurin d'aukan tane yaga kwalbar fiya fiyan data zuk'e , cikin sauri yayi da ita mota yana salati ,dukkansu sun birkice ,

Hospital d'insa ya kaita ,yana zuwa ya kira wasu kwararun likitoci guda biyu ,dashi suka zama su 'uku suka rufa kan Hajar ,dak'er suka samu suka ceceto rayuwan ta 'amman tasha wahala sannan aka samata ruwa..kwananta daya suka dawo gida, a gida ta cigaba da jinyar ta iyayenta suna bata cikakiyar kulawa ,wani 'ikon Allah cikin jikinta be zubeba, su Dad sunyi nadama sosai da suka gano gaskiya lokacin da Musa 'abokin Akram yazo yayi musu bayanin halayen Akram da kuma kudurinshi akan Hajar, Dad yayi nadama sai yanzu yasan Hajar bata da laifi shine me laifi da bai zurfafa bincike akan Akram ba, yabawa Hajar hakurin duk abunda ya faru, Rayuwa ta koma dai-dai tsakaninta da iyayenta ,tana samun cikakiyar kulawa , sai dai kuma kunci da ,damuwa da tunani basu bartaba don kullum sai tayi kuka idan ta, tuna 'abunda ya faru, dalilin Hakan yasa Mami da, Dad yanke hukuncin zasu kaita london ko tad'an samu kwanciyar Hankali , idan yaso idan ta haihu saita dawo, don tabuk'aci azubar da cikin Dad yak'i yarda , Tow Hakan dai sukayi sun turata london ,zata zauna gidan k'anin Mami...


Hajar ta,tafi london duk da hakan bata samun kwanciyar hankali, don adul lokacin da taga cikin jikinta, sai taji duk ta,tsani kanta duniyar ma gaba d'aya taji baya mata dad'i , tana dai zaune kullum cikin damuwa, wata rana ta je wani clinic kusa da gidan ,da take zaune tace maganin zubarda ciki take so ,subata, k'in bata sukayi saida tayi, tayi musu magiya sanan tasamu suka bata ,koda takoma gida tasha tana jiran taji ciki ya zube, amman wani ,ikon Allah ko ciwan ciki bataji ba , bare taji wani laulayi , haka babu yanda ta iya tahakura tabar cikin tare da 'alwashin idan har tahaife cikin bazata ,zauna da koma,meta haifa ba yasar dashi zatayi ko ta kaishi gidan marayu don bazata ,zauna da jinin akram ba, (shin hakan da hajar take da niyar yi menene hukuncin sa , me d'ancikin ta yasani da zatayi masa haka meyasa laifin da banana ba zai shafeshi , ?), Haka rayuwa tacigaba da kasan ce mata babu dad'i babu walwala cikin ta kuwa sai k'ara girma yakeyi, akwana 'a tashi ba wuya 'a gurin Allah cikin Hajar har yakai lokacin haihuwa , harda, d'oriya..

Ranar wata litinin da misalin k'arfe shabiyu Hajar ta fara nak'uda , nan danan suka tafi asibiti, duka -duka awansu biyu da zuwa cikin hukuncin ubangiji ta haifo santaleliyar yarta, k'arfe shabiyu ga watan shabi ranar , wani abin alajabi shine anhaifi yarinyar da kunshin magani a hannun ta , koda Hajar taga maganin sai ta ,tuna ranar da tasha ganin zubar da ciki shine aka haifo yar dashi a hannun ta 'a damk'e (kunji wani 'ikon Allah wannan kadai ya isheta ishara ), Hajar jikinta saida yayi sanyi kuma taji aduniya bata da yarda takeso ,sama da ita ,tanajin bazata iya rabuwa da ita ba , bayan anyi suna yarinya taci sunan mahaifiyar Hajar su Mami da ,Dady ma duk sunje...

Bayan Shakara Daya

Yesmin harta girma ta yi wayo kuma tana ,tafiya 'amman ba'a yaye taba. Hakan ya bawa Hajar daman komawa school don tayi masters d'inta 'agida take barin Yesmeen bata ,tab'a zuwa da ita school ba ,

Bayan ta koma da wata biyu ne ,ta had'u da ,Doctor Samir lokacin ya tafi k'arin karatu kon fannun aikin shi, koda suka had'u kafun ta yarda su fara 'abota saida ,suka, kusan shafe shekara ,sannan dataga shi ba irin mazan banza bane yasa, ta 'amince da suyi abota ..

After two years

Yesmin ,nada shekara ukku ,lokacin ta kamala karatunta, suka dawo gida, tunda suka dawo abunda ya faru da ita ya dawo mata sabo tamkar a lokacin yake faruwa ,duk wani walwala da farin ciki suka, kuma gushe mata barin ma idan ,ta kalli Yesmeen , Hajar da tadawo ba zama tayi ba 'aiki tafara yi a asibitin su, awajen ,ne ta, tadda Khadee ma ta soma 'aiki dasu..

Dawowa labari



By Dija_waziri
[18/12 7:32 pm] Dija Waziri: 💉💉💉💉💉💉💉
*DOCTOR HAJAR*👩🏻‍🔬
💉💉💉💉💉💉





*Amfanin ilimi da hankali shine kayi aiki dasu wajen aikata 'abin da zai amfaneka da kuma guje ma dukkan abinda zai cuceka.*

*Duk yadda kike son mutum ,indai ya fara jefo miki kalaman batsa ,ko kuma yayi kokarin ta'b'a jikinki ,to ki rabu dashi yaje ya nemi wata mai irin halinsa...amma bake ba..*

*ki sani cewa duk wanda rashin kunyar sa takai har ya tab'a jikin wacce yake fatan ta zama uwar yaranshi, tow hak'ika shi acikin mazinatan ma shi ba k'arami bane.*

*Babu wacce zata 'auri mazinaci sai ,idan ita d'inma, mazi naciyar ce ko kuma mushrika...Hakanan babu mai aurar mazinaciya sai mazinaci ko mushrika (Allah ne ya fad'a)*

*duk ma'auratan da suka fara zina tun kafin aure sun riga sun gurbata tarbiyyar zuriyar da zasu haifa ...ya Allah ka ,kiyayemu don qarfin ikonka ka rabamu da sharrin duk wani me sharri ka rabamu da mugayen maza*


Chapter 13

Bayan Dad ya dawo daga London ya kira hajar yayimata nasiha sosai akan ta kwantar da hankalinta , Hakan shine Alkairi a gareta shi yasa 'Allah be nufa ta zama ,matar Akram ba ,yayi mata nasihohi sosai ,Hajar kallon mahaifin ,nata kawai takeyi tare da tausayin kanta,da kuma tausayin halin da zai shiga idan yasan me Akram yayi mata, tow meyasa ma ,Mami ta b'oye masa bata sanar dashi ba? Anya kuwa bazata sanar dashi ba? tow yanzu ita da wani 'idon zata iya sanar dashi wannan mummunan labarin ,da wainan tunanin ta ,tashi ta koma d'aki...

A kwana 'a tashi babu wuya 'a gurin Allah yau Hajar satinta biyu a gida kuma har yau dady besan me ake ciki ba ,Mama tayi tunanin sanar dashi amman tana tsoran kar wani abu ya sameshi dalilin dayasa tayi shiru ta b'oye masa kenan..

Yau Friday kamar kullum duk ,k'arshen sati Kakar su Hajar takanzo ta gansu ,tow yauma tazo ,tana zaune a falo Khalifa da Hajar sukazo amman Hajar batada walwala duk wanda ya ganta zai gane kamar akwai abunda ke damun ta duk ta rame sai dai kuma tayi fari sosai skin d'inta yayi kyau , tunda satinan ya kama takejin bata jin dad'in jikinta ga yawan kasala da ciwan kai da takeji , kallo d'aya Kakar tayi mata kawai jikinta ya bata 'akwai matsala yanayin yanda taga Hajar d'inne yasa hankalinta ,tashi ,cikin fargaba da tashin Hankali ta nufi ,inda Hajar d'in ke tsaye tace..

"Hajjo meke damunki ,ki fad'amin gsky karki b'oye min" dai -dai lokacin da Granny ke tmbyr Hajar dai -dai lokacin Mami ta shigo falon , kallon ta Hajar tayi suka had'a ido ,saurin Kauda kanta Mamin tayi don ko son su had'a hanya da Hajar din batason yi tun sanda 'abun ya faru tadena kulata ,wuri tanema tazauna tana kallo ba tare da tace dasu ,uffan ba..

"Hajjo dakefa nakeyi kinyi shiru".

"Babu abinda ke damuna Granny" Hajar ta fad'a kamar zatayi kuka.

"Karya kikeyi zo nan" hanunta ,ta kama ta zaunar da ita kan ,kujera ta fara duba hanayenta da goshinta ,su k'asan idon ta duk taduba , fuskarta Babu anuri tace "kutashi kuje daga nan kice wa Babanku yazo "...

Suna fita Mami ta tsuguna ta gaida Granny sanan tacigaba da kallon ta ,yayin da ta kawo mata kayan motsa baki , kallon Mami Granny tayi "Fatima ,meke damun Hajjo ? ta fara bin maza ne?" Gaban Mamine ya fad'i "Bin maza kuma Hajiya me kika gani?" Tow Hajjo dai kamar ciki gareta"..kofin shayin dake hanun Dad ne yayi saurin sub'u cewa daga hanunsa "ciki kuma Hajiya ? " Mami ko dafe k'irji tayi ,tana hawaye ba k'aryata 'abunda Granny tace ba don zai ,iya ,yuwuwa tow amman idan hakanne Hajjo ta cucesu ..

"Eh ciki gareta kuma ,kakira Doc... Yanzu ya gwadata ku gani " jikin Dad na rawa ya danan number d'in Doc...bugu d'aya ,ya d'aga nan yasanar dashi yazo gida 'akwai matsala ,aiko ba'a wani jimaba saiga shi ya iso,koda ya iso darect d'akin Hajar suka shiga ,da mamaki taji Dad nayiwa Doc..bayani ,ita dai tasan bata sanar da ,dad cewa bata da lfy ba tow me Doc..zeyi mata ,nan dai ,Dad suka gama ,magana da Doc...sanan yafice a tsakin yabar Granny da Mami da kuma Doc...gwaje gwaje Doc..yayi mata bayan wasu yan mintuna ya kalli Mami yana Murmushi ya fice a d'akin suma suka mara ,masa baya ,ita ko Hajar binsu tayi da kallo tare da tunane -tunane kala -kala

"Congat Dr Galadanci yarka tana da ciki " Inna lillahi wa...." Granny bata k'arasa ba sai jinta sukayi a k'asa , Doc.. Ne yayi hanzarin taimakon ta don Mami da Dad sun daskare Agurin saida ,Doc ya tab'a Dad sanan ya dawo Hayacin sa, suka samu suka ,kwantar da Granny kan kujera sanan ya raka Doc....ya tafi shikuma ya yo gida zuciyarshi a cushe ranshi a jagule koda ya dawo Kalifa da Mami yagani kan Granny suna mata firfita har a lokacin bata farfad'o ba...

Kasa tsayuwa yayi da kafafun shi zuciyarshi na masa zafi ,yanzu wannan wace irin abun kunya Hajar ta jawo masa duk jajircewan da rokon Allah da yawaita yi musu nasiha 'akan zamantakewa da tsoratar da su akan azabar Allah da kwanciyar kabari zai yi wuya ta faran d'aya, ya 'aminta da 'abunda ,Doc...ya sanar dashi, mu samman ma daya kasance Hajar yarinya mafi soyuwa gareshi wacce yakeji kuma ya ,yarda ,da irin kamun kanta ,Innalillahi wa inna ilaihirraajiun Allamuma 'Ajurni fi musibatin , shine kawai abunda yake iya furtawa , suna cikin hakane Hajar ta sauko ba tare da tasan me yake faruwa ba ,ganinta yasa wani zuciyarshi harzuk'a be san ,sanda yayi kanta ba ya hauta da ,duka ta ko ina yana magana,"Ashe ke yar iskace bansani ba? Dole yaron ,yace bazai aurekiba Hajara ! A gidana ? Kin zubarmin da mutunci kaico wannan wace irin rayuwa ce ?koki gayamin wayamiki ciki kona kasheki yau don dana dinga, ganinki ,ina ganin bakin ciki gara na kashe ki nima 'akasheni "duka yake yi ko ta ina batare da ya dakata ba, Mami ko Runtsa idon ta ,tayi tana hawaye ba tare da tace komai ba , Dad ko sai dukan Hajar yake ba k'ak'au tawa itakuwa ta kasa gane meke faruwa da ita yanzu Ashe Akram ciki yayi mata, kuka take kamar ,ranta ze fita Dad ko be dena jabgar taba yana fad'in "waya miki ciki don Ubanki"....

Mami dataga Abun yak'i ,karewa tayi k'arfin halin mik'ewa tsaye tana me kiran sunan Allah "

"Alhaji don Allah kayi hakuri ka rabu da ita zafa ta iya mutuwa koka manta cikine ajikin ta" Barin dukan Hajar yayi ,yadubi Mami dake tsaye gabanta cikin zafin ,nama yace ,idan tamutu sai me wlh dana ,dunga kallon wannan bak'in cikin gara babu ita 'a doran k'asa ae duk iskanci da takeyi da saninki takeyi kece kike d'aure mata gindi yanzu ae gaki gata sai kisan yanda zakiyi da ita ,ki tattara mata kayanta ,taje tanemi wani uban don ,nikam nariga dana sal......"wlh idan ka ,k'arasa furucinki saina d'aga maka nono kuma Babu inda zataje Wannan abunda ya faru k'addara ce kuma dole mu d'auketa , Hajiya ta furta, tana daga kan kujera

"Ha..ha.. Kiran sunan Hajiya Dad keson yi sai dai kuma ya gagara kiran ,nata ,kawai gani sukayi, ya, yanke jiki ya fad'i ,da sauri suka nufeshi, ganin haka yasa hankalin Granny tashi ,Dad ! Dady!! Dad!!! Shine abunda Kalifa ke furtawa ,a gigice Mami da Granny sukayi kanshi suna girgiza shi, Hajar ko ,kuka ta sanya don jikinta babu laka ,ko tashi bazata iyayi ba jirine ke d'iban ta ,yanzu idan Dad yamutu fa itace sila ita yanzu ina zata saka ,kanta ? ...

Ruwa Kalifa ya sunkuta ya fara yayyafa masa 'amman ina Dad ko motsi bayayi ,mukullin mota ya d'auka da taimakon su Mami aka shigar dashi mota Mami da Kalifa ne suka wuce da, Dad Hospital Granny kuma taji da Hajar..

Suna zuwa Hosptal d'inshi suka ,kaishi suna zuwa Doc...d'in gaba d'ayansu ,sukabar abunda sukeyi cikin gaggawa suka, karb'eshi saida suka yi masa yan abubuwan da zasuyi sanan sukace abarshi ya huta zai farfad'o anjima kad'an

Basma tadawo dama taje gidan yan uwan Baban tane kwananta uku sai yau ta dawo ,Hajar tagani kwance kan ,kujera jikinta jina jina Granny zaune kusa da ita...

"Hajjo kinga 'abunda kika jamana ko ? Yanzu wannan abun kunyar dame yayi kama? Ga mahaifinki cen a Hospital kuma duk ,kece sanadi ki fad'a min gsky waya miki ciki?"..

Zoro ido Basma tayi waje bata san ,sanda ta furtaba "ciki" OMG Ya salam , wannan ..

Hajar na kuka tabawa Granny labarin duk abunda ya faru A-z bata ,b'oye mata komai ba , Granny duk tayarda ,da 'abunda Hajar tace don Hajar bata k'arya idan zata fad'i abu iya gaskiyar ta zata fad'a kuma tasan Hajar bazata 'aikata hakan da gangan ba, " Tow meyasa tun farko ba'a sanar damu ba ? Laifin mahaifiyar kice " itadai Hajar batace komai ba don zafin ciwo ya dameta dak'er ma taiya bawa Granny labari don bata koson tuna 'abunda ya faru ,koda taji tana da ciki ,kukan kin zuwa yayi ,yanda takeso kasa kuka tayi don Idanunta sun bushe tun randa tarabu da 'Akram kullum cikin kuka takeyi tow yanzu kukan ma tadenayi saidai tayi azuciyar ta..


Granny tayi mata nasiha sosai ,sanan ta gasa mata jikinta suka taimaka, mata ita da Basma zuwa d'aki.


Dad ya farfad'o sai dai ya kasa, samun nutsuwa sai ,sambatu yakeyi ganin hakanne yasa,Doc...yi masa 'aluran bacci ,nan danan ya fara bacci ,sanan Doc ... Ya juyo garesu yace "ku kyaleshi ya huta,da 'alama 'an fad'amishi wata maganar da ta daki zuciyarsa, yana cikin shock ne, Amman insha 'Allah zai tashi cikin koshin lfy ya razana, ne sosai".


Mami dake faman kuka bata iya cewa komai ba Kalifa nema,yayi k'arfin halin iya, iyawa Doc... Magana .

Dad bai tashi ba sai wurin k'arfe hudu na rana, koda suka, koma gida be nemi Hajar ba ,kuma be sake zancen abunda ya faru da ita ba saidai duk randa ya ganta saiya tuna kuma yana jin zafin Hakan, Granny ta had'asu dagashi Har Mami tayi musu bayanin yanda sukayi da Hajar sanan kuma ta nuna musu ba laifin ta bane , duk da haka Dad be hakura ba don ko ,kula Hajar d'in basayi dagashi ,har Mami..

Koda yaji cewa 'Akram ,ne yayi mata ciki ya d'auki alwashin saiya kamashi ya rufeshi amman babu irin ,neman da beyiba ,Babu Akram babu dalilin shi,

Rayuwa tayiwa Hajar zafi, su Mami duk sun juyamata baya basa kulata, basa ,sauraranta gaciki ga rashin lfy da take fama dashi, komai ya daina mata dad'i gidan ma ya zame ,mata kamar mak'abarta batajin dad'in komai na rayuwa, bata fitowa kullum tana d'aki ,idan kuwa taga su Dad ,da Kalifa da Mami suna hira 'a falo suna ganinta duk zasu watse Kalifa ne kad'ai ke tausayinta 'a gidan gashi Basma ta koma Khadee ma ta koma gida 'Amman takan d'an zo , wajen Granny nine kawai take samun kwanciyar hankali , duk ta rame tayi wani 'iri kamar ba Hajar sarkin gayu ba sosai take nadamar Had'uwa da 'Akram da tayi da kuma irin saken da tayi masa harya lalata mata rayuwa ,rayuwa ta yi mata kunci ji take ,kamar ta dora hannu aka ta kurma ihu duk lokacin da tatuna 'abunda 'Akram yayi mata ,kullum cikin kuka takeyi....


Bayan wata d'aya da sati d'aya kwance take tana ,kallon POP d'in dake dak'in ta ,tana zubda ruwan hawaye bak'in cikine far cikin zuciyar ta don rabon da ta ,tsinci kanta cikin farin ciki harta manta, wannan wace irin rayuwa ce ina zan saka raina da 'bak'in cikin Akram zanji ko da bak'in cikin rashin kulani da iyayena basayi ? Wai shin su basusan kaddara bane? Ya sukeso nayi da raina ,yaushe abu zai k'are gare ni. Ni kaina nagaji da ,duniyar gabad'aya ya zanyi da Rayuwata da 'ace mutun zai iya goge abin da ya faru a baya cikin rayuwar sa ya zama tamkar bai faru ba da na saida raina don ,nayi hakan.a wannan rana Hajar ko fita daga d'aki batayi ba har wurin sallar magrib tun safe take ,kwance sallah ce kawai ke d'agata, Bayan sallar isha tafita falo taga su Mami suna hira ita da ,Dad ganinta yasa duk suka tsume kamar basu tab'a dariya ba , ganin haka yasa ,tayi niyar komawa 'Amman da yake tana so tanemi gafaran iyayenta kafun ta koma ga ubangijin ta yasa ta dawo ,don bata da tabbacin zasu kuma had'uwa daga wannan ranar..


*BY DIJA _WAZIRI*🤞
[18/12 7:32 pm] Dija Waziri: 💉💉💉💉💉💉💉
*DOCTOR HAJAR*👩🏻‍🔬
💉💉💉💉💉💉


masu biyoni privet akan ,na turo musu novel don Allah kuyi hakuri ,karkuce na shareku abubuwa ne sukamin yawa shiyasa don Allah kudinga tmby a group ,zan bude group duk meso saiya shiga idan yaso saina tura muku acen base nabiku daya bayan daya ba nagode da kulawar ku ,kuma nagode ,da k'aunar da kuke nunawa littafin nan 😍😍😍😍

*DIJA_WAZIRI*

Chapter 15


Dak'ar ta iya tashi ,tashiga toilet domin d'auro alola koda ta fito ,salaya ta d'auka ta ,tada salan nafila saida tayi raka'a goma ,sannan tayi salama ta d'anyi addu'ointa ,ta kama karatun kur'ani ba ita tabar kan salaya ba sai k'arfe 9 bayan ta idar da sallar isha , wayanta ,ta d'auka ta duba time ,sannan ta kashe wayar ta jona taji, tahau gado ta kanta ,kanta na fuskantar p.op d'in d'akin ,tunane tunane kawai take kala ,kala ,inama ace Allah zai d'auki ranta 'a yanzu da taji dad'i da 'ace akwai inda ake sayar da mutuwa da taje ta siyo ko nawa ne don tabar duniya ,haka ta dinga sak'e sak'e marasa kan gado , hannun ta d'aga sama tana rok'on Allah kan ya shige mata gaba 'akan dukkan lamuran ta sannan ya bata sa'ar cin jarabawa ya kuma bata juriya da, dangana 'akan duk halin rayuwan data ,tsunci kanta ciki , wasu zafafan hawaye ta fara fitarwa d'aya na bin d'aya ,haka har bacci b'arawo ya sace ta , bata san sanda Basmad, da Yesmeen suka shigo d'akin ba....Read more
[18/12 7:32 pm] Dija Waziri: 💉💉💉💉💉💉💉
*DOCTOR HAJAR*👩🏻‍🔬
💉💉💉💉💉💉



Chapter 16

INDIAN

"Yanda ka sanya Mahaifiyata kuka ,ka rabata da farin cikin ta, karaba da jin dad'in rayuwan ta ,kaci Amanar ta ,kaima wlh! wlh!! saina rabaka da ,duk wani farin cikin ka ,saina rabaka da ,duk wani jin dad'in ka ,kuma saina kashe ka . wlh saina maka ila kamar yanda kayiwa mahaifiyata ,abu mafi soyuwa 'a gareni wlh kaima sai kashiga kuncin rayuwan dakasa mahaifiyata ciki "

Yar ,yarice k'an -k'anuwa ,wacce a shekaru bazata wuce shekara biyar zuwa shida ba, tana sanye da jajayen kaya doguwan rigace iya cinya ,sai bak'in gashin kanta da ya rufe mata fuskar ,k'afarta sanye da wani bakin snikas me ratsin ja, hanunta rike da wani k'aton zarto me kaifi , nufar inda yake tayi gurine me ,masifar duhu babu abunda 'ake gani sai haske wani fitilan kwai wanda hasken be gama haske dajin ba ,babu abin dake tashi cikin dajin sai k'aran kukan jab'a da muka motsin ,namun daji ,babu komai gurin sai dogayen ciyayi koraye shar da suka tsiro , "yanzu ne lokacin daya dace na fara d'aukan FANSA 'akan Abunda kayiwa 'Abunda nafi so kuma nafi tausayi Hak'ika ,kai kacika cikaken mayaudari, maci amana ,be Ankara ba yaji saukan zauto a dede kwawalwar kansa...

"Ihun daya sakine yasa ,Hajja saurin banko ,kofar d'akin ba tare da salama ba, ganin shi tayi zaune kan gode ya dafe kansa yana sharara gumi duk sanyi ac dake cikin dakin be hanashi ,fitar da zufa kanar ,ruwa ba ,

"Lafiyan ka ,kuwa 'Akram?".

Kallon ta yayi ba tare da yace da ita komai ba yaciba da jan

Please Login or Register in order to submit comment