Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tausayin ta yakeji da tasan halin da yake ciki da ko magana bazata iyayi ba , yanzu idan ya mutu ya Ummi zataji yayi rayuwanta ze kasance ? Da' ace mutun yana d'aukewa kansa ciwo daya cire ma kansa larurar da take damun sa kodon Ummin sa, Wasu zafafan hawaye ne suka fara fita, ta gefen idon shi ba tare da kowa ya sani ba yayi saurin gogewa, duk abunda yake idon Dr Hajar na kansa , itama hawayen taji sun fara yinkurin zubo mata ,wani sabon tausayin shi taji ya kama ta, da sauri ta mik'e tabar d'akin ba tare da kowa ya sani ba...

"Ummi banajin yinwa yanzu ki bari anjima zanci" dak'er yake iya maganar yanayi yana ,nishi Dr Aiman da ,Dr Khadee ne suka shigo d'akin hanayensu dauke da wasu na'urori...

"Sanu Doc... Ya jikin ?" Cewar Dr Khadee da ,Dr Aiman "jiki Alhmdullah na samu sauki" tow Hakan muke so dama, ka shirya dai ko ?" Dr Aiman ya tambaya..

"Shiri kuma name?" Dr Samir ya tambaya ," kwantar da hankalin ka ba wani abu ,bene wanki zuciya za'a maka ,kuma ,muna fatan insha 'Allah zaka tashi lfy "cewar Khadee...

Binsu da Kallo Dr Samir yayi ,yana magana d'ekar "taya kuka san zan tashi nifa nace muku nawarke saboda haka babu inda zani" , duk abunda akace Allah ae angama Dr samir da yardar ubangiji zaka tashi kayi hakuri muje hakan shine ze iya kub'utar da rayuwan ka daga had'arin dake tare dakai, kai kasan komai basai nama bayani ba " cewar Dr Aiman...

"Look Doc.. Nifa nariga na gama ,magana " Haba 'abokina me kake nufi da hakan kenan kana ,nufin haka zamu zuba maka ido ciwo ya kashe ka tun ajalinka beyi ba?" Captian ya tambaya ranshi a b'ace. "Junaid ka tab'a ganin wanda ya mutu lokacin sa beyi ba? Duk wanda kaga ya mutu ,tow dama iya kwanakin da 'aka yanke masa ne ya k'are don haka ,ko amin wanki zuciya ko ,kar'a min wlh dama idan ajalina yayi dole natafi kuma dole kuyi hakuri dama haka 'Allah ya k'addara min saboda haka ina so kuyi ,imani da'Allah kawai"..

"Anya Samir kana son farin cikina kuwa ?".da sauri Dr Samir ya juyo da kallon shi kan Ummi "kamar ya Ummi ban gane me kike nufi ba?".

Jakar dake hanunta ,ta 'ajje tana hawaye tayo inda yake ta kama hanun shi "idan har kana ,sona kuma kana son farin cikina tow kaje " .duk yadda yaso da, danne hawayen idon shi amman ya kasa, saida suka zubo" shikenan Ummina zanje Amman ina so ki yarda, da k'addara kuma kisani cewa duk abunda ya faru dani haka 'Allah yariga ya k'addara min ina so kisani cewa ina sonki ,ina k'aun....... Wani 'irin tari ya farayi me had'e da jini duk yadda yaso daya k'arasa maganar da zeyi ,ya kasa .....

"Innalilahi wa inna ilaihi raji'un" shine abunda Dr Hajar ta iya furtawa yayin data shigo taga Halin da samir ke ciki..

Da sauri nurses suka shigo suka tafi dashi Ummi na rik'e da hanunsa tana kuka ,dak'er aka b'anb'are ta daga rik'on data masa ,suka wuce dashi itako Hajar office idinta ,ta shige tana kuka me tsuma zuciya Captian ko ,kama Ummi yayi suka zauna yana rarashin ta..

Dr Aiman da wasu manyan likitoci ne suka rufu kan Dr Samir don ceto rayuwan sa ..

"Hajjo "

"Na'am Khadee".

"Hajjo kina cikin damuwa ki fad'a min meke damun ki ,miye halak'arki da Dr don akwai wata 'a k'asa ?"..

Gilashin dake idonta ,ta cire ta fara goge hawayen fiskar ta"Khadee ni kaina ,narasa me nikeji game da Dr Samar Khadee bazan b'oye maki ba ina jin Dr Samir a raina kamar yanda nakejin Akram a wancen lokacin".

"Ban gane ba Hajjo kina ,nufin kice min kina son Dr Samir?".

"Kusan hakanne Khadee bazan iya auren Captian ba , kuka ne ya kufce ma ta.

"Ya ilahi tow meyasa kika b'oye man baki sanar dani ba Hajar?".

"Alokacin banyi tunanin da gaske son shi nike ba sai yanzu na tabbatar da hakan don Allah Khadee karku bari ya mutu ,mutuwar Dr ze ,zama barazana ga rayuwa ta kuma kiyimin Alk'awarin bazaki fad'awa kowa ba ina nufin amana ,na baki ,ko bayan raina karki fad'a ma kowa kinde san girman amana ?".

Cikin tausayin Halin da Hajar keciki ,Khadee tace "tayaya zesan kinayi Hajjo matsawar ba'a sanar dashi ba, kina ganin hakan bazai zama barazana ga rayuwan kiba?".

"Bazan iya bayyana masa ba Khadee cox ba lalle bane shi ya soni Amman inaso ki sani cewa komai ,ma ze iya faruwa dani har idan ,narasa shi".

Dafa ta Khadee tayi "ki dena kuka ,k'awata insha 'Allah zanyi iya kokari na, naganin ya samu sauki, Allah ya mana jagora."

Hajar da kanta ke, kife tana kuka ,tace "Ameen "


Bayan Awa biyu.

Ganin fitowar Dr Aiman, ne yasa su Ummi saurin ,nufo shi "lfy dai kow Doc"..cewar Captian ,murmushi Dr Aiman yayi "lfy qlau sai mugode wa 'Allah anyi masa 'aiki lfy ,yanzu ,za'a gyarashi a kaishi d'akin daze huta sai kud'an barshi ya samu hutu kamar na awa goma " wani ajiyar zuciya Ummi ta sauke tare da hamdala da godewa Allah


Nasan kuna hakuri dani kudai kara komai ya kusa dawowa nomal ku sani ina k'aunar ku❤❤❤❤❤


*BY DIJA_WAZIRI*💉
[18/12 7:32 pm] Dija Waziri: 💉💉💉💉💉💉💉
*DOCTOR HAJAR*👩🏻‍🔬
💉💉💉💉💉💉



Chapter 26


*KAD'AN DAGA CIKIN ILOLIN CIN AMANA*

*TUNA TARWA*

*Cin Amana wata 'abace da wanda 'Allah ha hana yinta cin Amana yana d'aya daga cikin halayen munafurci manzon Allah ya lissafta wasu halaye guda uku ,yace duk wanda yake dasu acikin halayensa ,to hakika shi munafiki ne. koda yayi sallah yayi Azumi yayi hajji yayi umrah, koda yace shi musulmi ne (subhanallah!!)*

*Cin Amana yana sanya mutun yayi baqin jini acikin al'ummah, darajarsa da mutuncinsa su zube, sannan kuma al'ummah su rik'a gudunsa.*

*Yana daga cikin abubuwan da suke tauye imanin mutum. Matuk'ar mutum zai rik'a cin amanar mutane ,to kullum imaninsa raguwa yakeyi*

*Yana d'aya daga cikin halayen da suke qaskantar da darajar mutum awajen Allah.matuk'ar mutum bai rike amanar bayin Allah ba,*

*wannan tuna tarwa ce garemu baki daya yan uwa musulmai, ya zama wajibi mu rik'a kiyaye amanar junanmu don samun mutunci a wajen Allah da bayin Allah.*

*Idan kasan bazaka iya rik'e waba tow karma ka ,karb'a bare ya zame maka ,kaya*👐

*Allah yasa mudace ya kuma bamu ikon rik'e amanar yan uwan mu Ameen*

Chapter 26

TWO WEEKS LETAR


Kwance yake kan Sofa yana kallon MBC action, Ummi na gefen shi tana had'a kan magun gunan data gama bashi "Likita "Ummi takira sunan shi tana cigaba da zuba magun gunan cikin wani basket, "Na'am Ummi" ya 'amsa yana cigaba da kallon film d'in 4 brothes d'in da 'akeyi .

Saida ta gama kwashe magun gunan sannan ta mik'e ta nufi wurin Tv ta kashi ,ta dawo ta zauna kusa da ,Dr Samir "munyi magana da Dr Aiman wancen satin daya wuce bayan an salame ka , ya shedamun cewa 'akwai damuwa 'a tattare dakai don haka na tmby ka , kasan baka da kowa 'aduniyar nan saini baka da wanda yafini a yanzu ,da wannan damar nike rok'on ka daka sanar dani damuwar ka likita ina son ka rashin kwanciyar hankalin ka babban matsala ce a rayuwa ta rashin ganinka cikin walwala ba k'aramin dagamin hankali yake ba don Allah kasanar dani damuwar ka", murmushin da iya karshi fatar baki yayi sannan ya mik'e daga shingid'ar da yayi ,ya kama hanunta yana shafawa"Ummina ki ,kwantar da hankalin ki ,insha Allah ina tare dake har gaban (ABADAN) Littafin safiya Bani da wata damuwa Ummi yau rabon da ciwona ya tashi ,irin haka ,kinga 'ai anjima yan zun ma Allah ne yayi ze tashi" tow Likita naji tunda kace baka da matsala 'Allah yasa hakanne , yanzu dai na yanke wani hukunci Amatsayina ,na mahaifiyar ka ,nasan bazaka ,k'i abunda zan sanar dakai yanzun ba ,ni bazan tursasa maka dole ba idan kaga bema ba hukuncin ,dana yanke ,karka b'oye man ina so ka sanar dani ,na zauna ,nayi nazari da tunani ,kuma naga yadace na sanar daikai buk'atata mezai hana ka 'auri Salma...."

Kayan abincin da Salma tashigo dasu ne sukayi saurin sub'ucewa daga hanunta, yayin da taji furucin Mami, "subhanallah lfy Salma tunanin me kike haka ?" Cewar Ummi , Salma jiki babu laka fuskar ta,babu walwala tsugunawa tayi tana tsince kofin tangaran d'in daya fashe ,idon ta na son zubda hawaye Amman ta danne alamun damuwa suka bayyana 'a fuskar ta ,kanta na k'asa ta maida hankalin ta kan kofin da take tsincewa tace"Afuwan Ummi tuntub'e naci ban sani ba " tayi saurin daukan farantin ta koma kitchen .

Shiko Samir sanda rewa yayi ,yana k'ara maimaita furucin Ummi cikin k'asan zuciyar shi ka auri Salma! Ka auri Salma!! Da wani ,idon ze kalli Salma taya ze iya 'auren k'anwar matar shi ? Wata zuciyar shice tace tow ae ba haramun bane ,yaya zeyi da soyayyar Hajar ? Wannan shine rana zafi 'inuwa kuna dole ya janye kudurinshi akan Hajar saboda tamai nisa baze tab'a furta mata cewa yana son taba koda hakan zeyi barazana ga rayuwan shi ,tunda Captian yariga shi dole ya cire duk wani soyayyar da ya jima yana ginawa cikin zuciyar sa koda hakan zesa ya rasa, rayuwan shi da wannan tunanin ya ,yanke hukuncin karb'an umarnin Mahaifiyar sa ,don bashi da zab'i sai wanda 'Allah yayi masa dole ze koyawa Salma son shi ze koyawa zuciyar shi son ta, tow Amman tayaya? Bayan shi ya d'auketa ,tamkar kanwar da suka sha mama tare. Anya baze cutar da ita ba kuwa baya so ta d'and'ana kwatan kwacin abunda ya d'an d'ana lokacin da 'akace ya rasa Jamila ,shi yanzu bame nisan kwana bane ya riga yasan iya adanin watanin daze k'ara nan gaba likita ya shaida masa cewa kodar sa ta kagar ,gaje matsawar beje ancire taba ,nan dayan watanin ze iya rasa, rayuwan sa yaki sanar da Ummi ne saboda besan irin halin dazata shiga ba, bayan ta sani

"Ya naji kayi shiru Likita bafa umarni ,nike baka ba shawara ce , idan kaga bema ba babu dole kaji d'ana ban tab'a ma dole ba kuma bazan tab'a ba insha Allah abunda kake so kake muradi shine ,nawa ".

Salma dake jikin k'ofar kitchen tana jin duk abunda ke faruwa 'addu'a kawai takeyi Allah yasa karya ce ya 'amince don ko bazata ,tab'a iya 'auren saba zata cikawa yayar ta burin ta , kuka take wanda babu hawaye , tunanin rayuwanta na baya ta farayi tare da irin wahal halun data sha.

"Ummi nasan bazaki tab'a min zabi mummuna ba ,kuma bazaki tab'a bani abunda kika san ze cutar dani ba , Nasan Salma bata da matsala mace me hakuri da sanin ya kamata, na 'amince zan aureta kamar yanda kika buk'ata ".


Ajiyar, zuciya Ummi ta saki tare da hamdala ga ubangiji, rungume shi tayi "na gode d'ana kai ,kadai zaka iya rike marainiyar Allah Salma yar uwar kace nasan bazaka cutar da ita ba, shiyasa na zab'i ka zauna da ita badon komai ba, Allah ya maka 'Albarka ya k'ara maka lfy". Ameen Ummi na fahimce ki " tashi yayi ya kunna tv ya cigaba da kallon shi ,Ummi kuma ta d'auki jaridan Daly trust wanda tun wancen satin Habu drive ya siyo mata bata karan taba kasan cewar ita ma'a bociyar karance karancen labarai ce dalilin dayasa kullum safiya da maraici Habu saiya siyo mata


Salma ko, kasa b'oye damur da tashiga a wannan yammacin tayi, sama tahau zuwa d'akin ta ,ta kulle tafara, rusa kuka,

"Innalilahi wa inna ilaihi rajiun Samir " Na'am Ummi lfy?" Yayi saurin matsowa kusa da ita " inafa lfy kaga Mahaifiyar d'an uwanka 'ankama ta da coken cikin kaya " subhanallah " karban jaridan yayi ,ya kalleta sosai yaga tabbas itace ,tacikin hoton da mahaifiyar shi ta bashi yaje ya nemo su, karan tawa yayi anan yaga sunan gidan yarin da 'aka rufeta 'anan birnin tarayya 'abuja...



Ga wannan bubu yawa sai anamin uzuri buk din ma yazo karshe 👐



*By Dija_Waziri*💉
[18/12 7:32 pm] Dija Waziri: 💉💉💉💉💉💉💉
*DOCTOR HAJAR*👩🏻‍🔬
💉💉💉💉💉💉

*WANNAN SHAFIN NAKUNE TEAM CAPTAIN JUNAID INAJIN DADIN COMMENTS DINKU LOVE YOU GUYS* 😍😍


*Allah ya halicci dan adam akan halaye daban daban .don haka ake samun masu sauk'i da masu tsanani cikin mu'amalar mu ta yau da gobe.*

*Yana daga cikin shiriyar Annabi an nusar damu neman tsarin Allah daga sharrin kawunan mu da miyagun aiyukan mu, don haka duk wanda zakayi mu'amala dashi to yana iya yi maka dai-dai kuma yana iya yi maka kuskure.*

*Mu sani duk wata tawaya ko jinya ko laruri data same ka maganinta shine ayi hakuri a mayar da abin ga Allah .yana da wuya ace kullum sai anyi maka yadda kakeso ,ko sai kaji abinda zaiyi maka dad'i, ko sai idon ka yaga abinda zai faranta maka rai. Don haka rayuwa sai ka had'a da hakuri akan komi.*

*Hakika ba wanda kuskure ko matsala ba zata riskeshi ba cikin harkokin rayuwar sa a tsakanin sa da iyalan sa, makusantan sa ko al'ummar da yake raye a cikin ta.maganin kowacce irin damuwa shine hakuri ,addu'oi da mayar da al'amarin ga Allah, gamuwa da kunci ,wahala tsanani da ,damuwa duk mai yiwuwa ne ga kowa gwargwadon yadda aka qaddara masa ,kuma ba wanda zai iya kaucewa abinda 'aka qaddara masa na sauki ko tsanani a rayuwar sa don haka anan ma hakuri da duk halin da ake ciki shine mafita ga kowa*


*Ya ubangiji ka bamu juriya da hakuri akan abunda kana iya ramawa ko daukar fansa Allah ka sawa zuciyoyin mu kasa mana hakuri alokacin da muke cikin damuwa*

Chapter 27

ABUJA
Cike gidan su Basmad yake da ,d'unbin jama'a yan uwa da 'abokan arziki,

Zaune suke cikin daki su wurin biyar suna , ta yiwa 'amarya tsiya Hajar ko ta koma gefe tayi shiru hanunta bisa kumatun ta zabga uban tagumi, "Hajjo wai meke damun kine tunda kuka zo kin ,kasa ,sakewa kow kina kewar Jawahir ne?" Cewar Basmad Hajar bata masan Basmad nayi ba don ko ta lula duniyar tunani, saida Khadee ta ,tab'ata ,tukun ta zabura hankalinta ya dawo gareta"lfy Khadee ?" Cewar Hajar "nice nace ta ,tab'a min ke nace meke damun kine wai" Basmad ta ,tambaya..

"Babu komai me kika gani wlh kurum ina tuna rayuwan dane " Eyyah ki dena wannan tunanin ke ,kinsan babu abinda ze haifar maki na farin ciki ,yanzu kitashi muje ku anso d'inki ,ku daga nan su Khadee su dawo gida ke ,kuma sai kirakani gidan su lusey" Basmad ,da kunje kawai keda su khadee in yaso idan kun karb'o d'inkin Farida ta rakaki gidan su luseyn ,ni kaina ke ciwo" kedai kawai kice bazaki rakani ba karki wani fake da ciwan kai Khadee muje kurakani".

"Hmm Basmad kinsan de bazan maki ,k'arya ba kow? Amman tunda kikace haka muje" taja mayafin ta suka fice, koke fa 'Amman da ,duk ,kinbi kin takure kanki cewar Khadee

*****
"Samir wai mekazo yi abuja ne ma?" Captian ya tambaya "wlh wani Babban abune ya kawoni, ina sadiq k'anina dana ce maka zanje neman shi kwanakin baya ? Tow shine mukaga mahaifiyar shi wai ankama ta da coken cikin kayan ta ,kai meya kawo ka?" Eyyah nagane Allah dai yayi da rabon zaku gana da k'anin ka da har ance sun mutu ,wlh Dady ne ya turo ni wai na yi masa wani aiki ".

"Masha Allah yanzu tunda 'Allah yasa mun hadu dakai zaka rakani gidan yarin bayan sallar azahar" ok Allah ya nuna mana cewar Junaid.


"Tow na manta ban sanar da kai ba zanyi aure nan bada jimawa ba " what kana ,nufin kace min kasamu wacce kake so?" A'a 'ae ni bazan kuma samun wacce nike so ba sama da Jamila , kawai zanyi auren ,ne bisa bani da yanda na iya sai abunda 'Allah ya tsara mi. " tow ,Wacece madam d 'in tamu ?" Murmushin da bekai zuciya ba Dr Samar yayi ba kowa bace kuma kama santa Salma ce".

Zaro ido Captian yayi ,yace "Salma fa kace ?", Eh itafa kaji mamaki ,kow umarnin Ummita zanbi " ba dole nayi mamaki ba 'Allah ya tabbatar da 'Alkairi, nima dai na kosa wlh naga nayi aure Amman wannan k'awar taka tak'i bani dama na tura magabata na".

"Ni ba k'awata bace Hajjo k'anwa tace don ko najima da cireta sahun k'awaye na , kad'an k'ara hakuri nasan zata baka daman , duk da ban saniba ina tunanin dakwai dalilin daya hanata baka daman Amman ka ,k'ara hakuri " tow ae gashi munayi ni yanzu ita kawai nake jira ", sun jima suna hira sai gurin k'arfe shabiyu suka rabu..

"Kinga tsabar iskanci Hayati yabar mu sai jiran sa mukeyi Hajjo". Wai ma ,mezai kawo maki ne Basma nifa kaina ciwo yake idan bazai zoba muwuce gidan su lusiy idan yaso ,yaje cen ya sameki , tun shabiyu ,ya shanya mutane gefen titi gashi har d'aya tayi".

"Yi Hakuri barin kuma ,kiran shi shaddar dazan sa jibi zeban , angon ,nawa ne ya shanya ki?" Basmad ta fad'a 'a zolaye , Hajar bata kula taba taci gaba da, danne dannen wayar ta ,suna cikin zaune ,ne wani yazo ya kwan-kwasa gefen glass d'in Basmad kansa d'auke da farantin kifi ga dukkan alamu na siyar wa ne , bud'ewa Basmad tayi ,tana "Malam lfy?" Lfy qlau Hajiya zaku sai kifi gasheshe?" A'a Allah bada sa'a " Hajar ce ta d'ago da sauri "sai...." Ganin mutumin yasa ta kasa k'arasa furta 'abunda take da niyya bakinta ne ya fara, rawa tana, nunashi da yatsa "wannan ba Musa bene?" Innalilahi wlh saida kika fad'a na gane shine mana 'abokin Akram kow?".

"Tabbas nine Musa 'Abokin akram wlh najima ina ,neman ki Hajjo na rok'i gafaran ki ,Akan abunda 'aka had'a baki dani akayi maki ,kinga yanda 'Allah yayi dani kow , hakika bayan tafiyar Akram naga rayuwa nahadu ,da balai masu yawa 'a wannan lokacin , nayi nadamar abota da 'Akram ina cikin zamana yazo ya d'aurani a hanyar banza .

Yanzu kunga yanda rayuwata, ta kasance don Allah ina rok'on ki da kiyafe man wlh nayi nadama ,nine babban mutumin dayafi bawa 'Akram gurb'a taciyar shawara Akan yaga ya ci nasara 'a kanki".

Hajar da kuka yaci k'arfin ta bata iya cewa komai ba , basmad cema ta samu kwarin gwaiwar yin magana "yunzu Musa miye riban ka na 'abunda kayi jibeka fa yanzu kabi son zuciyar ka ,yanzu ji yanda 'Allah yayi da rayuwan ka ,kai kenan ma shi kuma 'Akram d'in Allah shine masanin irin halin da yake ciki , wannan kad'ai ya isheku darasi a rayuwa dama ance duk wanda ya zalunci d'an uwansa tow Allah saiya saka masa fad'ar manzon Allah ne, ku cin amanar ma kurasa wanda zakuyiwa sai mace me hakuri sanin ya kamata mace me karamci kasani cewa yanzu ka fara ganin rayuwa inde ku junanku cin Amana ce , cin Amana yana daga cikin abubuwan da suke tauye imanin mutum .mutukar mutum zai rika cin amanar mutane, tow kullum imaninsa raguwa yakeyi, haka zalika yana zama sanadiyyar dulmiyar mutum acikin wutar jahannama. Kamar yadda yazo acikin hadisi , Allah zai sanya amanar acikin chan qasan wutar jahannama , sannan a umurci maciyin amanar cewa ya shiga ya dauko -ta sai ya dauko ya hauro wani babban tudu, sannan sai ita kuma Amanar ta subuce ta koma chan qasan ramin jahannama .sai mala'iku su daka masa tsawa suce ya koma ya daukota. Haka zai yi ta yi har illa masha'Allah .

Tow kaga kuwa kuncin rayuwa da bala'in rayuwa da masifa yanzu kuka ,fara fuskanta tunda junanku b'ata yaran jam'a".

Kuka Musa yakeyi sosai "Nasan ,na 'aikata ba daidai ba Hajiya don Allah ku gafarce ni".

Sai Alakacin Hajar ta d'ago daga ,durk'ufar da kanta da tayi tana kuka ,cikin kakkausar murya tace " bani da buri a duniya daya wuce naga Akram da ma duk wani wanda 'aka had'a baki dashi akaci mutunci na sun wulak'anta sun tozarta sun zama 'abun kwatance a duniya 'Allah ya isa tsakanina da 'Akram Allah ya isa tsakanina daku Basmad ja motar nan mutafi " Babu ,b'ata lokaci Basmad taja sukabar gurin ,suka barshi yana kuka .

Doc... Kaga wancen motar kamar Hajjo ce aciki " kallon gun Doc...yayi ,yace itace ma " tow me tazoyi abuja kar dai har bikin cousin d'in ,nata yayi ?" Tow ,wata k'ila " don Allah bari mu bisu Doc...sorry " murmushi kawai Dr Samir yayi ,yace muje


Kuyi hakuri da wannan babu yawa




















*By Dija_Waziri*💉
[18/12 7:32 pm] Dija Waziri: 💉💉💉💉💉💉💉
*DOCTOR HAJAR*👩🏻‍🔬
💉💉💉💉💉💉

Dedicated this page to my mom who has love and taken care, of me for all of my life she has taught me to love others and to always tell...i love you so very much my mother Allah ya k'ara maki lfy da nisan kwana 😘😘😘

Chapter 28

Dede kofar gidan su Lusy sukayi parking , Dr Hajar ce ta fara fitowa , sai Basmad ma ta fito dede zasu shiga cikin gidan sukaji an kwala musu kira.

"Hajjo"

tsayawa hajar tayi cak ba tare da ta juya ba ,Basmad ne tayi saurin juyawa tana "suwaye kuma haka" ganin Captin yasa tayi shiru..

Har inda su Hajar ke tsaye sukazo , "Barka 'Amarya, ya garin munyi fushi tunda mu ba'a gaya cemu bikin ba " Cewar Captian

Murmushi Basmad tasa "sanun ku gari lfy qlau ae nazaci Hajjo ta gaya maku " kallon Hajar tayi da kanta ke ,k'asa "Hajjo damun baki sanar dashi ba ?" Ko d'agowa Hajar batayi ba ,bare ta basu amsa. Shiko Dr Samir tunda suka tsaya 'agun hankalin shi ke ,kanta shi a yanzu ya hakura da ita duk ,da har cikin zuciyar shi yana jin zafin rashin samun ta, Amman kuma yana jin dadi had'uwarta da Captian don kuwa dashi ta ,dace yana da masaniya' akan idan ta 'auri Captian zataji dad'in rayuwar ta zata manta da komai, Amman shi 'idan ta 'aureshi babu abinda ze haifar mata sai tarin wani k'unci da ,damuwar zeyi 'iya kokarin shi na ganin ya taimaki abokinshi wajen shawo kanta, har soyayyar sa tayi tasiri a cikin zuciyar ta, wannan shine halacin daze iya, yiwa 'abokin nashi kamar yanda suma suka masa halaci shida mahaifiyar sa 'alokacin da suke tsananin buk'atar taimako da ,d'auki..

"Yau kuma ko yar gaisuwar bazamuyi ba Hajjo naga kin b'ata rai kamar kina cikin damuwa hope lfy dai kow?" Captian ,ne yayi maganar

D'agowa tayi ,tana wasa da k'asan gelen ta , murmushin da bekai zuciba tayi "wlh babu 'abinda 'akamin kaina ke ciwo ,ina wunin ku?".

"Allah sarki Allah ya sawak'e hope kinsha nagani dai kow ? ".

"Eh nasha kafun ,na fito me kuka zoyi abuja?".

Dr Samir haka ,kurum yaji baze iya tsayawa yana kallon suba, don komai ma ze iya faruwa dashi matsawar ya ciba da kallon su "Hajar Allah ya sawak'e , idan kinajin ciwon sosai ,idan kin koma kisha panadol nyt insha 'Allah zaki samu ,sauki" Abokina ,ni bari naje mota na jiraka , kasan ban cika tson tsayuwa ba "..

"Tow nima yanzu ,zanzo bazan jima ba sorry nashiga lokacin ka 'Amman insha Allah yanzu ,zanzo mutafi "

"Karka damu ku gama hiran ku a tsanake ko 4 ne zamuje".

"Tow nagode abokina".

Har ze wuce ya tsinto muryan Hajar tana " sai anjima Doc...".

Batare da ya kalle taba yace sai kin dawo kusha biki lfy ni gobe zan koma"

Basmad ce tace ae ko Doc... Sai kajira anyi daurin aure tukun kakoma, gama card ,d'inku "..

Captian ,ne ya k'elk'ele da ,dariya "dama nace kajira mu koma tare kaki, yanzu ae ka jira"...

Murmushi Dr Samir yayi ,yace "sorry Basmad wlh ina da 'aiki cikin kwanakinnan kwata ,kwata bana zama 'aiki sunmin yawa yanzun ma Ummi ta ,tursasani ,nazo "..

"Eyyah tow babu damuwa Doc... Nama uziri , Amman idan munzo shan bikin Hajjo baka zo ba karkayi tunanin zamu ,ma 'uzuri"..

"Ae dolen shima yazo yana babban abokin ,nawa 'ai idan bezoba ,bani bashi"...

Murmushi Hajar tasa tace "Haba Captian kai, kobaka uzuri ,kasani lokacin bikin ,naka ya kasan ce kuma yana muhimmin wani abun ?"..

"Tow tayani tmby Kanwata , ae wannan saurayin naki besan uzuri ba"..

Hajar najin Dr Samir yace saurayin ta, ta wani hadarai ta sunkuyar da kanta...

"Ae abokin ,nawa ne bashi da kirki Hajjo" cewar Captian..

"Tow nikam

Please Login or Register in order to submit comment