Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

,HAUWA ,NAJMA(BABBAR YAYA)*😎 *AND AUTARAS HUSNA*

*SOYAYYAR KU DABAN TAKE BASAI NA TSAYA DOGON TURANCI BA*πŸ’˜πŸ’˜


Chapter 39

Kwantar da ita 'akayi akan kujera Dady yasa, Mami ta kawo ruwan d'umi da farin k'ele ya fara ,saka mata'a goshin ta, cikin min tuna kad'an ta farka ,tana farkawa sunan Dr Samir ta fara kira, ganin mutanen dake kanta yasa ta mik'e ta fara kallon su d'aya bayan d'aya har ta sauke, idon ta kan Mami da gudu ta mik'e tayi kanta, tana kuka tana "Mami shi kenan Dr Samir ya rasu shi kenan mun rasa ,shi "rik'eta Mami tayi, tana rarashin ta Dady kuwa kallon Mami yayi ,yace "wai meke faruwa ne waye kuma Samir kode tayi gamo ne?" Ba gamo tayi ba 'Alhaji har ka manta Samir d'in wannan abokin ,nata doc.." Ok natuna shi meya sameshi ?" Dady ,ya tambaya" Wlh ina zan sani Alhaji gashi dai munji tana ya mutu Khadee ko ,kunsan meke faruwa?" Mami ta ,tambayi Khadee "wlh bamu sani ba Mami kawai muna kallon had'arin jirgin saman da ya faru d'azu ne mukaga ta yanki jiki ta fad'i".

"Tow Allah dai yasa lfy "cewar Dady duban Hajar Mami tayi ,tace "Hajjo lfy meya samu Samir d'in" hajar na kuka tace "Mami mun rasa, Samir har dashi cikin jirgin d'azu Junaid yake cemin yana hanya daga turkey ze dawo kano"..

Gaba d'aya falon suka ,fara salati, Khadee ma bata, san lokacin da kwala yazo mata ba , ki dena kuka Mamana ba lalle harda shi ba tunda 'ance da 'akwai ragowan biyu suna hospital d'inmu ,kuje ku duba cikin su ko Allah zesa yana ciki".

Babu musu Hajar ta zari hijabi da takalmi suka, kama hanya ita da Khadee da wata yar uwar su ,sukaje kasan cewar Basmad tayi nauyi bazata iya zuwa ba ..

Suna isa kafun ma su shiga sukayi karo da Captian da Ummi da Salma sun fito, ganin su yasa Hajar tayi saurin nufar inda suke ko gaishe da Ummi batayi ba tace "Captian Allah yasa dai be mutu ba kun ganshi?" A firgice take maganar ,murmushi ya saki mata yace "kwantar da hankalin ki bashi bane yanzu ,nakira wayan shi ya shiga kuma wai yana legos ,sai gobe da safe zasu iso an dakatar dasu tun 7:30 na dare suka sauka, rashin charge yasa be kira ba" lokaci guda Hajar tayi wani ajiyar zuciya tace Alhmdlh wlh yau ,mun tsorata mun girgiza ni wlh har hantar cikina saida ya k'ad'a ubangiji mun gode maka, Salma ina tayaki murna " murmushin yak'e Salma tayi ,tace nagode Hajjo harkin d'an fad'a , wlh kowa yaganki zesan da 'alamun tashin hankali a tare dake "ba dole ba Salma rashin Dr Samir a garemu babban rashi ne a rayuwan aluma baki d'aya 'ae rabon da nashiga tashin hankalin dana shiga yau har na manta" ae abun babu da d'i "cewar Salma "ae Hajjo har suma saida tayi na gaya miki Salma tsabar tashin hankali" Khadee ta fad'a fuskar ta d'auke da fara'a "suma lalle Hajjo kina son wannan yayan ,naki "Captian ya fad'a yana dariya murmushi kawai Hajar tayi suka durk'usa har k'asa ita da su Khadee suka gaida Ummi , sannan su Captian suka wuce ,suma su Hajar d'in ko ,k'arasawa cikin asibitin basuyi ba suka juya suka, koma gida....

"Junaid wai wacece ,wannan yarinyar "Ummi ta ,tambaya "au dama baki san taba Ummi ?ae itace me wannan hospital d'in diyar Dr Galadanci ,ce itace first bon d'in shi ,kuma k'awar Samir ce sunfi 5 years tare kuma itace dai Hajar d'in matar da zan aura" Allah sarki ni 'ina zan sani kasan Samir miskilin mutune shi ko hira baya wani tsayawa muyi sosai bare nasan da ita, kanaga har Salma ta santa da yake ita matar sace ae har ya nuna mata ita, kuma kaima tun yaushe nakece ka nuna min hoton matar taka, kak'i yau dai gashi na ganta ,gsky kayi sa'a duk da ban san halin taba 'amman daga ,ganin alamu tana da tarbiyayya da kunya Allah ya baku zaman lfy" sunkuyar dakai Salma tayi batace komai ba " a kunyace Captian yace "Ameen ".

"Junaid kaga yaron da muka gani cikin wainda sukayi hatsarinan d'ayan med'an gashi akai d'innan me bak'in riga ,wlh kamar d'an uwan Samir ne, don ,naga kamar yana kama da wanda mahaifiyar shi ta. Nuna mana hoton shi" Allah Sarki ze kuma iya kasan cewa shid'inne amman gsky ,yana jin jika Ummi har fa yafi d'ayan don gsky ina tunanin k'afar sa ,sai dai a yanke don duk ta dadage ko ,k'ashi fa ba'a iya gani tun daga cinyar shi har zuwa d'an yasan hanun shi, gashi kanshi yayi mugun fashewa sai jini yakeyi hanun daman shima gsky zeyi wuya ,ya kuma 'aiki don shima ya dadage kuma daga k'asan cibiyar shi yayi k'asan shi duk ya k'one zafin wuta ,wlh abun ,babu ken gani bari gobe idan Samir ya iso ,sai mukuma zuwa mu duba ko shine".

"Innalilah Allah ya bashi lfy ,shiyasa na fito ina ganin k'afar sa naga bazan iya tsayawa ba, fuskar shice kawai batayi komai ba ,wlh duk me imani tow zai tausaya masa, gsky ,yana jin jiki" Ameen Ummi wlh ya wahala kam" Captian sai da yakai su Ummi har gida sannan shima ya koma gida..


WASHE GARI

Da misalin k'arfe sha biyu na rana Captian yaje filin jirgi ya d'auko Dr Samir , koda ya d'auko shi cewa yayi ,su wuce asibitin Hajar don yaje yaga ko d'an uwan shine ,don tun jiya Ummi ta fad'a masa cewa taga me kama da ,d'an uwan shi cikin masu hatsari..

"Abokina jiya ka firgita mutane da ,dama Hajjo harda suma duk mun zata ka rasu" Uhm Allah Sarki tow ranar da 'akace nayi mutuwan gsky ,kuma ya zakuyi?"zaka fara kow tow mubar zancen ya isa haka"cewar Captian .

"Tow dama ae kai kafara kawowa kuma, mutuwa dai ta zame ,mana dole ko munaso ko bama so " Captian bece komai ba ya cenza ,zancen .

"Wai ,kai awani gida zaku zauna kaida Salma naga bakayi tanadi ba?" Ni bazan rabu da Ummi ba 'a sashina zata zauna babu wani gida ,dazan siya".

"A'a kaji d'an gidan Umma hakan ma yayi, nikam a zoo road zamu zauna 'anan ,nasai gida 'amman gsky zaman mu zefi yawa 'a Faris " Allah dai ya nuna mana "Ameen ae saura 4 days "cewan Captian.

Parking yayi , cikin Haraban asibitin, lokaci guda Dr Samir yaji wata fad'uwar gaba da fargaba sun ruski zuciyar shi.

Gabaki d'aya ,yaji ,jikinshi yayi sanyi har suka ,k'arasa cikin d'akin , shi kad'ai ne kwance a ciki babu kowa kusa dashi an saka mishi ruwa d'ayan hanun kuma roban jini ce ,sai kuma roban abinci da 'aka sa masa , k'afar shi ta dama 'an rufeshi da wani farin k'elle kan shi kuma 'an d'aure shi da bandeji.

Hanun shi na haguma da wani farin k'ellen aka rufe, yanda mutun bazai 'iya sanin me 'akayi ma gurin ba.

"Innalilahi wa inna ilaihi raji'un "

Shine abunda ,Dr Samir ya iya furtawa.

"Lfy Dr Samir".

Cikin fargaba da tashin hankali Captian ya tambaye shi.

Dak'er Dr Samir ya iya 'amsa masa bakin shi na rawa.

"Shine Jinaid Shine D'an uwana da nake ,nema wlh shine".

Ganin yanda Dr Samir ya rikice yasa Captian dafashi yana ,bashi hakuri, kasa jurewa Dr Samir yayi ya nufi kofar fita daga ,d'akin don bazai 'iya jure ganin d'an uwan ,nashi cikin irin halin da yake ciki ba.

Don tunda ya ganshi yanzu yaji wani k'aunar shi da soyayyar shi, sun mamaye shi, dama ya jima yana son yaga yana da yaya ko ,k'ani a duniya 'amman hakan be yuwu ba, yau gashi rana tsaka ya ga d'an uwan ,nashi amman yana shirin rasashi.

Dede ze fita likita ya banko ,k'ofar d'akin da sauri ganin likitan yasa Dr Samir daka tawa .

Har inda 'Akram ke ,kwance yaje ya duduba shi yaga be tashi daga bacci ba kuma yaga komai yana tafiya daidai.

Sanun ku pls ko ,kune yan uwan, wannan bawan Allah don yanzu wata nurs tace min wasu, sun zo?".

Junaid ne ya iya amsa Doc.. D'in.

"Eh mune Doc ya jikin ,nashi wlh bamu samu labari da wuri bane sai d'azu muke ji".

D'an jim kad'an Doc... Yayi sannan yace.

"Tow jiki gadai shinan zance, Amman ina son ku sameni a office yanzu idan ba damuwa".

Ya wuce ya barsu gurin.

Kallon Captian Dr Samir yayi ,Fuskar shi da'alamun tsoro da fargaba ya girgiza ma Captian kai alamun suje.

Γ—Γ—Γ—Γ—Γ—Γ—

"Yawwa 'a jiya da 'aka ,kawo mana wainnan mutane guda biyu d'aya ,yan uwan shi sun sameshi kuma sun tattara shi sun tafi da 'abun su ba tare da munsan ina suka ,kai shiba,

Shi kuma wannan d'an uwan ,naku ,mun zauna mu jira ko, Allah zesa wani ,nashi yazo mukaji shiru ,har wurin k'arfe uku na dare babu wanda yazo.

Ga ciwo ajikin mutun Hakan yasa ,muka ,kira Dr Galadanci muka sanar dashi ,halin da 'ake ciki yace muyi mishi duk abunda ya kamata.

Kafun a samu yan uwan shi suji . hakan yasa muka yanke hukunci yi masa 'aikin daya dace .

Tow sai dai kuyi hak'uri da 'abun da zan fad'a kun san ita kadaddara takan fad'a kan ,kowa ne aduk sanda tazo ma bawa , jarabawa ce ,wacce sai mai rabo ke iya cenye ta.

Ina so kuyi tawakali da Ubangijin mu, kuma ku gode masa ku d'auka cewa komai ba komai bane face tsarin ubangiji ,kusani duk abunda ze faru da bawa dama cen rubutatce ne ku......."

"Doc....ka fad'a mana meke faruwa pls shi muke buk'atar sani ayanzu".

Dr Samir ya tsaida shi.

Sai daya d'anyi jim kad'an sannan yace.

"D'an uwan ku ,kanshi ya bugu sosai ,muna 'addu a da fatan kar Allah yasa wani abu ya faru da kwakwalwar shi.

Sannan ya rasa k'afar shi na dama da hanun shi na hagu ina ,nufin an yanke su don koda an barsu bazasu kuma 'aiki ba.

Daga cinyar shi yayi kasan shima ya samu konuwa sosai wanda nake tunani abubu ,abinda ze kuma 'aiki a gurin.

Ya kuma samu karaya a k'ashin bayan shi bazai kuma tashi ba, ze k'are ,rayuwan shi a hakane har Allah ya kawo ranar daya, kayade mishi a duniya "

"Ya 'Allah "

Dr Samir ya fad'a yayin daya dafe kanshi yana ,jin yana masa wani 'irin nauyi zuciyar shi na masa wani 'irin zafi da zugi

Magan ganun Dr ne kawai suke tayi masa yawo a konyar kanshi .

Lalle rayuwa ba komai bace babu komai a duniyar nan face tarin daud'a da takaici ,

Abu mafi sauk'i a rayuwa da zakayi wa kanka shine kusanci da ubangijin ka , yau ga 'Akram yazo da lfyan shi yana murnan ze sadu ,da mahaifiyar shi .

Yana tunanin ze nemi gafaran ta ,tare da, duk wanda ya b'atawa ,sai dai kash ya makara don kuwa 'Allah ya fara nuna masa jarabawan shi".

Dr Samir be iya cewa Da Doc... Komai ba ya mik'e ya fita, yana rik'e gefen zuciyar shi ,Captian ,nema ya iya ,yiwa Dr godiya, ya fice yabi ,bayan Dr Samir.

Dak'er yake iya takawa don k'afar shi tayi masa wani 'irin ,nauyi sai nishi yake ,k'asa kasa.

Ko gabanshi baya iya gani ko ina ya koma, masa duhu tafiya kawai yake ba tare da yasan inda yake nufa ba.

Saida yazo dede kofar da zata sadashi da waje ya rik'e kofar yana fitar da wani ,irin ,nishi me zafi .

"Lfy kuwa Samir? Barin kira Dr Aiman karka fad'i "

"Kar kaje ,Junaid "


Dr Samir ya tsaida shi.

Zan iya tafiya

" kamani pls jiri nakeji ".

Cikin rashin fahimta Junaid yace .

"Meyasa Samir? Meyasa bakaso a sanar ma Doctor d'inka halin da kake ciki , kafi kowa sanin damuwar ka".

"Zan gaya maka Captain idan har zakayi mun alfarma guda ,d'aya"


Da sauri Captian yace


"Wata irin Alfarma ce?"

Sai da ,Dr Samir ya k'ara jingina da jikin ,kofar don ji yake, kamar ze fad'i shi kad'ai yasan abunda yakeji cikin cikin shi don komai ,ma ciwo take masa.

"Mu tafi gida pls shine Alfarman da nake so daga ,gareka".

Kallon shi kawai Captian yake, yana tunanin anya kuwa samir be fara zaucewa ba.

Kamar Dr Samir yasan tunanin da yake cikin zuciyar shi,

Langofar da kanshi yayi a shagwab'e yace

"Ka yarda ,dani pls".

Tau sayin shi Captian yaji ,ya taimaka ya kama shi suka fice.



Saida ya ,saisai ta kanshi tukun ya shiga ,gida ,don kar Ummi ta gane Halin da yake ciki.

Captian kuma gida ya koma tare dayi masa 'Alk'awarin ze dawo da yamma.

Ummi na ganin shi taji wani fad'uwar gaba don ko ba'a fad'a mata ba tasan d'an ,nata yana cikin damu kuma yau kam ta yanke hukunci sai ,ta ,tambayeshi abunda ke damun shi.

Duk da ramar da yayi be hana kenshi fitowa ba, gani tayi ,ya k'ara mata kyau da fari kamar bashi ba.

"Ummi ,ina wuni ya gida".

Sai a lokacin ta dawo hankalin ta don har ya k'araso cikin falon bata kula ba.

"Lfy qlau Doc... Ya naganka ha ,kamar...."

"Babu komai Ummi ".

Yayi saurin katseta.

"Ka tabbata Samir? Bana so ina ganin ka cikin damuwa fa jibi yanda ka rame

Ka fad'a min damuwar ka, wlh inde ina da halin da zan iya , yaye maka shi zanyi , idan kuma na 'addu'a ne sai na tayaka".

Da Murmushi d'auke a fuskar shi yace.

"Babu komai Ummi kedai ki tayamu da 'addu kawai Allah yasa mucika dakyau da imani yakuma yafe mana zunuban mu.

Shiru tayi kamar me karantar wani abu daga ,gare shi ,me yake nufi da hakan?.

Itafa bata so taji yana irin wainnan zantukan ,Amman kuma gsky ,ya fad'a.

Kamar yasan me take fad'a cikin zuciyar ta yayi saurin cewa.

"Karki d'auka wani abune fa Ummi kawai ,naji kwad'ayin ,nace miki hakanne don shine babban Addu'ar da mukafine a gareku ,ku iyayen mu".

Murmishin k'arfin hali tayi ,tace.

"Hakane Dana 'Allah ya maka 'Albarka ya k'ara maka lfy .

Ya jikin ,naka ina fatan dai kana shan magun gunan ka, akan lokaci ?".

Ina sha Ummi jiki ,kuma da sauk'i mun gode Allah".


Shi kad'ai yasan abunda yakeji cikin jikin shi, Ummi tana karya masa zuciya 'aduk lokutan da zata kalle shi sai yaji abubu dadi

Don kuwa barin ta 'abune me wuya 'a gareshi amman ta zame ,masa dole duk da yasan mutuwa ba'a hunun shi take ba ,baya tunanin kuma ,kwanaki da watani da shekarun da yayi a baya.

Ba mutuwan yake tsoro ba yanda rayuwan Ummi ze kasance bayan ta rasashi ,shi yafi d'aga masa hankali .

Yana son ya sanar da ita wani abu amman yana tsoron abunda ze haifar bashi da kowa 'a duniya sai Ummi bashi da wanda ze iya sadaukar da rayuwan shi sai Ummi.

Amman baze iya fad'a mata komai ba, bakuma ze tab'a bari ta rasa life d'inta saboda shiba.

Wasu zafafan hawaye ne suka zubo mishi ba tare da ya bari ta gani ba yayi saurin goge su.

Sai daya d'an sai saita kanshi sannan yace.

"Ummi naje asibitin kafun ,na shogo gida shine Ummi" babu wani b'ata lokaci ya sanar wa da Ummi duk yanda sukayi da Doc...a hospilat.

"Ya ilahi ya Allah ,mun san komai dayake samun bawa 'a duniya jarabawa ce kuma rubutacce ne a gurin ka.

Dama kariga da ka rubuta 'acikin Allon k'adaddara 'Allah kai maji rok'on bayin kane Allah ka sausauta mana wannan irin jarabobi da kake ta jaraftar mu dashi".


Cikin tausayawa tace .

Barin shiya sai ka ,kaini gurin shi na zauna karmu barshi ,shi kad'ai.


*Dija_waziri*πŸ’‰
[18/12 7:33 pm] Dija Waziri: πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰
DR HAJARπŸ‘©β€πŸ”¬
πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰

Chapter 40

Yana sauke Hajiya asibiti ya wuce gidan su Junaid ,don yana son ya keb'e shi kad'ai bazai ,iya zuwa 'asibiti a yanzun ba.

Koda yaje be samu Junaid a gida ba d'akin shi ya shiga ya kwanta , kanshi na mishi wani ,irin ,nauyi

Yinwa yakeji amman bazai ,iya cikin komai ba duk da halin da yake ciki be hana bacci d'aukar shiba.


Γ—Γ—Γ—Γ—Γ—Γ—

"Samir".

Captian ya biga pillon da Dr Samir ke kwance a kai

"Haba ,Junaid meyasa zaka tasheni kasan daya nayi baccin ya d'auke ni?".

"Sorry ban san bacci kakeyi ba".

Ya nemi guri ya zauna gefen shi.

Tsaki Dr Samir yaja ya mik'e yad'an jingina da gadon dake ,kwance kai.

Ruwa Captian ya d'auko ya dawo ya zauna yana sha.

"Samir miye abunda kace zaka fad'a min".

Ajiyar zuciya Dr Samir ya saki lokaci goda Captian ya tayar masa da ciwan dake damun shi wanda ya samu yad'an kwanta.

"Junaid Allah ya sani ,ina son Ummi na.

Bani da kowa 'arayuwa ta sai ,ita itace komai na Junaid,

Ina tsoron Halin da zata shiga idan ta rasani Junaid, ba mutuwa nake tsoro ba tunda tana kan kowa jiran ta yakeyi.

Abunda nake tsoro shine abunda ze faru bayan ta rasani. "

Kallon shine Captian yakeyi kawai cikin rashin fahimta yace.

"Ban gane ba Samir wai me kake fad'a haka ne ?"

Darin takaici Dr Samir ya saki.

"Dama bazaka gane ba Junaid har sai na ganar dakai .

Dakai ,kad'ai na yarda Junaid shiyasa zan fad'a maka damuwa ta".

Jiki a sanyaye Dr Samir ya cire ,rigan jikin shi ya zama dagashi sai bes d'aga rigan cikin yayi ,ya nunawa Captian cikin shi.

Da murmushi yace

"Me kagani Junaid?".

Zaro ido junaid yayi ,lokaci guda yaji ,yawun bakin shi duk sun k'afe dak'er ya iya tattaro wani yawu me d'aci ya had'iya.

Cikin fargaba da tashin hankali yace.

"Miye a jikin ,ka haka Samir?".

Saida ,Dr Samir ya d'anyi jim kad'an sannan yace .

"Ciwo ne Junaid bayan tafiya na Turkey da kwana hud'u na kwanta rashin lfy da naje asibiti .

Doc...ya dubani sosai ya kuma gano cutar Cancer d'in da nake mafa dashi ,wanda ni ban sanar dashi ba.

Yace ina da wata d'aya 'anan gaba idan har ba'a cire kidney d'ina ba tow zan iya rasa raina.

Yace duk kidney d'ina sun lalace saka makon ciwan dayake jikina ,

Bani da kowa da ze iya magan cemin wannan damuwar sai Ummi na , kuma itama kedney d'aya gareta .

Har idan Ummi tasan meke faruwa dani zata iya sadaukar da rayuwan ta sabo dani, kuma ni bazan so hakan ba Junaid shiyasa kawai kaga na bar komai ku...."

Cikin b'acin rai Captian ya tsaida shi ,idanuwanshi sunyi jazur alamun b'acin rai .

"Me matsayin abotar mu Samir ,da zaka dinga tunanin baka da kowa mud'in kenan baka d'aukemu yan uwan kaba kenan?

Samir ina jinka ,kamar d'an uwana kuma jinini!!

Babu abinda bazan iyayi makaba 'a rayuwa matsawar wanda nasan zan iyayi ne.

Idan har ka d'aukeni d'an uwanka ba 'abokin kaba, ka yarda zan baka ,kidney d'ina guda ,d'aya matsawar zesa ka rayu".

Daro ido Dr Samir yayi ,yanajin wani dad'i cikin zuciyar shi ,da irin karamcin da ,Junaid yayi mishi.

Yasan babu ,abinda Captian bazai yi masa shiba 'arayu don yaga ya samu lfy , Amman idan har ya bari aka cire kodar Junaid tow ya tabbata, yaso kanshi da yawa.

Hawan da tun d'azu suka ciko idon shi ya barsu ,suka fara fita.

Murmushi yayi wanda iya kanshi fatar baki ne yace.

"Junaid nagode ,da karamci nagode bani da 'abunda zance maka dayafi haka,

Amman kayi hak'uri bazan iya bari a cire k'odar kaba idan ,nayi haka naso kaina da yawa.

Mutuwa bata salama koda anyi mun bashe ze hana ,na mutuba idan har kwanana ya k'are ,

Junaid yanda ,nakeji yanzu ya wuce kwatance ina ganin mutuwa ita kad'ai ce hutu a gareni.

Shine k'arshen k'addara ta , Allah ya nuna min jarabobi da, dama 'a rayuwa ta, Hakan yana ,nuna shine k'adaddara ta,

Rubutu ne wanda 'akayi kamar akan dutse wanda baze tab'a gogewa ba sai dai , ya wuce Amman tarihin sa baze wuce ba har abada"

A wannan lokacin Captian kasa jurewa yayi ,wasu Zafafan hawaye ,yaji sun zubo mishi.

Dafa kafad'ar Dr Samir yayi zuciyar shi na k'una yace.

"Idan har baka yarda ba Samir nasan matsayina 'a gurin ka kuma........"

Saurin katsashi Samir yayi , ya mik'e ya tako har inda Junaid yake ya tsuguna gaban shi.

"Na yarda 'Abokina ,nagode da wannan karamcin dakayi mun Allah ya saka maka da mafificin Alkairi.

Samun aboki 'irinka sai an tona Junaid ba kowa ze iya, yimun abunda kamun ba?"


Murmushi Captian yayi ,yace.

"Is ok babu god'iya tsakanina daikai Ana tare ,tashi mu koma 'asibiti".

Babu musu ,Samir ya tashi suka tafi



***********


Tun jiya takejin bugun zuciya ta rasa dalilin hakan , kawai tana tunanin akwai abubuwan da zasu faru da ita cikin kwanakin .

Tun safe data, tashi bataji komai ba, babu yanda Khadee batayi da ita, taci abinci ba 'Amman tace ta k'oshi bata jin cin komai a ranar.

Haka ,Khadee ta hak'ura ta rabu da ita.

K'arfe tak'as da kusan rabi Hajar ta shirya cikin wani daguwan riga na material ruwan madara, da zanen fulawa ruwan ganye ,

Ba tayi kwaliya ba mai kawai ta shafa , tad'an goga hoda ,ta yane kanta da wani mayafi ruwan ganye ,

Duk ,da rashin kwaliyan dake fuskar ta be hana kenta fitowa ba.

"Khadee kiyi sauri mutafi pls kinga ina so na biya hospital ,akwai abunda zan d'auka 'a office d'ina ".

Kadee ,dake jikin mirro tana kwaliya tace.

"Sorry na gama barin saka, kaya 'Amarsu ".

Hajar batace da ita komai ba sai murmushi data saki ,har yanzu tanajin bugun zuciyar ta me ,makon ya ragu k'aruwa ma yayi..


*DIJA_WAZIRI*
[18/12 7:33 pm] Dija Waziri: πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰
DR HAJARπŸ‘©β€πŸ”¬
πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰

Chapter 41


Suna cikin mota Hajar tace wa Khadee.

"Nifa yau tunda natashi ,nakejin ,jikina babu dad'i Khadee.

Sai bugun zuciya da fad'uwar gaba nakeji ,sai ,ina tunanin akwai abunda ke shirin faruwa dani".

Khadee dake tuk'i tace.

"Kiyi ta innalilahi insha 'Allah babu ,abinda ze faru dake".

Yanda Khadee ta fad'a hakan tayi tayi har suka k'arasa hospital.

Sai dai suna shiga taji bugun zuciyar nata ,na k'aruwa da fad'uwar gaba, Addu'a take tayi har ta k'arasa ciki.

"Hajjo barin shiga office dina zan ,zo na sameki".

Cewar Khadee

Dak'er Hajar ta iya ce mata .

"Don Allah kar ki jima Khadee kinga bamu da isashen lokaci"

D'aga mata gira kawai Khadee tayi ,ta wuce ,

Itama Office d'inta ,ta nufa da mamaki taga Captian ,na tahowa hanun shi d'auke da ledan magani da ruwa ,shi ko kula da ita beyi ba har zai wuce tayi saurin tsaida shi da fad'in.

"Captian lfy na ganka 'a nan waye ba lfy baka fad'a mun ba?".

Sai lokacin ya juyo ,ya kalleta da fara'a.

Gani tayi ,ya k'ara kyau da haske hancin sa ya k'ara tsayi .

"Hajjo sanun ki ,kinyi kyau ".

Ya fad'a yana murmushi.

"Tnx me kake anan ?".

Ta tambaya fuskar ta babu fara'a.

"Wlh k'anin Dr Samir ne yayi hatsari har dashi cin wainda sukayi hatsrin jirgin samman"

Magan ganun Captian ,ne suka fara yawo a kwanyar kanta dama Dr samir yana da k'ani ?.

Tambayar da takeyi wa kanta kenan a fili kuma tace.

"Allah sarki ae daka ,kira kagaya mun, damur Doc...ae tamuce duka, kodon mutuncin sa.

Bari idan ,nafito daga office zan shigo na duba shi ".

"Ok babu damuwa muna room 15".

Yana gama fad'ar haka ya wuce ,

Itama office d'in ta shiga tare da tunanuka bar katai.

Abunda ta zo daniyar d'auka shi kawai ta d'auka ta fice daga office din don sauri takeyi,

Dakin da su Dr Samir ke ciki ta nufa dede kofar dakin taji fad'uwar da gabanta yake, ya sake tsanta ,taji wani 'irin ciwan kai da bata, tab'aji ba , subhanallah kawai take ta furtawa har ta shiga d'akin.

A zaune ta samu ,Ummi kan darduma tana jan cerbi ga dukkan alamu idar ,da sallah tayi gefen ta Dr Samir ne ya kifar da kanshi ,cen gefe guda kuma Captian ,ne zaune , bata kalli gadon da 'akram ke ,kwance akaiba ba.

"Asalamu alaikum "

Shine abunda ta furta, gabaki d'aya hankalinsu ya koma, kan ta su duka saku 'amsa da

"wa'alaikum salam".

K'ara sawa tayi ,inda Ummi ke zaune ta durk'usa.

"Ina wuni Ummi yame jiki?".

Hajar ta, tambaya

Ummi da fara'a tace.

"Lfy qlau jiki da sauk'i ya shirye shiryen biki ?".

Akunyace ta amsa da.lfy qlau ,sai alokacin ta kali Dr Samir suka gaisa ta, tambayeshi me jiki sannan ta maida ,duban ta kan Akram.

Wani fargaba da tashin hankali taji na ruskar ta, lokaci guda taji komai ya tsaya ,mata wani ,irin dokawa taji zuciyar ta, tayi.

Ko a mafarki bazata ,tab'a mancewa da wannan fuskar ba, ta kasa gasgata shid'inne kuwa gaban ta yau rana tsaka.

K'afafun ta, taji sun fara rawa lokaci guda taji zuciyar ta na wani ,irin dokawa.

Kallon Dr Samir tayi ,tana son yi mishi magana, yayin da take nuna 'Akram da ,d'an yatsan ta sai dai kalma ko d'aya ta kasa fita daga bakin ta.

Lokaci guda taji wani jiri na d'ibar ta, lu ta ,tafi zata fad'i Junaid yayi saurin rik'ota yana .

"Lfy Hajjo" .

Sai lokacin Dr Samir yayi saurin tashi daga inda yake zaune ,han kalin shi a mugun tashe ,

Ummi ,ma

Please Login or Register in order to submit comment