Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kawai zaki je ki tadawa baiwar Allah wuta" hhhhh barni da shegiya gara namata warning tun kafun abu yayi nisa, don wlh Akan Junaidu zan iya b'atawa da koma waye ke har iyayena zan iya rabuwa dasu akan shi".

"Towfa babban magana kenan ,Tali wlh kinyi nisa shekara da shekaru kina bin wannan bawan Allah ya nuna bayayi dake amman kin ,nace ,ni wlh dariya ma kike bani kinfa girme, masa nesa ba kusa ba 'amman waike dole saishi kike so ,"hmmm Susu kenan wato dariya ma nake baki ,kow ? Tow ,wlh !wlh!! Wlh!!! Kinji na rantse ko saina 'auri Junaidu ko yak'i ,koya so ina ruwana dana girmeshi aiba haramun bane don ,na 'aure shi donko ya halasta , koma yak'i amincewa ,wlh shida farin ciki har abada saina ruguza masa rayuwan sa nasa ya dena jin dad'in komai na daga rayuwan shi, ke wlh idan be aureni ba sai yayi nadamar zuwa duniya sai ya fara neman ,mutuwa ido rufe kuma wlh ,harna kusa dashi bazan bari suji dad'i ba ,zan ,nuna masa wacece Talatu diyar Alk'ali matar soja 'ada " dariya Susu tasa tace "Allah ya baki nasara tow

*BAYAN SATI D'AYA*

tafe yake cikin asibitin sai kalle -kalle yakeyi ganin ya iso ciki yasa ya fiddo da wayar shi daga 'aljihon sa ya kirawo Khadee bugu d'aya ta d'auka, ya sanar da ita ya iso ,sannan ya kashe wayar ya cigaba da kallon zubi da tsarin asibitin komai da tsayi akayishi gwanin ban shi'awa ,be kula da sunan da ,dake rubuje ,jikin asibitin ba yadai san shekaru masu yawa sunan asibitin get well rabon shi da zuwa tun sanda 'aka ,kwantar da kakar sa ,shekaru masu yawa lokacin yana matakin ,k'arshe a karatun sa na secondary school yanzu yaga komai ya cenza masa 'asibitin ya balain burge shi donko za'a iya sashi a sahun farko gurin kyau da tsari, "Father tunanin me kakeyi minti na uku anan fa " Uhm wlh kawai 'ina tuna yanda hospital d'innan yake dane shekaru baya da suka wuce maybe ma lokacin kina jaririya "azolaye ,yayi maganar "Amman ,niko Dr Galadncin yana raye kuwa? Idan ban manta sunan saba?" Suna tafiya suna hiran ,murmushi Khadee tayi tace "Halan baka tab'a kallon kofar gidan su Hajjo ba ko? ina ,nufin baka tab'a d'aga kankaba " gsky ban kula ba meya faru ?" Murmushi tayi tace"tow shine mahaifin ta kuma yana raye be mutuba, sai da 'alamun tsufa sun bayyana masa sosai, don yanzu baya zuwa ma Asibitin sai jifa jifa " ikon Allah ,Allah sarki rayuwa Dr Galadanci yasan darajan mutane yayi mana halacin da bako wani likita ne ze iya mana irin shiba yasan aikin shi Allah ya k'ara masa nisan kwana "Ameen "Khadee ta fad'a da haka suka ,k'arasa cikin tangamemen office d'in wanda komai da tsari akayi shi nuni tayi masa daya zauna kan wata kujera me laushin gaske sannan tayi gurin tangamemen tagan dake cikin office d'in taja labulen dake wangale ta rufe ta kunna iyacondishan ta bud'e farji d'in dake girke gaban teburin royal ta fiddo ruwan gora da memon kwali ta 'ajje masa ,sannan ta d'auko ,kofin tangaran ta 'ajje masa ,sannan ta koma ,mazaunin ta, ta zauna ,"captin ina wuni ya 'aiki? ".
"Lfy qlau Khadee ya naki aikin?".

"Masha 'Allah aiki gashinan muna ta fama".

"Tow Allah ya taimaka, niko meyasa yanzu Hajjo bata d'aga wayata sai yayi ta ringin amman bazata d'aga ba?, kuma sau 'uku ina zuwa gidan su ,sai acemin batanan hope lfy dai kow?".

"Tow bazan ce maka ba lfy ba captin amman akwai matsala, batun zuwa gidan su da kake baka samun ta zai ,iya yuwuwa lokacin da take gurin aiki ,kake zuwa, zai kuma iya, yiwuwa sab'ani kuke samu, d'aukan wayan ka, kuma da batayi wata yar uwar kace tayo mata lettar.............tow kaji abunda ya faru " OMG "shine abunda ya fad'a yayin daya rik'e ,kansa tashi yayi ,yabar offce d'in ba tare da yace da Khadee uffan ba ya shige cikin motarsa ya figa zuciyar shi na suya ,ita ko ,Khadee kallo ta bishi dashi...

Be tsaye ko inaba sai Rijiyar zaki dede kofar gidan su Tali yayi parking ya fito ya shiga ,gidan ya koyi sa'a babu kowa daga ita sai k'anwar ta Susu , ko salama beyiba yasa kai cikin falon idonshi jawuri, Susu ya tadda falon tana kallo, ganinshi yasata yak'e hakora"A'a yau Captin ,ne agidan ,namu lale maraba " Tale dake cikin d'aki jin anboton sunansa da Susu tayi ,yasa ta saurin fitow tana yak'e hak'ora kamar gonar auduga "A'a lale maraba sannu da zuwa masoyina ga wuri ka zauna".

Fuskar shi a d'aure yace "ba zama nazoyi ba "ya fara nunata da yatsa "Talatu kifita harkata ki fita daga rayuwata, wlh!! Zumuncin mu zai' iya ,yankewa muddin baki fita daga ,gonata ba waikekam wace irin matace me kike nima dani ? Nace bana sonki banayi dake ,koko ana so dole ne? Wancen karon ,kin ruguzamin auren da nayi niya shekarun baya kuma ,kinyi nasara tow ,kuwa ,wannan karon baki 'isa ba ,ki fita harkana tun muna cikin lalami da 'arziki ,ki zauna 'a matayin ki na yar uwata "yana gamawa ya juya ze tafi ,kawai ya tsinci muryan Tali "idan kuma nak'i fita sai yaya ?wlh !idan ina raye baka isa ka 'auri ko wacce mataba face ni ,idan kuma ka musa tomuzuba nidakai muga waye,xeyi nasara ,ni dakalin majinace kowa ya hauni ya sule kuma zama dani ya zama dole , kai ,idan ma banda jaraba irin taka me zakayi da yar iska wacce ta gama zubar da mutuncin ta 'a titi ".

"Haka nake son ta duk mugayen kalaman da zaki jefeta dashi tunda ni ,nasan ba haka takeba 'aeshikenan ,ke Allah ne kad'ai yasan me kikeyi kina neman shekara 45 amman kin kasa zaman aure, kin gommace kiyi ta yawo a titi ,sannan yanzu ki rasa wanda zakice ,kina so saini sabodani lusari ne kuma saina 'aure ki Allah ya sawak'e"yaja tsak'i ya fice zuciyar shi na suya...

"Lalle wannan mutumin zesan ya tab'a Talatu ,wai harni zeciwa fuska tow ,wlh be isa ba yayi bye bye da farin ciki har abada kuma itama yarinyar ya jaza ma "fuuuuu ta shige d'aki tad'au mayafin ta, ta fice..

Shikuwa yana barin layin gidan su Talatu layin Dr Samir ya kira ya tambayeshi ko yana gida gashinan zuwa ,ya koyi sa'a yana gari hakan yasa shi k'ara gudu ,don ya isa da wuri


Karku manta comments d'inku sheke k'ara min k'arfin gwaiwa


Tow fa 'ana wata ga wataπŸ˜ƒ Talatu kuma ta faso

Shin wacece ita wannan Talatun ?

Ashedai wahalan Hajar be k'are ba?

Tow Dr Samir ya dawo sabon cause


Kucigaba da kasan cewa dani



*Dija_Waziri*πŸ’‰
[18/12 7:32 pm] Dija Waziri: πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰
*DOCTOR HAJAR*πŸ‘©πŸ»β€πŸ”¬
πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰



Chapter 21

Wasu indiyawa ne su uku ,sukayi parking dede k'ofar gidan su Akram ,samarine guda biyu sai wani datijo yana sanye da bak'ar riga na yadi ,da farin k'ale daya daura 'a kunkumin sa kamar d'aurin zani ya had'e gashin kansa guri guda ya tufke, fuskarshi duk yazane da kala, ga duk, kan alamu daga ,gurin bautayake ,cikin harshen indiyanci yace "muje ciki" shiya fara shiga sannan suma, suka mara masa baya ,door bell ya dannan , Jin k'aran ,ne yasa Maman Akram saurin mik'ewa daga kan sofar da take kwance zuwa tayi bakin wendo ta duba ko suwaye ganin mutanin ya sata zare ido ,da ,dafe k'irji fargaba da tashin hankali suka riski zuciyar ta damuwar da take danewa 'alokacin ya bayana hawayen da take danewa tun shekaran jiya karya zubo amman saida ya zubo a wannan lokacin, jin ank'ara tab'a kofar ne yasa ta goge kwalar idon ta sannan taje ta bud'e kofar tana murmushin dabekai zuci ba ...

Cikin harshen indiyanci tace "sanunku da zuwa ina wunin ku"..

Wannan datijon daya had'e rai ne yace"lfy qlau munzo karb'an kudin haya ne yaukam babu alfarma wata shida kenan baku biya ba kullum saidai kubamu ,hakuri to yau wlh idan baku biyani kud'ina ba jami'ar tsorone zasu rabamu daku ,kuma bazaki ,kuma zamamin agida ba ".

"Ya subuhanallah don Allah kayi hakuri wlh yarona yau sati d'aya kenan ina, neman shi na rasa shi, daya dawo zan had'a maka ,kud'inka na baka" cikin zafin ,nama mutumin yace "bazai yuwu ba "ya umarci wa inannan mutanin dasu kamata sutafi da ita chargi office, yanda yace suyin kuwa haka sukayi tana ihu suka tafi da ita ,shikuma ya shiga ,gidan ya dinga musu watsida kayan su waje daga bisani kuma yasa kwad'o ya datse gidan ya tafi da mukulin...

Acen chargi office yaje ya samesu, akayi magan ganu masu yawa ,police suka umarceta data bashi kud'insa ita kuma tace bata da kud'i don akram dukya kwashe duk wani abu data malaka ya gudu yau sati d'aya kenan rabon ta dashi ita yanzu bata da komai sai kud'in jirgin da tabiya zata koma najeriya , tow jami'an tsaro dai sun jefa Mahaifiyar akram a gidan kaso harsai randa 'akayi belin ta ,tukun


Nigeria

Hajar yau kwanan su biyar da tafiya 'abuja Mami kwananta biyu ta dawo kano tabar Hajar acen , zaune suke ita da Basmad Jawahir ,na kan ciyar Hajar tana game suna tatauna yanda bikin Basmad ze kasan ce don Ansa rana ,nan da wata d'aya za'ayi ,

"Hajjo maganar anko idan kin ,koma kano zaki fitar d'in?" Kai gsky ban maki ,alk'awari ba ,Basmad , ina da 'aiki ,kuma ba lalle abunda nina zab'a shi friend d'inki suke so ba, gara kibar su kawai su zab'i wanda ransu ke so, mu idan yaso Family sai muyi namu ,muma ,mekyau ", tow ranar dennar fa?" Ae ranar dennar dama nake magana ,ranar kamu ,kuma atamfa za'a fitar me tsada me kyau wainda bazasu iyaba saisu ,sai me arhan kud'i koya kika gani?" Hakan ma is ok"...

"Hajjo wai ,ina Captin ,ne ,ni tunda kikazo banji kunyi waya dashi ba" tsaki Hajar taja tace"mun b'ata" tow meya had'a ku?" Nan Hajar ta kwashe labari ta bata, "kinji dalili ,ni bana son tashin hankali kuma itama ,matar bansan wacece itaba ,bansan wace iri bace, gara na janye jikina tunkan a kuma ,maimaita ,tarihi tunkan inkuma shiga bala'i kwatan kwacin wanda na shiga 'a baya "..

"Gsky gara da kika janye ,don ko baki san wace iri bace Allah yayi maki zab'i mafi Alkairi ,Amman ,nikam mezai hana ki auri Dr Samir wlh haka ,kurum nake shi'awar naga kin aure shi don ko, kun dace kuma ki kali yanda yake kula dake ,kullum sai ya kiraki", Murmushi Hajar ta saki "tow ar Doc....ba saurayi na bane Basmad Friend d'inane kuma ba soyayyah mukeyi ba mutunci kawai mukeyi dashi "..

"Tow ae daga 'Abokantaka yake juyawa ya koma love, koma dai miye nidai nafi sonki da likita, kuma insha 'Allah saikun fara soyayyah ko bajima ko ba dad'i zanyi ta 'Addu'a " murmushi Hajar ta saki har cikin zuciyar ta dad'i take ji bata san ,sanda ta furta Ameen ba sannan ta wayence da "kinga muyi abundake gaban mu kinga dai gobe zan koma ,kano"..

Sun juma suna tattaunawa ,sannan daga bisani Basmad tayiwa hajar list d'in abunda take buk'atar tasiya mata daga kano wanda zatayi amfani dashi.....


*BY Dija_Waziri*πŸ’‰
[18/12 7:32 pm] Dija Waziri: πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰
*DOCTOR HAJAR*πŸ‘©πŸ»β€πŸ”¬
πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰



Chapter 20


Jiya nayi mestake gurin numbers 18 zansa nasa19 inafatan zaku gane


*Wanan shafin na sadaukar dashi gareku Hauwa (jidda) , it's me nd Hauwa sani umar Allah ya Barmu tare ,idan kun karanta kunban lbr don shafin nakune lol*😺😺😺

Talatu na fita bata ,tsaya ko inaba sai gidan Hajiya Jumai k'awar ta, ko salama babu ta fad'a mata cikin gida tana huci .

"Lafiyan ki ,kuwa Taliy zaki shigomin gida ko salama ?". Hmm ba lfy ba Maman Hanif ". Tow meya faru kuma waya tab'amin ke?" wancen yaron wai harni zeciwa fuska don yaga ina sonshi tow ,wlh idan yasan wata besan wata ba zan shayar dashi madaran mamaki zan ,nuna masa cewa haryanzu beyikwari ba shi yaro ne " wani yaro kuma ?Kardai Junaidu ?" Shifa ".

Dariya Haj ,Jumai ta saki "kai Taliy kina da matsala ,najima ina gaya maki, kifita harkan gayenan bafa 'auren ki zeyi ba 'amman kince no, karfa ki manta keba sa'ar sa bace ke idan banda ma shirme irin ,naki mezakiya da yaro kamar Jumaid wlh da 'ace kin zauna gidan mijin ki, da yanzu kina da d'a kodai bekai shiba ze kusa kaishi"..

"Kinga Maman Hanif ba dogon zance nazo kimin ba ,kin gane kow taimako nazo nema " tow Taliy ,yanzu me kike so ayi ?" Yawwa yanzu kikayi zance gurin bokan nan ,nakeson ki rakani wanda shekarun baya mukaje akan batun wannan buduruwan tashi " tow fa 'Allah yasa be mutuba don yanzu rabon mu da zuwa gurin she ana neman 7 year harda ,d'oriya ,yaushe kike son muje?" Gobe nakeso muje " kai banda gobe Baban su Hanif yana gari ki bari jumu'a ze koma bakin aikin shi asabar sai muje ,tunda guri banan kusaba "tow Allah ya kaimu ,"cewar Talatu sannan suka shentake da wata hiran ...


Wacece Talatu?

Talatu d'aya ga Alhaji muntari wanda 'akafi sani da Judge Muntari ,Mahaifin Talatu cheef judge ne dashi da Mahaifin Captin Junaid yaya da k'ani ne Alhaji Muntari shine babba sannan Mahaifin Junaid sai kuma k'anansu mata guda uku susu biyar ne agurin mahifin su kafun ya rasu ,Talatu itace jika ta biyar a family d'in su Junaid ,Amman yanzun itace jika ta farko saboda sauran hud'un duk Allah ya karb'i abinshi , shekarun Talatu 45 auren ta d'aya tun tana yar shekara 14 mahaifinta ya d'aura mata 'aure da wani datijon arziki Talatu badon tana soba tayi auren, don ita 'a rayuwan ta ,tana k'aunar taga tayi zurfi a karatu, tow kuma dokar mahaifin ta shine dasun gama aji shida yake masu aure , tunda Talatu ,tayi aure take musgunawa mijin ,nata take jifarshi da mugayen kalamu da habaice habaice, gata dama gwanace gurin masifa da bala'i don kaf ,family sunsan ta, bata barin ta kwana ,Saida suka shafe shekara biyar suna 'abu daya kullum babu dad'i mijin baya jin dad'in zama da ita ,haka har Allah yasa Talatu ,ta samu ciki ,tana tabatar wa da cewa ciki gareta ,ta inda take shiga ba tanan take fita ba , mijin ta kuwa yasha ruwan ashar ,har saida ranshi ya b'aci ,shi dama darajan mahaifinta da kuma ganin mutuncin sa yasa shi yake ragwantawa ,Talatun bega dalilin da zesa datijo dashi zata dinga zagewa haka ba don ahaife ze haifeta don dai kawai Allah be,bashi haihuwa bane duk matan da yake aura guduwa sukeyi saboda baya haihuwa, Talatu kuwa tayi alk'awarin saita zubar da cikin ,babu irin lalab'i da rok'on da beyi mata ba 'amman tak'i fir shiko dayaji haushi yace idan har ta zubar masa da ciki tow, karta dawo masa gida ta koma gidan ubanta, itako tayi gud'a tace gaba ta kaita ,yanda ta fad'a ,d'in kuwa hakan tayi tazubar da cikin sannan kuma ta koma gida ta shera k'aryan ta kuma yan gidan su ,sukahau suka zauna , bayan auren ta ya mutu da shekara 4 wata ,rana da Junaid ya dawo hutu daga makaranta, tunda ta k'elara idonta, ta ganshi tace idan bashiba sai rijiya ,lokacin ta bashi shekara tara, shiko yak'i yarda shine take ta bibiyar shi ,ita kuwa tundaga lokacin bata sake aure ba mahaifinta babu yanda beyi da itaba 'amman tak'i yace zeyi mata nadole tace koyayi wlh saita kashe ta fito, su ,harsun fara tunanin ko aljani gareta , har Allah ya d'aukin ran mahaifin Talatu batayi aure ba ,babu yanda mamansu batayi da itaba 'amman tace ita 'arabu da ita ,ita Junaid take jira, hhhhhh lol tow kunji kad'an daga cikin wacece Talatu


*****
Zaune take kan prayer mat tana karanta Al-Ma'thuuraat, Mami ce ta shigo d'akin ta zauna gefen gado har Hajar ta salame "Mami lfy ?" Lfy qlau Hajjo ina son ki shirya gobe zamu tafi Abuja maganar bikin Basmad za'a kawo kayan ta kuma, kinga dole naje "lah ,har bikin yayi kusa haka 'amman Basmad bata sanar dani ba wlh Allah ya kaimu dama nayi Missing Beby na" Murmushi kawai Mami tayi ,ta mik'e ta fice tare da sanar da ita idan tagama taje falon k'asa Dady na ,neman ta .


"Abokina lfy kuwa naganka haka?" Samir akwai matsala narasa me ,matarnan take nufi dani ,nace bana son ta amman duk lokacin dataji labarin inada budurwa sai tasan yanda tayi ta rabani da ita" wace matace haka"Samir ya tambaya "wace kuwa idan banda Talatu" dariya Samir yasa ,yace kacemin "masoyiyar yanzu metayi maka" tsaki Captin yaje yace "kaga bana son iskanci ya ina mata magana zaka wani fara min dariya duniya ce ba masoyiya ba " duk yanda Samir yaso da ,danne dariya saida ya fito"sorry wlh ban san yazo ba dariyan, me tayi maka?"

Captin duk ya gama kulewa dama tuncan a kulen yake, mik'ewa yayi ze fice Dr yayi saurin tsaida shi "sorry mana kai matsalata dakai saurin fushi" tow ya bazan yi fushi ba nazo ma da matsala ta zaka fara wani mun dariya " tow ya hakuri nadena gayamin ,meke faruwa" nan Captin ya kwashe duk yanda sukayi da Talatu ya gaya masa da kuma 'abunda Khadee ta fad'a masa "ni yanzu taimakon da zakamin shine muje dakai ,ka tayani bata hak'uri" tow babu damuwa yaushe zamu ?" Ni gobe ma don Allah "tow Allah ya kaimu " tsale yayi ,ya rungume abokin ,nashi sannan yace"kaga nama ,manta ban tambayeka jikin ,kaba ya jiki ,-jiki? da sauk'i ni ciwan zuciyata ma nake ganin yanzu babu don gsky ya kwana biyu be tashi ba ,tow d'ayan ciwanne dai kawai sai hamdalah amman kwana biyu kam sai a hankali " tow shima 'Allah ya k'ara sauk'i na zuciyar ma kardon ka samu sauk'i ka watsar da shan magani don ,nasan halinka ,gara kaci gaba" kai wlh bazan iya ba magun gunan sunmin yawa tunda wannan sauk'i ya samu wlh nikam na watsar " tow ko ,kamar a kunnen Ummi" sanin cewa babu wanda Samir ke tsoro sama da Ummi yasa shi cewa hakan, hak'uri samir yayi ta bashi daga bisani sukad'anyi hira sannan Samir yayi wanka suka fice...

Tun dare Hajar ta gama shirin ta ,tsaf don ko idan taje sati d'aya zatayi , bayan ta gama had'a kayan tane tana kwance tana kallon kind of heart na Philippines wayan ta ya fara ,ruri ganin ,number d'in wandake ,kiran yasata ,sakin Murmushi ,d'auka tayi ba tare da tayi magana ba daga b'angaren me kiran, ne ya fara magana..

"Asalamu alaikum".

"Wa'alaikum Salam barka da ,dare likita".

Murmushi ya saki tare da 'ajiyar zuciya don duk lokacin dayaji muryan ta saiya tsinci kansa cikin farin ciki mara misal tuwa "barka dai Doc...lefin me nayi kwana biyu akamin yaji?".

Ajiyar zuciya ta saki ta had'iyi wani yawu me zafi, dama tasan dole saiya tmby murmushin da baikai zuciya ba tayi "wlh babu komai wayar ce ta samu matsala".

Murmushi ya sak'i yasan akwai alamar ,rashin gaskiya cikin zancen ta "wayyo ina fatan yanzu angyarata ?".

"Eh angyara yanzu kam".

"Tow masha 'Allah idan babu damuwa next week ina son ,nazo gurin ki akwai abunda nake son tmbyn ki".

"Tow Allah ya kaimu" dak'er ta iya bashi amsa don tasan tambayar da zeyi mata yana da nasaba da 'abunda ya faru kwanaki.

"Yawwa tow dama na bugo na gaishe kine kuma na shaida maki nadowa "..

"Nagode sanu da, dawowa ".

Nan sukayi salama ya kashe wayar shi...

Indian



*BY DIJA WAZIRI*πŸ’‰
[18/12 7:32 pm] Dija Waziri: πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰
*DOCTOR HAJAR*πŸ‘©πŸ»β€πŸ”¬
πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰



Chapter 22

Aduk, k'arshen wata Hajar tana ziyartan manyan asibitocin kano kamar su Murtala da 'Aminu kano , da asibitin k'ashi don bada gudumawar ta ga marasa lfy da kuma yi musu 'addu'a ,kwanan ta yau ,uku da ,dawowa ita da Jawahir saka makon sun koma school yasa ta dawo da ita..

Tafe take cikin tangamemen asibitin Aminu kano , tayi shigan ja da bak'i materiyal tasa ja da ratsin baki ajiki d'inkin A shep gwon saita yane kanta da bak'in mayafi tayi kyau sosai idon ta d'auke da farin gilashi wanda ya k'ara fito da 'asalin kenta dede emergency tayi parking motar, ta, tafito, ta shiga tayiwa marasa lfy addu'oin samun sauk'i sosai takuma basu goma ta 'arziki daga nan ta fita tayi part d'in marasa lfy suma ta dubasu ,tare da musu fatan samun sauk'i ,daga,gurinta wuce gainic word anane ma tafi jimawa saboda yanda taga mata kejin ,jiki wata ma haihuwa zatayi 'amman saboda basu da kud'in da zasu biya, yasa likitocin barin su gurin batare da ankula suba ,gsky ta, tau sayawa mutane da ,dama cikin guri a k'ala saida ta, taimaki wurin mutane 6 yan kud'in data shiga dashi duk anan ya k'are takuma bawa marasa lfy shawar warin yanda zasu kula da kansu dadai sauran abubuwa, a wannan rana Dr Hajar saida ta zageye ko wani b'angare na marasa lfy ta dinga musu addu'a da fatan sauk'i ,bangaren masu fama da laruwan kwakwalwa ne kawai ya rage mata bataje ba ,dama tunda take ziyartar marsa lafiyan asibitin ,nanne kawai Allah be tab'a bata ikon zuwa ba 'amman yau kam tasha 'Alwashin sai taje ,tafe take tana waye dade kofar da ze sadata da cikin gurin ,ne kawai taji tayi karo da mutun ,kayan dake hanunsa duk suka zube, "subhanallah "shine abunda tace ba tare da ta kali mutumin ba taduk'a ta fara kwashe takardun da suka zube ,shiko tsayawa kawai yayi ,yana binta da kallo yana murmushi ,saida ta gama kwashewa sanan ta d'ago ta kaleshi tana"don Allah kayi hakuri wlh...." ganin wanda ke tsaye a gurin,ne yasa ta kasa k'arasa furta 'abunda take fad'a...

"Is ok ae nasan ba da gangan kika bigeni ba ,tunda kika fara tsenewa na tsaya kawai 'ina kalon ki"...

"Doc...wlh tunda ,nadoso kaine a zuciya ta ina ta zuci zucin ,nagama wayanan, nakira ka naji ko ,kana kusa na k'araso mu gaisa ,sai ko gashi Allah ya had'ani dakai "....

"Eyyah nima yau nake da niyar zuwa ,wurin ki ,kinga kowa yanzu na huta me kikazoyi nan ?"..

Murmushi ta saki sannan ta ce"ziyara " kai Amman kin kyauta wlh ,har kina da lokacin ziyara 'Allah ya biya ki"..

"Ameen yanzu ina kayi ?" Office zan koma " ok tow bari ni, nak'arasa ciki ,idan yaso inagama na k'araso ,office d'in ,naka "...

"Ok tow sai kinzo"..

Anan suka rabu shiya wuce office ita kuma ta k'arasa ciki, ba wani jimawa tayi sosai ba ta fito...


*****

Captin ,ne zaune cikin office d'inshi yana da danna system d'inshi ,wayar sa ya jawo yayi dailing number d'in Samir bugu d'aya ,ya d'aga ..

"Hello freind ya kake ya 'aiki?"..

"Lfy qlau ya naka?".

"Gashi muna fama, dama nakira na tuna maka cewa yau zamuje gidan su Hajjo "...

"Tow Allah kaimu Amman gsky sai zuwa dare ,don yau inada 'aiki sosai ,sai 5 zanbar asibiti"...

"Tow Allah ya kaimu idan ma kagaji saimu bari gobe muje tunda Satuday ne babu aiki"...

"Yawwa hakan ma zefi kam ,zan kiraka lettar ina 'kan aiki yanzu bye"...

Dede ya kashe wayar dede lokacin harjar ta shigo cikin office d'in , tsayawa tayi tana kallon cikin office d'in komai tsaf-staf gonin ban shi'awa kamai a tsare gashi office d'in babba ne sosai don harda gado da Tv ,tsayawa tayi ,ta fara kallon komai na cikin office d'in , wani elargiment ,ta gani hoton mace da namiji ne sai kuma d'an jariri dake rik'e hanun mace, pic d'in babu kala 'amman duk wanda yaga matar jiki yasan ba k'aramar kyakyawar mace bace ,ko ina cikin office d'in hoton tane dama ,mijin sai nawata datijuwar mata da wani tatijo shima 'anyi masa gurin sa daban a 'ajiye....

"Harkin gama ne bisimillah ga wuri ki zauna"yayi mata nunu da wani kujera, sai a lokacin ta ,tuna 'a ina take wuri ta nema ta zauna ,shi kuma ya kawo mata ruwa da cake da lemo, Amman ko d'aya bata ,tab'a ba don kuwa tadena wannan gangancin,...

"Bismillah kisha lemo don ,nasan zirga-zirgan da kikayi ma kurin ta ishe ki" A'a wlh nagode kafun nazo ,nan saida na tsaya 'a wani shago nasai ruwa nasha"...

"Tow nawa nedai ba'a so ae shikenan"...

"A'a wlh ba haka bane" tun daga haka babu wanda ya sake ce

Please Login or Register in order to submit comment