Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

mbc2, bayan su mum sun gamane mai girkinsu taje ta gyara gun tas, su mum suna zaune a palo suhail ya kashe TV sannan ya koma k'asa ya zauna tare da cewa mum nasan abinda yake ranki, amma ki kwantar da hankalinki nisam ban aikatawa yarinyarnan komaiba wlh, ina fata kinsha magungunanki karkisa komai a ranki mum d'ina😊, ba mum kad'aiba harda hafsat seda sukaji sanyi a ransu tare da sauke ajiyar zuciya, mum tace Alhamdulillah Suhail naji dad'in haka Allah ya maka albarka Allah ya kara kareka da aikata abinda ALLAH ya hana ina alfahari da kai sosai d'ana😄 dad'i yaji ya e ameeen mum kema ALLAH ya baki lfy suka sake cewa ameeen hafsat natajin dad'i a ranta kome dalili oho.
Sallama sukaji, suka amsa tare da juyowa, mik'ewa suhail yayi tare da cewa ABOKINA sauk'an yaushe? Yace sauk'an yanzu kanwata jeki zubomin abinci dan yunwa nakeji, da sauri hafsata ta tashi ta wuce kichine, ya k'araso har gun mum ya zauna a k'asa tare da cewa mum ina wuni, mum tayi murmushi tace lfy KAMAL ya hanya ya kuma ka baro mummy, kamal yace lfy lau wlh tace in gaisheku sosai ya jikin naki mum, mum tace toh Alhamdulillah jiki da sauki muna amsawa sannunka da isowa, yawwa mum sannan ya kalli Suhail datun d'azu yana tsaye yana bin kamal da kallo, kamal yace yadai abokina kayi hakuri karkayi fushi ban sanar dakai bane saboda inyi muku zuwan bazata😉, daining ya nufa na zauna tare dacin abinci ko kallon suhail bai k'ara yiba seda ya k'oshi dam sannan yace mum bari naje nad'an watsa ruwa😊, mum tayi dariya tare da cewa toh tana kallon suhail, kamal yace abokina muje ka had'amin ruwan mana kuma albishirinka na samo maka matar aure dan naga ka kusa ka tsufa ba mata😉 aguje suhail ya bishi kamal ya shige d'aki da sauri mum da hafsat se dariya sukeyi😀. Bayan kamal ya fito daga wankane yana goge jikinsa tare da cewa abokina next week zaka tafi fa, suhail yace haba dai gaskya bazanjeba harse mum ta sami lfy sosai, kamal yace tobaganiba ai tunda ina nan shikenan zuwanka yana da muhimmanci gaskya, ajiyar zuciya suhail ya sauke yace toh shikenan ALLAH ya kaimu😒. Kamal yace abokina yana ganka haka, akwai wani abune, suhail yace ba wani abu kawai dai wani abune ya faru yau nan suhail ya kwashe lbr tas ya gayamishi, kamal yace amma basuda imani yanzu dukkansu sukai mata fyad'en? Suhail yace eh sema ka ganta da k'yar take iya tfy wlh abun tausayi. Kamal yace Allah zai sakama kuma naga ka damu sosai, suhail yace eh nadamu abokina dan naso inga fiskanta koda wataran zamu sake had'uwa inaso in taimaka mata dan kamar basu da karfi sosai adai yadda na ganta, kuma d'ankwalinta na guna inaso in mayar mata, kamal yace tobase mu sake komawa ta gunba ko ALLAH zaisa mu ganta, suhail yace jejinefa babu gidaje tagun gaskya sedai k'ila ta ciki, kasan me kamal nidai idanun yarinyar kawai nake iya tunowa, kamal yace toya za'ayi kenan yanzu dama kasan sunantane da abin zaizo mana da sauki amma bakasan komai game da itaba, suhail yace koma menene dai "TANA RAINA" kuma bazan tab'a manta kyawawan idanuntaba sannan kuma.. kamal yace kuma me? Suhail yayi murmushi yace "TANA RAINA" abokina, ok na d'auka zakace kana sontane ai dase ince maka bazai yuba saboda ba cikakkiyar mace bace maza har 3 suka mata fyad'e kaga kuwa babu sauran wani abu a tare da ita. Suhail ya sauke zazzafar ajiyar zuciya tare da rufe idanunsa ya kwanta akan gado yac[9:58am, 12/9/2016] Sadiya Taheer: 🌺💐TANA🌹RAINA💕💞

By Mmn Shureim
(Sad-Nas)


11-12 Washe gari da safe bayan sabreen ta gama sharan gida tas ta gyara ko ina sannan suka zauna a tsakar gida suna suna shan koko da kosai😋, sabreen tace mammina ina sauraronki akan lbrn mahaifina, mammi tace to bari mu gama karyawa koh, to mammi da sauri ta kare ta tattare komai seta dawo ta zauna ta zubawa mamminta ido👀. Mammi tace haba sabreen wannan irin ido da kika samin haka, sabreen tayi murmushi tace nafiso inyita kallon fiskarki yayinda kike magana mammina sam bana gajiya da kallon kyakkyawar fiskarki, mammi tace fiskar nawa har takai naki kyau? To mammi ai kyawunki na d'auko😀, mammi ta mik'e tare da shafar kumatun sabreen tace Allah ya rayamin ke sabreen Allah ya miki albarka bari naje band'aki sena dawo kinji, Ameeen mammina toh ina jiranki, har mammi ta dauki buta zata shige bayi, se sabreen tace mamminah, juyowa mammi tayi ta kalleta seta taso aguje ta rungume mamminta sosai kawai se taji hawaye nabin kumatunta, mammi ta ajiye buta tace sabreen hawayen me haka kuma? Sabreen tace wlh mammina haka kawai naji inaso in rungumeki kuma in zubar da kwalla😥, mammi ta share kwallan idanunta ita tace to shikenan sabreen jeki jirani yanzu zan fito, seda suka rungume junansu kafin ta koma ta zauna. Hayaniya sabreen taji a waje ana cewa maciji maciji, ai da sauri ta fito waje dan ganin macijin, mutane ta gani dewa suna bin macijin a guje ana cewa wannan macijin babbane gaskya zai cutar da mutane idan ba'a kasheba, itama seta fara binsu can setaga macicin ya haura ta katangar band'akinsu tun kafin ya gama haurawa aketa kai mai jifa da duwatsu har an samesa daga wutsiyarsa amma seya haura band'akin, nan jama'a suka ce ya shiga gidansu sabreen muje mu kash...basu karasa maganaba sejin ihu sukayi daga cikin gidan, da gudu sabreen tayi cikin gida dan jin mahaifiyarta na ihu, tana shigowa taga mamminta ta fito da buta a hannu idanunta sun fara juyawa, da sauri mutane suka karaso sabreen ta fara kuka tare da rungume mamminta tana cewa lfy mammina meya samekine, mammi ta fara mata nuni da bayan wuyanta, lekawa tayi taga saran macijine a bayan wuyanta, seta hango macijin yana nema hanyan guduwa, da sauri tace gashican ku kasheshi ya ciji mahaifiyata, ai kuwa macijin kamar yaji abinda akace ya juya zai koma ta katangar, lokacin mammi tana ta cewa sabreen ki kula da kanki ki rek'e ibada da gaskya, mammi kiyi shuru zamu kaiki gun malam dare yanzu babu abinda zai sameki se kuka takeyi tana rungume da mamminta, saukar mutum taji daga sama ammab kuma bataga komaiba, da sauri mammi ta d'ago kanta dan taji wata irin murya yana cewa kiyi hakuri mammi nazo a makare macijin wannan MACEN ta sari kansa batare dakan ya rabu da jikinsaba sannan tazo hargun dasu mammin suke, su kuwa jama sunga dai macijin akan garu bai saukaba kuma basuga wani nauni a jikinsa dan haka sukayita kai masa sanda da duwatsu da kuma sara, take macijin ya fara fidda jini a jikinsa nan sukaita murna sun kashe maciji, basusan MACEN NAN bane ta kashesa. Mammi takai dubanta ga MACEN, macen tayi murmushi tace kiyi hakuri mammi seyau Allah yayi zaki ganni nine dai wannan yarinyar da mijinki ya rasu ta dalilina, nayi miki alk'awarin kula da sabreen insha Allah bazan bari a cutar da itaba😰, murmushi mammitayi😊 tare da cewa nagode, sabreen ta kalli mammi ta kalli inda mammi take kallo ita dai jama'an da suka kashe maciji kawai take gani, sabreen tace mammi ba godiya zaki musuba ku taimaka mu kaita gun malam dare, hawaye itama macen tafarayi dan yadda taga mammi nayi dan mammin ne kad'ai take kallonta. Atake MACEN ta b'ace,sannan mammi ta juyo tana kallon sabreen tace base ankaini ko inaba sabreen kicewa kakanki ya baki labarin mahaifinki sannan kuma sabreen ki kulada kanki ina kaunarki sabre....😭😭😭
Allahu Akbar! Kulli nafsi za'ikatil maut. Shikenan mammi ta tafi, kuka soai sabreen takeyi tare da jama'an gurin, dakyar aka d'aga sabreen daga jikin mamminta aka kaita gidan su munna😰😰😰
[9:58am, 12/9/2016] Sadiya Taheer: 🌺💐TANA🌹RAINA💕💞

By Mmn Shureim
(Sad-Nas)


13-14 Suhail da kamal ne a hanyan tfyansu kauyen su Sabreen, suna tafe suna hira har suka iso daidai gurin daya had'u dasu sabreen, se uace kamal a daidai nan ne amma dai mu kara gaba kadan, ahankali,suke tfy se suka hango hanya shiga garin sukai tfy kad'an se suka hangi kakan sabreen yana komawa rike da cefene a hannunsa, gunsa suka tsaya da motan tare da dayi masa sallama, bayan sun fitone suka gaishesa cikin girmamawa sannan sukace baba dan Allah muna tambayane, yace toh ina jinku, suhail yace wata yarinya nake nema ko Allah yasa ka santa, kaka yace menene sunanta? Suhail ya kalli kamal se kamal yace wato dai baba muma basusan komai game da itaba kawai dai mun gantane tanan tana sanye da riga da zani da kuma bak'in himar sannan tasa nik'af a fiskanta, kaka yace to gaskya bayin Allah bazan ganetaba, dama ace kun gayamin sunantane ko sunan mahaifinta ko kuma kamanninta,toda zan iya ganewa, suhail yace baba yarinyar an mata fyad'e jiya jiyan nan kuma dai muna kyautata zaton atanan take, kaka yace fad'e kuma subhanalillah to gaskya bata nan bane, domin duk abinda ya faru a kauyennan baya b'uya a masallaci ake sanar da koma menene, kamal yace to ai k'ila baza a iya sanar da magana irin na fyad'e ba, kaka yace za'a sanar ina tabbatar muku da cewa babu abinda yake b'uya a kauyennan namu, wai samari me kuke nema agun yarinyarnan ne, kamal yayi saurin cewa dama daga cikin gari muke, muna neman masu aiki ne, kaka yace wani irin aiki kuma, kamal yace mata dai wanda suke aikin wanke wanke da shara da kuma girki za'a dinga biyansu a wata. Kaka yace haba da gaske, ina da jikata nasan zatayi farin cikin hakan dan ta dad'e da gama secondary tana so taci gaba da karatu amma bamu da hali, tayita neman aikin a kauyennan amma bata samuba, sedai kuma aiyukan daka lissafo sunyi yawa, Suhail yace a'a dama girkine kawai zata dingayiwa mahaifiyata dan bata da lfy, kaka yaji dad'i sosai yace indai wannan ne shikenan jikata ta iya girki amma na gargajiya ne ko kuma ince namu na karkara sam bata iya naku na birnineba. Kamal yace ba damuwa muma ai muna cin abincin gargajiyan sosai dan haka ba matsala zamusa a koya mata😊. Kaka yace to shikenan kud'an bani lokaci inyaso seku dawo daga baya koh? Suhail yace to shikenan mun gode sosai baba, kaka yace bakomai nine da godiya nasan jikata zatayi farin ciki sosai dan haka sekun sake dawowa...wasu samarine suka karaso a guje suna haki suna cewa kaka gara da muka had'u dakai, Allah yayiwa mammin SABREEN rasuwa yanzu yanzun nan shine aka aikomu donmin muzo mu kiraka, 😳Innalillahi wa inna ilaihir raji'un dukkansu suka amsa, kaka yace me kace SALE, Mammi ta rasu😰? Sale yace eh kaka macijine ya sareta a bayan wuyanta kuma harta cika😭. Kaka yace ina sabreen jikata take a wani hali take ciki? Suhail ya kamo hannun kaka yace baba shiga muje tare, ba musu suka shige gabad'ayansu suka isa har kofar gidan inda suka iske mutane a cike. Fitowa sukayi dukkansu suka wuce cikin gidan, lokacin har matan makota sunyi mata wanka an suturceta kaka ya isa yayita mata addu'a sannan aka fito da gawanta zuwa waje nan akai mata sallah aka d'auketa dan kaita gidanta na gaskya sega sabreen ta fito a guje tanata kuka tana cewa kaka dan Allah karku tafi min da mammina ina sonta wlh karku kaimin mammina rami dan Allah ku tausayamin ita kad'ai ta ragemin fa kaka😭. Kowa ya tausayawa sabreen musamman kaka da iyayen munira, munirane ta biyota da hijabi danko d'ankwali babu akanta bare takalmi, gashin kanta duk ya tattashi kamar wata mahaukaciya, bayan munna tasa mata himar d'inne se take k'okarin janyota amma ta kasa, kaka yace da suhail dan Allah yaro taimaka ka mayar min da ita gida kaji, ba musu suhail ya kamo hannunta yana kokarin maidata gida seta gantsara masa cizo tana cewa dan Allah ka sakeni zasu tafimin da mammina nefa nika sakeni😭. Kuka sosai takeyi hakama munira, Suhail ya rasa meke masa dad'i sam bayaso yaji mace na kuka, ahaka har suka k'arasa kofar gidansu munira wata mata ta riko hannunta suka k'arasa da ita cikin gidansu muniran. Shi kuwa suhail hannunsa yayi jahjazir dan cizon da sabreen tayita mishi, binsu yayi mak'abartan akai mata komai sannan suka dawo sukai musu gaisuwa se suka tafi suna masu tausaya musu sosai😔😔😔
[9:58am, 12/9/2016] Sadiya Taheer: 🌺💐TANA🌹RAINA💕💞

By Mmn Shureim
(Sad-Nas)


15-16 Bayan su suhail sun dawo gidane suka sami mum a palo, bayan sun zauna ne kamal ya dauki ruwa a frigj yasha sannan yamikawa suhail mayasha, mum tana ta binsu da kallo tace lfy kuwa kodai baku sami mai girkin bane? Kamal yace mum samu mum nan dai suka bata lbrn abinda ya faru, sosai mum itama abin ya bata tausayi, tace Allah sarki Allah ya jikanta yanzu dai za'a d'auki lokaci kafin tazo, can se idonta yakai kan hannun suhail, tace suhail me nake gani a hannunka, suhail ya shafi gurin yace cizon da yarinyan tayitamin ne lokacin dana rik'e hannunta, shi kansa kamal baisan da batun cizonba se yanzu dayaga hannun suhail yayi jah kuma ya kunbura, mikewa suhail yayi ya shiga d'aki ya watsa ruwa sannan ya fito ya goga mantileta a hannun nasa seya kwanta yana tunanin abunda ya faru, kamal ne ya shigo shima wankan yayi,yazo ya zauna kusa da suhail fiskar sabreen kawai yake gani dana munira, mamakin irin kyawu na sabreen yakeyi, yace suhail amma kaga fiskan sabreen kuwa, gashi dai kauyene amma har ana samun kyawawa haka, gaskya irin kyawun sabrin sedai a kasar larabawa da indians bade nigeria ba.
Suhail yayi murmushi yace abokina ni gaskya banganta sosai ba, saboda gabad'a kukanta ya d'aga min hankali, kamal yace dama na tuna hakan a raina wlh, yauzu me abin yi? Suhail yace se ranan da za'ayi uku semu koma muyi musu gaisuwa, tunda wani sati zanyi tfy zuwa ranar da za'ayi bakwai seka sake komawa kaji me kakan nata zaice. Haka za'ayi suhail Allah ya kaimu.
Haka sabreen ta kasance cikin kuka koda yaushe, nasiha sosai malaman kauyen nasu suke mata harta dena kukan, amma dai ba'a rasa ganin hawaye a fiskanta. Kullum zaka ganta tare da munira dan a gidansu take zaune, maganganu masu kwantar da hankali munna take mata harta d'an ci abinci kad'an, amma idanunta sun kubura dan kukan mamminta.
Yau ne za'ayi uku, suhail da kamal suka shirya cikin fararen shadda dasu akayi addu'oi sakamakon sunzo da wuri, bayan an gamane suka sake keb'ewa da kakan sabreen sukace sunaso su mata gaisuwa, kaka da kansa yaje ya kirata, himar suka saka ita da munira suka fito lokacin kaka yaje gaisawa da wasu. Kamal ne ya fara magana yace sabreen ya hakuri, kanta ta d'ago tace Alhamdulillah tana kallon kamal din, yace Allah ya jikanta, tace ameen sannan ya juya gun munira suna gaisawa se suhail yace sabreen ya hakuri, kai ta d'ago don kamar taso ta gane muryarsa, idonsu na had'uwa ta ganeshi tana masa kallon mamaki, Alhamdulillah tace dashi, yace toh Allah ya jikanta da rahama, ameen tace nagode sosai harda yar mirmushinta😊. Suhail ma kallonta yakeyi har cikin ido, se kuma ya kau da kansa yace kamal muje koh, kamal yace to sabreen ya sunan kawarki ne, sabreen tace sunanta munira, ok dukkanku kuna da suna masu dad'i mu😊, sabreen tace mungode Allah ya bada lada tana kallon suhail shida yake kokarin wucewa gun motansa yace ameen mum d'inmu tace amik'a mata gaisuwa agareku, sabreen tace mungode sosai, murmushi suhail yayi mata sannan ya kira wasu yara tare da bud'e but na motarshi yara suka fara shigowa da kayan abinci juice, taliya, indomie dasu buhun shinkafa. Sabreen ta kalli kamal tace wannan fa, kamal yace sadakace muka kawo muku, hawayene yake fitowa daga fiskarta daidai lokacin suhail ya karaso, hanki ya ciro a aljihunsa ya mika mata, hannu tasa ta karb'a tana kallonsa har cikin ido tana zancen zuci, duk lokacin da nake cikin wani hali se in ganka agun ya akayi kazo nan kuma? Suhail ne ya katseta da cewa shide mamaci babu abinda yafi bukata irin addu'a kukanki azabane agunta sabreen, dad'in zancen nashi taji atake tare hawayenta da hankinsa sannan ta mika mishi tace mungode sosai Allah ya bada lada, ameen sukace se suhail yace ki rik'e nabar miki😊, itama murmushin tayi tace se anjumanku sannan tajawo hannun munira suka wuce gida. Kamal se binsu da leke yakeyi, suhail ne ya janyo rigansa yace inaga dai ba k'alau kakeba, gaisuwafa mukazoyi ba kallonsuba malam, dai dai lokacin kaka ya k'araso yana musu godiya sannan sukaci gaba dayin magana. Sabreen kuwa mamaki takeyi ya akai suhail yazo nan🤔, maman munirace tace sabreen wannan fa suwaye suka kawo, sabreen tace sune wanda muka gaisa dasu yanzu nima ban sansuba sedai mu tambayi kaka idan ya shigo k'ila shiya sansu😉.
Bayan kaka yayi sallama da kowane saiya shigo gidan su muniran, nan gaya kayan abinci kam dewa. Baban munirane yake tambayan kaka suwaye suka kawo wannan sadakan haka? Nan kaka ya kwashe lbrn had'uwansu dasu suhail tas ya gaya musu. Munira tayi saurin juyowa ta kalli sabreen, sabreen ta kyafta mata ido😉 sannan ta fara murmushi a zuciyarta tace to meyasa yake nemana, kodai d'ankwalina zai bani? Alhamdulillah tunda baiga fiskanaba, kuma koda naje yin aiki a gidansu bazan tab'a sanar dashiba tunda nidai nasan ba'amin fyad'eba kuma ina farin ciki zan koma makaranta dan haka na amince zanyi musu aikin☺
[9:58am, 12/9/2016] Sadiya Taheer: 🌺💐TANA🌹RAINA💕💞

By Mmn Shureim
(Sad-Nas)


17-18 Sabreen da munirane suna zaune a d'akinsu bayan sunyi sallan isha suna cin abinci, munira ta kalli sabreen tace dama shine suhail d'in? Sabreen tace eh shine bai ganenibane saboda nik'af ne a fiskata ranan. Munira tace to ai yakamata ki sanar dashi tunda kinga nemanki ne yasa suka sake dawowa nan d'in, sabreen tace a'a munna wannan maganar sirri ce tsakanin nida ke pls, munna tace to ai shikenan kika san koya kyasa ne yasa ya biyoki, gashi da alama masu haline kinga shikenan mun fito fari😜, dariya sukayi dukkansu sannan sukaci gaba da hiransu.
B'angaren suhail kuwa, tunda suka dawo kowa da tunanin da yakeyi, hafsat ne tazo ta samesu a palo tace yah suhail ina kukajene inata nemanku, suhail yayi murmushi yace munje gaisuwa ne hafsat akwai wani abu ne, a'a kawai dai dan ban ganku bane. Kamal yace nidai zan tafi gida seda safenku, suhail ya tashi ya rakasa hargun mota sukai sallama sannan ya dawo gun mum sukaita hira har zuwa 9pm kafin suka wuce donyi bacci. Shidai suhail yana ta kallon idanun sabreen a ransa dan yayi mishi kama dana wannan yarinyar, sedai na sabreen sun kumbura kuma sunyi jah, to shine dai yake kokonto akan kila kamace kawai, kuma kaka ya tabbatar musu da cewa babu yarinyar da akayiwa fyad'e a kauyen, ya shiga rud'ani sosai da haka yayi bacci...


Yau wata guda kenan da rasuwan mammin sabreen. Shikuwa Suhail yana can pakistan kusan 3week kenan. Kamal ne a kofar gidansu munira yana jiran fitowar kaka da sabreen, can segasu sun fito suna rungume da juna suna kukan rabuwa, maman munirane taketa basu hakuri tana cewa munna kiyi hakuri aiba rabuwa kukayiba 'yan watannine kawai zatayi seta dawo kinji, da kyar dai suka rabu kamal ya bud'ewa kaka gaba sannan sabreen ta shiga baya suka tafi tanata yiwa munira bye tana kwalla. Tunda suka fara tfy sabreen taketa kuka har suka iso wani gida mai kyau, hon kamal yayi aka bud'e suka shiga, bayan motan ya tsayane kamal yaje ya bud'ewa kaka dan sabreen kam harta fito tana rik'e da yar jakanta, kamal yace bissimillah kaka muje, kofa ya bude sika shiga k'aton palo mai kyan gani, anan suka zauna kamal yace sannunku da zuwa kaka😊, kaka yace yawwa sannu kamal, ruwa mai sanyi ya kawo musu tare da juice ya zuba musu, ahankali suka karb'a suka sha tare dayi mishi godiya. Kamal yace kaka nan gidan mahaifinane amma Allah yayi musu rasuwa shida mahaifin suhail a k'asar saudiya, iyayenmu aminan junane sosai suna business a wani kamfani dake pakistan, lokaci lokaci suna zuwa duba kasuwancin nasu. bayan rasuwansune mahaifiyata tayi aure a pakistan d'in, inda ni kuma nake zaune a gidan mahaifina, nida suhail mukaci gaba dayin business kamar dai yadda iyayenmu sukeyi, idan naje wannan karon, wani karon kuma suhail ne yake zuwa, mahaifiyar suhail tak'i yin aure sam tana zaune damu anan da kuma 'yar yayan baban suhail wato hafsat, itama marainiyace dan bata da uwa bare uba. Mahaifiyar suhail ta rik'e hafsat kamar 'yarta na cikinta, inda mu kuma muka zame mata yayyu. Matar da take musu girki d'anta ya samu aikin yine shine yace mamansa zata dena girki, shiyasa muke neman wanda zata dinga musu girki ana biyanta duk wata. Kaka yayi ajiyar zuciya yace Allah ya jikansu da rahama suka amsa da ameen dukkansu. Kamal yace na kawoku nanne saboda kace sabreen bata iya girkin zamaniba sena gargajiya, shine nakeso ku zauna anan koda na tsawon wata biyu ne na samo wanda zata dinga koyawa sabreen girke girken zamani idan ta iya sena kaiku gidansu suhail koya kagani kaka? Kaka yace bakomai kamal na fahimceka kuma na amince danna yaba da halaiyarku nasan bazaka cutar damuba zamu zaunan anan d'in harse ta gama koyon. Kamal yayi murmushi yace to alhamdulillah kaka ina tabbatar maka da cewa bazan tab'a cutar dakuba shiyasama nace mu taho tare dakai koda ruwa seka dinga ba flawer kaima ana biyanka. Godiya sosai kaka yayi sannan kamal yace muje in nuna muku masauk'inku, tare suka mik'e sabreen tana binsu a abaya, d'akin mummynsa yaba sabreen, sannan yaba kaka d'akin babansa, manyan d'akunane da komai a ciki, murna sosai sukayi tare da k'arayin godiya.
Kamal ne kwance a d'akinsa ya kira suhail a waya yace abokina se nanda 2month su kaka sasu zo, suhail yace toba damuwa Allah ya nuna mana, kamal yace amin sannan sukaci gaba dansu. Bayan sun gama wayanne kamal yace bazan iya sanar dakai suna gunaba abokina, harse sabreen ta k'ware sosai da girkin zamani anan, insha Allah gobe zanje inyi musu cefene sosai zuwa jibi RUKAYYA zatazo ta fara koya miki sabreen, da wannan shawaran kamal yayi bacci tare da jin dad'i a ransa wanda bansan dalilin saba😊😊😊
[9:59am, 12/9/2016] Sadiya Taheer: 🌺💐TANA🌹RAINA💕💞

By Mmn Shureim
(Sad-Nas)


19-20 Washe gari da safe bayan sun gabatar da sallan asuba se sabreen ta fito tayi hanyar d'akin da kakanta yake, muryan kamal taji a bayanta yana cewa sabreen gurin kaka zakiji? Tsayawa tayi cak sannan ta juyo da d'an murmushi kad'an a fiskarta tace eh zanje mu gaisa ne dama, ina kwana, kamal yace lfy lau kin tashi lfy ya bak'on guri😊, tace lfya lau, lokacin kamal ya karaso inda take yace to muje nima dama gunsa zanje, tare suke tfy har suka isa d'akin da sallamarsu, bayan kaka ya amsa sallamarne suka zauna akan carpet se sabreen tace kaka ina kwana, kaka yace lfy lau sabreen ya kika tashi, lfyata lau😊, sannan kamal ma ya gaishesa, sabreen ta juyo tana kallon kamal tace tome za'a dafa yanzu, kamal yayi murmushi yace yanzu dai kije kiyi bacci se zuwa anjuma, sabreen tace aimu da wiri kuke karyawa a kauyenmu, kamal yace tona gane kina jin yunwane? Kaka yace mudai muna karyawa da muri amma sabreen tana kaiwa har k'arfe goma kafin ta karya, kamal yace to shikenan kaka barin in samo maka abinda zakaci, ke kuma kije kiyi baccinki, zuwa anjuma zamuje kasuwa dake don muyi sayayyan abinci kinji, toh dama babu abincinne, kamal yayi murmushi yace kinsan a gidan su suhail nake cin abinci da komaima baccine kawai yake dawo dani gida,

Please Login or Register in order to submit comment