Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sanreen tace to mai gadifa, wayake basa abinci, kamal yace kud'i na bar masa duk abinda yaga dama shi yake saya, sabreen tayi murmushi tace kayi hakuri na fiye tambaya ko😉, karki damu sabreen ki d'aukeni kamar yayanki wanda muke ciki d'aya dan nikam kin zama k'anwata ta jini, dad'i sosai sabreen da kaka sukaji dan haka suka sake sake jiki da kamal sosai. Sabreen tace nagode HAMMA KAMAL daka zamemin yaya😊 sannan ta mik'e ta wuce toilet d'in kaka ta wanke tas ta fito ta goge ko ina a d'akin dan yayi kura sabo da bakowa amma sam babu wani dattin kirki, bayan ta gamane ta wuce nata d'akin ta gyara ko ina ta nufi paloma tas ta share tayi moping, d'akin kamal take nema amma bata ganiba, dan haka ta bishi kichine lokacin ya dafawa kaka indomie harda kwai, kamshi taji yana tashi ta karasa a hankali tace hamma kamal da ka iya girkine😋, juyowa yayi yana murmushi yace ina dai koyone sabreen sannu da aiki, haba bakomai ai dama na saba hamma kamal, yace to ina zuwa bari na kaiwa kaka kinji, toh tace dashi sannan ta fara gyara kichine komai blue ne tas tiles d'in ya fara sheki kichin d'in yayi bala'in burgeta, shuru ya kamal bai dawoba seta fito taci gaba da neman d'akinsa can ta hango kofan, da sauri ta shiga tare da sallama, sanyin AC ne ya daki fiskanta ahankali ta shiga se taga ko ina tas babu abinda za'a gyara, kofan toilet ta nufa shima tas ta jawo kofan ta tsaya a d'akin tana jin dad'in sanyin AC da kuma wani kamshi da yake tashi☺, hoton kamal da suhail ta hango sunyi kyau sosai sanye da suit fari, gun hoton ta k'arasa tanata kallonsu tace ayya suhail bazan tab'a mantawa da kaiba "KANA RAINA" itama kuma MACEN bazan manta da itaba domin "TANA RAINA" barin gurin tayi da niyan fitowa se taji an bud'e kofa🙄, kamal ya lura da razanar datayi, kanta ta sunkuyar tace kayi hakuri dama nazo gyara maka d'akin ne se kuma naga ashe harkgyara😔, kamal yayi murmushi yace bakomai sabreen ina gyarawa sakamakon kwanan da nakeyi aciki karki damu nagode kinji sannunki da aiki, cikin k'ank'anin lokaci kin gyara gidatas😀, murmushi tayi tace bakomai zan wuce, matsawa gefe yayi sannan ta fita da Sauri tana murmushi. Gun kaka ta koma ta zauna sunata hira cikin kwanciyan hankali abunsu, 9:00am cip kamal ya shigo da tirai a hannunsa, da Sauri sabreen taje ta karb'esa tare da cewa sannu da aiki, yawwa k'anwata kema sannu, chips ne da kwai da kuma kayan tea, ya sake komawa ya d'auko flacks da cups, da Kansas ya had'a musu tea d'in yabasu sannan yace to kaka ga abin karyawanku, kaka yace nikam ai a koshe nake wlh sedai sabreen d'in, sabreen tace yah kamal ashe dai ka iya girksosai😀, kamal yayi murmushi yace ina koyo dai, kaka yace wannan ai yafi k'arfin koyo, kamal ya mik'e yace to bisimillah k'anwata kici seki shirya muje sayayyan koh, to tace dashi sannan ya fita ya nufi daining yaje yana cin nashi abincin yana murmushi..
[9:59am, 12/9/2016] Sadiya Taheer: 🌺💐TANA🌹RAINA💕💞

By Mmn Shureim
(Sad-Nas)


21-22 Bayan sabreen ta gama karyawane taje tayi wanka tasa d'inkin doguwar riga na atamfa ta d'aura d'ankwalinta sannan tasa farin himar komai bata shafaba ta fito. Kamal ya shirya cikin blue shet da black jeans yana zaune a palo yana jiran fitowanta, can segata ta fito da murmushi a fiskanta tace hamma kamal na shirya, kalonta yayi tare dayin murmushi yace toh muje, atare suka fito lokacin kaka yanaba flower ruwa sunata hira da mai gadi,segasu sabreen sun fito tace kaka zamuje mu dawo, kaka yace toh sabreen sekun dawo. Tunda suka fara tfy babu wanda yace komai acikinsu har suka karasa super market, nanne kamal yace muje sabreen😊, a hankali ta fito suka shiga se kallo takeyi dan bata tab'a zuwa super market ba. Kayan abinci suka saya sosai, sannan kamal ya kaita gun kayan sawa yace ta d'auki duk abunda taga ya mata kartaji kunya, nan sabreen tayita d'iban atamfofi da material da kuma dogayen riguns, ta kalli kamal taga yana can nesa da ita, gunsa ta nufa tace hamma kamal zan iya d'auka ko wanne 2? Murmushi yayi yace ko 5 5 nema ki dauka kinji😊, murmushin itama tayi sannan tace nagode ta juya yana binta da kallo yana murmushi, komai 2 take d'auka wai ita da muniranta. Bayan sun gama da kayane yace ta biyosa suje gaba, sun isa wani gun maiyukan shafawa suka nufa da turaruka, NATURAL HONEY shine mai d'inda take shafawa ita da munna, dan haka shima ta d'auki 2 sannan ta d'auki turaren FASIO shima 2 dasu body spray, kamal yace kayan kwalliya fa, sabreen tace sedai in d'aukawa munna danni bana kwalliya, murmushi yayi yace koda gazal da janbaki da hoda nedai ki dauka, dariya tayi tace hamma kamal ai to na d'iba kayan kwalliyan gaba d'aya kenan, yace eh idan kina kwalliya zakifi haka kyau, ba musu ta d'iba suka d'ibi takalmi da jaka, sayayya dai sukai sosai sannan suka wuce gun tela aka bashi d'in kaya kala 24 nata dana munna. Daga nan suka wuce gida, kaka ya tayasu shiga da kayan komai aka shiryashi a store, kayan,tea kuma suna daining drinks a frij, komaidai gun zaman suna nama akai kaisa babban friza. Sabreen ta nunawa kaka irin sayayyan daya mata ita da munna tace kuma munbada d'inkin kaya, kaka yayita masa godiya dasa masa albarka hakan yayiwa kamal dad'i sannan yabaiwa kaka takalma da turare yace kayanka anjuma zankai makasu d'inki, godiya sosai sukayi sannan kamal yace shizai fita zaije ya duba mum d'in suhail da hafsat ze zuwa dare zai dawo sabreen ki dafawa muku koma menene kinji, toh seka dawo😊.
A gidansu suhail kamal ya yini yayita bacci harseda yayi sallan isha sukaita hira kamar yadda suka saba sannan ya koma gida. Lokacin 8:30pm kaka suna zaune a palo suna kallon sunna TV kamal yayi sallama tare da shigowa, bayan ya zauna ne yace kaka sannunku da gida😊, yawwa kamal sannu da dawowa yaka barosu, lfyansu lau wlh, sabreen tace sannu da zuwa hamma kamal ga abincinka akan daining, yawwa sabreen ta bari naje nad'an watsa ruwa senazo naci girkin k'anwata😀. Bayan yayi wanka ya fitone yasa jallabiya tare da fesa turare ya wuce daining, sabreen ta mik'e taje ta zuba mishi tuwon shinkafa da miyar egushi yaji manja da dry fish ga nama😋, tunda sabreen ta bud'e kulan kamshi ya daki hancinsa take nyawunsa ya tsinke, da bissimillah ya fara cin abincin yana lumshe ido☺😊, sabeen ya kirata, tace na'am tare da mik'ewa, irin wannan miya mai dad'i aibase a samo mai koya miki girkiba domin ni ban tab'a cin miya mai dad'n wannanba, dad'i sosai taji tana dariya tare da cewa nagode amma ina bukata dai akoyamin wad'anda ban iyasuba na zamani. Kamal yace badamuwa gobe zatazo ta fara nuna miki kinji, tace toh Allah ya kaimu goben yace ameen.
Washe gari da safe RUKAYYA tazo bayan sun gaggaisa ne se suka wuce kichine da sabreen suka fara had'a breakfast, duk abinda RUKAYYA takeyi idon sabreen nakai har suka gama sukayi breakfast gabad'ayansu kuma sunji dad'in girkin nata😋. Haka sukayi na rana suka sake yin na dare, kullum kuma RUKAYYA so 3 takeyin abinci wato safe rana da kuma dare, seda tayi girki harna tsawon 1 week sannan tace sabreen ta sake maimaita duk abinda ta dafa na tsawon satin. Tsab kuwa sabreen tayi kamar yadda RUKAYYA takeyi kuma yayi dad'i sosai, Aunty rukayya shine sunan da sabreen take kiranta dashi, cikin k'ank'anin lokaci suka shaku da juna sosai kuma sabreen taci gaba dasa hankali akan koyan girkin. Shikuwa kamal dad'i yakeji sosai yana zuwa dubasu mum kullum dan acanma yafi zama se dare yake dawowa.
[9:59am, 12/9/2016] Sadiya Taheer: 🌺💐TANA🌹RAINA💕💞

By Mmn Shureim
(Sad-Nas)


23-24 Lokaci nata fty har aunty Rukayya ta gama koyawa sabreen girki na tsawo 2month, sannan babu abinda zakace sabreen ta dafa makashi wanda bata iyaba, ta k'ware sosai itama yanzu sedai ta koyar da wasu, harta snacks da drinks na gida wabu wanda sabreen taba iyaba. Yaune kamal ya sallami aunty rukayya da kud'ad'e masu yawa wanda nima bansan adadinsu, sabreen suke tsaue da aunty rukayya suna bankwana, sabreen tace aunty rukayya ki bani number wayanki dukka dai bani da waya amma zanso kiban number'nki kakana yace jibi zai sayo min waya, aunty rukayya tace to badamuwa nan ta ciro card d'inta tabawa sabreen sannan tace gaskya kinada hankali da dad'in sha'ani sabreen Allah ya baki miji na gari😊, sabreen tayi murmushi tace ameen aunty rukayya bazan tab'a mancekiba nagode sosai Allah ya biyaki😀, aunty rukayya tace ameeen sannan tayiwa su kaka da kamal sallama ta tafi.
Duk hiran da aunty rukayya sukeyi da sabreen kamal yana jinsu, dan haka ya shirya zai fita se sabreen tabi bayansa tace yah kamal zaka fita ne, eh sabreen akwai wani abune, a'a dama inaso inyi maka godiyane akan girki dakasa aka koyamin nagode sosai😀, murmushi yayi yace bakomai sabreen nizan fita se dare zan dawo, ok dama inaso inje gurin munira ne tunda muka rabu bamu sake had'uwa ina kewarsu sosai☺, kamal yace to shikenan ki bari zuwa gobe semuje harda kaka koh, dad'i taji sosai tana maiyin murmushi wanda yake k'ara mata kyau tace nagode yah kamal Allah ya kaimu goben😊, ameen sabreen na tafi. Bayan kamal ya fitane ya kira aunty rukayya yake tambayarta ko sabreen ta tab'a gaya mata irin wayar da takeso, aunty rukayya tace eh toh akwai randa muke hira take cemin akwaia wayan malaminsu na secondary skul wai wayan yana da camera sosai idan ya d'aukesu hoto a ciki, tun daga ranan take son wayan a ranta samsung galacky x5, kamal yace toh shikenan nagode. Shagon waya ya tsaya ya saya mata sabuwar samsung x5 sannan ya wuce gunsu mum.
Kamar kullum se yaban isha kamal ya dawo bayan yaci abinci ne yazo palo yasamesu sunata hira, wayan daya sayawa sabreen ya mik'a mata gashi sabreen wayane na sayo miki na miki charging sannan nasa miki sim d'in MTN aciki, karb'a tayi hannun biyu tana farin ciki tare da cewa nagode yah kamal Allah ya biyaka da gidan aljannah, ameeen sabreen Allah ya bamu dukkanmu sannan kakama yayi masa godiya yace kamal kaibaka gajiyane, kud'adenka zasu kare dan Allah ya isa haka ka dena b'arnatar da kud'inka akanmu zaman da mukeyima kad'ai ya ishemu wlh ka mana gata sosai Allah ne kad'ai zai biyaka, kamal yace haba kaka bakomai wlh ni zanje in kwanta saboda da safe nakeso mu tafi dan kud'an yini acan zuwa yamma semu dawo, kaka yace to badamuwa Allah ya kaimu, wayarsace tayi kara ya d'auka tare da sawa a hands free yace hello abokina, suhail yace eyyy yane gwabro kak'i dai kayi aure koh, kamal yayi murmushi yace wannan ai bani kad'ai kake tsokanaba harda kanka, dariya suhail yayi yace toh garin yasu mum, kamal yace yanzu na dawo daga gunsu lfyansu lau ya pakistan, suhail yace lfya lau wlh mummy ce take cemin wai munk'i muyi aure semu tsufa ai mun rasa matan aure😀, kamal yayi dariya yace aiseka yi kafin nima nayi dan haka kai nake jira, suhail yace zan dawo ran friday insha Allah ya maganan su kakane dan mum tacemin ran wenesday mai girkinsu zata tafi, kamal ya kalli kaka da sabreen yace eh nima d'azu danaje ta gayamin kuma na tabbatar mata da cewa ran talata zan kawo mata mai girki, suhail yace ok to yaushe zakaje garinsu kakan? Kamal yayi murmushi yace gobe insha Allah, suhail yace to nagode abokina ka gaida su kakan inkaje, kamal yace suna jinka, suhail yace me kace? Kamal yace sorry nace zasuji😉, bayan sunyi sallama ne kaka da sabreen suke ta dariya😀, kunya kamal yaji seya mik'e tare da cewa seda safenmu😉, har yanzu dariya sukeyi sannan kaka yace to Allah ya tashemu lfy yace amenn sannan ya shige d'akinsa.
Washegari suka shirya tsab se k'auyensu, murna sosai mutanen k'aunuen sukayi da ganinsu kaka musamman ma nunna, tace sabreen me sirrin ne kin ganki kuwa yadda kika kara kyau se wani shek'i kikeyi, sabreen tayi dariya tace kema kin canjafa me sirrinne k'awas? Nan munira ta bata lbrn saurayin da tayi me suna ABUBAKAR SADDIQ shi doctor ne kuma yana da hankali sosai gashi yana kulawa da ita sosai kingama harya sayamin wayanmu galacky x5 sannan komai ya sayamin sena ajiyei miki naki kinga nan munira tayita nunawa sabreen kayan alkhairin da Abbakar yake mata harda iyayenta. Bayan ta gama ganine tace lallai k'awata kin paso gari Allah ya tabbatar da alkhairi ya kuma nuna mana bikin💃🏻munira tace amenn toya birnin bani lbr mana, sabreen ta kwashe lbrn birnin tun daga farkon zuwansu har karshe ta fad'awa munna sannan ta bata sayayyan kayan da kamal yayi musu harda k'arin jaka da takalmi nasu mama ma dabanne. Munna ta bud'e baki tana ganin abun duniya tare dayin godiya ita dasu mama sukaiwa kamal godiya sosai, munna tace kodai yana sonkine sabreen? Sabreen tace SO kuma, oho nidai bai tab'a gayaminba nima kuma bansa komai a rainaba, SUHAIL shine a raina amma kuma duk randa yah kamal ya furtamin cewa yana sona nad'au alk'awarin amince masa tare da bashi soyayyata danya cancanci hakan daga gareni kuma kowace mace zataso mutum irin yah kamal dan baida wata matsala wlh. Munna tace to Allah ya zab'a miki mafi alkhairi sabreen, ameen Amaryan abbakar mu zamu koma se wani lokaci kuma😀.
Bayan sun komane kamal yace to kaka seku shirya jibi talata zaku koma gidansu suhail ran laraba mai girkinsu zata tafi sabreen zata fara girki ran alhamis yayinda suhail zai dawo k'asar ran FRIDAY. Daga kaka har sabreen basuso hakanba, shima kamal d'in babu yadda zaiyine amma sam bayason tfyarsu, kaka yace toba komai Allah ya nuna mana, kamal yace ameen sannan ya wuce d'akinsa suma sukai nasu d'akin da tunani kowannensu yayi bacci😲😵😲
[9:59am, 12/9/2016] Sadiya Taheer: 🌺💐TANA🌹RAINA💕💞

By Mmn Shureim
(Sad-Nas)


25-26 Kamal ne dasu sabreen akan daining suna breakfast, babu wanda yake cewa komai gabad'aya jikinsu a mace yake tunba kamal ba. Bayan sun gamane sabreen ta koma d'akinta tana kwance akan gadonta suna waya da munira tana dariya, bayan sun gamane ta kira aunty rukayyama sukasha hira sosai dayake kamal yasa mata credit aciki.
Wani number ta gani yana kiranta, ta d'auka tare da cewa hello, muryan yah kamal taji yace sabreen kamal ne na kirakine in sanar dake wannan number nane kiyi saving kinji, ok toh nagode ya kamal ka fita ne? A'a yanzu dai zan fita akwai wani abune, emmm dama inaso inje shago ne akwai abinda nakeso in saya, toh menene gayamin se in sayo miki koh, shuru tayi batace komaiba, yace "sabreen" tace emmm nafiso inje da kainane yah kamal😉, murmushi yayi yace toh shikenan fito muje kisaya, toh nagode sannan ta katse wayan ta dauki himar d'inta tasa tayiwa kaka sallama sannan ta sami ya kamal agun motansa, gaba ta bud'e ta shiga sannan yaja suka isa wani d'an babban shago, sabreen tayi saurin cewa yah kamal ka zauna kawai ni zanje yanzu zan fito, toh yace mata sannan ta fita ta wuce shagon, bayan shigantane kamal ya fito yana biye da ita a baya batare data saniba ya shiga. Part kawai sabreen ta dauka guda 2 sannan tazo gun biyan kud'in, mai karaban kud'in yace ki barshi kawai, tace yah za'ayi kace in barshi ungo karb'i kud'inka, mai shagon yace wani ya riga daya biya miki, tace wani kuma waye shi? Mai shagon ya nuna mata motan kamal, kunya sosai taji tace yanzu yasan abinda na saya kenan😁, k'in fita tayi tana tsaye a cikin shagon segashi ya shigo fiskansa a d'an d'aure yace baki gama bane sabreen, shuru tayi ta wuceshi ta nufin gun motan kunya kamar ta shiga k'atsa.
Tunda suka fara tfy batace komaiba kanta na gefe, kamal yace sabreen ya kikayi shuru, tace bakomai, murmushi yayi yace aida kin gayamin in sayo miki me aciki muna sayowa hafsat ai nida suhail, kunya taji sosai tasa himar d'inta ta rufe fiskanta tana dariya batare dayajiba, shima dariyan yayi yace kidena kunyata sabreen domin ni bana kunyanki kinji koh? Batace dashi komai shima bai sake cewa komaiba har suka iso gida, bayan ya tsayane ta bud'e kofan tare da cewa nagode batare data kalleshiba, dariya yayimata wanda ya kara masa kyau yace bakomai na tafi gun mum se dare zan dawo, toh zallah ya tsare, ya ameeen sannan ta rufe motan ya tafi. 9:00pm kamal ya dawo gida, bayan yayi wanka yaci abincine seya kira sabreen a waya yace inason magana dake ina palo, doguwar rigan atamfane a jikinta da d'ankwalinsa da tayi lullub'i dashi yana hango gashin kanta harta k'araso gunsa sannan ta zauna akan kujera tace gani yah kamal, kamal ya gyara zama yace sabreen kin tab'a yin soyayya? Wani iri taji dan bata tsanmaci wannan tambayar daga garesaba, daurewa tayi tace a'a yah kamal, ya sake cewa amma dai nasan kina da masoya ko, tace eh akwai amma gaskya ban tab'a kula ko wani d'a na mijiba, kamal yace shin ko akwai wanda kikeso aranki? Ananne sabreen tayi shuru dan bata san me zata ce mishiba, sake maimaita tambayan yayi tareda cewa ina sauraronki sabreen, kanta a sunkuye tace a'a babu. Kamal ya sauke ajiyan zuciya yace ko zan iya sanin dalilin k'inyi soyayyar? Sabree tace babu wani dalili yah kamal, yace toh shikenan tashi kije😊, kallonsa takeyi har cikin ido shima haka sannan ta wuce d'aki. Murmushn jin dad'i kamal yayi tare da tashi ya shige d'akinsa da farinciki sosai aransa. Ita kuwa sabreen mamakin tambayoyin da yah kamal yayita mata takeyi har bacci ya d'auketa
[9:59am, 12/9/2016] Sadiya Taheer: 🌺💐TANA🌹RAINA💕💞

By Mmn Shureim
(Sad-Nas)


27-28 Ayaune sabreen zasu koma gidansu suhail, bayan ta gyara ko ina ta kimtsane tayiwa ya kaml girki ta ajiye a daining, da yamma yazo ya tarar dasu a palo suna zaune. Bayan yaci abincine yace to bari ind'an watsa riwa semu tafi koh, sabreen tace to sannan taje ta d'auki plate d'in ta wanke ta dawo ta zauna, daidai lokacin kamal ya fito daga d'akinsa se kamshin turare yakeyi yace toh kaka muje ko sannan ya d'auki kayan kaka ita kuwa sabreen ta d'auki nata suka tafi. Maigadi baiso rabuwansu da kakaba harma da sabreen domin mutanen kirkine suna da dad'in zama sosai. Tunda suka fara tfy babu wanda yace komai se wayan kamal ya fara ringing, ya d'auka tare da cewa hello abokina ya akayine, suhail yace ka d'aukosu kakan kuwa, eh na d'aukosu yanzu hakama muna dab da shiga gidane, suhail yace"thankyou dud" pls ka gaishemin da kaka, kamal yace kaka yana jinka, se kaka yace ina amsawa Allah ya dawo dakai lfy, suhail yace ameen kaka nagode, kamal yace to abokina zan kiraka anjuma, ok sena jika sannan ya katse wayar, dai dai lokacin kamal yayi hon aka bud'e gate suka shiga, tun daga wajen gidanma kasan gidan manyane bare kuma inka shiga ciki, bayan sun fitone kamal ya d'auki kayan kaka yana musu jagora har suka k'arasa da sallamarsu, mum ce da hafsat zaune suna kallon "THE GARDINERS DAUGHTER" wani series film ne mai dad'in gaske. Tun shigowarsu suka sawa sabreen ido suna ganin irin kyawunta ai atake kirjin hafsat ya buga da karfi, bayan sun zauna ne suka gaggaisa hafsat tace bro kamal kardai ince sune bak'in namu? Kamal yayi murmushi yace kwarai kuwa sis sune, wannan itace sabreen wannan kuma kakanta, shi zaici gaba daba flawer ruwa ita kuma zata dinga yin girki, mum tace Allah sarki sannu sabreen ya hakurin mahaifiyarki kuma, sabreen tace hakuri ya zama dole, mum tace to Allah ya jikanta ya jikan dukkan 'yan'uwa musulmai, gabad'aya suka amsa da ameeen. Se mummy tace toh hafsat tashi ki nunawa sabreen d'akinta ko, hafsat tayi murmushi tace taso muje, mikewa sabreen tayi tare da d'aukan akwatinta tabi bayan hafsat, shi kuwa kaka masaikin bak'i dake tsakar gidan ta gefe aka kaisa, d'akin harda AC da komai dakomai dai gwanin sha'awa. Bayan hafsat takaita d'akinne ta bud'e wall drop sannan ta karb'i akwatin sabrren ta ajiye mata a ciki ta juyo tace nan shine d'akinki, sannan ga toilet naki nan, idan akwai wani abu da kike buk'ata toki sanar dani kinji😊, sabreen taji dad'i sosai tace nagode hafsat😊. Bayan hafsat ta fitane sabreen ta k'arewa d'akin kallo tas d'an daidai ne bayi da girma sosai amma an zuba kayan duniya, kwanciya tayi tana ta tunanin yah kamal, tace oh yah kamal yau shi kad'ai a gidan bazaiji dad'iba hakama mai gadi. Bayan isha hafsat tazo ta kira sabreen wai kizo kici abinci, a baya take biye da hafsat har suka k'arasa daining, kamal na zaunne kusa da mum suna cin abinci, hafsat ta zubawa sabreen ta ajiye tare da cewa bisimillah zauna muci, sabreen tace zanje inci a d'aki, mum tace meyasa zakije d'aki bayan gamunan anan kodai kunyan d'an nawa kikeyine kamal, kamal yace kunyana kuma mum meyasa zataji kunyata kawai dai k'ila kunyanki tajeji, mum tace toh shikenan hafsat mik'a mata ta tafi d'akin tunda hakan tafiso, sabreen ta karb'a tare da cewa nagode emm kaka fa? Kamal yace kaka yana d'akinsa yanzu na kai mishi nashi abincin jekici abincin seki dawo muyi hira kinji, toh tace sannan ta wuce d'akinta taje ta zauna tana cin abincin, abincin yayi dad'i sosai dan haka taci sosai sedai bata cinyeba. Wani murya taji kamar daga sama an SABREEN, d'ago da kanta tayi tana kallon bakin kofan shigowa😳 wannan MACEN tagani a tsaye tana kallonta tana mata murmushi, itadai sabreen sam bataji an bud'e kofaba kawai ganin mutum tayi a tsaye, ahankali MACEN take takowa inda sabreen take, 😳😳🙆🏻ihu mai karfi sabreen ta sake tare da wurgi da plate d'in abincin hannunta tasss kakejin fad'uwan shi a k'asan tiles take ya tarwatse. Ganin yadda sabreen ta tsoratane yasa MACEN tayi saurin b'acewa segasu mum da kamal sun shigo da saurinsu, kamal dake waya da suhail yace abokina bani 2minit zan kiraka, da gudu sabreen taje ta rungume mum tanata kuka tare da waige waigen bayanta🙄😳🤔
[9:59am, 12/9/2016] Sadiya Taheer: 🌺💐TANA🌹RAINA💕💞

By Mmn Shureim
(Sad-Nas)


29-30 Mum ta d'ago da sabreen tace lfy sabreen, menene, sabreen ya rasa me zatace se tace musu mammina na gani anan mammina tana nan d'akin naganta, kamal ya matso kusa da mum yace ki kwantar da hankalinki sabreen mamminki ta rasu ai ba yadda za'ayi ki ganta anan wanda ya rasu baya dawowa kinji "may be dai kin razana ne kawai" har yanzu dai sabreen waigawa takeyi tanata k'arewa d'akin kallo. Mum tace shikenan hafsat kwashe plate da abincin can, sabreen muje daining kici abinci.
Da sauri tabi mum suka isa daining ta zauna mum ta zuba mata abincin, kad'an sabreen taci tace ya isheta, ruwa mum ta mik'a mata yasha sannan tace nagode mum, hafsat ce ta k'araso tace mum ko zamu kwana da ita a d'akina idan ta dena tsoron seta koma d'akinta, mum tace toh hakanma yafi sabreen ku kwana tare kinji, kai sabreen ta d'ago batare datace komaiba hankalinta yana gun wannan MACEN. Wayan kamal ne ya sake yin kara ya d'auka hello abokina, suhail yace meke faruwa ne a gidan? Kamal ya gayawa suhail komai, sannan suhail yace ina sabreen d'in bata wayan, sabreen da tayi nisa cikin tunani kamal yana ta mata magana tare da mik'a mata wayan amma sam bata jinsa, hafsat dake zaune a gefentane ta tab'a kafad'arta tace sabreen tunanin me kikeyi haka akanata miki magana bakyaji, se a lokacin ta dawo hayyacinta a zabure ta kalli

Please Login or Register in order to submit comment