Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

"ur wlcum" sannan ta fita ta tura mata kofan motan yana ta kallonta harata shiga ciki. Farin cikine sosai a zuciyar kamal har ana iya gani a waje😇, fitowa yayi ya shiga ciki tare da wucewa d'akin suhail ko sallama babu ya daka tsalle se kan suhail ya fad'a yana murmushi tare da cewa abokina nayi nasara😄, murmushi suhail yayi tare da cewa matsoraci kawai to Alhamdulillah "congrats"😃. Kamal yace "thanks friend" saura kai, suhail yace gaskya har yau babu wacce nake"SO" wannan yarinyarce kawai a raina wlh kamal, kamal yace haba abokina har yaushe zakayita ajiyeta a ranka ne, kuma yarinyar da MAZA UKU sukayiwa fyad'e me zakayi da ita? Suhail yace wlh nima ban saniba, kawai dai Allah yasamin KAUNAR yarinyar a zuciyata ne fatana shine Allah yasa in sake had'uwa da ita😒. Kamal yace kana nufin ka kamu da SONTA kenan zaka iya aurenta a hakan? Suhail ya mik'e yaje walldrop nashi ya bud'e ya d'auko d'ankwalinta yana shinshinawa a hancinsa yace tabbas kuwa abokina domin kuwa "TANA RAINA" har abada.
Ita kuwa sabreen tunda ta shiga d'akinta kuka kawai takeyi tana cewa shikenan SUHAIL na rasaka kenan yanzu tunda har yah kamal ya baiyanamin soyayyarsa kuma na amince masa😥, naso inji dalilin dayasa ka sake komawa k'auyenmu nemana amma yanzu duk hakan baida amfani, inaso kasan cewa har abada "KANA RAINA" kai kad'ai ne a "ARAINA SUHAIL" hawayenta ta share sannan ta bud'e abinda yah kamal ya bata, zobe ne "💍" mai kyan gaske na gold, murmushi tayi sannan ta sanyashi a hannunta tana tsunbatar zoben tace na amince da soyayyarka yah kamal kuma daga yau zan fara "SONKA" dan ka cancanci hakan, kai kuma yah suhail har abada "KAINE A RAINA"😰.
Bayan sunje sunyi sallan isha ne suka dawo suka wuce daining Inda mum da hafsat suke zaune, bayan hafsat ta zuba musu ne suka faraci se santi sukeyi dukkansu har suka gamaci, sannan suka tab'a hira kamal yayi musu sallama sannan ya tafi. Bayan tfyar kamal ne su suhail suketa hira a Palo hafsat se dad'i takeji aranta tana farin ciki yayinda kaunar suhail yake k'aruwranta💘💘💘 Hmmm.


Sad-Nas
[10:00am, 12/9/2016] Sadiya Taheer: 🌺💐TANA🌹RAINA💕💞

By Mmn Shureim
(Sad-Nas)


41-42 Kamal yana komawa gida ya watsa ruwa a jikinsa sannan yayi shirin bacci, wayarsa ya d'auka ya kira mummynsa ya gaya mata komai akan sabreen. Farin ciki sosai tayi mishi tare da addu'oi tace kaga se'a had'a aurenku dana suhail, kamal yace insha Allah mummy sannan sukayi sallama seya kira sabreen.
Ringing d'aya ta d'auka hello, murmushi yayi yace hello sabreen kardai har kinyi bacci, a'a idona biyu ka tafine? Eh natafi kodai kinaso in dawone, a'a kawai dai na tambayane😊, yace bakinki fitowa muyi sallama ba, bahaka bane yah kamal kawai dai... se kuma tayi shuru, yace kawai dai me, tace bakomai ka isa gida lfy, lfya lau mummyna tace ingaisheki sosai, murmushi tayi tace nagode ka gaisheta, zataji me kikeyi yanzu? Bakomai ina kwamcene, har zakiyi bacci kenan, eh tace dashi, yace ok to shikenan bari in barki ki huta kinji, to nagode seda safe, ehen "I luv you so much sabreen" kunya taji sosai bata ce komaiba, yace sabreen, tace na'am a hankali, ya sake cewa "i luv u" itama tace "i luv u too" cikin wata irin murya wanda yaji dad'insa, murmushi yayi yace "ok good night" tace ok sannan tayi saurin katse wayar tare da sauke ajiyar zuciya tana murmushi. Mikewa tayi ta fito palo da niyan d'iban abinci dama bata ciba, anan taga su mum sunata hira inda yah suhail yake cewa hafsat yakamata ki dinga zuwa kichine kina ganin yadda sabreen take girki dan kinsan bazata dauwama agidannanba dole wataran zatayi aure, mum tace ai nima yanzu na samu sauki dan haka zan dingayi. Sabreen tace dasu sannunku hajiya, mum tace yawwa sabreen se yanzu zakici abincin? 😊eh hajiya, sannan ta wuce inda ya suhail ya mike yayi gun daining d'in dan d'auko wayansa. Bayan ta gama d'iban abincinne ta juya zata koma se kafanta ya zame a tiles din saura kadan ta fad'i suhail ya tallafota da hannunsa biyu inda ta rike plate d'in da kyau suna kallon idon junansu🙄, sabreen taga kamar suhail yaso ya gane idanunta, da sauri ta mike tate da janye jikinta ta sunkuyar da kai tace nagode sannan ta wuce d'aki yanata binta da kallo🤔. Sabreen tana shigewa d'aki ta sauke wani ajiyar zuciya tare dayin murmushi tana jin dad'i a ranata😇 ta d'ayan b'angaren kuma kallon da suhail yake mata alokacin daya tallafota kamar kallon sani yake mata, tace to yanzu idan yah suhail ya gane idanuna fa, gaskya nayi kuskure bazan sake yarda mu had'a idoba. Shi kuwa suhail bayan ya d'auki wayansa ne seya fita waje zuciyarsa cike da waswasi akan sabreen, dan gaskya idanunta sunyi mishi kama dana wannan yarinyar🤔, kaka ya hango a tsakar gida suna hira da maigadi, ya karasa gunsu yace kaka nazo gurinkane. Kaka ya mik'e tare da cewa to muje daga can koh, gefe suka koma tagun ajiye motoci suka zauna a fararen kujeran roba, suhail yace kaka inaso in maka tambaya akan sabreen ne, kaka yace ina jinka. Suhail yace wato kaka gaskya bazan b'oye maka aduk lokacin dana kalli sabreen se inga kamar itace wannan yarinyar da neke nema mai nik'af d'innan dan gaskya bazan tab'a mancewa da idanuntaba, kakaji yaji k'irjinsa ya buga dan SALMA ta gaya masa komai kuma ta tabbatar mishi da cewa suhail shine wannan saurayin, kaka ya dawo daga duniyar tunani yace gaskya d'annan nidai jikata bata taba sa nik'af ba kuma ba'a mata fyad'eba sannan kasan babu yadda za'ayi ace an mata fyad'e kuma tab'oye mana kai kanka kasan bazai tab'a b'oyuwaba tunda kace MAZA ne harsu UKU kuma manya. Shi kansa suhail yabinda yake basa mamaki kenan yacewa kaka kwarai kuwa hakane to k'ila kamannine kawai idanunsun yayi, kaka yace eh zaiyu amma kai meyasa ka damu hakane d'annan? Suhail yace kaka bazan b'oye makaba wlh tun a wannan lokacin yarinyar "TANA RAINA" Allah ya d'auramin SONTA kaka fatana shine in sake had'uwa da ita dan in gaya mata sak'on zuciyata. Kaka yace kana nufin zaka aureta a hakan? Kwarai kuwa kaka don haka zuciyata take gayamin, kaka yaji dad'in hakan a ransa yace lallai sabreen tayi sa'an samun suhail a rayuwa gashi zai rik'eta tsakaninsa da Allah kuma jikarsa zata huta dan haka gobe zai sanar da sabreen komai sannan kuma zaice ta gayawa suhail d'in cewa itace wannan yarinyar kuma ba'a mata fyad'eba. Suhail ne ya katseshi da cewa shikenan kaka nizan shiga ciki seda safe, tare suka mik'e sannan kaka yace toh Allah ya tashemu lfy, suhail yace ameen sannan yayiwa maigadi sallama seya shiga cikin gida. Koda ya shiga su mum sun shiga bacci, sabreen ne ta fito da plate d'in abinci kanta ko d'ankwali babu dan tasan babu kowa a palo ta nufi kichine bata lura da suhail ya shigo palon ba, shi kuwa suhail gashin kanta kawai yakebi da kallo mai tsayi sosai dan batasa ribom ba yana baje a bayanta. Kichine d'in ya bita lokacin tana wanke hanunta akan sink yaje dab da bayanta ya tsaya, bayan ta gama wanke hannuntane seta juyo dan komawa d'akinta aiseta tsorata ganin mutum a bayanta har hannayenta sun tab'a kirjinsa inda ruwan hannunta ya jik'a mishi rigansa tana kallonsa cikintsoro😳 suhail yace wlh kece kece wanan yarinyar daga razanarki na gane kece dan bazan tab'a mantawaba😇


Sad-Nas
[10:00am, 12/9/2016] Sadiya Taheer: 🌺💐TANA🌹RAINA💕💞

By Mmn Shureim
(Sad-Nas)


43-44 Murmushi sosai suhail yakeyi yana kallon idanun sabreen, da sauri ta matsa baya tana cewa me kake cewane yah suhail wata yarinya kenan kake magana akai, cicefa sabreen ba wata yarinyaba. Suhail ya dawo haiyacinsa tare da sosa k'eyarsa yace kiyi hakuri sabreen idanunkune sukayi kama sosai da nata kiyi hakuri kinji😔, kai zanba hakuri yah suhail dana jik'a maka riga😊, karki damu ba komai seya juya zai fita se sukaga hafsat tsaye a kofar kichine d'in🙄. Suhail ya tsaya yana kallon hafsat yace hafsat me kikazo d'auka, ta d'an wayance tace nazo d'aukan ruwane se naji murya a kichine shine na shigo ashe kune, tana kaiwa nan ta juya da sauri ta koma d'akinta, suhail yasan hafsat tasa wani abu a ranta, ita kuwa sabreen jikinta a mave yake dan hafsat ta gansu da suhail a kichine gashi da daddare, da sauri tazo gun kofan inda suhail yake tsaye tace dashi barin wuce, juyowa yayi yana kallonta ita kuwa kanta a sunkuye ya matsa mata yana kare mata kallo harta wuce sannan shima ya wuce d'akinsa da damuwa sosai a ransa. Hafsat ranta se tafasa yakeyi ita dai batan me sukaceba amma to me yah suhail yakeyi a kichine gurin sabreen bayan sam shi bayama shiga kichine😠 lallai zan koyawa sabreen hankali idan dai har tayi kok'arin shigewa suhail d'ina, kai ina bazai yuba gobe zanyiwa mum magana akan aurenmu da suhail😠. Ita kuwa sabreen mamaki takeyi akan ganeta da suhail yaso yayi, lallai akwai aiki gobe zan sanar da kaka lbrn soyayyata da yah kamal gara kawai ayi aurenmu kar azo a samu matsala, sannan ita kanta taga yadda ran hafsat ya b'aci tace toko son yah suhail d'in takeyi oho, kishine ya tokarin sabreen a k'irjinta tace Allah sarki yah suhail shikenan zan rasaka, kuma na tabbatar daka fara sonane yanzu nima kuma ina sonka wlh😥.
Washe gari da safe sabreen bata fitoba dan basa karyawa da wuri kuma bata sallah. Harse 8:00am tayi wanka tasa riga da siket cikin kayan da kamal ya saya mata material ne blue ya mata kyau sosai ta fesa turare sannan ta yafa gyale a kafad'arta ta fito ta wuce kichin toasted bread tayi musu wanda tasa saidin a ciki se kamshine yake tashi ta sake soya egg sannan ta tafasa ruwan tea da kayan yaji taje ta shirya komai a daining sega hasat tayi wanka tasha english wears riga da siket tayi ado tazo har daining tana k'arewa kayan jikin sabreen kallo ita kanta tasan mai t'sadane dukda tasan cewa itama kyakkyawace amma kuma tasan bazata had'a kanta da sabreenba ko kusa. Ta k'arasa tace ke sabreen me kukeyi da yah suhail jiya a kichine? Sabreen ta juyo tace ina kwana hafsat, 😏hafsat tace ba wannan na tambayekiba ai, sabreen tace bakomai hannuna naje wankewa shi kuma bansan meyaje yiba, daidai lokacin suhail ya shigo palon lokacin hafsat tana cewa to wlh ki kame kanki ina gayamiki suhail shine mijin da zan aura dan haka ki dena wannan rawan kan naki😚sannan ta juya suka had'a ido da suhail ta wuce d'aki ko gaishesa bata yiba yanata binta da kallo. Jikin sabreen yayi sanyi dan maganan ya b'ata mata rai ta kalli suhail tace ina kwana yah suhail sannan ta wuce batare data jira amsarsaba ta d'auko abincincin su kaka dana mai gadi takai musu. Shi kuwa suhail yana tsaye agun yana binta da kallo harta fita sannan yayi sallama a kofar d'akin hafsat tazo ta bud'e yana tsaye fiskarta a had'e yace yau bazaki gaisheni bane hafsat, shuru tayi nad'an lokaci sannan tace ina kwana😏, yace lfy fushi kikeyi dani kenan ko? Ta marairaice murya tace gaskya yah suhail inaga lokaci yayi daya kamata muyi aure indai har kana sona😠, suhail yace to shikenan ki denayin fushi zanyiwa mum magana kinji, 😊murmushi tayi tace to nagode muje muci abinci to, shima murmushin😊 yayi mata yace to muje sannan suka nufi daining inda mum take zaune agun tana karyawa, dad'in ganinsu tare taji sosai suka zauna suna gaisawa. Sabreen kuwa bayan ta kai musu ta zauna agun kaka tana gaya masa yadda sukayi da kamal kuma ta amince. Kaka ayi ajiyar zuciya sannan yace sabreen shikenan tunda dai kina sonshi kema, amma shi suhail ya riga fara sonki tun lokacin da kuka fara had'uwa, sabreen SALMA ta gayamin komai kuma jiya da darema suhail yazo min da zancen yarinyar akan yanaga kamar kece ni kuma Sam ban gaya masa cewa kece d'inba, dukda dai shi atunaninsa an miki fyad'ene ahakan kuma yake sonki sosai sabreen. Sabreen ta sauke ajiyar zuciya tace kaka wlh Nima ina sonshi amma kuma yah kamal fa, kuma kaka hafsat tana son suhail sosai nan taba kaka lbrn abinda ya faru tas. Kaka ya tausayawa jikarsa sosai yace to shikenan sabreen shima kamal d'in ai mutumin kirkine Allah ya zab'a miki mafi alkhairi, tace ameen kaka maganan me kukayi da salman? Kaka yace mun dad'e Muna jiran zuwan salma da iyayenta tun bayan rasuwan mahaifinki da kwana 7 suka dawo suka gayamana gaskyar yadda mahaifinki ya rasu kuma suka bamu hak'uri sannan suka tabbatar mana da cewa duk lokacin da Muke buk'atar taimako zasuzo garemu nan kaka ya gaya mata cewa wannan macijin daya sari mamminkima salman CE ta kasheshi ba jama'an gariba babu Wanda yasan hakan saboda suba mutane bane ALJANUNE😳🙄😱


Sad-Nas
[10:00am, 12/9/2016] Sadiya Taheer: 🌺💐TANA🌹RAINA💕💞

By Mmn Shureim
(Sad-Nas)


45-46 ALJANU, Aljanufa kace kaka, kana nufin salma aljanace shine nayita hankad'ata jiya? Kaka yace kwarai kuwa shiyasa naketa dakatar dake, danma kinyi sa'a salma tana sonki a ranta ne tace ranan tazo gunki a d'akinki ganin,yadda kika tsoratane yasa ta canja salon zuwa ta yadda kowa zai ganta dan karki tsorata, amma wannan maganan ya zama tsakaninmu mu uku kinji? Sabreen ta sauke tsorataccen ajiyar zuciya tace to kaka shikenan nizanje in karya, yace toh sannan ta fito har zata shiga palo se taji hon, bayan maigadi ya bud'ene se taga motar kamal ne yake shigowa, hon yayi mata tare da kunnan wutan motan yana hankata, murmushi tayi sannan ta k'arasa gun motan ta tsaya ta gefensa, fitowa yayi cikin farin shets da blue jeens yayi kyau sosai ga kamshi da yake tashi, "good morning my luv" yace da ita yana murmushi😊, kunya taji sosai ta kauda kanta gefe tace morng ya kake😊, lfyta lau kin fito gurin kakane? Eh nakai mishi abincine, ok to muje ciki kafin ya gama cin abincin se indawo gunsa. Ayate suke tfy yana kallonta tare da cewa gaskya wannan wankan yayi kuma na yaba😘, dariya tayi dai dai lokacin sun shiga palo tare da sallama, wani irin abu ne ya tokari suhail a k'irkinsa ayayinda ya hangosu suna tahowa, sabteen ta karasa ta gaida hajiya sannan ta wuce ciki sunaya binta da kallo dukkansu😍. Bayan kamal ya zauna ne suka gaisa sannan hafsat ma ta gaishesa tare da had'a mashi tea, suna sha suna hira. Anan ne kamal yake sanar da mum k'udirinsa akan sabreen, mum taji dad'i sosai kuma tayi farin ciki tace to ai gara dai kam kuyi aure zaifi, kaima suhail yanzu kam lokaci yayi da za'ayi aurenku da hafsat kamar yadda iyayenku sukeso. Wani irin dad'i hafsat taji a ranta tace kamar kina raina mum😊, suhail ya kalli hafsat yace mum tunda tana karatu a dai bari seta gama tundama saura 1year ne ta gama. Mum tace to shikenan Allah ya nuna mana, yace ameen, kamal yace to gaskya nidai zan rigaka dan banaso in wuce nan da 6 month, suhail yayi murmushi yace to Allah ya sanya alkhairi, sukace ameen.
Ita kuwa sabreen tunda ta shiga d'aki taketa tunanin maganan da sukayi da kaka, nan ta kira munira ta gaya mata komai a waya. Munira tayi mamaki sosai tace yanzu bakya tsoro sabreen gaskya ina son ganinta, kuma inaso ta zama kawata wlh😀, sabreen tace lallai kam to idan ta sake dawowa zan had'aku. Munira tace to yanzu shikenan kin hakura da suhail d'in? Sabreen tace eh nahakura munna kawai zan auri yah kamal tunda ma kinga ga abinda hafsat tace min, munnira tace to shikenan Allah yasa hakan shine mafi alkhairi agareki k'awata, sabreen tace ameen ina abbakar sadiq d'inki? Munna tace yanan shimafa ya dage wai miyi aire se inci gaba da karatuna, sabreen tace eh tundai zai barki ai shikenan nima hakan zanyi, munna tace eyye ashe fa kina son kamal d'innan😜, sabreen tayi dariya tace bakida kyau fa munna nikam se anjuma ki gaida su mama😀, munna tace to nagode zasuji ki gaidamin "ango to bee" hmm zaiji sannan ta katse wayar tana dariya😃.
Bayan su mum sun gama cin abincine kamal da suhail sukaje gun kaka kamal ya gaya masa buk'atarsa akan sabreen, kaka yaji dad'i sosai kuma ya tabbatarwa kamal cewa yabashi tunda dai sabreen d'in ta amince, murna sosai kamal yayi sannan sukayiwa kaka godiya suka tafi. Suhail da kamal ne suke tfya a cikin motansu suna hira, suhail yace abokina ka kusa ka zama angon sabreen, kamal yace bawannanba tukunna, kasanfa matsalata suhail yanzu in gayawa sabreen ne ko dai inyi shuru? Suhail yace ina kace nanda 6month kake son auren, kaga daidai kenan kafin lokacin auren komai zai daidaita kamar yadda doctors sukace insha Allah. Daganan kuma shikenan seka jah kaya abokina gaskya zaka morefa da wannan sabreen d'in naka😋😃, 👊🏽duka kamal yakai masa yana dariya tare da cewa kaima ai k'i kayi damunyi tare. Suhail yace abokina kafi kowa sanin cewa ban tab'a "SON" hafsat a matsayin matar aurenaba sedai "SO" amatsayin 'yar'uwata na jini, nidai wannan yarinyar "TANA RAINA" itace nake "SO" a matsayin matar aurena dan haka sedai in auri mata biyu a rana d'aya wannan shine burina, da zab'in mahaifina da kuma zab'i nah. Kamal yace "ar u serious?" Suhail yace wlh abokina shiyasa nake so ka tayani da addu'a Allah ya sake had'ani da "TANA RAINA" kamal yace tofa harka lak'ana mata suna kenan toh ai semu sake komawa k'auyen gobe ko Allah zaisa mu dace, suhail yace hakan za'ayi kuwa, kamal yana kallon abokinsa kallon mamaki da irin son da yakewa wanda akaiwa fyad'e, yace sekayi angon "TANA RAINA" dariya suhail yayi😃 yace eyyy angon sabreen sannan suka tafa✋🏻suna dariya nima "SAD-NAS" na tayasu😆😆😆
[10:00am, 12/9/2016] Sadiya Taheer: 🌺💐TANA🌹RAINA💕💞

By Mmn Shureim
(Sad-Nas)


47-48 Washe gari bayan su suhail sunyi breakfast ne sukayiwa mum sallama akan zasu fita, mum ta musu fatan alkhairi sannan suka wuce tsakar gida gun kaka inda yakeba flawer ruwa, kamal ya kira sabrenn a waya dan yau tunda yazo baigantaba, sunata hira da kaka sega sabreen ta fito da himar har k'asa tana tafiya a hankali, juyowa sukayi suna binta da kallo, tunda kaka ya hangota yasan cewa tayi kuka. Ta k'araso tare da gaishesu kanta na gefe, daga kamal har suhail sunsan akwai wani abu a k'asa dan sam babu ko fara'a a fiskarta. Kaka yace sabreen lfy kuwa yana ganki haka? Hawaye suka zubo a fiskanta ta share da hannunta tace bakomai kaka, kaka yace bakomai kike kuka kuma gashi sam babu fara'a a fiskarki meya samekine? Kakana karka damu bakomai kawai dai mun d'an samu matsala ne da hafsat😥 kaka kasan cewa ina da hakui akan komai, amma kalamanta sunmin zafi sosai wanda idan na tuna tuna suna min zafi sosai, ta goge hawayenta ta juyo tana kallon kamal tare da cewa yah kamal dan Allah ka janye soyayyata kaje ka nemo daidai da kai, ni talakace 'yar kauye sannan jahila k'azama wanda take bin duk wata hanya koda ya sab'awa Allah ne taya yinshi dan ta janyo hankali yayyuna biyu da suke cikin gidan, akan suhail dai asirinki baiyi aikiba, shima bro kamal d'in ahankali asirin zai karye daga nan kuma ta k'are miki 'yar gidan matsiyata wanda bata da gatan uwa bare na uba😭.
Kallon kamal da suhail takeyi har cikin ido tana kuka tare da cewa wannan sune kalmomin da hafsat ta gayaminsu saboda nazo yin aiki a gidansu, kaka yau da asuba danazo gaisheka ban gaya maka bane saboda nasan hakuri zaka bani, amma su yayyuntane na gaya musune saboda su zama shaida dan gaskya hafsat bazata sake gayamin hakan ban mayar mata da martani, gudun faruwan hakanne yasa nakeso mubar gidan kawai nida kakana masu girki suna nan dewa a gari na gwammace inci gama da zamana a k'auyenmu. Tana kaiwa nan ta juya da saurinta ta koma ciki tanata kuka. Gaba d'ayansu abin ya musu zafi, kaka yace karku damu da zaran ta huce shikenan😒. Ran kamal inyayi dubu ya b'aci, yace dama haka hafsat take🤔, suhail kuwa cikin gidan ya koma yana kwalawa hafsat kira, da sauri ta fito don jin muryarsa da karfi. Ta k'araso tare da cewa na'am bro suhail gani, ransa a b'ace yace meya had'aku da sabreen? Atake ta b'ata rai tace bakomai, suhail yace kamar ya bakomai, kimin bayani meya had'aku da ita? Hafsat ta b'ata rai tace bro yanzu saboda sabreen d'inne kake min ihu haka har kana b'ata rai, nifa kanwarkace kuma wanda zaka aura, hafsat ba wannan na tambayekiba dan ke k'anwatace seki aikata laifi? Tace laifin me kuma na aikata bro wato takai k'arata gunka kenan😣 harta samu fiskan kai kara agunka tabd'i to shisshigemin takeyi ni kuma bana son hakan shine nace mata ta fita harkata danni ba sa'arta bace😏. Suhail yace hafsat yaushe kika zama haka, wlh kinban kunya ban tab'a tunanin haka daga garekiba a irin tarbiyan da kika taso. Yah suhail waime ta gaya makane dahar ka yadda dashi haka kaketa min fad'a? Suhail yace abunda kika mata shita gayamana dan haka wannan ya zama na farko kuma na karshe kar in sakejin kin mata haka kina jina? Rai a b'ace tace naji sannan ta wuce d'aki kamar zata fashe😡. Mum ce ta fito tana cewa suhail meke faruwane kaida hafsat naji kamar fad'a kake mata? Suhail yace bakomai mum ki barni da ita kawai laifi tayi, laifi kuma, hafsat d'in laifin me tayi toh? Suhail yace sund'an sami rashi jituwane ita da sabreen kuma ita hafsat d'ince da laifi. Toh yau kuma hafsat da fad'a bari inje inji toh, se mum tabi hafsat d'aki shi kuwa suhail ya shiga d'akin sabreen tare dayin sallama. Tana zaune akan gadonta tana share hawaye da hannunta, mik'ewa tayi tare da amsa sallamar cikin muryan kuka kanta a sunkuye, hanki ya ciro a aljihunsa ya mik'a mata, wani iri taji sannan tasa hannunta ta karb'a tace nagode. Yana tsaye daga kofa yace sabreen dan Allah kiyi hakuri kinji, na mata magana hakan bazai sake faruwa kinji? Wani sanyi taji a ranta ta d'aga kai alamun toh, murmushi yayi yace toki dena kukan pls😊, kawai setaji tana son kallon fiskarsa seta d'ago da kanta tana kallonshi tace "thankyou"☺. Muryar nata yayi mishi kama dana wannan yarinyar wlh suna kallon juna har cikin ido setayi saurin sunkuyar da kanta k'asa saboda wani irin kaunarsa da yake ratsa jikinta, shidai baisan me zaiceba seya bud'e kofan ta d'ago da kanta sunata kallon juna harya fita. Sabreen ta sauke ajiyar zuciya tanaji dad'i acikin ranta😇 wani gefen kuwa cewa takeyi kawai zancewa yah kamal yafito muyi aure dan gaskya bazan iya jurewa soyayyar suhail ba matukar ina sashi a idanuna gaskya. Afili kuma tace suhail kai nakeso tun ranar daka zubar da jininka akaina nice fa sabreen nice yarinyar da kake nema😒 "I LOVE YOU SO MUCH SUHAIL😰". Suhail da yake tsaye a bakin kofa kuma dai yasan ba karya kunnensa yayi mishiba tabbas yaji abinda sabreen tace😳🤔😳...




Please Login or Register in order to submit comment