Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

hafsat sannan ta karbi wayan tasa a kunne tare da cewa hello, suhail yace sabreen naji abinda ya faru amma inaso kisani shi mamaci baya dawowa k'ila dai kinsa tunaninta arankine har kike ganinta a naki tunanin yakama ki d'auki kaddara kisa a ranki cewa ta rasu ba kuma zata dawo garemuba har abada kinji? Shuru tayi tana had'iyan kukanta batace dashi komaiba, suhail yaji tayi shuru batace komaiba seya kira sunanta "sabreen are you there"? Se alokacinne tace "yeah naji kuma na gode" sannan ta mik'awa yah kamal wayan, lokacin suhail nacewa sabreen muryaeki yamin kama dana wata yarinya, karaf a kunne kamal amma seyayi kamar baiji yace hello abokina yane, suhail yayi ajiyar zuciya yace bakomai nan dai sukaci gaba da hiransu har kamal yayi musu sallama ya tafi suma suka wuce d'akunansu donyi bacci. Kamal dai tunda ya koma gida tunanine cike a zuciyarsa game da sabreen da kuma abinda yaji a bakin suhail, da kyar bacci ya d'aukesa. Shima suhail acan pakistan kasa bacci yayi yanata tunanin wannan yarinyar mai nik'af, tabbas yanzu da yayi magana da sabreen seyaji irin wannan muryance datace mishi "Thankyou so much SUHAIL" yace toh kodai kawai dan nasata a rainane shiyasa naji muryanta irin na sabreen, da wannan tunanin shima yayi bacci. Itama sabreen kasa bacci tayi dukda kashen wutan d'akin da hafsat tayi amma sam ta kasa bacci, fiskan MACENNAN dai shiyake mata yawo a kwakwalwarta, tace dama na sani dabanyi ihuba tunda dama na dad'e inaso in sake ganinta domin inyi mata godiya, insha Allah duk randa na ganta bazan sake tsorataba zanso inji metakeson gayamin sannan nima kuma inyi mata tambayoyi, ta wani gefe kuwa dad'in kalaman suhail takeji har cikin ranta tana ta murmushi tare da mamakin suhail tana zamcen zuci, yanzu shi suhail kota muryata bazai ganeniba😊, murmushi tayi tana tuna lokacin da suke shak'ar numfashin junansu yayinda suke kallon idanun junansu, kyakkyawar fiskarsa take gani a idanunta tare da murmushin yayi mata😌 dad'i sosai take ji har cikin ranta tace koda wasa bazan sanar dashiba, kuma bazan tab'a bari ya ganeniba😊 da wannan tunanin itama bacci yayi gaba da ita.
Bayan sunyi breakfast ne taje gun kakanta sunata hira har azahar kafin ta shigo dama bata sallah. A palo suke zaune sunata hira da mum da yah kamal da kuma hafsat sabreen dai dariya kawai takeyi tana sauraron tsokanar da yah kamal yakeyiwa hafsat, har la'asar bayan sunyi sallah ne kamal yace zai fita se dare zai dawo, mai girkinsu tana gama abincin dare d'anta yazo ya d'auketa, alkhairi sosai mum ta mata harma da hafsat sannan suka tafi. Bayan isha yah kamal yayi cefene sosai ya kawo gida saboda gobene alhamis sabreen zata fara girki. Washegari ta shiga kichine ta fara girki, dama kunsani base na k'ara maimaitawaba. Kowa yaji dad'in girkin nata harma da masu gadin gidan sunata cewa ai tafi nadama iya kirki wlh, dad'i kaka yaji har cikin ransa don yadda aketa yaba girkin jirarsa😊. Haka tayi na rana dana dare mum farin cikine a fiskarta sosai danko gaskya girkin sabreen bakarya, sun yaba sosai harda hafsat tana cewa gaskya zaki koyamin girki sabreen, yah kamal yace da lalacinkinne zaki koyi girki? Hafsat ta b'ata rai mum kinji abinda bro kamal yake cewa ko, mum tace rabu dashi zaki bashi mamaki kuwa, sabreem tace zan koya miki hafsat karki damu. Haka sukaita ta hira har suka gama cin abinci se yah kamal ya mik'e tare da cewa mum nizan tafi seda safenmu, mum tace yau da wuri haka babu hira kenan, kamal yace mum kinsanfa gobene abokina zai dawo, dan haka bazan samu zuwa da safe bama sedai zuwa yamma. Mum tace to shikena Allah ya bamu alkhairi, kamal yace ameen sannan ya wuce gun kaka sukai sallama seya tafi, su mum kuwa sun d'an tab'a hira sannan suka wuce donyin bacci, Hafsat se murna takeyi gobe bro suhail d'inta zai dawo, ita kuwa sabreen binta kawai takeyi da kallo tana mamakin hafsat, dan sam basa wani hiran kirki da hafsat d'in, amma gashi yanzu tanata murna tana cewa sabreen zakiga d'ayan bro na gobe kinji, sabreen tayi murmushi tace to Allah ya kaimu goben Allah kuma ya dawo dashi lfy😊, hafsat tace ameen sannan ta kashe wuta suka kwanta kowacce da tunaninda takeyi a ranta da haka har bacci ya d'aukesu...

Sad-Nas
[9:59am, 12/9/2016] Sadiya Taheer: 🌺💐TANA🌹RAINA💕💞

By Mmn Shureim
(Sad-Nas)


31-32 Washe gari da safe safreen da hafsat suka kintsa gida tas ko ina se kamshi yakeyi, hafsat ce taje d'akin bro suhail ta wanke masa ta gyara ko ina tsab. Sabreen ta had'a musu breakfast bayan sunci ne taje gun kakanta suka d'an tab'a hira dayake bata da wani aiki se girkin kawai. Sabreen ne da mum a palo tana tambayanta Hajiya me za'a dafa, mum tace karki damu sabreen d'ana suhail babu abinda baya ci se gwaten doya da kuma duk wani juice na gargajiya da ake had'awa to baya sha, shidai a drinks coke yafi so. Sabreen tace toshikenan Hajiya yau zan koma d'akina da zama, mum tace meyasa, sabreen tace bakomai ai yanzu na dena tsoron😊, murmushi mum tayi tace to shikenan kiyi yadda kike so kinji, nagode Hajiya sannan ta tashi ta wuce d'akin hafsat ta kwashe kayanta tas ta mayar d'akinta sannan ta kwanta a gadonta tana jiran wannan MACEN ta sake zuwa, ganin ba wani abinda zatayine seta kira munira sunata hira abinsu, daga nan ta kira yah kamal tace kar yace ni bana kiransa. Ringing d'aya ya katse sannan ya kirata, murmushi tayi ta d'auka tare da cewa hello yah kamal ina kwana, lfy lau sabreen ya kike, lfyta lau yau bakazo kayi karin kumallo ba, eh wlh nasha tea nd bread karki damu zanzo da suhail bayan la'asar muci daddad'ar girkinki kinji, murmushi tayi tace toba damuwa se kun zo dama na kirane mu gaisa se anjuma, ok sabreen nagode sosai ki gaishemin da kaka, to zaiji insha Allah sannan ta katse wayar tayi baccinta.
20:00pm daidai sabreen ta farka tare da duba wayanta taga time, 🙄 wuce kichine tayi da saurinta domin had'a domin had'a abinci, peppe soup d'in kaza tayi da rice nd stew sannan ta hada cor-slow mai dad'i kuma yasha had'i, sannan ga friut salad. Da misalin 3:50pm ta gama komai seta zubawa kaka da maigadi kowa da nasa takai musu sannan ta wuce d'akinta tayi wanka tare da shafa mai tasa doguwan riga after dress batayi kwalliyaba sam se d'an turare data fesa ajikinta "WISAL" wanda yah kamal ya saya mata. Kichine taje ta d'ibi abincinta ta koma d'aki taci sannan ta mayar da plate d'in kichine ta dawo d'aki tana ta game a wayanta dan ya kaml yasa mata games masu yawa.
4:15pm motar kamal tayi hon a gate, da sairi mai gadi ya bud'e gate yana yiwa suhail maraba da dawowa sannan suka gaisa dukkansu seya k'arasa ciki. Hafsat ne ta fito d'auke da ado sosai a fiskarta tayi matukar kyau ta k'arasa gunsu da mirnarta tana cewa oyoyo bro suhail "yoir wlcum" murmushi suhail yayi yace wannan kwalliyar dukni akwai wa? Murmushi tayi tace sosai ma kuwa😊, kit d'insa ta karb'a a hannun ya kamal tace sannu da kokari yah kamal, yawwa hafsat, suhail yace gaskya naga wannan wankan naki yar'uwata kuma zan biya😊, dad'i taji sosai sannan suka wuce suna dauke da kaya a hannunsu. Mum tana mirmushi tace maraba da dawowa ya hanya, suhail yace Alhamdulillah mum kuna lfy, lfy lau sannunka da hanya, yawwa mum sannan ya wuce tare da cewa bari nad'an watsa ruwa, ok kamal yace sannan hafsat ta shiga da kayan d'akinsa.
Bayan suhail ya fito ne ya wuce daining inda suke zaman jiransa, ya k'arasa ya zauna tare da gaishar da mum d'insa, sannan suka gaisa da hafsat yace ta zuba mishi aminci. Suna cin abinci dukkansu suna hira sega sabreen ta fito ta iso hargun daining tace ya kamal sannu da zuwa, ya suhail sannu da dawowa ya hanya? Kamal ne ya fara magana yace yawwa sannu sabreen yana mata murmushi😊, suhaila yace yawwa hanya Alhamdulillah ya karin hakuri kuma, sabreen tace hakuri alhamdulillah kanta na kallon hafsat, yace to allah ya jikanta, tace ameen seta kalli mum tace hajiya bari naje gun kaka, mum tace toh sabreen sekin shigo, murmushi tayi sannan ta wuce kamal da suhail sunata binta da kallo harta fita. Mum da hafsat duk sun lura da kallon da sukeyiwa sabreen ita kuwa sabreen batama san sunayiba, bayan fitantane suka maiyar da idonsu kan abincinsu, ita kuwa hafsat wani kishine taji har cikin ranta😬😁
[9:59am, 12/9/2016] Sadiya Taheer: 🌺💐TANA🌹RAINA💕💞
By Mmn shureim
(Sad-nas)

WASUNKU SUNA TAMBAYA KO NICE MAMAN SHUREIM DATA RASU WATO (ZARA'U BABA YAKASAI ALLAH YA JIK'ANTA DA RAHAMA AMEEN) TO GASKYA DAI NI BANKAI MATSAYINTABA DANNI BA BARUBUCIYA BACE KAWAI DAI ABIN YANA BAN SHA'AWA NE SHINE NACE BARI DAI IN GWADA, CIKIN IKON ALLAH WANNAN SHINE LITTAFINA NA UKU, NAGODE DA SOYAYYARKU.
Love you all💞💐🌹🌺


33-34 Sabreen ta shiga gun kaka yana ta karatun Qur'ani mai girma, bayan ya idar ne ya juyo yana kallon sabreen data shafa addu'an a fiskanta tace ameeen kakana, kaka yace naji mai gadi yana cewa sannu da dawowa kardai har SHULE d'in ya dawowo, 😅dariya sosai sabreen tayi sannan tace kaka ba shule ake cewaba SUHAIL sunansa, kaka yayi dariya yace to ai sunan nasane da wahala gara dai shi kamal d'in nasan sunan, amma shi shule kam bamma tab'a jiba se agunsu. 😄kai kaka kaban dariya wlh EH yadawo, kaka yace dakike dariyannan se kikayi kama da mahaifinki sosai, 😰hawayene atake ya cikowa sabreen a idanunta ta fara magana Allah sarki ABBA NAH Allah ya jikanku da rahama ameeen, kaka naso ace ina tare da iyayena inga soyayyar da ABBA zai nunamin amma kai da mammi ne kawai na samu naku itama yau babu ita a duniya😭😭😭 har abada bazan tab'a mantawa dakuba "KUNA RAINA" kaka ma kwallaya yake sharewa a fiskarsa, ganin hakanne yasa sabreen ta tashi ta fita tana ta kuka harta shigo palon ko sallama babu ta wuce d'akinta yayinda su mum suke binta da kallo. Kamal yace hafsat jeki kiji meya sami sabreen take kuka, hafsat ta mik'e ta wuce lokacin sabreen ta kifu a gado tanata kuka babu irin tambayan da hafsat batayiwa sabreen ba, amma ko kallon hafsat batayiba bare tace mata wani abu. Hafsat ta dawo palo tace batacemin komaiba tanata kukanta, suhail yace hafsat jeki kirata, bayan hafsat ta gaya mata ne seta fito, sabreen ta dena kukan amma hawayene cike a fiskarta taja gyalen kayanta ya rufe mata ido taje ta zauna a kan kapet. Mum tace sabreen meya faru kike kuka, cikin wani irin murya mai cike da tausayi tace bakoma hajiya, wani iri kamal yakeji a ransa kamar yaje ya rungumeta. Sallamar kakane ya katsesu, bayan sun amsane kamal da suhail suka mik'e suka karsa gunsa dama basu gaisaba, wata yarinyace kakkyawa biye da kaka, bayan sun gaisane itama yarinyar ta gaishesu se kamal yace kaka meya samu sabreen ne? Kaka yace ta tuna da iyayentane shiyasata kuka😒. Suhail yace Allah sarki nayi tunanin hakan kuwa, kamal ya kalli yarinyar da take sanye da doguwar riga jah da gyalensa yace wannan fa kaka? Kaka ya kalleta yace dasu kawar sabreen ce tazo guntane, kamal yace ok shiga tana ciki, a nitse ta wucesu kamal yace sabreen kinyi bak'uwa, sabreen ta d'ago da kanta don ganin bak'uwan nata🤔🙄 wazata gani wannan MACENNE ta karaso tare dayin sallama taje ta zauna kusa da sabreen sannan ta gaida mum cikin girmamawa ta gaida hafsat sannan ta juyo tana kallon sabreen da mamaki ya cikata tare da d'an tsoro kad'an. MACEN tana murmushi tare da tab'a hannun sabreen tace kaka yacemin kinata kuka tare da d'aga mata gira😉ma'ana su shiga d'aki, sabreen tad'anyi murmushin karfin hali tare da wayancewa tace muje ciki toh, mik'ewa sukayi a tare suka wuce d'akin sabreen, shidai kamal idonsa nakan sabreen har suka shige ciki yayinda kaka yake lura da irin kallon da kamal yake yiwa sabreen...

Sad-Nas
[10:00am, 12/9/2016] Sadiya Taheer: 🌺💐TANA🌹RAINA💕💞

By Mmn Shureim
(Sad-Nas)


35-36 Bayan su sabreen sun shiga d'akine MACEEN tasa key ta rufe, da sauri sabreen ta juyo tace meyasa kika rufe kofan? MACEN tace karki damu sabreen bazan cutar dakeba nazone dan inyi magana dake. Bayan sun zaunane macen ta rik'e hannayen sabreen dukka biyu ta fara magana suna kallon junansu.
Sunana SALMA kuma ni kad'ai ne agun iyayena, tun kafin a haifeki mahaifinki ya rasu ata dalilin cetona.
Wata rana nida iyayena muna zaune a cikin jeji suna koyamin harbi da kwari da baka, ina zaune daga nesa su kuwa iyayena suna tsaye agu d'aya mahaifina ya saita kwari da baka a daidai inda nake zaune akan zai gwada kona iya kwaucewa kamar yadda yake koyar dani, nima jira nake ya harbo in nuna masa kwarewata na kaucewa. Kawai sega wani bafulatani yana wucewa se idonsa yakai gun iyayena kuma yaga suna da niyan harbinane, bafulataninnan ya kalli lokacin ina zaune bazan wuce shekaru 7 ba, dai dai lokacin da mahaifina ya harba kwarinne se wannan bafulatani yayi sauri tare dayin tsalle danya tareni, amma se wannan kwarin ya sameshi a daidai setin zuciyarsa, nan take ya fad'i. Iyayena dani dukkanmu mukazo kansa lokacin jini nata zuba sosai daga jikinsa, hannuna ya kamo yana magana da kyar yana cewa haba bayin Allah wannan yarinyar kuma metamuku da zaku kasheta dan Allah ku kyaleta sannan ya juya yana kallona yace yarinya tashi ki gudu kinji ki gudu zasu kasheki, mahaifina ya share kwallan fiskarsa yace bawan Allah ba kasheta zamuyiba, hasalima 'yarmuce wannan na cikinmu gwaji kawai muke mata akan koyar da ita danayi, gashi abisa rashin sani na cutar dakai gurin kokarinka na ceton 'yata😰, dan Allah ka yafemin bawan Allah ba'a son rainabane. Bafulatanin yayi murmushi yace bakomai na fahimta, haka Allah ya tsaramin nikuma, ta wannan hanyar zan koma ga mahaliccina, nayafe maka har cikin zuciyata, sedai ina neman taimakonku, mahaifina yace taimakon me kenan? Bafulatanin yace matata tana gida d'auke da tsohon ciki ita da surukina suna can gida a wannan kauyen da yake gaba danan, inaso ku taimaka ku k'arasa dani gidana dan baajin zan iya karasawa da kaina dan yadda nakeji ayanzu. Dukda cewa mahaifina ya cire kifiyar daya soki bafulatanin, amma sam jini bai dena zubaba gashi daga gani yana shan azaba, haka mahaifina ya d'aukeshi mukaje har kauyenku, nan mutane suka taru a kanshi agun mai unguwa. Matarsa da surukinsa aka kira sukazo tana ganinsa ta fara kuka sosai, mai anguwa yace meya sameshi haka? Har mahaifina ya bud'e baki zaiyi gaya musu abinda ya faru, kawai se bafulatanin ya fara magana da k'yar yana cewa ina cikin tfy ne se nayi tuntub'e da wani abu, kafin in ankara se naji na fad'i akan wani abu mai kaifi kuma mai tsini, ban iya tashiba se naji mutane na zuwa, shine nace su taimakamin su kawoni kauyenmu, bafulatanin ya nuna mahaifina yace wannan shine wanda ya ciremin kifiyar data sokeni kuma ya kawoni gida. Hawayene sosai a fiskar iyayena dajin lbrn da bafulataninnan ya fad'awa yan kaiyensu. Matarsa da surukinsa suka fara kuka gashi asibiti se cikin garin, mahaifina ya d'aukesa yace muje asibiti, nan aka tashi da wuri domin zuwa asibiti, se mata mai cikinnan ta rike hannunsa tanata kuka tana cewa maigida karka tafi ka barni tun bakaga abinda zan haifa manaba, banaso abin cikina ya zama maraya dan Allah karka barmu. Bafulatanin ya rik'e hannun matarsa yana kokarin magana amma se mukaji yana salati tare da cikawa😰. Kuka sosai matarsa takeyi da kuma jama'an dake gurin musamman iyayena dani, matarsa kuka takeyi tare da rungume gawan mijinta kowa ya tausaya mata, da kyar mahaifinta ya janyeta ya kaita gidan makota inda nida mahaifiyata mukabi bayanta, bayan mahaifinta yakaitane seya koma gunsu mahaifina akayi mishi wanka tare da suturceshi akai masa sallah se gidansa na gaskya😭. Salma ta tsaya da lbrnta anan tana kallon sabreen da idanunta yayi jah dan kuka datakeyi😭 SALMA ta dad'a matse hannayenta acikin na sabreen tana kwalla itama tace sabreen bakowa bane wannan bafulatanin illa MAHAIFINKI dan Allah ki gafarcemu nida iyayena😰👏🏻. 😳🙄😭😭 idanu sabreen ta bud'e tare da tsananta kukanta sosai ta hankad'e Salma tare da mikewa tabud'e kofa ta fita a guje segun kakanta yana baiwa flawer ruwa, tunkafin ta karasa gunsa ya juyo ya tareta dan yasan komai. Sabreen tana kuka tana cewa kaka itacefa sanadiyan rasuwan mahaifina wannan ita da iyayenta sune sila kaka😭😭😭. Salma ta k'araso gunsu tana cewa sabreen kakanki yasan komai ke kad'aice baki saniba dama, sabreen da take kallon salma seta juya tana kallon kaka tace kaka wai kasan komai😡😰😭??

Sad-Nas
[10:00am, 12/9/2016] Sadiya Taheer: 🌺💐TANA🌹RAINA💕💞

By Mmn Shureim
(Sad-Nas)


37-38 Kaka yace eh nasan komai sabreen, mamminkine tace karna gaya miki ita zata gaya miki da kanta shiyasa nayi shuru😰. Sabreen tace to kaka amma dukda kasan hakan shine kabarta tazo guna akan me zatazo guna bayan ita da iyayentane nasadiyar kasancewata marainiya, juyawa tayi afusa ta sake hankad'a salma tana cewa kibar gidannan banason ganinki kuma bana buk'atan jin sauran bayaninki kawai ki fita a gidannan karki sake zuwa inda muke adalilinki mahaifina ya sadaukar da ransa😭, salma ma kuka takeyi tace kiyi hakuri sabreen ki saurareni, sabreen tace bana buk'atan jin komai kawai ki fita nace😰, salma tace haba sabreen nasan dama hakan zai faru amma dan Allah kiyi hakuri ki yafe mana hakan shiyasa nad'au alk'awarin taimakonki kota wani hanyane dan ki yafe mana, sabreen shiyasa na saudaukar da budurcina dan in taimakeki a hannun wannan MUTANE UKUN a tunanina hakan zaisa ki yafemin sabreen dan Allah😰. Murmushin takaici sabreen tayi tace kina nufin zan yafe mikine, to ai shi mahaifina RANSA ya baki saboda da haka ban yafeba kuma kibar gidannan salma😭. Shi kaka dayake yasan wacece salma da sauri yaje ya janyo sabreen yana cewa haba sabreen kefa musulmace bai kamata ki dinga fad'an hakanba mahaifinki kwanansane ya kare koda hakan bai faruba to a wannan ranan zai mutu. Da sauri sabreen ta cewa kaka da bazai mutuba kaka ka dena bin bayanta nidai ban yafeba salma kibar gidannan😭, kaka yace salma yi hakuri kije karki damu zata yafe muku dama bakuyi komaiba jeki kinji mun gode sosai banaso 'yan gidan su dawo suji me muke ciki. Kuka sosai salma takeyi sannan ta tafi tana fita daga wajen gate d'insu seta b'ace.
Kuka sosai sabreen takeyi kaka yana ta rarrashinta tana cewa wayyo Abbana wayyo mammaina Allah ya jik'anku da rahama😭. Kuka tayi mai isarta sannan tayi shuru ta wuce d'akinta tanata tunanin abin a ranta, toilet ta shiga ta wanke fiskanta sannan ta fito zataje kichin ta d'aura abinci dare, wayartace ta fara kara ta duba taga yah kamal ne, ta dauka tare da cewa hello, kamal yace hello sabreen ina fata dai kin dena kukan yanzu? Murmushin karfin hali tayi tace EH nadena, yace to shikenan mun fitane dukkanmu hardasu mum amma zuwa anju kafin magrib zamu dawo kinji, to yah kamal sekun dawo nagode, yace sabreen kawar naki ta tafine? Eh tafi😠, ko to shikenan semun dawo, toh sannan ta katse wayar.
Itadai bats ganewa yah kamal ba alamu dai ya Nuna sonta yakeyi, kuma gaskya yah kamal mutum ne nagari Wanda ko wace mace zatayi fatan samu a rayuwarta. Yana da kyawawan halaiya ga nutsuwa da Sanin darajan mutane, bugu da k'ari kyakkyawane shi sosai Dan yafi SUHAIL kyau gaskya, kawai dai shi SUHAIL farine tas kamar balarabe, shi kuwa kamal bak'ine sannan yana da saje mai kyau Wanda shi suhail Sam bayi da saje se gashin kai mai laushi. Kunsan kuma farin mutum da d'auke ido da kuma d'aukan hankalin 'yan mata gashi sun iya dressing sosai da iya d'aukan kamshi😘 kuma suhail yafi kamal tsayi sannan suhail baida yawan dariya kamar kamal, wannan shine bambancinsu. Sabreen tanata tunani a zuciyarta tana had'a abinci har ta gama tuwo miyan kuka yaji DRY FISH. 6:20pm su mum suka dawo gida lokacin sabreen tana kwance a d'akinta, mikewa tayi dan taji dawowarsu ta karasa Palo tace HAJIYA sannuku da dawowa, mum tace yawwa sabreen sannunki da gida ya fama da aiki, sabreetayi😊 tace alhamdulillah sannan tace ya kamal yah suhail sannunku da dawowa, sukai mata 😊sukace yawwa sannu da aiki, ta kalli HAFSAT sukaiwa juna murmushi tace sannu da dawowa, HAFSAT tace yawwa sannu sanna itama ta shige d'aki. Suhail yace muyi alwala ko semu wuce masallaci, kamal yace to Kaje ina zuwa sannan suhail ya wuce ya barsu a tsaya, sabreen ta juya zata koma d'aki se kamal yace sabreen inasonyin magana dake, sabreen ta juyo tana kallonsa tace toh yah kamal ina sauraronka, daga Inda yake tsaye yace baridai muyi sallan magrib tukunna kinji, tace to badamuwa, murmushi yayi mata sannan ya wuce d'akin suhail ita kuwa tanata binshi da kallo harya shige sannan tayi ajiyar zuciya ta wuce d'akinta.
Bayan sun dawo daga masallacine suhail yace toni bari in ciga ciki seka shigo, OK kamal yace dashi sannan ya kira sabreen a waya yace mata yana tsakar gida acikin mota, tace to ina zuwa shi kuwa ya shige mota ya zauna yana jiran fitowarta. Saida ta sake fesa turare sannan ta fito bakowa a Palo ta wuce gun Motansa ta bud'e gaba tare da sallama bayan ya amsa sallamarne seta shiga ta zauna tare da rufe kofan tace gani yah kamal kanta na kallon gate d'in gidansu shi kuwa yana kallonta yayinda take ganinsa da gefen idonta.😜

Sad-Nas
[10:00am, 12/9/2016] Sadiya Taheer: 🌺💐TANA🌹RAINA💕💞

By Mmn Shureim
(Sad-Nas)


39-40 Kamal yayi shuru nad'an wani lokaci sannan yace sabreen zuciyata ta dad'e dajin k'ishin ruwanki, ban samu daman sanar dakeba se yau, ina fata zan samu karb'uwa a zuciyarki, shuru sabreen tayi batace komaiba dan kunyansa daya kamata. Kamal ya sake magana cikin muryansa mai cike da so da k'auna yace sabreen ina matuk'ar k'aunarki tun randa na fara ganinki a rayuwata amma idan akwai wanda yake ranki dan Allah karki b'oyemin ki sanar dani kinji? Ajiyar zuciya sabreen ta sauk'e sannan tace bakomai yah kamal tabbas akwai wanda yake raina amma dukda haka na amince maka. Kamal yace ua za'ayi haka kuma sabreen, tace karka damu yah kamal nima ina sonka har cikin raina kuma nagode sannan ta b'ude kofan motan da niyan fita se yayi saurin rik'o hannunta ta zauna sannan ya saki hannunta yace kin tabbata da abinda kika fad'a min? Kai kawai ta d'aga ba tare data yadda sun had'a ido ba. Kamal ya had'iyi nyawu tare da sauke numfashinsa a hankali sannan ya sake rik'o hannunta yasa mata wani abu tare da cewa nagode da amincewarki sabreen, yau mahaifiyata zatayi farin ciki sosai da wannan lbrn dazan bata anjuma, saurin me kikeyi sabreen ina zakije haka? Hannunta ta janye daga nashi kanta a sunkuye tace zan koma cikin gidane😉, murmushi yayi yace kunyata kikeji kenan😊, to shikenan kije dama kiran dana miki kenan. Abinda ya samata a hannunta ta mik'a mishi tace gashi, kamal yace "gift" d'inkine sabreen na amincemin da kikayi, kanta ta d'ago ta kalleshi tare da cewa nagode tana murmushi😊. Shima murmushin yayi mata mai d'auke da "SO" yace mata

Please Login or Register in order to submit comment