Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya gama karanta texs d'in sabreen ne seyaji sanyi a ransa yanata murmushi😊 yace tome kuma (SABSU)🤔🤔? Karan wayansa ya sakeji, amma sam yak'i d'auka dan yafiso yayita ganin texs d'inta. Sabreen bata sake kiransaba kuma bata sake tura texs d'inba da tunaninsa tayi bacci.
Tun daga wannan ranan wasu sake wayawa har ranan da suhail ya dawo NIGERIA. kamal da hafsat ne sukaje airport d'aukosu, koda suka iso gida sabreen tana shirya abinci a daining suka shigo. K'arasowa tayi har inda suke ta tsaya ta gefen hafsat tana murmushi tace yah suhail sannu da dawowa, shima murmushin yayi yace yawwa sabreen na sameku lfy? Tace lfy lau yau kam hafsat zatayi bacci mai kyau dan kullum seta dameni da yah suhail d'inta😀, suhail yace to ai shikenan gani na dawo nima nayi kewarta sosai wannan karon har ciwo seda nayi dan ita😉, murmushi sabreen tayi tare da dafe hafsat a kafad'a tace todai kinji😜, hafsat kam dad'i sosai taji mara misaltuwa dan gaskya suhail ya rame sosai☺. Sabreen tace yah kamal sannu da zuwa, yace yawwa wifey😊, hafsat tace tun ba'a d'aura ba🙄? Kamal yace kwana nawane? Zuciyan suhail k'una ya mishi sosai seyi d'an murmushi yace bari naje in watsa ruwa, kamal yace okey seka fito sannan ya wuce hafsat ta bishi da kayansa. Sabreen tace nima bari naje na k'arasa shirya abincin, kamal yace muje in tayaki, sabreen tace a'a nagode, yace nidai muje ai soon zamu faryi tare, hakadai suka wuce yana tayata yana mata hira ita kuwa maganan da sukayi da suhail yanzune kawai taketa maimaitawa a ranta tana murmushi dan tasan bada hafsat d'in sukeyiba da junansu sukeyi💕. Shi kuwa kamal yaga se murmushi sabreen takeyi ya d'auka kodon hiran da yake matane😆. A haka suhail ya fito ya samesu lokacin kamal yana cewa kina girki ina miki hira da daka, se a lokacin sabreen ma tadawo daga duniyar tunani tace kaid'in harka iya daka😀? Yace sosaima babu abinda bazan koyaba ta dalilinki my luv😊 kallon juna sukeyi suna murmushi💘 dan basusan suhail yana tsaye yana kallonsuba zuciyarsa se tafasa yakeyi😱😠 ko kusan dalili kuwa masu karatu???


Sad-Nas
[10:00am, 12/9/2016] Sadiya Taheer: 🌺💐TANA🌹RAINA💕💞

By Mmn Shureim
(Sad-Nas)


59-60 Sabreen ta sunkuyar da kanta tace bari na shiga ciki, ta juya kenan se suka had'a ido da suhail da sauri ya kawar da kansa itama sabreen haka ta wuce d'akinta. Bayan sun gama cin abincine kamal yace mum jibi zan wuce pakistan insha Allah suhail zanbar komai a hannunka pls ka kula min da sabreen bare kuma zasu koma gida itada kaka so pls kayi duk wani abu dakaga ya dace, tace bazatayi program ba, amma wanda zai auri munira k'awarta ya kirani munyi magana akan za'a had'a gabad'ayane zamuyi dinner zan baka number'nshi seku had'u. Suhail yace ok badamuwa, mum tace toh shikenan seku maidasu gida gobe donyi shirye shiryensu tunda yanzu sabreen ta koyawa hafsat girki harta kware😀, hafsat tace mum nima zan bisu raka sabreen😊, kamal yace shikenan zamuje k'anwata. Shidai suhail zuciyarsa ciwo take mishi amma seya daure sunata hira cikin farin ciki.
Washe gari su sabreen suka shirya tsab suka fito, alkhairi sosai mum tamusu dama kuma kamal ya bud'e mata account tun suna gidanshi aciki yake sa mata kud'in aikinta ita da kaka, dan yana musu kyaitan kud'in kashewa sosai shiyasa bata tab'a na account d'in.
Can k'auye kuwa munnira tayi musu girki mai kyau kuma mai dad'i ga fura da nono ta share tsakar gidansu tas dama k'asane sosai a tsakar gidan dan haka ta shareshi tas komai dai yayi. 3:10pm su sabreen suka iso k'auyensu, da sauri munna ta fito ta rungume sabreen tana murna sosai tacewa hafsat sannu da zuwa, hafsat tace yawwa sannu, sannan ta kalli su suhail tace angwaye marabanku da zuwa, sukace yawwa amare😀, kakane yace bisimillah ku shigo, su sabreen suka wuce ciki su kaka suna biye dasu. D'akin munna suna wuce ko ina a gyare, dukda dai su talakawane amma sam hafsat bata kyamacesuba gidan nasu ya burgeta ko ina tsab, k'auyen ya bata sha'awa sosai, munna ta kawo musu abinci da fura dukkansu sukaci tare sannan sukasha fura, sabreen tace hafsat kinga gidan namu koh😉, hafsat tace wlh nikam gurin ya birgeni dasu yah suhail zasu yarda su barni in kwana se gobe in koma😊, sabreen tace ko'in tambayesu? Hafsat tace eh ki gwada😀, tafawa sukayi suna murna. Bayan su suhail sunci abincine sun koshi sosai se baban munira ya kaisu gun aminan mahaifan sabreen suka gaggaisa tare dayi musu addu'oi sosai, suhail da kamal sunyi musu alkhairai dewa sosai ga kuma kyautar kud'i, sunji dad'i sosai sannan suka kira su sabreen akan hafsat ta fito su tafi. Sabreen ne ta fito lokacin suhail ne kawai ajikin mota yana tsaye, ta karasa gunshi tace yah suhail dan Allah kabar hafsat ta kwana nan zuwa gobe seta koma, kallonta yakeyi sama da k'asa yace wazai maida ita goben? Sabreen tana kallonshi har cikin ido tace yah suhail base kazo ka d'auketaba gobe, suhail ya kauda kai gefe yace sabreen bata gayawa mum ba kuma skul fa? Sabreen tace yah suhail zamu kira mum yanzu kuma hafsat bata da class gobe pls ka barta mukwana😉, to sabreen hafsat bata rik'e kayabafa, ya suhail inada sabon d'inki nasan zai mata pls, ok shikenanto zan dawo gobe in d'auketa, 😃nagode yah suhail, shima murmushi yake mata mai cike da kauna yace sabreen me ma'anar (SABSU)? Sabreen zatayi magana kenan sega kamal da kaka🙊.

Sad-Nase cewa nayi "TANA RAINA"[10:00am, 12/9/2016] Sadiya Taheer: 🌺💐TANA🌹RAINA💕💞

By Mmn Shureim
(Sad-Nas)


61-62 Kamal ya k'araso gunsu shi kuwa kaka ya wuce, kamal yace to luv mu zamu tafi gaskya dan kar dare ya mana ina hafsat? Sabreen tace yah kamal hafsat zata kwana anan se gobe, kamal ya kalli suhail sega hafsat da munira sun fito, suhail yace eh ta kwana tunda tanaso, hafsat tace nagode yah suhail amma zanyi kewarka😒, kamal yace to tunda hakane kawai mu tafi, suhail yace karki damu zamuyi waya ai koh😊? Murmushi tayi tare da komawa gefensa ta tsaya suna shira. Kamal ya matso inda sabreen da munira suke tsaye yace munna pls ga amaryata ki kulamin da ita sosai banda yawan fita yawo sannan karki bari tayi kuka ko dai wata damuwa👏🏻, munira tayi murmushi tace insha Allah zan kula maka da ita sosai😊, yace tona gode sannan ya maida kallonsa gun sabreen yace "LUV" yadai naga kinyi shuru? Ta marairaice fiska tace tagiyafa zakayi ka barni😔, yace kiyi hakuri luv ai bazan dad'eba kinji😊, kai kawai ta d'aga suna kallon juna cike da so, munnira tace to nidai na shiga Allah ya kiyaye hanya, kama yace amenn nagode kigayar min da ango, 😀zaiji sannan tayiwa suhail sallama ta shige gida. Kamal yace luv yane? Tace babu, kin tabbata kodai bakyason na tafine? Shuru tayi kanta na kallon gefe, yace to muje na rakaki, juyawa tayi tace yah suhail Allah ya kiyaye hanya, ameen mungode kuka zakiyine naga kamar bakyaso ya tafi, murmushi tayi kawai batare datace komaiba tayi gaba kamal yanabin bayanta, shi kuwa suhail yanata binsu da kallo😟. A zauren gidan suka tsaya sabreen tana rakub'e a jikin bango fiskanta babu murmushi tace se yaushe? Kamal ya matso kusa da ita yace meyake damunki "LUV" pls bana son ganinki hakan, sabreen ta marairaice tace zanyi kewarka😒, dad'i sosai yaji yace nima haka my luv, amma bazan jimaba ai kiyi hakuri kinji? To Allah ya kiyaye hanya ka gaida mummy😊, ameen luv mummy zataji insha Allah tare zamu dawo dasu ai, kamal ya ciro emvalop a aljihunsa ya mik'awa sabreen ga wannan koda zaki buk'aci wani abun. Sabreen tace wlh ka barshi ni bani da bukatar kud'i nauyin daka d'auke manama ya ishemu wlh Allah ya saka da alheri, kamal ya riko hannayenta yace nasani ammadai sekin karb'a, uhm uhm wlh bani da wani abin saye, LUV banason haka ki karba nace seyasa mata a hannunta tace nagode😊. Hafsat ce tazo tace yah kamal waikaje ku tafi, kamal yace ok LUV byeee😉, sabreen tace bye Allah ya kare, yace ameen sannan ya wuce suma suka shiga gida.
Bayan sallan isha ne sabreen ta had'awa hafsat ruwan wanka takai mata bayi, pallen zani ta bata ta d'aura sannan tasa himar ta nufi bayin, shima tas yake simintine k'asan kumaga kamshin "IZAL" dayake tashi. Bayan ta fitone suma sukaje sabuwar rigan bacci ne sabreen taba hafsat suta hira har lokacin da angon munira yazo se suka fita dukkansu da himar har kasa sukaje gaisawa, hira sosai sukayi dashi gashi da son dariya yace dasu yagode sosai lokacin da sukace zasu tafi, sukace mune da godiya sannan suka wuce gida kowacce tana waya da sauranta. Munira ta dawo da ledan kaji da kuma juice, takaiwasu mama nasu sannan suma sukaci nasu suna yar hiransu da raha suna dariya😄. Washe gari da safe suhail yakai kamal airpot sannan jirginsu ya tashi se pakistan. Bayan suhail ya dawone seya wuce d'akinsa ya kwanta yana rungume da d'ankwalin sabreen har yayi bacci😴😒.


Sad-Nas
[10:00am, 12/9/2016] Sadiya Taheer: 🌺💐TANA🌹RAINA💕💞

By Mmn Shureim
(Sad-Nas)


63-64 Suhail ne a tsaye jikin mota sega sabreen ta fito tana murmushi tare da karasowa gunsa tayi hugging nashi hannayenta suna mak'ale a wuyansa suna kallon junansu cike da so da kaunan juna💗, kiss ya manna mata a lips nata yace shine kika shanyani ko, tace sorry kasan abinka da mai ciki se' slow tana shafar fiskarsa da hannayenta, yace sabreen koda yaushe k'ara shiga raina kikeyi wlh bansan daliliba duk randa nake tare dake se inga kamar rananne na fara kaunarki a raina, murmushi tayi wanda ya k'ara mata kyau tace nima haka "swt hrt" d'ina uban yarana😘 kiss mai zafi ta manna mishi a kumatunsa sannan ta shige kirjinta suka k'ank'ame junansu😋😋😋.
Mum ce tazo tanata nocking kofan suhail, a firgice ya tashi yana kallon d'akin nasa😟, wani haushi yaji aransa se yace na'am mum😔. Mum tace lfy kuwa kaketa bacci ko breakfast bakayiba gashi har 12:20pm kace zakaje ka d'auko hafsat, suhail yace wlh mum baccinne yamin dad'i ina zuwa, murmushi mum tayi sannan ta tafi. 😁😬 suhail shi kad'ai yasan meyaji a wannan mafarkin, yace mum dabakizoba k'ilama d'aki zamuje da sabreen d'ina mu farantawa juna rai, oohhh😁,seya koma ya kwanta tare da rufe ido yace pls mafarki kaci gaba daga inda na tsaya mezai faru daga wannan gun da muke rungume da juna? Ohh noooo mum why, dakin barini ai nad'an huta wlh😟, d'ankwalin sabreen ya tsunbata yace dukda dai nasan mafarkine amma naji sanyi a raina sabreen, kuma kaunarki ta dad'u a zuciyata I LOVE YOU SO MUCH SABREEN😨😨
[10:01am, 12/9/2016] Sadiya Taheer: 🌺💐TANA🌹RAINA💕💞

By Mmn Shureim
(Sad-Nas)


65-66 Bayan yayi wankane ya shirya tsaf, bayi breakfast sannan ya wuce kauyen su sabreen ciki da tunaninta a ranshi harya isa. Wayan hafsat ya kira tace to suna zuwa, basu jimaba suka fito dukkansu sunyi wanka sunyi kyau😘, tunda suka fito suhail yake kallon sabreen a sace yana maganan zuci😒inama da abinda ya faru a mafarkina zai faru yanzuma, sabreen ne ta katseshi da cewa sannu da zuwa uah suhail, mirmushi yayi yace yawwa sabreen ya kuke sukace lfy lau itada munira😊, yace ya mutanen gida, sukace lfy lau, sabteen tace ya mum? Uace mum lfyanta k'alau tayi kewarki, mirmushi tayi tace nima nayi kewarta wlh😊. Hafsat ta gaisheshi cike da so, ya amsa yana mata murmushi yace toya kwanan garin, tace wlh dad'i yah suhail kamar in sake kwana😜, yace to shikenan bari in koma😉, dariya sukayi dukkansu sannan yace kaka fa? Sabreen tace wlh sun shiga gari amma dai inaga sun kusa dawowa, ok yace sannan sukace bisimillah ka iso, yace a'a tfy zamuyi dama nazo d'aukantane. Hafsat tace yah suhail girki na musamman fa sabreen ta maka na dambun kuskus, suhail ya kalli sabreen yace to shikenan muje, gaba sukayi ita da munira suka barsu a baya har suka shiga ciki ya gaisa da mmn munna sannan suka isar dashi zauren baba. Wani yarone yazo yace wai ana kiran munira a waje, munna tace to kaje kace ina zuwa, sannan tace hafsat abbakar ya iso zomuje, hafsat tace ok muje sannan tace yah suhail bari inyi magana da angon munira akan shirin bikin ina zuwa, ok yace ta ita, azuciyarsa kuwa dad'i yaji yace zansamu inyi magan da sabreen. Bayan sabreen ta kawo mishi abincine seta zauna tana zuba mishi abincin yanata kallonta yana tuna mafarkinsa😊, yah suhail bisimillah ta ajiye mashi a gabanshi, murmushi yayi yace nagode sannan ya faraci suna kallon juna, wani sabon k'aunarshi ne yake shigan sabreen seta sunkuyar da kanta k'asa, suhail yace kunyi waya da abokina? Tace eh, yace gaskya naji dad'in wannan dambun nagode sosai, murmushi tayi tace akwai wani a kula seka tafi dashi, yace a'a ina kunyan mama, dariya tayi tace wlh bakomai dama nasamaka dewa dan nasan mum ma tana so, yace to shikenan sabreen? Tace na'am batare data kalleshiba, yace menene "SABSU"? Tace zan turo maka da ma'anarsa a waya, yace noo nidai ki gayamin anan, tace to ina zuwa sannan ta koma d'aki ta d'auki wayanta ta mishi texs.
"SABSU" yana nufin sabreen nd suhail, tunda bazan samekaba wannan suna zai zauna a raina har abada kuma dashi zan dinga kiranka a raina😔😔.
Bayan suhail ya gama karanta texs d'inne seya tsunbaci texs d'in nata tare da rufe idanunsa yana mai tausayamusu dukkansu😔. Da sauri ya mayar da phone d'insa aljihu danyaji shigowar hafsat gidan, gunsa ta wuce tace kayi hakuri yah suhail nabarka kai kad'ai yace bakomai ina abbakar d'in? Hafsat tace yana waje yana jiranka dan munce mishi kana cin abinci. Suhail ya mik'e yace mujeto nagama, tare suka fita yayiwa mama sallama alokacinne sabreen ta goge kwallan idonta ta fito tace yah suhail har zaka tafi😊, zan tafi sabreen sannan suka fito dukkansu. Bayan sun gaisane sukayi hira sosai kamar sunsan juna sannan sukayimusu sallama sabbreen taje ta d'auko musu kuskus din suka tafi suna kewar hafsat itama haka.[10:01am, 12/9/2016] Sadiya Taheer: 🌺💐TANA🌹RAINA💕💞

By Mmn Shureim
(Sad-Nas)


67-68 Da daddare munna da sabreen suna d'aki suna hira ce munna take cewa ayyah har yanzufa suhail yana sonki wlh kinga yadda yaketa kallonki asace kuwa, nikamma har tausayi yake bani wlh. Sabreen tace hmm toya za'ayi munna nidai har ga Allah bason yah kamal nakeyiba, kawai dai zan aureshine kodon hafsat dan tana son suhail sosai kuma kinga hafsat mutumiyar kirkice Allah ya tabbayar musu da alkhairi, munna tace ameen sannan suka kwanta ko wacce tana waya da mijinta.
Bayan sabreen sun gama waya da kamal ne seta kira yah suhail, bai d'aukaba seya sake kiranta ta d'aika hello yah suhail kun isa lfy? Yace lfy lau ya muka barku? Tace lfy lau na kira hafsat shine nace kaima bari na kiraka inji, yace eyuah tnx, yace yo seda safe, suhail yace sabreen? Tace na'am, yace sabreen inaga lokaci yayi da zamu hakura da juna, na amince zan auri hafsat kema kuma ki koyi son kamal a ranki pls tunda kinga yanzu lokacin bikin ya kusa😔, to yah suhail insha Allah, kuma nagode Allah yasanya alkhairi😰, uace ameen by... tun bai gama cewa byee d'inba sabreen ta katse wayan tana ta kuka😭. Munira ta juya tana cewa haba sabreen pls ki dena kukannan, sabreen cikin miryan kuka tace munna kibarni inyi kuka kefa wanda kike so zaki aura shiyasa bazaki gane me nakejiba😰, munna tace sabreen toki fito fili ki gayawa kamal d'in mana, sabreen tace munna da zan iya da tuni nayi hakan, amma bazan iyabane😭😭😭 Munna zatayi magana kenan wayan sabreen ya fara k'ara, minna ce ta d'auka don ganin suhail ne yake kiranta, hello suhail munna ce, suhail yana jiyo sautin kukan sabreen yace munna sabreen d'in fa? Munna tace wlh gatanan tanata kuka babu irin rarrashin daban mataba amma taki tayi shiru, suhail yace bata wayan pls, munna tasa mata a kunne suhail cikin sanyin murya yake magana, sabreen dan Allah ki dena kuka bawai dan nadena sonki bane yasa na fad'a hakan kawai dai naga babu yanda zamuyine shiyasa na fad'a miki hakan dan abin ya fita a ranki kafin bikin kin saba, amma ki sani har abada "KINA RAINA" babu abinda zai canja ta b'angarena domin ina miki k'aunar da banayiwa kaina sabreen I LUV U😰 pls kidena kukannan don har cikin raina nake jinshi😔. Sabreen ta tsagaita kukanta tace I LUV U TOO YAH SUHAIL, I LUV U SOO MUCH😭, suhail ya share kwallan fiskarsa yace "ok then stop craying pls SABSU" ya manna mata kiss😘 har cikin kunnenta taji, shuru tayi tana share hawayenta seta kira sunanshi a hankali SUHAIL, yace "yes" SWEET HEART😥, idanunta ta rufe😔 taji dad'i sosai dajin sunan daya kirata dashi tace pls yah suhail karkayi aure dan Allah😪, yace bazanyiba "SWEET HEART" nayi miki alk'awarin bazanyi aureba harse lokacin da kikace min kin fara "SON" kamal😔, dad'i taji sosai😊 tace "thankyou" yace wlcum "SABSU" tokiyi bacci pls karki sakeyin kuka kinji😊? Naji kuma nagode😊 byee, yace ok byee💕. Munira da tuntuni take kallonta cike da mamaki🙄, sabreen ta murgud'awa munna baki😚 sannan ta kashe wutan d'akin taja bargo tarufu😴. Munna tace hmmm sabon salo, tomudai namu ido 👀.


Sad-Nas
[10:01am, 12/9/2016] Sadiya Taheer: 🌺💐TANA🌹RAINA💕💞

By Mmn Shureim
(Sad-Nas)


69-70 Washegari da safe munira da sabreen suna karyawa se munira take cewa jiya kince Allah ya tabbatarwa hafsat da suhail alkhairi, sannan kuma naji kina cewa karyayi aure mekike nufu kenan? Sabreen tace ina ruwanki, dama ashe kunnenki nagunmu😙, munna tayi dariya tace mude namu eye👀.
Lokaci se tfy yakeyi kamal da mummynsa da kuma mijin mummynshi wanda suke kira da "UNCLE D" suna ta shirye shiryen zuwa biki, tare da abokansu na pakistan d'in. Gidan kamal da yake nigeri an sake gyarashi an canja komai na gidan d'akin sane kawai ba'a canjaba, dan bai dad'e da canjashiba, guri yayi kyau sosai abin se wanda ya gani😊. Mum kuwa tana ta shirye shiryen zuwan su mummyn kamal, hafsat kuwa tana can gurin su sabreen suna nasu shirin harda salma. Munira dad'i sosai taji wai yau gata ga aljana suna ta shirye shiryensu cikin kwanciyan hankali, itama sabreen ta sake jikinta anata mata gyara sosai😘. Su kakama dukda dai kamal tace baya bukatan suyi komai amma sunyi mata garan abinci sosai da kuma kayan sawa masu tsada. Gidansu Abbakar d'in munirama shiri sosai sukeyi abindai seni (SAD-NAS) danake d'auko muku rahoton😎
Shi kuwa suhail yana can yana gudanar da nashi shirye shiryen dan ganin bikin AMININSA da kuma SABSU d'inshi yayi kyau, dan shi kansa baisan adadin kud'in dayake kashewaba. Yau laraba ne su kamal suka shigo nigeria inda suhail da sauran friends nasu na nigeria sukaje d'aukosu. Hotel mai kyau suka sauk'esu da kuma UNCLE D, ita kuwa mummyn kamal tana gidansu suhail agun k'awarta mum. Bayan sunci abinci sun watsa ruwane se kamal yace to nidai zanje inga amaryata dan nayi missing d'inta😍, dukkansu suka kama hanya su 8 se k'auyen su sabreen🚘.
Kwaliya sukayi sosai amma ita sabreen light make-up hafsat tayi mata sunyi kyau sosai suka fito😘. Kamal dad'i yaji sosai kamar yaje ya rungumota😁, shi kuwa gogan naku SABSU murmushi kawai yakeyi a fili kome yakeji a zuciyarsa kuma oho😔😒. K'arasowa sukayi tare da sallama, angwaye suka amsa sallamar sannan su gaggaisa sabreen tana jin kunya😉. D'aya daga cikin angwaye se kallon salma yakeyi🙄, ita kuwa matsowa tayi kusada suhail tace nasan dai kaine suhail koh? Suhail yace eh nine😊, tace hafsat ta damemi da suhail tin d'azu😊 to Allah ya sanya alkhairi, suhail yayi murmushi yace ameen. Salma tacewa kamal to ango nidai zan tafi amma dai zan dawo, kamal yace to mingode bari a saukeki, salma tace a'a wlh ana jirana a bakin titi, suhail yace dukda haka dai zamu kaiki bakin hanyan to kodon addu'an da kika mana😉, hafsat tace to shikenan sannan tacewa su sabreen sena juyo🙋🏻, suma hannun suka d'aga mata sannan suhail tace SADIQ shiga muje, salma ta shiga baya suka tafi suna d'agawa junhannu🙋🏻. Tun kafin su k'arasa suka hango wata farin PRADO tana tsaye a gefen titi. Bayan sun k'arasone se wani kyakkyawan saurayi fari tas dashi wane balarabe ya fito ya k'araso gunsu tareda yimusu sallama ya mik'awa suhail hannunsa mai sanyi kuma mai laushi suka gaisa yana mishi murmushi😊, sannan suka gaisa da sadiq. Salma ta Matso kusa dashi ta gabatar mishi da suhail da kuma SADIQ sannan suka tafi, su suhail ma suka tafi suna yaba saurayin😎.


Sad-Nas[10:01am, 12/9/2016] Sadiya Taheer: 🌺💐TANA🌹RAINA💕💞

By Mmn Shureim
(Sad-Nas)


71-72 Kamal dai se kallon sabreen yakeyi ya kasa ce mata komai😊, hafsat ce tace yah kamal yadai ai kallon yayi yawa😉, se'a lokacinne yace to ai na kasa d'aga idona daga kantane😘. Munira tace to bari mi baku guri zamu tattauna da abokan ango, kamal yace wifeynah zonan mana😍, gefensa ta koma ta tsaya abokinshi mai suna ALIYU yace wifey tun daga yau? Kamal yace kun samin ido fa wifey zomu zauna a mota😜. Motan ua bud'e mata ta shiga sannan ya rufe shima yaje ya shiga, sukuwa sunata hira abinsu. Sabreen tace sannu da dawowa uah kamal😉, yawwa "wifeynah" yanaga kin ramene, sabreen tace hidima mana, yace kodai kina missing nane😃? Mirmushi tayi tace eh harda shid'inma, dad'i yaji yace kinyi kyau fa sosai😘, nagode tace dashi ina mummy? Mummy tana gun mum, gobe zasu kawo kayanki😉, murmushi kawai batace komaiba, yace kaka fa? Tace baiyi nisaba yanzu zai dawo, ok bari yazo mu gaisa semu muce wlh agajiue nake, kallonsa tayi tace sannu😊, tabbas sabreen tayi missing d'in kamal sosai. Kamal yace gaskya suhail yayi k'okari sosai wlh Allah dai ya biyasa da gidan aljanna, sabreen tace ameen yah kamal zan shiga gida, meyasa kodai rowan fiskannaki kike min? A'a dai ni kawai inaso in komane☺, kallonta yakeyi cike daso yace to muje😊, tare suka bud'e motan suka fito daidai lokacin su suhail suka iso, tare da kaka da baban munira dan sun had'u a hanyane se suka d'aukosu. Su sabreen gida suka wuce sannan kaka ya iso dasu ciki suka gaisa aka kawo musu abinci sunci kad'an sannan sukayi sallama suka fito. Su hafsat suka fito musu da peppe chikeen da dambun kuskus wai nasu da kuma nasu mummy. Dad'i sosai kamal yaji dan dama ta tambayeshi me mummy tafi so yace mata kuskus. Sabreen ta fito tayi musu godiya da Allah kiyaye sannan suka tafi.
Washe gari ran alhamis shine ranan walima, da sassafe suhail ya kawo mata Mayan da zatasa a biki wanda shiya saya da kudinsa. Itada hafsat suka fito yaso yayi magana da sabreen ita kad'ai amma hakan baiyuba, godiya tayi sannan yace su mum zasuzo kawo kaya yanzu, dan haka nina tafi semunzo d'aukanku walima kodai akwai wani abune? Hafsat tace eh muna buk'atan d'an kud'kad'an😉. Dad'i suhail yaji yace jeki dash bord ki d'auko min kud'i, bayan hafsat ta tafine suhail yace SABSU nah ya kike, sabreen tace ina cikin damuwa yah suhail, suhail yace ki kwantar da hankalinki pls "KINA RAINA" har abada SABSU😰, sabreen zatayi magana kenan Sega hafsat😷, kud'in ya karb'a yace nawa kuke buk'ata? Hafsat tace 30k ma yayi, 50k suhail yabasu yace toni na tafi su kamal suna jirana, to mungode sannan ya tafi yana sauri.

Please Login or Register in order to submit comment