Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

GORAN DUMA
Na Maimuna Idris Beli.
Ebook Publish by http://hausaebooks.cf

Izan kuna bukatan wasu litttafan sai ku ziyarci shafinmuu na yanar gizo akan adireshi
http://hausaebooks.cf
Farkon littafi.

.
.
Rumaisa'u wankan tarwadar mace matsakaiciyar tsawo
da kiba, fuskar ta nada alamun hakuri da sanyin hali a
wajen wanda ya karanci mata, amma mai rashin matsaya
ga mutumin da ya cikawa kansa zargi a cikin mutane
saboda rashin son maganar ta da karancin fara'ar ta.
Ta na xaune a matsakaicin palon gidan su ita kadai, a
tsakiyar palon bisa kapet tayi kaca-kaca da takardu. Ga
wayoyin ta da na'urar kwanfuta(laptop) dake kapet, ga
kuma robar ruwa da kwalin lemo a gepe.
Wannan yasa ba sai an padi ayyuka ke caja gabban ta
wanda fuskar ta da gabban suka kasa nuna gajia, watakila
dan juria da son aikin har zuci.
Can daya daga cikin wayan ta dake zube ta saki wata
siririyar kara amma abun mamaki duk da haka sai ta
firgita, ta dubi wayar da sauri kuma a tsorace xuciar ta na
bugawa, duk da haka ta latsa sakon ya pito.
A pili cikin ta Ya bayar da wani kuuu... Har sai da ta dan
rankwapa na alamar ba a karar ya tsaya ba har da haipar
mata ciwo.
Ga abun da ke rubuce a cikin wayar '' yaushe ne kika
shirya barin nunpashi na ya huta?
Duk yadda kike jin aiki da dawainiya a rayuwa bana jin
kin kama kapa ta, amma kin san wani abu?
Mamakin yadda kike share al'amra na ma wani tapkeken
babi ne a kundin da na ware miki, wanda ko wannan
babin aka barni dashi ya isa abin wahalar da xucia.
Rumaisa'u bayyana min siririn ki wanda ya rike ni na kasa
ampani da Karpi wajen maganin ku ke da zucia ta!
Ware min ko sakan goma ne daga lokutan ayyukan ki kiyi
min wannan aikin Rumaisa.
Daga MAHAUKACIN MASOYI.
Tayi wurgi da wayar kamar wadda ta galla mata cixo a
bayan ta, bayan ta kammala karanta sakon, tana satar
kallon wayar, san nan ta koma satar bin palon da kallo,
musamman jikin labulaye, harshen ta pal ambaton
Hasbun Allahu wa ni'imal wakil, ta dora da padin '' A uzu
bi kalimatuLlahi tammat min sharri makhalak ''
Duk illahirin gabobin ta sunyi sakayau, babu nauyi
tamkar idan an yanketa jini baxai bullo ba saboda tsoro
da wasi wasi
Tsawon piye sati hudu kenan tana pama da sakonnin
wanda ke Kiran kansa da MAHAUKACIN MASOYI mutun
da a yanxu ta para shakkar mutun ne ko aljan, mutun da
aljan din na xahiri ko kuma ifiritai ne (hackers) suka
hauro layukan wayoyi kamar yadda akan same su a yanar
gizo?
Cikin zarginta uku kowanne ta canka babu dama a cikim
sa, in mutum ne ta wanne bututun yake hango halin da
take ciki a lokacin da yake turo mata sako?

Kamar yanzu da yayi maganar cakudewar ayyuka.
Idan aljani ne ma wani bakin tashin hankalin ne dan babu
ta inda aka gwamutsa mu'amalar mutane da ta aljamu
bare har a gayyato musu batun soyayewa a irin haka.
Zargin 'hackers' din ne ma mai dam sauki wai idan ta
kawar da kai ga rashin yawan bayyanarsu a layukan waya
ta wannan sigar, ko kuma lissapin nemo manuparsu a
kanta da suka dame ta ita kadai...
Wata dattijuwar mace para mai tsawo da kiba , tayi
sallama ta shigo palon, da sauri rumaisau ta gyara sahu ta
hadiye maitarta ta amsa sallamar matar, purkarta da
gabobinta suka nuna ladabi, tana murmushi ta amsa
sallamar matar mai alamin zapin nama ta dubeta tace,
'' Rumaisau ki saki aikin nan ki huta haka,ga pura mai
kyau can Alhaji ya shigo da ita, kije ki dama kisha...
Rumaisamu tayi kokarin tattare tashin hankalim da take
ciki tabawa cikin ta ajiyarsa, ta tare matar da rawar
murya dake kokarin komai ya zama ba komai ba,
''Oh Abba ya shigo Hajia?
Hajia tayi murmushi ta amsa mata tun da hamida ta bar
mu gidan ya zame mana kamar hurumi, kirikiri alhaji ke
nuna pipiko tsakanin mu, ni kaina sai na zage nake sanin
shiga da pitar sa.
Rumaisau tabi wayar ta da kallo tana murmishin hadawa
zuciyar ta ayyuk biyu, tunanin gudan jinin ta Hamida, da
kuma tausayin ta a matsayinta na mace mai rauni, wanda
kuma zata tsaso kila cikin ratuwar da tapi tata wadda take
tapia a cikin ta yanzu muni. Sai kawai taji hawaye na son
cika mata ido, amma ta dage ta dadiye, ta cewa hajia '' to
hajia wannan dai tsakanin ku ne''
hajia ta bar amsawa Rumaisau maganarta tabi ruwa,
saboda damum kanta da nazarin rumaisau'un da take
sonyi wanda puskar ta ke son karyata abun da zuciyarta
ke kokarin bayewa, amma data hada nazarin nata da
wasu daban sai ta yi saurin sharewa gudun batawa kai
lokaci, ta jima da sanin rumaisa duk inda ake neman
mutun mai kawaici ta cika mizami, mawuyacin abu ne
kaji korapi a bakin ta duk yadda ka kai ga kwarewa hilarsa
wani ya amayar da abun da zuciyarsa ta boye.
'' baki da bukata ko ta neman addu'a ce daga gare ni!''
hajia ta sami kanta da furta wa rumaisau cikin tsura mata
ido, sai rumaisaun ta dan diririce saboda pargabar ko tayi
wani abu da ya dago halin matsin da take ciki. Ta hau
hada takardu tana cewa '' hajia kiyi min izinin gobe na kai
rubutun nan abuja nayi submiting.
Hajia taci gaba da kallon ta, kallo mai cike da tuhuma. ''
rumaisau kwanan ki nawa da zuwa Abuja kuma tunda
kike rubutun nan kin taba kai shi takanas?
Ji nake ta Email kike tura musu?''
a ladabce Rumaisau ta shiga kokarin kare kanta.
''akwai matsala ne hajia, kinga ban gama bugawa ba
kuma ka'ida gobe laraba mujallar ke pitowa. Ba wai lallai

ya zama sai nakai din ba,amma dai ina neman alparmar
zuwan hajia saboda muhimmanacin rubutun''
hajia tayi siririyar daria tana ci gaba da yi mata wani irin
kallo, wanda rumaisau ta kasa daurewa har sai da hajia ta
ci gaba.
Ko dai alkunyarki ke son gazawa ba zaki iya rashin
Hamida ba ko?
Ni dai abun da zuciata ta karantar dani ke nan,
da sauri rumaisau ta tareta cikin zaro idaon bijirewa
batun hajiyar tace ''ah! Hajia to na pasa zuwa tunda kin
zargi hakan..
Wallahi ko kadan ba dan hamida zanje ba hajia.
Nan da nan hajia ta tareta da na yarda daje rumaisau zan
kuma sanarwa Alhj amma da sharadin zaki tashi yanzu ki
nemi wani abu kisa a cikin ki.
Cike dq jin dadin kulawar da hajia take mata ta yalwata
para'arta da murmushi tace "ai na bari tuni
tun bayan pitar hajia ta janyo wayarta a gajiye tankar
wadda tayi gudun shekara ta kasheta, ta jepa akan kujera
samnan ta pice debo purar da hajia ke mata tayi.
Ta kori hataniya da rudin wannan duniyar da tilastawa
kanta shan purar sosai har ta gamsar da ita,
tayi wamda ta sallaci Isha'i, sannan ta zauna azkar din
yammaci da bata samu damar yun sa a kan lokaci ba, sai
tayi shi a yanzu tana mai nutsuwa da kaskantar da kai ga
Mahalicci.
Abin da ya karpapa mata gwuiwar isa gadon baccinta da
wuri tare da tsammanin zatayi barci a nutse shine a zacin
da tayi na kashe waya tare da yunkurin barin kano a gobe
dan ganin gudun ruwan MAHAUKACIN MASOYI , wayar
da yake kiran ta ta kashe, garin kano idan ma kyamarar
sirri (CCTB) ya makala a garin to ta bar shi, cikin kwana
biyu kuma sai ta gani ta ina zai leko ya rikitata?
ABUJA
karpe biyu da rabi na rana ta pito ofishin da jaridar
Aminiya dake jabi da komawa masaukinta wajen Innarta
a anguwar wuse.
Duk a rikice take tun saukarta Abuja taji wata bala'in
rashin nutsuwa ya mamaye ranta har yake bayyana a
gabban ta, wayi ayyuka.
Misali. Tana sauka bus din da ta kawota garin a
matsayinta na wadda ta taho Abuja a gaggauce, dan zuwa
opis maimakon ta dauki shatar motar da zata kaita Jabi
kawai sai ta buge da daukar wadda zata kaita gidansu
Wuse cikin wasiwasi,
a cikin tadi din ne ta budo naurarta mai kwakwalwa ta
lalubo rubutunta tana nazari da shawarar ta tura shi
kawai ta Email din ta wuce gidan ta kwanta,
anan kuma ta lalubo Moderm dinta cikin jakar sai ta tarar
ta baro shi a kano, nan take ta yanke shawarar tsayawa
wani kataparen kantin harkokin sadarwa da ke nan titin
da zai sada ta da wuse daga Utaho kawai, ta tsaya anan ta

tura rubutun,
ana isowa Annur ta yiwa direba umarnin ya tsaya anan ta
shiga ta pito.
Ta kwashi i laptop tayi ciki , kataparen waje mai kamar
komai da ruwan ka a bangaren sadarwa, wayoyin hannu ,
layukan waya, katin wayam kwanputa da sauran tarkacen
da suka dangance ta,
modem din da ta baro a gida ma wancan zuwan nata ta
saye shi anan,
haka dai gurin yake bangare bangare ko ina da abubuwan
da ya kunsa.
Yau tana shiga bangaren cafe ta tunkara, amma kamar
wadda tazo daga kauye duk kaparta rawa take sai
sassarpa take har ta isa inda ta nupa.
Ba wani abu ne ya janyo hakan ba sai gain yadda kamar
kowa a wajen ya zuba mata ido ne,
da yake yawancin katangar dake tsakanin bangarorin ta
gilas ce, kamar duk ma'aikatan wajen sun doro
hankalinsu akanta.
A gajiye ta karasa wajen ta zube a kujera tana
numparpashi tamkar wadda tayi gudun pampalaki, ta yar
da jakar naurar gepe ta zube wayoyinta akan tebur,
mai kula da bangaren ya dago kansa daga printer da yake
zaro wasu takardu yayi mata wani kallo shi ya tsinke
tunanin ta,
ta shiga zargin ko wani mummunan abu ne a jikin ta da
mutane ke binta da kallo haka?
A dabarance ta para nazarin shigarta , tana sanye ne da
bakar after dress mai sheki da abon shudayen kananan
dumatsu kalar riga da siket din material dinta na ciki,
kanta nade shi da mayapin rigar kuma da yake ba zata iya
putowa a haka ba sai ta kara da nade kapadar ta da
lallausan mayapi mai matsakaicin girma shi ma shudi,
jakarta da takalmin ta duk shudaye , idon ta sanye da
siririn parin gilas,
a zatonta ko ba ganin idon ta ba, ganin idon kowa ma
babu kauyanci ko digo a cikin shigarta,
duk da haka bata gamsu ba sai ta saci ido ta bude jaka da
sunan lalube ta kalle puskarta tsab ta cikin jalar komai
pes hatta hodar puskarta da man lebe (wetlips) babu abin
da ya gigita su.
Ta zuge jaka tana sauke ajiyar zucia cikin tsananin tashin
hankali wanda ya karu lokaicn da ta lura mai wajen ya
kapa mata ido ya pada da karpi laa kamar barauniyar da
tazo tayi sata jiya... Lol.
.
GORAN DUMA 2
.
.
Ta zuge jaka tana sauke ajiyar xucia cikin tsananin tashin
hankali wanda ya karu lokacin da ta lura mai wajen ya
kapa mata ido kamar barauniyar da tazo tayi masa sata

jiya yau ma ta dawo.
Sai bakin su ya hau rawa shi da ita.
'' madam... Madam.. Me kike bukata?
Ita kuma tana rawar bakin cewa don Allah... Zan tura
wani aiki... Ta na'urar kwanputa, ta me zan tura...
Bai iya amsa mata ba sai gyada kai kawai yake kamar
kadangare yana kallon ta kai tsaye , hannunta sai
karkarwa yake ta parke jakar system dinta shi kuma da
sauri ya karaso ya tura mata foot stool waiko zata dora
kapa.
Da wasa ba zata dorar da abun da tayi a naurar kwanputa
ba, musamman da shi mai wajen ya dauki waya yana
magana da wani harshe da bata samshi ba alamunsa
kuma na nuna hankalinsa na kanta.
Ba a dauki ko cikakken minti daya ba sai ga wani matsashi
ya shigo mai matsakaicin tsayi da kaurin jiki puskarsa na
da alamun para'a amma a halin yanzu kai tsaye ba za a yi
masa passara ba , ya nemi guri ya zauna bayan sun gaisa
da mai kula da wajen sai ya nemi kujerar da ke
puskantarta ya zauna yana satar kallon ta, tana latselatsen
keyboard,
can tayi namijin kokarin dagowa suka dubi juna ido cikin
ido shi ya kawar kamar a razane ita kuma ta hade puska.
Ta nuna masa TV plasma dake makale a sama tace.
'' bawan Allah kaga abun kallon can.'
yayi pirgit ya dubi talabijin din sannan ya dube ta
muryarsa na rawa yace ina... Patan dai ba tsarguwa kikayi
ba?
Ya mayar da kanta rai a bace tana matsawa siririn
hancinta hura iska. Alamar dai haushin ta ji, amma bata
tanka ba.
Shi ma ya kawar da kai yana cewa batawa kai lokaci ne
kayi abun kallo kace baza a kalle ka ba.
Ta dago da sauri ta dube shi amma ba ita yake lallo ba
balle ko a puskarsa ta karanci abun da yake nupi. Ta
kokarta tace ko?
Ya juyo cikin kada kai haka nace. Saboda haka kallon naki
yapi kallon wannan akwatin da kike nuna min kaye...
Yanayin yadda yake magana duk kwakwalwarta ta kasa
gane inda ya dosa , puskarsa babu walwala bare ayi
zargin irin mazan nan ne masu latselatsen yanmata.
Tsam! Sai ta tattara kwanputarta ta mayar a haka ta zuge
jaka tana cewa bari na bar muku wurin ko? Kila kuyi abin
da zai ampane ku, dan kallona babu ma'anar da zai baku..
Malam nawane kudina?
Ta mike rataye da jaka tana duban mai wajen ya girgiza
kai kamar a darare me kika yi na kudi? Kije kawai .
Ba ta ko tanka ba ta juya ta pice kaparta na hardewa
kowa na damuwa da kallon ta har ta pice cikin sassarpa.
Bata sami direban da ta bari cikin mota ba, sai kawai ta
rungume hannu ta jingina da motar cikin rudani tana
zuba idon ta inda zai billo.

Cam sai gashi da mujalla a hanu cikin zapin nama ya
bude motar yana neman apuwar ta , ta hango wannan
gajeran mutumin da yake kallonta yapi talabijin yana
doso inda suke.
A hanzarce ta cewa direna sauri mubar wajen nan, cikin
direba ya dauki wani kugi da yasa shi kasa bin umarninta
yanayin yadda tayi maganar ya sa yayi zargin babu gaskia
a tare da ita, tsoro ya ke ko wani abun ta sato tasa shi
taka sawun barawa.
Yakai ta ya sauke lambar motarsa kuma ta shiga kundin
masu laipuka. Saboda haka kawai sai yaki tapia har
gajeren mutumin ya karaso ya mika mata wayoyinta ta
windon motar.
Madan sanyin AC wajenmu ya sabbaba miki mantuwa.?
Ta karba tana mayar masa da raddi haka ne musamman
da yake daga kauyen mahudar rana na pito ba.
Ya juya ya koma da karamin murmushi a puskar sa.
''Allah ya baki hakuri idan gaskiar tawa zapi tayi miki.
Direba yayi ajiyar zucia ya tashi motar yana cewa kinga
gara ma da muka tsaya. Ko kala bata ce masaba har suka
hau titi, sanan tayi masa umarnin ya kaita opishin jaridar
Aminiya kai tsaye ta gyara shirmen da tayi. Acam kuma ta
watsar da dimuwarta tayi abin da ya kamata, karpe biyu
da rabin nan ta pito da dokin zuwa gida don samun
nustuwar zucia amma dai ta san wahalar da kai ne dan
gaba daya tsarge take, sai kissipawa kanta take wani na
biye da ita, bata jima bakin titi ba ta samu mota kuma da
yake tsakiyar rana ne titin babu cunkoson ababen hawa,
sai nan da nan tapiyar tayi musu sauri suna kan Berger
flyover kiran innarta ya shigo wayarta da ke kunne ta dag
cikin muryar ladabi tace Momi ina hanya kusa da isowa
tana sauke wayar sai tabi ta da sabon sako hankalin ta
kwance ta bude shi, dan a amintacciyar wayarta sakon
yake, wayar da bata taba hadata da gigitaccen sakon
Mahaukacin masoyi ba, saboda haka karsashinta ta para
karantawa.'' Rumaisau garin Abuja ni'imtaccen gari ne
ma'abocin dauke kewa da gadar da nutsuwa tankar
yadda salihar puskarki take, amma yau na shiga rudani
da nake ganin puskarki da ayyukanki a gigice.
Kila kin halarci Abuja ne bisa radin kanki ban kuma cire
tsammanin dan ki samarwa kanki nustuwa bane, amma
yaya kika hana zuciyarki da gangar jikinki hakan
Rumaisa?
Laipin me wayarki tayi kika kashe ta?
Inajiran amsa.
naki MAHAUKACIN MASOYI.
A Uzu bi kalimatuLlahi Tammat min sharri ma khalak.
Wannan adduar ta karabto tana juya wayar duk da kuwa
tayi mata nauyi a hannun, a yau kam taji a ranta ba
bil'adama bane mahaukacin masoyi ba, kuma ba hackers
bane duk yadda ake yi yana daga shaidanun aljanu da
zata tashi tsaye neman tsarin Allah da shi

har ta shiga gida cikin wannan ruwanin biyu take na
mahaukacin masoyi da kuma na son canko dalilin da
yasa ta zama madubin mutane a yau.
Bakinta da Ayatul Kursiyu har da wattaba'u ta shiga gidan,
innarta ce kadai a palon tana mata marhabin amma sai ta
wayance da matsuwar shiga toilet, inda ta ajiye jaka a
palo cikin sauri ta shige bandaki.
Tayi tsaye gaban katon madubi tana kallon kata daga
sama har kasa iyakar ganin da kwakwar juya bayanta ta
kallo bataga abun kushewa ko abun kayen da za a damu
halittarta da kallo haka ba, wannan yasa taji tausayin
kanta ya mamayeta, duniyar nan kamar ba ta karbeta ba,
duk inda ta shiga sai rayuwa ta zame mata kwado, ta rasa
abun da take so ko kubucewarsa in ta samu, ko kuma
puskartar kiyayya daga wanda rayuwa ta yarda su rayu
tare.
Da kyar ta rarrashi kanta yayin da zuciyarta ta samu dan
wani sarari sakamakon jiyo kawar diyarda Hamida.
Tayi alwalar sallar la'asar ta pito palon innarta da mai
aikin dauke da kyakkyawa hamida yar kimanin shakara
biyu da rabi, sa'a mai aiki ta dire Hamida da sauri tana
cewa Yauwa tapi da gudu ki yiwa momi oyoyo.
Kamar Hamida ta gane manuparta ta tahi a guje ta tari
Rumaisau wadda kunyar idon tata uwar ya hanata tarar
hamidan, sai ta bige da rike mata hannu kawai, idon ta
akan sa'a tace.
Sa'a ta amsa. Muna ciki uwar dakina daga wasa jiyo
Hamida tayi bacci kawai sai kwantar da ita wajena.
Suka karasa kujera Rumaisau ta zauna tana yar daria,
yanxu wannan katuwar yarinyar kike goyawa Sa'a?
Sa'a tayi daria tace ai shi yasa nace miki wasan goyo. Duk
sukayi daria har innar Rumaisau wadda hankalin ta ke
kanta, tana yi mata wani irin kallon tausayi.
Sa'a ta mike tana cewa dan Allah dora yar nan a cinyarki
taji sanyi kin kama kin wani rike mata hannu kamar yar
awo, wannen abinci zan kawo miki?
Ba ni ruwan zapi kawai, wato ta share korapin sa'a a
parkon maganarta.
Momi ina wuni, mun same ku lapia?
Momi tayi murmishi irin na manya masu son karantawa
kai korapi tace lapia kalau rumaisau yaya ayyuka?
Taki duban momi kai tsaye saboda tsarguwa da tayi da
kallon da momin take mata ta amsa AlhamduliLlahi
momi, yaya Abba yana lapia?
momi ta amsa lapiyarsa kalau ya halarci taron karawa
juna sani a lagos sai jibi zai dawo ranar da zaki tapi
kenan, kila ki dan jira shi ko?
Tunda na san da sapiya zai dawo. Da sauri Rumaisau tace
ai na pasa kwana biyun gobe da sape zan koma...
Nan ma sai momi ta bita da kallon nazari amma sai ta
kasa cigaba da yi mata kawaici.
'' rumaisau kina tare da wata matsala ne?

A dan gigice Rumaisau ta para girgiza kai A.a momi, me
kika gani?
Kai tsaye momi ta amsa puskarki na nuna babu nutsuwa
a cikin ta, yakenki na nuna karpin halinki kawai, hajia ta
sanar min kwana buyi kika ce mata zakiyi, yanxu kina dira
kince da sanyin sapia gobe zaki tapi me ya kawo wannan
sauye sauyen ko kina puskantar wata barazana ne?
Rumaisau ta daddage ta bayyanar da karpin halin ta a
puskarta da muryarta tace babu komai momi, wani aiki
ne zai mayar dani kano a geben wanda ban san da shi ba
sai da nazo yau, momi ta rausaya kai gepe cikin saduda
ba tare da rai ya so ba tace ai shike nan idan hakane
wannan aikin ba karami bane kamar yadda kika pada
mana kapin para shi, in dai kuwa ojan-ojan din tapiyetapiye za su dinga padowa cikin sa ai yapi karpin karami
rumaisa u...
Rumaisau ta tare innarta da daria mai sauti. Momi bai
canja ba daga yadda na pada muku ni dai kuci gaba da yi
min adduar patah alkhairi a dukkan al'amurana sanyaye
momi tace shikenan Allah Ya yi miki albarka, Ya yi miki
katanga da kuncin dunia dana alkiyama.
Cikin murna da parin ciki ta amsa da Aamiin na gode.
Momin tace da ita to dauketa taji duminki mana wata kila
ma kewar ganinta ya kawo ki..
Raimaisau ta sa hannu ta dauki Hamida tana daria tace
zolayata kawai kike momi yarinyar da ta pi sonku dani
zan batawa kaina lokacin zuwa ganinta takanas?
Suna daria su duka Sa'a ta shigo da parantin kayan ruwan
zapi.
25/12/2012
ratar kwanaki goma sha hudu aka samu da zuwanta
Abuja cikin kwanakin nan duk yadda mahaukacin masoyi
ke son muna mata hatsabinbancinsa ta hanyar
sakonninsa ya muna mata kwarewarsa a wayoyinta biyu,
ta kala-kalar tsoro da hasashe babu wanda bata
gayyatowa zuciyarta ba har idan abun yayi tsamari sai ta
kashe wayoyi duk lokacin data kunna kuma shayar da ita
tsoro da mamaki a tsarin kalamansa.
Wannan pargaba da tashin hankalin suka dinga motsa
mata larurarta ta hawan jini da ta gamu da ita wasu
shekaru da suka wuce, abin boyewar ya zamar mata biyu,
wato boye barazanar mahaukacin masoyi da take
puskanta da kuma boye cutar da barazanar ke haipar
mata gudun kada ta tashi hankalin iyayen ta da
marikanta.
Cikin dabara take zuwa asibiyi ganin likita haka zalika
cikin dabara take shan magungunan ta,
akwai wani ciwon nata mai hadari da ta taba haduwa da
shi na rudewar kwakwalwa da gazawar wasu sassanta a
cam lokacin baya.
Paruwar wannan rudani da motsawar hawan jininta ya sa
likitanta ya bata shawarar ta rika kwantar da hankali da

bawa kwakwalwarta hutu saboda gudun motsawa
wancan ciwon.
.
GORAN DUMA 3
.
.
Likitanta ya bata shawarar ta rika kwantar da hankali da
bawa kwakwalwarta hutu saboda gudum motsawan
wancan ciwon.
Sanin girman hatsarin ciwon a tare da ita yasa take son
watsar da captar mahaukacin masoyi ta dauke ta miyar
da babu gishiri, amma sai hakan ya paskara wani lokacin
sai ta zabi kashe waya in ta kashe kuma sai ta rasa abun
dauke kewa ko sadarwa tsakanin ta da mutane,
30/01/2013
yau laraba da dare wajen karpe tara, ta gundura da
kallon talabijin sai ta dauko na'ura mai kwakwalwarta ta
lika modem ta hau yanar gizo kai tsaye ta nupi kapar sada
zumunci ta facebook cike da dokin shiga dandalin
duniyar marubuta da wata kawarta marubucia mai suna
kamshi ( Hawwa Abubakar Lawam maiturare) ta gayyace
ta.
Dandalin duniar marubuta na fb cike yake da daruruwan
marubuta da makaranta ana ta harkokin arziki tare da
kuma abubuwan karuwa da na nishadantarda, tana shiga
taci karo da wani rubutu da marubuci Muhammad
Lawan Barista yayi mai take '' zaman 'ya 'yana nake''
duk lokacin da wani sabani ya shiga tsakanin Mamuda da
matarsa Aliya sai ta bude baki ta ce masa Mudi nipa
zaman yayana nakeyi in bandan su ba Wallahi da tuni ka
manta da ka taba sanina,
abun na damunsa kwarai tun yana ji yana hadiyewa abun
a ransa yau dai ya yunkura ya sanar dani yana kuma jira
yaji daga gareni shin matar tasa tana sonsa kenan?
Kuma wane mataki ya kamata ya dauka akanta?
Ni dai ya rantse min yace babu wani abu da yake mata na
cutarwa sai dai ma tsabar kyautatawa ,wacce shawara ya
kamata na bashi?
Da dokinta ta shiga rubutun tana juya abun a ranta ''
zaman yaya kamar wata kalmar ado ce ko ta panshe
takaici a bakin mace lokacin da sabani ya shiga tsakanin
su da mazajensu, duk da

2 Comments On GORAN DUMA
avatar
jannat

1 year ago

Reply

08062236094

avatar
jannat

1 year ago

Reply

08062236094

Please Login or Register in order to submit comment