Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Tabbata
Bai tanka Ba Ya Kirga Dubu Goman Ya Zubemata Kan
Durowa Ya Kwashi Lesunan Yafice Sannan Ta Kwashi
Kudin Tajefa Ajaka Ta Kulle Gidan Ta Fice Sai Gidan Wata
Kawar Mominta Hajiyar Dubai Da China
Ta Kwaso Lesunan Bashi Ta Wuce Gurin Dinki Ta Bayar Da
Dubu Goman Yushau A Kudin Dinkin,
gidan Abokinsa Mai Kudi Ya Nufa Inda Matar Sa Tasha
Fada Masa Matsalar Sikila Da Bukatar Su Ayanzu Kam
Yanade Hannu Zaitafi Neman Iliminsa
Kaga Na Jaruma Sumayya Mai Zizar Sunan Sumoli,kaga
Mutum Na Musamman Wanda Kiyayyar Ruwa Kesashi
Kiba Soyayyar Sumoli Ke Sanyashi Rama,,
irin Wannan Kirarin Maikudi Abokinsa Kemasa Yushau
Kam Kasa Magana yayi.
Haka Dai Tazage Tana Bashi Bayanin Masu Ciwan Sikila
Saboda Sunadasu A Danginsu Inda Duk Wata Alama
Yushau Yaji Tafada Yanaganinsa Ga Ruma Hartagama
Yatafi Abinsa Tare Da Yunkurin Komai Zai Daidaita Tunda
Yagano Bakin Zaren,
*********
garin Rana Sosai Ruma Damai Adaidaita Sahunta Keke
Napep Suka Hau Titin Layin Gidan Atika A Unguwar
Hotoro Ruma Na Cike Da Dokin Akarasa Gidan taga Dangi
Taga Kuma Sabuwar Bakuwar
Dasuka Samu,dahaka Tadinga Binne Mahaukacin Masoyi
Da Matsalar Sa Koda Na Wuni Dayane Tall,wato Taje
Tadawo,basui Nisa Da Hawa Titinba Sai Ga Adaidaita
Sahun Ya Mutu A Titin,subhan Allahi
Kabiru Meyafaru??
Karfen Nan Yagaji Dani Hajiya Shekaran Jiya Fa na
Karboshi Daga Gurin Mai Gyara Inda Yacimin Naira Dubu
Ashirin Da Takwas Amma
Tunjiya Yafara Yimin Mahangurba,ruma Tadan Yi Dariya
Kalmarsata Karshe,ta Duba Agogo Taleko Kai Tana
Kokarin Hango Kabiru Wanda Yadawo Ya Shi Ga Turata

Gefen Hanya Inda Ya Tsayar Da Shi Gefen Wani Mota
B,M,W, Series 5 Wadda Ke Kafe Gurin Tun Kafin Keke
Napep Dinsu Takaraso Nan Dukda Akwai Dan Duhu
Gilashin Motar Ana Iya Gane Matashin Direban Dake
Kwance,mazauninsa Yana Sauraren Wakar The Power
Love,maitashi Kasa Kasa Daga Bakin Celine Dion,sama Da
Mintuna
Goma Ruma Na Cikin Adaidita Sahu Zafi Da Ciwon Jira Na
Dimarta Har Ta Kosa Tafito Ta Tsaya Akan
Kabiru Wanda Yake Tabe Tabe A Injin BaBurdin,haryanzu
Dai Kabiru?Wallahi Kuwa Tundazu Nake Faman Taremaki
Adaidaita Din Dazai Karasa Dake Amma Kinga Duk A Cike
Suke Zuwa,ikon Allah Tabi Titin Da Kallo Tana Rayawa
Aranta Inama
Zata Iya Data Karasa A Kafa Ta Huta Da Tsayuwar Ta Dora
Da Zolayar Sa To In Hakane Kuwa Zanbaka Hutu Tunda Ga
Ya Shirya Hadamu Yayimana Mahangurbar Tare Yau
Wannan Zafinda Ake Kwadawa Idan Ya Rikide Yazama
Hadari Yazubda Ruwa Fa?
Kabir Yafara Yunkurin Tare Wani
Adaidaita Dayashigo Layin Yana Amsamata Nima Haka
Nafara Tunani Ai Karshen Watan Nan Ma In Allah Yaso
Zan Sauya Yana karasowa Sukaga Ai Cike Yake Da Mutane
Ruma Ta Rungume Hannu Ta Ce Bar tarewa Ka Koma Ka
Lallaba Ko Zai Hakura Ya Bari Ka Karasa Dani,
Dukansu Sukai Dariya YakoMa Yana Tabata Mintuna Biyar
Tsakani Matashin Nan Ya Bude Motar Sa Yafito Ya Riski
Kabiru Baidamu Da Kallon Rumasau Ba Sam,kamar Yadda
Itama Bata Mayar Da Hankali Akansa,saida Maganar Sa
Taja Hankalinta
Ranka Yadade Meyasami Keken Naka Dazaka Shanyata
Arana Haka?
Abinda Kabiru Ya Kaddara Shine Ruma Tasan Matashin
Danhaka Ya Amsa Da Kar Sashi,tsautsayine Yallabai Kuma
Muna Ta Kokarin Tare Wanda Zaikarasa Da Ita Bamu
samuba,ya Dago Suka Gaisa Yacigaba Da Duba Injin
Din,sai Ya Bar Ruma Da Tunanin Ina Tasan Matashin
Saurayin Baki Mai Dogon Hanci Da Fararen Idanu,?
Bata Canka Ba,takuma Kasa Kojin Kunyar Kallon da take
Masa Bare Ta Hakura Cikin Faduwar Gaba Da Raunin
Zuciya Iri Iri,can Yajuyo
Yadubeta Duban Da Bai Nuna Mamaki Ko Tuhumar Kallan
Datake Masa Ba Yadago Ya Dubeta Aransa
Yana Mamakin Kota san shine Takemasa Kallo Haka
Yanuna Motar Sa Kinga Muje Inkarasa Dake, Tajima
Mamaki Yadda Yake Kokarin Bata Umarni Irin Na Yaya Da
Kanwa Amma Hakan Bai Hana Ta Daure
Gira Ta Cemasa Bisa Wace Hujjar,,?
Ragowar Maganar Tamakale A Makoshinta Bayan Tagane
Motar Data Dan Gifta Su Kadan Yanzu Ta Yushau Ce Kuma
Da Alamu Ya Ganta Dan Gashi Can Yana Kokarin Samun
Guri Ya Tsaya Nantake Taji Haushi

Da Kyashin Ya Ce Tazo Yakaita Kuma Itama Ta Bishi Suje
Gidan Mutane Da Kowa Yagansu Tare Zai Ga Bakinta
Arashin Zuciya Kawai Saita Zabi Bin Matashin Nan Wanda
Zuciyarta Ta Darsa Mata Kila Irin Kannen Mijin Anti
Atikane,tunda Gashi Yasan Ta Ita Kuma Tanai Masa Kallon
Sani,to Nagode Tasami Kanta Da Fada Tare Da Kada Kai
Alamar Amincewa Ta Dubi Kabiru Ka Kyale Shi Kaje Ka
Nemo Mai Gyara Idan Na Dawo Da Yamma Kazo
Kasameni Da Sauri Ta Bi Bayan Saurin A Zuwan Bataga
Yushau Wanda Ya Bude Mota Ba,da Alama Shima
Matashin Kamar Yagane Abinda take Gudu Cikin Zafin
Nama Yadaga Motar Suka Bude Yushau Da Kura,daidai
Lokacin
Dayake Daga Musu Hannu,
matashin Ya Figi Motar Kamar Mai Shirin Tashi Sama
Fuska Ba Yabo Ba
Fallasa Idansa Ga Titi,hakan Kuwa Ya Kada Hantar Ruma
Tafara Zargin Kanta Da Gangancin Kaikanta Makasa,
Har Suka Kusa Gidan Anti Atika Ba Wanda Yai Motsin
Ha,inci Atare Dashi Bai Dubeta, Ba Illa Yanata
Hidimar Tukin Motar Sa Yanabin Wakar Sa,can Yajuyo
Yana Rage Karar Sautin Au Namanta,ruma
Yayajiki,nauyin Da Zuciyarta Tai Wajen Kokarin Ta Gano
Inda Tasanshi Kokuma Tasan Muryarsa Ya Sanya Ta
jinkirin Amsa Masa,da Sauki,dafatan Iyali Da Kowa Lfya,ta
Kara Da Cewa Muryarta Na Rawa,akwai Alamun Ya
Shanye Mamaki Lokacin Dayake Amsamata Kowa Lfyar
Su Lau,kayi Hakuri Banfa Ganeka Ba Wallahi,,
murmushi Kawai Yai Ya Basar Har Suka Karaso Batare
Datamasa Iziniba Yanemi Guri Ya Tsaya Da Mota,adan
Zuciye Zatafita Bakiji ba?
Da Sauri Ta Tsaya Bayan Tafitarda Kafarta Na
Farko,yanawasa Da Key Holder Inkinshiga Dan Allah Ki
Gaidamin Mai Jegon,takarasa Ficewa Cikin Fusatarta
Wadda Kuzarin Gangar Jikinta Ce Kawai Kenunawa Ta
Rufemasa Motar Nagode Wazance Yanamata Barkar?
Idanta Akan Makullin Motar Dayake Kadawa Cikin Sakanni
Kadan Hantar
Cikinta Yai Mugun Kadawa Sukadinga Lugude Abubuwa
Biyune,wani Irin Kallo Dayake Mata,sannan Da Da
Tambarin Milkyway Datagani Manne A Key Holder
Sa,batagama Rudewa Ba Bare Tanemi Mafita
Ya Tashi Motar Yafara Ja Sannu Yana Amsamata Cikin
Murmushi MAHAUKACIN MASOYI Da Sauri ta
Janye Jiki Tare Da Kokarin Tantance Shi Duk Da yaja
Motar Aguje Haryana Neman Bugeta Ita Ma Kamar Zubin
Haukar Bana Ta Diba A Guje Cikin Gida Daidai Lokacinda
Yushau Ya Tsayar Da Motar Sa Inda
Mahaukacin Masoyi Yadaga A Kidime Tafada Falon Atika
Wanda Ke Cike Da Dangi,asiya MAIMUNA
HAFSAT,DA YA'YAN KANWAR HAJIYAR SU HASANA DA
HUSAINA,jiyo Sallamar Ta Kafinta Shigo Falon Ya Sanya

Kowa Yadau Murna musamman Hafsat Wadda Tatashi
Yiwa Ruma Oyoyo,amma Ina Ruma
A Birkicetake,tana Zuwa Ta Suri Wayar Asiya Komai nata
Rawa Sai Gashi Takarde Dakin Da Muryar
Abdullahi Madarut Acikin Suratul Bakara Ta Ajiye Akan
Kujera Taja Jiki Gefe A Hankali Ta Zauna,,falon Yai Tsit
Cikin Alamar Tambaya Kuma Danta Gajarta Musu Aiki
Saita Hada Tambayoyin duk Ta Amsa A Kalmomi
Kadan,motar Aljani Na Hau Shiyakowani Har Kofar Gida
Suka Dinga Duban Juna Anrasa Wanda zai yi magana.....
.
Dan Aunty
GORAN DUMA (P.56)
.
.
Hafsat Ta Ce Shine Wannan Ya Shigo Ta Girgiza Kai Toyaya
Akai?Kowa Saitambayarta Yake Sai Ga Yushau Da Kyar
Suka Kori Rudu Aka Gaisa Idan Aka Cire Ruma Wadda
Take Takure Tana Karkarwa Yushau Yakore Kunya Da
Nauyi Cikin Kishi Da Fargaba Da So,cikin Rada Hafsat Ta
Matsa Kusa Da Ruma Ko Yaya Yushau Ne Aljanin?
Ruma Ta Girgiza Kai ,to Ku Kashe Karatun Mana Kunata
Faman Sheka Surutu Kuma Kun Ware Kuna Sheka Kuka
Suka Kashe,,,kekuma Kalau?Yanzufa Naganki Lfya Harkina
Shuka Min Wulakanci Ki Barni Tsaye
Yanzu kuma Gaki A Burkice,duk datana Cikin Rikita Bata
fasa Jin Haushin Son Nuna Mata Iko Da Yushau Yakeba
Waita Wulakan tashi?
Dan kawai Ta Guji Hawa Motar Sa Ta Ce Kai Yaya Yushau
Kadaina
Mayar Da Allura Garma Wulakancin Mena Shuka Maka?
Amma Nasanar Dake Takanas Yau Zan Zo Gidan Nan
Donke Daidaine Acce Kin Ganni Kin Shareni?
Saima Budeni Da Kurar Dakikayi?Bisa Wani Dalili Zakazo
Gidan Nan Domin Ni?
Cikin Dacin Murya,kowa Kallansa Kawai Yake Yakore
Kunya Kan Tsinkawar Da Ruma Taimasa Gaban Kannansa
Inkin Kwantar Hankali Tunda Nazo Ai zan Fadamaki
Dalili,,
cikin Ci Da Zuci Ta Ce Saidai Wani Lokaci,ni Wallahi Yanzu
Banda Sukuni,
ran Yushau Ya Baci Sosai,amma Dole Yashanye Yana
Nazarin Ruma Saikawai Ya Kaddara Aljanarta Ce Ta Bijiro
Take Masa Rashin Kunya A Fahimtar Dayaima Matar
Maikudi Amininsa Kenan Amma Tuniya Kwana Da Sanin
Ruma Ba Halinta Ba,amma Dai Makakin Kishin
Saurayin Ruma Ta Hawo Motar Sa Ya Gallabi Zuciyar Sa Ya
Ce Wanne Shegen Ne kika Hawo Motar Sa Ya
Badamin Kura?
Ta Dauki Lokaci Bata Amsa Ba Kowa
Yai Tsit Inka Cire Hafsa Wanda Dukkan Alamunta Kenuna
Ita Idan An Bar Ta Zata Iya Bada Amsar,

Kamar Aiken Amsar Daga Mahaukacin Masoyi Sai Ga
Sakon Tex Dinsa Yafado Wayar Zuciyarta Tadinga
Azalzalawa Ta Karanta Kozata Ga Abinda Zai Bata
Tabbacin Kasantuwar Sa Jinsin Aljanu,INA
MAIYIMIKI RANTSUWA DA ALLAH NI NAFI KOWA
CANCANTAR ZAMOWA JAGORANKI,BA A SO KAWAI BA
HAR DA BARAZANAR KAMUWA DA CIWAN
ZUCIYA IDAN AN SOKEKI KO A TUKUICINE KAWAI BATARE
DA SO BA,KI TAIMAKA AKARE NAWA MUTUNCIN KAR KI
BARI A AIBATA MIKI NI.
NAKI MAHAUKACIN MASOYI BA SHEGE BANE DAN HALAK
NE!
Tasami Kanta Da Kallon Tsakiyar Idansa Cikin Kuka Ta
Ambata,a Maimakon Tasanar Dashi Cewa Aljani Ya Dauko
Ta Bayan Ta Ga Tabbacin Aljanancinsa A Sakonsa,amma
Aljanin Baiyi Tasirin Komai A
Zuciyarta Da Fargabarta Ba,illa Zuciyarta Data Yi Mugun
Raunin An Ce Masa Shege Bata Hana Ba,wani Mugun Kishi
Ya Turnuke Yushau Yanata Kallanta Kallan Dake Son Dawo
Da Ita Hayyacinta Tagane Cewa Ta,addanci Fatakewa
Zuciyar Sa A Kokarinta Nafifita Wani A Kansa,amma
Maimakon Haka Sai Ruma Takara Wani Taddancin Cikin
Kuka Ta Maimaita Kalma Daya WALLAHI BA SHEGE BANE,
yushau Dayaji Ashar Naneman Kwace Masa Saiya Fice
Daga Falon ,falon Yai Tsit Illah Sheshekar Kukar Ruma Sai
Can Hassana Tafasa Shirun Cikin Yanayi Na Zolaya Da
Nuna Tausayi, ABIN TAUSAYI
WALLAHI,YAYA YUSHAU YA FARKA DAHDAI LOKACIN
YAKUSA MAKARA YASAMI WANI MAI KWANJI YAYI FASHIN
ZUCIYAR, Hakan Yasa Kowa A
Falon Yah Dariya Ruma Kuma Ta Tsagaita Da Kuka
Takoma Hidimar Goge Hawaye,dan Allah Wai Yaya
Akaine?
Kin Barmu Cikin Duhu.Da Gaske Aljanine Yakawoki Kuma
Shi Kika Zaba Kikabar Yaya Yushau?
Maimuna Ta Cehaka ,hafsat Ta Zabga Mata Harara,a
Kayan Miya Meyeshi Yaya Yushau Da Baza A Barshi Azabi
Waniba?
Zuciyar Ruma Kam Arude Take, Tamike Ta Isa Ga Usaina
Ta Amsa Jaririn Tana Amsa Tambayar Maimuna A SURA
KYAWAWAN
DABIU DA SHIRYA KALAMAI MUTUM NE BA
ALJANBA,AMMA A WASU AYYUKA YANAKAMA DANA
ALJAN,NASHIGA WANI HALI,WANDA YASANYA NIKAINA
NAKE MAMAKIN ZUCIYATADA IDAN BANYI KARYA BA ZAN
FADI TA FADA TARKON SON ABINDA BATASANI BA,KO
ALJANINE WALLAHI NAFADA TARKON SONSA,CIKIN
TSANANIN RAUNI TAKARASA MAGANAR Duk Suka
Tsagaita Da Alama Bada Wasa take Ba Hafsa Ta Ce
Waiwanene?
Mahaukacin Masoyi,lahaula Wala Kuwata Illah
Billah,kinganshi

Da Idanki?
Shiya Daukoni Yakawoni Nan, Bayan Ta Zayyanamasu
Yadda Haduwar Su Takaya Tare Kuma Da Cewa Tariski
Sakonsa Akancewa Na Yana Dab Da Bayyana Mata
Kansa,kun Barmu A Duhu Ku Warware mana?
Inji Asiya,
hafsat Takalli Ruma Kallan Neman Izini,ruma Tamike
Tadauki Jariri Tana Ce Kisanar Dasu,
Ta Wuce Kaitsaye Dakin Barcin Atika Kozata Samu Damar
Wassafo Surar Mahaukacin Masoyi, Amma Tana Sauraran
Hafsa Datake Basu Labarin Mahaukacin Masoyi Da Nuna
Musu Tex Din Sa A Wayarta Bayan ta gama Kowa Ya
Jinjina,wasu Suka Shiga Rudu,amma Abu Daya Ya
Karfafamata Guiwa
Maganganun Da Hafsa Take Kuma Cikin Yakini Da Gasgata
Kai,na Bawa Kaina Sati Biyu Da Izinin Allah Sainabinciko
Mutuminnan Haka,kawai Bazai Zautamin Yaruwa Ba
Wallahi,ta Wace Hanyar?
Atika Ta Tambaya Kin Manta Mijina Dan sandan Cikine?
Lambobin Wayar Sa Nadauka Sun Isa Nagano Indayake,
**********
Bayan Wuni Cikin Sake Sake Yushau Ya Yanke Shawarar
Daukan Kwaryar Ban Hakuri Zuwa Ga Alhajinsa Bisa
Abinda Yafaru A Baya Da Kokon Barar A Mayar Masa Da
Ruma Yagyara Aurensa,yagama Shakulacin Bangaransa
Wajen Hajiya,haryakai Ga Isa Ga Alhji Wanda Yasanyashi
A Kwandan Shara,yajuyo Ya Fuskantanceshi,NASO NA
TUNA WANNAN FUSKARKUWA?
YALLABAI DAGA INA?
Duk Dakuwa Wutar Dake Zuciyar Sa Tana Raya masa Kuka
Yakamata Yayi Danhakan Kadai Ya Isa Nuna masa Saiya
Wahala
Malam Banfa Ganeka Ba Daga Ina?Kawai Sai Yushau
Yasami Kansa Da Fashewa Da Dariya Yana Kallon Alhji
Wanda Ko Kadan Dariyar Batasa Shi Ya Sassauta Damarar
Dayai Wa Fuskarsa Ba,saima
Yakawar Dakai Yaitsaki,hakan Ne Yasanya Yushau Yadan
Shiga Taitayinsa,yadinga Kokawar Gyara
Zama Yafara Bada Hakuri Na Tsawan Minti Gowa Sha
Biyar,alhji Na Saurarensa Har Saida Takaici Ya Sanya Shi
Tare Yushau Cikin Sarkewar Murya Dan Allah Malam Bari
Batawa Kanka Lokaci,wai Hakuri Kadaine Kawai Yakamata
A Rayuwa?
Bashi Kadai Nara Sa Ba,abubuwa Da Yawa Wadanda Na
Sasa A Bangarenka Wadanda Sukafi Su Muhimmanci
Suna Fi Bukata,,,cikin Zumudi Yushau Yatare Shi Saboda
Yana Zaton Alhji Zaice Ya Mayarda Auren Ruma Amma
Sabanin Haka Kaitsaye Cikin Muryar Tura
Haushi Alhji Ya Amsa,biya Na Kudaden Dasuke Wuyanka
Mana,wadanda Nadinga Hidimar Iyalinka
Dasu Tun Bayanda Ka Saki Uwar Su ,saima Ka Daukemin
Kafa Da Aljihu Ka Barni Da Nauyi Danka Tabbatar Lallai

Bazan Iya Kaisu Bola Na Zubarba!
Ka Yi Ta Banzar Yushau Domin Komai Na Nan Arubuce
Na Na Adana Ko Mutuwa Nai Na Sanar Da Magada
Sunemi Hakkinsu A Wajenka,,,
cike Da Rauni Yushau Yatare Shi,,kayi Hakuri Zan Biya
Alhji,a Bani Adadi Sainafara Biya Daga Wannan Watan,
daka Kyauta Wa Kanka,cikin Ko Inkula Alhji Yafada,falon
Yai Tsit Inbanda Bugawar Zuciyar Yushau Wadda Ke
Tattara Dukan Kafofin Da Zata Sauke Karfin Halin Data
Wanko,akarshe Dai Da Ya Hattama Sai Bakinsa Ya Karbi
Karfin Halin Yafurta Cikin Sarkewar Harshe,idan Rabuwa
Da Ruma Ne Ya Nisanta Ni
Daku?
Kuma Har Shine Yaisa Abin Sanyawa Ka Manta
Kamannina Alhji Ina Neman Alfarma Kadawo Dani Kusa
Daku,,ku Mayar Da Diyancina Dan Haka Inaso Ka Sanya
Albarkarka Ka Bani Dama Na Mayar
Da Aurena Da Ruma...
tunkafin Ya Dire Akwatin Tara Fushin Alhji Ta Cika,ya
Yunkuro Da Fushi Yatareshi,,,wallahi Tallahi Danasan
Maganar Dazakai Minkenan Na Rantse Da Allah Da
Samsam Ban Saurareka Ka Sarayar Min Da Lokaci
Ba,saboda Haka Idan Ba Son In Sassaba Maka Kamannin
Ka Ba,to Ka Digawa Wannan Maganar Aya,
yushau Yai Tsita Cike Da Fargabar Ta Inda Zai Billowa
Alhjin..
Dan Girman Allah Alhji Ka Bani Dama Na Fahimtar Dakai
Akasin Da Aka Samu Cike Da Takaici Alhji Yake Kallon
Yushau Cikin Yanayi Nata Gina-ba-ta-shiga Ba Ya Cemasa
Ahau!Inajinka Yushau Ya Gyara
Zama Jiki Na Bari Ina Son Ruma Alhji Duk Wata Mace a
Duniya Bayanta Zata Bi A Zuciyata,ban Fahimci Hakan Ba
Sai Bayan Rabuwarmu Amma Fushin Da
Kuke Ciki Ya Dinga Tsoratani Yana Hanani Kawo Kaina.....
.
Dan Anti.
.
.
Sannan Sai Gurguwar Fahimtar Dana Yiwa Ciwonta
Wanda Shine Kashi Casa'in Na Rashin Jituwarmu,ayanzu
Kuwa na Nemo Iliminsa Na
Tabbatar Matsala A Dalilinsa Takare Kuma Idan An Bani
Dama Na Ci Alwashin Sai Ruma Ta Rabu Da Ciwon Nan
Haihata Haihata Cikin Izinin Allah,
oh Kana Da Kudin Daza a Canza ,mata Bargo Ko?
Alhji Yakatse Shi A Shashance Cike Da Ladabi Yushau Ya
Amsa A Iyakar Gaskiyarsa,a Binciken Danayi Nagano
Shafar Jinnu Ce Naci Alwashin Daganan Har Saudiya
Zandauki Nauyinsa Ayimata Rukiya,
alhji Yafara Yiwa Yushau Duban Mahaukaci,da Kyar Ya
Hadiye Wani Yawu Daya Cikamasa Makogwaro,yanunawa
Yushau Kofa,tashi Ka Barmin Gida,,,,,,,,!,,

Nima Ina Da Malaminda Zan Nemo Yaimaka Rukiyar
Dankafi Ta Bukatar Rukiya,,,
yushau Yai Funfurus Yakitashi Sai Shi Alhjin Yamike To Ni
Barina Barmaka Dakin
Kafin Yushau Yai Magana Tuni Ya Fice Danshima Ya Mike
Jiki A Sanyaye Yana Kokarin Ficewa Zuciyar Sa Na
Karkatar Dashi Cewa Kawai Yadage Ya Nemo Kan Ruma
Dakanta Inta Kawo Wa Alhji Maganar Komen Ai Bazai
kiba,
***********
Kwanaki Uku Da Suka Biyo Baya Mahaukacin Masoyi Ya
Bace A Rayuwar Ruma Ta Zahiri,wato Ba
Bushi A Sakonninsa Kuma Ba Bu Shi A Zahiri Kamar Yadda
Ya Billo A Matsayin Direban,dayakai Ta Gidan
Atika Amma A Badininta Yananan Yana Ninkaya,wuni Da
Kwana Yana Shige Da Fice A Zuciyarta Mai Wassafa
Kamaninsa Tanakara Kawata Wa kanta Shi,abuna Biyu
Kuma Tana Canke,canken Mutum Ne Shiko Aljan Sai Abu
Na Uku Tana
Tunanin Koma Waneneshi Wato Mutum Din Dai Ko Aljan
Dinshine Wannan Nazifi Muhammad Daga
Milkyway,sai Abu Na Karshe Shine,tanason Ganinsa A Fili
Rayuwarta Ba Irin Yanzu Daya Ke Kan Katangarta
Ba,kowace Irin Rawa Zaitaka A Fili Saita Cika Kanta
Tsakar Dare Ana Gobe Sunan Jaririn Atika,bacci Ya
Kaurace Mata Fau-fau Bayan ta gama Laluben
Mahaukacin Masoyi A Dukkan Kafar Daya Taba Lalubota
Bata riskeshi Ba,kama Daga Kiran Waya Akwatin Tura
Sako,social Network Da Sauransu Amma Shiru Ba Bu
Alamar Shi,da Bacci Ya Kaura
Cewa Idanta Sai Gata A Zaune Tanakaranta Wasikar
Jaki,kamar Daga Sama Wayarta Tayi Tsuwwa Cikin Razana
Da Barin Jiki Ta Wawurota Amma Sai Taga Hafsat
Damamaki Ta Daga Da Sauri Ko Sallama Batai Ba Hafsat
Lfya?
Cikin Doki Ta Ce Lfya Kalau Nakasa
Jiran Wayewar Gari Da Tsegumina Meyafaru?
Ruma Tatare Ta Cikin Doki Hafsat Ta Ce Sani Munafikine
Yasan Abubuwa Dayawa Dangane Da Mutuminnan,
Wanne Mutumin?
Hafsat Ta Ce Harkin Manta?
Mahaukacin Masoyi Mana Sai Ga Ruma A Tsaye Cikin
Tsananin Rudani Ta Ambata Da Gaske?
Yanzu Dama Canda Sa Hannun Sani Abinda Mutumin Nan
Kemin?
Hafsa Tatare Ta Cikin Sauri Ko Daya Satin daya Gabata
Shima Yasani Ruma Ta Sauke Kakkarfar
Ajhyar Zuciya Innalillahi Wa Inna Ilai Hirajiun To Mutum
Ne Ko Aljani?Kuma Meye Takamar Sa?
Hafsat Na Shirin Amsamata Sani Ya Karbe Wayar Ya Ce
Haba Shekara Uku Ba Bu Aure Wasane?
Kin Manta Cewa Katon A Addancin Ne Ka Bugowa Amare

Waya Tsakar Dare Irin Haka Ko Baki Duba Agogo bane?
Su Waye Amaren Waiku?
Tafada Cikin Zolaya Tare Da Jin Ciwom Yayankemata
Samun Haske Akan Majanuninta Sani Ya Ce Mu Mana!
Saida Safe Kafin Ka Ajiye Saika Amsamin Tambayar
Danaimata Sarkin Kulle Kullue Kanaganin Ana Neman
Kasheni Da Raina Amma Ashe Kaine Mai Bada
Gudumawa,saiki Hau Duro Ki Fada Ya Ce Cikin
Zolaya Yakashe Wayar Gabadaya,tafada Gado Tana
Ambatan Allah Wato Mahaukacin Masoyh Mutum Ne Ba
Aljani Kamar Yadda Tayi Tsammani Ba Indai Sani Yasanshi
To Ta Tabbata A Duniyar Su Ta Mutane Yake To Amma
Tayaya Yakemata Sidda Baru?
Tajima Tanakokarin Amsa Tambayar Amma Takasa Saita
Hakura Ta Kamo Tashar Wadda Ta Tarar Da Shiryayyun
Wasu Tambayoyin Ba Bu Amsa Wato Mene Ne ManuFar
Sa Akanta?
Yana Da Masaniyar Cewa Ita Sikila Ce?
Kamar Amsa Ga Tambayoyinta Sai Ga Wani Kira Daga
Hafsa Da Sauri Ta Amsa Ta Ce Yi Saurin Amsamin Kafin
Kafin Sani Yadawo,cike Da Zolaya Hafsa Ta Ce Aiyana Kusa
Kwalar Rigarsa Naci Ya Sallama Na fada miki Wani Abu
Daya Da Zai Kwantar Miki Da Hankali
Inajinki,
hafsa Tai Kasakasa Da Murya Ta Ce
Mahaukacin Masoyi Wato Nazifi Muhammad Mutum Ne
Kuma Da Gaske Mahaukacikine A So,yayi Nisa
Fiye Da Yadda Kike Tsammani,kuma A Nawa Tsammanin
Ba A Ta Ba Sonki Kamarki Haka Ba Rumaisa"u
Karyakike Hafsa,ruma Tafada A Fusace Cikin Sauri Maitafe
Da Kuka Mai Tuna Baya Ni Ban Taba Wani Kamar Auwal
Ba,kuma Ban Yarda Za A Sami Wanda Zaiso Ni Fiye Da Shi
Ba Tanason Zarcewa Da Kuka Hafsa Ta Tareta Cikin
Rudani Rage Kukan Karki Janyo Hankalin Iyayenki Gobe
na Sha Luguden Fada,duk Da Tuntuni Maganar Taje
Kunnen Alhji,rumaisa Tanemi Dauke Numfashi Cikin
Rudani Amma Kafin Ta Tanka Hafsata Ta Rigata Indai Za A
Sami Mai Son Naki Zuciyarki Ta Yarda Da Haka,ba Wai
Angama Samun Mai Sonkine Kwata Kwata Ba,kidan Bude
Wa Wannan Dan Tahalikin Zuciyarki Kadan Yasami Guri
Ina Mai Tabbatarmiki
Lokaci Kadan Zai Gawurta Harki Gane Nisan Fifikonsa Da
Au...
Ke Tafi Can Ruma Tafada A Fusace Ta Kashe Wayar Cikin
Zafin Zuciya,kwana Tai Safa Da Marwa Da Rashin
Barci,saboda Damuwa Da Rikita Yajanyo Mata Wani
Matsananchn Ciwon Kafa Da Misalin Karfe Takwas Na
Safiyar Ranar Inda Ciwon Kafa Da Misalin Karfe Takwas
Na Safiyar Ranar Inda Ciwan Yadinga Shan Sharafinsa Har
Fiye Da Awa Daya Saida Kowa A Gidan Hankalinsa Yatashi
Ita Ruma Mai Ciwon Kuka,mairo Mai Tausayi Kuka Hajiya
Da Alhji Da Mubarak Ba Bu Wanda Hankalinsa Ke Kwance

Har Saida Ciwan Ya Lafa Alhji Yatafi Da Ita Asibiti,daga
Asibitin Ne Kuma Taki Yadda Amayarda Ita Gida Saidai
Mubarak Yakaita Gidan Suna Kawah Duk Da Kuwa Bata
gama Wartsakewa Ba Ana Dai Abinda Yafi Ciwo Ajikinta
Shine Zuciyarta Dake neman Gazawa Da Lissafin
Mahaukacin Masoyi,hayaniya Bata Barta Ba Dole Atika Ta
Waremata Falon Mijinta Ta Kwanta Jefi Jefi Wasu Kanshi
Go Su Dubata Balaraba Yayarta Ta Shigo Ta Cemata Wai
Wanene Wancen Da Sani Keta Faman Nunawa Mutane A
Matsayin Mijinki?
Abin 'yar Hakane Ruma Kinyi Miji Ko Albishir Ba Bu?
Cikin Rudani Ruma Tatashi Zaune Ban Sanshi Ba
nima,balaraba
Takalleta Sororo Har Nawasu Lokuta Ta Ce Dagaske?
Ruma Takoma A Kasalce Ta Kwanta Balaraba Tamike Cikin
Sanyin Jiki Ban So Haka Ba Gaskiya Naso Ace Kinsan
Shi,kuma Kece Kika Bashi
Damar Yazama Mijinkh Saboda Nutsuwar Sa Da Kalamar
Sa Dakuma Abinda Bani Kadai Na Hango Ba Wato Tarin
Kaunarki Atare Da Shi,duk Kwakwar Balaraba Takasa
Fahimta Abinda Ruma Ke Rayawa Aranta Balaraba Tafara
Tfya Tana Cewa Nadanyi Hira Dashi Har Na Fahimce Shi
Dan Hadejane,kuma Mazaunin Abuja,yaushe Kakayi Hirar
Dashi?
Cikin Hanzari Ruma Tafada Tana Dagowa Balaraba Hannu
Alamar Dakatar Da Ita Barin Falon,saboda
Kasalar Gangar Jikinta Yanzunnan Balaraba Ta Amsa ,au
Ance Ma Nasanarmiki Zai Shigo Ya Dubaki,cikin Kuluwa
Ruma Ta Amsa Ba Bu Laifi Ta Koma Ta Kwanta,balaraba
Ta Fice Daga Falon Batare Da Ta Canka Dalilin Kuluwar
Ruma Ba Duk Da Tana Tunanin Ce Wa Marigayi Auwal Ta
Tuna Ruma Takasa Cankar Inda Zuciyarta Fada Dokin
Gani,fargaba Kojin Kallan Mahaukacin Masoyi?
Yau Kuma Yanzu?
A Haka Tajiyo Takun Sawaye Tare Da Muryar Sani Yana
Karadin Hirar Sa Ta Dora Idanta Kir Akan Kofa
Cike Da Dokin Ganin Inta Ga Nazifi Muhammad Kar To
Taga Kafar Sa Da Kofato Dan Kuwa Idanta Na Kan Inda
Kafafunsa Zasu Duro,sani Ne Yafara Shigowa Cikin
Yanayinsa Na Faraa Da Kuzari Kamar Koda Yaushe Nazifi
Biye Da Shi Cikin Matsananciyar Kasala Mai Alamun
Tasowa Daga Zuciya,ba Kamar
Ko Yaushe A Ganin Dataimasa Cikin Kananun Kaya Ba,yau
shiGar Manyar Kaya Yayi Na Shadda Ruwan Toka Yar Ciki
Da Babbar Riga Bata Damu Da Zolayar Sani Ba Ahankali Ta
Dauke Idonta Daga Kallansa Zuwa Wani Wajen ...
.
Dan Aunty
Al-Hada Hada Hausa Book stories
GORAN DUMA (P 58)
.
.

Sani Yadubi Ruma Wannan Wace Irin Tarba Ce?
Karkuma Ki Kalawa Ciwo Dan Fuskarki Tanuna Da
Sauki,takalli Sani Garau Ta Shiga Gyara Mayafi
Wanda Ta Lullube Kafafuwanta Dashi Tun Lokacin Dataji
Takun Shigowar Su Dahaka Ta Bar Tambayar Sani Tabi
Ruwa,hakan Yasa Sani Da Nazif Sukai Murmushi Nazifi Ya
Ce Ankuma Ce Tun Tuni Kina Dokin Ganina Ni Ma Ban
Zaci Wannan Tarbar Zansamu Daga Gareki Ba Sai Yanzu
Ta Fahimci
Kwakwalwarta Ta Tsaya, sani yatafi yabar Ruma da nazifi
alamu yanuna a tsorace take tundaga fitar sani daga falon
nazifi ya mike
cikin kwarin guiwa a tsorace cikin zafin nama sai gata a
zaune tana
kallon kofar cikin Gyara wuyar Riga yakaraso tsakiyar
falon ya zauna kan teburin dake girke a tsakiyar dakin
Wanda ya basu Damar kallon juna ruma cikin tsananin so
da farin cikin ganin masoyin Ruma tafara kauda kai cikin
cin magani yace najima INA kaucewa haduwa dake idan
kina cikin rudu ALLAH bai nufa ba amma dai nayi nasara
ba wani na ya rudaki ba nida kaina na rudaki yatsayar da
maganar saboda yaga bakinta na motsi alamar zatai
magana amma yana rufe baki sai yaga ta hadiye yaya jiki?
Nanma kallonsa kawai tayi ta kauda kai yace nasan
abinda yajanyo fushinnan lokacin da kika so ganina naki
ki ganni ba fushi ya dace kiyi ba Ruma kamata yai kinemi
ba'asi cikin karkarwar murya tace wa yace maka inason
ganinka?
kaitsaye ya amsa cikin daga gira kintashi daga kano
takanas zuwa abuja din kiganni cikin tilastawa kai
wani fushin face duk yafarune cikin kuskure Yanzu
najanye saboda haka kana iya tafiyarka idan kazone
domin na ganka takaj
da raunanniyar murya yace badon kiganni nazoba nine
nazo don na ganki domin nikadai kesonki nakuma cika
son kai Dan banbaki damar kisoni ba a tsammanina nawa
son ya wadatar tace masa
wannan bayanin naka sunyi hanzari domin kai yakamata
nafara sani ba kalaman soyayyarka
ba amma idan kagama boye boyen kenan
nagama yafada da sauri shiyasa nacemiki nafiye son kai
na boye mini kaina yayinda na zurfafa a sonki har nakai
bigiren da raina kejin in an raba shi da sonki bazai iya
cigaba da nunfasawa ba nantake kwalla tacika mata ido
domin maganarsa tatuno mata da
auwal babu alamun shakku ta amsa masa rashin masoyi
baya kisa dayanayi dabaka ganni a Raye ba har ka soni.
nazifi ya dauke wuta dad fuskarsa da gangar jikinsa sun
nuna damuwa kishi yajima cikin kallon shimfidar falon
kamar yadda taciga ba da kallon talabijin zuciyarta a
auwal batare da nadamar maganar dataiba said a ta
hangi inuwar nazifi a tsaye tajuyo ta dubeshi lokacin

yakusa kofar fita falon tagama yanke kaunar sai fice baice
komaiba amma sai ya jiyo a sanyaye yace nasan ba zafafa
cimma burina ne yasanya nijin cewa ALLAH ya
karbi ran Auwal ya barmin me ba don nafishi
cancantane.na fishi sonki na kuma fishi cancantar zama
mijinki RUMAISA'U sikila..,.
watakila sai lokaci yayi zaki fahimci hakan tai shuru tana
kallonsa da alama kamar laluben ta inda yafi Auwal
cancanta take
zanwuce masaukina yanzu badon zantakura mikaba
danazo gidan yau da dare gobe don inanan kano har
safiyar jibi itadai kam hawaye take face masa jimana
tareda karfin halin mikewa tsaye yajuyo ya kalleta tadanyi
kamar xatafadi a
kokarinta na gyara tsayuwa da sauri yadaga mata hannu ,
a, ah koma ki zauna ta koma ta xauna tace maasa kafin
goben inasan sanin kai waye I na tsammanin a duniya
babu abinda ya shige min gaba kamar son sanin amsar
wannan tambayar akwai wani suna dazan sake amsawa
ne banda
MAHAUKACIN MASOYI?
wannan sanin yakamata ki rike ba na tsammanin
zakisami Wanda yafishi da gaske ne ni MAHAUKACIN
sonkine ba wannan nake tambayaba ai tundazu akan
haka muke magana tambayata anan itace ta wace hanyar
kake shiga zuciyata?
tawace idon kake kaina hatta a lokutan da nakasance
nesa da idon kowa yakada kai yana dariya au hakanefa
duk naji zarge zargen
dakikemin wajen sani zargi ne wato ba gaskiya bane?
ta tambaya cike da mamaki kwarai da gaske ya amsamata
shikenan saika tabbatarmin da gaskiyar yanzu.
ya CE a irin wannan lokaci n dakika cakuda min zuciyata
da takaici ?
INA girmama Auwal don darajar zuciyarki tasoshi ni
kuma masoyin kine ke da komanki amma girmamawar
taki shafe kishina ya fice ya var falon tunbayan fitar
MAHAUKACIN MASOYI Gidan sunan yaimata zafi tatashi
tashiga cikin jamaa inda ake ta kayakaya murna da
daukan hotuna kozata manta amma hotunan
MAHAUKACIN MASOYI a cikin zuciyarta musamman
daidai lokacin da yake cewa NASAN BA ZAFAFA CIMMA
BURINE YA SANYA NAJI CEWA ALLAH YA KARBI RAN
Auwal YABAR MINKE BA DON NAFISHI CANCANTANE
NAFISHI sonki KUMA NAFISHI CANCANTAR ZAMOWA
MIJINKI RUMAISAU sickle INA GIRMAMA Auwal DON
DARAJAR ZUCIYARKI TASOSHI NI KUMA MASOYINKINE KE
DA KOMANKI AMMA GIRMAMAWARKI TAKI SHAFE
KISHINA
wadannan zantukannasa sunki bacewa daga zuciyarta da
alama duminsu ne yake ta faman kyankya sar son
ubangidansu wato MAHAUKACIN MASOYI a kirjinta

ta yarda ya iya so tunda ya iya sonta ita da son dataiwa
waninsa AUWAL kuma kishinsa ya na nan daram amma
baya runtse masa I do ya ya mayar masa da sonta
kiyayya ,tabbas ko yayane zai iya
zama waziri a fadar so da kaunarta yayinda auwal yake
sarkin sarakuna ,
##****************
Dan rumaisau yushau ya isa gidan sunan da gamma da
sunan wai yaje daukar sumoli wadda ta mayar da kanta
amarar biki da karfi da yaji yayi katari an kwakolo
rumaisau da kyar zuwa wajen daukar hotuna a harabar
gidan sai gashi dayin abinda babu shi a cikin tsarinsa
wato shiga sabgar bikin
mata ya rungume hannu ya tsaya kusa da kanin mijin
atika yana satar karewa Ruma kallo Wanda kaf Cikim
matan dasukazo sunan sinfita daukan ado amma a haka
it'a kadai kallon ta ke buga masa
zuciya musamman

2 Comments On GORAN DUMA
avatar
jannat

1 year ago

Reply

08062236094

avatar
jannat

1 year ago

Reply

08062236094

Please Login or Register in order to submit comment