Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ki sha magani, Hafsat
taimaka ki murza mata tafarnuwar ki ta ce ki
kaw mata".
Hafsat ta tashi ta 6arin jiki tana yiwa Rumasa'u
sannu ta wuce kicin ta d'ebo tafarnuwa masu
kyau ta 6are, ta dandaka sannan ta zuba ruwa
kofi daya ta tace da rariya ta kawowa Rumasa'u
ta shanye.
An fi awa daya kafin a samu ciwon cikin ya lafa,
wannan ne kuma ya sa Hajiya ta tsokano
maganar da ta ke jin yyinta ya zama dole dan ta
fahimci Rumasa'u, so ya rufe mata ido tana
shirin yin abin da za a ga laifinta.
"Rumasa'u kun ta6a maganar ciwonki da Auwalu
kuwa?"
Alamun damuwa da nadama ya bayyana a fuskar
Rumaisa'u, kwalla har ta cika mata ido, ta girgiza

kai ta ce.
"Ba mu ta6a ba Hajiya".
Cikin zura mata ido, Hajiya ta ce.
"Tyn farkon ne kika rasa hanyar sanar da shi
Rumasa'u?"
"Ban san za mu dore tare ba Hajiya".
Hajiya ta yi shiru alamar nazari, sannan ta nisa
ta ce.
"Ni har na fara zargin ko ganin yawan laulayinki
ya hana shi turo manyansa. Ga su Hafsa suna ta
faman jiranki".
Ta matse kwallar idonta tana amsawa.
"Ni ce na ke dakatar da shi Hajiya, kuma na kasa
sanar da shi dalili".
Hajiya ta girgiza kai ta ce.
"Wannan kuma ba dabara ba ce kika yi, za ki ta
zama haka ne Rumaisa'u? Ai a rashin kira karen
bebe yake 6ata, ki kokarta ku tattauna lamarin".
Cikin sanyin jiki Rumaisa'u ta ce.
"Shikenan zan kokarta Hajiya".
Ta gama shin bacci ke nan ya mmako mata
waya, ta dauka da kasalar rashin 'karfin jiki.
"Auwal ba ka jin bacci?"
Muryarsa a d'ashe ya amsa.
"Na kwanta ya 'ki zuwa Rumasa'u, abubuwa
barkatai sun cushe a 'kwa'kwalwata. Ga kadaici
ga matsaloli".
Ta dan yi dariya ta ce.
"Me ya dami ranka haka Auwal?"
Ya sauke numfashi.....
"Kafin mu rabu na fahimci kamar ba kya jin dad'i,
na taho da tauayinki da neman hanyoyin da zan
samar miki waraka ko da na dauke kewa da
'karfafa gwiwa ne, amma duk kin bi hanyoyin da
hakan za ta afku kin toshe. Na fara sarewa
Rumasa'u dan na fahimci kamar kin raba
zuciyarki biyu ne kin bar min daya na sani, dayar
kuma kike wahalar dani da ita.
Wata irin 'kaunarsa ta dingo bijiro mata, tana
nemansa ta 'kwalla, tana kokawar daurewa yana
gagara.
"Auwal wannan ne zai hanaka bacci? To in dai ni
ce ba za a haifi matsalolin da za su 6ata ranka
da ni ba. Za mu sami lokaci nan kusa mu
tattauna... Amma ina son ka a jiye a ranka
soyayyarka ce ke hana ni yin abin da kake
hasashe ina jinka da matsayin wani 6angare na
jikina, wanda rashinsa zai gutsire rayuwata,
amma na 'kure fatan hakan zai gaza faruwa".
A raunane ya ce "Saboda me? Rumaisa'u duk
yadda nake da matsayi a zuciyarki da sha'kar
numfashinki d'igo ne na matsayinki a wata

zuciyar, na kuma dami raina da son kai 'karshen
buri a kanki kafin mutuwa ta runtse ganina, ke
kuma kin kasa gane hakan..."
Ta yi saurin tare shi.
"Haba me ya kawo zancen mutuwa Auwal?"
Shi ma ya tareta da nasa batun.
"Ai ya zama dole, 'karuwar burika, cika wasu da
su6ucewar wasu alamu ne na kusantar kabari sai
raina yake ciwo da hasashen mutuwa zata iya
riksta ba tare da na cika burin samunki ba."
Ta fara hawaye sosai, dan haka ta jima ba ta
tanka ba, har ta fitar da sautin kukanta kadan,
sannan a cikinsa ta ce masa.
"Ba na fatan dai-dai da kwayar zarra in cutar da
kai Auwal, kuma bana son rabuwa da kai.."
Ya tare ta a dan 'kuntace.
"Shikenan sai ki bar mu muyi ta bulayi a
soyayyar da ba ta da rana, wadda ta ki ta zuciya
ta saba da ta fatar bakinki, kina sona amma kin
kasa ba ni damar mu kasance 'karkashin sunna...
wannan makahon so ne..."
Ta yi kokarin tare kukanta, ta ce.
"Akwai matsala ne Auwal, ni ke nan yau lafiya,
gobe babu. Zan zame maka dawainiya in gundure
ka, shi yasa ba na son cin karo da kukanka
Auwal".
Ya yi dariyar da ta fad'ad'a masa 'kirji ya ce.
"Wa ya ke dorawa wani lalura Rumaisa? In Allah
Ya so sai Ya yaye miki, ai babu cutar da ba ta da
magani. Ita kanta cutar ma wani maganin ce,
domin tana kankare zunubai... Ni ma da nake son
daukar dawainiyarki ladan zan samu idan na kula
da ke, duk sanda aka ce ba ki da lafiya sai na ji
da tare muke sai na fi samun nutsuwa..."
Ta 'kara fashewa da kukan da ya tsorata shi. A
rikice ya ce.
"Wai don Allah me yake faruwa ne? Rumaisa na
kaa canko dalilan wannan kukan naki".
Cikin kukan ta ce "Na gode da niyya da fatanka,
amma ciwo na mutuwa ce kadai zata raba...
Saoda haka aurena da kai yana nufin ka yi ta
danniya da hakuri a kaina har 'karshen rayuwata,
domin haka Allah Ya halicce ni, haka kuma Ya so
ya ganni..."
Ya rasa fassarar da zai wa maganganunta, rashin
yanke shawarar ya sa shi yi mata tambaya a
gajarce.
"Wai wanne irin ciwo ne?" Kai tsaye cikin dakewa
ta yi karfin halin amsa masa.
"Sickle cell" Ya ji kamar ta doka masa guduma a
'kirji, cikin 'yan sakanni wasu miliyoyin tausayinta
da fargabar yadda lamuransu zai kasance ya

mamaye masa 'kirji, dan ya san ciwon sickle cell
ba da wasa ba kasancewar wani abokinsa sikila
ne ya dad'e da sanin yadda masu ita suke shan
kashi sai dai wannan 'karamar matsala ce idan
aka kwatanta da neman makomar 'ya'yan da za
su haifa.
Duk da a rikice yake bai kasa 'ko'karin tattara
kalaman da zai 'karfafa mata gwiwa ba.
"Mene ne matsala a kasancewar sickle Rumaisa,
ko ke kika yi kanki dan me za ki raba kanki da ni
ballatana Ubangijin da Ya yi ni Ya yi ki, ba domin
na fiki ba? Ki zama mai tawakkali da ha'kuri da
rayuwa sai matsalolinki su zame miki kaffara. In
kuma domin wannan kike gina katanga tsakanin
da kasancewa tare, to ni ban fahimci gatan da
kike son yi min ko kike son son yi wakanki ba".
Yanzu ta rage kukan da ta ke, dan a zahiri
hankalinta ya soma kwanciya, duk da ta san bai
kamata ya kwanta din ba.
Ta nisa ta ce.
"Kar ka yi gaggawar yanke hukunci Auwal, ka
zauna ka yi tunani da kyaun duk matsaloli a
kaina ka lissafo suka ga yadda zaka iya tarbarsu,
yadda zaka dinga dawainiya da ni, dawainiyar
aljihu da ta KWANJI, ha'kuri da ni wajen kukan
ciwo da hakurin wasu kulawa daga gare ni
lokacin ciwo in duk wadannan sun zama sau'ki a
gareka Auwal makomar 'ya'yanmu ba zata zama
sau'ki ba matu'kar ba ka kasance wanda ba zai
bayar da gudunmowar da ba zaka haifi sickler
ba".
Ya ja numfashi sosai saboda rashin abin cewa,
amma dole ya nemo shi.
Ya ja numfashi sosai saboda rashin abin cewa,
amma dole ya nemo shi.
"Yin daainiya da ke, da kuma hakuri da laulayinki
ni ba zan ta6a kiransu matsala ba Rumaisa, ina
son ki soyayyar da nake jin ko mugun hali ne a
jininki ba zata gaza ba, bare wannan jarrabawar
ta Ubangiji da idan kika haye ta da tawakkali, na
haye ta da jurewa dawainiya da ke zamu iya
samun aljanna da ita.
Batun 'ya'yanmu shi ne hanzari, amma wannan
zai hana ki aure har abada ke nan Rumasa'u?
Kafin haduwa da ni wanne tanadi kika yiwa kanki
a fannin aure, me yasa kike ganin zan bayar da
gudunmowar da zamu haifi sickler?"
Ta amsa masa a raunane.
"Ban ta6a fitar da rai zan yi aure ba, sickle cell
kuma ba ciwo ne da za a ce ka auri mai shi ya
zama waraka ba, domin za ku samar da iyali
irinku ne gaba daya, amma dai ban ta6a hasaso

aurena da rayuwar auren wani abu ne mai sau'ki
ba. Ina sonka Auwal wallahi ba na fatan duk
wani abu da zai cutar da kai, na san kuma ko
yaya ne aure na zai iya zame maka matsala ko
ta fannin 'ya'yanmu..."
Ya tare ta da sauri.
"Shi yasa na tambaye ki, wacce irin gudunmowa
zan bayar da kike ala'kanta ta da haihuwar
sickler?"
Ta jima cikin shiru, sannan ta ce.
"Idan ka ji a ranka zaka iya aurena, kuma a
gidanku za a barka, shi ne zamu tuntu6i likitoci
dan samun shawarwari, a iya maka gwaji kuma a
gano kai waye, ta nan zamu iya sanin makomar
'ya'yan namu".
Yanzu ya fara samun nutsuwa, saboda haka cikin
doki ya ce.
"In Allah Ya so cikin satin nan sai mu je asibitin,
amma ki sani duk yadda bincike zai nuna ba na ji
zai iya yi min katanga da aurenki. Ki cire shakku
daga ranki Rumasa'u, ina yi miki soyayyar d aban
san matsaloli a tare da ke".
Ta yi shiru tsawon wasu sakanni sannan ta ce.
"Abin da na fi so da kai Auwal ka fara tuntu6ar
magabanka shawara a kaina, kar ka biyewa
soyayyar zuciyarka ka yi abin da ransu ba zai ji
dad'insa ba...q
Ya tare ta kamar a 'kufule
"Rumaisa'u sickle cell ne yakai girman da ba za a
auri mai shi ba? Haba! Wannan maganar banza ki
ke..."
.
Dan AuntyGORAN DUMA 7
.
.
Ita ma ta tare shi a tausashe "Auwal babu yadda
za a yi ni da kaina in 'kir'kiro abubuwan da zai
nesanta mu da juna, amma duk abin da yake
matsala ina guje mana shi kasancewara sickler
na san da yawanmu irin matsalolin da suke
fuskanta a rayuwa, ciki har da tsangamar da
dangin miji ke masu matsaloli (sicklers) da za yi
ta faman dawainiya da nauyi akan mijinsu ko
kuma haihuwar dawainiya da su. Auwal wani
lokacin ma mazajen ke tsangwamar matan akan
sun zame musu nauyi... Kai wata ba sikilar ba ce
idan suka taru ita da dangin mijin suka haifi sikila
sai ya tattara laifin ya dora mata, wata
mahaifiyar sikila da na sani ta ta6a bani labarin
yadda mijinta ya fito kai tsaye yake 'kalubantarta
akan cewa matansa hudu, amma ita kadai ta ishe
da haihuwar sickler duk da cewa tare da mijin

suka haifeta. Amma ka fahimta ba gudu nake a
tsangwame ni ba ko ko kuma a 'kalubalance ni,
na rantse maka babu wata wuya da ba zan iya
jurewa ba, kawai dai bana sn ka yi abin da magabatanka
za su yi kuka da kai. Idan aure zai
shiga tsakaninmu ya kamata mu kori duk wani
abu da muka san 'kalubale ne a rayuwarmu ta
gaba dan a gaban ba mu da lokacinsa abin da ke
gabanmu ma ya ishe mu".
A sanyaye ya nisa, ya ce.
"Na fahimce ki, in Allah Ya so zan yi abin da kika
ce, amma dai dole mu hanzarta zuwa gwajin, ina
son yin tanadin dukkanin wata juriya a kanki".
Ta yi murmushin karfin hali cikin saduda ta ce.
"To shikenan, Allah Ya za6a mana abin da fi
alkhairi Auwal".
Ya amsa cike da farin ciki.
"Amin Rumaisa'u, Allah Ya sa mutuwa ce zata
raba mu".
Ta yi dariya ta ce.
"Kuma ya zama ni zan rigaka mutuwa, na
tabbatar rayuwa zata yi min 'kunci idan babu
kai".
Shima ya yi dariyar, ya ce.
"To kin ga gara ni na riga ki mutuwar, saboda ni
ba zan iya jure rayuwar da babu ke din ba".
Da dad'i ya cikata kawai sai ta amsa masa da
cewa.
"Ina sonka Auwal!"
Ya nisa cikin wani irin shauki ya ce.
"Ni na san ina yi miki abin da ya fi So
Rumaisa'u".
Babu abin da ya motsa dan jua baya akan
soyayyar da Auwal ke mata, sai ma wani 'karin
tattali da tausayi da yake mata. Ya daura
d'amarar sanin duk wani abu da ake gudunsa ga
sickler, nisali ko a ina yake idan iska ta taso a
wajen sai ya nemi Rumasa'u a waya, idan ta
shiga motarsa sai ya zuge gilasai tsab, sannan
duk wata sabga ta aljihu da zai mata ya juyar su
kaf akan abubuwan da zai taimaki lafiyarta,
dangin kayan sawa masu kauri da rufe jiki,
dogayen riguna, hijabai, ni'kab har da safar 'kafa
da hannu. Haka nan 6angaren abinci mawuyacin
abu ne ya je mata ba tare da wani abinci da zai
amfaneta ba, ko da mafi 'kan'katarsu ne wato
rake.
Tun daga nan hankalin Rumaisa da na iyayenta
ya kwanta, suke ganin lallai ta sami mijin
marainiya, Auwal ya zama dan gida a nan Kano,
Rogo har ma da Abuja kowa a dangin Rumaisa'u.
A nasa dangin ma Rumaisa'u, saboda haka na'am

da girman gidan su Rumasa'u, saboda haka har
sun amince da aurensu.
Auwal ya kasa tarar mahaifansa ya sanar da su
Rumasa'u sickler ce, saboda ta tsorata shi da
yadda iyaye ke kar6ar lamarin dansu ya auri
sickler, sai ya ke shakkar goyan baya daga nasa
iyayen, musamman da yake shi kadai suka haifa,
yadda suke zumudin aurensa ya fahimci yadda
suka dora masa burin tara 'ya'ya saboda haka ya
yi kirmisisi ya 'ki sanar da su, haka ma zuwa
gwajin ya share shi saboda fargabar da ta cika
ransa, alhalin ko me ma suka samo ba zai iya
karya masa gwiwar auren Rumaisa'u ba.
A haka manyansa suka je nemar masa auren
Ruma aka yi duk yan hidimomi bisa al'adunsu aka
sanya musu rana, in ta kammala karatu za'ayi.
*BAYAN SHEKARU BIYU*
Wata biyu ya rage aurensu, wanda za a had'a da
na Hafsat da angonta Sani. Zancen duniya da ba
ya 6uya, sai ga batun cewa, Rumaisa'u sikila ce a
kunnen mahaifan Auwal.
Kwatsam wani dare ya bar wajenta ya koma
gida, ya shiga wajen Innarsa neman ruwan zafi,
mahaifinsa ya yi kiransa fuska babu walwala a
fuskarsa ko kad'an.
Ya nemi guri ya zauna cikin sanyin jiki, mahaifin
nasa ya ce.
"Daga ina haka?"
Sai ya ji tambayar ba wai, saboda babu irinta
tsakaninsa da mahaifin nasa ko da can ma da ba
shi da gurin zuwa ba a fiye tambayar ina ya je da
dare ba ko dan yanayin aikinsa. Amma yau shi
ne ake tuhumarsa inda ya je. Kawai sai ya yi
'kasa da kai, dan bai san abin fad'a ba, yana ji a
cikin ransa nan da wata biyu Baban nasa ba zai
ganshi a wannan lokacin ba ma bare ya tambate
shi.
Mahaifiyarsa ta shigo da fulas har da farantin
kayan shayi ta dire a gabansa, zata fara hada
masa ya yi sauri ya kar6e ta yana godiya. Ta
nemi guri ta zauna, shi kuma jiki a sanyaye ya
fara bude gwangwani yana sauraron mahaifinsa
da ya dora.
"Yaya me jikin?"
Ya dago da sauri ya dubi mahaifinsa hankalinsa a
tashe, amma fuskarsa ta kasa nunawa. Ya
tattare 'kululun da ya taso masa a ma'kogwaro
ya kora shi ta hanyar hamud'ar madarar ya
hadiye sannan ya ce wa mahaifin nasa.
"Abbba ina ka san ba ta da lafiya?"
"Zancen duniya ai ba ya 6uya".
Abban ya fada cikin rashin kulawa tun daga nan

Auwal ya sha jinin jikinsa, kawai sai ya ci gaba
da hidimar gabansa. Abban ya gyara zama ya ce.
"Wato Auwal ka san yarinyar nan sikila ce ba ka
sanar da mu ba, dan kawai ka na son abin da
zaka sanya mu 'karanta?"
Auwal ya dago cikin bugun zuciya ya dubi
mahaifinsa bakinsa na rawa ya ce.
"Abba... Mene ne 'karantar a auren sickler?"
Cikin 6acin rai Abba ya ce.
"Auren sickler ba 'karanta ba ne, kantafi ne kawai
da rayuwar 'ya'ya da ta aljihu... In da 'karantar ta
fito shi ne zuwan da zamu yi mu ce mun
janye..."
Tuni har hawaye ya fara zuba a idon Auwal,
wanda ke kallon mahaifinsa garau da alamun
rashin kwanciyar hankali bare kimtsa maganar da
zuciyarsa ya kamata ta haifa, bakinsa kuma ya
furta hakan ne kuma ya sa Innarsa ta sami
sararin shiga maganar.
"Wannan d'an ka yi wauta in dai ka san cewa
yarinyar nan sickler ce, amma ka juya wa
matsalolinta baya zaka aure ta... Muna zaune
'kalau ka kawo mana sickler dangi..."
A yanzu ya sami ga6ar abin cewa wanda ra'ayin
kansa da na zuciyarsa suka yi tarayya yana
'kokarin tsayar da hawayen ya tare mahaifiyarsa.
'Idan dai zan iya haihuwar da Rumasa'u, to lallai
zan iya haihuwar sickler da wata mai lafiya
wadda ba sickler ba ce..."
Shi ma mahaifinsa da yake zazzafan mutum ne
sai ya tare shi.
"Idan Allah Ya hukunto hakan na tabbatar idan za
ka haifi sickler goma da Rumaisa'u idan wata ce
sai Allah Ya ta'kaita ka haifi hud'u..."
Auwal kawai sai ya yi shiru ya ci gaba da shan
shayin da ya fi kama da shan magani, 'kwalwarsa
ta tsaya cak! Da 'kirkirar mafita ko ta 'kofofin da
duk ransa ya raya masa har ya gama kushe
masa aure da Rumasa'u tsab ya 'karkashe
batunda da haramta aurem.
Auwal dai bai tanka ba, har mahaifin nasa ya
diga aya sannan cikin rashin hayyaci ya tashi ya
fice daga falon.
.
Dan Aunty.GORAN DUMA 8
.
.
Tsawon daren nan ba zai iya dorar da wani abin
kirki da ya yi ko lissafinsa ya yi ba dangane da
yadda zai 6ullowa al'amarin, ya san dai ya gurji
kukan da tsananin 'kauna da tausayin Rumasa'u
ya haifa, kuma su suka hana shi hasala komai

bayan ya 'koshi da ji a ransa duk tsanani ba zai
iya rabuwa da Rumaisa'u ba.
Sai 'karshen dare ya sami runtsawa saboda haka
bai sami sallatar asubahi ba, 'karfe shidda dai-dai
wayar Rumasa'u ta farkar da shi.
Yana ganin sunanta kan wayar sai da 'kwalla ta
taru a idonsa, ya daga yana kokarin gyara
muryarsa saboda daskarewar bacci da kuma ta
ma'ka'kin tausayinta da ya ma'kale maasa a
ma'kogwaro.
"Rumaisa'u" Muryarta tar ta ce "Duk wadannan
gaibu ne Abba, babu wanda ya san abin da gaba
zata haifa, kamar yadda ba mu isa za6ar abin da
muke so mu 'kyale wanda tanmu yake hasashen
hadari cikinsa ba. Da dan Adam na da iko akan
za6in abin da yake so na matar da ta zarce
Rumaisa saboda abin da nake mata ya fi so, shi
yasa ban san ko wacce irin matsala ba a kanta,
amma da yake na san ba dukkan abin da mutum
ke so yake samu ba, tun bayan umarninka na jiya
na kwana ina gwajin yadda zan iya rayuwar da
babu Rumaisa'u. Na yi ta cin karo da gazawa,
har ta fara barazanar keta min zuciya. Ban fitar
da rai zan iya din ko kuma zan kasa ba, na san a
biyu daya ce zata faru, ko in iya d'in in wanzu
bisa tsarin da ka za6a min, ko kuma in gaza ta
dalilin in bijire maka ba, wanda babu irin haka a
tarbiyyar da ka ba ni... Abba kar ka damu da
yadda ka ganni har in mutu in Allah Ya so ba
zaka had'u da abin kuka ta silata ba..."
Yanzu hawaye ya fara cin 'karfinsa, kuma shi ne
ya tilasta shi diga aya ba don ya rasa abin cewa
ba.
Duk jikin mahaifinsa ya yi sanyi, sai kallon Auwal
yake shi ma kamar ya yi hawayen, amma wata
zuciyar na tuna masa siyasar Auwal ta dadin baki
da sadaukarwa har ka yi masa abu ba tare da
kana da niyyarsa ba, wannnan ne yasa ya daure
ya ce.
"Abin har ya yi zafi haka Auwal? Ba zaka iya fitar
da yarinyar nan a ranka cikin ruwan sanyi da
dalilin matsalarta a rayuwarka da ta 'ya'yanka
ba?"
Auwal ya muskuta da murmushin ya'ke alamar
akwai magana fal a cikinsa, sai dai yadda zai
furta ya yi girma, don haka ya hadiye ta kawai ya
bi mahaifinsa da shiru, har mahaifin nasa ya gaji
da jiran cewarsa ya nemi guri ya zauna idonsa
akan Auwal.
"Tun farko ka san Rumasa'u sickler ce?"
Auwal ya kad'a kai, mahaifin nasa ya dora wata
tambayar.

"Wanne mataki ka dauka akan yadda za ku rayu
tare, ko kaucewa yadda za ku haifi 'ya'yan
sicklers?"
Auwal ya jima kafin ya tattaro abin cewa.
"Ta yi 'kokarin hana ni aurenta tun ranar da
muka had'u na dage. Duk matsalolin da ka
lissafo min da bakinta ta lissafo min su, amma
ba su gigita ni yadda suke gigita ku ba... Da ta
ga haka sai ta shawarce ni yin gwaji dan sanin
makomar 'ya'yanmu, na amince a sannan amma
sai na ga gwajin 6atawa kai lokaci ne da tanadar
wa kai fargaba, don na ji a raina ko wane irin
sakamako gwajin zai haifar ba zan iya barinta ba,
saboda haka na ce ta bar maganar gwaji".
Mahaifinsa ya jima cikin shiru yana jiya
maganganunsa, kafin ya yanke hukuncin d ayake
jin shi ne na 'karshe.
"Gaskiya ta yi hange mai kyau saboda haka
shawararta ita ce abin bi. Ka je ka yi gwaji idan
akwai matserar 'ya'yanku sai ku yi aure, idan
kuma babu, to ku dubi girman Allah ku ceci
'ya'yanku ta hanyar ha'kura da juna".
Duk da Auwal ya ji maganar mahaifinsa da kamar
maimaici kawai, ma'ana babu wani sassauci
haka ya cije a ladabce ya gyad'a kai.
"To na gode Abba".
Ya m'ke kuma salin-alin ya fice ya shiga
'kwan'kwasa falon Innarsa.
Auwal bai 6oyewa Rumaisa'u komai ba dangane
da yadda suka yi da mahaifinsa da hujjarsa ta
sanin kukanta nasa ne, kukansa ma nata ne. Tuni
suka yiwa juna wannan al'kawarin na tarayya
akan matsalolinsu dan nemo hanyar araka.
Rumasa'u ta jima ba ta yi magana ba, ba dan
rashin abin cewa ba sai dan saisaita maganar
don gudun kada tayi muni a kunnen Auwal ko
kuma ya zama wani mataki na karyar masa da
gwiwa.
"Kin 'ki cewa komai Rumasa?"
Ya fada bayan ya gaji da jiran cewar tata.
Ta gyara tsaiwarta ta 'kara jingina sosai da
motarsa saboda tana jin jiri. Ta yi murmushin
'karfin hali ta ce.
"Abin da Abba ya yi shi ne ya kamata Auwal, so
ne tun farko ya ke runtse mana ido alhalin wani
dad'in gushi ne kawai a cikin rayuwar aure,
wanda ake 'kulla si domin kammaluwar iyali. Ya
wajaba ne mu samarwa iyalanmu makoma ta
gari, ba ya kamata ba Auwal".
Shi ma ya yi murmushin 'karfin hali bayan ya ji a
ransa kawai 'karfafa masa gwiwa ta ke so ta yi
ba ainihin abin da ke cikin ranta ke nan ba, ya

ce.
"Kamar ke da Abba kuna mantawa ba a yiwa
Allah wayo, ke kanki aya ce Rumasa'u, Innarki da
Abbanki babu sickler ciki, amma suka haife ki..."
Ta tare shi da dariya.
"Ba 'kokarin yin wayo ba ne, 'ko'karin amfani da
hankali ne, wanda Ubangiji Ya hore mu da shi dan
za6ar abin da zai amfane mu da gujewa abin da
zai cutar da mu, abin da ya faru da mu cikin
akasi mun yarda daga Ubangijinmu ne ba tare da
sakacinmu ba, sai mu yi fatan zamowarsa kaffa".
Auwal ya yi zuru kawai yana kallonta sannan ya
nisa ya ce.
"Ban sna me yasa duk cikin lissafinku ba kwa
duba uban yaran da samun su yake 'kila wa 'kala
ba, sa ku kuka himmata sarayar da shi alhalin shi
ne a hannunku. To zan fada miki abin d ana fada
Abba jiya na kwana da 'kokarin lissafa yadda zan
yi rayuwar da babu ke, na ji kamar numfashina
zai yanke daga lissafin kawai ba tare da fitar da
sakamako ba, amma dai ban cire rai daga
rahamar Ubangiji ba, duk za6in da ya yi min ina
fatan rahma da jin 'kanSa a ciki".
Ta zuba masa ido, dauriyarta na kokarin 'karewa.
Kasa gajiya da kalonsa da ta yi ne ya sa ita ma
ta tabbatarwa kanta wa'ka kawai ta ke, amma
tursasa kanta za6ar tsaka-tsakin al'amura, sai
dai kuma ta kasa hana zuciyarta rauni da son
nuna gazawa da ta tsaya kawai ga bayyanawa ta
hanyar 'kura masa ido cikin hawaye.
Haka suka tsaya ita kuka, shi hawaye, har daga
'karshe ya zagaya mota ya shige yana cewa.
"Zo mu je asibitin".
Ta yi saurin duba agogon hannnunta da ya nuna
'karfe sha daya da mintoci sha hud'u. Ta bude
motar ta sunkuya a tausashe ta ce masa.
"Bari na sanar da Hajiya".
Ya yi saurin tare da fadin.
"Rumaisa'u kar ki sanar da kowa matsalarmu fa,
umarni ne da kuma kokarin kwantar da
hankalinku ke da Abba zai kai ni gwaji, ba dan na
yarda da iya raba ni da ke ko ya yi wani abu a
cikin sonki ba. Ya kamata ki ri'ke wannan kada ki
yi 'kokarin raba ni da kanki, son da nake miki
mutuwa ce kawai zata iya raba ni da shi".
Ta sororo cikin sanyin jiki tana kallonsa. Ta
hadiye kwallarta ta ce masa.
"Auwal wai me yasa ka damu da kira mana
mutwa? Ai ba sai ka kirata zaka bayyana min
kana sona ba,.."
Ya tareta cikin kyalkuala dariya.
"Me yasa ba kya so na kirata? In akiranta ne dan

na sna ita ce mai YANKE 'KAUNA, duk yun'kurin
raba mu da kuke ni dai na tabbatar ita kadai ce
zata iya raba ni da son da nake miki. Amma na
san ba ni da karfi ko dabara a cikin aurenki
yadda Ubangiji Ya so haka zai yi".
Ta murza yatsu tana dariya, ita ma ce.
"Shikenan. In Allah Ya so ni da kai mutu ka
raba".
Ba ta jira cewarsa ba ta wuce. Ya bi ta da kira,
ta tsaya ba tare da ta juyo ba, ya dan daga
murya.
"Na fa gaya miki kar ki fad'a".
Sai kawai ta kad'a kai ta wuce tana dariya.
.
Allah sarki soyayya... Sai gobe in shaa Allahu.
Dan AuntyGORAN DUMA ****9
Akwai wani lokaci da Alhaji ya sanya shi kai
ta taronsu na masu cikon sankarar jini
(sickle cell) ya jirata har aka tashi taron. A
hanya sun taho yana faman cikarsa da
batsewa, har ya fashe da cewa.
"Inda za ka san ciwon shifcin gizo ne har a
wata 'kungiya, wai dan tsabar lalacewar
zamani ciwon ake wa 'kungiya, kowa ya san
ba ciwon ne ya dame ku ba, wata hanyar
neman kud'i kawai kuka mayar da ciwon!"
Rumaisa'u ta yi murmushi tana kallon tagar
motar kafin da kyar ta samo abin cewa.
"Yaya Yusha'u kamar yin 'kungiyar zai fi
rashinta amfani. Ni dai nan na 'kara min
imani da godiya ga Allah wanda Ya halicce
mu yadda Ya so ba dan 'kiyayya ba, sai dan
Ya zamo jarrabawa a gare mu. Kawai dai ka
yi mana fatan ya zamo kaffara".
Yusha'u ya yi wani gajeran tsaki, sannan ya
tsuke bakinsa.
Shekararta ta 'karshe a B.U.K, Hafsat ta
kammala N.C.E har ta fara aiki, mahaifanta
sun dawo Abuja da zama. A wannan
shekarar ne ta hadu da gwarzon masoyin
da ta ke jin har duniya ta nad'e ba zata yi
irinsa ba.
Ba wai tana rasa masoya ba tuni, sai
soyayyar ba ta wani nisa sabo rashin goyan
bayanta, ko kuma in sun san matsalarta su
kauce.
Sun hadu a wata laraba ne tana tsaye a bus
stop cikin B.U.K ner site tana jiran motar da
zata kai ta old site, ita kadai ce tsaye a
wajen, sai fama ta ke da ri'kon tafkekiyar
lema (umbrella) a hannu saboda hadarin da
ya fara d'aurewa, zai iya zubar da ruwa

bagatatan, saukar ruwa a jikinta kuwa wani
tushen tashin hankali ne da zai iya motsa
ciwonta.
Dai-dai wannan lokacin AUWAL ya zo
giftawa ta gabanta da motarsa.
Ta bi motar da kallo cikin tunanin yadda
suke kwashe da Mominta a hutun da ya
gabata.
Wani Uziri na son tsaida

2 Comments On GORAN DUMA
avatar
jannat

1 year ago

Reply

08062236094

avatar
jannat

1 year ago

Reply

08062236094

Please Login or Register in order to submit comment